Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ayi ayau sai ya nemo inda asmau take don kuwa wallahi bazai yiwu ace ya yi rashin ɗan sa ba


Don kuwa ya san indai suka shiga court ɗin nan da badia sannan suka ci case ɗin dole ne ace ya bata ɗan in kuwa ya bata shi ya zaiyi da rayuwarsa





Miƙewar nan da zai yi sai jiri ya kwashe shi ya faɗi ƙasa a sume, a guje akayi kansa inda mummy kuma ta fashe da kuka



Ruwa aka kawo aka yayyafa masa nan da nan ya farfaɗo jikin sa kamar garwashi saboda zafi


Yana farfaɗowa kuka ya saki ya riƙe hannun mahaifin sa

"daddy don Allah kar ka bari su raba ni da ɗana, ƙila shi kaɗai ne ɗan da zan so a duniyar nan don Allah daddy a nemo min asmau ta bani ɗana a maidawa badia ɗan ta saboda ta barshi a gidan nan"


Ko wa a wurin sai da hankalin sa ya tashi, isma'il ne ran shi ya ɓaci ya fara magana


"wallahi yarinyar nan idan na sake na ganta Allah ko su badia basu kai ta kotu ba ni sai na sa an hora ta wane irin abune wannan"


Lefi suka dinga ɗaurawa asmaun bayan sam basu san gaskiya suna ta ƙoƙarin cusa wa daddy magana saboda ya ji haushin yarinyar, da fannah ta ga haka sai kawai tace


"nasan inda asmau take"


Gabaɗaya kowa ya waigo gareta har da daddyn

"tana ina, suka haɗa baki"


Nan da nan fannah ta kwashe inda asmau take ta faɗa musu amma sam bata faɗi dalilin zuwan asmau gidan ba


Sabit shine a gaba ya fice domin tafiya, daddy ne ya tsai da shi

"kai baka da lfy yi zaman ka nida isma'il da ita fannah zamu je mu dawo da ita" inji daddy



"ka kira badia a waya su zo nan za a kashe maganar kafin aje court a kashe maganar a gida"


Amsawa sabit yayi ya ɗauko wayar sa yana neman number badia wacce tunda abin ya faru ta koma gidan su


Bayan ya samu badia ya faɗa mata ne ya zauna amma ba don ransa ba ya so ace yaje wallahi da sai asmau ta gane bata da wayo



Ina kwance sai jin muryar anty fannah nayi a kaina

"ki fito da daddy muke"


Rasa abinda zanyi nayi na ɗauka na ja mata kunne ashe sam bata ji

"asmau ki tashi mana na ce miki da daddy muke"


Miƙewa nayi jiki na a sanyaye, na fito na same shi yana zaune a falon gidan da isma'il da kuma wan anty fannah


Ina fitowa na gaishe su, daddy da fara'ar sa yace min

"me yaji munzo mai da ke ɗakinki maza ɗauko kayanki mu tafi"


Bazan iya masa musu ba na shiga ɗakin, anty fannah ce ta ɗauko min annur inda ni kuma na kwaso kayana muka fito


A mota ba wanda yace min komai sai ma ɗana dana karɓa daga hannun anty fannah na rungume shi duk da ƙaton cikin da ke jikina





Da sallama muka shiga babban falon gidan wanda yake cike da mutanen gidan harda mutan gidan su badia


Tana ganina ta yo kaina da zagi wai in bata ɗan ta


Daddy ne ya dakatar da ita inda yace duk a zauna a tattauna me yasa na ɗauke annur ɗin


Sai dana zauna sannan daddy ya buƙaci ai masa bayanin abin da ke faruwa, sabit ne ya wangale baki yai masa bayanin, yadda aka samu annur


Ba daddy ba hatta ƴan uwan sabit sai da suka jinjina maganar nan, daddy kuwa faɗa ya dinga yi yana ƙarawa sai da yai wa sabit wanki babban bargo sannan daga baya yace

"sabit wai duk bokon ne ya saka haka ko menene, dashe ka sa akayi wa matar ka saboda ɗayar matar taka ta cire mahaifar ta"



Rufe ido daddy yayi ya zage tas shi da badia bayan ya gama sannan kuma ya ɗaura da nasiha akan abinda muka aikata gabaɗayan mu haramun ne


Ko da kuwa dukan su matan ka ne bw hallata a ɗauki ƙwan ɗaya a saka wa ɗayar ba haram ne wannan


Duk wani abu daya danganci dashw na ciki indai akwai mutun na uku daya shigo cikin abun ko da kuwa ko wane kusanci ne tsakanin su to ya haramta


Faɗa sosai daddy yayi musu duk sai suka rasa bakin magana


"ai asmau tana gaskiya ɗa ɗan ta ne babu wata badia, tai wahalar ɗaukar ciki ta sha naƙuda yanzu kuzo kuce wani ɗan badia tayaya akayi ɗan ya zama nata, to ku sani wallahi daga yanzu na gama case ɗin nan asmau ki ɗauki ɗan ki zan ga wanda zai kuma kawo maganar annur anan, kai in banda ma kai sha sha sha namijin kawai ka ɗauki ƙwan matar ka ka dasawa wata idan ɗan ya girma kace masa wacce ce uwar sa, wacce ta ɗau cikin sa ko wacce yake da jinin ta"


Dukkan su jikin su ne yayi sanyi in banda badia wacce tace

"wallahi sai kotu ta ƙwatar min ɗana" ta faɗa tana kuka


"ai dole ne ɗa jinin ki ne duk inda aka je akai gwajin jini jinin ki za agani don haka ban ga dalilin da zai sa ace don mace bata da mahaifa ba ace kuma sam bazata
mallaki ɗan kanta ba" inji maman su





Gyara zama daddy ya yi ya fahimtar da mmn badia sharia akan duk wacce ta ɗau cikin ɗan adam ta kawo shi duniya itace mahaifiyar sa amma sam matar nan bata yadda fuuuuu haka ta ja badia suka fice


Sabit wanda jikin sa yai sanyi ya ƙaraso kusa da ni zai ɗau annur daka masa harara nayi na miƙe tare da daukar ɗana na fice



Babu wanda ya bashi gaskiya kowa sai rashin gaskiya yai ta bashi,


Ɗakin na da ke part ɗin mummy nan na koma na kwanta, sabit ne dai ya kuna shigowa,


" Na fahimci har yanzu taurin kan ki na nan, kina gani idan munje court gobe zasu baki annur ni ne dai uban annur kuma nace baza ki renar min ɗa ba"


"kai ma ai bamu fara da kai ba, idan an gama case ɗin annur a court ɗin dole ne ka bani takarda ta don kuwa na gama aure da kai"


"zan ga wanda ya isa ya sani sakin ki" ya faɗa a fusace

"wannan kuma in munje court ɗin na gabatar wa da alƙali buƙatata idan ya saka ka sake ni kace kai baka yadda ba"


Haushi ne ya kama shi sosai ya fice daga ɗakin ko ganin annur ɗin ma be yi, nima na bi ƙofar da mukulli sannan na kwanta sai da safe Allah ya kaimu court ɗin inga in za abata ɗan bayan bata san komai nashi ba





*******************


Kashegari da wuri na tashi na shirya ɗana don zuwa court duk da dai yanzu sam hankalina ba a kwance yake ba ga ciki amma hakan be hanani gyara fuskata ba


Mummy ce ta shigo wai daddy na kirana

Hijab ɗina na ɗauka na same shi a falo yana zaune, har ƙasa na durƙusa na gaishe shi ya amsa min sannan ya kuma kwantar min da hankali na


"nayi wa lawyer na magana shine zai kare ki koda kuwa jinin badia ne wannan yaron. Amtsayinki na wacce kika ɗau ɗawainiyar yaron nan sharia ta baki naki ne ko ina suka je ke kika haife shi ɗanki ne"


Hankali na ya kuma kwanciya, anty fannah ce ta shigo itama taci laffayar ta,


"daddy nima dani za aje, don kuwa nima shaida ce, kuma ina kamun ƙafa idan an gama case ɗinnan ni zan karɓe shi ko asmau" gyaɗa mata kai kawai nayi amma wallahi bazan iya bawa kowa ɗana ba


"to ai shike nan wannan ɗan ƙaramin case ne nasan ayau za a gama shi ma idan kun shirya sai ku fito"


Mummy har gabana ta zo nasiha tai min sosai wallahi har jikina yai sanyi, akan kar in sake in bari a ja shariar da tsaho don mafi akasari idan ana faɗa akan ƴaƴa to wallahi su take shafa


Gabana ne ya faɗi na ƙara matse abina a jikina in shaa Allah yau za a gama case ɗin tunda dai ƙiri ƙiri ga yadda abin yake



********************


Badia ce da mmn ta sai lawyern da suka ɗauko a zaune duk abin duniya ya ishe su,

"gaskiya hjy kamar yadda na faɗa miki duk inda aka je indak ƙasar nan ne baza a taɓa badia ɗan nan ba tun da dai a ƙundin tsarin mulki na ƙasar nan wacce ta kawo ɗa duniya itace uwa"


Kuka badia ta saki

" wallahi ƙwai na ne fa, ya za ayi in ɗau ƙwai na in bawa wata ƴar iska ita in banda rashin godiyar Allah ma gawani ɗan iskan ciki nan a jikin amma kuma bata godewa Allah ba sai ƙwaya ɗayan nan shine zata ce sai ta raba ni da shi, mummy don Allah ya zamu yi wallahi zan iya rasa rai na idan aka ƙwace min annur"


"yi shiru yi shiru inji mummy yanzu kai barister ya kake ganin za ayi"



Shiru yayi can sai ya e

"to akwai mafita amma sai in me gidan ya yadda da hakan" nan da nan ya tsara musu yadda za ayi


Ba musu suka yadda nan da nan badia ta kira waya lagos ta faɗa wa dr. ɗin nan da tayi dashe akan ta bar asibitin na ɗan wani lkc kuma ta kashe wayar ta



Shi ma sabit ta kiɗa shi ta faɗa masa shawarar da barister ya yanke, nan da nan ba tare da wani shawara ba yace ya yadda duk yadda suke so hakan za ayi


********************



*COURT*


Sai da aka gabatar da case 4 sannan aka kira su, inda magatarda ya gabatar da case ɗin su, aka kirawo badia da asmau kowacce ta gabatar da kanta


Alƙali ya nemi badia tai bayanin abinda ya faru

"asmau kishiyata ce, kusan a tare Allah ya azirta mu da samun ciki, amma ta riga ni haihuwa inda ita ɗanta be zo da rai ba, ni kuma nawa yazo da shi, kuma shine wannan na hannun natan


To kasancewar ban da ruwan nono sai mijin mu yace asmau ta dinga bawa ɗana nono, shine yanzu ta ɗauke min shi ta gudu da shi wai nata ne"



Sakin baki kawai su anty fannah sukai suna kallon ikon Allah, sai da alƙalin ya gama rubuce rubucen sa sannan ya tambayi asmau ita kuma ta faɗi me ya faru


Nan da nan na zayyano duk yadda akayi na samu cikin annur, kowa a court ɗin sai ya ɗau salati aka fara ƴan ƙananan surutai


Sai da alƙalin ya doka ƴar gudumar sa sannan akai shiru,


"ina me gidan nakun"alƙali ya tambaya


Nan da nan aka taso ƙeyar sabit ya fito, alƙalin ya tambayi cikin mu wake faɗar gaskiya, mutumin nan be ji kunyar Allah ba sai buɗar bakin sa yace


" badia ce take faɗar gaskiya"


Hmmm sabit in bakai haka ba ai baka cika ɗan halak ba

"to malama asmau kinji abinda mijinku yace ko ke kina da taki shaidar"

Gyaɗa kaina nayi sannan ya bani damar faɗar menene nan nace masa dr. ɗin da tayi min dashen kasancewar bata nan ya sa aka ɗaga ƙarar har sai dr. ɗin tazo da kanta



Daga nan sati biyu akan mu zo da dr. ɗin, aka sallame mu bayan alƙalin ya ja min kunne akan kar ya sake naji na bar gidan balle in tafi da ɗan




*******************


Tun a mota daddy yake faɗa akan abinda sabit yayi, yana komawa gida ya faɗawa mummy ita ma sam bata ji daɗin hakan ba


Daddy ya tambaye ni number dr. ɗin don a kira ta a faɗa mata abinda alƙalin yace


Tooo nan fa ake yi don gabaɗaya ban san komai na dr. ba ni ko sunan asibitin ban sani ba, don inda akai min dashen daban inda kuma muke zuwa nan ma daban ne


Babu yadda zasu yi dole ne aka nemo sabit don ya faɗi a ina za a samu, abin takaici wai sai sabit yace shi ma be sani ba wai badia ce ta san ta


Haka daddy ya zaunar da sabit yai mai masa nasiha, tunda ya ga faɗan ma sam baya shiga, amma ƙiri ƙiri sabit yace shi be san zance ba



Daddy ya rasa yadda zai yi da sha'anin mu, don yasan ko ana ha maza ha mata badia baza ta taɓa faɗar address ɗin dr. ɗin ba balle ayi contacting ɗin ta


Zaunar dani yayi yai ta min nasiha, sannan yace min in Allah yayi annur zan rayu a matsayin ɗana too in kuwa Allah yayi kotu zata bawa badia to a matsayi na na uwar sa ba abinda zai so daga gareni face in kasance ina masa addu amma shi sam baya son ai ta ja'inja akan yaron don kar abin yai affecting ɗin sa


Tabbas maganar daddy haka ne amma kuma in shaa Allah addua zan dage da ita kan Allah ya bayyana mana da dr ɗin nan
[7:15PM, 5/4/2018] ‪+234 806 779 9926‬: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




*HIKIMA WRITERS ASSO.*




P⃗a⃗g⃗e⃗ 24 🌹





Renon ciki na nake yi hankali na a kwance ga ɗana a kusa dani, sam su sabit basu tafi da shi ba nima na so hakan



Duk wani siyayya mummy tayi haihuwar kawai muke jira, amma saɓanin saɓanin cikin annur wannan cikin girma gare shi sosai da sosai


Har anty fannah tana cewa ko dai ƴan biyu ne, ko da muka je scanning twins ɗin ne kuwa


Muna dawo wa anty fannah ta faɗawa mummy, bashiri mummy ta kwashi anty suka tafi kasuwa aka sake sabuwar siyayya



Cikina yana da wata 8mths sabit suka dawo shida badia, sam duk wannan abunda ake yi badia bata san da cikin ba



Tun da suka zo bamu haɗu da sabit ba, dana ji alamar zai shigo sai in gudu ɗaki duk wannan abun Allah bai taɓa haɗa mu da shi ba



Kwanan su uku da dawo wa ya badia ta zo da kanta lkcn ina ɗaki ina bacci ta ɗauke annur, ita kanta badiar bata san da cikin ba


Ko da na tashi, sai ban ganshi ba, sai na tambayi mummy yana ina sai mummy tace min ai badia ce ta ɗauke shi


Ba badiar ba hatta mummyn ta bani haushi yadda har ta bar badia ɗaukar sa bayan tasan ƙyuya gare shi



"mummy bari inje in ɗauko shi kin san halin annur idan ya tashi be ganni ba"


"to shike nan ni sai da na hanata sai tace wai sabit ne yace ta ɗauke shi"


Ficewa nayi daga part ɗin na doshi part ɗin sabit da tsohon ciki na, a hankali nake tafiya don kuwa cikin yai girma dayawa fiye dana annur


Tun kafin in ƙarasa ciki nake jin kukan yaron nan yana kira na, sai na ƙara ɗaga ƙafa, da sallamat na shiga tana zaune akan kujera tana kallo shi kuma yana zaune a ƙasa a kusa da ƙafar ta yana kuka



Sallamata ce ta sata juyowa, ai kuwa ta ci karo da ƙaton cikina, wani ashar ta daddage ta ɗura sannan ta ƙaraso inda na ke kamar wacce zata dake ni


"uban waye ya miki cikin nan"

Kallon ta na tsaya ina yi yadda take huci kamar zaki, sai nishi take yi kamar wacce take shirin yin dambe


"tambayar ki nayi uban waye yayi miki cikin nan" ban kula ta ba saboda tsayawa ma kula ta ɓata lkc ne ai ta san zaman aure nake yi


Wuce ta nayi na ƙarasa kusa da annur zan ɗauko shi, ji nayi ta jawo ni sai saukar mari naji a fuskar ta, kammm bata ajiye ba nima na kai mata bama ɗaya nayi mata biyu


Sannan nace mata

"kina san ki san wanda yai ciki tooo mijina ne, kafin wannan ma na taɓa ɓari, kafin in haifi annur banza kawai wacce bata san inda yake mata ciwo ba"


Ban ankara ba kawai sai jin matar nan ta hau ni da kokawa tana ihu tana kuruwar

"ƙarya kike yi me sabit zai yi da ke" faɗa sosai mukai da ita


Kasancewar cikin da ke jikina yai min nauyi ya sata samun galaba akai na hai ta kaini ƙasa ta shaƙe ni tare da cewa


"wallahi duk macen da tace zata haihu da sabit sai na kashe ki na kashe abinda ke cikin naki inga abinda za ai min tunda ba wani gata gare ki"



Duka ni kuma na dinga mata inda tana ta ƙoƙarin haye min ruwan ciki Allah ya jeho anty fannah, da saurin ta ta zo ta hankaɗe badiar daga kaina



Tafiya tayi taje ta daki bango wanda har sai da kanta yai ciwo amma sam bata daddara ba kafin anty fannah ta ɗago ni tuni ta yo kaina



Wannan karon da ƙarfi anty fannah ta hankaɗa ta sai kuwa ta faɗa kan annur inajin yaro na ya ƙwalla wata irin ƙara, hankali na ne ya tashi na miƙe da ƙyar na yi wajen sa amma anty fannah ta hanani ta janye ni muka bar part ɗin


Hankalina sam ba a jikina yake ba naso in san me ya samu yaro na amma anty fannah ta hanani



Part ɗin mummy muka nufa anty fannah tana bata lbrin yadda ta ganmu ni kuma ina ce mata annur fa yaji ciwo


"ai dole sabit ya san wannan rashin hankalim da matar sa tayi" inji mummy


"Baki ciwo ba ko" girgiza kaina nayi,

"amma mummy annur kamar ya ji ciwo faaa"

"ina ruwanki da wani annur duk kin bi kin ɗaga hankalin ki akan yaro bayan uwar sa ba sanki take ba"


Kuka na saka musu ni kaɗai na san abinda yake damuna akan irin abinda sabit yake min gaskiya na kai matuƙar ƙarshe a haƙuri



Ganin ina kuka yasa mummy tace min in daina sanna in shiga ɗaki na in kwanta in huta tunda ba abinda ya same ni ita kuma badiar bari sabit ɗin ya dawo za ta ja masa kunne ya faɗawa matar sa ta fita hanya ta



Anty fannah ce ta taimaka min duk da bana jin komai har ɗakin nawa, ban daina de kuka ba, abin ya min ciwo, anty fannah ce ta zauna kusa da ni tana bani haƙuri


"wallahi anty fannah haƙuri na ya ƙare na zo ƙarshe wallahi sai na nuna wa duniya wacece mahaifiyar annur"


"ban gane ba"


Nan da nan na hau mata bayanin yadda aka samu annur, sai da naga tas sannan ta hau ni da faɗa wai nayi wauta ai duk inda muka je bani da gaskiya, tunda ga yadda aka haife shi har kuɗi na karɓa


Kuka na dinga mata ni dai a gaskiya ɗana nake so a hannuna, kukan da nake mata ne ya sa jikin ta yin sanyi, kuka wiwi haka na dinga mata



"yanzu asmau ya kike son in miki"


"ni wallahi in ba barin gidan nan nayi ba wallahi zan iya mutuwa don na gaji da matsalar gidan nan" kuka na dinga mata



Kasancewar tana sanyi ya sa ita ma ta saki kuka, muka haɗa kai muka dinga kukan,


"don Allah anty fannah ki taimaka min"


Kuka ne ya kuma ƙwace mata, mu kai me isar mu muka lallashi sannan ta hau ni da nasiha, ita dama anty fannah haka take sam bata da zafi bata taɓa ce min rama ba



"asmau wannan matsalar ke kika jefa kanki a ciki don haka ki cire annur a ranki ki mai da hankalin ki akan wannan Allah ya raba lfy"


"anty annur ɗana ne don me zaki ce in ƙyale shi"


"ba wai nace ki ƙyale shi har abada ba, amma 4 now ki ƙyale shi"


"wallahi anty na gaji da zaman gidan nan, don Allah ko wani gurin ne ki kai ni in huta in samu in sauka lfy kafin in haihu"


"in banda abin asmau ina kika taɓa jin gidan miji yai zafi, komai aka yi miki haƙuri zakiyi, kuma in shaa Allah wataran zai zama tarihi, dukkan me haƙuri wataran dole ya ga amfanin hakurin"


Kuka na dinga yi tana bani haƙuri tare da cewa ita ba inda zani kawai in zauna in shaa Allah akwai ranar ƙin dillanci, amma don Allah sai yaushe ne zan ga wannan lkcn Lallashi na ta dinga yi tun ina kuka har na zo na haƙura amma wallahi daga yanzu bazan kuma ɗaukar cin kashin shi ba



Sai da ta tabbatar na haƙura na kwanta sannan ta tafi, kuka na kuma fashewa shike nan ni ke nan a haka zan ƙare banni da wanda zai kare min ya Allah ka kawo min ɗauki, bacci ne ya kwashe ni




********************



Sabit yana wajen abokan sa yaji call ɗin badia tana kuka wai ya zo yaga asmau da fannah sun haɗa su ita da annur sun musu duka


A guje ya garzayo ya zo ya tarar da su cikin jini, shi ma kanshi annur ɗin ya kuje a goshin sa




Ita kuma ta ciwo a ƙafar ta yana ta jini, tana ganin shi ta fashe masa da kuka


"sabit kaga abinda asmau tai min, wai don kawai na ganta da ciki na tambayeta na waye shi ne tace nata ne wai zuwa tayi ta kashe mu ni da annur tunda yanzu ta kusa haihuwa bata son ƴaƴan ta su samu ɗan uba"


Sam sabit be fahimci abinda badia take cewa ba shidai kawai kallon annur yake wanda yake kwance a yashe goshi na ta jini


Ɗaukar shi yayi ya shiga da shi toilet ya wanke masa sannan ya fito da shi ya gyara masa ciwon ya saka masa plaster sannan ya ajiye shi


Itama badiar first aid box ɗin ya ɗauko ya gyara mata ciwon nata wanda daga gani wuƙa ce ta yanke da ita


Takaici ne ya hana sabit magana, yana gama gyara su ya shirya su sai da ya tabbatar sun kimtsu sannan ya fito daga part ɗin nasan directly part ɗin mummy ya taho a fusace





Ina kwance kawai naji an janyo ni daga kan gadon na faɗo ƙasa sannan ya shaƙe min wuya tare da miƙar da ni sama sannan sauke min yatsun sa guda biyar a kan fuska ta



Tuni na watstsake na ware ina kallon sa

"sabida baki da mutunci har ki shiga part ɗina ki yi mata ta illa sannan ki cutar min da ɗa........


Be gama ba sai ga mummy ta shigo


"wallahi ko ka sake ta ko in ɓata maka rai"




Wancakar da ni yayi ya fice in da mummy ta ɗago ni sannan tace min

" kiyi haƙuri komai me wucewa ne"

Wucewa wallahi an gama da ni haƙuri

Please Login or Register in order to submit comment