Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nam ne ya juyar miki da ƙwaƙwalwa, naga duk kin rikice kin zama wata ba asmaun da na sani ba"


"wallahi anty fannah nice hankali kawai nayi, kuma nasan ciwon kaina wanda yayi sanadiyyar rasa baby na innace na barshi haka ai banyi ba wallahi sai na ƙun sa masa abinda har abada bazai taɓa mantawa ba amma sai da taimakon ki sai na haifa masa baƙaƙen ƴaƴa iya son raina, goma ma zan haifa masa ko sha biyar"



Tabbas asmau ta zauce inji fannah, zaman dirshen nayi a gaban ta ina ta lissafo mata irin plan ɗin dana ɗauka zan aiwatar akan sabit da matar sa wallahi sai sun san shayi ruwa ne


Tun tana basarwa har tazo ta fara bani tips na mallakar miji a hannun na ada in tana faɗa min yana shiga ne ta kunnen hagu yana fita ta kunnen dama


Amma yanzu tsab nake haddace wa ai yanzu za a fara wasan ada ba komai akayi ba, amma yanzu wasan zai fara


Sai yamma na kama hanyar part ɗin mu abinci na naje na dafa lafiyayye na zuba a cooler na ajiye, na shiga ɗaki na ɗau wanka na sai da na turare jikina da turare na daƙƙo wata fitted gown da mukai da anty fannah na saka



Falo na fito ashe ita uwar gidan ta dawo ma abanji dawowar ta ba, cooler dana ajiye akan dinning table ta buɗe ɗan wake ta ci karo da shi da mai da yaji sai kunun tsamiya


Wani shegen kallo ta bini da shi

"bana cin wannan ki sake ɗaura min wani"

"ai ba naki bane nawa ne, ai na dena yi wa kowa girki duk wanda ya ji yunwa ya shiga kitchen muga in zai iya"


Hannu ta ɗaga zata kwaɗa min mari a dai dai lkcn sabit ya shigo


"ke badia me ya haɗa ku zaki mare ta"


" *SD* wannan yarinyar wai me take taƙama da shi ne, gaskiya na fara gajiya da zama da ita ya kamata a sallame ta"


Juyowa yayi zai min faɗan da yasa wani ƙayataccen murmushi na sakar masa tare da kaɗa masa ido cikin kissa



Tuni ya maida wuƙar tasan sannan yai gyaran murya


"me tayi miki ne da zaki dake ta, bana son hayaniya"


"ni dai kawai na gaji da ganinta" in da inda ya fara ya rasa kalma ɗaya ma da zai ce sai wani kame kame yake



Dining na nufa n zauna na fara cin abinci na ina jinta tama jarabar wai ban kai wannan matsayin ba tana ƙara yi wa sabit maganar ya kore ni ko ita ta barmana gidan


Lallaɓa ta yayi ya hau sama inda ni kuma na zauna ina ta cin abincina, nai mamakin da ya gama kintsawa ya sauko ya ci ɗanwaken


Ita kuma badia tana nan kan bakan ta bazata ci ɗan wake ba sai dai in dafa mata wani abun, iskar da ta ɗauko ta ma ban kalla ba balle ita sabit ɗin ma nai mamaki dana ga sam be ce komai ba
[8:22PM, 5/1/2018] ‪+234 806 779 9926‬: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 21🌹







Tun daga lkcn na zame musu ciwon ido sai haƙuri sai abinda na ga dama nake yi a falon sam sabit sai yayi wani sanyi ashe abun nashi ma iskanci ne



Tuni na ajiye girkin sai abinda naga dama nake dafawa wank lkcn badia taci wani lkcn kuma tace ita bata so kuma wallahi ruwa bana bata balle in ɗaura mata wani abu



Tuni na ƙwatar wa ƴanci sam yanzu sabit baya min abun da yake min ada kamar ma shakka ta yake yi ko ince tsoron badia tasan akwai abinda yake shiga tsakanin mu yake oho mishi



Lallaɓawa kuwa sai dai in be shigo ɗakina ba yai ta lallaɓa ni yana min wani daɗin bakin wai in kwantar da hankalina zai sanar da badia cewar ya mai da ni matar sa official



Hmmm kawai nake bin sa da shi besan ni da nawa ƙudurin a raina ba, abu kaɗan idan tayi sai in fara "ke kin san meke faruwa a gidan nan in ƙafa ta ɗauke kuwa, kina can kin saki baki kina bacci kamar mushe" 🤣🤣🤣🤣🤣



A lkcn zaku ga rawar ƙafar sabit nan da nan sai ya janye ta yai ɗaki da ita sam bazai bari mu ƙarasa faɗan ba, da gayya nake tsokanar faɗa, ko shi ma gogan yana zaune yana kallo sai inzo in canja channel ɗin kuma in ajiye remote ɗin inyi gaba sam bazai taɓa ce min ko mai



Duk wata hanyar dana san zan bi in takalo sabit faɗa muyi don in tona masa asirin shiga ɗakina da yake yi nayi amma sam ba nasara



Daga ƙarshe na tattarar na watsar na ci gaba target ɗina na neman ciki ido rufe abu kamar me ba ciki ba alamar sa, har wurin anty fannah naje ta bani maganin da take sha amma shiru, lallai ma kodai sabit yana yin wani abu ne a nashi ɓangaren sam ban sani ba amma ciki de ina nan ko ba daɗe ko ba jima sai nayi shi




********************



Wani project ne aka tura sabit lagos zai je yayi na shekara uku, sam ban so ba saboda ba lallai bane ya tafi da mu ba tunda ina lagos ina abuja ai ba wani nisa bane kuma ba lallai ne mummy ta barshi ya tafi da mu ba amma gaskiya ni ina son bin sa don haka ko daya dawo ɗakina da daddare ranar na kai shi makka da madina a ƙafa da haɗine na karɓo na musammam a wajen anty fannah na sha



Muna kwance yana min wasa da gashi na sai nace masa


"sabit kai da wa zaku koma lagos ɗin"


"kina son zuwa ne, kinga yarinyar nan ƴaɗ ƙaramar ki da ke amma baki son rabuwa da mijinki ko, shike nan zan wa mummy magana sai mu koma tare kin ga sai muci karen mu babu babbaka tunda badia baza ta ba"


"cewa zaka yi ka daina bin dare de kana lalube" mintsini ya mannara min au lalube ma nake yi



Wasa mukai da sabit sosai kafin mu kwanta bacci,



Ko da lkcn tafiyar yayi badia taji da ni za a wai don in dinga yi masa girki sai hankalinta ya tashi, itama sai taje



Sam sabit be so badia tace zata ba amma babu yadda ya iya har wani nuna jin daɗin sa yayi wai zamuje tare hmmm ni dai kallo shine nawa



Shirye shiryen komawar mu lagos ya kankama inda sabit ne ya karɓo wa badia transfer na wajen aiki, sannan muka kama hanyae birnin yanki



Mun sauka lagos lfy gidan flat ne me 4bedroom a apapa kowccen mu ta ɗau ɗaya inda sabit ya ɗau master bedroom ɗin



Zaman mu lfy sam bana shiga sabgar su haka suna basa shiga tawa girki ne inna yi in badia na da ra'ayi taci in bata da ra'ayi kuma sai ta siyo nata ba wanda yake shigar sabgae wani tsakani na da ita



Rannan da daddare sai sabit yace badia ta shirya su fita, ina kallom su aka ci kwalliya har tana cewa


" *SD* dinner zaka kaini restuarant" sam be tanka mata ba suka fice, ni kaɗai ma ci dinner ta ranar kuma sam abin ma be dame ni ba saboda ni akwai zaman da nake yi kuma wallahi ko baɗe ko ba jima sai na cimma buri na



Kusan awan su guda a waje sai gasu sun dawo, fuskar sabit kamar wacce aka aiko wa da mala'ikan mutuwa tai jajawur kamar bashi ba



Inda ita kuma badia ita ma tata fuskar sharkaf da hawaye



"wallahi bazata saɓu ba lallai ma badiar nan wallahi bazan yadda ba"


"don Allah sabit kayi haƙuri wallahi bada son raina banr naga jikina ne yake attracting ɗinka zuwa gare ni kuma idan haihu nayi loosing shape ba lallai ne ka so ni ba shiya sa na cire mahaifar" 😱😱😱


Wai kunne na ne yajiye min ko kuma mafarki nake yi


"wannan ma maganar banza ce kice min wai kin cire mahaifar ki akan wani banzan excuse naki, ni da naƙe expecting ƴaƴa na daga gare ki amma shime kika cire mahaifar ki"



Faɗa ya shiga yi sosai ni dai dana ga abin nasu ba na ƙare bane sai na ahige ɗakina amma gaskiya badia tayi kuskuren cire mahaifa



Wallahi akan wani ƙato bazan cire mahaifata ba, har kusan 11 :30 na dard suna bala'i akan cire mahaifar


Ni dai bacci na nayi na ƙyale su, ko da na tashi da safe ma atmosphere ɗin gidan ba daɗi tunda dai masu gidan suna faɗa



Haka dai akai ta zama ba daɗi don ɗan zuwa ɗakina ma sam ya daina ni ma ta shafe ni, duk ya bi ya tsangwami kansa



Allah ya ƙara shine kawai abinda yake fita daga bakina, da ka barmin cikina da tuni na haife shi amma gashi yanzu inda ya kai kansa Allah ya ƙara ai yanzu bashi da wani mafita sai dai ta haihuwa da ni



********************


Sabit yana zaune duk abin duniya ya ishe shi, yanzu ya zaiyi shi fara neman matar ma da zai aura ta haifa masa fararen ƴaƴa shine aiki


Yawancin matan yanzu ba farara bane farin kanti ne, kuma baya son kawo fara kamar badia ya ƙara ƙarawa kansa aiki, inda ace zai samu fara kamar asmau wallahi da ba abinda zai dame shi amma yanzu ga shi nan ya zama shi ba ga tsunstu ba baga tarko ba



Har yanzu bashi da ra'ayin haihuwa da asmau kai sam ma bazai taɓa yadda ya haihu da itaba, shiyasa ya bata turaren da take amfani da shi


Daga china ya taho da shi muddin mutun zai juri saka shi to har abada bazai taɓa bari asmau ta haihu da shi ba, turare ne kamar kowanne amma ƙamshin same illa ne, ƙamshin sa yana lalata ƙwan haihuwa



Buɗewar ƙofa yaji yasan ba me shigo masa ɗaki sai badia don haka sai ya haɗe rai sannan yace


"me ya kawo ki" ko kallon inda take be yi ba


" *SD* na zo ne muyi magana, wallahi ban cire mahaifa ta ba har sai da san zamu samu solution"

Jin kalmar solution ɗinne ya sashi juyowa tare da tsare ta da idon sa


Ganin ya kalle ta ya sa ta ƙaraso qa har da riƙe masa hannun sa

" *SD* me zai hana mu samo surrogate mother, wacce zata haife mana ƴaƴan mu da ƙwai na da sperm ɗin ka kaga shike nan, ni ban yi loosing shape ɗina ba, kuma ga ƴaƴan mu"



Zame hannun sa yayi daga nata


"kina nufin mu nemi wata arniya ta renar mana ɗa a cikin ta sannan ta haifa mana shi sam baza ayi haka da ni ba"


"ba arniya ba, ga asmau ai an ɗaura muku aure ba sai muyi amfani da ita ba, ba hankali gareta ba sam ba ganewa zatai ba"


Shiru yayi yana tunani tabbas wannan shine hanyar sa kawai ta samun fararen yaran da yake so wato kenan ƙaddarar sa ce sai asmau ta haifa masa ƴaƴan sa kenan ko


"to kije kiyi mata maganaa inta yadda shi kenan in kuma bata yadda ba wallahi sai na ƙara auren wacce zata haifa min ƴaƴa"


"zama ta yadda" ta faɗa da murnar ta tana miƙewa



Ina kwance a ɗaki ima ta shiɗin kwanciya sai badia ta shigo nai mamakin ganin ta amma kuma sai na dake tunda take bata taɓa shigo min ɗaki ba nasan akwai abinda ya kawo ta



stool na bata ta zauna, sannan sai tace min

"asmaj kamar yadda kika sani na cire mahaifa ta saboda wallahi ni bana son haihuwa, amma kuma sabit yana so don haka sai muka yanke hukunci sabit zamu dasa miki cikin a jikin ki in ya so sai ki haife mana shi"


"ban gane ba " nace mata


"za a saka miki ƙwai na da sperm ɗin sabit a cikin ki sai ki haife mana"


"kina gani sabit zai yadda da hakan" na tambaye ta

"ƙwarai kuwa da sabit muka tattauna shi yace ma in miki maganar" takaicine yazo min har maƙogwaro na wani abu ya tokare min wato sabit jini nane baya so ko wai sai yaushe zan samu ƴanci ne sai yaushe zan samu cikar buri na



Kallon ta nayi cike da tsana sannan nace mata

"kije ki gaya masa ciki na bazai ɗauki renon sa ba don haka yaje ya samu wacce zai biya kuyi abunku amma wallahi ni asmau bazan yadda ayi wannan abun da ni ba"



Kuka na fashe da shi na takaici lallai sabit ashe abin nashi har ya kai haka wallahi bazan renar masa ɗa ba


Kukan da taga ina yi ne ya sata miƙewa sannan ta fice, kwanciya nayi akan gado na fashe da kuka


Wannan wulaƙancin da me yayi kama, wai me nayi wa sabit ne haka daya tsani sooooo much shin baƙi laifi ne ko kuma haɗa mun da Allah yayi sam be ɗau wannan a matsayin ƙaddara ba



Wallahi baza ta saɓu ba yacce matar sa ta cire mahaifar ta ya kasance baza ta ƙara haihuwa ba dole ne ya haƙura nima gashi tunda nai ɓarin nan ban kuma samun ciki ba ko menene dalilin oho


Takaicin sabit ranar hanani bacci yayi kwana nai ina kuka dana gaji da kukan sai na miƙe na ɗauro alwala ina kuka ina faɗawa Allah matsololina duk da yasan a halin da nake ciki amma kuma ina sake gaya masa ya kawo min ɗauki



Anan kan sallayar bacci ya kwashe ni da asuba na farka sakayau haka naji ni, da wuri na haɗa breakfast ɗina sannan na zauna ina cin abinci na kasa ci nayi



Maganar badia ce ta faɗo min a raina, wai in zama wacce zan reni cikin su, lallai ma sun rena ni


Amma kuma wani ɓangare na zuciyata na son yi, ko ba komai zan dai ɗauki cikin da ba a son in ɗauka


Miƙewa nayi kawai na yi na kama hanyar ɗakin sabit hankalina Akwance, suna zaune shida badia sun yi jugum jugum abin duniya ya ishe su


"na yadda zan ɗau cikin ku amma ina da sharaɗi" kallo suka juyo wa sukai gare ni


"meye sharaɗin naki" suka haɗa baki


Kallo na bisu da shi sannan nace

"sai an biya ni ladan ɗaukar cikin"


"faɗi ko nawa kike so ni zan biya" inji sabit, tsayawa nayi na ƙare masa kallo sannan nace

"250k kuma cash nake soo"


Badia ce ta miƙe ta fita daga ɗakin bata daɗe ba sai gata da kuɗi


"gashi nan 300k ne na ƙara miki 50k" karɓa nayi ina murmushi sannan nace


"kun biya sai a saka lkcn dashen" murna sosai ya kama su badia har da rungume sabit


Fita nayi daga ɗakin naje na adana kuɗina akwai ranar da zakuyi amfani, nace a raina



Fara shirye shiryen dashen cikin muke yi abin mamaki shine na nemi turare na ko sama ko ƙasa


Babu neman da banyi ba amma babu har sabit na faɗawa sai yace min zai sai min sabo


Gaskiya nai missing wannan turaren zan so ace be ɓata ba haka nai ta neman har na haƙura


Ranar laraba muka shirya muka je asibitin akai mana test da komai da komai, komai ya kasance normal kawai lkcn dashe aka saka sati biyu



*****************


Ranar da kawo za ai dashen da kuɗi na na fita 200k a tattare da ni, sai da muka gama komai na shiga ɗakin dashen sannan nace wa dr. ɗin wacce ta kasance macece kuma bayarabiya


"nawa aka biya ki kuɗin dashen nan" kallo na tayi kamar batai magana ba, kuɗin da ke jikina na fito mata dashi kallon su kawai tayi sai ta washe baki tare da cewa


"30k"

Ɗari biyu na ɗauko gabaɗaya sannan na bata na ce mata

"kiyi aikin ki da kyau" kallo na tayi sannan tai murmushi tare da soke kuɗin sannan aka fara dashen fatana dai Allah ya bada sa a



Lafiya aka gama sai da nayi awa ɗaya bayan dashen sannan tace min in miƙe, kuma aka kafa min sharaɗin kar in kwanta da kowane namiji sai an tabbatar da cikin



Badia ce me cewa ai dr. kar ki damu bata da miji, tunda muka koma gida sabit yake nan nan da ni,


Komai na tashi zanyi sai a hana ni, har Allah ya kai mu 2 weeks inda muka koma asibitin aka tabbatar da cikina



Murna kamar me a wajen sabit da badia, kallon su kawai nake yi dafe cikin nawa nayi sannan nace Allah ya kawo min kai duniya lfy


[7:24PM, 5/3/2018] ‪+234 806 779 9926‬: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 23




Bayan kwana biyu sai ga mummy nai murnar ganin ta sosai har da saƙo na daga anty fannah Allah sarki anty fannah nayi kewar ki sosai



Mummy tai ta faɗa wai badia mahaifar ta bata da ƙwari kuma gashi ta kuma samun ciki amma ta ƙi zama ta kula da kanta



ba wanda ya tanka sai dai lallashi da suke ta bata wai zasu kula da cikin, ni dai ina gefe ina kallon ikon Allah wannan rayuwa wato akwai abin mamaki sosai



Kwanan mummy biyar sannan ta kama hanyar gida, kamar nayi kuka ranar da ta tafi, don kuwa yanzu zan koma rayuwa ni kaɗai


A hankali cikin ya ci gaba da girma har lkcn da zai zo duniya yayi


Rannan da yamma sai ga mmn badia tazo gidan ita da wata mata, ɗakin badia suka sauka sam ban sam me ya kawo su ba amma kuma bini bini a bini da ido



ranar wata talata da safe na tashi da nakuda, tun ina yi ni kaɗai har dai dana ga abin bana ƙare bane na fita, ina fita naci karo da wannan matar zata shigo ɗakina


"kar dai naƙuda kike yi ƴannan" gyaɗa mata kai nayi don bazan iya magana ba sabida ciwon da ke damuna



Sabit ta kira shima ya fito jiki si ɓari yake yi yaji ina labour, asibiti muka je, inda aka shigar da ni labour room Awa uku cur na ɗauka sannan Allah ya sauke ni lfy, ajiyar zuciya na saki dana ji Allah ya raba ni da wannan cikin lfy



Ɗagowa nayi na kalli yaron......... Fari tas da shi kana ganin shi kaga sabit


Miƙo min shi nurse ɗin tayi na karɓi kayana na tsaya ina kallon sa, godiya nai wa Allah daya sani ina da rabon ganin jini na



Sai da nurse ɗin gama gyara ni sannan ta karɓi babyn don gyara shi, shima, ko da aka gama shirya shi zata fita da shi na kira ta na karɓi abuna



Ƙare masa kallo nayi kamar sabit yayi kaki ya yar addua nayi masa sosai, na so ace yaron kamata ya ɗauko


Ko kuma ace baƙi ne amma ba komai duk abinda Allah yaso haka zan karɓa, kuma ina fatan ya zama me jin ƙan iyaye


Ɗa na yana hannuna na fito daga labour room, da sauri suka ƙaraso tare da karɓar sa mmn badia ce ta fara karɓar sa


"namiji ne ko mace" ta tambaye ni kalmar tai bala'in ƙona min rai ba Allah ya raya ba komai amma wai ita burin ta namiji ne ko mace


sabit ne ya karɓi shi shima daga gani maganar tai masa ciwo, karɓar sa kawai yayi ya wuce ɗakin da aka bamu na hutu


Addua ya dinga masa, ina amsa wa da amin, duk wannan abun da muke ita uwar ɗan bata sani ba don sammako tayi ta tafi kwatano wai ta tafi siyo kayan da zata saka da suna



Sai da ya gama masa addua sannan mmn badia ta kuma karɓar sa ta buɗe masa diaper inda ta gano namiji ne



Nan da nan murna kamar me, har wani ƙara ruƙunƙume shi take yi, mijinta ta kira ta shaida masa badia ta haihu,


Shima yai mata murna sannan yace a bawa badiar, nan ta hau ƙarya wai badiar bacci take yi

Mummy sabit ya kira yace mata badia ta haihu ita ma mummyn tai murna sannan tace a bawa badiar tai mata barka shima duk ɗaya yace tana bacci



Haka suka dinga kiraye kirayen waya suna shaidawa badia ta haihu, ni dai kallo ne nawa


Zuwa can baby ya fara mutsu mutsun yunwa, dabino sabit ya tauna ya lasa masa a bakin sa sannan aka bishi da zam zam



Wajen azahar aka sallame daga asibitin muka kama hanyar gida, wai don renin hankali babu wanda yake ta kaina ni dana haihun sai ta baby,


Ɗakina na shige na samu na watsa ruwan zafi a jikin sannan na fito kitchen na ɗaura indomie na ci na ƙoshi sannan na wuce ɗaki na na kwanta



Wajen ƙarfe 06:00 na yamma sai ga mummy, ina kitchen ina dafa shayi
Sai ga mummy, da sauri naje na tare ta

"mummy ashe kina tafe" tsayawa tayi tana kallona


"ya naga kamar ma kece me jegon duk kin wani ɗashe"

Ta faɗa tana kai hannun ta kan fuska ta, murmushi na saki sannan naja hannun ta zuwa ɗakin badia

"zo muje kiga jikan naki"


Bina tayi, da sallama na shiga, suna zaune a bakin gado shi kuma babyn yana cikin gadon sa na jarirai yana ta baccin sa



A razane suke da suka ga mummy, sai suka fara kame kame


"hjy fatima yaushe kika ƙaraso, muje falo mu zauna yaron yana bacci" inji mmn badia


"ni da nazo ganin baby sai ace min yana bacci, ina ita mejegon"


Tsuru tsuru sukai, nidai tunda naga na haɗa su sai nai ficewa ta na barsu


Ɗakin nawa naji an turo ƙofar, ashe mummy ce ta shigo, sai da ta ƙaraso da sannan na bata wurin zama


"har yanzu sabit ɗin basu dawo bane ko dai wani abun ne ya samu badiar"


Ni dai ban tanka mata ba saboda sam ban san ma ina ta dosa ba,


"ni wallahi duk a gajiye nake, nace musu su shirya gobee mu koma abuja ai suna acen dama dalilin zuwa na kenan"


Ni dam ban tanka

Please Login or Register in order to submit comment