Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nishaɗi 🙈


Juyawa yayi ya fice inda na bi bayan sa da gwalo sam ban san zai waigo ba sai gashi mun yi ido huɗu da shi ina masa, shan kunu nayi na ƙara ɗaga muciyata ƙwafa ya kuma yi


"wallahi sai kin rena kanki" ya faɗa yana ficewa, ina jin shi yana waya da badia inda yake cewa


"yanzu only kin riga kin yi booking ba za ku iya canceling flight ɗin ba ki ƙara hutawa" ban san me tace masa ba na dai ji yana ce mata ok safe jorney



Ranar wuni nai ina murna badia zata dawo in huta da jarabar wannan jarababben nata ta dawo can suje su ƙarata ni ma in samu in sakata in wala



Ina gama abinda nake yi na shiga part ɗin anty fannah na bata lbr ina ta dariya ita ma dariyar ta taya ni sai da muka gama sannan tace


" bari in baki wani haɗi ki shaa, idan kika shaa badia tana dawo wa idan ya kwana a ɗakin zai manta da ke saboda salanta mace yake"


Da murnata na ce mata tooo nice har da taya ta haɗa shi da zuma a ke sha sai tsimi wanda ta haɗa tace nata ne shi sam ban sha shi ba haka kurum ina neman hanyar gujewa sabit me zai kaini shan wani tsimi *ƙila ma na mmn fareeda ne sunan shi maƙale mata*





Da yamma kuma ta haɗa min wani shayi mara daɗi wai in shanye na tambaya ta ko na menene haɗe rai tayi tace min

"kin taɓa jin ance shayi yana maganin mata barin ma baƙi kawai ki sha" ɗaga takashin kofin nayi nayi ɗaɗɗake shi sam ba daɗi


Sai farfesu da ta haɗa mana muka sha shima sam ba wani daɗi gare shi ba, anty fannah a wannan lkcn ta iya girki amma wani lkcn in tai maka girki sai dai kawai aci da haƙuri barin ma ace pepper soup ne sam baya daɗi wani spice take sakawa me gari gari wai haka ake yi a garin su ni sam baya min daɗi


Tare mukai dinner da ita anan part ɗin nata kasancewar shima isma'il ɗin ana part ɗin ta yake


Sai yamma lis sannan na tafi da guzurin abinci na, ina shiga toilet na faɗa nai wanka na ɗauro alwalar sallah magariba



Yau gogan be dawo da wuri don har akai magariba sam banji ɗuriyar saba, sai can kusan tara sannan naji shigowar sa



Ban bi ta kansa ba don komai na buƙata na tanadar masa, bashi ga shigo ɗakin nawa ba sai ƙarfe 10 :30 na dare gashi ya hanani bacci indai br shigo ba haka na zauna ina ta gyangyaɗi



Ranar munyi wani abu wai shi till dawn 🤣 daɗin abun i was enjoying myself all along 💃🏼💃🏼💃🏼


A ɗakin ya ƙarasa baccin sa bayan ya tasa ƙeya ta toilet munyi wanka tare, Allah sabit ɗin nan yana son ɓata min tarbiyya ta



Wajen ƙarfe shida ya fita ɗauko badia kamar sallah haka nake jin kaina, ko da ya fita sai daya karta min warning ɗin kar badia ta sake ta dawo ban gama girki ba sannan yace min


"idan kika sake naji wani abu daga gare ki zaki ga yadda zan miki" yana ficewa nai tsalle tare da cewa


*FREEEEDOM* 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼


********************



Yana tafe a mota yana tunani abinda asmau tai masa sam be ji daɗi ba, wannan ƴar iskar yarinyar sam ban gama mission ɗina akan ta ba ta ruguza min budget ɗina yanzu in badia ta dawo tayaya za ayi in samu sake wa da ita


Ga wani shegen abu a tattare da ita da sam mutum baya gajiya da ita, wani abun da ke birgeshi da ita shine duk da taurin kanta amma yakan juyata son ranshi


Kamar kissing sam badia bata son kissing sai tace wai ƙazantar hakan take gani, ita kuwa wannan sarkin taurin kan yaga har ta fara responding sannan wanka tare



Wannan no go area ne a wajen badia wankan ma a ɗakin shi sam bata yi balle yayi joining ɗin ta sai ta tafi ɗakin ta ta saka key a toilet sannan take wanka


Amma asmau tuni ta saba da wanka da shi duk da dai kullum kamar bata so amma shi hakan sam be dame shi ba


Sai kuma bacci tare wannan ma haram ne ga badia yana son yaga yana kwance matar shi a jikin sa amma sam badia bata so wai bata son ya farka ya ganta ba makeup


Amma ita wannan sam makeup ɗin be dame ta ba ita dai tayi wanka ta saka turaren ta me shegen tayar masa da hankali


Gaskiya tsakanin su akwai banbanci sosai amma matsalar asmau ɗaya ce baƙa ce shi sam har yanzu bashi da taste akan baƙar mace balle har ace zata haifa masa baƙaƙen ƴaƴa subhanalli ai da anyi yaƙi da shi ina shi ina baƙaƙen ƴaƴa


Ai dole ne ma ya ɗau mataki akan asmau don kar ta haihu shi sai yanzu ma ya kawo maganar cikin ashe zata iya samun ciki gaskiya dole ne ya ɗau precaution akan asmau haka kurum kar ta haɗa shi da baƙaƙen ƴaƴa ta cuce shi ya rasa yadda zai yi da su



Da wannan tunanin ya ƙarasa airport ɗin inda ya tarar jirgin nasu haɗ ya sauka, sam ba kamar da ba yadda idan badia ta dawo yake rawar ƙafa yanzu kawai sai yaji wani iri amma sai ya dake yai mata welcome kamar yadda yake mata adaa sannan suka kama hanyar gida 🚕
[10:55PM, 5/2/2018] ‪+234 806 399 9164‬: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 18🌹










Kafin ma su ƙaraso na gama komai na gyara gidan tsab, banji tsayuwar motar su ba kasancewar parking lot ɗin yana can wajen gidan



Sallamar su kawai naji inda na tafi da gudu naje na rungume badia tare da cewa

"anty badia sannu da zuwa wallahi nayi bala'in murnar dawo warki" abin mamaki ya bata inda take ta ƙoƙari yakice ni daga jikin ta


Bayan ta ɓanɓareni sai ta kai duban ta ga sabit

" *SD* yarinyar nan lfyr ta ƙalau kuwa" be kai ga amsa mata ba na ƙara ruƙunƙume ta


"wallahi anty badia ba komai kawai dai nai murnar dawowar kine" ina kallon sabit yana ta doka min harara sai na share shi


"yanzu tunda kin dawo sai ki karɓi duty ɗin kula da mijinki in huta da........." ban kai da ƙarasawa ba naji sabit ya toshe min baki tare da hankaɗa ni cikin falon


"wuce ki ba mutane wuri da shegen surutun ki faɗi ba a tambaye ki ba"


" *SD* wane duty ne kuma asmaun take magana na kula da kai"


Ɓata rai yayi sannan yace

"wa yake bani abinci in ba ita ba, ya yake kula da gidan duk ai itace take yi, muje only na san kin gaji ne da wannan tafiyar da kika"



Jan hannunta yayi suka shige ni kuma na tsaya ina kallon wannan wawiyar tunda kika ji nace duty ai sai ki harbo jirgin



Sai da suka jima sosai a sama sannan suka sauko kowanne su yai wanka ya canza kaya a zuciyata nace tabbas me wuri ya zo me tabarma dole ya naɗe


Yanayin fuskar sabit sam be nuna wani alamar farin ciki ba ko wani abu,



ba kadaran kadahan dai kamar ba wani abun da ya shiga tsakanin su ko me yasa sam ba haka yake yi ba in ya kwana a ɗakina da fara'ar sa da nishaɗin sa yake fitowa


Ko ma dai menene su suka sani sunfi kusa can ta matse musu ni dai na samu freedom


Ranar da wuri na gama dinner naje na jera musu bayan sun gama na kwashi, wanka naje nayi na samu na kwanta, nai juyi sosai akan gadon kamar ranar na fara kwanciya akan gado



Wani lafiyayyan bacci ne yayi awan gaba da ni, ina cikin mafarkina me daɗi kawai naji an ɗaka min duka


"bana ce miki kar ki kwanta banzo ba, maza wuce kije kiyi brush ki sake wanka kizo ina jiranki"


" Kai mafarki nake yi koo" na faɗa, ranƙwashi naji a tsakiyar kaina


"wannan ma a mafarkin kika ji shi"

Kallon shi nayi sannan nace


"wallahi ko ka fitar min daga ɗaki ko in maka ihi ai yanzu matar ka ta dawo"


"Allah ya baki sa ar ihun baza ta jiba don na ɗura mata maganin bacci, wai zaki tashi ki gyara jikin ki ko musu zaki zauna kina min"


Banni da bakin magana haka na miƙe na shige toilet ina cikin wankan ne ma sai gashi tare muka yi kamar yadda yake so sannan ya nannaɗo ni a towel na fito kamar yadda nake gani a littafi




ƙwiiiii wasa nake yi da ƙafa ta na tako ko ta kaina ma be biba, a ɗakin ya kwana, nai mamakin da ko a jikin sa haka ya kwantar da ni a jikin sa har yayi bacci


Ko cikin baccin idan nai birgima na koma ƙarshen gadon sai ya jawo ni jikin sa mun cigaba da baccin mu,


Da asubar fari ya bar ɗakin a zuciyata nace an dai ji kunya



********************


Tun daga lkcn ya tsiri min shigar dare amma ba kullum ba kwana bibbiyu zaku ga ya shigo ya kwana in kwana biyu kuma ya zagayo ko ƙeyar sa bana gani


A yanzu ma fara sabawa da sabit sosai, amma duk wannan abun da ake yi badia bata da masaniya


Rannan tafiya ta kama shi, ƙiri ƙiri na dinga nuna masa ina murnar tafiyar sa, ranar da zai tafi da daddare ya shigo ɗakina


Muna kwance sai yace min

"naga alamar murnan tafiyar nan tawa kike ji ko, bakya ganin zakiyi kewa ta"


"ko kaɗan" na amsa masa, mintsini kawai naji wanda ya saka ni zabura


"ni ma ba zan yi missing ɗinki ba da daddare ne kawai zanyi kewar ki amma zan kira badia musha hirar mu"


Ban tanka ba don nasan halin muguntar sa sai ya ƙara min wani salon muguntar tasan


Kashegari da safe sai gashi da sabuwar wayar sa ya kawo min sqm badia bata ji daɗi ba wai meye na sai min waya


Ina jin shi yana ta lallaɓe ta akan wai ko idan suna son abinci kafin in dawo sai in haɗa musu,


Yana zaune a falo kafin lkcn tafiyar sa yayi, ita kuma gimbiyar tana kan cinyar sa sai wani shagwaɓa take zuba masa wai zatai kewar sa, shi kuma sai wani biye mata yake yi sai kace gaske


Ada idan badia tai masa wannan shagwaɓar tata jin sa yake yi kamar ba yashi a duniyar nan, amma yanzi sai ganinta yake yi wani banbarakwai ba kyan gani akan cinyar sa, kyan cinyar sa asmau amma ita matsalar ta shegen taurin kai ne da ita



Ni kunya ce ma ta sake su ta kama ni, lallai ma namiji sai a gaishe shi jiya yana ɗakina anan ya kwana amma da safe yana wajen ɗayar har da wani zaiyi missing ɗin ta


Wallahi na dawo daga rakiyar sabit tabbas me fuska biyu ne, ɗakina na shige sam ban ma san lkcn daya tafi ba



Yana tafiya naje part ɗin anty fannah na nuna mata ita ta nunnuna min yadda ake operating ɗin ta ranar wuni nayi acan sai da daddare dana ci na ƙoshi sannan na tafi inda na tarar da bala'in badia wai na barta da yunwa kallo bata ishe ni ɗakina kawai ma wuce inda tabi ni da zagi




Da daddare da wuri na kwanta ban daɗe da kwanciya ba sai naji wayar na ringing, ɗaukar ta nayi number sabit kawai nagani


Sai da ta kusa tsinkewa sannan na ɗaga


"hello" nace masa

"baki iya sallama ba sai hello" sallamar nayi masa sannan ya amsa


"me kike yi"

"ba komai na dai kwanta ne bacci zanyi" na bashi amsa


"ke baki san mijinki yayi tafiya ba ki kira shi ki tambayi ya ya sauka ba ko"


"yi haƙuri ya ka sauka, yau wuni nayi ina koyon wayar nan shiyasa shap na manta da kai"


"meeeyeee kika manta dani saboda wata ƴar iskar waya lallai ma ke ɗin nan wai fannah bata koya miki yadda ake kula da miji bane"



Masifar sa daya saba ya hauyi shiru nai masa ya gaji dayi ya kashe wayar sa

Nima ajiye tawa nayi sannan na kuma kwanciya, can sai ya kuma kira, ohhhhh yanzu kuma menene ina ɗauka naji yace


"ke baki san mijinki ya yi fushi ya ajiye wayar sa ba ki kira shi ki bashi haƙuri ba" shiru nayi don sam ban san me zance ba


"asmau" naji ya ambaci sunana da harufa masu sanyi har cikin zuciyata sai da naji su


"na'am ai ban san fushin kayi ba kayi haƙuri"


"sai dana roƙa, to punishment ɗinki shine ki bani labari kawai" shiru nayi to ni labarin me ma zan bawa sabit ni sam bamu saba hira ba balle in ce ga lbrn da zan bashi


"baki jini bane"

"naji ai na rasa ko name zan baka ne"


"bani lbrin akai na" toofaaa ba gwanda yace in bashi lbr a kan garin da ban taɓa zuwa ba nayo sharhin daya zo min akaina amma labari akan kan sa me na sani



Shirun daya ji yayi yawa ne ya sa shicewar

"to gaya min abu goma da bakya son nake yi" ban wani ɓata lkc ba na fara lissafo su



"na ɗaya kana da wulaƙanci, na biyu ga mugunta,........ Haka na dinga lissafo masa halayen sa da bana soo har ya dakatar ni sannan yace


"naji yanzu ki gaya min me kike so a dangane da ni" to faaa anzo wajen


Hmmmmmmmmmmmmmmm kawai na dinga yi ashe ya ƙulu, masifar tasa dai ya hauyi, nidai nawa jine sai da yayi ya gama sannan ya kashe wayar nima sai na kashe wayar gabaɗaya na kwanta, tunda lkcn be kuma kirana ba har ya dawo gida



********************



Rannan da sassafe ya shirya inda Allah ya taimake sa na san da fitar sa da wuri don haka sai na haɗa masa breakfast da wuri



Ina kitchen ina wanke wanke badia ta kira ni wai sabit ya manta da agogon sa in kai masa agogon part ɗin mummy don kuwa a lkcn be ci ace ya tafi ba



Karɓa nayi sannan na kama hanyar part ɗin a daidai ƙofar shiga naji kamar ana magana ana ambatan sunana sai na tsaya don inji meye ake ta ambaton sunana


"kai kuwa sabit ai na ɗauka son yarinyar nan kake yi, to me zai hana ka bari ta haihu ɗin" inji mummy


"gaskiya mummy bana son haihuwa da asmau haka kurum ta haifa min baƙaƙen ƴaƴa inyi da su, ni dai kawai ina zaki san dabarar da zaki dinga yi mata har ta dinga shan ƙwayar kullum to gaskiya zan so hakan"



Duk da dai mummy taga rashin dacewar hakan amma kuma bata iya yiwa ƴaƴan ta musu, sam bata so ba amma kuma sabit be san a a ba


"to shi kenan amma baka tunanin ya kamata ka bari ko ɗaya ne ta gwada kafin a hanata"


"mummy akwai probability na asmau zata haifi baƙin ɗa kuma abinda bana soo kenan inda ace dukkan chances ɗin na fararen ƴaƴa me da zan fi kowa murna amma baƙin ƴaƴa inyi yaya da su"


Duk yadda mummy ta so hana abin amma sam sabit ya ƙi yadda ba yadda ta iya haka ta karɓa tare da yiasa alƙawari kullum asmau zata dinga shaaa



Sulale wa nayi na zauna a ƙasa gabaɗaya duk wani service nawa ya ɗauke, shin wai baƙi lefi ne da mijina baya son kalar nan


Na ɗauka Allah ne ya hallicce mu kuma yake son ganin mu a haka, kallon skin ɗina yayi wanda yake a chocolate colour, wanda a kowane lkc yake glowing


Kusan sai dai in ban fita amma sai an ta yaba kyau na amma wannan kyaun nawa sam baya burgr mijina, shi kawai baƙin nawa yake gani



Sam be damu da abinda yake cikin zuciyata ba, jin takun sa ya sani miƙewa a tare muka buɗe ƙofar falon



Sam ban nuna masa wani abu ba inda na miƙa masa agogon nasan sannan na shige don gaida mummy



Tana zaune da sachet ɗin maganin a hannun ta tana kallo, tana ganina sai ta ɗan firgita amma kuma sai ta ɗake


Zama nayi sam sai na nuna mata ma ni ban san me ake ciki ba, gaisawa mukayi sannan na miƙe zan fita


"asmauk naji ta kira ni, komawa nayi na zauna sannan nace

"na'am mummy kina son wani abun ne"


"sam ko ɗaya maganine dai na samo miki, naga ƴar uwar ki har yanzu bata haihu ba shiyasa nace bari na samo miki magani ke sai ki dinga sha ko a dace"


Murmushi ne sosai a fuskar ta da badan naji komai ba da abinda zai sa ince ƙarya ne, tashi nayi na shiga kitchen na ɗebo ruwa na kawo



Guda ɗaya ta bani na haɗiya da in haihu da sabit ɗan ya hanani barin sa gwanda ban haihu da shi in yaso in lkcn tafiya ta yayi babu abinda zai hanani tafiya



Hawaye ne taf ido na wanda a hankali suka dinga gangarowa duk wannan abunda nake wa sabit be sa shi ya fara so na ba to sai yaushe, shin wai baƙi laifi ne


Ya Allah ka dube ni ka saka min cutar wa nan da nake fuskanta ba tare da wani hakkin na ba, ganin ina kuka ya sa mummy tambayar menene


"ba komai mummy kawai da ina farin ciki ne yadda kike nuna min soo" sanyi jikin ta yayi ta jawo ni ta rungume ni sannan tace


"wani lkcn ni kaina nakan yi judging abinda nake yi amma i cant help it, wataran idan kika haihu zaki fahimci halin da nake shiga in terms of deciding wat mah kids want"


Sam ban fahimci abinda take nufi ba amma na san cewar ita uwa wacce bata saba kwaɓar ƴaƴanta ba balle ta nuna musu sun yi ba dai dai ba, wannan shine weekness ɗin ta



Her weekness is her boys kuma ban taɓa jin haushin ta ba saboda kowa a duniyar nan yana weekness ɗina sa


Amma wannan karon gaskiya ta kaini bango sam na daina ganin mutumci ta at least in ɗan ta ya tashi yin abu wanda tasan be dace ba ai sai ta kwaɓe su ko amma sam ba haka take ba



Tashi nayi na kama hanyar part ɗin mu ina shiga ɗakina kawai nayi, na kwanta kuka ne ya ƙwace min lallai maraici be yi ba


Inda ace iyayena suna nan a raye da ko hakan zata same ni zai kasance ya zo min da sauki, amma yanzu bani da wanda zan tunkara


Don ko idan na faɗa wa anty fannah hana ni shan maganin zata yi tace sai na yadda na yi cikin ni kuma kamar yadda baya son haihuwa da ni, nima haka na tsani haɗa jini na da shi, wani wahalallen bacci ne yayi gaba da ni



Sai la'asar na tashi gabaɗaya bana jin daɗim jikina da kyar ma nayi dinner, ko da na gama ma sam banci ba shayi na haɗa na sha sannan na kwanta sai bacci


Ina cikin bacci naji mutum yana tashina tare da balbale ni faɗan nayi bacci ban jira shi ba


Kaina ciwo kawai ya ɗauka sakamakom tashin nan da yayi min, toilet na shiga nayi wanka kamar yadda na saba in yazo nayi bacci nayi brush sannan na fito



Yana matsowa kusa da ni da ƙamshin turaren nan nasa ya doki hanci na sai naji amai yana taso min, danne zuciyata mayi amma a gaskiya na ina cutuwa


Yana shirin ɗaga ni wani yunƙuri da nayi sai amai ya fito gabaɗaya na wanke masa fuska da shi, sai da na amaye duk abinda ke cikina sannan na iya maida numfashi


A gaskiya turaren nan ya cutar da ni dani dayawa, ido na a rufe banyi aune sai jin saukar mari nayi, na kuma jin wani a ɗayan gefe


Dafe fuskar tawa nayi na buɗe idon nawa, nan naci karo da fuskar sa wanke tas da amai na, duk da zafin marin nan da nake ji amma hakan be hanani murmusa wa Allah ya kara ya faɗa a raina



Ɗaga ni yayi ya shige toilet inda ya watsa ruwa yana fitowa ran shi a ɓace yace

"ki kwashe bedshit ɗin nan ki wanke min su tas idan na dawo da asuba na tarar da su ba a wanke ba a bushe ba zaki gane kuren ki"


Ficewa yayi daga ɗakin ni kuma na miƙe tare da kwashe kayan shinfiɗar na nufi toilet don wanke su, to me ya saka ni aman nan, ni ko kaɗan banci wani abun a zo a gani ba balle ince ko shi ya ɓata min ciki



Ina wankin ina tunani na, ko da na gama sai na fita waje na shanya su sannan na samu na tsarkake jikina ni ko ya gama ma oho masa, ban damu ba zani na na shinfiɗa sannan na kwanta

Asuba ta gari 😴😴😴😴😴😴🤤🤤🤤🤤🤤🤤
[10:56PM, 5/2/2018] ‪+234 806 399 9164‬: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 19🌹





Da asubar fari ya zo lallai mutumin ya iya doka sammako tashi na yayi sannan ya karta min warning kar ya sake ya dawo daga masallaci ban gyara ɗakin ba


Wanka na fara yi sannan na ɗauko shayata na gyara ɗakin, sannan nayi sallah asuba, na idar ina lazimi ne ya shigo ɗakin nawa lkcn garin ya fara wayewa


Ƙamshin turaren sa ya fara dukan hanci ma wanda hakan ya sa zuciyata ƙara tashi, da gudu na ruga toilet na fara amai, har banɗakin ya biyo ni


"wane irin iskanci ne yake saki wannan aman"

"wallahi ban sani ba ni bama abinda na ci" na faɗa a marairaice



Matsowa yayi kusa da ni ya damƙi gashi kaina sannan ya ɗago min fuskata wani azaba naji ya ziyarci kaina fuskar nan tasa a tamke sam ba fara'a


"yaushe rabon ki da menstruation" ya tambaye


Shiru nayi don wallahi ni na manta ba calculating nake yi ba, indai yazo min shikenan in bai zo

Please Login or Register in order to submit comment