Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟCompiled By Deeja 0ne Love




๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)




*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~โ„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*





*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated to
Maryam khamis*
*ALHAMDULILLAHI ALA NI'IMATIHI, ALLAZIY MANNA ALAINA*


*ina taya daukacin musulmai na duniya baki daya murnar yin idil fidr*


Yan kasa ta nigeria dafatan anyi sallah lafiya, allah yasa haka ameen.


*Zazzagawa bayin Allah,na gaishe daku ku din na daban ne a duk inda nake zan amsa da nidin bazazzagiya ce,so proudly zage-zagi*.

Kungiya mai albarka, kece sama dasu, a cikin su kin zama zara,suna sukar ki kina kara haskakawa, makiyan ki fadawan ki,kinfi karfin su sai dai idanu, kin zarce sa'a

*_GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION _*.

Big bro angon katifa da filo babban yaya mai ji damu *UMAR DALHAT*fatan anyi sallah lafiya.


*yan uwana marubuta a kungiyar*:-
Nabeelert
Feenert(matar soja)
Dr fatee
Harira(yar fillo)
Khadeejert haidar(namesy tawa)
Ameeshert
Zinariya
Ummu noor
Ummee yusuf
Maman ashefat
Maman mamy
Princess
Da sauran wa'inda ban ambato ba ga bayan sallah yayi allah ya kawo mu, dafatan za'a faso da karfin allah.



*Masoyana dake fadin kowacce jaha a nigeria ina muku fatan alkairi*.

Ammatul mannan
Shamsiyya m magaji
A'eesha adam(daughter)
Maryam musa1
Hanane mohammad
Ramlat
Maryam musa
Zulaihat sani
Mustapha marakisiyya
Abuakar ahmad
Starboy umar
*Members of*:-
Hafsat hausa novels(Hยฒ)
Dandalin littafan jarumai and hausa novels
Hausa novels ayau
Aunty fatee hausa novels
Da duk wanda ban ambata ba ku sani duka ina yin ku kamar yadda kuke yi na.



*Yan uwana marubuta*
*Deejency* ina miko gaisuwa ta
*Mamuh gee* ina ganin girman ki har gobe
*Bashier sufyein(sarduna)*banga kayan sallah na ba ๐Ÿ˜.

*Bismillahir rahmanir rahim*
001-002

Daidai murtala muhammad way titi daya dauke hanya yayi kudu,motatoci ne gasu nan babu iyaka a tsaye kowa ya San yanayin cinko son kano.



Wata mota ash colour high lander wacce take jerin motocin dake tsaye suna jiran traffic,wata matashiyar mace na hango wacce daka ganta kasan hutu ya ratsa ta.


Agogon kamfanin rolex dake daure a farin hannun ta ta kalla,Dan karamin tsaki taja,ta San yanzu baby na can na jiran ta.



Yana nuna green ta figi motar da gudu,wayar ta samsug galaxy S8 ta fara ringing,ko kallon wayar bata yi ba.




Dai dai bakin get din,dalibai ne da yawa kowa yana harkar gaban shi,masu trekking nayi masu jiran a zo a dauke su suma suna zaune.



Cikin sauri ta bude motar ta fito,subhanallah kyakkyawa ce to d extend,doguwa ce tana da jiki dai dai Wanda baza'a ce mai kiba ba kuma ita ba siririya bace,tana da manyan idanu grey colour,Wanda ta boye su cikin goggle hancin ta dogo,hakoran ta farare tas yayin da pink lips din ta suka adana su ta ciki,dogayen yatsun ta ta dago ta rataya swag din ta,cikin ta sanye da doguwar riga light yellow da brown kanta ta yane da mayafi light yellow.



Cikin tafiyar kasaita da tsananin yanga ta fara takawa,gaban makarantar ta karasa.


Wani farin yaro wanda bazai wuce 7yrs ba ta riko hannun shi,murmushi tayi Wanda gefen kumatun ta ya lotsa a hankali ta bude baki tace"haba baby baka ganni bane come and hug me mana".



Juya baya yayi,cikin sauri ta janyo shi tace"oya come and see something",kwace hannun shi yayi ya cuno baki yace"please leave me alone",manyan idanun ta me kama da na mage ta zaro tace"to baby yau kuma fitina kake ji kenan".



Jakar shi ya amsa a hannun wani yaro kamar shi ya wuce cikin mota,a sanyaye ta mike ta bi bayan shi,ganin ya shiga baya yasa ta daure fuska tace"dawo gaba",banza yayi da ita.


Daka mishi tsawa tayi tace"ba da kai nake ba oya dawo gaba",jikin shi har rawa yake yi wajen dawowa".



Tunda suka fara tafiya babu wanda yace da kowa komi,dai dai haske shoprite tayi parking,kallon shi tayi kafin tace"baby am sorry na taho traffic ya tsayar dani",tabe fuska yayi yace"ai nayi ta jiran ki baki zo ba",hannun shi ta rike tace"yanzu jira ni na shiga wannan shoprite din yanzu zan dawo.



Jinjina kai yayi yace"a dawo lafiya,"murmushi ta Mayar mishi kafin ta bude mota ta fita.



Tana shiga ta mai da goggle din ta fuska ta ja basket,duk inda ta gifta maza bin ta da idanu suke yi,hakan be dame ta ba kamar ta saba da hakan ne.



Siyayyar ta take hankalin ta kwance,har ta fito wani ya biyo ta,cikin sauri yace"assalamu alaikum,madam zan sami lambarki?inji ogana.




Watsa mishi idanun ta tayi,cikin sauri ya sauke kan shi kasa,murmushin gefen baki tayi tace"kaje ka cewa ogan ka ni ba'a mini aike yana son lamba ta yazo da kan shi",tana gama fadin haka ta bude motar ta ta shiga ta figa da gudu ta bar shi tsaye.




Cikin sauri ya koma cikin shoprite din,mutumi ne wanda yake babba Dan dattijo ne ga body guard za gaye da shi,tashi yayi a zafafe bayan wanda ya aika ya dawo mishi da sakon data bashi,cikin huci yace"ita yar gidan uban waye da zata wulakanta ni dan haka skype ka binciko mini waye uban ta a garin nan.


Wanda aka Kira da Skype ya amsa da"an gama yallabai",wuce wa yayi cikin sauri,masu daukar jaka nayi masu daukar phones suka kwashe sannan suka bishi.



Tuki take cikin natsuwa har ta iso zoo road,a dai dai bakin wani katon gida ta tsaya horn tayi,mai gadi cikin girmama wa ya bude Mata get din,parking lot tayi parking, a tare suka bude kofar suka fito.



Jakar hannun shi ta amsa sannan ta rike mishi hannu suka shiga ciki.



Wow gida ne babba Wanda ya amsa sunan gida,wani hadadden falo ne wanda aka kawata shi da kayan more rayuwa.



Amina!Ameena!!Ameena!!!ta kwala mata Kira,wata yar shekara 17 ta fito cikin sauri,kallon ta tayi tace"baby ya dawo a kai mishi abinci",jiki na rawa ta amsa da to.


Ameena ta kuma cewa"aunty ke ba zaki ci abincin bane?",kamar baza ta amsa ba tace"eh na koshi",daga haka ta juya ta tafi.



Wani kofa ta bude,wani falon ne sai dai wannan be kai wancan girma ba,komai milk da brown ne,a hankali ta isa gaban center table din wayar ta da key ta ajiye,wata kofar ta sake budewa,hadadden bedroom ne white and pink komai na ciki,rigar jikin ta ta cire ta shige bathroom.



Wanka tayi sannan ta fito,simple make up tayi,wata doguwar riga ta saka armless peach colour,farin mayafi ta yane kan ta dashi jikin ta sai tashin kamshin laylatus-Sahara yake yi.




Cikin takun ta ta nufo Falon ta,kan center table taje ta dau wayar ta,main palour ta nufa tana tafe tana yin waya.



Cikin muryar ta mai kama da busar sarewa tayi sallama.



A ta can bangaren aka amsa,tace"yadai beelert mai ya faru naga kiran ki lokacin ina driving ne",



Beelert tace"cat eyes feenert tace"anjima mu hadu a 021 saffah 20:009,"murmushi tayi tace"ok sai na zo din akwai new story kenan",eh i think so gaskiya"beelert ta bata amsa",cikin sanyin murya tace"okay.




Kashe wayar tayi kafin ta zauna,Ameena ta kwalawa Kira,cikin sauri ta karaso,tace"ina baby yake?"cikin sauri ta bata amsa da "da yana dakin shi",mikewa tayi tace"jeki cigaba da abinda kike yi.




Tura kofar tayi ta shiga,a zaune ta same shi yana game a tablet din shi,gefen shi ta zauna sannan tace"baby kaci abinci?,daga Mata kai kawai yayi ya cigaba da abinda yake yi.



Shiru dakin yayi kafin tace"baby wai me yake faruwa ne da yanzu kwata kwata baka da farin cikin da?,a Dan karkace ya kalle ta kan ya juyar da kai cikin sanyin murya yace"baby ai yanzu baki damu Dani ba kamar da",da mamaki tace"bangane ba me nake maka Wanda yanzu bana maka?".




Hawaye ya goge yace"da baki fita ki barni yanzu kuwa kina fita,a da kikan tsaya kiji meye damuwa ta yanzu kuma bakiyi yaya na kwana me naci duka basu da meki ba kamar dai kin daina sona yanzu",cikin sauri ta riko hannun shi tace"har yanzu ina son ka mana baby wa nake dashi bayan kai",girgiza kai yayi yace"baby kina da mum feenert da mum beelert da sauran mazan da kike yawo dasu,"tsawa ta daka mishi tace"baka da hankali ne ni kake zargi baby?",mikewa yayi yace"kin gani da baki yi mini tsawa but yanzu kina yi mini kawai kije nidai abu daya na San zan gaya miki shine kiji tsoron Allah",yana gama fadin haka ya mike ya shiga bathroom.




Ai galala ta tsaya tana juya maganar shi wato taji taji tsoron allah ma,yaro sai kace wani babba,girgiza kai kawai tayi ta fita.


Falon ta ta koma gaban wani karamin frame ta karasa,hoton kyawawan yan Mata ne guda biyu da check a jikin su alamun a makarantar boarding aka dauke shi,fuskar daya duk gari ta Dan bata rai Dan rigar ta ma ajike take,ita kuma wacce tafi waccan kyau ta nuna ta tana dariya.




Shafa wacce take da gari a fuska tayi tana murmushi,hawaye ya ziraro Mata.


_Ga yarona nan ki kula dashi ikhlas kamar yadda zaki kula da kanki,kada ki bari yayi maraicin uwa, ki maye masa gurbin uwa da uba da yan uwa_.

_Kiyi mini alkawarin baza ki bari yayi Kuka ba ikhlas,kiyi mini alkawari ikhlas......._



Kalaman dake yawo a kwakwalwar ta kenan,jinjina kai tayi tace"sister na kasa cika alkawarin dana daukar miki,yau baby yayi kuka kuma nice sanadi",kuka ta fashe dashi.



"Tabbas ban rike alkawari ba!naci amanar da yar uwata ta bani",kuka take kamar wacce ran ta zai fita.



Zama tayi a wajen tana tuno rayuwar ta ta baya.




15yrs ago

Wasu yara ne da baza su wuce shekara goma ba Mata suke gudu,kyawawa ne sai dai daya tafi daya haske,wani gida suka shiga wanda daga gani basu da wani hali sosai.



Wata yar tsohuwa dake tsugune tana alwala,cikin sauri ta mike ta rufa musu baya,duka daki suka shige,kowacce kokarin ta ta shige kasan gado,da sauri wannan tsohuwar ta tura kofa tana haki.



Kallon su tayi kowacce haki take idanu kawai suke zarewa kamar wa'inda suka yi karya a gaban sarki,cikin rawar baki tace"meye faru imanu naga kuna gudu haka,kura ce ta kwance ko zaki ne ya shigo cikin gari?",dariya suka kwashe dashi suna kasan gado.



Wacce take da duhun fatar ta cuno baki tace"kai gwaggo wallahi kin iya batawa mutum suna wai imanu",dakuwa tayi Mata tace"kin ci gidan ku kafurar yarinya kun gaya mini me ya biyo Ku ko kuwa",kafin suce wani abu suka jiyo muryar shi yana sallama.


Kallon juna suka yi suka Kara shigewa kasan gadon,kofar ya kwankwasa yana fadin"gwaggo ki bude kofar nan yau sai na zane yaran nan.



Gwaggo jin abinda yake fada yasa tayi saurin budewa tace"su waye zaka daka din?",da mamaki yace"gwaggo iman da iklas suna ina?",hararar shi tayi tace ajiyarsu ka bani ne,ina tambayar ka kana tambaya ta?",sunkuyar da kai yayi yace"yi hakuri gwaggo wallahi yaran nan wai maman hafeeza suka rinka jefa wai Dan dazu da safe sunje dibar ruwa tace sai ta diba shine fa suka rinka yi Mata ruwan duwatsu".










๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)




*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~โ„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*





*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated to
Maryam khamis*



003-004

Salati gwaggo ta fara tana fadin"na shiga uku ni binta me zan gani haka",jin hakan yasa ikhlas fitowa ta cuno baki tace"gwaggo meye na salati kamar wa'inda suka yi sata haba",takalmi gwaggo ta jefo mata wanda yayi sanadiyar sata tayi shiru.




Kallon sadik tayi ta galla masa harara,zaro idanu yayi yace"ke baki da hankali ni kike harara?",magana tayi niyar yi amma ganin ya nufo dakin ya sata buga tsalle ta haye saman gadon gwaggo,kan ya cafko ta ta zille ta diro,janyo iman tayi dake tsaye tana zare idanu suka yi waje da gudu.



Cikin sauri gwaggo ta matsa daga bakin kofar kada su hada da ita.



Suna fita gidan suka fada gidan dake kusa dashi,matar tana tsaye tana daka suka shigo,girgiza kai kawai tayi,sai da suka danna sakata sannan suka kwashe da dariya.



Iman tace"wallahi mun shiga uku idan yaya sadik ya kama mu,murguda baki tayi tace"ba sai ya kama mu gani ba.



Sai da suka ji sun fara jin yunwa sannan suka bude kofa,sai kace munafikai suka nufi kitchen.



Umma ta daka musu tsawa tace"gidan uban wa zakuje me kuka ajiye mini a kitchen din",iman ta sunkuyar da kai tace"umma Dan allah kiyi hakuri yunwa muke ji wallahi",harara ta aika musu tace"me kuka yi mini da zaku bani hakuri abinci ne ban girka da Ku ba",kan suce wani abu sadik yayi sallama ya shigo,ai rige-rigen shiga daki suke.




Dariya kawai yayi sannan ya karasa kusa da umma ya gaishe ta,cikin farin ciki ta amsa sannan tace"watakila wani laifin suka yi naga suna rige-rigen shiga daki ne?",sadik yayi murmushi sannan ya bata labarin abin da ya faru,shiru tayi ta kasa cewa komai.



Sadik yace"to shine fa suke guduwa",umma ta jinjina kai tace"ubangiji allah ya shirya wa'inan yaran",sadik yace"babu komai allah ya kyauta gaba",ameen,mama ta amsa sannan tace"ya dai sadik an dace kuwa?",gurgiza kai kawai yayi,cikin damuwa yace"umma wallahi har yanzu shiru",jinjina kai umman tayi tace"allah ya kawo hanya",amsawa yayi da ameen,sannan ya mike ya fita.




Ikhlas ta leko tace"wallahi iman kin cika tsoro da yawa dalla ki fito mu tafi",iman tayi kwalkwal da idanu tace"wallahi ikhlas ina tsoron yaya sadik ya rike mu",finciko hannun ta tayi tace"wallahi yunwa bazata kashe ni a banza ba".




Cikin sanda suka fice daga gidan gidan gwaggo suka koma,sun yi sa'a gwaggon na barci,a hankali ikhlas ta bude kwano taga abincin gwaggon da bata ci ba tana barci,cikin sauri ta dauke kwanon tayi waje.



A tsakar gida suka zauna,ikhlas ta bude kwanon ta fara ci,iman ta zuba Mata idanu,ganin idan bata ciba ba rage mata Zara yi ba kuma idan dukan yazo duka za'a Zane su yasa ta saka hannun suka fara ci.




Sai da suka cinye tas sannan suka bude randa suka sha ruwan sannan suka fice,gidan su suka koma,umma ta bisu da idanu,buta suka dauka suka yi alwala suka yi sallah sannan suka cigaba da harkokin su.



La'asar nayi suka yi sallah sannan suka tafi makaranta,kasancewar babu nisa daga gidan su yasa suke tafiya a kasa,duk wanda suka gani sai sun tsokana sannan suke wucewa.



Suna shiga makarantar ba'a taru ba sosai dan da wuri suka taho,ikhlas tace"ba na gaya miki ba'a taru kika damu mu taho ai gashi nan,iman tace"ai gwara mu taho tun kan gwaggo ta farka ta tarar da abinda muka yi mata",ikhlas tace"to tashi mu zagaya gari kafin a taru",girgiza kai iman tayi tace'"gaskiya babu inda zanje kawai azo a fara dukan latti".



Finciko hannun ta tayi tace"wallahi sai kinje",janta ta dinga yi har suka fice.




Suna fita daga makarantar suka fara gudu,dai dai bakin wani gida suka tsaya,ikhlas tace"mu fara tsorata su",a sanda ikhlas ta shiga ita kuma iman ta tsaya daga bakin kofa,kansancewar iman Nada karamar murya yasa ta makale murya ta fara sallama,wacce ke zaune tana wanke wanke ta tsorata cikin sauri ta mike ta shige daki.



Ikhlas ta danne dariyar ta ta kara mannewa da bango,bude murya ikhlas tayi ta Kara buga sallama,jin muryar har cikin daki yasa suka fito a guje,ganin mutum jikin bango da idanun mage tana kara kwalalo su yasa suka koma cikin dakin da gudu.



Iman ta shigo tana dariya,bude kofar bayi Kairat tayi ta fito tana hararar su tace"wallahi sai na gurza muku rashin mutunci,yan gidan namu kuke tsorata wa.



Iman tayi dariya tace"allah sune sun cika tsoro",khairat tace"da kyau sai naga Ku baku da tsoro ne barin ma ke",ikhlas tace"ya isa haka pls muje ki shirya mu wuce makaranta",cikin sauri ta shiga daki suma suka bita.


A can karshen daki suka tarar dasu har lokacin suna manne da juna,khairat tace"umma su ikhlas ne fa",cikin sauri tace"amma dai Ku akwai yan banzan yara yanzu shine kuka tsorata ni",dariya suka kwashe dashi.




Koda ta gama shiryawa sai da umman ta kuma ja musu kunne sannan suka tafi.




Suna fitowa suka wuce wajen lilon haya,iman tace"kuna da kudi ne,na dai San ikhlas baki da kudi khairat ta murguda baki tace"ni ai ina dashi",cikin washe baki suka hau kowa daya-daya,me hayan ganin sun tsare wajen gashi basu bada ko biyar ba yasa ya musu magana.



Khairat tace"ka bari mu sauko gaba daya mana",me hayan yace"a'a bazai yiwu ba Ku bani kudina kawai",ganin yaki yarda yasa suka sauko.



Ikhlas tace"bashi kudin shi mu wuce",khairat tayi dariya tace"wallahi ko biyar bana dashi",kwalalo idanu iman tayi tace"na shiga uku yanzu ya za muyi?,khairat tace"mu gudu kawai dan wallahi suka rike mu mun shiga uku.



Tsugunawa suka yi suka kwashi takalma a hannu suka zuba da gudu,me hayan ya daura hannu aka yace"na shiga uku wallahi duka na za'ayi",daya daga cikin wa'inda ke wajen yace"kada ka damu nasan gidan su",nan suka rankaya sai gidan su ikhlas.



Umma tana aikin Dora abincin dare taji sallama,gaban ta sai da ya fadi,shigowa sukayi da yan rakiyar da yaron,kallon su tayi tace"lafiya kuwa?",me hayan yace"su ikhlas ne suka hau mini lilo kuma suka hanani kudin suka gudu.



Shiru umma tayi tabbas zasu aikata abinda yafi haka ma,dauko naira Dari tayi ta mika masa tace"bani canji",naira arba'in ya bata canjin,ta Kara cewa"kayi hakuri kaji".



Gwaggo tayi sallama ta shigo,bayan ta amsa tace"ya akayi asiya naji yara a gidan nan,nisawa umma tayi tace"hmm gwaggo wa'inda suka saba ne suka yi aikin su",gwaggo tace"allah ya kyauta gaba,nikam nace yau an manta dani da abinci ne?",umma tace"kamar ya fa?",gwaggo tace"to ni tun da na farka daga barci nake jiran naga an aiko mini da abinci naji shiru shine na biyo",umma ta kwashe da dariya tace"wallahi sai da nayi tunanin haka",gwaggo tace"kamarya fa?",umma tace"su ikhlas sun cinye miki abincin.




Kafin tace wani abu sadik yayi sallama ya shigo yace"gwaggo na shiga na Tarar da gidan babu kowa",gwaggo tace"abinci na biyo na tarar da shakiyancin yaran can",da sauri yace"meya faru kuma?",nan umma ta bashi Labari,shiru yayi kafin yace"bari na siyo miki wani abin kici",yana fadin hakan ya juya ya fice.



Koda ya dawo nan wajen umman ya kawo Mata abincin.



Bangaren su ikhlas kuwa sai wajen shida samnan suka isa makarantar,ta baya suka za gaya,ikhlas da khairat suka cicciba iman suka dira da ita,ikhlas ta tsuguna ita kuma khairat ta haye saman ta kama katangar tayi ta dire,ita kuwa ikhlas kamar biri haka ta kama ta dire.



Allah ya taimake su babu kowa a wajen a tsugune suke bi ta jikin ajujuwa har suka isa nasu ajin,lekawa khairat tayi ta hango malam anas a ciki,sunkuyawa tayi da sauri tace"shiga uku malam anas ne aciki",idanun iman da yake tafi kowa tsoro har ta fara hawaye,nan suka tsaya har aka tashi sannan suka biyo ayarin dalibai suka shiga daukar Jakar su.


Suna fitowa suka tarar da malam anas da malam Khalid a tsaye,sunkuyar da kai suka yi zasu wuce,da idanu suka bisu kafin malam anas ya jinjina kai yace"allah ya shirya",malam Khalid ya amsa da"ameen.



Suna isa gida suka sami yaya sadik a zaune,fuska a daure yace"Ku zo nan",iman da sauri ta karasa gaban shi,ikhlas kuwa baya ta fara ja,sannin cewa zata iya guduwa yasa da sauri ya mike ya janyo ta,hararar iman yayi yace"biyo ni",ikhlas kuwa hannun ta ya rike yana janta.



Dakin shi ya bude ya jefa ta ciki sannan ya dakawa iman tsawa yace"shiga kafin nayi kwallo Dake",cikin sauri ta shige jikin ta na bari.




Fuska daure yace"ku kama mini kunne",zaro idanu tayi tace"tab wallahi baya na ciwo yake",bakin ya buge ta tsandara ihu lips din ta ya kama ya hade ya matse da karfi,hawaye ta fara tana yarfe hannu,iman ma ta fashe da kuka tana bashi hakuri.



Kallon daya Mata ne yasa tayi saurin kame bakin ta ta tsugunna ta fara kama kunne,sakin lips din yayi yace"zaki tsuguna ko kuwa",da sauri ta tsuguna ta kama kunne,kwado yasa ta baya ya rufe kofar sannan ya fita domin yayi sallah.



Yana fita suka nemi waje suka zauna suna haki,ikhlas tace"wallahi allah ya isa kuma wallahi sai na rama.



Suna zaune suna fira,ikhlas ta mike tace "wallahi daya zo guduwa za muyi",iman tace"ta yaya?",murmushi ikhlas tayi sannan ta rada Mata a kunne.



Suna nan zaune suka ji alamun bude kofa,tashi ikhlas tayi ta matsa jikin kofar ita kuma iman ta tsaya ta dayan barin,kofar na bude iman ta zuba da gudu da wuce,kan ya ankara ikhlas ta tsugunna ta wuce ta kasa,tsayawa kawai yayi yana mamakin yaran kamar ana kada musu gangar shedan.




Su ikhlas kuwa a bakin kofa suka tsaya sai da suka huta sannan suka shiga gidan,gefe suka zauna suka rabe,iman da bata da juriyar yunwa ta marairaice tace"umma Dan allah kiyi hakur.......",kasa karasawa tayi saboda kallon da umman tayi Mata.





Ana sallar isha suka dauki buta sukayi alwala suka yi sallah,suna idarwa ikhlas tace"iman kinajin yunwa kuwa?",hararar wasa tayi Mata tace"nama fiki jin ta wallahi",murmushi ikhlas tayi tace"duk abinda nayi ki goyi bayana kinji",daga kai kawai tayi.










๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)



*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~โ„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*





*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated to
Maryam khamis*


005-006


Cikin sanda suka fito,ikhlas ta leka dakin umma ganin tana lazimi yasa tayi murmushi taja hannun iman suka zauna a zaure,ikhlas tana jin alamar tsayuwar mashi ta tabe fuska ta langwabar da kai,da sallama ya shigo,ganin alamun mutum yasa yace"waye nan a zaune",ikhlas harda nishi ta marairaice fuska tace"abba mune nan",Kara tayi kadan tana fadin

Please Login or Register in order to submit comment