Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a falo daki suka shige shiryawa FANAN tayi kasancewar tayi wanka agidan anty dauko liffaya tayi Wanda sukayi a auren wata yar makarantarsu farin Riga me dogon hannu tasa kafin tasa wando legins aciki nada sarin tayi dakyau ajikinta sky blue ne me touches na fari ajiki dauko dankwali tayi tadaura danrin ture tasa dankunne fari da plate shoe dinta fari handbag dintama fari bawani kwalliya tayi afuskanta ba as usual powder Tashafa sannan tasa kwalli a idonta tasa libstick ta fesa turare bakaramin kyau tayi ba suhaima ce tazo tace sis Kinga irin kyaun da kikayi kuwa Amma biki zakijeki ko fari tayi da manyan idonta Dan Allah nayi kyau sosaima kuwa zo in miki hoto fitowa cikin falo sukayi tafara kafta mata hotuna mamace tafito tasamesu kundawo kenan eh mama suka gaisheta FANAN irin wannan ado inazuwa mama zanje duba patient Dina ne daga nan Kuma zanbiya asibiti to shikenan adawo lafiya kibude pause dinna kidau kudin napep dinki fitowa sukayi har titi ta tari napep tashiga tanama suhaima bye bye.



Tsaye yake a can saman mansion din gidan duk abinda yake faruwa Yana ganin shiga da fitan mutane kasancewar Yana sama tun saukanta a napep yake hangota tsayawa yaga tayi tana magana da wani kwata kwata beyarda dashiba kallonsu yakeyi bako qiftawa knocking tayi baba me gadi yabude kasancewar yasan itace me duba azaad tafiya takeyi cikin nutsuwa hartashigo falonsu fawwaz da areef tagani gaisawa sukayi cikin wasa da dariya kafin tace Ina mama da zeenat da anty Amina aiduk suna falon sama kijeki mana tom haurawa tayi anan tasamesu tsugunawa tayi tagaida ummi da anty Amina cikin jindadi suka amsa zoki zauna mana zama tayi wow FANAN kinyi kyau sosai wlh inji anty Amina cikin zolaya ummi tace wai dama Fulani ma suna sa luffayane dariya sukayi kafin tace eh mana ummi munasawa duk dama ni wannan na aurene mukayi aikuwa kinyi kyau murmushi tayi tace nagode Ina zeenat yanzun nan ta tashi taje hada corn flakes kafin ummi tagama rufe Baki zeenat tashiga tana ganin fanan tace oyoyo Ashe kina hanya zama tayi suka gaisa bari inhado miki kema ah ah kibarshi ummi ce tace to Zaki fara ko bakyau fulako fah bayan 5mint zeenat tadawo Tamika mata nata sunasha suna hira ajiye cup din tayi tamike ummi bari inje indubashi inzo to sekin dawo fita tayi tanufi part din Azaad zaune akan kujeran dakinsa tasameshi gaishesa tayi ciki ciki ya amsa Yana kallonta ta kasa bayan tamishi abinda yakamata ne tazo zata fita yace kizo zuwa tayi tatsaya shuru bece mata komai ba sedaga baya yace kizauna zama tayi yace waye naga Kuna magana dashi dazun dayaushe kenan dago Kai yayi yakalleta kafin kishigo gidan nan ohhhh wai tambayana keyi inmishi kwatance shine nace Mai ni bama yar anguwar bace iya abinda yafaru kenan ehh iyashi kenan okay haryanzu bangama yarda ba kilama karya kikamin Dan dan Adam ba abun yarda bane mikewa tayi tace okay tunda karya namaka shikaje kasameshi nasan bazema karyaba tana magana ta tafiya mikewa yayi yaje ze rike kafadarta Dan yatsayar da ita mistakely yarike liffayan Dayake Saman kanta guduwa zatayi shikuma Yana tsaye a inda yake Yana rike da liffayan warwarewa nadin sarin yafara duk juyawan da zatayi seya warware fita gaba Daya yayi ajikinta yakasance daga ita SE dogon wando da Riga gashi yamugun matseta daskarewa yayi Yana kare mata kallo daga sama har kasa idonshine yasauka kan kirjinta dasuke cike kamar zasu faso waje ahankali yake tafiya harya karasa kusa da ita itakuwa ganin inda idonshi yake yasa tayi saurin sa hannunta duka biyu tarufe kirjinta.......





Tom SE munhadu gobe muji yanda zata kasance 😲😜😜😜😜

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story Written by ( MRS 🌹 ISHAM 🌹)



Da sunan allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen πŸ™πŸ™πŸŒΉπŸ€Ž





Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci πŸ₯°πŸ₯°






____________________________________________




Page 1️⃣4️⃣




Ganin inda idonshi yake ne yasa tayi saurin sa hannunta duka biyu tarufe kirjinta ahankali yasa hannunshi yarike kugunta wani irin kasalane yasauko mishi lokaci daya idonshi harwani lumshewa sukeyi kokarin kwace kanta takeyi Amma yamata rikon da bazata iyaba dayan hannunshi ne ahankali yake mata tafiyan tsutsa harya iso kirjinta dawo da kallonsa yayi kansu Yana kare musu kallo bakaramin tsokale mishi ido sukayi ba cikin bacin Rai FANAN tace wannan wani irin iskancine kasakeni banaso kallonta yayi yatsanshi Daya yadaura akan libs dinta shhhh kimin shuru cikin murya me sanyi yake magana bazanyi dinba kasakeni ko in maka ihu kafeta yayi da rikitattun idanunshi kawo bakinshi yayi Dede nata kamar zeyi kissing dinta runtse ido tayi bakinshi yakai kunneta Yana mata magana mekama da rada wayace miki kisa irin wannan kayan akufule tace Ina abinda yadameka ne Ina ruwanka da abinda nasaka Kara matseta yayi yace akwai gashi kinyi tsirara agabana innalillahi wainna ilaijiraji unnn azuciya take magana dama haka yake dama azaad Dan Iska ne jiyanda yakemin maganar banza wayyo Allah na ka kawomin dauki gaba Daya tagama kashe mishi jiki bayaji ze iya saketa nan kusa suna ahaka sukaji takun tafiya wani irin karfine yazo mata ta tureshi da iya karfinta kwashe liffayanta tayi da gudu tashige toilet tana danasanin abinda yakawota dakinsa dubashi daga yau afalo zatake dubashi Yana tsaye yanda tabarshi yakasa Koda daga kafarshine zeenat ce tashigo dakin Yaya Ina fanan najita shuru Kuma abinci zamuci uhmmm yanzu tafita kidubata afalon kasa ko waje okay tace sannan tafice fanan najin fitanta tafito dasauri tana gyara nadin liffayan datayi a toilet hartakai bakin kofa taji anruko hannunta dasauri tajuya jawota yayi tafada kan faffadar kirjinshi cikin kasala yace kidena irin wannan shigan kinji gudun karya bata mata lokaci ne wani yasake dawowa yasamesu ahaka ne tace to saketa yayi harta kusa fita afalon tace allah ya Isa tabamin jiki dakayi tagama magana tana murguda mishi Dan bakinta kafin tafita dagudu Dan karya biyota cize libs dinshi nakasa yayi yafada kan gadonshi Yana kallon celling rufe idonshi yayi shape dintane yahasko dasauri yabude idonshi.


Gyara nutsuwarta tayi kafin tahaura falon ummi anty Amina ce tace Ina kikaje naji tundazun zeenat take nemanki uhmmm Ina falon kasane tana karasa maganar tana inda inda zama tayi ummi fah? tana bacci tashiga zata Dan huta ahankali tace afito lafiya ameen daukan hand bag dinta tayi tace anty Amina zanwuce SE zuwa gobe tofa tafiya tun yanzu eh zanshiga asibiti ne ayyah shikenan se gobe allah yakaimu Ameen fitowa tayi afalon kasa tahadu da zeenat zaune take tana chatting tom madam zeenat sarkin chatt nawuce dama kamar kinsan kenake nema yanzu tafiya zakiyi bamuci abinci ba noo karki damu sewani lokaci fitowa sukayi suna hira hangota zeenat tayi nan take tabata fuska tazo Dede da FANAN ta bangajeta seda takusa faduwa da sauri zeenat ta tarota ke ramlat wannan wani irin haukane iyeee bakiga mutane bane wani kallon Tara saura tamata tana nunata da yatsa keni tsarar kice dazaki tsaya fadamin magana anfada miki kiyi abinda zakiyi ganin abin na neman jawo fadane yasa FANAN ta ja zeenat tana bata hakuri kekuma awa Karar kada Miya shegiya yar matsiyata dukda zagin yabatawa FANAN Rai Amma seta danne tana Jan zeenat ramlat ganin bata kulata bane yasa tace bagidajiya dakin kulani dayau Banga me hanani cin uwarki ba afusace fanan Takoma wajanta tana zuwa batayi wata wata ba ta dauketa da Mari masu zafi har biyu kafin ta nunata da yatsa ke inbakisan darajan naki iyayen ba Ninasan nawa Kuma kece babbar bagidajiya wacce batasan inda yake mata ciwo ba tafiya tayi tabarta agun har titi zeenat tarakota tana bata hakuri akan abinda ramlat tayi bakomai senazo gobe to shikenan semunyi chatt okay tashige napep yaja suka tafi


Duk abinda yafaru akan idon mommy ranta yayi matukar baci har hancinta nafito da hayaki wannan yarinyar tafara wuce gona da iri yata zatasa hannu ta mara lallai taja ruwan dama kanta ciki ta koma tana cika tana batsewa.


Wanka yayi yafito daure da towel akugunshi da yar karama Yana goge gashin kansa zama yayi kan kujeran Dake gaban mirror shafa Mai da perfume yayi kafin yasa kayan bacci yakoma falo yadau laptop dinsa yakoma ciki yazauna yafara aiki Kiran layin zeenat yayi yace tasa akawo mishi coffee β˜• bayan kamar 5mint me aiki takawo Yana sipping Yana aiki.




Bayan fitar fanan asibiti tawuce taje taduba mutane tazo zataje office din doctor ammar ne taci karo da doctor Ib bata fuska tayi ciki ciki ta gaishesa my sweet baby kinganki kuwa bakaramin kyau kikayi ba dole in biya kudin kwalliyan nan ba bukata nagode muje office dina innuna miki wani abu girgiza Kai tayi tace okay bari inje in amsa Kiran doctor ammar SE in sameka a office dinnaka washe baki yayi Jin abinda tace yau gaskiya yanada saa tunda ita dakanta tace zatazo office dinsa wucesa tayi, tayi gaba abinta abakin kofa tahadu dashi Yana rufe office din ah ah fanan kece eh nice dama nazo gunkane gaisawa sukayi kafin yace gashi Kuma zanshiga urgent meeting to shikenan doctor SE gobe innazo okay yau kinje kinduba azaad ne eh naje dama akan batunshi nazo okay muje tafiya sukeyi tafara da am dama sonake inji haryanzu begama recovery bane eh to gaskiya FANAN da Dan saura tukun nan Kinga alluranshima saura na 1week daga nan shikenan kingama hamdala tayi Amma meyasa kike tambayata dasauri tace nooo bakomai kawai inaso injine natafi seda safe to shikenan allah yakaimu kan mangrib Takoma gida tasamu kowa yahallara afalo kallone yadawo kanta oyoyo oyoyo suhaima ce taje ta rungumeta darling sis seyanzu gaskiya nayi missing dinki hhhhh sekace dagaske Danaga kiranki ai sorry banida charge ne to naji zubaida gaishesu tayi suka amsa mata jekiyi sallah kizo babane yayi maganar fuskanshi ahade jiki asanyaye tashiga daki tabbas wani Abu yafaru kokuma tayi laifi alwala tadauro tazo tagabatar da sallah kafin tafito da dogon hijab dinta tazo tazauna akasa tace gani baba wato yanzu FANAN ni ban Isa dakeba kenan ban Isa ince kiyi Abu kiyi ba ko dasauri tadago tana kallonshi mena fada miki kobance miki duk sanda kikaga alamar zakiyi dare awaje ki kira azo adaukeki ba ahankali tace kafada baba kayi hakuri in sha Allah bazan sake ba allah yasa sannan yace bawai batun bazakisake ko Zaki sake ba FANAN tunda kike arayuwarki kintaba ganin munbari kinyi dare awaje girgiza Kai tayi Masha Allah sesau Daya Shima namiki uzurine sbd shine karonki nafarko karnaji Karna gani yanda muke kiyayewa kema ki kiyaye to baba hakan baze Kara faruwa ba allah yasa Ameen suka amsa kitashi kisa muku abinci to abinci tadibo musu tuwon semo da Miyan ganye wucewa daki sukayi gaba Daya jikin FANAN yayi sanyi dafata suhaima tayi kallonta tayi suhaima jikina Yana bani akwai wani Abu Amma sunkasa fitowa sufadamin ajiyar zuciya suhaima tayi tace nima nakula dahakan saboda kafin kishigo sekinga yanda hankalinsu yake atashe gashi wayarki bata shiga baba yayi fada sosai hmm rananma fah dazakuje siyan fruit nace zanje mama tace babu inda zani sau kusan 5 kenan innace zanfita gidansu Amira bayan sallah mangrib ake hanani itakuma tana zuwa karki damu Zakiji komai bata wani ci abincin sosai ba



via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)





Da sunan Allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen πŸ₯°πŸ₯°






Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina Allah yabar zumunci πŸ₯°πŸ€Ž








___________________________________________





Page 1️⃣5️⃣




Goge hawayen Daya zubo a idonta tayi Sannan tace"yanzu duk bawan nan ba muyi isha semu kwanta yau da wuri zanyi bacci" sallah sukayi kafin suka Dan taba hira kirane yashigo wayar FANAN dubawa tayi taga Ashe zeenat ce picking tayi tasa akunne "assalamualaikum zeenat yakike? "Lfy Lau ya gida yasu mama dama ya azaad dazun mungama cin abinci yatashi ze haura sama shine yafadi Amma yanzu ya farfado shine ummi tace nakiraki Dan Allah gobe kizo da wuri"zeenat tagama magana tana jiran amsan FANAN ajiyar zuciya FANAN tayi Sannan tace"Allah sarki in sha Allah zanzo da wuri kigaishe da kowa " sallama sukayi kafin ta ajiye wayar suhaima ce tace"ayyah jikin patient din nakine yatashi eh wlh kekam gobe dole infita da wuri Allah yakaimu Ameen kwanciya sukayi tare dayin adduah.





Washe gari karfe 5:00am suka tashi nafila sukayi kafin aka shiga masallaci bayan sun idarne FANAN tace "bari inje in fara aiki" okay sena fito kitchen tawuce tahada kayan wanke_ wanke tayi tazo tayi shara da mopping sannan tadaura abin karyawa karfe 7:30 tagama komai tashiryasu afalo sannan Takoma tashiga wanka fitowa tayi tasamu suhaima nata sharara baccinta hankali kwance "ke mayyar bacci dallah tashi kije kiyi wanka kizo muyi breakfast" mikewa suhaima tayi tana salati da Mika kafin ta harareta "nifa bansan irin haka dole SE tare zamu karya Ina bacci na me dadi kin wani tasheni" Koh kulata FANAN batayi ba kayanta tadauko a wardrobe Riga da skirt ne na atamfa orange da touch din Baki sakawa tayi skirt din yadan kamata fakin din gashinta tayi tasa ribom Baki harta dauko dankwali zata daura seta fasa, shafa powder tayi tasa kwalli a idonta sannan tafesa turare hijab dinta Baki tasaka dogo harkasa me hannu daukan handbag dinta tayi da plate shoe
Hartazo fita tajuyo takalli suhaima data koma bacci dudduba dakin tayi can taga guntun pure water taje setin fuskanta tadaga ledan tafara sheka mata ruwan afuska azabure ta mike tafara banbami aikuwa dasauri FANAN tabar mata dakin tana dariyan mugunta falo tashiga taje dakin mama haduwa sukayi da mama tana kokarin fitowa gaisheta tayi "nagama abun karyawan" to muje falon suka dawo Basu fi mintuna dashigowa ba su ya Usman suka shigo suna musu "Kai wlh zanbaka shawara ka koma man city kawai" inji ya Usman "allah yakyauta mu ai Madrid bagudu baja da baya karka ga Dan abdulkareem benzema yabar Madrid kuyi tunanin yawargaje zamu dawo" dariya sosai ya al Ameen yayi kude kawai yanzu kunzama losers oho koma de Meye munji gaida mama sukayi kafin fanan ta gaishe dasu amsawa sukayi Al Ameen yace "Ina suhaima bangantaba kode haryanzu tana baccin asara" ya al Ameen natasheta tana zuwa okay zuba musu abincin tayi alele ne da Miya SE farfesu da kunun gyada Basu faracin abincin ba seda baba yashigo duka gaishesa sukayi zama yayi Yana amsawa gaisuwan nasu kallon su yayi duka kafin yace Ina suhaima , suhaima Dake bakin kofan shigowa tace baba gani nan karasowa falon tayi tana gallawa FANAN harara dariya kasa _kasa fanan takeyi Dan tasan abinda ta aikata gaida mutanen falon tayi kafin tazauna suka fara karyawa abinci sukeci Amma daga zaran suhaima da fanan sun hada ido hararanta suhaima takeyi itakuwa FANAN abin dariya yake bata harara suhaima tawatsa mata wani irin dariya ta fashe dashi Wanda seda falon yadauka kowa yatsaya yazuba mata ido takai kusan 3mint tana dariyar kafin ta tsaqaita ganin datayi kowa yazuba mata ido suna kallonta da mamaki ne yasa tashiga nutsuwarta gaba Dayansu sunkasa dauke idonsu akanta mama kam ta gumi tayi tana kallon iKon god baba ne yace "FANAN fatan de lafiyanki kalau" eh baba tana sunkuyar dakai to Allah yasa ya Usman ne cikin zolaya yace " majinyatan mu na gida Dana asibiti Allah yabasu lfy dariya sukayi duka suna Ameen bayan sungama ne FANAN tace zan tafi as usual kudin transport baba yabata Yana mata adduah dawowa lafiya kallon suhaima tayi tace "yar uwa yau ba rakiyane " eh din bazaa rakaba fita tayi tana yar dariya.


Baba ne yace "ohhh FANAN Allah yashiryeki" mama ce ta amsa da Ameen kome yasata dariya haka se Allah ya al Ameen Dake Shan kunu ne yafara fadin "aiduk abinda sukeyi ita da suhaima Ina kallonsu suhaima ce ke hararanta itakuwa hararan ne yabata dariya shine take dariya" hhhhhhh Abin dariya yabasu baba yace "alamu sun nuna yau fa sun kwabe anyi fada kenan ".






Shiga falon tayi da sallama abakinta dukkansu afalo ta samesu Banda azaad Dake dakinshi Yana bacci, yaseer ma yazo Dan agidan yakwana gaidasu tayi kafin tamusu yame jiki amsawa sukayi dasauki alhamdulillah ummi ce tace " ki haura Yana ciki " to ummi haurawa upstairs tayi tashiga part dinsa afalo ta tsaya tana tunanin yatashine ko Yana baccin yankewa tayi baride inje induba ajiye jakanta tayi afalonshi tashiga dakin kwance tasameshi Yana bacci bubbuga filo tafarayi Mr azaad katashi ahankali yafara Bude idonshi dasuka Dan kumbura kadan gashi yayi ja idon shine yasauka akan fuskanta ahankali yamike yazauna abakin gado farar jallabiya ce ajikinshi tunda suka dawo daga masallaci be cire ba yakwanta babu Wanda yayi magana acikinsu tashi yayi yashige toilet zama tayi akan kujera tana jiranshi bayan kaman 30mint yafito sanye da towel direct gaban mirror yaje yagama duk wani abinda zeyi kafin yashige dressing room dinshi FANAN kuwa tunda tazauna tafara game awayarta bata Kara dagowa ba fitowa yayi sanye da Riga armless fari jikin rigan anyi manyan rubuta MAN IS BORN TO HUSTLE da dogon wando na jeans zama yayi akan gadonshi yafara latsa wayarsa sunfi 30mint ahaka gajiya tayi da zaman tace " kasa akawo maka breakfast kayi insamu inma alluranka" ko dago Kai beyiba balle yasan ana mishi magana gajiya tayi takira zeenat" zanma yayanku allura gashi be ci komai ba" to kawai zeenat tace ta katse Kiran 5mint latter tashigo da kayan abinci Yaya mezansa maka be mata magana ba ya mata nuni da ta Bude duka food flask din Bude su tayi kulan farko yam balls ne aciki nabiyu Kuma chips ne dasukaji egg SE na ukun farfesun naman rago ne yaji kayan hadi se tiriri yakeyi nuni yamata da farfesun zuba mishi tayi Ta ajiye mishi a table din Dake gabansa kafin tahada mishi tea tafita. Fanan kuwa tacika fam kamar zata fashe gaba Daya yagama bata mata lokaci sewani Jiji Dakai yakeyi mtsssw tsaki taja Wanda batasan yafito ba dagowa yayi ya kalleta hada ido sukayi takawar da kanta gefe taci gaba da game dinta seda yakwashe mintoci kafin yagama hamdala yayi cikin sexy voice dinshi yace" am done kizokiyi abinda zakiyi I have something to do" sake Baki FANAN tayi tana kallonshi wato shi yanada abinda zeyi nice banida abinyi lallai wannan yacika babban Dan renin hankali mikewa tayi tadau ruwan alluran taja a syringe πŸ’‰ da cotton hannunshi yamika mata ta daure tasamo jijiya kafin tamishi alluran tasamai cotton dustbin taje tayar da syringe din maganinshi taballa mishi tabashi da ruwa yakarba yasha sannan ta tambayeshi "yanzu Meye yake damunka" kamar bazeyi magana ba yace "nothing" fita tayi a dakin tadau jakanta tabar part din falo tadawo tasamesu sunata hira zama tayi kusa da anty Amina suna hira, shigowa tayi falon batare da tayi sallama ba Kai tsaye inda fawwaz yake taje tatsaya " Kai Ina baby yake " juyowa su ummi dasu FANAN sukayi Dan basusan da shigowanta ba sanye take da wando crazy Baki se wata yar ficikan Riga pink kan nan babu Dankwali yasha attachment two color kafarta sanye da takalmi Sau ciki Shima pink fuskan nan yasha uban makeup FANAN kam mamakine yakamata Amma wannan kam arniya ce fawwaz kuwa cigaba da kallon ball din dayakeyi yayi beko dago Kai ba ganin baze kulata bane yasa takarasa kusa dasu ummi "hi guys Ina baby yaje" zeenat ce ta iya " kulata kinbamu ajiyansa ne" to karamar mara kunya banyi Dake ba kikama kanki Dani tam duk abinda sukeyi ummi batace musu ci kanku ba haka anty Amina ma FANAN kam Takoma yar kallo " tunda bawanda ze iya fadamin inda yake zanje indubasa da kaina" takarasa maganar tana nufan part din Azaad ganin baya falo yasa tawuce dakinsa akwance tasameshi zuwa tayi takwanta akanshi tana fadin "baby wake up am here" Bude ido yayi yaganta kwance ajikinshi tashi yayi yadan tureta daga jikinsa Yana fadin "aneesa meyasa Baki da hankali ne wai yanzu haka Kika fito daga gida kamar wata arniya " kallon jikinta tayi tace "baby what's wrong with my dress tell me if there's something wrong on it " takaicine yakamasa wato ita bata masan shigar datayi be dace ba harwani tambaya take what's wrong with her dress unbelievable Kuma wai ahaka ita ze aura yafada duniyar tunani yaji tana fadin "baby when are we going back to US " ke bansaniba ko dole sedani Zaki koma please don't disturb me aneesa kukan shagwaba tafara mishi tashi yayi ya dauki wayarsa yafita falon kasa yadawo tana biye dashi abaya gaida ummi yayi da anty Amina suka amsa yajikin naka dasauki kawai yace pressing phone dinshi yafara karasowa aneesa tayi tazauna a kujeran dayake tamanne dashi tana mishi magana ko kulata beyi ba yaci gaba da abinda yakeyi yaseer ne yace aneesa nikam bakyajin kunyane ga surkanki akusa Amma kina irin wannan abun murguda mishi Baki tayi Ina ruwanka ummi de tashi tayi abunta tayi sama anty Amina ma bayanta tabi yarage su zeenat ne afalon kallo takunna musu a TV tashan MBC action suna kallo areef ne yace " zeenat kaimana tashan MBC 2 nasan yanzu suna day breaking" to tace Dan batama San wani film bane shiga tayi aikuwa sukaga anhasko inda wata horror takecin kayan cikin wani ihu suka fasa da ita da FANAN yaseer da fawwaz mezasuyi inbanda dariya harda rike ciki kallon su kawai azaad yayi yadaga musu tsawa "wani irin haukane wannan" shiga cikin rigan nutsuwar su sukayi gashi areef yace baze canza Tasha ba SE rokonsa sukeyi karshema cillawa fawwaz remote din yayi.ganin hakane yasa FANAN da zeenat suka rungume juna da anyi abin tsoro suyi ihu mazan Kuma SE dariya sukeyi Banda azaad da aneesa datayi bacci tana kwance akan kafadar azaad wani wajan dayafi ko Ina tsoro aka nuna wani mutum horrorin suka kwantar suka dauko katon guduma sukayi kaca_kaca da kanshi yatarwatse wani irin ihu suka buga hannu FANAN takai tana ihu tana nuna TV wani irin spark TV yakeyi Yana kawowa Yana daukewa duk Basu luraba still hannun nata nasetin TV duk motsine da zatayi se tv yayi spark tun Basu ankaraba harsuka dawo da hankalinsu wajan itakuwa batama San tanayi ba dungule hannunta tayi da karfi tsabar tsoro tana kokarin rungume zeenat fat!fat!fat! TV yatarwatse yayi condem SE hayaki yakeyi zaro ido sukayi suka kalli TV sesu kalli FANAN ganin suna kallonta ne yasa tace meyafaru ya yaseer nuna mata TV yayi zeyi mata maganan abinda tayi azaad yayi saurin mishi signal da ido akan yayi shuru domin daga gani batasan tayi hakan ba Amma gaba Dayansu sun tsorata da abinda yafaru karasawa tayi kusa da TV tayi tace "subhanallhi meyasameshi yayi haka" bata gama rufe Baki ba jiri yadibeta zata fadi cikin zafin nama azaad ya rungumota kafin ya Ankara harta Suma daukanta chak yayi kamar yar baby ya kwantar da ita akan kujera ana kwantar da ita su ummi suka fito tana fadin " nikam yaran nan lafiya kuke mana ihu " sauka idonta yayi akan FANAN Dake kwance akan sofa dasauri suka karaso meya sameta fawwaz ne yabasu labarin abinda yafaru dukkansu mamaki yacikasu anty Amina ce tace" to me hakan yake nufi shafa kan FANAN takeyi ahankali Kuban ruwa Mika mata ruwa zeenat tayi shafa mata tayi afuska ajiyar zuciya tayi ta tashi tana rike kanta Dake mata azaban ciwo murya narawa tace "wayyo kaina zefita ya Allah,ummi kaina " kwantar da ita ajikinta ummi tayi "sannu kinji bari Kisha magani zedena to aneesa data danyi baccine tafarka tazo gun azaad baby natafi gida okay kawai yace mata kafin ta tafi ......




Tom semun hadu gobe in da Rai da lfy muhadu a comment section 😍😍😍😍😲



via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)




Da sunan Allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen πŸ₯°πŸ₯°







____________________________________________




Page 1️⃣6️⃣





Duka suna zaune cirko cirko sunyi shuru sunrasa abinyi ahaka har aka kira mangrib mazan duka masallaci suka tafi dakyar suka iya tashin FANAN da

Please Login or Register in order to submit comment