Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bacci yadauketa taimaka mata sukayi tamike tana rike da kanta dakin zeenat sukaje adaddafe tayi sallah tadawo tazauna shuru kanta akasa can Kuma kamar wacce aka mintsina ta tuna gida dawo Dede tayi aidasauri tafito dakin duk sundawo daga masallaci suna zaune afalo tafito gudu_gudu mikewa sukayi suma sun dauka wani abun ne yafaru ummi ce tariketa tana fadin" FANAN lafiya" arude tace " wayyo ummi yau nashiga uku Dama mangrib yayi innalillahi wainna ilaijiraji unnn yanzu mezan fada agida anhanani Kai dare awaje "takarasa magana idonta nazubo da hawaye yaseer ne yace "karki damu kizo sena kaiki inwa Yan gidanku bayani" kallonshi tayi tana girgiza Kai "ya yaseer bazaka gane bane daga zarran 5:40 yayi duk inda nake ana San ran dawowana wlh yau nasan mama da baba zasuyi matukar fushi Dani " tafashe da kuka dukkansu tabasu tausayi rungumeta anty Amina tayi tana rarrashinta, azaad da gaba Daya kukanta yadameshi tacika mishi kunne jiyake kamar zeyi hauka saboda ya tsani kukan mace kamar yarufeta da duka haka yakeji ummi tace" azaad daughter (anty Amina kasancewar itace yar farinta bata Kiran sunanta) yaseer Dani da zeenat zamuje gidansu fanan mukaita gida semu bawa iyayenta hakuri duka sunyarda da shawaranta .




Matukar tashin hankali da firgicine yabayyana akan fuskokin mama da baba gaba Dayansu babu Wanda yake cikin hayyacinsa duk sunfito compound din gidan suna jiran dawowar FANAN mama kam takasa jurewa inbanda hawaye ba abinda takeyi damin kuwa sukadai sukasan mezeje yadawo har inde tabiyo Daren nan tafito suhaima ce take rarrashin mama baba ne yace " nasan yata da gangan bazata tabayin abinda ze batamin rai ba da dawowarta awannan dare gwara ta Kwana aduk inda take domin nasan tana hannu nagari fitowarta awannan dare barazana ce ya Allah ka kawo mana sauki " ya al ameen,ya Usman, suhaima duk da hankalinsu atashe Amma kansu adaure yake meyene suke gudun faruwansa domin sun sasu aduhu shuru sukayi suka zubawa sarautar Allah ido.




Bayan sun idar da sallah isha ne suka fito da motoci Dan sukai FANAN gida itakam tsabar tsoron abinda zata tarar agida yahanata magana fitowa sukayi daga falon shiga cikin motar sukayi ummi da azaad da FANAN suna motor Daya SE anty Amina da yaseer SE zeenat motar yaseer ce tafarayin gaba, me gadi yawangale musu gate suna fita na azaad yabi bayanshi guguwane yatashi lokaci Daya Wanda yasa seda suka Dan tsaya domin jiran tsaqaitawansa yafi 10mint kafin yatsaya .







Hhhhhhhhhhhhhhhhhhh TAFITOOOOOO! TAFITOOOOOO SARAUNIYAR tafitoooooo tabayyana burinmu yakusa cika shugabansu ne yake magana Yana kallon madubin Dake gabansa mutum ne zaune akan kujera ta sarauta kansa da kaho๐Ÿ‘น๐Ÿ‘น Daya Baki Daya ja, katone Wanda zaa iya kiransa da basamude halittarsa rabi mutum rabi daba Yana sanye da jan Riga juyawa yayi ga mutanen sa dasuke irinsa sede dukkansu babu Wanda yakaishi girma daga musu hannu yayi kafin yace abinda muke Jira tsawon shekaru 18 yau yagabato garemu ihu suka farayi mara dadinji suna kururuwa shagali sukeyi bana wasa ba.






TANZARZAR nahango Yana zaune akan kujeran mulkinsa tare da Yan kungiyarsa dagaba Dayansu suke sanye da bakaken kaya jikinsu duk gashi๐Ÿ‘บ๐Ÿ˜ˆ Kai bakyaun gani kansu akasa idonsu arufe hannunsu ne dayake dauke da zuku zukun yatsu suka daga sama suna wani irin jujjuyashi suna lankwasashi kamar wasu masuyin rawa gaba Daya wajan yaturnuke da hayaki SE wani irin dariya sukeyi Wanda idan bil adama nawajan baze iya jurewa ba. Cikin wata irin murya me ban tsoro tanzarzar yace" tafito dole mune zamu mallaketa domin tana kunshe da dukan wata irin karfi da jaaazana atare da ita duk wani bayanai Yana dauke da ita tundaga lokacin datake ciki har izuwa yanzu abun da muke Jira yazo garemu hhhhhhhhhhhhhh.








Wani irin gurine Daya kasance komai fari kamshine me dadin gaske ke tashi bana tunanin nan duniyar mutane ne kowa tafiya yakeyi akan iska masu firewa ma sunayi furanni ne tako Ina masu gwanin burgewa Wanda bazakaso ace inde kana wajan nan kabar gunba hango tarin mutane nayi atare Wanda a iya hasashena sunfi karfin dubun nai karasowa nayi sanye suke da fararen kaya komai nasu fari bantaba kallon masu kyau da kyawun halitta irin suba mazansu da matan su , wani irin kujera nagani Wanda yake na zinari yasha ado da gwala gwale wani irin sheki yakeyi wani tsohone yataso me matukar kyau yatsaya agabansu Yana fuskantar gaba Dayansu kafin yafara dacewa " Ni Abdul_shakur Ina me sanar daku yaune ranar da SARAUNIYAR mu ta taka mataki nafarko arayuwarta Wanda ze kusantota damu sannan ze kusantota da wayancan azzaluman makiyanmu nasan yanzu zasu fara kokarin Kaimata farmaki saboda yanzu ne suke da iKon yimata abinda zasuyi dukda ita haryanzu bata gama sannin wacece itaba Kuma menene take dauke dashi ba batasan ma yazata fara amfani da karfinta ba Amma baze dau lokaci ba jaaazana ze bayyana agareta dolene mukareta da iyayinmu " kammala magana yayi fuskanshi dauke da murmushi dakuma damuwa (iKon Allah wannan aisede aljani Taya lokaci Daya Abu biyu zasu bayyana afuskan mutum Tabb nide nayi nan)๐Ÿƒ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ๐Ÿƒ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ๐Ÿƒ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ.





Tafiya suketasha akan titi kwatance gidansu tayiwa azaad har suka iso kofar gidansu fitowa sukayi daga motar yaseer ne yayi knocking gate din FANAN buya tayi abayan ummi ya Usman ne yabude sukayi musabaha "dama Baki kukayi Muna tare da FANAN " cewar yaseer ya Usman yanajin an ambaci FANAN yace "Bismillah kushigo " dasauri yakoma yafada musu sunyi Baki shigowa sukayi da sallama abakinsu falo suka shigo ummi ce tashigo akarshe FANAN Dake bayanta ne tayi sallama ahankali gaggaisawa sukayi ganin yanda FANAN ta takurene yasa mama tamata alama datazo mikewa tayi taje gun mama ta rungumta cikin muryan kuka tace " Dan Allah kuyafemin nasan nayi muku laifi nakarya dokan dakuka gindaya min " shafa bayanta mama takeyi " kedin yace me biyayya munsan bazaki tabayin abinda ze bata mana ba kedin ta musamman ce yata" zuba musu ido mutanen falon sukayi suna jinjina irin soyayyan Dake tsakanin uwa da yarta gyaran murya ummi tayi cike da Kamala tafara Basu labarin abinda yafaru daga spark din da TV yayi harzuwa suman datayi har izuwansu gidan nan bakaramin tashin hankali suka shigaba abinda suke gudu yafaru baba ne yamike yafara safa da marwa Yana nanata Kalmar innalillahi wainna ilaijiraji unnn gumine yawanke mishi fuska kafin yakalli mama yace" mamansu abinda muke gudu yafaru abinda muke tsoron tsawon shekaru 18 yafaru ya Ubangiji Allah katarwatsa mumunar kudirinsu akan wannan baiwar taka dabataji ba bata gani ba ka tsareta da tsarewarka " amsawa sukayi da Ameen ya hayyu ya qayyum duk da yasasu aduhu komawa yayi yazauna fanan ce ta rarrafo gabanshi tarike hannayensa" baba Dan Allah kutaimakamin ku fadamin gaskiyar abinda yake faruwa" shafa fuskanta yayi karki damu lokaci yariga da yazo Amma sekin Jira kadan duka mutanen falon jikinsu yayi sanyi duk da Basu San meyake faruwa ba Amma alamu yanuna wannan ahalin suna cikin hard time.

Azaad cikin cool voice yafara magana" idan badamuwa zamu iya sanin abinda yake faruwa" girgiza Kai mama tayi tace" bazeyu muyi muku bayani ba domin yin hakan zezama bayyanar FANAN ne cikin sauri da karfi" kamarya bayyanar FANAN bayan gata nan abayyane agabamu Muna kallonta zeenat takarasa maganar tana binsu da kallo duk da basa cikin yanayi me dadi Amma hakan be hanasu murmusawa ba ummi ce tamata signal da ido akan tayi shuru mama ce tamike takira FANAN da suhaima biyota sukayi kitchen drinks tabasu dasu fruit a trays suka kawo falo Bismillah suka musu Dan tabawa sukayi kadan kafin ummi tace" yakamata mu gabatar muka da kanmu sunana Aysha Muhammad azaad mainasara sannan tanuna anty Amina itace first born Dina sannan tanuna azaad Shima danane shine nabiyu Wanda FANAN take kulawa dashi se wannan tanuna zeenat itace auta ta akwai yayyunta maza guda biyu a gida SE wannan Shima Dana ne Dan kawata ne Kuma abokin azaad tun suna yara " Masha Allah, Ubangiji Allah yaraya miki zuriyarki yakara hada kanku babane yake musu adduah duka falon suka amsa da Ameen. Ganin dare nayi ne yasa suka ce zasu tafi sallama sukayi mazan suka rakasu har bakin motar su suka tafi.


Bayan sun dawo ne baba yake ma FANAN Yan tambayoyi "mekikeji ajikinki yanzu karki boyemin" kallonshi tayi cikin nutsuwa tace " banajin komai baba " ajiyar zuciya suka sauke atare shida mama sude sunzuba musu ido kawai tunda sunki fada musu komai, to shikenan kowa yaje yakwanta dare yayi seda safe sukayi suka shige daki FANAN da suhaima hira sukayi kafin suka kwanta tare dayin adduah bacci........









Meye FANAN take dauke dashi ? Menene jaaazana dasuke son karba daga gareta? Suwaye wayanda suke shirya farmakan FANAN??? Shin wasu irin kungiyoyi ne wannan??? Meye abinda Tanzarzar yake bukata atare da ita?????? Taya akayi fanan takasance sarauniya ๐Ÿ‘ธ????????




Kubiyoni domin kuji amsoshin tambayarku senajiku a comment section ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜











via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

๐Ÿง‘โ€โš•๏ธ๐Ÿง‘โ€โš•๏ธ NIDA PATIENT DINA ๐Ÿฉบ๐Ÿฉบ


Story Written by (MRS ๐ŸŒน ISHAM ๐ŸŒน)





Da sunan Allah me rahama mejinkai ๐Ÿ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen ๐Ÿ™๐ŸŒน๐ŸคŽ







Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina Allah yabar zumunci ๐Ÿฅฐ๐ŸคŽ







____________________________________________






Page 1๏ธโƒฃ7๏ธโƒฃ






5:20am suka farka daga bacci sallah sukayi bayan sun gama azkar ne FANAN ta tashi ta haye gado taci gaba da bacci saboda bacci takeji sosai suhaima ce tafito tayi aikin gidan gaba Daya tamusu breakfast harsun fara karyawa mama tace "suhaima Ina fanan din take " Takoma bacci cewar suhaima Jin hakan yasa Basu Kara magana ba sukaci gaba da karyawa , har karfe 11 tagota bata tashi ba time din su baba duk sun fita yarage daga mama SE suhaima da fanan Dake bacci. Tashi tayi daga bacci tana salati da Mika zuro kafanta kasa tayi gashin kanta duk ya babbaje toilet tanufa bayan 7mint tafito daure da towel gaban mirror tazo ta shafa man gashi tasa cum ta tajeshi ta hadasu guri Daya ta daure Mai Tashafa ajikinta sannan tadauko kaya wando ne falazo me manyan fulawa SE riga body hook ja tasa hula Baki bakaramin kyau tayi ba wayarta tadauka takunna ganin time din tayi "wai gaskiya yau nayi bacci sosai" falo tafito tasamu mama da suhaima gaishe da mama tayi kafin tazauna sallaman Amira sukaji tashigo gidan afalo tasamesu tagaida mama, besty ykk suhaima ya gajiya zama tayi suna hira dasu tana rike da yar karamar bakar jaka ahannunta kallon mama tayi tace " mama dama nazo in tambayeki ne FANAN zata rakani gidan anty fati hajiya ce ta aikeni " mama har cikin zuciyarta bataso FANAN tafita Amma kawai tace "to shikenan Amma karku Dade kunji " to sukace suhaima ganin zasu tafi subartane yasa tace nima zani bari in dauko hijab dina" sallama sukawa mama suka fito su uku suna tafiya suna hira Amira ce tace " bakusan meyafaru jiya ba hajiya ta aikeni cafene nayarda kudin duka dakyar na iya dawowa gida Dan banma San yazanyi ba" suhaima tace"wai garin Yaya haka katuwa Dake kika zubar da kudi " lallai kam to ai tsautsayi bata yanda bata kamawa Kuma Allah yayi ba rabo bane " cewar FANAN "ato fada mata de sukaci gaba da tafiya suna hira , wata corner suka sha aikuwa turus suka tsaya sakamakon abinda suka gani karnuka ne guda 3 suna kwance abinsu , tsoro ne yarufe su "wayyo Allah kare yazamuyi mu wuce nan Dan Allah gashi hanyar dayane "amira tagama magana tana rike hannun FANAN Da karfi FANAN cire takalmanta tayi tarike ahannun tafara fadin " karkuja abinda zesa karnukan nan subimu muwuce kawai karma ma mu nuna mungansu kundeji Ina" takarasa maganarta tana kallonsu to shikenan tafiya sukeyi sanda sanda kamar wasu marasa gaskiya harsun kusa wucesu suhaima ta dantabo Amira, ke Amira kindauka karene aikuwa ihu tafasa tasa gudu karnukan๐Ÿฆฎ na ganin haka suka fara haushi kan kace me sun bisu gudu sukeyi kamar kafarsu ze fita fanan kam da take rike da takalmanta ko juyawa batayi ba balle ta kallesu gaba Dayansu rabuwa sukayi kowa hanyanta daban tabi Ashe karnukan ma sundade da Dena binsu Basu sani ba Amira ce tajuya taga basa binta tsayawa tayi tana Maida numfashi hango bishiya tayi taje tazauna agun tana tunanin inasu FANAN sukayi, ke suhaima dataga gudun baze kaita ba kawai tafada wani gida suna ganin tashigo da gudu Suma sukashige daku nansu a tamanin๐Ÿ˜‚ can wata tace baiwar Allah meyake faruwa ne awajan cikin Maida numfashi tace "wlh karnuka ne suka bimu "sake Baki sukayi suna kallonta yanzu akan kare kike irin wannan gudun lallai kam sannunki fitowa tsakar gida sukayi Daya daga cikin matan gidan taleka waje tace" sunkoma bakowa awajen sallama tamusu tafito tana ta leke_leke tafiya tafarayi yanzu yazanyi innemo su Amira gashi nabar wayata agida yanke shawara tayi gwara in koma gida seyafi min takama hanyar gida , gudu takeyi kamar Wanda Zaki yake bi harta hau kan titi bata sani dukda titin shuru ba motoci, tafiya yakeyi a motor kamar walkiya tagilma wul๐Ÿƒ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ ta gabanshi taci gaba da gudunta birki yataka Yana mamakin wacece haka take wannan uban gudun duk yanda akayi wasu ne suka biyota, bin bayanta yayi da mota harya iso kusa da ita da sauri yafito gashi taki tsayawa taku uku mekyau yayi yariko hijabinta yajawota baya aikuwa kamar wacce take Jira Takoma bayansa ta kankameshi tana fadin " kataimakeni zasu kamani " sa hannu yayi yajawota yadawo da ita gabanshi zaro ido yayi ganin itace " ke Meye kikeyi akan titi kamar wata mahaukaciya kalan motar yabigeki ko " Jin daddadar muryanshi ne yasa tadago ido cikin muryan tsoro tace " Mr azaad wlh karnukane suka bimu zasu cije mu Dan Allah kataimakeni " zuba mata ido kawai yayi tsaban takaici yarasama bakin magana yarinyar nan da kanwarshi ce irin dukan dazemata seta koma hankalinta yanzu dama duk uban gudun nan datakeyi WA karene ba abinda yakeyi Banda jefa mata harara gashi a ido de kamar wata me hankali Jan hannunta yayi yaje yabude motar yajefata ciki kafin yashigo yaja be tsaya Ako inaba SE akofar gidansu. Ahankali yace "saukamin a motar tunkafin in karkaryaki " dasauri tasauko tana nagode Mr azaad kaceci rayuwata tana magana tana haki shiga gida tayi abunta , shide lamarin yarinyar nan mamaki yake bashi daga gani an sakalta tane tsaki yaja kafin yaja motar shi yayi gaba.


Tundaga tsakar gida takejin muryan Amira da suhaima suna bawa mama labarin abinda yafaru shigowa falon tayi tana galla musu harara " kufa kwata kwata bakwajin magana seda nace mutafi ahankali Amma seda kukasa suka bimu" zama tayi taci gaba da Maida numfashi"nikam garin Yaya muka rabune kowa yadawo daban daban " inji suhaima aikuwa dariya suka fashe dashi ba qaqqautawa seyanzu ma suke tuna irin gudun dasukayi dariya sukeyi kamar cikinsu zeyi ciwo hhhhhhhhh ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ mama kanta abin yabata dariya dama tunda tagansu Daya bayan Daya jikinta yabata wani Abu Ashe karnuka ne suka fafuresu Kai " to yanzu yabatun aikan hajiyar taku kunkai dinne?? mama ce take tambayarsu " Ina mukaga takai aika " nikam ai yau senayi jinyar kafata gaskiya FANAN tagama magana tana mamatsa kafanta




๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿฆฎ๐Ÿฆฎ๐Ÿฆฎ๐Ÿฆฎ Gaskiya yau dog sunyi aiki

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

๐Ÿง‘โ€โš•๏ธ๐Ÿง‘โ€โš•๏ธ NIDA PATIENT DINA ๐Ÿฉบ๐Ÿฉบ

Story Written by (MRS ๐ŸŒน ISHAM ๐ŸŒน)




Da sunan Allah me rahama mejinkai ๐Ÿ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐ŸคŽ







Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci ๐Ÿฅฐ๐ŸคŽ







____________________________________________





Page 1๏ธโƒฃ8๏ธโƒฃ






"Gaskiya nikam yau senayi jinyar kafata " FANAN tagama magana tana mamatsa kafanta din datakeji Yana mata zugi tsabar gudun dasu kasha, uhmmm Amira ce tamike tana fadin "gwara daku nide bari inkoma gida kar hajiya taga na Dade tayi tunanin Kona tafine" saka hijab dinta tayi tamusu sallama ta tafi sukuma suka cigaba da hiransu.



Driving yakeyi Yana Dan duba agogon Rolex Dake hannunshi ganin dayayi 11:00 saura ne yasa yadanyi tsaki ya tsani bata lokaci saboda komai nasa akan time yakeyi kowani lokaci Yana basa mahimmancisa , gashi meeting zetafi haduwan dayayi da FANAN ne tabata mishi lokaci. Abakin gate din Government house yatsaya Yana horn ga sojoji awaje suna aikinsu sanin sunsan shidin wayene shisa Basuyi gigin tareshi ba cikin sauri gate man yabude yashiga packing space yaje yayi packing yafito Yana sanye da suit ruwan toka ga bakin glass manne a face dinshi fuskan nan a murtuke kamar Wanda aka aikowa da sakon mutuwa Yana tunkaro bakin meeting room din me gadin wajan yabude mishi yashiga , samunsu yayi gaba Daya sungama hallara shi kadai suke Jira ko kallonsu beyiba yasamu waje yazauna kallon me girma gomna yayi ciki ciki yace " barka da warhaka excellency" fuska asake yace " barka de my son " be amsa Shiba yaci gaba da danna wayarsa cikin bacin Rai alhaji lamido yace " lallai yaro ka girma tabbas kayi girman da bazaka iya gaidamu ba saboda karenamu kana ganin tsayinka yazo Dede da namu" kallonsa azaad yayi kafin yayi killer smile dinshi Wanda aduk lokacin dayayi irin wannan murmushin bakin ciki ne yake kamasu suji kamar su shakeshi yamutu kowama yahuta. Harzuka alhaji lamido yayi zesake magana alhaji sambo daurayi yayi saurin rikeshi Yana fadin " kaikuwa mezesa katsaya kana kula Dan cikinka" dukansu kallonshi sukeyi shikuma ko ajikinshi duba time yayi kafin yadago calmly cikin kwanciyar hankali yafara magana" kunci 40mint acikin 2hours din da kuka bukata awajena nazo Kuma naga kamar you have nothing to say idan babu nizan wuce yanzu saboda inada Abubuwa masu mahimmanci dazanyi " yagama maganar sa Yana cigaba da danna wayarsa gyaran murya me girma gomna yayi kafin yabude taro da adduah yamaida kallonsa kan AZAAD dayayi relax yana pressing phone dinshi sannan yace "AZAAD MUHAMMAD MAINASARA Ina bukatar hankalinka anan " yayi maganar Yana zuba mishi ido ajiye wayar yayi yadaura Daya kan Daya yazuba musu ido. Sauran kuwa zuciyarsu ne take tafarfasa tsananin tsanan azaad ne yabayyana afuskansu , excellency ne ya gyara mic๐ŸŽค din gabanshi yacigaba da magana" wato dalilin da yasa aka hada wannan Taron shine asamo masalaha tsakaninka da Yan uwanka Yan kasuwa domin kuwa sunkawo kararka kan cewa kana son tarwatsa musu kasuwancin su ta hanyar sassauto da farashin kayan company ka komai karage masa kudi tayanda ake kokarin Dena siyan kaya a company's su saboda arhan da naka yayi ko zaka iya mana dalilin dayasa kake haka azaad Muhammad "

Bayan yagama Jin bayanin da gomna yayi ne yasa yayi yar murmushi dama yasan zaa rina domin kuwa wannan shine karo na 7 sunasanyi zama dashi Amma yanuna musu bayida lokacin haka shisaka suka kawo karanshi wajan excellency, zamanshi yagyara kafin ya seta mic din da kyau yafara magana cikin Isa da mulki " da farko de danasan akan haka aka kirani nan wajan Dan abatamin lokaci to bazanzo ba, na biyu Kuma karata da kuka kawo Kuma akan yanda nake gudanar da kasuwancina wannan bekamata yazama matsalarku ba yanda nagadama nayi niyya haka zansiyarda kayana Kuma kuje kusiyar danaku aduk farashin dakukeso , na uku ko kyauta naraba kayan banida matsala da hakan saboda riba sam baya gabana ni inada kudaden dazan iya barin kayan company na ata rabawa talakawa har natsawon shekara 10 ko fiyeda hakan" yagama maganarshi Yana gyara necktie din wuyanshi kafin yaci gaba da danna wayarsa. Tunda yafara magana alhaji Ibrahim tijjani (mahaifi agun aneesa) ya kafeshi da ido Yana aiyana ta idan ze bullo mishi .
Excellency ya jinjina da taurin Kai dakuma ranshin tsoro na azaad saboda yasan irin hatsarin dasu alhaji Ibrahim tijjani da alhaji sambo daurayi suke dashi Amma shi kwata kwata bayajin tsoron haka, ajiyar zuciya yayi kafin yace " azaad baka mana kwakwaran bayanin dazamu gamsu dashi ba" cikin kakkausar murya yace" babu wani bayanin dazanwa wani anan saboda you don't owe me any explanation" afusace alhaji sambo yamike yabugi table din yace " kai karamin kwaro kayi kadan katsaya kana juyamu yaushe kazo duniyar to wallahi tallahi kabi asannu karkasa rayuwarka ahadari domin bakasan dasuwa kake jaba " yagama magana Yana diri kafin alh lamido yace" ku kyaleshi de mugani ko tusa ze hura wuta " dukansu dasuke magana beko dago kansa ba balle susa ran zetanka musu ba, girgiza Kai alh Ibrahim tijjani yayi yace" azaad yata tana matukar sanka bazanyi abinda itama zatasha wahala ba Amma kasani kayi adduah allah yasa kana Daya daga cikin masu tsawon Rai sirkina" dariya meyar sauti yayi Wanda yakara masa matukar kyau mikewa yayi yayi da murmushi akan fuskanshi yadauki wayarsa kafin yace" meyi baya fada ai zanfijin dadin ku aiwatar da abinda kuke fada Amma kuntsaya kunata haushi kamar wasu kana nan karnuka zanso kununamin ku Yan halak ne " yakarasa Yana tafiya alh lamido ne cikin daga murya yace "Kai azaaaaaaaad dawani irin action azaad yajuya yadaura yatsanshi Daya akan libs dinsa shhhhhhhhhhhhhhh๐Ÿคซ sannan yace " idan Ina waje baa daga murya ko kuma dass ya kyasta yatsunshi guda biyu suka bada sauti" gaba Dayansu shuru sukayi kamar wayanda ruwa yashanye su, fita yayi daga meeting room din ya fisgi motar shi Yana driving Yana murmushin da shikadai yasan maanarshi , kamar ance yakalli mirror motar yaga katuwar trailer tabiyoshi da mugun gudu shafa sajen fuskanshi yayi yasake wata kayittaciyar murmushi Kara speed yayi Yana gudu kamar Wanda zefire sama drivers din trailer ganin dasukayi yabacewa ganinsu yasa suka packer suna tunanin ta Ina zasu samoshi fitowa sukayi daga motar suna Kunna sigari kamar daga sama dayan yaji anyi sama dashi anbugashi dakasa taka ruwan cikinsa azaad yayi dakarfasa dayan da gudu yazo yacakumeshi tabaya juyawa yayi yakai mishi kyakyawar naushi afuska nan take yafadi kasa hancinshi da bakinsa na zubar da jini komawa kan na farkon yayi yamishi mugun duka kafin yakarya mishi kafan hagu da hannun dama Shima dayan hakan ya mishi Sannan yazauna akan wata dutse yadauki wayarsa acikin aljihu yakira police station sukazo suka kwashesu shikuma yakoma gida,. Yanda abun yafaru bayan yakara gudun speed din seda yatabbatar da yamusu Nisan dabazasuyi tunanin binshi ba shikuma yayi xagaye yakoma bayansu can nesa ya hangosu suna busa sigari anan yayi packing motar shi yakaraso gunsu batare dasun sani ba.



Adamawa Yola



Alhaji badamasi me ruwa ne zaune shida ahalinshi afalo suna hira lura yayi da nusaiba dataketa bata fuska yasan abinda yasata hakan Dan taba Madina yayi yace kalli yarki tabe Baki tayi kafin tace " to alhaji aikasan abinda kakeso Amma kahanata yazatayi to " takarasa magana tana hada fuska Kiran sunanta alhaji badamasi yayi my nusy tashi kizo tasowa tayi tazo tazauna akan kujeran dayake kafin yafara magana " nusaiba meyasa kikeson wahalar dakanki akan Wanda bemasan kinayi ba kindauki son azaad kin kwallafawa ranki bayan kinsan ko kallo Baki isheshi ba" dago Kai tayi dad ni ahaka nakesonshi Kuma nasan zan aureshi SE yanzuma na kare mata kallo fara ce soll doguwa batada wani shape irin na mata tana da dogon fuska da ido madedeta se hanci dakuma Bakinta Yana da Dan tudu ataikaice de bawata kyakyawar azo agani bace kawai de farin ne yaceceta tunda dama maza sunce( fara doguwa ko maiyace suna so๐Ÿ˜‚๐Ÿคฃ) haidar dakejinsu yadoka uban tsaki wlh nusaiba Bakida hankali azaad din da wacce aka musu baiko ma be kulata ba seke toseki bar garin mugani ai , "Kai Dallah rufewa mutane Baki ina ruwanka da abinda takeso kabi kasa mata ido kahana yarinya sakatt to bari kaji inde gombe ne gobe goben nan zata tafi " Madina tagama magana tana hura hanci hajiya Hussaina de bata tanka musu ba fruit dinta kawai takesha

Ahalin alhaji badamasi me ruwa kenan matanshi biyu hajiya Hussaina itace uwargidanshi SE Madina tabiyu sunkasance masu Hali mabanbanta hajiya Hussaina bata da damuwa ko kadan hasalima batason yawan rigima akasin Madina da takasance masifaffiya ta gidan gaba ko alhaji badamasi kanshi be tsiraba, haidar 27yrs,hibba 20yrs SE autansu Sadiq 16yrs sune wayan nan sune yaran hajiya Hussaina, nusaiba 19yrs SE kaninta Abdul 12yrs su biyu Madina tahaifa

"Shikenan nusaiba kishirya gobe zakibi flight โœˆ๏ธ

Please Login or Register in order to submit comment