Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda tacemin Dan Iska zataga iskanci " bata hanya yayi tawuce tana Harare_harare ita kadai murmushi yayi inya tuna irin hukunci daze mata nan gaba bazata kara cewa wani dan Iska ba balle shi. Shige falo tayi ganin basa falon kasa yasa tahaura sama aikuwa anan tasamesu Amma Banda ummi da anty Amina data koma gidanta, zeenat ce tafara ganinta tsalle tayi tafada jikinta suka rungume juna " wayyo kawata gaskiya nayi missing dinki sosai yau nake cewa zanje gidanku" hararanta fanan tayi " uhmmm sekace dagaske aida kinyi niyya Dana ganki kafin inzo ninayi fushi malama ban hanya in wuce " areef da fawwaz se dariya suke musu jin draman su areef ne yace " tabb gaskiya fanan karki yarda datayi niyya aida tazo " " to sannu dan hana ruwa gudu wato zaka hada bom ko!?" Cewar fawwaz dariya sukayi Jin dogon tsakin da nusaiba tajane yasasu juyawa suna kallonta, fanan ganin bakuwar fuskane yasa tace "mata sannunki" ba yabo ba fallasa ta amsa da "yawwa" jan hannun fanan zeenat tayi zuwa falon ummi samunta sukayi tana rike da Qur'anic tana Karatu zama sukayi suna sauraron kira'anta medadin sauraro sunfi tsawon 20mint kafin ta dasa ayah, kallonsu tayi murmushi dauke afuskanta tafara magana" fanan dama kina tafe kenan" cike da kunya tace"iyi ummi! Ina kwana " lfy Lau ya mutanen gidan" kowa na lfy " Masha Allah kin dubashi din ne!? Gyara zama fanan tayi kafin tace " ah ah nazo zanshigo muka hadu dashi kamar akwai inda zashi" okay, hiransu sukaci gaba dayi.


Mommy da aneesa nahango zaune akan kujera mommy nata kimtsawa aneesa makirci da yanda zatayi danta dinga jan hankalin azaad yadawo kanta " yanzu abinda nakeso dake kitashi kitafi part dinsu kije wajenshi kiyi duk abinda nafada miki saura kiyi falling dina " Mikewa aneesa tayi tadauki wayarta tabar part din, tadoshi part dinsu ummi tsayawa tayi daga bakin kofan falo tana kallon nusaiba da ita kadai tarage a falon tana chatting shigowa tayi taje ta zauna a kujera dake facing din nusaiban , tun tsayuwarta abakin kofa nusaiba taganta ko dago Kai batayi ba tacigaba da chat dinta , ganin datayi nusaiba taki kulata ne yasa tace" ke uban me kikazoyi a gidan nan " kallon renin hankali nusaiba tawatsa mata kafin tace " kedin uban meye yakawoki gidan nan din? " gyara zama aneesa tayi tafara magana"aini inada right din da zanzo gidan nan aduk lokacin danake so Kuma intafi aduk sanda nakeso tunda very soon am going to be their daughter in_law Kinga gidan nan yanzu nafara zuwa " wani irin kululun bakin ciki ne yatokare wuyan nusaiba " hmmmm kikace Zaki zama surkansu ko to bari mugani mana ko zaayi auren, aneesa inkinga kin auri azaad to sede ko in mutuwa nayi " dariya aneesa tafashe dashi " nusaiba kenan ke yarinyace haryanzu to bari infada miki in duniya da abinda yake cikinta zasu hadu banga abinda ze fasa aurena da azaad ba" ajiyar zuciya nusaiba tasauke cikin izgili tacigaba da magana" aneesa inasan ki rubuta wannan a littafi ki ajiye ko uban daya haifeki be isa yasa ayi wannan auren nan ba wallahi tallahi inharde ban mallaki azaad amatsayin mijina ba to kema bazaki taba auran saba har abada kinji narantse miki " a hassale aneesa ta shako wuyan rigan nusaiba " nusaiba kinyi kadan ki dakatar da aurena da azaad tunda akamana baiko Kuma anwuce layin banza jaka mebin namiji " dauketa da mari nusaiba tayi tana mejin zafin zaginta datayi, nan take suka kaure da dambe , dambe sukeyi bana wasa ba , tsaye yake abakin kofa ya harde hannunshi akirji yazuba musu ido suna dakuwa daga bisani yakoma part dinshi yadauko belt din fata Wanda a ido ma kadai kana ganinta kasan zatayi masifar zafi ajiki, yadawo falon tsaban yanda sukecin uban fada basuma san dazuwanshi ba saukan belt suka faraji ajikin su baji ba gani ihu suka farayi suna bashi hakuri be saurara musu ba yaci gaba da jibgarshi dan yanzu iskancin nasu yafara ya ishansa sun kuresa.
Fanan ce tamike zumbur takara kasa kunne domin inba gizo ba kamar ihu takeji a falon kasa kallonta ummi da zeenat sukayi suna tambayarta lafiya " ah ah ummi ba lafiya ba ihun mata nakeji a falon kasa kamar ana fada kowani abu" Suma mikewa sukayi da sauri suka nufa downstairs din karo sukaci dasu areef dasuma hayaniyar ne yafito dasu tundaga nesa suka hango azaad ya ritse aneesa da nusaiba Yana bugu kamar yasamu yayan cikinsa dagudu fawwaz yaje yarike hannunsa dago kansa yayi ya mishi mugun kallo ja baya fawwaz yayi atime din su ummi sun karaso cikin sauri taje tarike belt din fuska adaure tace " haba son meyasa zaka musu irin wannan dukan dan fisabilillah kalle yanda kafasa musu jiki" kallon ummi yayi data hada fuska tana kallonshi sosa sajenshi yayi sannan yace" ummi bakisan meye nasamesu suke aikatawa bane dambe fa sukeyi shisa nace to bari tunda duka sukeso bari inmusu me dalili" girgiza Kai ummi tayi batasan yaushe azaad ze canza ba mutum kenan ko kadan baya daukan reni Kuma tanada yakini yanzu da awaje yagansu suna wannan fadan wallahi kota kansu bazebiba sede su kashe kansu amma dake cikin gidane hayaniyarsu zedameshi shisa yamusu mugun duka " to naji koma de miye bekamata ka musu irin wannan dukan ba kajiba jikin fiance dinka yanda kamata duba jikin nusy mafah " kara tsuke fuska yayi yace " banasan kara kallon fuskan ku agidan nan kowacce ta tattara takoma gidan ubanta inkuma ba hakaba zakuyi bayani" tunda suka sauko kasa fanan ke boye abayan ummi takasa fitowa dan wani irin tsoron shine yakamata se zare manyan idonta takeyi dama haka yake da mugunta lekasu aneesa dasuke kuka tayi jikinsu yayi jina_jina Dan duka yamusu kamar wanda aka aikosa bakaramin tausayi suka bata ba , duk abinda takeyi yana kallonta dariya taso tabashi yanda yaga take zazzare ido ga tsoro ga rashin kunya, zeenat de inbada murmushi babu abinda takeyi dan yau jitakeyi kamar ta goya azaad abaya dan yabiyata dama bakaramin haushinsu takeji ba. Wucewa part dinsa yayi seda yayi wanka tukun yakira layin zeenat yace tacewa yarinyar tazo tasameshi,suna tsaye suna jimami zeenat tace mata" Yaya azaad yace kije kidubashi yagama" seda gabanta yafadi Jin sunan azaad da zeenat tafada Kuma gashi wai ita yake Jira babu yanda ta iya haka takama hanyar zuwa part dinshi shigowa falon tayi Jin alamun babu alamar mutum yasa tashiga dakinsa da sallama abakinta zaune yake akan kujeran dakinsa da table agabanshi se laptop dinsa dayake aiki acikinsa dagashi se short da singilet idonshi sanye da farar glass kasa_kasa ya amsa sallaman yana cigaba da aikinshi kasa mishi magana tayi dan yau taga true color dinshi tana tsaye abakin kofa seda suka kwashe kusan 30mint ahaka kafin yakashe laptop din yarufe yadago yakalleta " in bazakiyi abinda yakawo kiba barmin daki " cikin sauri tashigo taje tabude dirowan da kayan maganinshi da alluransa suke tafito dasu tana jan ruwan allura a syringe tana kallonshi gaba daya atsorace take gani takeyi kamar ze rufeta da duka itama, barinma inta tuna rashin kunyar data masa dazun , duk wani move dinta akan idonshi a ankare yake da ita zuwa tayi gabanshi yamiko mata hannun nashi, daure hannun nashi tayi da tonicate tasamo jijiya alluran tamishi sannan ta balla mishi magungunansa yasha kokarin barin dakin tayi tana tafiya tana adduah Allah yasa karya tsayar dani wayyo ni aikuwa karaff taji muryanshi yana fadin " dakike kokarin tafiya nace kitafine kona sallame kine!?" Cikin tsiwa tajuyo " da danake tafiya Kai kake cewa intafine!?" Seda tagama maganar Kuma tarufe bakinta Dan duka hannunta tafara danasani harga Allah batasan abinda zata furta ba kenan datasani da bazama tabude baki da sunan magana ba yau tasan azaad seya karkaryata kafin tabar gidan , murya na rawa tabara bashi hakuri " ayyah Dan Allah Mr azaad kayi hakuri wallahi ba abinda nakeson fada ba kenan bansan taya bakina yafurtaba" tana magana tana yarfe hannu kamar me shirin kuka ganin yamike yanufota yasa tafara ja dabaya seda suka kure bangon dakin rumfa yamata da hannunshi da kirjinsa yana kallon yanda gaba Daya ta daburce hannunsa yasa yadago habarta sama yaza mana suna kallon cikin kwayar idon juna kasa kallon cikin nashi idon tayi taruntse idonta fuskanshi yamatso daff da nata har hancinshi na gogan nata,dawani irin gudu zuciyarta take bugawa Jin fuskansu ahade yasa tayi saurin Bude kyawawan idonta tazuba mishi Shima ita yake kallo cikin kasalaliyar murya yafara magana " meyasa kikeson min rashin kunya?? Muryanta nadan rawa tace" kkk kayi hakuri bazan sake ba " mamakinta yake wani lokacin intana magana kamar me hankali amma se rashin kunya tunani yafara to kode nikadai takeyiwa ne yanda naji gaba daya su ummi suke yabonta wai tana da hankali kallonshi yamaida kan dan karamin libs dinta datake ta motsasu hannu yakai yarike libs din kasan " meyasa kikacemin Dan Iska dazun ? Miyasa kika renani da yawane uhumm magana yakeyi Amma gaba daya kasala yarufeshi fuskanta kawai yakurawa ido baki tabude zata bashi hakuri, hade bakinsu waje daya yayi Yana kissing dinta, mutsu_mutsu takeyi saboda ta kwace kanta amma Ina yafi karfinta , hot kiss πŸ’‹ kawai yake bata tun tana kokarin hanashi harta hakura se hawayen datakeyi ahankali yazagayo da hannunshi bayanta kan zuwa zib din riganta Jin yafara ja mata jib din Riga ne yasa tafara tureshi da karfi ko motsawa beyiba seda yajasa daura tafin hannunshi yayi a tsakiyar bayanta wani irin shock yaji kamar wanda wuta tajashi , shafa bayanta yakeyi ahankali daga bisani Kuma yamatseta sosai seda tasa Kara cikin dasheshiyar murya yace" Zaki karamin rashin kunya!? Girgiza tayi " bazan karaba inna Kara kamin duk abinda kagadama dan Allah kayi hakuri mr azaad " saketa yayi yatureta daga jikinshi Yana galla mata harara " karamar mara kunya kawai" yakoma yazauna yashiga danna wayarsa sautin kukanta ne ya ishesa kallonta yayi yaga tana tsaye yanda yabarta " okay indawo ne baki gaji da kiss din bane " magana yakeyi Yana kokarin mikewa ganin datayi dagaske wajanta zedawo yasa tafara kokarin Jan zib din riganta carkewa yayi yaki moving tafi 5mint ahaka ganin haka yasashi mikewa yakarasa inda take a tsorace tace " please am sorry " hannu yasa yajawota tafada jikinshi kafin yasa hannu yaja mata zib din yakoma inda yataso goge hawayen fuskanta tayi tabar dakin tana hararanshi azuciya Kuma se Allah ya isa take ja simi_simi tabar dakin.....

Tom yanda nafada de hakan take yawan comment dinku yawan read more dinku kenan asha karatu lafiya semun hadu Monday inme duka yakaimu da Rai da lfy πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ™

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe

πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)









Da sunan Allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen πŸ₯°πŸ€Ž









Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci πŸ₯°πŸ€ŽπŸ˜˜








Free book πŸ“šπŸ“šπŸ“š









____________________________________________








Page2️⃣2️⃣








Bayan barinta dakin ne yakoma ya kwanta Yana ajiyar zuciya Yana tuna abinda yafaru tsakaninshi da fanan karo nafarko kenan arayuwarshi daya taba wata mace murmushi yayi aranshi yana fadin " mara kunya kawai"


In serious tone fanan tafuskan ci Zeenat kafin tafara magana "nikam dan Allah intambayeki mana zee!?" Kallonta zeenat tayi taga yanda tanutsu tana jiran amsanta tasan dole abinda zata tambayeta is very important gyara zama tayi tabata attention sannan tace " inajinki" " nikam yayankun nan wayan nan matan dukansu biyu ze aura ne danaga suna fada akansa!?" Ajiye wayar hannunta zeenat tana fadin " wallahi kekam ah ah ita nusaiba yar abokin Abba ne wato alhaji badamasi me ruwa kuma hajiya Hussaina kawar ummi ce tom nusaiba yarinyar kishiyar hajiya Hussaina ce to itace take mugun son ya azaad inde kinganta tazo gombe to danshi tazo Amma inbanda yau inagama inkin tambayi ya azaad ya kamaninta yake besaniba dan ko kallo bata isheshi ba bare yatsaya magana da ita gashi tanada mugun rawan kai kamar wata amaryan kareπŸ˜‚ , itakuma aneesa babanta yayan mommy ne Kuma suna mutunci da Abba tom time din da ya azaad yatafi US ne yin wani meeting akan business shine suka hadu da ita time din tana final year a university tunda tasa idonta akansa nanike mishi kamar chew gum kwata_kwata ya azaad baya sonta saboda bakaramar marajin magana bace inkina neman shedaniya ta gidan gaba to kisamu aneesa da ta lura bata gaban ya azaad kawai taje tasamu baban tana kuka kamar zata mutu tace mishi ita duk duniyar nan bataga mijin aure ba sama da azaad ba, shikuma tsaban son da yake mata ne yadaure mata gindi yasamu mommy da maganar nan sukayi kulla kullansu sukama Abba magana duk da abba bewani maraba da maganar ba amma ganin suna mutunci yace mishi bakomai dama gashi sun dade sunabin ya azaad yayi aure Amma se kakkaucewa yakeyi , ummi dataji maganar ko kadan hankalinta be kwanta da yarinyar ba amma bazata iya musu da mijinta ba , adaren ranar Abba yakira ya azaad yasanar dashi abinda ya yanke mishi dan ba shawara yabashi ba umarni ne. Babu yanda ya azaad ya iya haka yabi umarninsu amma bawai Dan yanason taba bayan wata uku aka musu baiko tunda nusaiba taji labarin tadinga rashin lafiya nan ne tadau aniyar tarwatsa aurensu dan bata shakka agaban kowa tasha fadan inde ita bata auri azaad ba to wlh aneesa bazata auresa ba inde tana raye bazaayi auren ba to kinji abinda yahadasu" tunda tafara magana fanan take kallonta bako kyaftawa ganin yanda take magana kamar wata yar jarida dariya fanan tadanyi "Kai zeenat kin iya bayani irin wannan dogon jawabin haka sannu " murmushi zeenat tayi tace " to ai namiki dalla_dalla ne saboda kigane " " aikuwa nagane yanzu" cewar fanan data tafi duniyar tunani "gaskiya taga wautan su aneesa yanzu ji yanda suke zubar da kima da daraja irin nasu namata sunzo suna nacewa Wanda bemasan sunayi ba balle yakula su, hmmm nide banga abinda zesa innacewa namiji haka ba wai dan inasanshi sede inmutu da sonshi araina ballema Azaad banga abin so atare dashi ba bugu da kari Dan Iska ne wata zuciyar tace mata amma ai yanada mugun kyau tsaki tayi dan yanada kyau Kuma seme ai Hali me kyau akeso ba kyaun fuska ba" "fanan tunanin mekikeyi haka tundazun fa nake miki magana" kwanciya fanan tayi akan lallausan gadon zeenat kafin tace" hmmm kede bari kawai dear inata mamakin su nusaiba ne " "ohhhhh kyalesu wahala ce bata ishesu ba saboda nide da hankalina ba namijin dazanwa irin wannan son haukan " girgiza Kai fanan tayi" karkice haka Suma bason ransu bane babu yanda zasuyine saboda naji ana cewa so mugun abune inya rikeka ni wallahi tausayi suke bani " hmmm kede fanan haka kikace de ke kintaba soyayya ne!?" "Ah ah bantabayi ba" da mamaki zeenat takalleta saboda batayi tunanin yanda fanan take da kyau da hankalin nan ace wai bata taba soyayya ba "Amma meyasa baki tabayi ba !?" Rike Kai tayi dan tagaji da da surutun zeenat bacci takesonyi" saboda babu wanda yataba cewa yana Sona mana bantaba tsayawa dawani namiji da sunan muna hiran soyayya ba" girgiza Kai zeenat tayi tana mamaki sosai, ahaka sukaci gaba da hira har bacci yayi gaba da fanan ganin haka yasa zeenat barin dakin taje gun ummi tasameta tana waya da yan dubai cikin harshen larabci take magana zama tayi tana jiran ta tagama saboda akwai abinda takeson fada mata,ajiye wayar ummi tayi bayan ta kammala tana kallon yar autar tata yanda ta nutsu tasan abu me mahimmanci takeson fada " zee ya akayi akwai labarine " zeenat kamar wacce take Jira ummi tamata magana ta fara fadin " ummi intambayeki Dan Allah fanan bata burgeki!? " Tana burgeni mana" cewar ummi , Jin haka daga bakin ummi yakarawa zeenat karfin guiwa ta cigaba da magana " wallahi ummi fanan tanada hankali sosai gata da nutsuwa ga ilimin addini dana boko" murmushin ummi tayi irin nasu na manya dan tariga da tasan inda zance zeenat din yadosa amma seta ce mata "cigaba inajinki" " ummi Zakiyi matukar Jindadi inta zama surkanki bakaramin farin ciki zamuyi ba " tagama maganar ta tana kallon ummin nata da itama kallonta takeyi " tom hajiya zeenat naji bayananki amma waye kikeson ta aura din " dan fari da ido zeenat tayi tace " Matar ya azaad mana ummi" dariya ummi tafashe dashi " nikam klau dinki kuwa bakisan yayanki yanada wacce zai aura ba ko kuma ita fanan din cemiki tayi bata da wanda take tare dashine " sanyi jikinta yayi jin maganar ummi duk dahaka de bata karaya ba tasake cewa " to ai ummi ya azaad yanada daman daze auri mata daga daya har hudu kinga ze iya auren fanan Kuma wlh bakaramin dacewa zasuyi ba " maganar zeenat ba karamin tasiri yayi azuciyar ummi ba tabbas tana son fanan har ranta saboda kyawawan halinta zataji dadin hakan inde fanan tazamo surkanta amma zata gwada tuntuban abbansu da maganar taji mezece dukda tasan bazaa samu matsala tagunsa ba sede ko in azaad din, ganin ummi tayi shuru ne yasa tace " ummm ummi nikam natafi tunda baayi accepting din request dina ba" cikin zolaya ummi tace " gaskiya kam baayi ba tattara ki koma inda kika fito" komawa dakin tayi ta tadda fanan tagama shiryawa zata tafi fitowa tare sukayi taje tama ummi sallama ta tafi.




Tattaunawa sukeyi tsakanin su duk Wanda yaga yanda suke maganan nan yasan babu alkhari acikinsa. Alhaji sambo daurayi ne yace " nide inzaku bi shawarata dase ince wani Abu" duk hankalinsu suka dawo dashi kansa hannu alhaji Ibrahim tijjani yadaga masa alamar yafadi abinda ze fada, cigaba da magana yayi " nide aganina karmu ce zamu kashesa saboda inde mukayi hakan idon duniya kanmu zata dawo aganina kamata yayi muhada mishi target wanda idan ya fada tashi tagama " tafi alh Ibrahim tijjani yayi Yana fadin" good point alh sambo tabbas ka kawo shawara mafi dacewa amma yanzu dameye yakama muhada mishi tarko" shuru sukayi dukkansu suna tunani can cikin sauri alh lamido yace " mace! Tabbas da mace zamu hada mishi tarkon dakuwa tabbas ze kamashi " kallonsa alh Ibrahim yayi " eh hakane wannan ma point ne amma sanin kankane azaad shidin ba manemin mata bane kwata_kwata mata basa gabanshi" alh Umar baita ne yayi gyaran murya wanda tunda suke magana bece musu komai ba yafara fadin" azaad ba manemin mata bane abinda ze faru zamusa asa mishi idone adinga bibiyarshi dama daya kawai zamuyi amfani dashi domin cika burinmu bamuda matsala da koma wacece aka gansu adauka mana hoto kawai" raf!raf!raf tafi kawai sukeyi saboda bakaramin dadin maganar alh Umar baita sukaji ba, cikin farin ciki alh Ibrahim yadaura da " sharri zamu hada mishi wanda ze matukar taba career shi wanda ze taba mishi kasuwanci domin babu Wanda zeso siyan kaya agun mazinaci me lalata yayan mutane koya kuka gani !?" Hahahahahah babu abinda sukeyi inbanda dariyar mugunta yanzu kam sunsamo hanya mafi sauki dazasuyi maganin taurin kai dakuma jiji dakan azaad ahaka suka watse.

Yau sati daya kenan rabon da fanan taje gidansu azaad saboda alluransa yakare tagama mishi duk wani treatment dinsa Kuma alhamdulillah yasamu sauki sosai dan bayama Nigeria kwanansa uku da tafiya Germany gabatar da wani business daga nan Kuma zewuce Malaysia sudawo tare da Abba . Su ummi kuwa bakaramin missing din fanan sukayi ba adan zaman dasukayi da ita sun shaku sosai.


MAINASARA'S family

Yau gidan se girke_girke da gyare_gyare akeyi duk wani me aiki agidan basu zauna ba sunata faman aiki kamar ba gobe saboda tarban Abba da azaad dasuke hanyar dawowa ummi dakanta take kitchen se masu tayata aiki sunata girki, Basu suka samu kansu ba se around 2 suka jera komai akan dinning area kulolin abinci sunfi goma ga drinks kala_kala dukansu suna zaune afalo ummi tayi kyau sosai tana sanye da dakekkiyar lace me matukar tsada tasha gold's zeenat ma tayi kyau sosai abunta sanye take da abaya baka fawwaz ne yakalli agogon hannunshi yamike Yana fadin" areef tashi mutafi sunkusa landing" mikewa sukayi suka tafi airport din tsayuwar mintuna 10 sukayi kafin jirgin su yayi landing, mutane nata fitowa daya bayan daya , wani farin dattijo ne yafito sanye da shadda blue color da gare (malum_malum) bafulatani kyakyawa me gwarjini gashi atsaye yake kallo Daya zaka mishi kasan cewa kudi da hutu sunzauna ajikinshi Abba kenan ALHAJI MUHAMMAD B MAINASARA bakaramin kama sukeyi da azaad ba ta bangaren zubin halitta , azaad nahango abayanshi suna fitowa tare yanayin jikin su da tsayinsu kusan daya sede azaad yafishi murdewan jiki dakuma tsayi kasancewar shi saurayine...








Nafada mukuma zansake fada yawan comment dinku yawan read more dinku kusha karatu lafiya,se mun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy πŸ‘

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe

πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺


Story Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)






Da sunan Allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen πŸ₯°







Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci πŸ₯°πŸ₯°πŸ€Ž







Free book πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š









____________________________________________






Page. 2️⃣3️⃣








Yana sanye da suit white color se bakin takalminshi ga agogon diamond adaure ahannun shi yasha bakin son glass fuskan nan ahade kamar hadari bakaramin masifar kyau yayi ba azaad kyakyawane nakarshe bugu da kari half-cast ne duk Wanda yakalleshi baya mishi kallon hausa fulani kallon balarabe akemai saboda yadauko umminsa ne kirar jikine yadauko na Abba sekuma farinsu daya hada shisa yakasance fari sosai dan duk yafi mutanen gidan fari tsabar hutu fatar jikinsa Kamar kataba jini yafito, babban abinda yakesa mata suke rushing akansa kenan gashi dogo me murdadden jiki ga manyan idanu farare tass hancinsa kuwa kamar shiya zana abinsa dogon hanci bakin nan dan karami dashi pink yanada dimple Wanda ko magana yakeyi sesun lotsa gashin kanshi yasha gyara atare yake sosai andan sha gefe da gefe seyayi kamar fonk, kunsan irin gashin turawa da na larabawa base nafada muku ba yanada kwantaccen saje baki Wanda shima yasha gyara daga dan gefen wuyanshi akwai zanen tattoo daya fito waje alaman jikinsa akwai tattoo azaad cikekken namijine wanda ko wace mace zatayi mafarkin samu amatsayin miji( nikuwa ISHAM nace aibanga laifin su nusaiba da aneesa ba dasuka nanike masa kamar magnet) Saukowa sukeyi daga matakalan jirgin cikin takun kasaita , hannun azaad narike da jacket din suit dinshi, tunda suka sauko suka tadda yan jarida sun kewaye ko Ina na airport din ga manyan abokanan kasuwancin su tako Ina, ga sojoji kewaye dagurin domin basu tsaro se fadawa dakuma yan uwansu yan masarautar gombe dasuma yanzu suka iso domin tarbansu cika airport din yayi bako matsaka tsinke, tambayoyi Yan jarida suke ta aika musu dakuma faman daukansu hoto ko takansu basubi ba sukaci gaba da tafiya, kirari fadawan nan suka farayi tare da busa sarewa, karasowa fawwaz da areef sukayi atare suka rungume Abba suna mishi sannu da hanya cikin farin ciki da jindadi Abba yake shafa bayansu yana murmushi kafin suka zame jikinsu suka rungume azaad ko wannen su kagani zakaga farin ciki dauke afuskokinsu amma banda azaad da fuskan nan take kamar kullum, bubude musu murfin motar sukayi suka shiga ajere motocin suke, suka jera akan titi suna tafiya slowly, motocin sojoji ne agaba wanda akalla zasu kai motar 10,se motocin gidan sarkin gombe color su fari Suma akalla zasukai guda 8, se motocin gidan MAINASARA family bakake ne su sunkai goma sha hudu 14, daga tsakiya Kuma motocin abokanan kasuwancin su ne wanda kowa da kalan motar sa se karshe motocin polisawa ne wanda suka taho daga government house se jiniya kawai kakeji

Please Login or Register in order to submit comment