Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana tashi, duk masu ababen hawa sun faka suna jiran wucewarsu , minti 40 ne yakawosu gida Bude musu motar akayi suka fito atsaye a compound din gidan suka samu su ummi, zeenat,anty Amina da itama dazun tazo da yaranta, mommy , Mansoor, anty Zainab ,anty shayida duk suna tsaye suna jiransu, da gudu zeenat tafada jikin Abba tana murna " oyoyo yarinyar abbanta ! Yar autan abbanta " cewan Abba dake rike da zeenat din sakeshi tayi tana kare masa kallo cikin zolaya tace" wow abbana kaga yanda ka Kara kyau da kumatu kuwa Meye sirrin !?" Ta tambayesa tana rike da duka hannayensa biyu dariya jamaan wajan sukayi saboda tabasu da dariya dakuma burgesu yanda suke da mahaifin nasu, lakatan hancinta Abba yayi" uhmmm zee Meye kuwa sirrin daya wuce kwana biyu nahuta da rigimanki Kinga aidole nayi kumatu " nanma kara tuntsirewa akayi da dariya saboda dama Abba ba bayaba wajan barkwanci wucewa ciki azaad yayi dan baze iya da wannan hiran nasu ba Dan yaga bana karewa bane yana mamakin Abba daya tsaya yake biyewa zeenat, da gudu_gudu Faisal babban yaron azaad yabi bayansa yaron sane na amana kusan shekara 10 suna tare Yana mishi hidima black beauty dashi. Part dinsa direct suka wuce Yana shiga dakinsa ya cire necktie dinsa yayi wurgi dashi.


Acikin gida kuwa tunda zeenat taji abinda Abba yafada tayi narai narai da ido kamar zatayi kuka dariya tabashi yariko hannunta suka fara tafiya Yana ce mata " haba yar autata am just kidding you" ahaka harsuka karasa kusa da su ummi dasuke tsaye wani irin kallon love Abba yakebin ummi dashi bakaramin kyau tayi mishi ba seyagama kayan hausawa yafi karbanta itakuwa se murmushi takeyi tana sunnar dakai dan ita kunya yake bata agaban yayanta , mommy kuwa bakin ciki kamar yakasheta fuskan nan adaure. Kiran areef Abba yayi yamishi magana akunne Sannan yawuce part din ummi su ummi sukabi bayanshi , mommy kuwa fuuuuu tawuce part dinsu rai abace, karasawa areef yayi yacema jamaan wajan " Abba yace in fada muku kujirashi a part dinsa " yawuce ciki.

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story & Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)





Da sunan Allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen πŸ₯°πŸ₯°










Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina Allah yabar zumunci πŸ₯°πŸ₯°πŸ€Ž





Free book πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š







&_______________________________________&






Page 2️⃣4️⃣ & 2️⃣5️⃣







Part din Abba bakin suka shiga suka zauna suna jiran fitowarshi babban part ne dan yafi duka part din gidan girma gashi yasha kayan dukiya kam kamar zasuyi magana.
Zaune suke a babban falon kasa sunata hira yaran anty amina aslam da islam se wasan su sukeyi mikewa ummi tayi tahaura upstairs direct dakinta tawuce taje toilet dan tahadawa abba ruwan wanka jin motsi tayi a dakin nata fitowa tayi taga Abba atsaye atsakiyar dakin fuskanshi dauke da murmushin so da kauna yabude mata hannu ahankali taje tayi hugging dinsa dagowa tayi tana kallon fuskansa cike da kaunar mijin nata magana Abba yafara yana fadin" i really miss you my zaujat " " I missed you too" ummi tafadi haka fuskanta yana canzawa ganin kamar ranta adan bace ne yasa Abba tambayarta " meyafaru kuma naga ranki abaci ko bakiyi farin ciki da dawowata bane!?" Jan hannunsa tayi suka zauna abakin gado tana fuskantar shi tace " bahaka bane nafi kowa murna da dawuwarka saboda nayi missing dinka sosai, kawai de abinda kakeyine banajin dadinsa domin baka kyautawa banason ran tashin al'qiyama mijina yatashi da shanyeyen barin jiki dukda nasan iya kokarinka kana kwatanta adalci a tsakanina da mommynsu amma dan Allah kadinga adalci kaga itace uwargidanka uwar manyan yayanka abangarenta yakamata kasauka ba anan ba kokuma kasauka apart dinka nasan yanzu dole zataji badadi kuma tana da gaskiya ko nice zanji badadin hakan mijina kayi hakuri in akwai abinda nafada daya bata maka rai bazan iya zuwa ido inga kana irin haka a tsakaninmu ba " tagama maganarta kanta akasa ( gareku mata masu kishiyoyi karkiyi murna dan wai mijinku yafi fifitaki akan yar uwarki kita farin ciki, zakiga wani namijin Yana fifita daya akan daya Kuma baya iya boyewa wannan rashin Adalci ne zakiga in ranar Kwanan dayan ce zeshiga dakin yar uwarta yaki fitowa dawuri kokuma yaje ya yini agunta , kekuma a maimakon kimishi magana akan hakan badacewa bane sekiyita farin ciki harma yazama kina mata gori tom karkiyi tunanin wai shikadai ne da hakkin rashin Adalci kema harda nake komishon din kema kin bada naki gudunmawan Dan dabaki sakar mishi fuska ba babu yanda haka zefaru kokuma kimishi nasiha akan hakan be kyautu ba zakiga jikinshi yayi sanyi nan gaba dole zeji nauyin sakewa, Amma maimakon hakan se mata suka maidashi ado suna tutiya da miji nasonsu yana banzatar da kishiyarta bazakiyi tunanin namijine fah abinda yawa yar uwata nima inbanyi wasa ba wata rana dole zejuyo kaina saboda zaman aure zamane nahar abada ba kullum bane ake cikin jindadi ba zamane na yar hakuri , tom tunasar da mazajenku akan hakan zesa arage wani rashin Adalcin Allah yakyauta). Tunda ummi tafara magana Abba kebinta da ido wutan sonta nakara ruruwa acikin zuciyarshi tabbas yayi dacen mata aysha macece da har kullum yake alfahari da ita macen kwarai datasan yakamata wani irin tausayinta ne yakamashi aranshi yana fadin "baiwar Allah datasan wacece hafsat dabata tsaya tana cewa bana mata adalci ba datasan irin mugun nufinta akansu da setaji ta tsaneta amma banga laifinki ba dan nasan bakisan ba aure a tsakanina da itaba " ajiyar zuciya yayi yariko hannunta yace " bakomai my wife in sha Allah zangyara karki damu " murmushi tayi tace" yauwwa shukhuran ya Habibi" mikewa yayi yashiga toilet din yasamu yayi wanka ta fito masa da kayan sawansa sannan ta koma kasa. Suna zaune afalon yafito suka je dinning area akayi saving din kowa abinci, kallon Abu tayi tace " ankaiwa bakin dake part din abbansu abinci !? Eh hajiya nakai musu" okay ankaiwa son nashi ne?" girgiza Kai Abu tayi tace " ah ah yanzu aka gama shirya mishi nashi zaakai mai" gyada kai ummi tayi kafin suka faracin abinci shuru sukayi bakajin karan komai se cokula bayan sun kammala ne Abba yamike Yana fadin " bari inleka jamaata " to sukace mai.



" Sir wannan sune list din kayan da muka fitar awannan shekaran Kuma alhamdulillah duk sun kare komai yatafi smoothly, a motoci kwaya Dari shida na company duka sun kare saura guda gomane suka rage range Rovers , sekuma company shinkafa nanma abuhu million biyar da aka fitar duk sun kare,haka company sauran kayan abincin Suma komai yatafi yanda yakamata kuma ansayar da komai akan farashin daka fada, sekuma azaad unlimited company (inda ake sarrafa kowani irin nau in kayan sawa) nanma duk kayan ciki sun kare anzuba wasu, se manyan super market dinka dakuma manyan shagunanka na furniture Suma haka komai na wannan shekaran yakare anzuba wasu , se gidajen da akeyin renting ( gidan haya) Suma kowa yabada payment dinsa, masu napep masu taxi πŸš• kowa yakawo nashi balance din, se gidan gona Shima anzuba wasu kayan aciki , shopping mall dinkama haka, bayan hakama Muna bukatar sabbin ma aikata akalla guda dari ko sama da hakan wannan shine list din wannan shekaran sir" Faisal yagama magana yana juyawa azaad dake kwance akan lallausan gadonshi laptop din dan yagani , mikewa yayi yace " good job faisal karka damu base kanuna min ba kamanta komai inde abinda yashafi system dinka dana duk sauran ma aikatana ninake juyashi bane, you did a great job, yanzu abu nagaba shine kafadawa marketing manager yakaro sabbin ma aikata sannan kuma kaje kasamu accounter kowani employee dina akara masa salary akalla 50k each employee, sannan kayi arranging din ziyaran daza mukai gidajen marayu in this week" yana magana yana bata fuska kamar wanda akawa dole seyayi maganar, faisal kam ko ajikinshi inda sabo yasaba da halin ogan nashi shekara 10 bawasa ba , cigaba da magana faisal yayi " sir kanada meeting jibi misalin karfe biyu da kautal Jude company, sekuma jiri brothers and son's sunyi request din appointment dakai zaayi accepting dinsu neko Kuma!?" dan daga kai sama yayi kamar wani me tunani can kuma yace "okay I will think about it" okay sir suna cikin haka me aiki takawo musu abincin ta ajiye a dinning area na falonshi kafin tadan daga murya tace" sir your food is ready" tana gama fadin haka ta tafi ko motsawa azaad beyiba ,tashi Faisal yayi yaje dinning din yaga food flask sunkai takwas ajere bude nafarkon yayi yaga fried rice taji nama zuku_zuku plate yadauka yayi serving kanshi yazauna yafaracin abinci yaci yakoshi yasha drinks dinshi tukun yakoma gun azaad yace " sir cikina yadauka nizan wuce se anjuma" yadauki system dinshi dan dama beyi tsammanin amsa ba yatafi.


Safa da marwa mommy takeyi afalonta fuskanta ahade kamar anmata sako da mutuwa ita kadai se sambatu takeyi " ni Muhammad zeyi kokarin tozartawa wlh be isaba karyanshi yasha karya itakuma aysha senayi maganinta munafukar banza da wofi mtsssw" gaba Daya yaranta tagumi sukayi suka zuba mata ido ganin yanda take maganganu kamar wacce ta zauce anty shayida ce tace " please calm down mommy meyasa kike yawan tayar da hankalinki akan abinda betaka kara yakarya ba wannan aibawani abu bane nide nasan wallahi ummi nasonki tsakani da Allah " wani irin uwar harara mommy ta wurga mata " nide kam banji dadin rayuwata ba Allah yaban yara marasa kishin uwarsu Yan iska marasa zuciya,barinma ke tanuna anty shayida da yatsa nayi dana sanin haihuwarki saboda bazeyu ace nahaifi yarda bata kaunata ba banza laa'nanniya shisa kika kasa samun ci gaba arayuwa keda yara Kuma sede kiga ana haihuwa " ( iyaye yakamata musan irin kalman da zamu dinga furtawa yayanmu domin bakin uwa nada matukar kaifi akan danta walau adduah'ta walau mumunar Baki, Koda yakasance dah namaka laifi duk muninsa karkiwa danki baki domin rayuwarsa ne zetabbare Kuma daga karshe kema kizo kina danasani to miye riban haka, yaro tun Yana dan karami dashi Zaki tankwarashi takan farki mekyau yanda kinsan nan gaba inya girma baza kisha wahala ba, in laifi yayi kimishi fada sosai sannan kijashi ajiki kimai fada yanda nan gaba bazeyi shaawar Kara aikata hakan ba , sannan duka wasu iyayen suna ganin idan yaro yayi laifi akamashi amishi dan bazan duka shine dede to nanma bako wani laifi bane ake bugun yaro, saboda idan jikin yaro yasaba da duka nan gaba koya ganki da bulala wallahi baze gudu ba kokuma kiga alamar tsoro akan fuskanshi ba saboda yariga daya saba da dukan ahakane zakiga yaro yataso marajin magana da rashin ji,.)
Jin irin mugayen kalaman da mommy take binta dasune yasa kukanta da take dannewa yafito Fili, tashi tayi tahaura upstairs dakinsu dasuke ciki time din yanmatancin su ta cigaba da kukanta bin bayanta anty Zainab tayi tana rarrashinta "kiyi hakuri shayida komai lokacine wata rana se lbr yakamata yanzu inda sabo kisaba da halin mommy Kuma kidinga sata a adduah Allah yasa tagane gaskiya " cikin muryan kuka anty shayida tace" anty Zainab irin abinda mommy take mana kamar ba ita tahaifemu ba narasa dalilin dayasa bata kaunar mu tadauki Karan tsana tadaura mana barinma ni tafi tsanata shisa yanzu inbadan Abba da ummi ba wlh se infi watan ni banzo gidan nan ba, anty Zainab ninasan bakin cikine ze kasheni acikin Wanda sukemin gorin haihuwa ace harda uwata wacce yakamata itace zatana rarrashina amma harda baki take
min wai bazan taba haihuwa ba innalillahi wainna ilaijiraji unnn ya Allah kakawomin mafita " tagama magana tana Kara rushewa da marayan kuka rungumeta anty Zainab tayi tana bubbuga bayanta "is okay kinji kokin manta haihuwa na Allah ne shiyake bayarwa alokacin da yagadama in lokacin dazaki samu ciki yayi babu wani mahalukin daze hanaki samu kuma kici gaba da kai kukanki wajan Allah , kidena sawa kanki damuwa kokin manta munada ummi da abba ne ga kannanmu duk suna sonmu ga Amina ma " haka taci gaba da kwantar mata da hankali hartasamu tayi shuru.




Abangaren gidan su fanan kuwa yanzu shirye_shiryen saukan fanan akeyi haka gidansu amira ma Dan makaranta daya sukayi DHARUL_HUDA.
Dukansu suna zaune afalo harsu baba yau basu fita kasuwa ba saboda shirye_shiryen saukan gobe dazaayi, fanan nazaune itada suhaima atsakiyar falon hannunta dauke da jotter da pen tana rubuta list din mutanen dazasuzo tana sanye da wando falazo black me manyan fulawi fari tanason falazo sosai dan tafi sakewa acikinshi, se farar riga kanta da hula ita kuma suhaima list din abubuwan da ake bukata take rubutawa,
Dago Kai fanan tayi tace "mama nagama rubutawa bansan ko akwai wayanda suka rage ba " suhaima ce tace " kin saka gidansu ummi a list kuwa " " ah ah bansa ba basuma san zanyi saukan ba shisa bansa ba" cewar fanan dake kokarin rubuta sunan nasu a jotter ta, mama ce tace " aikuwa de yakamata asa inyaso tunda basu saniba anjuma al ameen seya kaiku gidan kubasu kati " to shikenan, mikawa ya usman list suhaima tayi dan tagama rubutawa karba yayi yana dubawa can kuma yace " iyakacin abinda ake bukata kenan !? Naga kamar list din yayi guntu" Yana magana yana kallon list din Jin abinda yafada ne yasa mama tace " inga ni" tashi yayi yaje yabata yadawo yazauna , duddubawa takeyi pen tadauko ta kara rubuta abubuwan dabata gani aciki ba bayan tagamane tamikawa baba yakarba yace" shikenan ko " eh sukace, mikewa baba yayi yadauki car key dinshi yace " Usman tashi ka tada mashin dinka ka kaini indauko motar muje kasuwa kaikuma Al ameen seku shirya kuje ka kaisu " dukansu Mikewa sukayi mazan su ya al ameen sukayi waje sukabi baba , ya usman yatada mashin baba yahau suka fita daukan motar saboda gidan baze dau motar biyu ba shisa baba yake baro nashi a inda ake gadin motoci yacewa ya al ameen yadinga packing din nashin kawai, fitowa fanan sukayi harda auta itama zatabisu dogon hijab duka sukasa , suka sameshi a motar shiga sukayi yatada motar suka kama hanyar gidansu azaad, fanan kwatance tadinga yimishi harsuka iso fitowa baba me gadi yayi ganin bakuwar mota yasa yazo dubawa dan leko kai fanan tayi tagaisheshi washe fuska yayi ganin itace yakoma yawangale musu gate shiga cikin gidan yayi , bayan yayi packing suka fito, hango zeenat da fawwaz fanan tayi alamun fita zasuyi karasowa wajan su sukayi mikawa ya al ameen hannu fawwaz yayi sukayi musabaha idon fawwaz ne yasauka acikin na suhaima dake gaisheshi murmushi yayi ya amsa kafin ya amsa na fanan cike da farin ciki ganin fanan zeenat tace" Allah kawata gaskiya nayi missing dinki naso zuwa sekuma Abba suka dawo jiya yanzu kuma ya fawwaz ne zekaini shopping segaku nan tom muje ciki " dariya suhaima tayi tace " ummm nadauka nikadai akecewa inada surutu yau naga wanda tafini " dariya zeenat tayi cikin yauki tace " yanzu dan Allah ni inada surutu yar shuru_shuru dani" fanan de shuru tamusu dan wayan nan biyun intace zata biye musu suta hiran basu taba gajiya ba , kallon suhaima da auta tayi taga suna kama da fanan nan tagane yan uwanta ne riko hannun auta tayi tace " zo muyi gaba fine girl tunda antynki taki kulani yau " wucewa sukayi ya fawwaz sukabi bayansu afalon kasa suka samu duk yan gidan harda su abba banda azaad dake can yana kwance shigowa sukayi da sallama abakinsu bismillah fawwaz yamusu basu zauna ba se suka tsunguna har kasa suna gaishe da Abba kafin suka gaida ummi da anty Amina bin mazan falon ya al ameen yayi yana basu hannu suka gaisa cikin mutuntawa kafin yazauna, ummi ce takalli fanan " su fanan tunda patient dinki yasamu lafiya aka guje mu ko !?" Cikin jin kunya ta sunkuyar dakai sannan tace " ah ah ummi bahaka bane shirye_shiryen sauka nane yasha min kai shisa kuka jini shuru " Abba tunda fanan tafara magana yake kallonta Jin yanda take magana cikin nutsuwa seta burgeshi sosai cikin barkwanci yace" ah ah umminsu kice wannan itace nurse din tamu kenan !" dariya suka danyi kafin ya cigaba " yaushene saukan naku ?" Cikin nutsuwa da kunya fanan tace " gobe ne yanzuma kati muka kawo muku " gyada kai abba yayi yace " Masha Allah awata makaranta ne!? Cikin zakin murya da yarinta auta tace" sunan makarantan Dharul_huda gobe da karfe 9 na safe zaafara atashi karfe 3 in akayi nasu anty semuma inmun je ajiya 6 muma zaayi namu yanzu ina aji uku ne" tagumi fanan da suhaima sukayi suna ganin iKon Allah yanda auta ke zaro zance sekace an tambayeta batasan mutane ba tazo tana musu surutu kamar wata parrot, ya al ameen de rike baki yayi , bakaramin dariya auta tabasu ba cikin dariya ummi tace" fanan kanwarki ce ko naga kuna kama sosai " karaff auta zatayi magana fanan tadaka mata harara aikuwa ba shiri tayi shuru harda sa hannu abakinta,nanma dariya suka karasawa dan sunga hararan da fanan tamata bakaramin nishadi auta tabasu ba mikewa fanan tayi tamikawa Abba katin karba yayi Yana karantawa kafin yace " fateema amma ya akayi makarantanku se yanzu takeyin nata saukan bayan yanzu wata biyu kenan da haddace Al qur'ani!?" " Eh Abba dama haka tsarin islamiyarmu take inmuka gama aji shida semunje hutu mundawo zaayi saukan " jinjina kai Abba yayi cikin gamsuwa da bayananta, ummi tace " in sha Allah zaki ganmu" mikewa zeenat tayi tace " kuzo muje daki " dukansu mikewa sukayi sukabi bayanta Abba ne yace " ohhh to zaku gudu dakin zeee kenan to ke zomuyi hira ko " yafada yana nuna auta da hannu zuwa tayi tazauna akusa dashi ya tambayeta sunanta aikuwa nantake tafara zuba zance se dariya sukeyi dan sun lura auta ita kanta comedy ce girgiza kai fanan tayi Jin yanda auta tacigaba da zuba kamar ba dazun ta hanata ba aranta tana cewa Allah yashiryeki auta, fitowa azaad yayi yawucesu afalon yatafi garden dan yaseer yafada mai yana wajan, mikewa Abba yayi yacema auta " karki je ko Ina kijirani anan indawo yanzu nan " gyada kai tayi shikuma yawuce yabi bayan azaad dan akwai abinda yakeson su tattauna harya kusa shiga garden din yaji kamar ana binshi abaya juyawa yayi yaga Abba ne tsayawa yayi abba yakaraso suka shiga garden din tare gaida Abba yaseer yayi Yana mishi ya hanya suka zauna akan kujerun wajan . hira suke tasha adakin zeenat tana basu labarin time din datayi graduate nata se kallon photos sukeyi awayarta can zeenat tace "kutashi muje garden muyi pics " " nide sekun dawo ba inda zani " fanan tayi maganar tana kokarin kwanciya, riko hannunta zeenat tayi tace " wlh Baki isaba sekinzo munje munyi pics din nan " mikewa tayi tace " nide bazaku taba barina inhuta ba koh semuje ai " tagama magana tana hararansu da dara_daran idanunta, ta corridor suka bi yakaisu bangaren azaad daga nan suka gangaro kasa sukabi ta kitchen suka shiga garden din basuma lura da su azaad ba da Abba se yaseer dasuke zaune suna magana ba, suhaima da zeenat suna gaba seda suka shiga tukun suka lura dasu Abba dake zaune zeenat ce tace " laaaaah Abba ashe kuna nan Kuma " juyowa sukayi suna kallonsu " eh gamu nan munadan magana ne " cewar abba, murmushi yaseer yayi yace " ku karaso mana kuka tsaya agun" shide azaad ko tanka musu beyi ba suka karaso wajan, shigowa garden din fanan tayi cikin tafiyanta me kama dana mahauniya tana kallon flowers 🌺 din bakaramin burgeta sukayi ba hartazo zata wuce taga wani kyakyawan bunch of flowers din masu kaloli daban daban tafiya sukayi da hankalinta tanufi wajansu duk abinda takeyi batasan su Abba na garden din ba suna hiransu suna kallonta, gaban flowers din taje ta tsaya can Kuma tasa hannunta tafara shafa su cikin nishadi tafi 5mint agun kafin ta juya zata tafi,cikin rada taji ance " muna godiya sosai agareki da kika tabamu da hannunki me cike da karfin ikon jaaazana " asukwane tajuyo Dan taga wayeke magana gani tayi bakowa awajan dan duk tunaninta bekawo mata akan maganar daga gun flowers din bane ganin bakowa ne yasa aranta tace" kila kawai gizo ne kunne na kemin" tafiya taci gaba dayi abunta sannu ahankali flowers din data taba suka fara girma sunayin tsayi harsuka fi tsayinta duk batasaniba tafiyanta kawai takeyi amatukar razane su Abba suka mike dan duk wani motsinta suna lura dashi ganin flowers din sunzo dabb da itane kamar zasu tabata suhaima tafasa ihu tana fadin " wayyo fanan bayanki" jin ihun da suhaima tayine yasa azaad dagowa yana kallonsu ganin sun kafe waje daya da ido ne yasa yakai idonsa direction din dasuke kallo " ohhh shit " yafurta lokacin da yake kokarin tashi itakuwa fanan jin abinda suhaima tafada ne yasata zurawa aguje dan tamaki juyawa taga meye abayan nata, taku hudu zuwa biyar azaad yayi yakaishi inda take yarikota, rungumeshi tayi kam_kam kamar wacce zata koma jikinshi karasowa su yaseer sukayi inda suke suna ganin iKon Allah, azaad kallonshi yamayar kan flowers din dasuka girma suka zama kamar wasu bishiyoyi yayi ganin har time din basu koma ba suna tsaye kiqam yatsaya yayi wani tunani bakinshi yakawo dede kunnenta yace mata" kibude idonki sannan kijuya kikalli abinda ke gabanki " lokaci daya taji duk wani tsoron datakeji ya yaye ahankali tabude manyan idanunta tadaurashi akan cute face nashi dashima kallontan yake runtse idonta tayi dan bazata iya kallon cikin idonshi ba danji take kamar lantarki najanta, su Abba de suna ta kallonsu ,juyawa tayi kafin tadanyi step kadan tanufi flowers din tafuskance su, nan take yayi wani irin girgiza kamar ze fado kasa furanni ne suka fara zubowa akanta suna zubewe akasa ga dadin kamshi seda suka zubo duka flowers din gaba daya seda suka kare ajikinta yanda suke zuban abun burgewa kamar a India ,seda yazamana wajan bakomai kasa kuwa kamar anyi ruwan fure tsaban yanda suka zuba, wani irin juyowa tayi kamar wata robot seda sukadan ja baya da irin juyin datayin kamar ba lafiya ba banda azaad dako motsawa beyiba, kanta akasa kafin slowly tadago fuskanta idonta arufe eyelashes dinta yayi zara_zara kamar wanda ruwa yataba shi , Abba de tunda yake arayuwarshi betaba ganin irin wannan Al amarin ba se a film yau gashi yafaru agidanshi mamaki kamar yakasheshi, haka suhaima da yaseer suma mamakin sukeyi banda zeenat da azaad dansu abinda suka gani ranan ma yarufe komai tunda TV yatarwatse wannan ai kadan ne, ganin dasukayi komatsawa batayi ne yasa Abba yace " azaad jeka daukota " zuwa yayi yakai hannunshi kan kafadarta yadan tabata , slowly tafado jikinshi ganin tasake nauyintane yagane ta suma cakk yadagata kamar yar baby yayi falo da ita su abba sukabi bayanshi, ganin azaad yashigo da fanan ahannu ne yasa duk suka mike kwantar da ita yayi akan kujera yadauko bottle water yabude goran yashafa mata afuska , da mamaki ummi take tambayar abba meya sameta bece mata bakomai ba yadauko wani zancen Yana cewa zeenat tamiko mishi agogonshi ,sauke ajiyar zuciya tayi kafin taware idonta ganin mutane atsaye akantane yasa tamike tanabin falon da kallo tunawa tayi da abinda yafaru a garden kokarin tashi takeyi anty Amina ta taimaka mata tazauna ya al ameen ne yakaraso kusa da ita yarike hannunta yace" yar kanwa dama bakida lafiyane!?" Yagama maganar yana jiran amsarta girgiza mishi kai tayi alamar ah ah " to mutafi gida kinji " nanma still gyada mishi kai tayi, azaad nazaune yana binsu da kallo musamman fanan din Aransa yake magana "tabbas wannan yarinyar akwai

Please Login or Register in order to submit comment