Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

👩‍🔬 *Dr. ZAHRA* 👩‍🔬

_*Funny love story*_


*By Asmeety Ce*




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*




*Free Book*



*Page-1&2*



**WATTPAD LINK**Asma'u Aji Ibrahim

https://www.wattpad.com/story/302746450?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=ASMAUAJIIBRAHIM&wp_originator=mpzyPESu8LQOti9aB44TSAWdBLMfYyHXI2bTd%2F4xBGBoopEqZJVmZEtpYTjP3JfXV6X2Fj2EaDLHFWpku7oEsQX5xGWGb330DhtPLZnKCqh%2FAM7%2FAqJMgKjgMLG%2FeIY9


**Short Story**


*_Bismillah Rahman Rahim_*

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai._
_Allah Muna maka godiya da kasa muna daya daga cikin masu rai,_
_Ya Allah kasa mu cika da imani, ameeen._



_Ina miƙa godiya ta ga ɗuk Masoya na, ina kuma alfahari daku._
_Allah ya sake haÉ—e zuciyoyin mu gabaki É—aya_.

**Alhmdllhi Ala kulli Hamid**


*Wannan littafin ƙirƙirar ran labari ne Wadda Ni Asmeety na karkiro shi domin faranta Masoya na Ina Alfahari daku*


**Tsokaci**
*Ban yadda wata ko wani ya juya min littafi ba, idan hakan ta kasance kuma na bar ku da Allah*

*Idan akwai abinda kaga Ni ranka ko makamancin hakan to Please ka sanar min saboda zanji daÉ—in Hakan sosai, Allah yabar zuminci*



_Abuja_


Gidane Babba Mai shegen kyau da tsari. Gidan babba ne sosai wadda daga waje bakin Get zagaye yake da Flowers masu kyau green shar.

Cikin harabar gidan wasu furanni ne masu ƙyau da ɗaukan ido, ga Motoci daga wajan Parking space sun kai Shida suna a tsaye.

Wata kyakkyawar Budurwa na hango ta nufi wata kofa da yake nuni da nanne Mashigar cikin gidan

Budurwar tana isa kofar taja ta tsaya cak, tare da gyara jakar ta dake bayan ta a rataye.

A hankali ta murɗa Handle ɗin kofar tana sanya kanta cikin babban falon ta leƙa, ganin babu kowa yasa ta jin daɗi. Cikin sanɗa ta tura kanta ciki.

A hankali take takawa zuwa ciki tana waige waige
Ta kai kafar ta zata aza kan stairs É—in Benen ta jiyo Muryar a bayan ta.

"Sannu da ƙoƙari''.
Zaro ido tayi tana juyowa suna haÉ—a ido ta sakarwa Matar murmushi tana É“oye itacan dake hannun ta a bayan ta kafin tace,"Good Morning My lovely Ammeiy".

Harara Ammeiy ta dalla mata kafin ta fara kallonta tun daga sama har zuwa ƙasa.

Tana sanye da wando iya guiwa sai takalmi irin na Ć´an Ball da doguwar Safar ta, rigar ta mai dogon hannu ce wanda ta É—ame ta, sai ta É—aure gashin kanta da karamin robbon ta sanya hula face cap, hannun ta Kuma sanye take da bakin Safa.


"Is a Bad day is not a good day".
Cewar Ammeiy tana hararar ta.

Shakwaɓar da fuska tayi tarw da fadin,"Ohh Dear Ammeiy... What Happen?".


"MIMA is this good for you?"

Tana zunɓura baki tace,"To Ni Ammeiy maye nayi kuma?".

"Baza kisan Manene kike aikatawa ba, sai Son yazo kafin kı sani". Ammeiy na gama faɗin haka ta wuce Kitchen.

Bin ta MIMA tayi da ido ta shige kafin tayi Murmushi ta haura zuwa Bedroom dinta tana tsalle tana waka.

BuÉ—e kofar É—akin tayi dau dai kuma itama MIMA tana tura kofar suka ci karo

A tare suka sanya kara suna É—afe goshin su

"Wai ƙya baƙe gani ne?"

Tana Dariya tace"Naga dai bani kaÉ—ai bace mara ganin ko?"

Girgiza kai Maryam tayi tana kallon MIMA kafin taja hannun ta taja ta zuwa cikin ɗakin tana leko wajan kafin ta kulle kofar cikin ƙasa da murya tace"Hee Baby What a good News"


Murmushi MIMA tayi tana kallon Maryam tace"Mary kenan sai kace bani ba MASTER ZEE ce fa Haba É—ai ai na cinye wasan"

Ihu Mary tayi tana rungume MIMA tace"I You serious"

Harara MIMA ta dalla mata cikin matsifa tace"a a I'm lie to you"

Murmushi Mary tayi tace"Ai bamuyin haka daƙe, gaskiya I'm very very Happy"

Washe baki MIMA tayi tana baza gashin kanta tace"Kin taɓa jin inɗa Master yaji ƙasa?"

"A a Wllhy" cewar Mary tana Dariya

Tashi MIMA tayi tana É—auko Towel É—in wanka tace"Let Me shower first"

Tana ƙoƙarin shiga Toilet taji muryar Mary na faɗin "Kiyi sauri ki shirya ina jiranki a falo Wai UNCLE HERO zai zo"

Cak MIMA ta tsaya tana zaro ido kafin tayi Magana Mary ta fice daga É—akin

Bin bayan ta tayi da kallo tana jin faÉ—uwar gaba, takai kusan 30mnt a haka kafin jiki a sanyaye ta shige Toilet É—in


Mary turo kofar É—akin tayi ta shige tana kai idon ta kan bed nan ta hango MIMA lullube tana kwance

Zaro ido tayi cikin faduwar gaba tace"Sis are you fine?"

Bakin ta na karkarwa tace"No...no I'm feeling fine is an Fever"

"Innadillahi wa'inna ilaihi raju'un Sorry let Me tell for Ammeiy" tana ƙoƙarin tashi MIMA tasa hannu ta riko hannun Mary tana girgiza mata kai tace"No don't ba tare zakuje ɗauko UNCLE HERO ba?"
GyaÉ—a Mata kai tayi tana kallon ta

Cikin Muryan marasa lafiya MIMA tace"Kawai kuta fi kinga nima zansa mu yin Bacci É—aga nan"

Tausayi Ta bawa Mary cikin tausaya wa tace"No sis Idan kuma kafin muzo kika mutu fa"

Aiko MIMA tashi tayi cikin Matsifa tace"Kan uba to Wllhy sai kin rigani mutuwa Bara ki gani je ki abinki ki kyale ni aha"

Da Mamak Mary ƙe kallon MIMA cikin ranta faɗi taƙe"Mutumin da bayida lafiya shine da yin waddan uban faɗan"

Harara MIMA ta galla mata ta tashi ta shige Toilet tana mita ƙasa ƙasa


Numfashi Mary taja kafin ta fice a É—akin



A falo ta sami Ammeiy zaune tana jiran su

"Ammeiy mu wuce ko?"

"Ina ita Mara kunya Ć´ar uwar taki?"

"Haba Ammeiy nice bani da kunya yau kuma?"

Tana zaro mata ido cikin dagawar murya tace"I say Where is she"

Cikin tsoro Mary tace"Sh....she say she's not feeling well"

Tsaki Ammeiy taja ta fice daga Falon
Ajiyar zuciya Mary ta sauƙe tana fadin"Ohhh Thank God"

Fita tayi suka shige Mota Driver yaja suka bar gidan


A Airport suna zuwa dai dain kuma shima yana kan fitowa

Riƙe yaƙe da Trolling sa yana ja
Sanye yaƙe da ƙananun kaya riga fari da blue Black ɗin gins
Ga Kyakkyawan sajan fuskan sa Kwance taƙe lublub baki kir ga gashin kansa da ƙe Kwance tana yalki saban yasha gyara da mai
Fuskan sa manne yaƙe da farin glass


Driver na ganin sa yaje da gudu ya ansa akwatin yana masa maraba

Ammeiy sai Murmushi taƙe sakar masa

Shima Murmushi ya sakar Mata

Mary daƙe tsaye a gyafen Ammeiy itama sai Murmushi taƙe tayi tana kallon kyakkyawan fuskarsa cikin ranta faɗi taƙe"Woow this Man So Handsome guy yo"


Yana zuwa ya rungume Ammeiy yana Murmushi

Ammeiy cikin jin daÉ—i itama ta rungume sa tana masa maraba

"Welcome Uncle?"

Fuska babu wabo ya amsa mata

Shiga Mota sukayi kafin suka koma gida


Suna zuwa gida Direct Side É—insa ya wuce
Yana zuwa ya faÉ—a Toilet ya sakat wa kansa Shower
Bayan yayi wanka ya fito ya shirya cikin Manyan kayan sa Shadda light blue da ta kalmin sa baki Mai yatsu babu hula a kansa saboda shi baya damuwa da hula
Wayoyin sa ya É—auka ya fice yana sauri

A falo ya sami Ammeiy da Abbeiy suna zaune shima Abbeiy ya shirya cikin kayan sa Shadda fari da garen sa da hulan sa,

Zuwa yayi ya zauna kasan Kapet ya gaida Abbeiy

Murmushi Abbeiy yayi yace"Sannu da zuwa Son yaya aikin kuma "

Cikin zazzakar Muryan sa yace"Alhmdllhi Abbeiy"

"Matar ta samu sauƙi ko?"

"Eh wllhy sai dai godiya"

"Gud Allah ya Kara Lafiya"

"Amen"yace yana ƙoƙarin miƙewa

Kallon sa Abbeiy yayi yace"Kaima Juma'an zaka ko?"

"Eh Abbeiy"

Yana tashi Yace, "Ok Muje nima can zani daman".

Ya kalli Ammeiy tare da fadin,"Bilkisu Bara mu wuce".

Suna ƙoƙarin fita dai dai alokacin MIMA na saukowa daga stairs tana fadin,"Abbeiy kazo min da ice cream yau bazan ci abincin dare ba..............''.






*More comment*
*More Typing*
*Share Fisabilillah*

👩‍🔬 *Dr. ZAHRA* 👩‍🔬

_*Funny, love story*_


*By Asmeety Ce*




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*




*Free Book*



*Page-3&4*



**WATTPAD LINK**Asma'u Aji Ibrahim

https://www.wattpad.com/story/302746450?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=ASMAUAJIIBRAHIM&wp_originator=mpzyPESu8LQOti9aB44TSAWdBLMfYyHXI2bTd%2F4xBGBoopEqZJVmZEtpYTjP3JfXV6X2Fj2EaDLHFWpku7oEsQX5xGWGb330DhtPLZnKCqh%2FAM7%2FAqJMgKjgMLG%2FeIY9


**Short Story**


*_Bismillah Rahman Rahim_*

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai._


**Alhmdllhi Ala kulli Hamid**




Wani irin kallo ZAIF yayiwa MIMA
Ita ko MIMA ko ajikinta

Murmushi Abbeiy yayi yace"Ok Dear"
Juyowa yayi ya kallesa yace"Son mu tafi ko"
Murmushi yayi yana kallon MIMA girgiza kansa yayi suka fice

Zama tayi kan kujera tana kallon TV
Ammeiy abin haushi ya bata ta kalleta tace"yanzu MIMA haka zaki cigaba da rayuwar ki babu ruwan ki da girmama na sama dake balle ki kalli darajar sa mmm?"

Turo baki tayi tace"To Ni Ammeiy shikenan dan nace Abbeiy yazo min da Ice Cream shine laifi sai ayita jin Haushin mutum dan yayi abinɗa ransa yaƙe so"

Cikin faÉ—a Ammeiy ta mike tayo kanta aiko MIMA na ganin haka data tashi a dari uku da tsintin ta ruga zuwa Bedroom dinta

"Shegiya da kin tsaya ai kinga abinda zayyi miki "

Da gudu ta shigo dakin tana haki
Mary daƙe Kwance tana waya ta tashi a firgice ta rufe kofar tana kallon MIMA itama tana haki

Bayan MIMA ta samu ta ɗan ji sauƙin numfashin nata sai kawai ta fashe da dariya harda rike ciki tana kwanciya kan bed
Mary binta tayi da kallo kafin taga MIMA na nunata da yatsa
"Wai maye kika gani kinshigo a guje haka?"

Tana dariya tace"na zaci kinsan dalilin gudun nawan fa naga ƙema kin ruga harda rife kofa"
Dariya takeyi sosai

Mary zama tayi kan bed tana jin Haushin Mima

Sausauta dariyar Mima tayi tana kallon Mary tace"Kai Wllhy Mary anyi Masauraciya Yasin" sai kuma ta kara fashewa da sabon dariya tana rub da ciki

Mary da kanta abin ya bata dariya itama dariyar ta shiga yi tana kallon Mima

Sosai suka sha dariyar su suna sauke numfashi

Tashi Mima tayi tana kallon Mary tace"yawwa tunÉ—a kin tayani da dariyar haukan sai mu sauka muci abinci dan yunwa nake ji kamar an hurse min kayan ciki na Yasin"

Cikin fada Mary tace"Wllhy banason iskan ci nice mahaukaciyar ko maye?"

Mima na shiga Toilet ta juya tayi mata gwalo tace"duk yadda kika ce Madam Maryam"da gudu ta shige tana rufe kofar

Girgiza kai Mary tayi tace"shegiya sai shegen tsoro sai kace farar kura"





Abbeiy suna hanyar komawa gida yace wa Zaif yabiya su sayawa Mima aikan ta
Wani irrin haushi ne Zaif yaji badan yaso ba ya siyo ice cream din

Bayan yayi Parking É—in Motan a Parking space suka fito
Kallonsa Abbeiy yayi yace"zan wuce Side dina sakon Mima Kayiwa ko Mary waya tazo ta amsa"

"No Abbeiy kabar shi kawai zan shigar mata shi" karba yayi ledan yana nufi Side din sa

Yana zuwa a falo ya ajiye ledan ya wuce Bedroom É—in sa
Bayan yayi wanka ya shirya cikin kananun kayansa kafin ya fito falon
Remote ya É—auka ya kai BBC Channel yana kallon labarai

Ya daÉ—e yana kallon kafin idanun sa ya sauka kan ledan da ya shigo dashi
Tsaki yaja yana daukan wayan sa ya kira Mary tana dagawa yace"kice tazo ta amsa " yana gama faÉ—in haka ya kashe wayan yana ayyana abinda zayyi Mata


Mary bayan Zaif ya faÉ—a mata sakon
Juyowa tayi ta kalli Mima wacce taƙe kwance tana karatun Novel Book na Hausa
Sosai ta shagala da karatun dan Book É—in ba karamin daÉ—i yayi ba Marubuciyar ta tsara Book natan yadda ya kamata
Bataji sanda Mary ke yi mata Magana ba dan gaskiya wannan Book a wajan Mima ba karamin daÉ—i yayi mata ba
Buginta Mary tayi tace"dalla Kitashi Uncle Yana kiranki"

"Ya bani Maye Kuma" ta bata amsa atakai ce tana kuma cigaba da karatun ta

"Wai Ni kike tambaya, idan kinje zaki sani ai"

Gyara kwanciyar ta tayi tana ci gaba da karatun ta

Ganin ko ajikinta yasa tace"Mima cewa fa yayi wai nagaya miki kije ki ansa, bansan maye zaki ansa ba"
Aiko da sauri ta tashi daga kwancan tana kallon Mary tace"Wllhy ice cream dina ne Wow"
Sauka tayi ta nufi hanyar fita taji muryar Mary tace"gaskiya a hado harda rabo na dan yau kam da rabon zan aza ruwan zafi"
Harara ta dalla mata cikin matsifa tace"Yasin zakiga aikin raban ki kuwa, kuma ai ban hanaki aza ruwan zafin ba "

Mary tana dariya tace"A iso lafiya"

Ko sauraron ta batayi ba ta fice tana magana ƙasa ƙasa

Babu kowa a falon hakan yasa ta fice tana salle tana waka

Tafiya tayi kadan ta samu waje ta zauna tana mai da Numfashin cikin jin haushi tace"gida babba haka sai kace filin wasan cricket, inama ace Abbeiy zai yarda na ringa kawo abokan wasan namu mu ringa buga wasa anan amma bazai bari ba"

Sadda ta huta sosai har ta fara salle tana gwada yadda wasan zayyi daÉ—i idan a filin gidan ne kafin ta tuna da abinda ya fito da ita taja tsaki ta nufi Side É—insa


Tana zuwa ta buÉ—e kofar falon ta tura kanta ta shiga ko Sallama babu
A tsaye a bakin window ta hango sa

Zaif kan yana tsaye yana kallon ta, ta glass duk abinÉ—a take yi akan idon sa
Cikin ransa faɗi yaƙe"yarinya kamar shaidaniya haka"

Tsayawa tayi a bayan sa kafin tasa hannu ta riko hannun sa cikin shagwaɓa fuska tace"Hero gani"

Kallon Up and down yayi mata kafin ya kamo hannun ta suka nufi wajan zama
Bayan ya zauna kan kujera itama ya zaunar da ita sannan yasa hannu ya É—auki ledan ya buÉ—e
Ice Cream É—in roba biyu ne duka biyu ya buÉ—e Marfin kafin ya É—auki spoon ya diba ya kai bakinta

A hankali ta ware Lips dinta ta karɓa tana Murmushi

Mika Mata spoon din yayi yace tasha

Nan Mima ta fara sha tana lumshe ido

Shiko Zaif cigaba yayi da kallonsa

Rabin roban tasha kafin ta kallesa tace"na kashi Hero"
Murmushin gyafen Baki yayi irrin ta mugunta kafin ya juya ya kalleta yace"bana wasa daƙe dan haka ki shanye All robans oya now"ya karishe maganan da karfi yana tashi ya zaro bel ɗin sa

Aiko MIMA babu bata lokaci ta fara shan ice cream
Roba daya tashi
Kafin ta kallesa taga yana zura Mata ido cikin kuka tace"Wllhy Yaya Zaif na kishi fa cikina fashewa zayyi"

Daga bell din yayi ya wasa mata shi a baya
Kara ta kwalla tana fashewa da kuka
Nan tashi shanye Ice Cream tana kuka

Bayan ta shanye tas ta fara ƙoƙarin tashi tana rike cikin ta, ta nufi hanyar fita

Zaif baice mata komai ba harta fice

Tafiya take daƙer harta iso kofar shiga falon su

Tana zuwa ta fashe da kuka mai sauti
Ammeiy ce ta leko daga Bedroom dinta tana kallon Mima da tarike cikinta tana kuka

"Wai maye haka" ta tambaye ta

"Ammeiy ice cream tasha fa"cewar Mary daƙe Zaune a kan kujera tana kallon su tana dariya

Wani irin kallo Mima tayi mata na zan kama ki ai

"Mami Ina rabo na" ta tambeta
Cikin matsifa tace"yana gidan ku Ć´ar rainin Sense kawai"

Ammeiy ce tace"bakin baya mutuwa kenan ko?"

GyaÉ—a Mata kai tayi tana tafiya kamar mata mai ciki rike da cikinta , ta shige Bedroom

Dariyar Ammeiy tayi tana girgiza kai ta shige Bedroom dinta


Da Daddare bayan sunyi shirin kwanciya Mima ta kalli Mary tace"Dariya kikai min dazun ko? Gud you see ur resort"

"A a ai Bama haka dake ai Sis yi hakuri" ta faÉ—a tana riko hannun ta

"Ok naji nayi Saida safe" tace tana jan Balanket ta rufu
Itama Mary rufuwa tayi ta kwanta tana bin abinda Mima zatayi mata dan karya ne Kayiwa Mima laifi ta kyale ka a haka har Bacci barawo ya sace ta


Da washe gari Tun karfe 3am Mima ta farka
Bayan tayi wanka ta É—auro Alwala ta fito ta shirya cikin kayan ta na wasa
Kallon Mary tayi tana Murmushi ta girgiza kanta ta fice daga dakin

SanÉ—a take a hankali tana waige waige har ta fita daga Falon
A waje ma babu kowa duk sun tafiyin sallah dan lokacin sallan Asuba yayi maza duka suna masallaci

BuÉ—e get tayi tana lekowa ganin babu kowa yasa ta fice da sauri tana waige waige

Wata bakin Mota ne na hango nan tana zuwa ta buÉ—e bayan mota ta shige tana faÉ—in " muyi sauri kadda sufito su ganmu"

Nan mai Motan yaja suka bar kofan gidan

Mary Bata tashi ba sai kusan karfe 8am
Salati ta farayi tana kallon window ganin rana ya fito rau

Tashi tayi da nufin shiga Toilet taji budewar kofa juyowa tayi tana kallon mai shigan
Zaro ido tayi tana kallon ta tace"wai har kin dawo daga wasan ko maye"

Tana ajiye karar nata tace"Gashi ko kinga newa idon ki kuwa"

"Shine baki tasheni yin Sallah ba duba fa
har karfe 8am fa "

"Wai kinason kice min bakiyi Sallah ba haryanzu?" Cewar Mima tana nufar Toilet

"Eh Mana ai kinki kita sheni ai"
"Ayya Sorry tunda bakiyi Sallah har yanzu ba Bara nayi wanka na fito kinga yau an yafe miki yin Sallah"
Tana gama faÉ—in haka ta shige Toilet da gudu ganin Mary ta nufo ta


Suna zaune kan Daining ta fito fuskarta a harÉ—e ta sami waje ta zauna
Gaida Abbeiy da Ammeiy tayi tana kallon Mima da take mata dariya ƙasa ƙasa

Ammeiy ce ta kalli Mary tace"Daughter lafiya naga Ranki duk a É“ace"

Tana hawaye tace"Ammeiy ai Gatanan "

Mima na dariya itama tai kwaikwayon tace"Ammeiy ai Gatanan"

Abbeiy sawa ya daga mata tayi shiru

"Maye tayi miki Daughter" inji Abbeiy yana kallon Mary da take share hawayen ta
Tace"taki ta tayar dani nayi sallan Asuba fa"

Mima na ajiye cofin hannunta ta kama baki tace"laaa jimin sharri Abbeiy itafa jiya tace kadda na tayar da ita da asuba nan gaba saboda a sanyin nan bazata iyayin sallah da asuba ba shiyasa fa naki na tayar da ita"

Kallon Mamaki Mary keyiwa Mima ji tayi Abbeiy yace"Ohh ashe kece da laifi Daughter Kuma kike kuka"
Cikin kuka Mary tace"Wllhy Abbeiy bamuyi haka da ita ba sharri ne kawai take yi min"
Aiko itama MIMA kukan ta fashe dashi tana tura Plat É—in dake gabanta tace"shikenan tunda baza ku yarda dani ba daman ba sona kuke yiba na sani ai"
Rungume ta Abbeiy yayi yace"Sorry is ok gaskiyar ki ne, look Daughter na karaji kunyi abu tukun nan Kizo kicanza magana to Wllhy sai nabata miki rai"

Mami na kwance kirjin Abbeiy tana kallon Mima tayi mata gwalo tana Dariya........



More Comment
More Typing
Share Fisabidillah

👩‍🔬 *Dr. ZAHRA* 👩‍🔬

_*Funny, love story*_


*By Asmeety Ce*




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*




*Free Book*



*Page-5&6*



**WATTPAD LINK**Asma'u Aji Ibrahim

https://www.wattpad.com/story/302746450?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=ASMAUAJIIBRAHIM&wp_originator=mpzyPESu8LQOti9aB44TSAWdBLMfYyHXI2bTd%2F4xBGBoopEqZJVmZEtpYTjP3JfXV6X2Fj2EaDLHFWpku7oEsQX5xGWGb330DhtPLZnKCqh%2FAM7%2FAqJMgKjgMLG%2FeIY9


**Short Story**


*_Bismillah Rahman Rahim_*

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai._


**Alhmdllhi Ala kulli Hamid**

Ammeiy kallon Abbeiy tayi tace"Amma Alhaji kana É“ata Yarinyar nan fa É—iyewa gaskiya hakan babu daÉ—i"

Ko kallonta Abbeiy bai yi ba ya fita yana faÉ—in"Ni na wuce "

"Allah ya bada Sa'a ya kiyaye"

"Amen"yace kafin ya fice

Ammeiy tashi tayi ta nufi Bedroom É—inta

Mima ce ta kalli Mary tana dariya tace"Malama ashe babu daÉ—i kenan, jiya kikai min dariya harda cewa(Ina rabo, kin kawomin rabon nawa) to kinga ai yanzu na rama kinsan ZAHRA bata bari ta kwana ta lalace ehe"
Tana gama faÉ—in haka ta tashi tana murguda baki tabara wajan


Mary sosai tayi da nasanin yiwa Mima dariya jiya, dan ita babu abinɗa tafi tsana kamar ace lokacin sallah ya barta abinda yana damin ta sosai , jiki a sanyaye ta miƙe tabar wajan zuwa Bedroom



Abbeiy ne zaune a office Yana aiki wayan sa yayi kara
Hannun yasa ya É—auka

"Na,am Dan iskan yaya kake"

Daga É—ayan bangaren yace"Nrml ya aiki ya kwana biyu"

Abbeiy yana dariya yace"Alhmdllhi ya iyali da sauran su"

"Duk suna lafiya"

"Yayi kyau" cewan Abbeiy yana Murmushi

"Abokina ya najika shiru fa haryanzu fa kai muƙe jira"

Abbeiy dariya yayi yace"Wllhy sorry fa na manta amma insha Allahu dana koma gida zakaji bayani "

"To ina jiranka , kagaida min da iyali"

"Insha Allahu zasuji sai anjima" Abbeiy yace yana kashe wayan


Da yamma suna zaune a falo ya shigo bakinsa É—auke da Sallama
Bayan ya zauna ya gaida Abbeiy da Ammeiy nan Mary da Mima suma suka gaida sa ,amsa yayi fuska babu yabo ba fallasa

Abbeiy ne ya kallesa yace"Uncle kasan abinda yasa na kira ka?"

Cikin ladabi da biyayya yace"a a Abbeiy"

Zama Abbeiy yayi yana kallon Zaif yace"munyi magana da Abokina Alhaji Tanimu akan Maganan auran ku da Aisha shiyasa nace gobe kaje ku fahimci junan ku kafin asa ranar auren"

Tunɗa Abbeiy ya fara magana Zaif zuciyan sa yaƙe bugawa, har Abbeiy ya kammala Maganan

Kamar mai koyon Magana yace"T..to Abbeiy" a rarrabe yayi Maganan yana lumshe idonsa jin kansa yayi masa wani irrin tsara wa


"Wow ashe zamusha biki kai Uncle Hero zai zama Ango wllhy harna hango ka cikin manyan kaya irrin ta angwaye" cewar Mima tana kallon Zaif


Wani irrin kallo Zaif yayi mata wadda ita batama san yana yiba tana ta shirmin ta

Abbeiy kallon ta yayi yace"Mama ta gobe kishirya É—an Abokina zaizo ku gaisa"

Kallonsa ya kai kan Mary yace"Yaya ta ƙema ki turo waccan yaron da na taba ganin ku tare kuna hira na tambaye Ammeiy ku tace kuna son junan ku so kiyi Masa Magana ya turo ayi zancan Auran ku kinji?"

Cikin jin daÉ—i tace"To Abbeiy"

Mima da tunÉ—a Abbeiy yayi Mata Maganan É—an abokin saa zaizo tayi shiru tana tunanin abinÉ—a zai biyo baya


Da Daddare misalin ƙarfe 9 yana zaune a babban falon sa, wayan sa daƙe gyafen sa ce tayi kara hannu yasa ya ɗauka kallon gaban screen ɗin yayi ganin mai kiran nasa yasa shi yin Picking

Shiru yayi kafin can kuma yace '' sai yanzu kaga daman kira na?"

Can bangaren Saddam yace"Sorry Wllhy aiki yayi min yawa shiyasa kajini shiru, ya maye labari?"

Numfashi Zaif yaja kana yace"Gobe inason zamuje da kai wani waje"

"Ina?" Saddam ya jefa masa da tambaya

É—afe kansa Zaif yayi yana hura iskar bakinsa, shi a rayuwarsa bayason yawan tambaya Shiyasa ma É—uk abinÉ—a ance masa yayi ko yace ayi bayason tambaya ayi É—in yafi

Saddam jin Zaif yayi shiru ne yasa shi gane abinÉ—a yasa shi yin shirun Murmushi yayi yace"Ok zanzo"

Kamar mai kowon Magana Zaif yace"Thank" Yana gama faÉ—in haka ya katse wayan

Kwantar da kansa ya yi kan kujera yana lumshe idonsa, tunani ya shiga yi can kuma sai ya fesar da numfashi ya miƙe ya shige Bedroom

Yana shiga Bathroom ya wuce ya sakar wa kansa Shower
Tsayawa yayi ruwan yana dukan tsakiyar kansa , lumshe idonsa yayi yana jin yadda ruwan ke shigan sa
Ya jima a hakan kafin ya

Please Login or Register in order to submit comment