Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaune zata yiwa Ammi magana sai ga Khamis nan , Ammi ce ta dubesa tace "daga kai mai bacci shine na jika shiru ko ?" sosa kansa yayi kana yace "Ammi labarin abinda ya faru take bani "Aisha na daga gefe ta rufe baki tana zaro ido , to maza tashi ka bamu guri zanyi magana da ɗiyata , Khamis na dariya ya miƙe kana ya fice .
juyowa Ammi tayi ta kai kallonta kan Aisha tace "ƴata "Aisha tace "na'am Ammi ce taci gaba da cewa "inason in tunatar dake kinada aure yanzu ko kin sani ?"eh mama Aisha ta faɗa tana kallon Ammi ta sunkuyar da kai "son mijinki ne kuma ni ki ɗaukeni a matsayin uwa ba suruka ba kinji ?" eh Aisha ta faɗa tare da share hawayen fuskarta.
[03/09, 2:08 pm] Mom Islam Ce 💃: 47 & 48

Ammi ta ci gaba da cewa "zan kula dake kamar inda zan kula da ɗan cikina ina fata kin ɗaukeni a matsayin mamanki ? eh Aisha tace good Ammi ta faɗa , zo muje bedroom Ammi tace "tare da riƙo hanun Aisha "binta Aisha tayi suna shiga Ammi ta zaunar da ita kan kujera ta ɗauko cup da cokali ta ɗibo wani garin magani da zuma ta bata ta shanye ta kuma ɗibo wani garin maganin ta haɗa mata da madara ta bata babu musu tasha , wani kwano Ammi ta buɗe da yake ɗauke da farfesun kaji sai tashin ƙamshi take amma jikinta duk magani , haka Ammi tace "sai ta cinye naman nan tsaf ai masoyayyarsa ce " shima babu musu ta fara ci tana gyatsa kasancewar taci abinci daga zuwanta tace "mama zuwa anjima zan ƙarasa na ƙoshi "to Ammi tace "ta rufe kwanon tace zan baki wasu turaruka inhar kikayi sallahar isha'i ki dinga shafawa a fuskarki kinji ?"to Aisha tace " kana Ammi tace " jeki kokuma zo babu gama ba , gobe insha Allah zaki koma ɗakinki banason ƙazanta duk da nasan ba halinki bane kuma ki iya magana kinga iya magana da sanyaya murya tana ƙoƙarin sanyawa mai gida yaji yana ƙara sonki ,ki iya tafiya da zarar kinga yana kallonki sauya salon tafiyarki kuna haɗa ido kiyi masa murmishi ,ki rage kunya bance ki zamo mara kunya ba inason inga kin yi fice kema kin zamo tauraruwa kin kawar da ƴan matan dake yi masa layi , dariya Aisha tasa kana tace "mama kenan "cikin gasgatawa Ammi tace "tom shi kenan "in kikayi wasa wata seta ƙwace miki mijin wlh ,dai daita nutsuwarta Aisha tace " tunda Ammi tace "ta cire kunya to bari tayi mata wata tambayar "Aisha ce tace "mama dama inason yi miki tambaya ne ?" ok ina jinki "Ammi tace "Aisha ce tace mama dama yaya ne yake riƙe min hannu kuma a islamiya ance babu kyau , bugar goshinta Ammi tayi kana tace "duk faɗan da nayi miki bai shiga jikinki ba kenan ?"da wane yare zan faɗa miki ne ?"kiyi haƙuri mama Aisha tace " da alamun damuwa " no ba zancen haƙuri bane amma zuwa gaba zan faɗa miki jeki kuma ban amince zuwanki gurinsa yau ba Ammi ta faɗa tana kallonta koda ya kiraki kice nace "karki fita ,to Aisha tace "jikinta a sanyaye ta fita , Ammi na zaune a bakin gado tace "wato wanan yarinyar akwai aiki na lura har yanzu ƙuruciya na yawo a kanta hhmm Ammi ta nisa kana ta miƙe ta nufi kitchen , samun baba tayi har ta gama aiyuka sannu Ammi tayi mata kana tace " tafasa min wanan maza pls , cikin ladabi baba ta karɓa tasa a tukunya ta kunna gas tasa ruwan da Ammi ta umarceta , bayan Ammi ta koma bedroom ɗinta ta zauna tana wasu tunani barkatai.
Washe gari mama suka shirya zuwa gidan su Aisha tare da kai mata ragowar akwatunanta malam ne yaba mama dubu biyu yace "ta shiga kasuwar nan anguwar ta siyowa Ammi lalle tunda sunga ƙafarta baya rabuwa da lalle da kuma citta da kaninfari ,bayan mama tayi masa godiya taje ta siyo , tana dawowa suka tari mashina suka wuce , basu sha wuya ba gurin samun gidan kasancewae mai gidan ba ɓoyayye bane duk da anguwar ta masu kuɗi ce ,mai sun sallami masu mashin sum sauka suka fara bubuga gidan suna ƙwaɗa sallama , cikin sauri mai gadi ya buɗe ƙaramar ƙofar kana yace "wa kuke nema ?"maman Ummi ce tace "nan ne gidan su Aisha ?"eh mai gadi yace " to barin isarwa masu gidan ya rufe ƙofar tare da komawa cikin gidan ,mama da ta gaji da tsayuwa tace "nifa shi yasa ban fiye san zuwa gidan masu get ɗinnan ba sai an dinga jawa mutane rai kafin a barsu su wuce mtsw, ba'a ɗau lokaci ba sai gashi yadawo yace "nace su maman Aisha kukace ko ?" eh suka amsa Aisha ce ta fito mai gadi ya durƙusa yace "Allah ya temaki amarya , ko kallonsa batayi ba ta buɗe get ɗin tare da kururuwar murna ta rungume su mama da maman Ummi tace "ku shigo , mama ma kanta taga saurin girman Aisha cikin fara'a suka bi bayanta ta shiga dasu cikin gidan kai tsaye palo ta kaisu nanfa kallo ya koma sama Allah yayi temako palon babu kowa , maman Ummi sai kallon kwaliyar dake malale a saman take tana jinjina kai mama ko bata tsaya kallo ba sbda karta nuna ƙyauyan cinta a gefe , dawowar Aisha daga kiran Ammi yasa maman Ummi kallon Aisha tace "ƴata ta girma , durƙusawa Aisha tayi ta gaishe su bayan sun gaisa ne Ammi ta fito zama tayi tana faɗaɗa fara 'arta suka gaisa bayan sun gaisa sai ga baba da plet plet na abinci har huɗu ta jere a gabansu da drinks da ruwan gora kana ta gaishe su , mai gadi da dirver da mai bawa flawa ruwa da mai kula da masu share share ne suka shigo da akwatunab da su mama suka zo dashi , masha Allah Ammi tace " nan suka ɗan taɓa hira mama taba Ammi kayan data siyo mata , godiya Ammi tayi kana tace "kuzo muje kuga part ɗin ƴata "dariya su mama sukasa kana suka miƙe , tafe suke suna kale kale har suka iso sashen Aishan da sallama suka shiga suka fara bin ɗakin da kallo wani farinciki da iskar ni 'ima ce ta fara ƙaɗa mama tana mai jin daɗin inda suka ɗauki Aisha kamar ƴarta gashi ta shigo cikin gata ɗakinta kamar na wata sarauniyar , sai da Ammi ta rakasu ko ina na gidan kana suka fito suka dawo part ɗin Ammi sukaci gaba da yi mata godiya da sanya albarka kasancewar basuda abinda zasu biyata komai muhimmancinsa , sosai Ammi taji daɗi da hakan Aisha kam baki yaƙi rufuwa gata gasu mama ,sai murna take cikin zumuɗi tace "da fa gobe zanzo amma tunda kunzo sai sati mai zuwa zanje harda gidan su yaya , Allah ya kaimu su mama da Ammi suka faɗa , maman Ummi ce tace "in kinzo kwa haɗu da Ummi dan ta dawo gida "cikin murna Aisha tace "ai kuwa , miƙewa Ammi tayi ta basu guri kunsan ance tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah ta koma bedroom ɗinta tana ƙara tuno adu'oin da su mama suka dinga yi mata tare da godiya , haƙiƙa taji daɗin wanan abu .
Mama ce ta dubi Aisha kana tace " Aisha ki riƙe baiwar Allahan nan tsakani da Allah dan a halin yanzu bakida kamarta ko mijinki ne ya ɓata miki rai karki sake ki nuna mata bare ki faɗa mata , ki zamo mai ɓoye sirrin mijinki haka kuma karki dinga yi masa gatsali dan zata iya dena yi miki duk wasu abubuwa , ki nunawa mijinki so na tsakani da Allah yin hakan zai sa ki sami gurbi a zuciyarta , bayan haka ki zamo mai tsafta duk da kunada ƴar aiki kena ki dinga taɓuka wani abin karkice dole sai ita , kuma kar ya zamo kina bada wanki harda wandon mijinki gajere da ƴar shimi lol ki cire ƙiuya ki wankesu lada zaki samu , banda faɗar maganar da bata dace ba banda rashin tausa murya banda ganin kayansa kice ai bai san dasu ba ki ɗauka ko ki kyautar wanan ba hali mai kyau bane tun wuri ki yi hankali yanzu fa kin girma ibada zaki fara wato neman aljannar ki inkinbi waɗan nan hanyoyin zaki sameta cikin sauƙi, Aisha na zubarda hawaye tace ,ɗazu mama tayimin faɗa sosai har ta bani wani abu ta haɗa da madara da kuma wanda ta haɗa da zuma da kuma kaza amma akwai magani a ciki "murmishi su mama sukayi kana mama tace "nikam bansan da me zan sakawa wanan baiwar Allahan ba wlh mama ta share hawayen fuskarta tace " duk mai son ɗanka ai yana sonka fatana karki watsamin ƙasa a ido kamar inda ta riƙeki tsakani da Allah kema ki riƙe ɗanta da amana , wlh kin gama min komai , ki zamo mai tattalin kayanki ko da yake ku bakwa jin garin amma kidai tattala shima yanada muhimmanci malam yace "a gaisheki , ina amsawa Aisha tace "idanunta sunyi ja alamar tayi kuka ta gaji , to bari mu tafi suka miƙe tare da cewa "Aisha tace "wa Ammi sun wuce , tafiya kiran Ammi tayi bayan tayi sallama Ammi ta buɗe ƙofa tace " wai su mama zasu tafi
[03/09, 3:53 pm] Mom Islam Ce 💃: 49 & 50

Fitowa Ammi tayi hanunta riƙe da wata leda mai kyau ta miƙawa Aisha tace "ta kai musu ga sunan tahowa "to Aisha tace "taje ta miƙawa maman Ummj kayan "godiya maman Ummi tayi wa Ammi dake tahowa suka fita Ammi ta kira driver tace "ya kaisu "shiga motar sukayi driver ya ɗaukesu sai anguwar su sunyi tafiya mai ɗan nisa kana suka iso anguwarsu , godiya suka yiwa drivern kowa yayi gidansa , mama na shiga ta samu malam harya gama dafa shinkafa dariya tasa tace "yau ga malam da aikin mata ,snnu da dawowa yayi mata ,a tsakar gida mama ta zauna kana tace "munsha tafiya wlh kuma mun samo abin arziƙi dawowa malam yayi ya zauna kana yace " to masha Allah , mama ce tace "aiko munga Aisha tayi dimir mir abinta har wasu kumatu ta ajiye wlh ,dariya malam yasa yace "Allah mun gode maka daka azurtamu da surikar arziƙi wanan mata tanada halin kirki wlh , suna tsaka da hira maman Ummi ta shigo da ledar da Aisha ta bata ta zauna bayan ta gaishe da malam tace "maman Aisha gafa abin arziƙi "mama ce tace "me muka samu ?"fifito da kayan maman Ummi tayi ledar maggi kala kala har huɗu ga mangyaɗa na gora ga manja roba bibiyu cikin farinciki malam yace "aiko mun gode Allah ya saka mata .
Washe gari yau ne Aisha zata koma part ɗinta Ammi ta gama yi mata duk wani shirye shirye da zata yi mata ,tun jiya Khamia yasa aka gyare part ɗin yau kam sai tashin ƙamshi yake kamar yau ta fara shigowa , Ammi da kanta ta kaita part ɗinta tare da dafa kanta ta dinga kwararo mata adu'a ,daganan ta barta ,kasancewar bayan isha'i ne yasa Aisha tashi ta buɗe drower ta ciro kayan baccinta riga da wando gajere iya guwaiwa , mai ruwan pink da hularsa tana da kwaliyar wani farin stone a gaba , kwanciya tayi bayan ta ɗauro alwalah tayi adu'ar bacci ta kwanta , ƙarfe tara dai dai Khamis ya shigo hanunsa ɗauke da kaza leda biyu yasa ɗaya a fridge ya shiga part ɗinta da ɗaya da sallama ya shiga kasancewar ƙofar a buɗe take ya shige , samunta yayi har tayi bacci ya zauna tare da ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo ya ɗau lokaci mai tsayi yana kallonta daga ƙarshe ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa ya sauya kaya i zuwa na bacci ya dawo ɗakinta ya kwanta gefenta tare da rungumeta yaja musu blanket asbha ta gari.
Bayan malam sun gama magana da baban Ummi akan Ummi mahaifin nata yace "ai ƴarshi ce malam kaima mai aurar da ita ne ,godiya malam yayi suka yake sadaki malam yace "insha Allah zan sanar masa , cikin sa'a zuwa yamma sai ga yaya Zakari ya shigo da malam ya sanar masa murna kamar me yace "tafe nake da kuɗina malam ba tun yanzu nake tarasu ba , mamaki ne ya kama malam yace "wato ni yanzu kama dena jin kunyata ko ?"dariya yaya Zakari yayi yana sosa kai wata leda ya janyo ya miƙawa malam kana yace "dubu ɗari ne malam zaro ido malam yayi yace "a kai musu duka ?"eh malam insha Allah har kuɗin da za'ayi hidimar komai baza'a rasa ba insha Allah "to malam yace "ya karɓi kuɗin da bismillah .
Washe gari komai ya kammalah an yanke biki saura wata biyu , murna gurin mama abin ba sauƙi a cewarta tayi surukar kirki masha Allah .
Yau da dddaddare yaya Zakari ya dawo daga gidan su mama ya shiga ɗakin anty Fiddausi kasancewar kaka har tayi bacci yana shiga ya sami anti Fiddausi ta haɗe cikin gajeran wando bai ƙarasa cinyarta ba tasa riga iya cibiya ,yana shiga da sallama taje ta runfumesa cikin farinciki ya riƙe mata hannu tare da shafo gefen fuskarta yace "ya kike da fatan kin wuni cikin farinciki , a ƙasan zuciyarsa kuma yana tunanin inda zai fara yi mata magana , hardai ya kare yace "muje mu zauna inasan magana dake "cike da murmishi tace "to gani zo muje hannunta ya riƙe ya zaunar da ita kana ya fara shafa sumar kanta a hankali ya dawo fuska yana yawo da hanunsa a jikinta har wani lumshe ido take tana cewa " yau da wani salon kazo ?"naganka cikin cikin shauƙi "lumshe idonsa yaya Zakari yayi kana yace "komai naki birgeni yake , a ƙasan zuciyarsa kuwa cewa "yake nakasa sanar mata da abinda ke cikin zuciyata wayo Allah na ,tallafo kansa tayi ta haɗe bakinsu guri ɗaya ta fara rikitashi da kisess masu zafi jin haka yasa yaya Zakari cewa " fiddausi nitsu muyi magana idonsa a lumshe zama tayi ta nitsu kana tace "ina jinka " aure nake san ƙarawa badan in cuceki ba sai dan ki sami matemakiya kuma ƴar uwa shiyasa , bayan haka karki ɗauka zanyi ne da nufin na wulaƙanta ki, bawai dan bana sanki ba ya ƙarashe maganar da bata haƙuri "sai da ta bari ya gama zubar surutunsa sanan ta fincike jikinta daga rungumar da yayi mata lokacin da zai fara magana ta ɗauki cup ɗin dake kusa da ita ta jefeshi dashi ta ɗauki ta duk wani abu dake kusa da ita ta dinga wurga masa tana kuka kana tace "nayi dana sanin haɗuwata da kai wlh wanan wace irin rayuwa ce ?"wlh bazan yarda ba ai dan ni kaɗai akayi gidannan badan ni ba bazakayi ginin ba ta dinga masifa tana ƙarawa , zata buga masa dutsen guga ya fice da gudu ya koma ɗakinsa ya rufo ƙofa yana dana sanin gaya mata abinda ya faɗa tare da kiran innalilahi wai dama haka mata suke inko haka suke sun shiga uku dan akan kishi , yaci gaba da maganar yana mamaki , da gudu ta nufo ɗakinsa tana kururuwa ta shiga bubuga ƙofar tana cewa "wlh ka buɗe ko in ɓalla ƙofar yau kaima sai kayi kwanan baƙinciki kamar yadda ka sani nayi taci gaba da ihu ,
Shidai yana zaune a takure takaici ya ishesa .

Washe gari da asbha Khamis ya tashi Aisha yin sallah salai tayi ta sauko daga gadon ta shiga toilet tayi alwalah ta fito shi lokacin ya wuce masallaci , bayan tayi sallah ne ta ninke sallahyar ta cire kayanta ta shiga wanka , tana fitowa ta shafe jikinta da mayuka masu ƙamshi kana ta shafa powder simple make up tayi kana tazo sauya kaya tayi zigidir tana duba kaya sai ga Khamis nan ya shigo ,a kunyace ta shige cikin drower kamar biri ta rufo kofar ta kulle ta ciki kasancewae drower tanada zurfi sosai , murmishi yayi mai sauti kana yace "my Esha kenan Allah ya barmu tare "ya juya ya fice, yana fita ta fito tana zare ido kana tace "oh na shiga uku nikam bazan iya haɗa ido da yaya ba wlh kalan yace "iskanci ne ya sani yin hakan taci gaba da surutunta tana dariya , doguwar riga ta ciro ja mai adon farin duwatsu masu ƙyali tayi rolling ɗankwalin a kanta kana ta buɗe akwatin sarƙa da ɗan kunne ta zaɓi farar sarƙa itama mai kwaliyar duwatsu farare ta sanya ta zauna tana tsoron fita ,turare ta ɗauko ta feshe ko ina na jikinta dashi nan da nan ta ɗau ƙamshi mai rikitarwa, tsayuwa tayi jikin mudubi ta kalli kanta ta juya tana farr da ido sai ta tuno faɗan da Ammi tayi mata na sauya tafiya , yanga ta fara tana yarfe hannu sai ga Khamis nan ya shigo bata sani ba , harɗe hannayensa yayi ya tsaya daga bakin ƙofa yanata kallonta , ta taho da gudu idonta a rufe ya caraf rungumeta yana murmishi ,zaro ido tayi batayi magana ba amma taji kunya shima bai yi maganar ba yana ta murmishi ya waye wanan ta fara faɗa kuma tasan ko waye ƙin yin yin magana yayi a karo na biyu yana tafiya da ita a hankali a hankali dan Allah koma waye ya sakeni bada niyya nayi ba pls ta haɗe hannayenta idonta a rufe sai da suka kai kan bed ya kwantar da ita tare da cewa "mijinki ne .

END END

ALHAMDULILH ALLAH NA GODE MAKA DAKA BANI IKON KAMMALA BOOK 2

Kura kuran dake ciki Allaj ka yafe mana Allah ka karemu daga dukkan sharri Allah ka tabbatar mana da alkairi a rayuwar mu alhmdulilh
Mu haɗu a book 3 08141799224.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment