Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

drivern yace " Khamis ya kashe waya.
Niƙi niƙi driver ya kwaso kaya ya fara shigowa dasu sai da yayi sahu huɗu sanan ya kammalah , tun daga nesa malam ya hango ana shiga da kaya gidan washe baki yayi kana a fili yace " kai masha Allah ga sabon aure ga abinci na warke wlh , yana isowa daf suka gaisa da drivern ya shige gida , yana shiga su Ammi na fitowa zasu tafi , da gudu Aisha taje tace " malam ina kwana a'a ƴar albarka ya gida ya ƙiriniya?" malam ya faɗa yana faɗaɗa fara'arsa....!

*MOM ISLAM*
[24/08, 6:33 pm] Mom Islam Ce 💃: 11 & 12

Bayan su Ammi sun gaisa da malam suka yiwa mama sallama , Khamis ya kira Aisha da gudu ta biyoshi kasancewar daya kirata waje yayi , Ammi dake zaune a gidan gaba ta jinjina kai tayi tana mamakin wanan soyayyar da Khamis ke nuna ma Aisha.
Yana tsaye ya harɗe hanunsa ɗaya kan ɗaya idanunsa a kanta , tana ƙarasowa ya lumshe ido kana yace " my Esha kizo mu tafi dan Allah ya marai raice fuska kamar mai shirin yin kuka , tuntsirewa da dariya Aisha tayi kana tace " a hayeee namiji da shagwaɓa zaro ido Khamis yayi yace " Ammi fa na jinki kiyi a hankali yanzu dai kizo mu tafi , maƙale kafaɗa Aisha tayi tace " inason zuwa gidan yaya gobe kuma anjima zani kasuwa , eh kasuwa fa kikace ?" wlh kar inji labari kina matar aure zakije kasuwa ? uhm ni fa ka dena cemin matar aure yarinya dani , innaje kasuwar ma innaga budurwa zanyi maka magana , janyo mata hannu yayi kana yace " aiko kinban kwana gobe na kawoki gidan yayan naki ya turata a mota shima ya shiga kana yace "wa driver muje karka tsaya , kafin Ammi tayi magana driver ya figi mota .
Faɗa ta kama yiwa Khamis akan mai yasa zai yi wa Aisha haka.
" Ammi kasuwa fa zataje tana matar aure , murmishi Ammi tayi tace " bafa sharaɗin da za'a gindaya wa babbar mace zakayi mata ba dole tana buƙatar wasu abubuwan na yara.
Fuskar Khamis a haɗe ya kalli Aisha yaga kuka take wiwi wanan hawayen dake zuba daga fuskarta kamar ana zuba masa wuta yake ji amma ya riga ya cika aiki dan har sun hau titi ya rungumeta , tana shash sheƙar kuka bacci mai nauyi yai awon gaba da ita , suna isa gida driver na parking ya fito ya buɗewa Ammi mota kana ya buɗewa Khamis dake back side shida Aisha , fitowa Ammi tayi bata tsaya kallonsu ba tayi part ɗinta , ɗaukar Aisha yayi shima ya nufi nasu part ɗin da ita , kwantar da ita yayi a bed ɗinsa kana ya shiga toilet ya watsa ruwa tare da ɗauro alwalar azhar , yana fitowa ya sanya farar jallabiya ya nufi masallaci , bayan an idar da sallah ne ya dawo gida yana dawowa yai part ɗin Ammi , a zaune ya sameta tana waya zama yayi yana jiranta gama yayi mata magana , tana ajiye wayar yace " my Ammi zani office yanzu , duba agogo Ammi tayi ƙarfe biyu da minti biyar ,tace " kayi haƙuri gobe kaje man ?" no Ammi akwai wasu fils da ban samu na cike ba shiyasa , Allah ya tsare Ammi tayi masa ya fice tare da cewa " Amen.
Part ɗinsu ya koma ya sauya kaya kana ya daɗa luluɓe Aisha ya kira baba mai aiki yace " ki kularmin da ita dan Allah kisamo min ƴar aiki kunyi kaɗan gaskiya , washe baki baba tayi tace " insha Allah ranka shi daɗe dama gobe zani ƙauyenmu akwai ƴar gurina tana ta so ta biyoni ina hanata kaga sai tazo ko ? ok Khamis yace " yana sanya farin gilashi a idanunsa ya fice .
Drivern sa na ganinsa ya fito da motarsa kana ya buɗe masa ya shiga yana shiga suka ɗauki hanyar zuwa ma'aikatar tasu ,
Sunyi tafiya mai nisa kana suka iso ana parking ya fito yai hanyar office yana shirin shiga ma'aikata suka taho suna gaishe sa ,amsawa yayi cikin ƙasaita suke tambayarsa ko lafiya bai zo da wuri ba ?" lafiya Khamis yace " naje anguwa ne shiyasa , ya shige office , zama yai a ƙayatacciyar kujerar dake juyi ya fara juyi yana nazarin wani abubuwa , nocking aka fara sai da yai jimm kana yace " yes , budurwar jiya ce dai wato muhibbat tana sanye da wani material yellow mai ratsn flower fari yana da adon duwatsu masu kyau , zama tayi batare da jiran izini ba ta dubi Khamis tace " barka da war hakan ranka shi daɗe dafatan dai lafiya muka jika shiru yau ?" lafiya lau sai alkairi Khamis yace" cikin ƙosawa da tabar office ɗin dan yasan abinda ya kawota , am nace ya maganar mu ta jiya ka amince ?" cewar Muhibbat wani kallon banza yayi mata kana yace " ke ki shiga hankalinki banison takura kikayi wasa zaki bar ma'aikatar nan gaba dayanta , zaro ido Muhibbat tayi kana tace " Allah ne ya haɗa jininmu ka yarda dani .
cikin faɗa faɗa Khamis yace " saboda rashin hankali da tunani baki sanni ba bakisan koni waye ba yaya halina yake mai kyau ne ko marar kyau amma kina iƙirarin in aureki aure abin wasa ne ?" to bari kiji Allah da kansa yace " ku zaɓawa ƴaƴanku iyaye na gari haka itama mace ta zaɓarwa ƴaƴanta uba na gari duk mazan da suke kai kawo bakiga wanda yayi miki ba sai ni ?" to wlh kina cikin matsala ya buga takardun daya ɗauka ya fice ya barta cikin zafin rai , ko kiran driver baiyi ba ya figi motar a ɗari yabar ma'aikatar , kuka ta fashe dashi mai tsuma zuciyar mai karatu .
Miƙewa tayi ta fice ta nemi guri ta zauna tana ci gaba da kuka har yamma tayi idanunta duk sun kumbura tsabar hawaye , ƙarfe shida nayi ta nufi bakin titi ta hau a dai daita ta nufi gida .
Yana komawa gida direct part ɗinsu ya shiga samun Aisha yayi tayi wanka tana cin soyayyen dankali , ganinta cikin kwanciyar hankali ba ƙaramin daɗi yayi masa ba hakan yasa ya sa hannu a aljihunsa ya ciro kuɗi ƙirga dubu biyar yayi yaba baba mai aiki dake zaune kusa da Aisha tana yi mata hira , gashi baba " Khamis ya faɗa yana miƙa mata .
Hannunta na rawa ta karɓa tana murna ta fara sanya masa albarka , sai da Aisha ta cinye tsaf sanan tazo gurinsa ta zauna kusa dashi tace " shine kayimin wayo ko ? murmishi kawai yayi sbda a halin yanzu bayason magana komi ƙanƙantar ta , kama kunnensa Aisha tayi tace " nifa ka kulani kokuma inta kuka sai ka maidani gidanmu , shiru yaƙi kulata , ihu ta zunduma tana shure shure a tsorace ya tashi tsaye dan wata maganar da take yi ba jinta yake ba kasancewar yayi nisa a kogin tunani , cak ya ɗagata sama yana juyi da ita tana dariya ga kuma hawaye , shima dariyar ya keyi amma ta dole dan karta dameshi da kukanta mai rikita mutum .
Na gaji ka saukeni , Aisha tace "tana dariya , sauketa yayi ya koma ya zauna , haka ya kwana cike da tunani iri iri.
Washe gari ji yayi gurin aikin ya fice masa a kai kwata kwata baya ma sha'awar zuwa , bayan ya fito daga sallah ya shiga sashen su , samun Aisha yayi har tayi wanka ɗakin ya gaure da ƙamshin turare iri iri ga wata kwalbar a ƙasa ta fashe , innalilahi wa ina illaihir raji'un Khamis yace " tare da cewa " Aisha mezan gani haka ta 'adi kikayi min ne ? jikinta a sanyaye ta rakuɓe gefen gado tana bashi haƙuri , kinsan tsadar wanan turaren kuwa Esha kika fasa min ?"cikin tsoro ta hau girgiza kai alamar a'a to dubu ɗari ne ya nuna kwalbar data fashe , kuka Aisha ta fara tana cewa " dan Allah karka dukeni wlh bazan ƙaraba bada sanina nayi ba nazo sawa a jikina ne kawai kwalbar ta faɗi , goshinsa ya buga kana ya nemi guri a gefen gadon ya zauna yana ƙarewa Aisha kallo , kwaliyar dai irinta jiya ita ta kuma yi yau kuma janbaki tasa mai ruwan toka inka ganta kamar wacce ta shafa farar ƙasa a baki , ga ɗige ɗige da tayi kamar yammatan ƙauye , bayajin yin dariyar yau ga fasa turare ko kwana uku ba'ayi ba da siyoshi ga Muhibbat da take neman juya masa kwanya.
babu abinda zanyi miki amma ki kiyaye kinji ?" to tace " kanta a sunkuye , a cikin akwatunan nan ai akwai turaruka ki duba zaki gani sai ki dinga shafawa , to Aisha tace " jiki a sanyaye ta ɗauka dukanta za'ayi sai sha biyu zan kaiki fa garama ki dena wani zumuɗi ,cuno baki Aisha tayi kana tace " ayya kyakkyawa in munje zakace ba kwana zanyi ba mu tafi yanzu .
No Khamis yace " yana girgiza mata kai daɓas ta zauna kusa dashi ta riƙe masa hannu zatayi magana ta kalli fuskarsa , a turɓune take kamar bai tama dariya ba , na fasa zuwa yanzu mu bari sai anjiman Aisha ta faɗa tana kuma kallon fuskarsa ko zaiyi dariya , duk da haka taga baiyi ba , juya baya tayi ta fara kuka , jin kukanta yasa Khamis ankara da ita kai Khamis yace " tare da ɗora hannu a ka yana mai jin zuciyarsa a cunkushe, wai Aisha ya kikeso inyi da rayuwata ne ko so kike nima kiga ina kukan? da sauri ta girgiza kai ta share hawayenta ta juyo tana masa dariya , shima dariyar ya mayar mata kana ya rungumota ya kwanta tare da ita yace " shafa min bayana my Esha yau babu musu tana gudun kar tayi magana yaƙi kulata , haka ta dinga shafa masa baya har ta gaji bata ce masa ta gaji ba sai sharar hawaye takeyi , jin ɗumin saukar hawaye ne yasa shi ɗagowa yace " mai kuma ya sake faruwa my Esha ?" na gaji Aisha tace " tare da rufe bakinta , am sorry nama mance kiyi haƙuri ankalina yayi gaba yau ko gaishe da Ammi banje ba barinje in dawo ko ?" cikin marai raicewa tace " zani no karki biyoni ki zauna da baba zanyi mata magana ta shigo ki gaya mata abinda kikeso a dafa miki inyaso sai tayi miki , dariya Aisha tasa tace " wayo daɗi yau zan wahalar da baba kuma ko tayata bazanyi ba bari ta shigo ta kuma ƙyal ƙyalewa da dariya , shikam yau duk abinda Aisha take ya kasa dariya sbda halin dayasa kansa ficewa yayi yana fita zau shiga palo yaga baba maj Aiki tana goge kujeru , sannu tayi masa tana yawa Khamis yace " kana ya dubeta yace " baba dan Allah in bada wuri zaki tafi ba kije gurin Aisha ta gaya miki abinda takeso a dafa mata , to ranka shi daɗe sai zuwa azahar zan tafi , to Khamis yace " ya nufi bedroom ɗin Ammi dan bata palo, sallama yayi Ammi tace " ya shigo guri ya samu ya zauna kana kuma ya sauko ya durƙusa ya gaida Ammi bayan sun gaisa ne Ammi tace " yau lafiya kuwa ? son naga yanayin ka duk ya sauya ?" shafa sumar kansa yayi kana yace " lafiya Ammi me kika gani ?" ina tambayarka kana tambayata son ?" sunkuyar da kai yayi yasan inhar matsala ta samesa in bai faɗa mata ba babu kwanciyar hankali ko kaɗan , son akwai abinda ke damunka baka saba ɓoyemin damuwarka ba kana kuma baka saba ƙin baiyana min damuwarka cikin gaggawa ba ina jinka maza gaya min meke faruwa da kai baza kaje office bane yau ?" eh Ammi Khamis ya bata amsa , meyasa ?" babu komai ya kuma bata amsa .
Akwai komai mana Ammi tace " tare da gyara zama , ka gayamin inba so kake raina ya ɓaci ba , uhm am Ammmmi ...katse shi Ammi tayi kana tace " ka fito kayimin magana sak banason jan layi ina sauraronka , gyaran murya Khamis yayi kana yace " ranar sana fara zuwa office wata budurwa ta shigomin office ta gabatar min da sunanta da rayuwar data fuskanta a gidansu ta ƙara da cewa " zan aureta ?" gaskiya bisa ga yanayinta koda banyi aure ba bazan aureta ba gaskiya bata yimin ba ya kwashe labarin duk inda sukayi yaba Ammi....!
[24/08, 6:34 pm] Mom Islam Ce 💃: 13 & 14

Nisawa Ammi tayi kana tace " a kanta ne zaka dena zuwa aiki ina ka zamo jarumi man babana karka zamo rago mace ɗaya tana neman hargitsama rayuwa .
Dafe kansa yayi kana ya miƙe yace " Ammi kaina ciwo zani in kwanta kuma anjima zan kai Aisha gidan su yayanta , badan Ammi taso rashin zuwansa office ba babh inda zatayi hakan yasa tayi masa fatan samun lpy mai ɗorewa ya fice , yana isa sashen su ya sami Aisha ta baje a kan kafet tana ta yagar naman kaza tana zaro ido , dariya ma ta basa ya ƙyalƙyale yana kallonta , murguɗa masa baki tayi tare da jefo masa harara , ni kike harara yau kuma ?" Khamis ya tambayeta yana ɓata rai kayi haƙuri bazan sake ba Aisha tace " tana gudun kar a ɗauke plet ɗin naman kazar , shigewa bedroom ɗinsa yayi ya barta a gurin ya kwanta , bacci yaƙi ɗaukarsa kasancewar yasa damuwa a ransa tashi yayi ya ɗauki key ɗin sabuwar motarsa da in ba shiba babu mai hawanta ya fito palo ya cewa " Aisha tazo su tafi ya fice , leda ta samu baƙa ta ƙulle ragowar kazar a ciki romon kuma ta shanye taje kitchen ta ɗibo ƙwai guda biyu suma ta zuba a ledar da magi ta ƙulle tasa hijab har ƙasa ta fito , kije ki yiwa Ammi sallama Khamis yace " mata to kawai Aisha tace " taje part ɗin cikin sa'a ta tarar da Ammi a palo cewa " tayi mama mun tafi , Ammi dake ƙarewa kwalliyarta kallo tace " haka zaki tafi da wanan kwalliyar maza zonon in gyar miki , da gudu Aisha ta ruga ta dawo gurin Khamis tace " mama tace " Allah ya tsare amin Khamis yace " tare da cewa " shiga mu tafi , gaba ta shiga ba suka bar gidan , yana hawa titi yace " da sharaɗi tun a nan zan fara faɗa miki kar muje kice ba haka ba tare zamu dawo ba kwana zakiyi ba , eh Aisha tace " ita dai burinta tana jaririya da kuma Ummi , suna isowa zata fice da gudu ya rungumota , ya ɗorata kan cinyarsa ya haɗe bakinsu guri ɗaya ya dara aika kisses yana lumshe ido ɗago kan da Aisha zatayi suka haɗa ido da Ummi , a zabure Aisha ta zamo tace " kyakkyawa na shiga uku Ummi zata iya gayawa malam muna iskanci kuma wlh ta ganmu yana shirin kamo mata hannu ya kamo ledar dake hanunta , meye wanan a ciki ?" Khamis ya jefo mata tambaya , babu komai , tana jujuya hannu aka fasa ƙwai anan ne Khamis ya gane ko me ta sa a ledar dan harda ƙashi yaji murmushi yayi kana yace " ƙuruci kenan yace " zo ki karɓa ki kaiwa Antyn naku , dubu biyu ya bata kana yace " zani gurin abokina anjima zanzo mu tafi tana zumuɗi tace" to tana ganin Ummi ta ɓata rai tace " to munafuka me kikaga munayi ?" zaro ido Ummi tayi tace " ke Aisha kice kinzama ƴar iska kuma sai na faɗawa yaya wlh bari ya shigo , matsalar ƙwallah Aisha ta fara tana haɗa Ummi da Allah akan karta gayawa yaya tayi haƙuri , nafa ganku keda wanan wanda ya kawoki , ke dallah can so kike suji to wlh nazo da abin daɗi bazakici ba kuma tunda naje kaza nake ci da dankalin turawa ke har girki ake yimin Aisha ta faɗa tana juya kai irinna yara , kee Allah Ummi ta faɗa tana tsalle , aiko zan biki wlh dariya Aisha tasa kana tace " kwaɗayayya kawai ,Ummi tace " kekuma ƴar iska kawai bin juna suka kamayi da gudu sukaci karo da yaya Zakari yana tahowa a ƙafa, durƙusawa Aisha tayi har ƙasa tace " ina yini yaya .
Lafiya lau yayan yace " yana ƙare mata kallo ,
Yaushe ki kazo ya tambayeta yana daɗa kallonta , ɗazu banama shiga gida ba Aisha tace " tana sunkuyar da kai to ku muje ,yayan ya faɗa yana kallon Ummi .
Da sallama suka shiga kaka suka samu zaune tana gyara tsintsiya , gaisheta Aisha tayi kana ta wuce ɗakin Anty Fiddausi a zaune ta sameta tana bawa jaririya nono suna kiranta da Afnan , a'a kaga amare anty Fiddausi tace " tana washe baki , sunkuyar da kai Aisha tayi tana dariya , miƙa mata yarinyar anty Fiddausi tayi tace " kinganta tana kama dake ko , dariya Aisha ta kumayi tace " ai batada dogon hanci suka sa dariya , fitowa Aisha tayi da yarinyar a hanunta suka shiga ɗakin da da yake mazaunin nata zama tayi ta bugi cinyar Ummi tace " wlh ki biyoni zaki dinga cin daɗi sosai har sawa za'ayi ayi miki girki , a gidan , cikin zumuɗi Ummi tace "ko ta bayan mota nabi ku ,dariya Aisha tasa tana kunce ɗaurin zani ta fito da baƙar ledar da ta ɗaure nama da ƙwai , ta mance ta rugur guje ƙwan duk ruwan ya ɓata mata jiki shirin kuka ta fara Ummi ta karɓi ledar taga nama ga kuma ƙwai shima ya haɗe sai ƙarni , kinsan me za'ayi Aisha zomuje kicin mu soya haɗe da naman , uhm wlh tsoron anty Fiddausi nakeyi cewar Aisha , dallah yaya na nan bazai fito yanzu ba zo muje , cikin sauri suka fito kaka na cewa ina zaku kuka haɗa kai kamar ƴan matan amarya , ganin sun nufi kitchen tace " me kuma zakuyi , duk cikinsu babu wanda ya kulata bare su nuna sunji abinda take faɗa , har suka gama suyarsu suka cika mangyaɗa da maggi anty Fiddausi bata sani ba kaka ce data jiyo ƙamshi take ta faman yi musu magana sunƙi kulata , fitowa sukayi da plet a hanun Ummi suka nufi ɗakinsu , jin maggi yayi yawa yasa Aisha cewa " bazanci ba nasan inna koma ma za'a soyamin ta cire hanunta , giwa ta daɗi Ummi sai murna ya daɗu Ummi tace " tana dariya kana ta kuma cewa " oh su Aisha ankoma masu kuɗi kina hutawa , kuɗin da Khamis ya bata taba anty Fiddausi ta ciro tace " kinga kuɗinnan me zamuyi dashi cewa " fa yayi inba anty Fiddausi , tashi muje kasuwa wlh mu kashe wa idonmu ƙwarƙwata , Ummi ta faɗa tana tafawa da Aisha aiko kin kawo shawara cewar Aisha .
Kayan kwaliyan da yaya Zakari ya siyawa Ummi suka ɗauko aka fara kwaliya ta hauka , kaka na ganinsu tace " tunda waccan yarinyar tazo mai kamada fulawa ido kamar gurjiya nake yi miki magana Ummi kinƙi kulani ko?" sai mun dawo kaka Ummu tace " tana ruƙo hanun Aisha , suna fita sukaci karo da motar Khamis Ummi bata san ko waye a motar ba dan ta mance motar da aka kawo Aisha , Aisha na ganinsa ta juya da gudu tayi gidan yaya ɗakin anty Fiddausi ta faɗa abinda ta gani ne yasata sunkuyar da kai anty Fiddausi akan cinyar yaya sun haɗe lips ɗinsu guri ɗaya. oh Aisha ta faɗa ashe suma sunayi to ba iskanci bane ?" duk a cikin zuciyarta take wanan zancen .maganar da taji ne yasa ta ankara da taji ana cewa " bazaki fita ba marar kunya , muryar yaya ta tsinkayo yana yi mata faɗa , kafin ta fice tace " ga Khamis nan yazo gaishe ku zai shigo ta fice , ɗakinsu na da ta koma tasa hannu a baki tana tambayar kanta to wai shin ba iskanci bane ?" ai kyakkyawa ma yana yimin haka aiko zan tambayi mama duk ranar dana koma , zama tayi sai ga Ummi nan ta shigo , ke wlh mijinki ne yazo kuma yace " kizo ya aikeni yace " incewa Anty Fiddausi zai shigo kuma tayimin faɗa jiya tace " in yaya ya shigo kar in sake in shigo mata ɗaki cewar Ummi .
Ke wlh karki sake ki shiga iiiskanci sukeyi kina shiga zai ɗura miki zagi dan haka karkishiga muje wajen gurin kyakkyawa , dakatar da ita Ummi tayi kana tace " zaku tafi dani ɗin? ke yaya ya dawo wlh kinsan basa shiri da kyakkyawa , to bazaku tafi dani ɗin ba kinenan Ummi tai rau rau da ido tana shirin yin kuka zomuje ko zamu sami kuɗi.....!

Mom Islam
[25/08, 4:34 pm] Mom Islam Ce 💃: 15 & 16

Suka fice , fitowar yaya Zakari ne yasa su dai daita nutsuwarsu ya miƙawa Khamis daya fito yanzu hannu suka gaisa , bayan sun gaisa yaya ya tambayesa ya al'amura yace lpy ya wuce , Khamis ne ya dubi Aisha yace " wanan ce Ummi ?" eh Aisha tace " tana washe baki , to ku rakani in gaida mutanen gidan , Khamis ya faɗa yana kamo hanun Aisha , a tare suka shiga ya da sallama ya durƙusa ya gaishe da kaka dake ta fama da haɗa tsintsiya , da gudu Ummi tayi ɗakin anty Fiddausi tace " ka shigo , babu musu ya shiga ya zauna kan kujera suka gaisa ta miƙa masa yarinya , miƙewa yai yace " zai tafi ya ajiye musu dubu goma yace" gashi a siyawa yarinya riga ya fita , ashe an bada kuɗi a kunenen kaka , tana ɗingishi ta taso kasancewar ta gashi da zama tace " a raba a bani nawa dama ina sha'awar cin kifi yau sai in shiga kasuwa , farr da ido anty Fiddausi tayi tare da kai kuɗin uwar ɗaki ta ɓoye su tana zaro ido tace " ai jaririya yaba ba kowa ba dan haka babu wanda zanba kuɗinnan a to .
Kambun uba wlh baki isa ba dole a raba ke Ummi nawa ya bayar ?" dubu goma Ummi tace " tsalle kaka ta buga tace " kan uba taɓɓ amma wlh baki isaba kai kinyi kaɗan bari zakari ya shigo ,Ummi ta ƙyalƙyale da dariya tace " kaka anji kuɗi an ruɗe , ke ƴar nan dole in ruɗe kuma tilas taban kaso na .
Ummi na gurin masu rabon kuɗi har Khamis ya tafi da Aisha bata sani ba tana fitowa taga wayam babu su babu alamar su ihu ta fasa tare rushe wa da kuka , yaya Zakari da yake tahowa yana waya ya ɗaga mata hannu alamar meke faruwa?" bata bashi amsa ba ta zauna tana ta shure shure , ɗagota yayi ya rungumeta ya kaita gida suna shiga yaji ana drama tsayawa yayi daga nesa da ɗakin anty Fiddausi yana fahimtar abinda ke wakana , murmishi yayi ya sauke Ummi yace " jeki kwanta .
Ɗakin anty Fiddausi ya shiga kaka ya samu a zaune tayi tagumi kamar wace aka yiwa mutuwa , ƙunshe dariyar data taho masa yayi yace " kaka lafiya kuwa naganki haka?" lafiya ɗannan kaka tace " tana nuna anty Fiddausi tace " kaganta nan kuɗi wanan yaron daya shigo ɗazu ya bamu har dubu goma shine ta ɓoye wlh kazo ka karɓar min haƙƙi na , dariyar da yake ɓoyewa ce ta kuɓuce masa sai da yayi mai isarsa kana ya dake ya dubi anty Fiddausi yace

Please Login or Register in order to submit comment