Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

watan Aisha biyu a gidan taji sauƙi kamar ba ita ba ,hakan ya yiwa Khamis daɗi .
Ƙarfe tara na safiya mai lesson yazo bayan su Ammi sun gaisa dashi ya buƙaci Aisha da tazo su fara , zama Khamis yayi a ranshi ya aiyana duk ranar da malamin nan yazo nima zama zanyi karya dinga kallemin Esha wlh badan ƙiuya ba ai da nina dinga koya mata , tamayar da aka fara yiwa Aisha ne ta katse masa tunani.
"kin taɓa zuwa makaranta kuwa?" eh Aisha tace " ina aji huɗu muka dena zuwa " wasu ƴan tambayoyi yayi mata game da karatu , amsa ta shiga bashi hakanne ya tabbatar masa da yarinyar tanada brain sosai , ta burge Khamis hakan ya ƙara rura wutar soyayyar ta a zuciyarsa , Ammi da ta shigo yanzu tace " oh kai kuma zama kayi ?" murmishi Khamis yayi kana yace " my Ammi nima ina tuni ne .
malamin ne ya dubi Ammi yace " wanan bazata bada wahala ba sbda tanada saurin fahimtar abu , masha Allah Ammi tace " to "kamar zuwa yaushe kake ganin zata fara zuwa School ?"
Kamar nan da two month haka , ok Ammi tace " kana ta shige ta barsu a gurin .
Zuwa ƙarfe sha ɗaya sun kammala yayi musu sallama ya tafi ,
Tsalle Aisha ta buga tace " wayaga Aisha a boko wlh da nafi kowa jin daɗi bakinta yaƙi rufuwa sai fara'a take " ganinta cikin farinciki yasa Khamis shima jin farinciki a zuciyarsa tana ta tsalle tana rawa , wayarsa ya ɗaga ya hau yi mata video yana murmishi yana ganin zata ankara ya sauke wayar .

mayafi kaka ta ɗauka tace "wa anty Fiddausi zani anguwa dan Allah ki kulamin da tsintsiyata , anty Fiddausi dake tsaye bakin ƙofa ta riƙe ƙugu tace " wlh koda ruwa yazo yayi musu duka ta koma ɗaki , riƙe baki kaka tayi tace " yarinyar nan kwai ƴar iska ko bata sanni ba ta dinga gayamin magana haka kamar tanayi da marar galinhu kaka ta tattara tsintsiyarta a buhu ta wurga ɗakin su Ummi dake kwaliya tayi wanka , Ummi na cewa "meye a ciki kaka tai kunen shegu da ita tace "nidai naje kasuwa , babu wanda ya kulata daga anty Fiddausin har Ummi haka ta tafi tana masifa a hanya .
Tana cikin tafiya taga mai tiren tsire , mai tsiren na ganinta yace "baba a kawo ne ?" a'...!

Ƴan VIP grp kuyi haƙuri dan Allah nayi baƙi ne bansami damar typing ba 👏
[27/08, 1:32 pm] Mom Islam Ce 💃: 21 & 22

Kaka dake gyara mayafinta data ɗora a kanta tace "ba anan zan siya ba sai naje kasuwa ƙila nasu zai fi araha , jin haka yasa mai tsire saukewa ya buɗe shi yawun kaka ne ya tsinke ba shiri tace " samin na ɗari biyu amma fa canji ne , to mai tsiren yace "kana ya zuge tsinke biyu ya baɗe shi da yaji wanda yaji ƙuli , gyara zama kaka tayi ta zauna a kan takalminta kana tace " karfa kayimin tsada dan zan baka abinka , mai tsire na yar yaɗa mangyaɗa yace " haba kaka ai ni ɗanki ne .
Kaka da tsire yayi mata daɗi har mai tsire ya tafi da canji bata karɓa ba sau da ta gama cin tsire ta duƙunƙune takarda sannan ta tuna da ai bata karɓi canji ba , kuka tasa tana salati haka ta miƙe tana tafiya tana jera masa Allah ya isa ace mutun kamar na Allah ya rasa wacce zai cuta sai tsohuwa ?" nikam na shiga uku waccan yarinyar ƴar duniya ta cuceni yanzu kuma gashi wanan ma cucin ya cuceni Allah ka bimin kadi na taci gaba da magana tana mita , har tayi nisa bata sani ba har sai da taji ta gaji ta tsare mai mashin tace " ya kaita bakin dogo nawa ne ?" kaka ta tambayesa ki barshi Allah ya kaimu lafiya baba "mai mashin yace " yana mai karkatawa kaka ta hau , cikin ikon Allah sai gasu sun iso godiya tayi masa tare da sa albarka ta shiga cikin kasuwar, wani dakali ta samu ta zauna kana ta fito da lalitarta ta fito da kuɗin ciki duka tana ƙirgawa , dubu uku da ɗari biyar ne kasancewar taba mai tsire ɗari biyar kuma tanada dubu ɗaya dama , tana cikin haɗa kan kuɗin taga an biyu wani da gudu ana cewa " ɓarawo ɓarawo ba shiri ta tattaro kuɗin a guje ta faɗa gidan da ta gani a gefen ta , wata mata dake shirin fitowa daga ɗakin tana ganin kaka ta dannawa ƙofa saƙata dama ita ɗayace a gdan gashi faɗa ya ɓarke a ƙofar gida , haka kaka ta nemi guri ta zauna tare da miƙe ƙafa , takai minti talatin a gidan sai da taji an dena faɗan sannan ta fita a gidan , tana fitowa ta riƙe baki tace " daga shiga gidanki sai ki gudu sai kace kinga mutuwarki kaji min shegiyar mata kaka ta faɗa tana daɗa ɗaure lalittar ta , mai tallan rama da zogale ta gani yana tafiya ƙwala masa kira tayi kana tace " bani na hamsin amma ɗari biyar ce "to akwai canji yaron yace "yana duba aljihunsa , ɗari huɗu da hamsin ya miƙa mata ita kuma ta miƙa masa ɗari biyar , kashi biyu ya bata kana ya barbaɗa mata ƙuli ya sanya mata a leda .
asi kilishi asi kilishi kaka taji ana cewa "kai mai kilishi kawo dama tunda na shigo kai nake nema "to mai kilishin yace " tare da ajiye kujerar hanunsa ya ɗora tirai a kai .
"na nawa za'a baki?"
Mai kilishin ya tambaya yana gyarawa yawwa bani na ɗari biyar kasa min a babbar leda saboda har gida zani dashi , to yace " mata yana sawa ya miƙa mata ya tafi kuma zama tayi taci rabi ta ƙulle rabi bata si komai ba sai wani bugujejen sikel ta tari mai mashin ta dawo gida .
Tana dawowa Ummi dake share tsakar gida tace " oyoyo Kaka kawo ledar , maƙale hannu kaka tayi kana tace " da zan tafi akwai wanda ya bani sautu dan haka a barni in huta ,ta shige ɗakin Ummi kasancewar anan take kwana wuni ne kawai take zama a waje , tana zama ta buɗe takardar nama ta fara ci tana suɗe hannu , faɗowar Ummi ɗakin ba tare da sallama ba yasa kaka ɗura mata zagi tana mata faɗa , zama Ummi tayi tana jira itama ace ga nata amma kaka ko kallonta batayi ba taci gaba da ci tana murguɗa baki ,duk da ran Ummi ya ɓaci hakan bai hanata dariya ba .
Ummi ce tace " anty wlh kaka ta siyo tsire, da ƙarfi take maganar,
To shikuma aka kwaso Anty Fiddausi dake fitowa tace " muma ɗazu muka yanka kaza muka soyeta , kitchen anty Fiddausi ta shiga ta ɗauko bokitin da ta juye naman kana ta shigo ɗakin da kaka take ta nuna mata ,
Kaka dake naɗe takarda tana hamdala ta kuma ruɗewa tana cewa " to in dan wanda naci ne na hamsin fa naci zaki tada hankali , anty Fiddausi dake dariya tace " ƙwalele .

Washe gari haka Ammi ta kuma matsawa Khamis akan yaje gurin aiki ranshi a ɓace ya tafi ko sallama bai yi mata ba hakan bai yiwa Ammi daɗi ba yaƙi fahimtar ta ko kaɗan amma tasha alwashin gobe insha Allahu bazata ce masa yaje ba inyaje dan kansa in kuma yaƙi to itama ta ƙyaleshi , yana parking bai kula masu gaishesa ba ya shige office zama yayi idanunsa sun kaɗa sunyi ja tsabar damuwa , har ya kai ƙarfe biyu Muhibbat bata shigo ba cikin zuciyarsa yace " lpy to ?" kawar da zancen yayi ya janyo takardun dake buƙatar dubawa .
Zuwa yamma ƙarfe biyar ya tattara komai ya ajiye ya haye mota ya dawo gida yana shigowa yaga Aisha zaune tana wasa da furannin gidan ta bar baza z tsakar gurin , yana parking ya fito yaje gurinta my Esha maiyasa kike haka ne ?" Khamis ya tambayeta ransa a ɓace " mai gadi ne yace " wlh oga babu inda bamuyi da ita ba amma taƙi denawa daga ƙarshe cewa " tayi inhar muka sake magana zata fasa mana kai tana nunomu da duwatsu , dariya ce taso kufcewa Khamis bai yita ba ya tare ta , riƙe da hanunta suka shiga part ɗin Ammi ' Ammj na ganinsu tace " dama yanzu zan fita nemanta a ina ka ganta ?" a gurin flawoyi na ganta tana ta 'adi oh ɗiyata "kinason a fara dukanki ne ?" girgiza kai Aisha tayi ta daka tsalle ta haye kan kujera tana wasa , ƙarfe shida da arba'in Ammi ta kammala girki ta jere a dining tace " wa Aisha taje tayi sallah , sai gobe Aisha tace " tana cigaba da tsalle , waro ido Ammi tayi tace "naga takaina nikam ace yarinya bata son yin sallah bari in haɗaki da son ya zaneki , da gudu ta duro tare da shiga toilet ɗin da yake a mazaunin na mutane yake nesa da palon amma a palon yake , alwalah ta tayi ta fito sa gudu ta bubuga sallah tace "fatiya da ƙarfi Ammi dake ɗakinta tana sallah sai da ta jiyota , batare da jiran kowa ba ta wuce dining ta ɗauki plet ta jiye rabin farfesun kifi ta fice da gudu ta nufi part ɗinsu, tana shiga taga Khamis yana waya yana dariya , a bayan kujerar daya zauna ta zauna tanayi tana tsotse ƙayar kifi bai san da ,zuwanta ba sai jin tauna yayi da sauri ya miƙe yana dube dube , hangota yayi kamar munafuka ta takure gefe ɗaya tana suɗe kwanon data cinye kifin , kyakkyawa inkaje gurin mama kace mata na ƙoshi tace " wa Khamis tare da yin hanyar bedroom tana shiga ta kwanta babu ko wanke hannu , abinka da yaro ko a jikinta sam bata san tayi wani abu ba, Khamis da ya bita da ido ya miƙe ya tafi palon Ammi samun Ammi yayi a dining tana zaune ta zuba tagumi ita fitinar Aisha ta fara damunta .
Khamis ne ya katse mata tunani ta hanyar cewa " Ammi lafiya na ganki haka ? lafiya son kaga yarinyar nan ta kwashe farfesun kifin da nayi kaga wanda ta bari Ammi ta buɗe foodflaks ɗin tana nuna masa kiyi haƙuri Ammi maganar da ta fito daga bakin Khamis kenan , bata kulasa ba ta zauna shiru tana daɗa zurfafa a tunani shima ya shiga damuwa ganin Ammi babu walwalah , a haka dai sukaci abincin sama sama ya yiwa Ammi sallama ya tafi part ɗinsu , samun Aisha yayi tayi ɗai ɗai a gado tana bacci ƙare mata kallo ya shiga yi tabbas kyakkyawa ce , yasan inda abinda ke ɓatawa Ammi rai bai wuce a ɗaukar mata abu ba'a tambayeta ba wanan abin yana yi mata ciwo , to shikam ya zaiyi gurin gayawa Aisha karta sake ɓatawa Amminsa rai oho , kwanciya yayi tare da rungumeta yana shafa cikinta , ganin cikin nata kamar ba komai yasan tsoron faɗa yasa taƙi komawa cin abinci yaci gaba da shafa cikinta yana wani tunani, a wanan cikin my Esha zata ajiye min baby sai kuma yayi murmishi yana shafa fuskarta , ƙara matseta yayi a jikinsa suna jin nunfashin juna yayi musu adu'a bacci yai nasarar ɗaukarsa asuba ta gari.
Guɗa ake rangaɗawa a gidan su mama , mama bata ma san ranar ɗaurin aure ba bare tasan ranar da za'a kawo amarya malam bai gaya mata komai taga anzo anyi jere a ɗakin yaya zakari na da ciki da palo ne , ita dai mama nata ido ƴan kawo amarya sunyi habaici sun gama shugowar maman Ummi ne yasa mama jin sanyi a ranta , maman Ummi bata bar gidan ba har sai da taga ƴan kawo amaryar sun watse tana ta yiwa mama nasiha gami da ban haƙuri dakuma tunatar da ita adu'oi kana da jan girma banda sanya ido ta kawar da idonta , hankalin mama ya ɗan kwanta kasancewar nasihar maman Ummi ta shigeta.
Washe gari da safe ƙawayen amarya suka zo gurin malam wai ya basu abin karyawa , ce musu yayi suje gurin mama suce ta ɗora musu abinci inji shi , da yake su ƴan aika ne sukaje suka isar da saƙo, mamace tace " kuce masa inya bada a nashi zan ɗora amma ni banida shi , haka sukazo suka gayawa malam wanan abu ya yiwa malam ciwo ɗakinsa yasa key ya buɗe kasancewar key yake sawa ɗakin indomie ya ɗibo musu guda goma ƙawayen ma basu wuce huɗu ba aiko suka karɓa suna far'a sukace kuɗin cefane , babu musu malam jiki na rawa ya miƙa musu ɗari biyar suka fice ,
Kai tsaye ɗakin mama ya shiga babu sallama yace " wato shine kika tsinkani a gaban ƙawayen matata ko ? mtsw mama taja tsaki tace " kaga malam ban shiga harkarka ba dan haka ka fitarmin a ɗaki karka janyomin raini in tusa tana hura wuta ayi dai mu gani ,a zuciye malam ya fice ya fita waje ya zauna kowa yazo wucewa sai yace " na gaida ango malam na washe baki , bayan ƙawayen sun ƙammalah girkinsu sunci harda amarya sukayi wanka suka yi kwaliya kowacce ta ɗauko jakarta , amaryar ce tace " bari in kira malam, waya ta ɗaga ta danna number sa tace " ƙawayenta zasu tafi cikin ƙanƙanin lokaci ya shigo yana washe baki ya miƙawa kowa 1k cikin farinciki sukayi masa godiya kana suka tafi.

inbaku manta ba Aisha taje gurin wata dillaliya a maƙotansu siyo anko.

To yau tazo yiwa mama Allah ya sanya alkairi, tun daga ƙofa ta fara sallama malam dake zaune da plet ɗin cin cin a hanunsa ya fito yana amsawa kasancewar mama na bacci , ganin dillaliya yasa malam cewa " maza koma nayi amarya banason munafurci itama wacce kikazo gurinta zan taka mata birkin fita ko ina bazan lamunta ba sam haka dillaliya ta koma tana jinjina kai .
Hayaniyar malam ce ta tada mama daga bacci fitowa tayi tana cewa " malam kai da waye naji kamar muryar dillaliya ?" eh itace korarata nayi ko da akwai wani abinne ?" a' a mama tace " dan taga yana neman faɗa ne ita kuma tana taka tsan tsan ɗin kar yarinyar da aka kawo ta rainata....!
[27/08, 5:50 pm] Mom Islam Ce 💃: 23 &24

Shiru mama tayi ba tare da ta tanka masa ba ta koma ɗaki.
Dare na yi kaka tayi sallama a ɗakin su anty Fiddausi tsaki anty Fiddausi tayi kana tace " ko me tazo yi oho kwance take kan cinyar yaya Zakari tana shafa sajen fuskarsa duk cikinsu babu wanda Allah ya bashi ikon cewa "shigo duk suna shirin yin nisa bankaɗo labule kaka tayi ta fara sababi abinda ta gani ne ya sanya ta mutuwar tsaye ta juya babu magana sarai anty Fiddausi ta ganta ta kuma kamo yaya Zakari tana riƙo hanunsa , tunda kaka ta fara tafiya ba ita ta tsaya ba sai da ta kai ƙofar gida ta sami dakali ta sunkuyar da kanta ,kana ta rafka tagumi gami da cewa " na shiga uku nikam naga abinda ya isheni yanzu da wane ido zan kalli yarannan on ta dinga zuba surutai tana riƙe haɓa,
Jin anata kiraye kirayen sallahar magrib yasa ta komawa gidan ta yi sauri tayi alwalah ta shige ɗakinsu Ummi har tana bugewa da bango , tanajin gyaran muryar yaya Zakari taji gabanta ya bada dummm ,zan tattara in tafi gida kaka tace " tana share hawaye ,Ummi dake kwance tayi kamar mai bacci ta tuntsire da dariya kana tace "kaɗan ma kika gani ashar kaka ta mulmula mata wanda ya bawa Ummi damar yin shiru , haka kaka tayi sallah zuviyarta babu daɗi .
Anty Fiddausi ce ta ƙwalawa Ummi kira tace " tazo ta ɗauki yarinya , ficewa tayi tana cigaba da darawa.
bayan malamin da yake koyawa Aisha karatu yazo ya tafi ,Khamis yace " wa Ammi zai kai Aisha gurin wankin kai da kitson Allah ya tsare Ammi tayi masa suka fice kasancewar tayi wanka ,
Bai buƙaci driver ya kaisu ba hakan yasa da kansa yai driving suna tafiya yana tambayarta wane subject tafi so a karatu yafi yi mata daɗi , hausa Aisha tace " tana dariya suna zuwa gurin wankin kan ya bada kuɗi aka gyare mata kanta ana cewa " za'ayi kitso Aisha tasa kuka tana cewa " bataso haka aka bar kan , juya kan motar yayi yace " bari muje gidan maman abokina ki gaisheta murna Aisha ta fara sbda yau zasuje anguwa tanason yawo a rayuwarta, sunyi tafiya mai nisa kana suka zo wata ƴar kasuwa da ake siyarda kayan marmari , parking Khamis yayi ya fito ya siyi lemu da abarba da kankana da ayaba da apple aka sanyasu a leda aka kai masa both ya biya kuɗin suka ji gaba da tafiya ,
Cikin ikon Allah sai gasu a anguwar anguwa ce ta masu kuɗi komai a tsri yake gunin sha'awa , horn yayi aka buɗe get ɗin ya shige yana shiga yayi parking suka fito yace " ma ɗan aikin gidan ka kwaso kayan cikin both ɗinnan da gudu ya taho ya buɗe ya shiga dasu cikin gidan , riƙe hanun Aisha Khamis yayi suka shiga cikin gidan ilahirin mutanen gidan suna zaune a palo da mahaifiyar abokin nasa da matar abokin nasa kana da yaran maman abokin nasa akwai mai shekara goma sha biyar kana akwai mai shekara sha ɗaya wato sa'ar Aisha , lale Momma take yi musu kasancewar sunan da yaran auke kiranta kenan , shiga sukayi hanunta a na Khamis suka zauna guri ɗaya , durƙusawa yayi ya gaida Momma kana suka gaisa da matar abokin nasa yace "ina Bashir ?" ya tafi bakin titi yanzu zai dawo matar tashi ta faɗa tare da ƙwalawa ƴar aiki kira ta kawowa baƙi drinks , Momma ce take tambayarsa ya Ammi kana tace " abokinka ya bani labarin kayi aure ya matar taka ? lafiya lau yace " sai a lokacin Aisha ta durƙusa tace " ina wuni ta gaida matar abokin Khamis bayan sun amsa ta koma ta zauna , godiya Momma tayi masa na tsaraba kana ya miƙe yace " zasu tafi janyo hanun Aisha Momma tayi ta shiga da ita bedroom ta bata hijab har ƙasa na makkah da doguwar riga sabuwa da turare kana ta bata wani ƙaton turare tace " ta kaiwa Ammi godiya Aisha tayi suka fito , Momma ce tace " amma wanan ƙanwarka ce ko ?" naga kuna kama , eh Khamis yace " Aisha ta nuna masa hanunta godiya ya yiwa Momma kana suka wuce ,
Suna tafe tana bin waƙar da yasa wato jirgin so wanda Umar m Sharif yayi dariya ma ta bashi har wani kareraya take tana rawa, har suka isa gida yana dariya , da ana buɗe mota Aisha ta fice da gudu tayi part ɗin Ammi tare da cewa " albishirinki Ammi -Ammi na dariya tace " goro ƴata maiya faru "Ammi na washe baki ta tambayi Aisha kamo hanun Ammi Aisha tayi ta haɗa da ledar hanunta , shigowar Khamis ne yasa Ammi tambayarsa taga Aisha na farinciki maiya faru " dariya yasa yace " Ammi gidan Momma mukaje fa shine aka baku abu take ta murna ayya Ammi tace " shine baka faɗamin ba ?" ka sameta lafiya ?" eh Khamis yace " ai tace " in gaishe ki, ina amsawa Ammi tace " tare da zama ta buɗe ledar dake hanunta , kayan da ta gani ne ya sata buɗe baki tace " kai kai amma nayi farinciki irin turaren dana dinga nema a garinnan na kasa samu tunda nawa dana taho dashi daga saudiya ya kare nayi baƙinciki ksi naji daɗi dole in kira inyi mata godiya ,murmishi Khamis yayi yace " na Aisha ma na ciki , cigaba da duba kayan Ammi tayu tace " kai masha Allah Allah ya biyata da aljannah maza kai part ɗinku ta miƙawa Aisha da gudu tayi part ɗin nasu ta watsa kan gado ta fito ta dawo a mai makon ta wuce gurinsu Ammi sai ta nufi bishiya tunda jiya sunzo fita ta hangi jan magoro to yau kwananka ya ƙare Aisha tace " tana sanya hannu a baki , bishiyar ta haye can sama sai da ta ciro mangoron sannan ta sauƙo ta hau bishiyar gwaiba itama ta tsinki ɗanyu ta sauko ganin sauran bishiyoyin basuyi ba yasa ta zaman dirshan tana maida nunfashi sai da ta gama shan mangoron sanan ta je gurin mai gadi tace " ka buɗemin , ina zaki" mai gadi ya tambayeta zani anguwa ne ,kallon sama da ƙasa yayi mata kana yace " yarinya dake kike maganar anguwa kafin ya ƙarasa zancen ta shatale ƙafarsa ta buɗe ta ruga a guje ta gane hanyar da suke bi ita da Khamis hakan yasa ta dinga tafiya tana waige ita kanta batasan ina zata ba , wani mai katafaren shago ne ya watso kwalaye ƙofar shagonsa , da gudu Aisha taje ta kwaso biyu ta juyo da nufin dawowa gida , tafiya take amma har yanzu bata isa gidan ba , zaman hutu tayi tana mayarda nunfashi dan ta gaji sosai tayi mamakin tafiyarta.
Koda Khamis ya je part ɗinsu bai ga Aisha ba ya shigo toilet nanma shiru ya fito ya shiga ɗakinta shima shiru , fitowa yayi ya zage gidan harda gurin bishiyoyi babu ita babu alamarta , gurin masu gadi yaje da suke zaune suna ta hirarsu , yace "musu dan Allah bakuga Aisha ba ?" mai gadi ne yace " tazo nan tace " sai na buɗe mata nikuma nace bazan buɗe ba shine ta shammace ni ta fice da....kafin ya ƙarasa Khamis ya zuba masa maruka uku lafiyayyu yana haki dan ubanka in Aisha ta ɓata kaine sanadi wlh tunda ai bata fi ƙarfinka ba maza kaje ka nemota duk inda ta shiga wlh ko in saɓa maka.
tafe take da alamun gajiya a tare da ita ita kanta batasan a tahowa tayi wanan uwar tafiyar ba taɓɓ zaman hutunta biyu a na ukun ne tana shirin zama ta hango wani gida ƙofarsa a buɗe amma fa haɗaɗɗe ne gidan na ƙarshe tace " barin shiga ko da wanda zai temakeni tana shiga taci karo da wani mahaukacin kare ya biyota da gudu , itama da gudu ta ƙara ta fice daga gidan ta miƙi hanya , hango mai gadin gidansu tayi da driver cikin ihu tace " kuzo ku temaka min dan Allah....!

Kuyi haƙuri da wanan👏
[29/08, 2:46 pm] Mom Islam Ce 💃: 25 & 26

Yawwa dama ita muke nema su mai gadi suka faɗa suna ƙarasawa gurinta da gudu, itama gurin nasu ta nufa kana ta baje a ƙasa tana mayar da nunfashi tace "dan Allah ku kaini gida ta fara hawaye , riƙo mata hannu mai gadi yayi zai tasheta su wuce tace " bazan iya tafiya ba ƙafafuwana zafi sukeyi , goyata yayi a baya suka ci gaba da tafiya shida driver buɗe get ɗin sukayi kana suka shiga cikin gidan , tsaye suka gansa a jikin mota yana karkaɗa keys ɗin dake hanunsa , sallamar su ce yasa shi ɗago kai bai ankara ba yaga Aisha a bayan mai gadi , baisan lokacin da yace " kutumar uba ya tafi gurin yana gurnani kamar mahaukacin zaki, cukumo wuyan rigar mai gadi yayi da ya sauke Aisha yana mata sannu " dan ubanka waye yace ka goyamin mata baka da hankali ne ko kanka ya kunce ne zaka goya matar wani ?" ya ƙara da sake masa mari har biyu kana yace " last worning wlh yaja hanun Aisha suka shiga part ɗin Ammi ,ganinshi fuska a murtuke yasa

Please Login or Register in order to submit comment