Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi mata cikin sauri yace "zankai Ummi asibiti " kan uba Anty Fiddausi ta faɗa tana riƙe ƙugu ta ƙara da cewa " lallai biri yayi kama da mutum tabbas ace in raini yarinyar tun batasan kanta ba amma ta nemi ƙwacemin miji wlh bazan yarda ba kan bala'i ,tana shirin shiga ɗakinsu Ummi ya tareta yace "zan wanka miki mari bakida tausayi da imani ne ?"yarinyar na kwance itafa ke tayaki aiki amma kina can kina kallo "in baki kauce ba wlh zakiyi mamakin abinda zanyi miki , sanin kanta faɗansa babu daɗi hakan ya sata haƙura ta matsa ta bashi guri tana gunguni , koda ya shiga ɗakin Ummi jikinta ya ƙara zafi sai rawar sanyi take ,anty Fiddausi na tsaye ya fito da Ummi rungume a hannunsa da gudu ta shige ɗakinta tare da kurma uban ihu tace " wayo Allah na na shiga uku kaka wlh sonta yake ga maganarki nan ta tabbbata kaka ki temakeni" kaka ce tace " kwantar da hankalinki akwai wani hamshaƙin malami fitacce a ƙayenmu aikinsa kamar yankan wuƙa wlh inhar kinada kuɗi to ki kawo gobe gobe zantafi kwana biyu zanyi in dawo kafin ma in dawo zakiga aiki ya fara kyau , idanun anty Fiddausi sun rufe tsabar kishi tace " aiko nagode kaka kamar nawa ne zayi , jimm kaka tayi kana tace "ƴan bariki ne suka buɗe masa ido da kuɗi to ni nawa ma zamce kar inzo in ƙayyade azo kuɗin yaƙi kaiwa gashi ba lamuni yake ba , anty Fiddausi ce tace " bari mu gani zuwa gobe zanyi amfani da maganin nan na mallaka da kika bani ko shi waye nasan dole ya sake bakin aljihu , yawwa ƴar arziƙi ai kishi halak ne cewar kaka " haka anty Fiddausi ta wuni babu walwalah sun ɗan daɗe sai gashi ya riƙo mata hannu sun shigo suna shigowa anty Fiddausi ta bisu da kallo ba tare da tace "komai ba ,kaka ce ta fito tayi ɗakin kana tace "Ummi ya jikin ?" da sauƙi Ummi tace "tana matse kanta, washe gari yaya Zakari na rungume da anty Fiddausi yace " gaskiya naji daɗi jiya Allah yayi miki albarka , farr tayi da ido cikin ƙissa tace "to mijina miye amfanina inhar ban sanyaka farinciki ba ?" shafo sumar kansa tayi tace " wlh matsala ce ta dameni kana ta fashe da kuka , cikin tashin hankali ya daɗa rungumota tare da cewa " matsalar me kuma ?" ƙara shagwaɓe fuska tayi kana tace " kaka ce zata tafi gobe kuma banida ko sisi "mtsw yaya Zakari yaja tsaki kana yace " shine kike wani neman ɓatawa mutane rai ?" amma kunso yimin rashin adalci yanzu kakan zata tafi kuƙi gayamin ko ?uhmm uhm anty Fiddausi tace " to ai itace tace " kar in gaya maka wai zan sanyaka ɗawainiya "ta ƙarashe maganar tana shafo sajen fuskarsa "amma ko taje ba daɗewa zatayi ba ko ?" eh anty Fiddausi tace "kwana biyu zatayi oky yace " kana ya janyeta a jikinsa ya shiga cikin ɗaki murmishin mugunta ta farayi tana murna , fitowa yayi da kuɗaɗe a hannunsa ya bawa anty Fiddausi kyautar dubu goma ya bata dubu biyar yace " ta bawa baba , gadiya tayi maga kana ta miƙe zata tafi ya kirawo ta , tana zuwa yace "in kinyi wanka ki haɗamin shayi "to tace "kana ta fice babu kowa a tsakar gidan ta shige wanka tana fitowa ta sanya doguwar riga ta shiga kitchen ta haɗo masa shayi ta dawo tana bashi ta fice " gurin kaka dake can tsakar fida tana gyara tsintsya ,kasancewar ba lallai ka jiyo abinda suke faɗa ba tace " kaka wlh magani yayi aiki gashi mun sami kuɗi naki dubu biyar nawa dubu goma yanzu nawa zan ciko ?" cikin murna kaka tace "kai aiko na gode ki ciko dubu goma kinga aikin da yawa kince a mallake mijin naki kuma kince a rabashi da wanan yarinyar tabar gidannan , cikin zumuɗi anty Fiddausi tace " aiko zan ciko Allah ya kaimu goben.
Washe gari ta kama monday kaka nata shiri yaya Zakari ne zai sauketa a tasha yana fitowa ta yi masa godiya yace " babu komai bayan anty Fiddausi ta sallameta ta fito Ummi ta riƙe mata kaya kasancewar jikin da ɗan dama dama ta raka kaka mota , kaka na gama shiga yaya Zakari yayiwa motar key suka nufi tasha , suna zuwa ana cewa " jos saura mutum ɗaya , kuɗin motar ya biya ta shiga tare da ƙara yi masa godiya a karo na biyu , sunyi tafiya mai nisa inda suka wuwuce garuruwa da da dama suka iso jos cikin ikon Allah ,parking driver yayi ya sauke kowa a tashar da suke sauke pasinja , tare da saukewa kowa kayansa mai mashin kaka ta tare ya kawota wani ƙauye ana kiransa da yalwa ,yara da manya sai murna ga kaka ta dawo ga kaka ta dawo suka karɓar mata kayanta , aka shigar mata dasu gida , tana shiga gida mutanen gidan suka fara yi mata sannu cikin farinciki suka gaisa ta buɗe ɗakinta ta shige , bayan an gana gaggaisawa matar ɗanta ta shigo kaka take tambayarta dabbobinta matar ce tace " ai kuwa suna lafiya jiya ma Sunusi ya kawo tallan wasu nace da kina nan da kin siya , cikin sauri tace "maza aika yaro ya kirawo shi zan siya guda nawa ne ?" kaka ta tambaya matar ce tace " guda biyu ne " amma kin tabbatar da lafiyansu lau ko ?"kaka ta tambaya eh tace " matar miƙewa tayi dan zuwa nemo yara ta aikasu, cikin sa'a taga ɗanta babban ta aikeshi nan da nan sai gashi tare da Sunusi sun taho yana janye da awakan fitowa kaka tayi ta tambayesa nawa ?" cewa "yayi to tinda kece ki kawo wanan babbar dubu goma wanan ƙaramar dubu biyar , cikin murna kaka ta haɗa kuɗi harda na anty Fiddausi data bata ta kaiwa malam ta bawa mai akuya , godiya yayi mata kana ya fice , tasa aka ɗaure mata awakan, dabbobin a halin yanzu sunyi biyar yanzu kuma burin siyan kaji take kamar guda biyar , mutanen gidan sai gulmar kaka sukeyi akan tana ta wadaƙa da kuɗi , dawowa ɗakinta kaka tayi kana tace "dole insan abinyi wlh inhar nace ban komawa yarinyar nan da komai ba zata cimin mutunci tunda batada kunya , barin shiga jeji in samo ganye in daka mata shi, jan mayafi kaka tayi ta tafi jeji ta samo sassaƙen mangoro da na ɓaure da sassaƙen ɗorawa ta kankare bayan ta bazasu a tirai ta ɗauko wani maganin mayu da ta barshi a gida tace "wanan zance ta sanya masa a abinci wanan sassaƙen kuma ta dinga sha zanyi tunanin abinda zan faɗa mata ,sai a lokacin hankalin kaka ya kwanata taji gaba da harkokinta , washe gari ta ɗaure kayanta tare da bawa matar ɗanta dubu uku tace "ta dinga siyawa dabbobi abinci , bayan ta karɓa kaka tace " to zamu koma dama nazo duuba awakai na ne to tunda suna lafiya masha Allah ,yara suka riƙe mata jaka ta fito domin tarar abin hawa,cikin sa'a sai ga mai mashi nan Bauchi road kaka tace "masa ɗari biyu yace "ba tare da neman ragi ba ya kaita suna isa ta shiga motar KD saura mutum biyu cikin ikon Allah sai ga wata mata ta shiga driver ya tada mota suka ɗauki hanya sai KD sunyi tafiya mai nisa , cikin ikon Allah sai gasu a Kaduna bayan an saukesu a tasha kaka ta nemi mashin ya kaita anguwarsu yaya Zakari tana sauka ta basa kuɗinsa ta shiga gidan , anty Fiddausi dake tsakar gida tana wanki tana ganin kaka ta buga tsalle ta rungumeta kamar wacce sukayi shekara basu haɗu ba.
[02/09, 3:11 pm] Mom Islam Ce 💃: 43 & 44


Cikin murna kaka tace " bari mu shiga daga ciki , ajiye wankin anty Fiddausi tayi tabi bayan kaka , suna shiga suka tarar da Ummi da littafin boko a hanunta kasancewar yaya ya sanyata , a tsawace anty Fiddausi tace " dallah tashi ki fice babu shiri Ummi ta fice jikinta a sanyaye , ta fita waje ta zauna tana tsane da tsinke a ƙasa , wani kyakyawan saurayi ne yazo ya tsaya a kanta tare da cewa "ƴan mata barka da wanan lokaci " ywwa Ummi tace "tana ɗago kai tare da miƙewa daga tsugunnen da take , dan Allah in bazaki damu ba inason ki bani numbern ki tare da daddaɗan sunanki nasan inda kike da kyau haka naki sunan ma , murmishi Ummi tayi kana tace " sunana Ummu Salma bani da waya gaskiya , tunda yaya Zakari ya karyo kwana ya gansu a tsaye suna hira baƙinciki da takaici duk sun dirar masa a zuciya , yana zuwa dai dai saitin inda suke yace " an yi mata miji inhar na sake ganinka a nan wlh sai kayi nadama , saurayin ne yace " kayi haƙuri itace bata faɗamin ba ya wuce " jan hanunta yaya Zakari yayi suka wuce gida suna shiga yaji kaka na cewa "wai koɗan soye soye ba'ayimin ba , da sallama ya shiga ɗakin da suke zaune Allah yasa duk kaka ta gama yiwa anty fiddausi bayanin maganin sun mayar jaka ya zaunar da Ummi yace " inga kin sake fitowa ya durƙusa ya gaida kaka bayan sun gaisa yace " Fiddausi kizo inason magana dake " to anty Fiddausi tace " tare da miƙewa tabi bayansa , tana shiga ta samesa kamar wanda aka yiwa saƙon mutuwa , zama tayi a gedensa ta ɗauka zai ce Ummi taje gida sai taji yace " baki jan yarinyar nan a jiki sam na ɗaukota domin ta tayaki aiki kina wulaƙantata yau zan mai data gida insha Allah taci gaba da karatu a gaban iyayenta , ayiri yiri wayo daɗi anty Fiddausi ta faɗa tare da manna masa kiss a kumatu ga mamakinta sai taga ya miƙe ya fice ya leƙa ɗakin su kaka yace "Ummi fito da kayanki mu tafi , cikin murna Ummi ta fito da komai nata aka sa a bayan mota suka ɗauki hanya , tunda suka fara tafiya babu mai yiwa kowa magana shikam tunani ne fall zuciyarsa da kuma fargabar abinda zuciyarsa ke nanata masa , ita kuma farincikin zuwa gidansu take dan ta gaji da cikashin da suke mata , cikin ikon Allah sai gasu a ƙofar gida , hanunta ya riƙe suka shiga gidan su Ummi a tskar gida yaga maman tana zaune da redio a hanunta tana ganinsu ta buɗe tabar ma tana cewa "sannunku da zuwa , bayan sun gaisa tace "Ummi ta ɗibo masa ruwa bayan ta ɗibo yasha yace " wa maman Ummi na kawo Ummi ne tayi hutu zanzo in ɗauketa "cike da farinciki maman Ummi tace " to ai babu damuwa mun goode Allah ya bar zumunci ya miƙe tare da ajiye maman Ummi dubu ɗaya ,godiya tayi masa tare da sanya albarka ya fita , kai tsaye gidan su ya shiga ya sami mamansa da malam suna zaune kan babbar tabarma , shima tunda yaga malam ya dena wulaƙanta mamansa shikenan yake jin daɗi a ransa har yake yi musu alkairi tare , bayan sun gaisa da iyayen nasa suke tambayarsa ya iyalan ?"suna lpy yace " kana sukace madallah , yaya Zakari ne ya kalli murhu yace " mama naga rana tayi bakiyi abinci ba ?" hmm mama tace " wlh duk kayan abincin ya ƙare dan ma mijin Aisha na zuwa yana kawo mana kayan abinci shiyasa wlh , malam ne yace " aikam bamuda bakin yi musu godiya gaskiya ,ficewa yaya Zakari yayi ya nufi gurin mai kayan abinci ya siyo galan ɗin manja da mangyaɗa a gora da shinkafa mudu bakwai da maggi da gishiri ,ya dawo da babban buhu a kansa , malam ne ya miƙe ya karɓesa yana cewa "Allah dai yayi maka albarka Allah yasa ka gama da duniya lafiya kai mungode ,malam harda ƴar ƙwallarsa kasancewar kaf kuɗinsa ya ƙarar dasu akan hidimar bikin amarya kuma aikin malintar ma babu sosai shiyasa jikinsa saurin yin sanyi , dubu biyar yaya Zakari ya ciro yaba malam dubu uku yaba mama dubu biyu , godiya suka dinga yi masa tare da sanya albarka , yaya Zakari ne yace " malam inason muyi wata magana , mama na shirin tashi malam ya dakatar da ita yace "ina zaki ?" dawowa tayi ta zauna "yaya Zakari yace "malam dama akan maganar Ummi ne sai kuma yayi shiru , malam ne yace "ina jinka ?" dama dama ,mama dake dariya dan ta harbo jirgin tace " ikon Allah dama tasa dariya , yaya Zakari ne yaci gaba da cewa dama inason Ummi ne murmishin su na manya malam yayi yasan dama za'ayi haka tabbas akwai wanan rana , ga mamakinsa sai yaji malam yace "Alhmdulilh mungode Allah tabbas naji daɗi , to zanyi wa mahaifinta magana muji ya abin zai kasance , cikin farinciki da maganar malam yaya Zakari ya tashi dan ya kasa cewa "komai sai murmishi da yake yi yana ƙarawa , yana fita ya shiga mota sai gida , yana dawowa gida ya wuce ɗakinsu ya kwanta kan gado yana ta murmishi anty Fiddausi da tayi amfani da maganin da kaka ta kawo mata ta ɗauka hankalin nasa ne ya fara dawowa gurinta , ta shigo ta zauna gefensa ta shafo sumar kansa tace "mijina har ka dawo ?ina fatan dai bazata sake dawowa ba ko ?"haɗe rai yayi yace " ai ta tafi kenan ya janyota cikin zuciyarsa yace "tun yanzu zan fara lallaɓa ta inba haka ba intaji maganar aurannan sunana sorry.

Yau ta kama ranar visiting kowa da kowa danginsa na zuwa Zaune Aisha take riƙe da wani littafi na hausa Khadija ce ta bata tace "ta dinga karantawa " tana cikin duba littafinne taji mutum ya rungumeta ta baya , har zatayi zagi sai kuma ta fasa ta juyo wa zata gani yayanta wato kyakkyawa dariya tayi kana tace "yaya baka taɓa yimin irin wasannan ba sai yau kuma babu kyau wlh , hannu Khamis ya haɗe yana murmishi yace " na dena ƙanwata yakk ya zagayo ya zauna ɗan nesa da ita , lafiya tace " tana murmishi dariya tasa tace " naga kayi ƙiba da haske ne "kaci kaji da romo ko ?" sukasa dariya " to ya karatu ?" yaya Zakari ya tambayeta yana ɗaga mata gira , karatu alhmdulilh ina " mamana ?" Aisha ta tambayi Khamis Ammi na lafiya tace "in kawo miki wani abu , amma ki rufe idonki har naje mota na dawo tana dariya ta rufe ido tace " nagaji fa cikin ɗaga murya , dawowa yayi da foodflaks a hanunsa ya ajiye mata a hannu yace " gashi buɗe ido , tana buɗewa taga farfesun kaji ne cike da kular wani irin farinciki taji dama tana sha'awar shi Allah sarki mamana ta faɗa a fili.
cokalin dake ciki taauka ta fara ci kasancewar duk an cire ƙashi sai tsoka yasa ta dinga cika baki tana ƙarawa , yana zaune yana ƙare mata kallo inda ta ƙara kyau sosai , komai nata yana brgesa musamman in tana shagwaɓa , wanan zan ajiyewa Khadija ne ta kalli Khamis , waye Khadija kuma ?" Khamis ya tambaya wata ƙawata ce wlh tana sona sosai , kirawo ta in ganta Khamis yace " yana kallon yanayin tafiyar Aisha, tare suka taho da Khadija ta ɗan risina ta gaishesa ya amsa zata juya ya sa hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu ya bata kana yace "dan Allah kici gaba da kularmin da ƙawarki "dariya Khadija tayi tace "insha Allah ta basu guri "yaya bayan kaza sai me kazo min dashi na ci ?"cewar Aisha , dai awara ya ƙyalƙyale da dariya ya tuno lokacin da taci awarar mutane ta gudu ya kuma sa dariya ,tashi tayi alamun tayi fushi zata wuce ya riƙo mata hannu yace " am sorry matata , zaro ido Aisha tayi kana tace " wai da gaske ni matarka ce yaya ?"
[03/09, 8:02 am] Mom Islam Ce 💃: 45 & 46

Eh man Khamis ya bata amsa "shiru tayi ba tare da ta sake magana ba , lokaci nayi yayi mata sallama ya tafi.
Washe gari , Aisha da Khadija na zaune kasancewar sun zamo manya babu mai takura musu sai malamai d s..

Wanan malamin da tayiwa laƙabi da ɗan iska shine yazo ta gabansu yace "Aisha ina san ganinki a office "cikin dakiyar murya tace "to koda ya tafi ya ɗauka zata taso nan da nan inaa taƙi tasowa har sai da Khadija tace " ba girmaki bane ki tashi man ki tafi da adu'a a bakinki kinji ?" tom Aisha tace " ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi office ko da taje ta samesa zaune yake kan kujera ya tura mata jujera da ƙafa , Aisha ce tace "ba zama zanyi ba , kizaunaa....ya daka mata tsawa a razane bai lura ba ta fice da gudu , Khadija ce ta nufota tana cewa "menene zai kasheni ki kaini gida Khadija , rungumeta Khadija tayi kana tace "haba Aisha maiyasa kike haka ko yayi miki wani abinne ?" a'a Aisha tace " tana ware ido , zake Khadija tayi kana ta ruga da gudu taje office ɗin da Khamis yake shiga in yazo , kafin ta shiga ta saita nutsuwarta kana ta shiga , samun malamin tayi zaune a kan kujera da jarida a hanunsa , durƙusawa tayi ta gaishesa kana tace " malam dan Allah ka kiramin yayana dan girman Allah , a nitse malamin yace " me zakiyi masa ?" babu komai jiya nayi mafarki ne shine nakeson inji yana lpy ?" Aisha ta ƙarashe maganar a marai raice , ɗaga waya malamin yayi ya kira number Khamis cikin sa'a ta shiga yana ɗagawa ya miƙawa Aisha , karɓa tayi tare da rugawa waje da gudu sbda gudun kar malamin yaji abinda zata faɗa , lungu ta samu tace "hello yaya "ina jinki Aisha yi magana Khamis ya faɗa" walh yaya ratuwata nacikin matsala wani ya sani a gaba a cikin makarantar nan wai sai dai inbashi kai na whattt....Khamis ya faɗa tare da kashe waya ya miƙe , Ammi dake zaune tace " lafiya kuwa son , Ammi zanje in ɗauko Aisha walh ta gama karatu gaskiya kinga irin abin ko Ammi ?"Khamis ya faɗa yana janyo keys ɗin motarsa , janyoshi Ammi tayi kana tace " to zauna man kayimin bayani "yama kasa gaya mata komai sai da ta matsa sosai ne yace " mata wani ne ya keson lalata rayuwar Aisha ,a tsorace Ammi ta miƙe kana tace "Ai maganar barin ta makaranta bata taso ba , ayi wa malaman magana kawai .
Inaaa Khamis yace " yana girgiza ka kana yace " Ammi kiyi min haƙuri wanan karon banbi son ranki ba nasani da tafiya jiya nace makarantar gashi yau ta kirani tana kuka kuma insha Allah yauma zan koma amma dirver zai kaini kiyimin adu'a Ammi na pls ,ya haɗe hannayensa guri ɗaya .
Ammi tasan inhar Aisha tabar makaaranta a wanan time ɗin to ta gama kenan dan bazata kuma yiba babu inda ta iya kamar yadda yake jin maganar ta da kuma kawo mata damuwarsa yasa ta cewa "Allah ya kiyaye hanya son "amen ya Allah yace "tare da ficewa yana fita driver yazo da gudu ya durƙusa tare da cewa "mai gida za'a kaika ne ?"eh Khamis yace "kano zamu tafi yi sauri , driver ne yace "a shirye nake muje ya buɗewa Khamis mota Khamis na shiga suka ɗauki hanya , tafiya suke amma Khamis na ganin kamar basa sauri ,dakatar da drivern yayi yace " sauko ni zanyi driving yana shiga mazaunin driver , shikuma driver ya zauna a gurin da ya tashi wani mahaukacin gudu ya fara kamar zasu tashi sama a titi ikon Allah ne ya kawosu Kano bai gama farinciki ba sai da ya gansa a bakin get ɗin makarantar a waje ya bar motar tare da driver shi kuma ya fice , kai tsaye office ɗin wanan malamin ya nufa wanda Aisha ta ari wayarsa , ya sameshi a zaune bayan sun gaisa ne Khamis yace " bakuda tsaro a makaranta tabbas yau zan cire ƙanwata ko ku yarda ko karku yarda zan tafi da ita da rayuwarta ta salwanta , yana fita cikin zafin rai ya hango Khadija ta fito daga wani aji , kira ya ƙwala mata kana yace "inason ganin Aisha bayan sun gaisa , tom tace " amma Aisha na ɗaki tana kuka nayi nayi ta gayamin damuwarta taƙi , da sauri ya shiga ɗakin da Khadija ta nuna masa ya hangota ta ƙudundune tana ta kuka ,my Esha Khamis ya faɗa cikin muryar damuwa maza haɗa kayanki mu tafi gara kibar makarantar ya faɗa yana cewa "tayi sauri , cikin mamaki Aisha tace" yaya kaine ta miƙe ta har haɗa kayan zata ɗibi kayan abinci yace "ki barwa Khadija man "Aisha ce ta ƙwalawa Khadija kira bayan Khadija tazo ta miƙa mata ragowar kayan abincinta sunada yawa , godiya Khadija ta dinga yiwa Aisha tana jin Aisha tace " ai tafiya zasuyi ta fashe da kuka sai da tayi mai isarta ta rakasu mota , kuɗi Khamis ya bawa Khaɗija dubu ɗaya tayi masa godiya suka wuce ,kaf malamai sai da suka fito amma babu mai magana kasancewar sun san ko waye shi , yanzun ma driver ne yaja su suka ɗauki hanya , sai da taga sun shiga wani gari sanan ta share fuskarta ta kalli fuskar Khamis taga yana kallon gefe , cikin zuciyarta tace " yanzu shikenan bazan kula samari ba "taɓɓ aikuwa duk wanda ya kulani zan kulasa taji gaba da zancen zuci ,taɓo hanunta da taji anyi ne ya sanyata zare ido alamar tayi shiru yayi mata da hannu ya juya da ita kana ya kwantar da ita kanta a kan cinyarsa yana mammatsa hanunta a hankali , ashe dama bacci take ji nan da nan tayi bacci , bata san har sun kawo KD ba , kai tsaye anguwarsu Khamis suka nufa horn driver yayi mai gadi ya buɗe get , suna shiga driver yayi parking tare da zagayowa ya buɗewa Khamis a kafaɗa ya rungumota kamar baby ma'aikatan gidan nata kallonsa sunata mamakin girman Aisha babu wuya , kai tsaye part ɗin Ammi ya wuce da ita dama tunda ta girma ko tazo a part ɗin Ammi take kwana , kwantar da ita yayi a kan kujera kana ya tafi bedroom ɗin Ammi , nockinh ya fara kana ya tsaya tare da jingina a jikin bango buɗewa Ammi tayi kana tace " har kun iso ? Eh Khamis yace "yana murmishi , fitowa Ammi tayi tana yiwa Aisha sannu da zuwa, ganin tana bacci yasa Ammi kallon Khamis tace "ka tasheta taje ɗaki man zaka barta a nan , ba hakan yaso ba yaso Ammi tace "ya wuce da ita part ɗinsu fuska babu walwalah ya ɗaukeya cak riƙe baki Ammi tayi dan tana mamakin rashin jin kunyarta da bayayi yanzu ko kaɗan , harda iya ɗaukar budurwa , yaje kwantar da ita ta tashi ta zauna tare da cewa "har munzo ne ?gaki a ɗakin Ammi ma "Khamis ya bata amsa , cikin murna tace " barinje dubo mama ƙila tana palo "kamo hanunta yayi ta faɗa kan cinyarsa ta zare ido tare da shirin zubawa da gudu , daɗa kamota yayi ya haɗe bakinsu guri ɗaya tare da matseta a jikinsa sun ɗau lokaci a hakan can kuma ya saketa ta goge bakinta tana cewa "kai ba mijina bane ma , zaro ido yayi kana yace "me kike cewa " wll zakisa ranki ya ɓaci inhar na kuma jin kalar wanam kalmar to bazakiji da daɗi ba , ficewa tayi ta sami Ammi dake

Please Login or Register in order to submit comment