Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da damuwa ya ishi mama ta zauna ta fara kuka tana salati malam na fita amaryar tayo ɗakin mama da icce zata daki mama shigowar Aisha kenan tana waƙa amaryar ta ɗaga iccen sai a kan Aisha ta sauke mata shi ji kake gimmm sumammiya ko mai rai Allah ne kaɗai yasan dai dai "da gudu mama ta miƙe tana salati tana kuka bata tunkari kan amaryar ba tayi kan Aisha tana kuka kamar ranta zai fita , bangaje amaryar mama tayi tana kuka ta fice dariya amarya tasa tana cewa "sa'a tafi sammako mama babu hijab ta leƙa ƙofar gida hakan ya bawa malam mamaki ya leƙo yace "wane irin hauka ne haka ?"da muryar kuka mama tace " an kashe Aisha "malam ne ya wurgar da redion hanunsa kana yace "me kika ce ?" mama bata ƙara bi takan malam ba ta koma ɗakinta inda tabar Aisha haka ta dawo ta sameta babu nunfashi hankalin malam a tashe yace "waye yayi mata haka ko faɗuwa tayi ?" mama dake sharar hawaye tace "amaryarka ta bigeta da icce a kai , ya salam malam yace "tare da ɗaukar Aisha Allah yasa suna fita sukaci karo da mai mashin sai asibiti , emergency aka wuce da ita inda aka fara bata kulawar gaggawa , hatta likitoccin sun fara karaya sosai da lamarin in suka fara aiki har wani uban gumi sukeyi kaf cikinsu babu wanda bai tausayawa Aisha ba"
Mama da ta koma kamar kurma sai sharar hawaye take tana ƙarawa malam kam ya kiɗime dan zirga zirgar da yake ne zai tabbatar maka yana cikin damuwa innalilahi yake ta mai maitawa yayinda ƙasan zuciyarsa ke tafasa kamar garwashi , da likitoci sun fito zaiyi kansu da gudu yace "musu lafiya ?" babu mai kulasa.
Washe gari har yanzu sunata ƙoƙari kan Aisha abin ya girmama har yanzu basu faɗi halin da take ciki ba , mama kwana tayi babu bacci malam kan ta kwana yana sallah , sai da yayi haske sosai malam ya fita ya siyowa mama abinci yace "mata ya tafi gida yana zuwa gida ya sami amarya ta sake waƙa a waya tana ta tiƙar rawa , a fusace ya buga wayar da ƙasa yana yi mata bala'i tana magana ya wanketa da mari kana ya janye ƙafarta ta faɗi ƙasa yace " wlh karki ɗauka kinci banza sai na zubar miki da jini kema "mtsw amaryar taja tsaki tace "a banza zama daram dan ɗan wanan abin sai ka tada hankalinka garama kazo musha soyayya nayimaka tanadi oyoyo mijina "kukane malam baiyi ba sai da ya nisa yace soyayyar ubanki shegiya mai mugun hali dana san gaka kike babu abinda zai sa na aureki ƴar iska kawai jaka jahila "amarya ce tace "nasan ta gama da kai kome zakace ba yin kanka bane nasani Allah ya bakaaa lpy malam malam dake ɗauko wa mama kaya yace " amen tare da ubanki shegiya jaraba ya fice daga gidan yana shirin fita ya hangi motar Khamis wani mummunan faɗuwar gaba ne ya riskeshi ,Khamis na shirin fitowa malam na shirin zuwa jikin Khamis tun jiya yake jin babu daɗi ko abinci bai ci ba jiya yace "wa malam ina wuni tare da durƙusawa malam ne yace "lpy ya iyayen naka ?"suna lpy Khamis yace "masu gidan sunan ko ?" Khamis ya tambaya "malam ne yace " suna asibiti ,gaban Khamis ne ya yanke ya faɗi yace "waye babu lafiya ?"malam ne yace "ƙanwar Aisha ce "Khamis ne yace "dama Aisha nada ƙanwa ne ?"malam bai iya bashi amsa ba zai shige yace " baba in asibitin zaka kazo muje nima zani ya faɗa murya kamar zaiyi kuka , shiga motar malam yayi suka tafi , cikin ikon Allah suka iso asibitin suna shiga hanyar da zai sadaka da ɗakin mai jinyar Khamis yaji gabansa na dukan uku uku , mama ya hango bai hango Aisha ba to ina take ya tambayi zuciyarsa" ƙarasawa gurin mama sukayi dake zaune a benchi ta ɗaga kai sama , durƙusawa Khamis yayi ya gaida mama tare da cewa "ya mai jiki ?"da sauƙi mama tace "Allah yasa su barka ka shiga " malam ne yace "wai har yanzu bata motsa bane ?"eh bata motsa ba wlh mama ta faɗa da alamum damuwa a fuskarta" miƙewa Khamis yayi kana yace "inane ɗakin marar lafiyar ?" gashinan mama tayi masa nuni da hannu buɗewa yayi da sallama yaga likitoci sunkai biyar akan wata kamar Aishansa diri diri yake gani kasancewar ganin Aisha da yayi kanta ɗaure da bandeji kamar babu nunfashi ,waya ya ɗaga ya kira Ammi taga ɗagawa yace " Aisha babu lafiya muna asibiti ya gaya mata sunan asibitin ,suna gama waya ya faɗi ƙasa sumamme jin hayaniya tayi yawa a ɗakin yasa malam shigowa ganin Khamis a kwance yasa shi salati ya ƙwalawa mama kira nan da nan aka bashi gado aka fara bashi kulawa , cikin mintuna ƙalilan sai ga Ammi nan ta iso tana cikin tambaya ne suka haɗu da malam yace " ga ɗakin da aka kwantar da Aisha can shiga Ammi tayi jiki a sanyaye ta zauna hawaye nabin fuskarta yarinya mai barkwanci" tambayar ina Khamis tayi" cikin in ina malam yace " ya ya ya....yaje ina ?" Ammi ta faɗa hankali a tashe tasan in akan Aisha ne babu abinda bazai yi ba.
Yana kwance an bashi gado , a kiɗime Ammi ta tambayi ɗakin aka gaya mata tana shiga ta gansa kamar wanda yayi ciwon shekara duk ya rame sosai shafa fuskarsa Ammi tayi tare da cewa "Allah ya baku lpy my son ta share hawayen daya kwaranyo mata ta nemi kujera ta zauna .
Malam da mama babu mai iya magana kowa da abinda yake kitsawa a zuciyarsa wani doctor ne ya fito kana yace "ana neman mahaifin yarinyar nan da take wancan ɗakin doctorn ya nunawa malam da hannu , cikin fargaba malam ya isa gurin yana salati a zuciyarsa samunsu yayi sun rufeta baya ko hangota bare yasan meke faruwa, ganin basu kulashi ba yasa shi ficewa ya zauna ya maida tagumi , tunowa yayi rabonsa da abinci tun jiya da rana tabba hausawa sukace inkaji ance baka iya kuka ba to uwarka bata mutu ba , tashi ɗaya mama ta rame Ammi na can ɗakin Khamis dake ta bacci anyi masa allura , zuwa can anjima sai gashi yana motsi da jikinsa cikin farinciki Ammi ta daɗa matsowa da kujerar da take zaune tace "my son ga Amminka ta share wasu hawayen da suja ƙara yi mata sintiri buɗe idonsa yayi a hankali ya kalli Ammi tare da kamo hanunta ya haɗe a nasa yana kallonta
[30/08, 4:41 pm] Mom Islam Ce 💃: 31&32

"Ammi na Aisha ta mutu ko ?"Khamis ya jefowa Ammi tambaya "bata mutu ba my son tana nan lafiya "Ammi ta faɗa tana kallonsa, Khamis ne yace "to Ammi riƙemin hannu muje in ganta "riƙe masa hannu Ammi tayi suka isa room ɗin da Aisha take babu likitocin sai mama da malam dake zaune fuskar su wasai suna dariya da sauri Khamis ya ƙarasa kan Aisha yace "ta warke ne ?"eh mama tace "amma ta koma bacci "ina Khamis ya faɗa da ƙarfi ta mutu ne kuke ɓoyemin walh Ammi ce ta riƙe hanunsa ta jashi zuwa gaban Aisha ta riƙo hanun Aisha ta haɗa da nashi jin haka yasa Aisha buɗe ido cikin murya irin ta marar lafiya tace "kyakkyawa "wayo Aisha na Allah nagode maka haƙiƙa ni mai sa'a ne a rayuwa wayo Allah Aisha taji sauƙi natafi masallaci yin sallah dan in nuna godiya ga Allah ya fice ya nufi masallaci, Malam da mama da Ammi mamakin irin soyayyar da Khamis ke yiwa Aisha sukeyi tabbas samun kamar Khamis sai an tona , bayan ya idar da sallah ne ya fara kwararo wa Aishansa adu'ar daɗin samun lafiya mai ɗorewa ya dawo ɗakin cike da fara'a har lokacin idon ta biyu , janyo kujera yayi ya zauna daf da gadon da take kwance su mama ficewa sukayi dukansu , kamo hanunta yayi yana kissing yace "my Esha bana son ki tafi ki barni ko a mafarki , Aisha dake shirin kuka tace " kyakkyawa amarya ce ta ƙwalamin icce a kai na shine na faɗi "waye amarya ?" Khamis ya tambaya , amaryar malam fa Aisha ta faɗa tana taɓa bandejin kanta , a zabure ya fice ya fito waje Ammi na ganinsa yana huci tace "son me kuma ya faru ?"tasowa malam yayi a firgice yace "jikin Aishan ne?" zani ɗaukar fansar bugawa Aisha icce ne ya faɗa babu ko jin ɗarr a zuciyarsa ,idanun malam na zubar da hawaye yace "ka rabu da ita kowa yayi nagari dan kansa ni kaina badan kar ashe nayi aure da wata manufa ba sati ɗaya na saki mata wlh da saina saketa , dakatar da Khamis Ammi tayi kana tace "abi komai a hankali Aisha ta gama samun lafiya.
Kwa nan su Aisha biyar su yaya Zakari da anty Fiddausi sukazo duba su tare da kawo kayan tsaraba Ammi kam kullum tana zuwa ta koma gida washe gari ta kuma dawowa Khamis kam sai wajen ƙarfe goma na dare yake barin asibitin .
Sosai taji sauƙi dan jikin ya ɗan warware har ana shirin sallamarsu gobe insha Allah, murna gurin Khamis abin babu sauƙi har yana gayawa Ammi ana sallamar Aisha tace "zata wuce da ita gida shiru Ammi tayi masa tafison ta ƙara samun lafiya sannan ta dawo .
Washe gari ana sallamar Aisha suka wuce gida suna shiga suka ci karo da amarya tana wanke wanke , ko kallon su batayi ba suka shige da malam da mama da Aisha , kai tsaye ɗakin mama suka wuce ta kwanta a gado kasancewae jikin babu ƙarfi.
kwana goma da faruwar hakan jikin Aisha yayi sauƙi har tana fita waje tayi wasa da safe ƙarfe 7:am amarya taje maƙota siyo kunu Aisha ta cinno wuta a icce tasa jikin labulen amarya kana ta ɗauki ragowar kananzir ɗin dake gorar da mamanta take hura wuta ta wartsa nan da nan wuta ta kama sosai kayan ɗakin ya fara cin wuta , buta Aisha ta ɗauka da gudu tayi bayi ta tsuguna tana jiran shigowar amarya.
Amarya ta shigo da waƙa harda tafi taci karo da ɗakinta na cin wuta salati tayi kana ta ƙwala ihun neman agaji wuta ta cinye kayan ɗaki harda gado da katifa jin muryarta a sama yasa malam shigowa da sauri ya ɗauka mama ce jikin Aisha ya tashi , yana shigowa ya sami amarya tana ta ɗaga hannu sama alamun temako mtw malam yaja tsaki tare da cewa "kin ɗauka Allah zai barki a haka ne ?"gashi banyi miki komai ba Allah ya sakawa baiwar Allah cikin ƙanƙanin lokaci , malam ka fita a idona in rufe wlh Allah daga kai har matsiyaciyar matarka sai kunyi dana sani wa yasani ma ko shegiyar ce ta sa wutar inko naje naji ance itace to ba shakka sai na daɗa fashe mata kai , a lallai malam ya faɗa yana jinjina kai tabbas biri yayi kama da mutum dama jiya akace min kin taɓa hauka nace ƙarya ne amma babanki ya cuceni da bai gayamin gaskiya ba , wani wawura ta kawowa malam ya ruga da gudu dan tsoronta yake ji amma bai nunar mata ba tana guduwa tace "daka tsaya dana nuna maka ni babbar ƴar iska ce kuma kaci bashi ai tunda kukace haka to an gama zaman lafiya a gidannan kowa sai ya kwashi kayansa a hannu , kana ta kuma rushewa da kuka tana nuna ɗakinta babu wanda ya shigo duk mai shirin shiga malam zai ce ai hauka yana tunanin ta fara anjima kaɗan zai kaita asibitin mahaukata sai su ja baya , maman Ummi da taji abin yayi yawa ta yafo gyalenta tana shirin shigowa taci karo da malam babu damar ya hanata dole ya barta ta shiga tana shiga taga amaryar gidan na kuka tare da sanya hannu a kai , gefen ɗakinta maman Ummi ta kalla taga duk ya kama da wuta Allah ya kyauta maman Ummi tace "tana shirin wucewa ɗakin mama amaryar tace "munafuka a haka zaku ƙare taci gaba da kururywarta , sai yanzu Aisha ta fito daga bayi tana cuno baki, saitin ɗakin amarya Aisha ta kallah suna haɗa ido amarya tace " to yarinyar munafukai, uban me kike kallo?" amarya dai ta koma kamar mahaukaciya sai bala'i take tana gamawa tasa kuka haka ta dingayi duk wanda ya shigo sai ta zageshi , maman Ummi ce tace "wa mama ya jikim Aisha bansami zuwa ba wlh baban Ummi ne babu lafiya jiya ma ya ban tsoro , subhannalah mama tace " Allah ya bashi lafiya mai ɗorewa amen maman Ummi ta faɗa kana tace "naji abu kwam a gari wai waccan ce ta bugawa Aisha icce a kai ?" hamm mama tace " eh itace ai da saidai kuji saƙon mutuwa wlh dan daga ni har malam bamuyi tsammanin Aisha zata tashi ba , taɓɓ to Allah ya ruda asiri maman Ummi ta faɗa tare da miƙewa ta fice, lokacin d tazo fita amarya ta koma ɗaki tana kuka tana surutai .
mama ta fito daga ɗakinta da niyar haɗa wuta sai yanzu ta lura da cin wutar da ɗakin amaryar yayi kuma hakan bazai sa tace "da ita Allah ya kyauta ba mama ta jinjina kai.
washe gari yau kwanansu biyu da sallamowa Khamis ya zo da safe lokacin ƙarfe goma da rabi ya kaawowa Aisha kayan marmari aiko yasha hira dan bata gayawa mama itace tasa wuta a ɗakin amarya ba amma Khamis na bata sweet tana cikin sha tace " kyakkyawa na rama abinda amarya tayi min na ƙona mata ɗaki waro ido Khamis yayi kana yace "da hankalinki kuwa Aisha sai na gaya mata , tsaki Aisha tayi tace "wlh jeka ni ba tsoranta nakeji ba , jinjina kai Khamis yayi kana yace "taɓɓ duk wanda ya taɓo Aisha ya taɓo wa kansa tsiya , dariya Aisha tasa tace "har monday ta wuce ba'a kaini makaranta ba kyakkyawa?" bakya ganin bakida lafiya ne my Esha amma tunda kinji sauƙi kina komawa za'a kaiki kwantar da hankalinki , tsalle Aisha tayi tace "jibi zan dawo gidanku kaji kyakkyawa ?"ywwa my Esha Khamis yace " aiko zansa a soya miki kaji da farfesun naman rago suka sa dariya , yace " to ni zan tafi sai jibin nima nakusa tafiya amma naji ance kamar tafiyar zata fasu , bata shi takeyi ba sai tsallenta take iya san ranta ,niko nace kaji kamar yana magana da babbar mata , ficewa yayi ransa fess a nesa da bakin ƙofa ya sami mama ya ƙirgo dubu biyar ya bata ƙin karɓa tayi sai da ya nuna bazai mayar aljihu ba sannan ta karɓa , amarya najin Khamis ya fita ta fito ta riƙe ƙugu tace "a bani nawa kason dan baza'a zalinceni ba ina gani ehe
[31/08, 2:24 pm] Mom Islam Ce 💃: 33 34

Ko ɗago kai mama batayi ba Aisha ce ta bata amsa tace " to ai ba mijin ƴarki bane "kan uba amarya ta faɗa cikin ɗaga murya to wlh yau za'ayita a cikin gidannan ace ko tausayina baza ayi ba nayi gobara ban ɗauki komai ba ace baza'a bani koda dubu biyu ba tana maganar tana tafi kamar ƴar dambe "malam da ya shigo ajiye buta yace "meke daruwa ne ?" kuɗi aka basu shine ta hanani malam ne ya shiga ɗakin mama yace "ki bata koda ɗari biyar ne a cikin kuɗin "babu musu mama ta bata shima darajar taga malam ya sakko tunda suka kwanta a asibiti , miƙa mata kuɗin malam yayi cikin masifa tace "kambu wlh baku isa ba dubu biyar fa naji wanan munafukar na cewa "taɓɓ ta wurgawa malam ɗari biyar ɗin , ɗauka yayi ya fice kai tsaye gurin mai shayi da indomie ya nufa yace "ayi masa haɗi yaji albasa da maggi kana yace "mai shayi ya bashi aron plet ,ana gamawa malam ya shigo da plet da baƙar leda a sama amarya dake tsaye tana jijiga tana surfa bala'i ta gansa da plet a hannu bata kulasa ba ta tsaya taga gudun ruwansa ,zama yayi kan kujera ƴar tsugunno kana ya buɗe indomie da ƙwai haɗe da shayi,ya fara aikawa cikinsa ,aikin banza harara a duhu amarya ta faɗa lokacin da ta fito da jakar kayanta wai tayi yaji , Allah ya kaiki lpy malam ya faɗa , kuka tasa tace " bakada tausayi ko kaɗan ɗakin nawa yayi gobara amma ka kasa temakamin da koda wani abu kwanan da zanci abinci ma bani da shi malam dai kansa a ƙasa bai kulata ba ta fice ta tafi.
Bayan kwana uku.
tun safe Khamis yazo yai parking kana ya shiga gidan samun mama da Aisha yayi a gaban murhu durƙusawa yayi ya gaid mama Aisha ta gaishe shi tare da cewa "kyakkyawa nafasa tafiya "Aisha ta faɗa tana maƙalewa a jikin mama "dariya mama tasa tace "aiko tafiya babu fashi shima Khamis murmishi yake , barin jiraki a mota Khamis yace "kana ya fice , zama yayi a mota ya ɗaga kansa sama yana murmishi mai sauti Allah yasa shi kaɗai ne a motar babu driver kasancewar in zaiyi tafiya da Aisha bayason driver ya kaisu .nhg gb
Ya daɗe a cikin momta sai gata cikin wata koriyar shadda riga da sket, duk da ba wata babba bace kayan sunyi mata kyau ta yafa farin mayafi ta iso gurinsa da wata leda a hanunta da jaka kuma , buɗe mata motar yayi ta shiga ta zauna a gaba shi da yake mazaunin driver ya jangota tare da zuge glass ɗin , kasancewarsa baƙi yasa bazaka hango kowa ba sai dai shi da yake ciki yana iya ganin masu wucewa "kyakkyawa ka dena fa wlh babu kyau kuma za'a dinga ce mana ƴan iska "murmishi Khamis yayi ya kuma janyota har sai da ta dawo kan cinyarsa ya haɗe fuskarsu guri ɗaya yana cewa "ina miƙa godiyata ga Allah da mafarkina bai kasance gaskiya ba tabbas na shiga ruɗu my Esha na ɗauka zaki tafi ki barni ne ashe zamu sake haɗuwa my Eshana , dariya Aisha tayi kana tace "kyakkyawa in baka labari naji ana cewa "amaryar malam tafara hauka "zaro ido Khamis yayi kana yace " innalilahi shine kike dariya my Esha suk da ta cuceki amma ai Allah yace

"AL MUSLIMU AWUL MUSLIMU"
musulmi ɗan uwan musulmi ne .

"Dan haka ki zamo mai tausayi ko gobarar da kika sa mata banso ba wlh amma karki ƙara kinji "kuka Aisha tasa tare da cewa "nama fasa binka buɗemin ƙofa na fita baza'aje ɗin ba , rungumeta yati tsamm yana shafa bayanta yace " dan nayi miki faɗa shine kikaji haushi ?"to ai Ammi tace "in baki koma yau ba maganar makaranta tasha ruwa ,ƙara ƙanƙameshi Aisha tayi kana tace " zani muje zani "jikinsa duk ya mutu haka ya tada motar suka bar anguwar sai gidan Ammi .
cikin ikon Allah sai gasu a ƙafar da horn yayi mai gadi ya buɗe masa get suka shiga , yana parking ɗin motarsa a parking spice Aisha ta buɗe da gudu zata ruga ya cafko ta yace "nafison in dinga ganinki kina tafiya irinta ƴammata my Esha "ya raɗa mata maganar a kunenta , dariya ta kwashe dashi tace "yaya kenan ni ka sakeni inje in cewa "mama na dawo yaushe za'a kaini makaranar ?" ok tom muje suka fito yana riƙe da hanunta ,suna shiga suka sameta ita da Afnan suna kallo ko kallon inda Afnan take Aisha bata yiba ta koma gefen Ammi ta zauna kana tace " mama na dawo , oyoyo ɗiyata Ammi tace "tare da rungumeta Afnan ce tace "brother ina wuni ?"lpy lau ya amsa fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "ya momy ?"tana lpy Afnan tace "cikin jin daɗi ya miƙe ya tafi bedroom ɗinsa dake part ɗin Ammi "Aisha bakiga antinki bane ?" Ammi ta tambayeta "na ganta ina wuni ?"lafiya Afnan tace "cikin harara a fakaice ba tare da Ammi ta gane ba "mama yaushe zan tafi makarantar ?"Aisha ta tambaya da alamar tausayi "Ammi ce tace "ki bari ki ƙara samun sauƙi man "na warke Aisha ta faɗa tana taɓa ɗinkin da aka yi mata da ka gansa kasan faɗarta ce ta yarinta , to naji maza jeki part ɗinku akwai abinci da yarinyar baba tayi miki zama ta dinga kwana a nan akwai ɗakin ƴan aiki , da tsalle Aisha ta tashi kana ta wuce tana murna ,tana zuwa ƙamshi ya bugi hancinta ta zauna a dining ta buɗe abincin kalolin abinci ta gani sunkai kala uku a cikin harda haɗin salad , zaro ido tayi tace " kabeji nayima bankwana wlh koda a mafarki bazan cika ba ta faɗa tana jujuya hannu , Khamis ne ta shigo yana sanye da koriyar shadda tasha aiki bayan yayi sallama Aisha ta amsa ,tace "laaaah kalar shadda ta ko kyau ma bakayi ba tunda kana gasa dani , murmishi Khamis yayi kana yace "akwai salad a gurin idan kina buƙata ya faɗa yana dariya ,wlh bazan ci kai kazo kaci ni banga ma naman bane ,taci gaba da bubuɗewa , kodai ba'a dafa bane ?" ta jefo masa tambayaa "kidai bude zaki gani Khamis ya faɗa yana kallonta ,cikin sa'a ta buɗe wani kwano mai murfi mai kyau taga soyayyun kaji harda yaji a gefe ,Khamis dake kusa da ita sai da yaji alamun haɗiyar yawun ta , mamaki yake shikam da har yanzu ta kasa sabawa kullum ƙwaɗayin cin kaza oh ,Aisha ce ta katse masa tunani da cewa " kallona kake ko ?" a'a Khamis yace "yana dariya "sai da ta cika cikinta damm sanan ta sauko ta dawo kan 2sitter ta zauna tana shafa ciki , kallo Khamis ya kunna a tashar Arewa 24 wani film suka sanya mai ban dariya , tunda Aisha ta fara kallo ko ƙiftawa batayi sai dariya take , Khamis ne ya canja kallon izuwa tashar mbc action turɓune fuska Aisha tayi ba tare da tayi magana ba ta juya baya , bacci ya fara ɗaukarsa juyowar da zatayi taga ankai wa wani mutum naushi itama ta kaiwa Khamis naushi a jinya ,a zabure ya miƙe tare da cewa "innalilahi lafiya kuwa ?" juyawa Aisha tayi tana dariya ciki ciki "Esha meke faruwa ne ?" Khamis ya tambayeta shiru tayi babu amsa dariya ta kuma sawa tace " nifa na matsu inganni boko wlh ko mutum ya sami sake ku nan ku dinga kulle mutane kamar masu lefi nama fita samo kayan wasa na samu wani mahaukacin kare ya biyoni wanan wacce irin jaraba ce ni duk gidan ma ya isheni namafi son in koma gida inga amaryar malam , duk wanan maganar da takeyi Khamis na jinta cikin zuciyarsa yace "tabbas hausawa sunyi gaskiya sukace in daɗi yayiwa mutum yawa sai yace "Allah kasheni shine wanan tabbas yaji haushin wata maganar a ciki amma bai kulata ba....!

Abban islam babu lpy shiyasa kuka jini shiru kuyimin afuwa😥🙏
[01/09, 3:55 pm] Mom Islam Ce 💃: 35 & 36

Kwananta biyar da dawowa taji sauƙi sosai har an kunce ɗinkin da akayi mata anfara maganar tafiya makaranta , yau Ammi ta matsawa Khamis akan sai yaje dubo office yaga abinda suke ciki duk da akwai shugaba a gurin shima zuwansa nada muhimmanci sosai, ransa bai soba ya shirya cikin ƙananun kaya yana fita zai ɗauki mota driver yazo da gudu da katar dashi Khamis yayi kana yace "ɓacemin da gani a hassale "Allah ya huci zuciyarka ranka shi daɗe driver yace "yana ranƙwafa kai yabar gurin "kasancewar tunda ya fito mai gadi ya lura da yanayinsa yasa ya buɗe get da wuri ya dawo ya zauna a guje Khamis ya fice daga gidan kamar mai shirin tashi sama ,tafiya yake zuciyarsa na ƙuna ikon Allah ne kawai ya kaishi ma'aikatar tasu , bama a gurin da aka tanadar

Please Login or Register in order to submit comment