Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hanunki , na dawo gurinki ne mama , murmishi Ammi tayi kana tace " to ƴata kai bedroom ɗin da kika kwana shekaran jiya kinji to Aisha tace " tunda Aisha ta shigo Afnan ke yi mata mugun kallo wanda bashida maraba da na tsaneki , hira suka ci gaba dayi da Ammi maganar Aisha ne ya katse musu tunanin, mama ina ragowar romon nan na jiya , tuntsirewa da dariya Afnan tayi kana tace " yarinya taji gidan masu kuɗi ba irin naku na talakawa ba , kamar ta wurgawa Ammi mashi a ƙirji haka taji saukar kalmomin ya ilahi , Ammi tace " tana kallon Afnan mai yasa bakida lafazi mai daɗii ne Ammi ta tambayi Afnan , cuno baki Afnan tayi alamar jin haushi.
Washe gari tun da asbha yai wanka yana dawowa daga masallaci ya ɗauki abubuwan buƙatarsa ya tafi ɗakin Ammi , yau sarautar ce ta motsa hakan yasa ya zauna a palo ya danna lambar wayarta , idar da sallahar ta kenan ta fito , ganinshi zaune da jaka a hanunsa yasata cewa " wai har ka shirya ne ?" eh Ammi na ya durƙusa ya gaisheta bayan ta amsa ne ya dawo ya zauna dai dai , zama Ammi tayi tace " to bakaci komai ba ?" no Ammi na bana buƙata yau ba lallai bane in karya da wuri yau monday , cewar Khamis adu'ar kariya Ammi tayi masa da kuma faɗan ya kula da aikinsa da mutunta mutane , insha Allah Khamis yace " kana ya miƙe ya bada ƴar wata leda mai ɗauke da dambun nama yace " a ajiywa Aisha ya tafi, bayan ya fita ne Ammi tace " son kana son Aisha sosai fatana Allah yasa lokacin da tasan kanta da zafin kanta ya ƙara sonka so mai tsananj , ta koma ɗaki ta kwanta.
Malam ne zaune a tsakar gida kan tabarma masifa yake ta zubawa san ransa a dole sai mama ta gaya masa lefin da yayi mata ta dena yawan magana , amma tayi shiru itama ɗin tana tskar gidan bata kulashi ba bare ta nuna alamun taji abinda yake faɗa , aure zan ƙara wlh dan naga iskancin yayi yawa acce kanada mata bazaku zauna ku kashe ku rufa ba , in na ƙara auren nasan zaki dawo da biyayyar da da bakyayimin , har yanzu batace komai ba , zuciya ce ta ɗibi malam ya shiga ɗakinsa ya ƙirgo kuɗi dubu ɗari ya fito tsakar gida ya zubesu gaban mama dake ɗinke bakin hijab ɗinta da alura , kinga wanan kuɗin sadaki zankai budurwa gangariya mai jini a jika , yai murmishi ya ɗauki kuɗinsa a karo na uku ma batace dashi komai ba ya fice , cikin sa'a ya sami baban Ummi a waje yana jin redio gaisawa sukayi malam ya nemi guri ya zauna kana yace " aure nakeson yi kuma banason bikin ya wuce wata biyu , da mamaki baban Ummi ya dubesa yace" haba malam ana fama da abinda za'aci a ciki ne ko ana fama da maganar aure dan Allah kabar wanan maganar kaji ?" rurɓune fuska malam yayi kana yace " oho kaima tanan ka biyu wato ni itace ne ? bana buƙatar kulawa ?" to yanzu babu ɗaya ƙanwar biyu duk ƴan uwanta sun zugeta kuma aure da kaji na ambata babu makawa wlh sai nayi budurwa gangariya akwai wata yarinya mai tallan kunu munyi magana da iyayenta mahaifinta dattijon arziƙi ne yace " in kawo dubu hamsin to yanzu kai na wakilta , malam ya ƙirga dubu hamsin ya bawa baban Ummi yace " gashi ka kai zuwa gobe kuma sai in fara maganar akwati muga inda abin zai kaya , babu yadda baban Ummi ya iya dole ya ɗauki kuɗinnan inhar bai ɗauka ba zasu iya samun matsala mai girma , hakam yasa ya ɗauki kuɗin yace " Allah yasa a dace " malam na shirin yi masa kwatancen gidan yace " ai na gane zan tafi zuwa anjima insha Allah sukayi sallama malam ya wuce ya barshi nan a zaune,
Tabbas ya jinjina wanan aure na malam to babu yadda zai yi ana yin la'asar ya tafi gidan su yarinya me kunu suka gana da mahaifinta cikin sa'a aka sami nasara harda sa rana akayi kwana hamsin kowa yayi wa kowa fatan alkairi , baban Ummi na dawowa ya kira malam a waya ya gaya masa inda sukayi farinciki fal zuciyarsa a dole zai bawa mama haushi.
Yaya Zakari ne yai parking ɗin motarsa a gefe ya shigo gidan su tare da sallama , mama na nan zaune a gurin da malam ya barta har yanzu bata tashi ba , amsa sallamar mama tayi tare da tura masa tabarma tace " shinfiɗa ya gidan naku ya mai jego ?" duka muna lafiya yaya yace " yana gyara zama to masha Allah mama tace " tare da sunkuyar da kai ƙasa , na lura kamar kina cikin damuwa mama duk kin rame ko kayan abincin ya ƙare ne ? yaya ya jero wa mama tambaya a'a basu ƙare ba bana cikin damuwa , hmm yaya yace mama dan Allah ki sanar dani yai rau rau da ido kamar ƙaramin yaro , babanku zai ƙara aure mtsw yaya yace " to yayi man sai me ki kwantar da hankalinki mama wlh karkisa damuwa a ranki insha Allah zan share miki kukanki , zan baki jari kici gaba da sana'ar ƙuli ƙulinki , aljihunsa ya taɓa ya ƙirgo kuɗi dubu goma sha biyar ya damƙawa mama , yana damƙa mata hawaye suka zubo a kan kuɗin ,hannu yasa ya shate mata hawayen shima idanunsa sun ciko , malam ne ya shigo da sallama yace " to anzo kenan ?" juyawa yaya yayi ya gaida malam bayan sun gaisa malam yace " ya masu jego lafiya laou yaya yace , malam yace " madallah , tabbas ya yarda da zancen mama tunda yaji malam yau bai haushi da faɗa ba zancen aure ya tabbata shima dan ya kwantar mata da hankali ne yasa shi cewa " karta damu Amma koshi beji daɗin jin zancen ba gaskiya , haka ya miƙe yayi musu sallama ya fita .
Yana fita ya wuce gurin aikinsu da tunanin halin da mamanshi take ciki wani lokacin yaji kamar yai kuka amma babu hali .
Koda Khamis ya isa gurin aiki office ya wuce kasancewar ma'aikatar tasu ce ma 'aikata ce da ake sarrafa robobi mai suna K &K wato Khamis Kabir sunan mahaifinsa kenan , shine babba gaba ɗaya a gurin hakan yasa ba wani aiki na shan wuya zaiyi ba ƴan cicike takaddu ne kawai sai abubuwan da ba'a rasa ba, sosai kamfanin ya birgeshi yana jin yanzu zai kauda komai ya duƙufa gurin kawo gyara da daɗa ƙawata kamfanin yakuma samun karɓuwa ta fannoni masu yawa , yana zaune yana tsaka da tunani yaji ana nock yes yace " come in murɗa handle ɗin ƙofar akayi , tare da shigowa , ƙamshin turarenta ne ya doki hancinsa , bai ɗago kai ba sai da aka sami mintuna sanan ya ɗago ya kai dubansa ga reta bai taɓa ganinta ba wani irin faɗuwa gabansa yayi lura da kyau irin nata kamar balarabiya gata fara doguwa mai dara daran idanuwa gashin girrar nan sun kwanta da gashin idonta suma zara zara bakinta ƙarami ne yayinda hancinta yake kamar biro dogo masha Allah nidai a ganina batada makusa dan in aka titsiye mutum zai ce ya haɗu da balarabiya , to ni meye na wani ƙare mata kallo bayan inada Aishana a gida mtsw yaja tsaki.....!

Dan Allah kar a futarmin da shi pls 👏.
[23/08, 3:31 pm] Mom Islam Ce 💃: 7&8

Have a sit Khamis ya yace " yana mai sunkuyar da kai kan takardun dake gabansa , zama budurwar tayi kana tace " thnks sunana Muhibbat nice sakatariyar ka , ok masha Allah Khamis yace " kana ya kuma maida hankalinsa kan takardun a karo na biyu , to na barka lafiya Muhibbat tace " ɗago kan da zeyi ta jefesa da wani sihirtaccen kallo mai wuyar fassara , tana fita yaja tsaki kana yace " inhar zan dinga haɗuwa da irin wa innan gaskiya da sake babu zancen zaman office gara zaman gida sbda ba matsalar kuɗi yasa na fara aikin ba , duk shi kaɗai yake wanan zancen , zuwa yamma ƙarfe biyar lokacin tashi yayi kowa yana haramar tafiya gida banda Muhibbat , zaune take kan ɗaya daga kujerun da aka tanadar a farandar ma'aikatan domin zaman mutane , buni buni ta duba agogon hanunta lokaci zuwa lokaci , ƙarfe shida dai dai gabanta yai wata mumunar faɗuwa , jin takun tafiyar Khamis wani gwauron nunfashi taja ta sunkuyar da kai alamun damuwa , abinka da mai tausayi ya dawo da baya cikin takunsa na ƙasaita yace " lafiya kowa ya tafi ke kona nan ?" lafiya lou Muhibbat tace " tare da kwaɓe fuska tace " temako nakeso kayimin dan Allah ka dubi girman Allah da ma'aikinsa ka ceci rayuwata taci gaba da maganar idanunta na zubar da hawaye , ina jinki Khamis yace " yana mai neman gurin zama dan jin meke faruwa, na taso cikin gata da nuna kulawa mahaifina da mahaifiyata suna sona so mai tsanani kowa na ƙoƙarin yaga ya faranta min , cikin ikon Allah Allah ya karɓi ran mahaifiyata lokacin inada shekara goma sha biyar a duniya , dady na yaci gaba da nunamin gata babu abinda baya siyamin na buƙatar mace kwatsam suka haɗu da wata bazawara mai suna Sajida , cikin ƙanƙanin lokaci ta ɗaukewa dady na hankali ya dena saurara ta tun kafin ma ayi auransu , anayin aure ta tare a wani katafaren gida da dady na ya gida mai tsadar gaske , har dani aka koma gidan kullum da safe sai tayi min duka ga ƴan aiki a gidan sai ta dinga sanya ni wahala nice wankin ta da wanke wanke dady na baya magana sam wani lokacin ma cewa " yakeyi ya mance dani , inyi kuka har in gaji , godiyar da nayiwa Allah shine kuɗin makaranta ta tundaga jami'a har sama ya gama biya amma badan haka ba karatun ma bazan samu ba , samun sauƙi na yanzu shine gurin aikinnan da nake zuwa , yanzu gashi nakai munzalin aure burin kowacce mace ta ganta a ɗakin mijinta to ni ko samarin sunzo matar dady na wato Sajida ita ke koremin su tace " wai anyimin baiko za suyi asarar kuɗinsu ne kawai , su kuma in sukaji haka sai su tafi , nisawa tayi kana taci gaba da cewa " ina zaune da daɗi babu daɗi wata rana kakata wato mahaifiyar momy na tazo gidan ta ganni ina kuka da girmana ganin jikina duk tabon duka yasata tattara min kayana muka bar gidan ko uffan Sajida batace ba shine na koma gidan kakata da zama mahaifina ma baya tambayata bare ya tambayi halin da nake ciki , da kuɗin aiki na nake komai na rayuwa .
Shirun da Khamis yaji tayi ne ya kalleta yaga ta share hawaye ta kifa kanta cikin matsin ƙafafunta tana kuka , kiyi haƙuri dama kowane ɗan Adam da tashi jarabtar ki daure ki ƙara yiwa Allah godiya to ni yanzu wane temako zanyi miki ?" ƙara fashewa da kuka tayi tace " ka aureni nasan bakada mata , ta share hawayeta , kana tace " tun lokacin da nakeda damar samari aka kore min su yanzu duk kyawun da Allah ya bani babu mai zuwa ƙofar gidan mu .
Hmmm Khamis yace " dan lamarin babba ne waye yace " miki banida aure ?" to aurena ko s weeks beyi ba , zaro ido tayi kana tace " nidai ina jiranka ka tausayawa rayuwata dan Allah bakada ƙanwa ne ? in itace a irin halin da nake ciki dole kayi yunƙurin samo mata mafita , mu talakawa ne , lokaci ɗaya tausayinta ya kamasa sosai tausawa rayuwar da ta shiga , Allah ya baki mafita , ƙirgo dubu hamsin yayi a aljihunsa ya miƙa mata kana ya nufi mota , tasowa tayi kamar zatace " ya temaka mata , taga yaja motar da uban gudu ya tafi , lokacin ƙarfe shida da arba'in anata kiraye kirayen sallahar magrib bakin titi ta nufa ta sami abin hawa ta wuce gida .
Yana parking ya fito da sauri bai jira an buɗe masa murfin mota ba , ya buɗe ya fito da sauri kai tsaye part ɗin Ammi yazo samun Aisha yayi zaune a palo ita kaɗai da hawaye shaɓe shaɓe a fuskarta , tana ganinsa ta rugo da gudu tana cewa " kyakkyawa gobe dani zaka tafi ko ? eh kawai yace " mata ya riƙe mata hannu suka nufi sashin Ammi bedroom suka shiga batanan dan haka suka dawo kitchen aiki suka ganta tanayi itada baba mai aiki , sannu Khamis yayi musu tare da cewa " my Ammi na gaji sosai , ayya Ammi tace " maza kayi wanka ga special food ɗinka na jiranka oya , tom Ammi na Khamis ya faɗa kana ya wuce part ɗinsu.
Da gudu Aisha ta bishi ta ɗafal fale masa dole ya ɗauketa yana dariya , suna isa ya sauketa kana ya nufi toilet dan yin alwalah , yana gama alwalar ya je masallaci yana fitowa yadawo yai wanka ya canza kaya , boyel yasa baƙi da farar hula da farin takalmi ,kyakkyawa kasan me ?" Aisha ta tambayeshi tana daga zaune kan gadonsa , sai kin faɗa my Esha Khamis ya faɗa yana murmishi , inkaje gurin budurwarka kace ta bani tsaraba kaji , ɓata rai yayi kana yace " ke a rayuwarki bakida damuwa banda ta tsaraba ?" iye , to naga kayi kyau ne haka fa yayanmu yake kwaliya yake tafiya hira gurin anty fiddausi , to ni ba shi bane gurinki zanzo hira , dariya tasa tace " ƴar ƙarama dani ta rufe fuska , tana ganin zai fita tace " nima zan bika , no part ɗin Ammi zani ki zauna yanzu zan dawo naga ma kamar bakiyi sallah ba , zan da asbha sai in haɗasu hakama jiya nayi , zaro ido Khamis yayi yace " to Allah ya kyauta amma dole in nemi bulala kodan marar yin sallah, ai mama tace " ba'a dukan matan aure inka dakeni sai na rama Aisha ta faɗa ko a jikinta , ring wayarsa ta fara dubawa yai yaga Ammi ce da sauri ya fice Aisha ta ruga da gudu tasha gabansa tare da cewa " sai na rigaka zuwa wlh ta ƙara da gudu , tana shiga taci karo da Afnan taci kwaliya leshi tasa mai tsadar gaske milk color mai ratsin jan zane gyalenta siriri ja da takalminta mai tsini shima ja , fuskarta na ɗauke da glass baƙi wanda ya mamaye ilahirin fuskar tata , ke gurin wa kikazo Afnan ta jefo ma Aisha tambaya tana harararta hakan yayi dai dai da zuwan Khamis yace " gurinki tazo tunda gidan naki ne ke kaɗai , shiru tayi kamar ruwa ya cinyeta ta koma gurin Ammi da ta shiga bedroom ɗinta ta cire kaya zata shiga wanka , turo ƙofar tayi tare da sallama , har kin shirya ne ?" Ammi ta tambayeta eh na shirya Ammi one week zanyi Ammi , to ki gaida momyn naki ga wanan ki kai mata , haɗin turaruka ne Ammi ta bawa momyn Afnan masu kama jiki sosai ga tsadar gaske , ficewa Afnan ɗin tayi ba tare da ta kalli su Khamis dake dining suna cin abinci ba , kira Ammi ta ƙwalawa Afnan , Afnan na zuwa Ammi tace " karki tari mashin a titi kiyiwa haliru magana ya kaiki tom Afnan tace " idonta na kan Khamis ko ƙiftawa batayi , ta fice Ammi dake sanye da hijab bata shiga wankan ba ta dubi Khamis tace " son ya kamata zuwa gobe akai yarinyar nan gidansu taga iyayenta fa , tom Khamis yace " Allah ya kaimu Ammi ta tafi ta barsu a gurin tsalle Aisha ta doka tace " waya ganni a cinyar mamanmu kai tasa dariya zani inga Ummi tanata surutunta shikam hankalinsa na kan soyayyar taliyar da Amminsa tayi masa, da gudu Aisha ta fice ta nufi part ɗinsu gurin kayanta tayi ta fara haɗawa a fili tana cewa " idan naje wata ɗaya zanyi in dawo .....!

😥ina fama da ciwon kai ina buƙatar adu'arku fans
[23/08, 8:02 pm] Mom Islam Ce 💃: 9 &10

yana kammala ci ya wuce masallaci sai da yayi shafa'i da wutiri kana ya dawo part ɗinsu , samunta yayi ta cika gadonta da kaya waro ido yayi yace " mezan gani wanan kayan fa ?" duk na tafiya gida ne Aisha ta faɗa tana ci gaba da haɗo kayan , sai da ta cika akwati da kaya tam har tana hawa kansa dan ya rufu tana zuge zip ɗin ta fito yau bakin yaki rufuwa , ƙarfe goma na dare bacci ne a idon sa sosai amma tsabar murnar gida da takeyi yasa taƙi koda rintsawa , sai yayi bacci sai tazo tana yi masa waƙa a kunne , kamar zai rafza ihu haka yake jinsa sai wajen ƙarfe ɗaya ya samu bacci ya ɗauketa gashi babu halin duka.
Washe gari tun asbha Aisha ta tashi ta shiga toilet ta ji jiƙa wankanta ta fito ta mulka mai ɗakinta ta nufa domin sa hoda ,tana sauko da akawatin kayan make up ta gigice dan ma mama ta rage wasu kayan , kwalliya ta fara tana yi tana kallon mudubi.
Jan baki ta ɗauko ja 24 hours ta damɓara tana ta gogawa har sai da saman bakinta ya samu idanunnan sunsha jan jambaki ga kwali data sashi kamar mai siyarwa , fitowa tayi sanye da ɗinkin doguwar riga na shadda da farin gyale duk da gogawa gyalen janbaki , cin karo sukayi da Khamis daya dawo daga masallaci innalilahi yace " bai kai ga ƙarasawa ba yaga ta wangale masa fararen haƙoranta tace " kyakkyawa nayi kyau kuwa ? dama akwai kayan kwalliya a wanan ɗakin shine kaƙi gayamin ko ?".
toshe bakinsa yayi kana yace " to ai kinfi kyau inbabu kwaliya , cuno bakinta tayi alamar fushi hakan ma ya kuma basa dariya .
" me ya sami gyalen ki naga duk jan abu ?" Khamis ya tambayeta yana dariya , ban sani ba ta bashi amsa tana mai ci gaba da tafiya ta fice daga sashen nasu ta nufi na Ammi , tana cikin tafiya sukaci karo da mai gadi zaro ido mai gadi yayi yana jinjina kai ,
" yada kallo ido ba kwalli Aisha tace " masa tana murguɗa baki ,bai dai kulata ba yasan halin ogan nasu ya wuce ya barta tayi part ɗin Ammi , Ammi dake zaune da ƙaramin cup a hanunta tana ganin Aisha ta zaro ido tare da cewa" mezan gani ?" ƴata kwalliyar ce haka , eh mama kinga kyakkyawa sai dariya yake yimin wlh kuma munyi faɗa dashi ma , " kiyi haƙuri to muje bedroom in wanke miki fuska inyi miki wata kwaliyar , maƙe kafaɗa Aisha tayi tace " ko a gida haka muke kwaliyar mu kuma munfi ƴan matan anguwarmu iya kwalliya nida Ummi.
" wacece Ummi ?" Ammi ta tambayeta , ƙawata ce mama dan Allah in munje ki taho da ita zamu dinga tayaki aiki , Aisha rigima Ammi tace " a cikin zuciyarta, zodai muyi mu shirya kar son yazo yana jiran mu Ammi tace " tare da janyo hanun Aisha.
Wanke mata kwaliyar tayi ta goge mata fuskar kana ta ɗauko mai da powder ta shafa mata ta kawo man baki ta goga mata da kwali ba ƙaramin kyau Aisha tayi ba kasancewarta ƴar fara mai manyan idanu "to jeki palo ki jirani nima barin shirya , tom Aisha tace " tana tafe tana rangwaɗa kamar zata faɗi ƙasa inka ganta abin sai ya baka dariya duba da yadda take karai raya ita a dole ƴan mata ,
Cikin shigarsa ta alfarma ya shigo palon Ammi, Ausha ya tarar a zaune ta ɗora ƙara ɗaya kan ɗaya tana zaro ido , gimbiya my Esha zo inyi miki photo Khamis ya faɗa yana murmishi , abin nema ya samu wai matar bakanike ta haifi sifana ,Aisha ta miƙe tare da tahowa tana yanga , Khamis bai san lokacin da ya tuntsure da dariya ba , cikin jin haushi Aisha tace " nama fasa ɗaukar hoton kalan in na ɗauka ka nunawa budurwarka kuyi ta yimin dariya , ta haɗe rai kamar mai shirin kuka " am sorry my Esha na tuba Khamis ya faɗa yana ɓata fuska alamar damuwa , fitowar Ammi ne yasa Khamis kama kanshi tace " kowa ya shirya ko ?" eh su Khamis da Aisha sukace , ficewa sukayi baba mai aiki tayi musu Allah ya kiyaye suka shiga mota , sai anguwar su Aisha Ammi ce tace " driver ya kaisu wata plaza dake gaban anguwarsu zasuyi siyayya ,babu musu ya kaisu yai parking a inda motoci suke fakawa , suka fito dukkan su hanun Aisha a na Khamis kai tsaye katafaren shagon suka shiga mai ɗauke da kayyayaki na amfani kayan abinci Ammi ta lodar musu da su maggi da kayan ƙamshi katan katan harda buhun shinkafa ƴar gwafnati lol.
ma'ai katan gurinne suka dinga loda musu a mota ana gamawa Khamis yaje gurin biyan kuɗi ya biya suka tafi.
Drivern yayi gudu cikin ikon Allah sai gasu a anguwar suna zuwa Aisha ta hau dariya tana yi musu shirme , ana parking Ammi na fitowa itama ta buɗe ta bugo ƙofar da gudu ta shige gida , mama da ta fito daga bayi har zata ruga sai taga Aisha ta faɗaɗa fara'arta tace " oh kekam bakya girma ko kaɗan keda wa kukazo ? nida maman kyakkyawa zaro ido mama tayi tace " waye kuma kyakkyawa , kodai mijin naki ne ?"eh Aisha tace tare da hayewa bishiyar mangoro , faɗa mama ta kama yi mata akan ta sako amma ina tayi nisa ko saurarar mama batayi ba , sallama su Ammi sukayi itada Khamis , cikin fara'a da karamawa mama ta karɓesu tare da yi musu marhabum , ku shigo mama tace " tana shirin shiga ɗakinta da ta gyareshi tsaf babu datti tabarma ta shimfiɗa musu akan sabuwar ledae ɗakin suka zauna tare da gaisawa , bayan sun gaisa ne Ammi take tambayar Aisha , ƙwala mata kira mama tayi tace " bazaki zoba ana kiranki , a ina take ne ?" Khamis ya tambaya " daga zuwa ta haye bishiyar mangoro wlh mama ta faɗa tana nuni da hannu , oh Khamis yace " Aisha rigima ya miƙe ya fita , tsayawa yayi a dai dai saitin bishiyar yace " haba mana my Esha pls ki sauƙo Ammi na kira.
"Taɓɓ Aisha tace " bazan sauƙo ba kasan kewar bishiyarnan da nayi kuwa ?" to a ita nake wuni kullum garama ka tafi , inkuma zakayi min tari to dan naga akwai wanda suka bra wata dariya ce ta tahowa Khamis banda so ba kamar Aisha ta dinga yi masa surkulle yana saurarar ta shima kansa ya fara mamakin irin son da yake yi mata har baya ganin yarintarta ko wautar ta, naji zanyi miki ai zamukai yamma a nan ki sauko dan Allah , to Aisha tace " ta sauko hanunta ɗauke da wani jan mangoro tace " wanan mama zan kaiwa tasha tasha taji irin mangoron gidan mu , hanunta ya kama suka shiga ɗakin mama , suna shiga Ammi ta kamo ta tace " baki fa gaida mamanki ba kika haye bishiya murmishi mama tayi daɗi ya kamata taga Aisha harda kumatu ga wata ƙiba da tayi.
" yiwa driver mgna ya shigo da kayan nan son , ok Khamis yace " tare da ɗaga wayarsa ya dannawa driver kira , driver dake zaune a mota yana ganin kira ya fito tare da amsawa , ka shigo da kaya inji Ammi to

Please Login or Register in order to submit comment