Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

" ki bata rabi , cuno baki anty Fiddausi tayi kana tace " ko sisi bazan bata ba kamaji da kyau.
Ina wasa dake ne FIDDAUSI cikin kakkausar murya yake maganar , tun wuri kibata nace miki , anty Fiddausi na bubuga ƙafa ta shiga cikin ɗaki ta fiddao dubu biyu ta miƙawa kaka kafin ya kai hanun kaka ta hango kuɗin dubu biyu ne ihu tasa tare da sanya hanunta a kai ta rushe da kuka , a razane Ummi ta fito jin kuka a gidan batare da neman izini ba ta shigo ɗakin anty Fiddausi samun kaka tayi a durƙushe da hawaye shaɓe shaɓe a fuskarta , nuna kaka tayi kana ta ƙyal ƙyale da dariya tace " Allah shi ƙara akan kuɗi kina kuka , dariya yaya Zakari ya ƙarayi a karo na biyu yace " kin ɗauko kuɗin ko sai na je na ɗauko nabata duka ?"sanin zai iya aikata hakan yasa ta shigewa da gudu ta kwashe kuɗin ta ƙaro dubu ɗaya akan dubu biyun da taba kaka ta miƙa mata ,share hawaye kaka tayi kamar ƙaramar yarinya tace " ai nasan tunda akaba kura ajiyar nama sai taci amana , gwalo anty Fiddausi tayi mata ta nemi guri ta zauna , miƙewa kaka tayi kana ta fice waje ta nemi guri ta zauna kusa da tsintsiyarta ta fara lisaafo abubuwan da zata siya da dubu uku , sai da ta lissafa inda kuɗin zai ƙare kaf ciki kuwa harda tsire , kana taci gaba da gyaran tsintsiya .
Fitowa Ummi tayi ta kalli kaka tace " su kaka anji jiki wlh harara kaka ta watsa mata tana murguɗa baki , dariya Ummi tasa tace " wai dama tsofaffi suna murguɗa baki kai abin dariya , wurga mata tsintsiya kaka tayi, Ummi ta shige ɗakinsu da gudu .
Suna mota Aisha na kuka wai sai dai Khamis ya koma ya taho da Ummi duk da haƙurin da yake bata taƙi saurararr sa parking ɗin motar yayi a gefen titi ya janyota jikinsa yana aikin rarrashi , jijigata yake kamar wata baby " am sorry my happiness pls kiyi haƙuri insha Allah za'a kawo Ummi zansa driver ya je ya ɗauko ta , yana ta shafa mata kai yana bata haƙuri da ƙyar ta haƙura sai da yace " zai sa ayi mata farfesu ta haƙura ya tada mota suka ɗauki hanya , suna isowa yayi parking a parking spice , drivern shi da ya taso jin shigowarsu yazo yaɗe masa mota kana ya buɗe na Aisha fitowa tayi ta ruga part ɗin Ammi da gudu tana dariya idanunta da alamun hawaye , janyota Ammi tayi tace " zauna kun dawo lafiya ?" lafiya lau Aisha tace " tana wasa da hijab ɗinta , naga kamar kinyi kuka Ammi ta watso mata tambaya " ba kyakkyawa bane ba yaƙi ɗauko Ummi kuma tana can tana kuka , ta karashe maganar tana shirin kuka , sorry Ammi tace " mata karki damu zansa a ɗauko ta ai sai an tambayi iyayenta , ko ?" girgiza kai Aisha tayi alamar eh.
Ammi ce tace " wa Aisha gobe mai yimiki lesson zai zo ku fara kafin a kaiki school , faɗaɗa fara'arta Aisha tayi tana tsalle akan kujera tace " to mama .
Su Ammi na fita malam ya leƙo ɗakin mama ganin kayan abinci lodi lodi yace" aiko sai dai a raba dan bazan yarda ba an jido kayan an kawo ɗakinki kece mai gidan ?"
Kai malam abinda kake yimin ya fara isata wlh dan kaga ina ƙyaleka kake yimin kowane abu to sam bazan lamunta ba dan zakayi aure shine zaka cigaba da wulaƙanta ni , mama tana huci ta faɗa cikin rashin jin tsoro , taɓɓ lallai wuyanki ya isa yanka wato ni kike gayawa baƙaƙen maganganu irin wanan ko ?" malam yaci gaba da cewa " aure kam babu fashi ko baƙin kishi ne ya taso to ya kwanta aure sai nayi .
Komawa ɗaki mama tayi tana mai jin ɗaci a zuciyarta , da takalmi malam ya shigo kana yace " a raba biyu a bani nawa in haka ne ma ai nine na yarda da maganar auran sbda ke baso kike ba , dama nasan zamu sami alkairi Allah sarki Aisha ɗiyar kirki malam ya faɗa yana share hawaye mama da dariya tazo mata tace " daga baya kenan wai anyi sadaka da bazawara , janyo kayan mama tayi ta fara rabawa kamar inda malam ya buƙata ta cire nata ta tura masa nasa kwasa yayi ya kaisu ɗakinsa kana ya fice.
Afnan na isa gidansu ta tarar da dadynta yayi tafiya zuwa india gurin aikinsa kasancewarsa baban likita , momynta ta samu zaune a palo tana kallo bayan tayi sallama momyn ta amsa ta faɗa jikinta tare da sakin kuka , cikin tsoro momyn nata tace " lafiya kuwa daughter maiya faru ?" ta jero mata tambayoyi , share hawayenta tayi kana tace " momy ya kusa kasheni duka yayi min har sai da aka kira doctor , kan uba ita yayan tana kallonsa ?" momyn ta jefo mata tambaya , to wlh bazata saɓu ba kema can da shegen son dangi gashinan kina matashiyar budurwa ya bar miki tabo a fiska dallah matsa ki bani guri , cikin tsanantar kuka Afnan ta ƙara riƙe momynta tana cewa " akan na daki wanan matsiyaciyar yarinyar nan ne fa shine yamin duka Ammi ce ta ƙwaceni wahattt momyn Afnan tace " kema anyi banza uban me kikeyi da baki rafka masa wani abun ba , buɗe baki Afnan tayi kana tace " ina sonsa fa momy inya ji ciwo fa ? dan ubanki in yaji ciwo kece kikaji banza wawuya kin damu dasu daga shi har uwar tashi amma basu damu dake ba , share hawayen fuskarta Afnan tayi kana tace " Ammi akwai milk a fridge ?" eh mazai hanashi samuwa , momyn ce ta ƙwalawa ƴar aikinsu mai suna Hanne kira , da sauri ta shigo momyn tace "kawowa daughter milk, tom Hajiya Hanne tace " tare da tashi daga durƙuson da tayi taje ɗauko milk, yanzu dai me kika fahimta a zaman yaronnan da figigiyar yarinyar nan ?" momyn Afnan ta tambayi Afnan , Afnan ce tace " am gaskiya na lura zata basa wuya Ammi kasancewar a haka kamar yanada buƙatar mace " amma soyayyar wanan shegiyar ta rufe masa ido wlh ta yarfe hannu , turrr wlh momyn Afnan ta faɗa tare da miƙewa tana zagaye palo , ta ƙara da cewa " shin yaya bazata lamunci haɗa auran zumunci bane ko yaya ?" tunda nayi mata magana tun kafin ya rakito wanan ƴar talakawan nake magana amma tayi yimin banza , ni banda tulin dukiya da ubansa ya mallaka wlh babu abinda zai sa in matsa da inason ya aureki , Afnan da ke shan milk ɗin da aka kawo mata yanzu tace " nidai gaskiya momy soyayya nake yimasa ta tsakani da Allah kuma ina fatan ya zamo min abokin rayuwa , ta ƙarashe maganar tana rufe fuska , banza wawuya momyn Afnan tace " tana hararrar Afnan , kenan ko kunyi auran bazaki yi mana hanyar tara dukiya ba ko ?" momyn ta faɗa tana kallon Afnan a kai kaice , no momy ba cutarsa zanyi ba , tsinka mata mari momyn tayi ta gurin da Khamis ya daketa , jin zafin dukan momyn nata yasa ta ganin wasu taurari na yawo , sai da jinta ya ɗauke na tsawon daƙiƙu kana ta dawo dai dai bata sami damar kuka ba sai da ta dawo normal ta fashe da kuka tana cewa " wlh sai na aureshi , momyn nata dake shirin ƙara mata wani tace " ki aureshin mu gani inhar bazaki cika min burina ba wlh keda auran Khamis kunyi hanun riga , kuka ta kuma fashewa dashi tana bawa momyn nata haƙuri , tureta tayi ta shige bedroom ɗinta tare da yiwa ƙofar key ta kwnta tana nazarin maganar Afnan na cewa " soyayyyar tskani da Allah za suyi , wato duk huɗubar da nake yiwa yarinyar nan duk a banza to inhar bazata nemo mana kuɗi ba to wlh babh ita babu auranshi ko da a mafarki , momyn ta faɗa tana cigaba da surutu kamar mai shirin yin hauka , bubuga ƙofar Afnan take amma momyn taƙi buɗewa a dole tayi fushi da ita tunda batason abinda take so , kuka take sosai mai ban tausayi ko a jikin momyn cikin ɗaga murya tace " ki koma inda kika fito , no momy karkiyimin haka dan Allah Afnan ta faɗa tana zubarda hawaye , palo ta dawo ta zauna jin zaman ya gundureta ya sata kwanciya ta lumshe ido , ƴar aikin gidan Hanne dake kaiwa da komowa ta ce " wa Afnan Hajiya da abinda za'a kawo ne ?" Afnan na huci ta wanke Hanne da mari tace " ubanki za'a kawo ko nace miki yunwa nakeji banza wawuya wuce ki bani guri ko in takaki , sum sum Hanne ta wuce tana tafiya tana waige ta shige kitchen tana gyare gyare tana kuka, a haka bacci ya ɗauki Afnan tana daga kwance tayi mafarki ga momynta nan da wuka tazo zata yankata , wani mahaukacin ihu ta darara ta miƙe da gudu zata fice , a take momyn ta fito cikin tsoro tace " daughter menene ?" babu komai Afnan tace " kana taci gaba da baccinta...!
[25/08, 8:47 pm] Mom Islam Ce 💃: 17 & 18

Itama momyn koma ɗaki tayi abinka da uwa da ɗa , ƴar aiki kam tunda taji mari bata kuma dawowa ba .
Khamis na shigowa ya sami Ammi da Aisha a zaune suna ta hira da fara'a ya zauna yace " Ammi na yunwa na keji , miƙewa Ammi tayi tace " aikin yau yayimin yawa baba mai aiki ta tafi gida , on Khamis yace " Ai nasa ta taho min da ƴar aiki saboda Aisha , juyowa Ammi tayi tace " wace ƴar aiki kuma ?" mai kula da ita Khamis yace " yana kallon yanayin fuskar Ammi da yaga sauyi tashi ɗaya , Ammina akwai wata matsalar ne ? ya jefo mata tambaya , Ammi na yin hanyar kitchen tace " babu komai , ta shige abin ya ɗaure masa kai amma bai fahimci komai ba , ɗauke da abinci a hanunta Ammi ta fito ta ajiyesu a dining ta koma ta ɗauko jug da ta haɗa kunun aya mai sanyi , zama Khamis yayi ya bude flaks ɗin abincin wani ƙamshi ne yayi masa sallama shinkafa ce mai miya taji kifi da naman kaza ga salad da akayi masa haɗi da bama coslw yaji yankaken ƙwai ga dankalin turawa da faffae Aisha na hangowa tayi gurin da gudu ta zauna a tata kujerar tace " kabeji za'a zubo mata , babu musu Khamis ya zuba mata kaɗan , ɓata rai tayi tace " a ƙara mata no Khamis yace " yana ɓata ciki inhar bai karɓeki ba , nidai ka samin Aisha tace "tana bubuga ƙafa , Ammi ce tace " zuba mata mana dan cikinka na lalacewa sai akace na kowa ma haka zaiyi ? yau da gudawa Aisha tace " tana buga tsalle , basu kulata ba amma Khamis ya kusa dawo da abincin bakinsa daurewa yayi , kyakkyawa zubomin romo harda kazar , Aisha ta faɗa tana shafa ciki , bazan zubo romon ba an faɗa miki kayan ɓata ciki ne nima yau cikin nawa sai ta Allah Khamis ya faɗa yana ci gaba da cin abincinsa , Ammi da ta gaji da damuwarsu tace " son wai maiyasa kakeson bawa yarinyar nan kuka ne ?" sa mata duk abinda tace " tana buƙata , sawa ya shiga yi a zuciyarsa ko yana tayata da adu'a , yawaa Aisha tace " ta hau tafi tana wurga ƙafafuwa ci take babu kama hanun yaro ta maida hankali inta tsoma ƙashin a cikin romon sai ta lashe haka ta dingayi tana ƙazantar ta miƙewa Ammi tayi dan ta gaji da surutu da kuma ganin ƙazanta tace "ni zani in kwanta , to Khamis yace " yana ganin Ammi ta shige yace " wlh ki dena shan romon nan haka , ina ko saurararsa Aisha batayi ba illa fari da ido da take yi masa tana gwalo , shima tashin yayi ya koma part ɗinsu ya kwanta kan kujera yana tuno maganganun Muhibbat .
Aisha na zuwa ta zauna kusa dashi tace " zan faɗa maka wani abu amma sirri ne kuma amanatul amana alahira azaba inka faɗawa wani wuta bal bal , zaro ido Khamis yayi kana yace " taɓɓ bar abinki wanan fitina haka ya faɗa yana jinjina kai , kayi shiru kaji in faɗa maka, ɗazu naga yaya da Anty yana yi mata kalar abinda kake yimin kuma nace anjima zan tambayi mama , ido Khamis ya firddo waje yace " wace maman ?" maman gidannan Aisha tace " tana dariya , haɗe hannayensa biyu yayi yace " dan girman Allah karki faɗa mata zatayi min faɗa , kai kai kai ashe babu kyau ma ko ?" akwai kyau man amma ai mu munyi yara da yawa shiyasa Ammi zata yimin faɗa , to bazan faɗa ba amma sai kayimin alƙawari , ina jinki Khamis yace " rufe ido Aisha tayi kana tace " danbun naman nan da ka siyomin to shi zaka ƙara siyomin , kawo kuɗi Khamis ya faɗa yana miƙo hannu , a firgice ace " ya akayi kasan na boye kuɗi kai nifa mancewa nayi , Khamis da idonsa ke rufe sai yanzu ya gane maganarta , yace " dama baki basu kuɗin ba ?" da kuma ban basu bafa , oho ga wanan dai Aisha ra kunto bakin zaninta ta miƙa masa kuɗin daya bata , karɓa yayi ya ajjjiyesu a gefe , my Esha zo kiyimin tausa pls da sauri tazo ta haye kansa tana ta tsalle yana cewa " ouch tana dariya jin yayi shiru ya sata sauka tare da kiran sunansa kyakkyawa , bacci ya ɗaukesa hakan yasa ta koma kitchen ta ɗibo cin cin da ruwan sanyi swan tana ci tana gama ci taji cikinta ya murɗa da gudu tayi toilet tana gamawa ta tsuguna tana maida nunfashi , jin wani kashin ya taho yasa ta riƙe ciki dama bata fita a toilet ɗin ba taji gaba da tsugawa tana nunfarfashi , tana gamawa tayi tsarki ta fito bedroom ɗin Khamis ta shiga ta faɗa gado tare da kifa cikinta hanunta akan cikin ta shiga zaro ido , ba shiri wani kashin ya biyo baya ta miƙe da gudu ta faɗa toilet tana yinshi gashi irin mai ƙarar nan ne , tana tsaka da kashi taga Khamis ya faɗo bayi da gudu yace " kekuma me kikeyi anan ne Esha , gudawa ta bashi amsa tana nishi , inkin gama sauƙo ki bani guri walh yanzu na fara Aisha na gudun kar ta sauka Khamis ya hau inkashin ya kuma matsarta ina zataje tayi shiyasa taƙi tashi , sai matse ƙafafu yake ya rasa inda zeyi da yaji alamun kashin ya kusa fitowa da gudu ya shiga bedroom ɗin Aisha ya fara sakewa yana nishi harda ruƙe bango , yana fitowa ya nemi bakin gado ya zauna tare da zuba tagumi , zai tashi ya fito wani kashi ya kuma tahowa da sauri ya koma toilet yana tafiya a sunkuye , Aisha na can tana aikin kashi shima gashi yana nashi aikin kashin , bayan ya fito ne yaji cikin nasa ya ɗan lafa masa fitowa yayi ya dawo palo ya ƙara gudun AC da fanka nanda nan palon ya ɗauki sanyi , laƙwam yayi a kujera kamar wanda yayi ciwon sati sai ido zuru zuru , leƙowa Aisha tayi tace " wai naka kashin ya tsaya ne ?" gimtse fuska Khamis yayi kana yace " waye ya gaya miki kashi nake ?" oho gani nayi kuma wlh ina bayinka naji ƙarar kashinka , bai kulata ba yace " ke naki ya tsaya ne ?" a'a har yanzu Aisha tace " tana yarfe hannu jiri na ɗibarta , to Allah ya sawwaƙe zo ki bani wayata in kira family doctor , bazan iya ƙarasowa ba Aisha ta faɗa tana ɗingisa ƙafa , shima jikinsa babu ƙarfi ya miƙe ya ɗauko wayar dake kan kujerar dake nesa dashi ya danna lambar doctor , kazo akwai mara lafiya Khamis ya faɗa bayan sun gaisa to doctor yace " kana yace " gashinan zuwa , ajiye wayar Khamis yayi ya gyara kwanciyarsa jin cikin nasa yake babh komai kamar wanda baici abinci ba , bubuga ƙofar da akeyi ne yasa Khamis miƙewa doctor ne shida Ammi suka shigo , Ammi ce tace" doctor yazo yace " min wai ka kirashi shine nace to barinzo inga ko lafiya , Aisha dake tsugunne tama kasa tsayuwa tace " mama gudawa mukeyi wlh , zaro ido Ammi tayi kana tace " dukkan ku ? eh Aisha tace " tana riƙe da ciki , kiranta doctor yayi ganin ta kasa tafiya yace " bari yazo ya ɗauketa , a hassale Khamis ya taso duk da jikinsa babu ƙarfi bai hanashi zuwa gurin Aisha ya ɗaukota ba , doctor dai yaga ikon Allah yarinyar da batafi shekara sha biyu ba ake yiwa haka duk cikin zuciyarsa yake magana , Ammi dai sai ido dan yanzu ko kunyarta ma bayaji .
doctor ne yace " sai an ƙara mata ruwa amma zai je ya dawo , kwanciya Aisha tayi tana juyi kasancewar cikinta dake murɗa mata, sannu Ammi tayi mata kana ta zauna kusa da ita take tambayarta ko tana buƙatar wani abun , a'a tace " mamaki ne ya kama Ammi sbda badai ka tambayi Aisha tace " a'a ba ko bazata ci ba tace " eh haka takeyi , lallai manyan mata babu lafiya Ammi ta faɗa a fili .
Khamis da idanunsa suke rufe yana shirin gyara kwanciya Ammi tace " amma gobe zaka office ko ?" Allah ya kaimu Khamis yace " badan yanajin zai je ɗin ba...!
[26/08, 7:41 pm] Mom Islam Ce 💃: 19 & 20

Bayan an gama yi mata ƙarin ruwa har wanda zai koya mata lesson ya zo Ammi tace "masa bata da lafiya haka ya koma.
Magani aka haɗawa Khamis kasancewar basa shiri da allura.
Washe gari jikin Aisha yayi sauƙi sai dai ƙarfi da babu sosai ,
Shima Khamis ɗin jinkin nasa alhmdulilh ,
Amma bai ko leƙa part ɗin Ammi har ƙarfe takwas na safiya , fitowa Ammi tayi kana ta shiga part ɗin nasu Aisha na cikin ɗaki Khamis ne zaune a palo da waya a hanunsa , shigowar Ammj yasa shi ajiye wayar ya maida hankali gurin jin abinda ya kawota , durƙusawaKhamis yayi ya gaida Ammi ya koma ya zauna .
Bayan Ammi ta amsa tace "son yaushe zaka fita ne naga ko shiri bakayi ba , haɗe fuska Khamis yayi yace "Ammi dan Allah kibar maganar zuwa aikinnan babu abinda muka rasa na rayuwa dan haka ni nadena zuwa ,
Yaro yaro ne Ammi ta faɗa tana ƙara kallon Khamis taci gaba da cewa "to kasani shi nema yanada amfani yanzu inhar ka rasa dukiyar me kake tunani baka taɓa wahalar da kanka ba kullum a cikin daɗi kake so ka kiyayye nidai inason komawarka gurin aiki , tom Ammi Khamis ya faɗa a baki amma cikin zuciyarsa sam baya buƙatar sake zuwa , miƙewa Ammi tayi kana tace " ya mai jikin ?"
" da sauƙi Khamis yaba Ammi amsa kana ta fice .
Bedroom ɗinsa ya shiga ya sauya kaya kasancewae yayi wanka ya feshe jikinsa da turare masu sanyin ƙamshi ya fito,
Har yanzu Aisha nata sharar bacci sbda magani da tasha.
direct part ɗin Ammi ya shiga a palo ya sameta tana goga kwakwa oh my Ammi baba ta barki ke kaɗai kinata wahala , murmishi Ammi tayi kana tace " wahala kuma ai bashida wuya inason dafa shinkafa ne anjima shiyasa nake aikin da wuri , amma zansa a cigiya min ƴan aiki gaskiya mutum ɗaya tayi kaɗan Ammi ta faɗa tana dariya , ywwa mai Ammi zan wuce gurin aiki ammafa yunwa nakeji , to ai na gama shayi maza kaje dining ka fara dashi kafin in sauke indomie ,
"No Khamis yace "zan wuce kawai yau ko driver bai buƙaci ya rakasa ba haka ya tafi zuciyarsa cikin ƙunci yana isa bakin get ɗin tangamemen ma'aikatar mutane suka fito suna gaishe sa , ɗaga musu hannu yayi alamar yana amsawa , kana ya shige office.
fils na mutane ya ɗauko kana ya ciro biro a aljihunsa zai cicike sbda tun ranar daya fara zuwa aka bashi bai duba ba sai yau,
Saura guda biyu ya gama cikewa ya tsaya tare da juyi a kujera tunanin yayi masa yawa.
Aslamu alaikum akace daga waje , bazai iya mance mai muryar ba tabbas kamar Muhibbat .
Walaikissalam Khamis ya amsa tare da cewa " zaki iya shigowa cikin takunta mai jan hankali ta shigo ta zauna kan kujera tare da gyara gaban mayafinta ilahirin ƙirjinta a waje ta sunkuyar da kai kana tace " ka temaka ka bani amsa rankashi daɗe ni marainiya ce ka duba pls ta kuma marai raicewa tana kashe masa ido , tana zaune a gurin har aka ci minti talatin yunwa Khamis yaji ta addabesa ,ya kalli muhibbat ya kawar da kai kana yace " kiramin masinja zan aikesa siyan abinci , lallh ranka shi daɗe badan karkace girkina babu daɗi ba ai da na baka ka taɓa kaji , wani mugun kallo yayi mata a kai kaice tai shiru da bakinta tare da miƙewa dan taga yau babu fuska bare ma ya tsaya suyi magana ficewa tayi tana mai dana sanin shigowarta na yau.
Bata daɗe da fita ba sai ga masinja nan ya shigo , 5k Khamis ya miƙa masa kana yayi masa bayanin kalar abincin da yake so .

Aisha na tashi taga babu Khamis palo ta fito sbda duba shi amma babu shi babu alamarsa , part ɗin Ammi ta wuce Ammin baya palo hakan yasa ta kwanta kan kujera, Ammi na fitowa tace " a'a ɗiyata jiki yayi sauƙi ko ?" eh Aisha tace " to Allah ya ƙara lafiya Ammi ta faɗa tare da cewa "to me kike son ci ?" babu komai Aisha tace "kasancewar bakin babu daɗi , bafa zaki zauna da yunwa ba tashi ga shinkafa na gama inkuma faten dankali kikeso akwai , uhm sai anjima Aisha tace " tana gyara kwanciya .
Zuwa yamma sai ga Khamis ya shigo yana riƙe da leda a hanunsa , miƙawa Ammi yayi bayan tayi masa sanu yace "keda Aisha ,buɗewa Ammi tayi taga dambun nama ne a roba mai murfi Allah yayi maka albarka Ammi tace "tare da ajiye ledar, plet taje ta ɗauko a kitchen ta juye na Aisha a ciki tace " ƴata nasan kina cin wanan sosai taso , shima sai anjima tace " Khamis da jikinsa yayi sanyi ya zauna a ƙasa kan kafet yana kallon Aisha da duk ta rame lokaci ɗaya , ka samu ka bata wanan taci ko zataji ƙarfi a cikinta ko ka ɗauko mata maltina tasha cewar Ammi ,
Tom yace " tare da miƙewa ya ɗauko mata tare da kofi ya tsiyaya mata ya bata tasha kaɗan tace "ta ƙoshi dambun naman ya ɗibo a cokali yace " maza buɗe bakin kiga zan baki wani abu ,
Da ƙyar ta buɗe bakin ta karɓa zai bata cokali na biyu tace " ta koshi .
Baiji daɗi ba haka ya tashi jiki babu ƙwari Ammi dake kallonsu ta girgiza kai sbda Khamis na bata tausayi .
Tashi yayi ya koma part ɗinsu ya zauna a palo ya ciro wayarsa ya shiga gallery yana ƙarewa hotunanta kallo gata lokacin da tayi kwaliya zasu gidan su murmishi yayi kasancewar kwaliyar da tayi kafin Ammi ta gyara mata , kiss ya yiwa photon tare da rungume wayar tsamm a ƙirjinsa yana jin soyayyarta na ratsa ko wani sassa na jikinsa .

Washe gari yau kwanan

Please Login or Register in order to submit comment