Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi tai ficewarta kawai,.

Koda da daddy nata ya daeo shima tace mai babu komai babu abun da yake dumunta dole ya hakura sannnna ya sanar mata daya tura wannnan kudin, tace Allah ya basu saa ya amsa da ameen.

Jman ne zaune a daki tunanin yadda zaiyi da wannnan kudin kawai yake baisan me zaiyi dashi ba kodai sana,a zai fara yanzu ma a ganka da kudi tashi daya zaa dauka kaidin dan yankan kaine shi yasa ma bai wani yi amfani da kudin har yanzun ba ammma yasan yaddda zaiyi kawai zai jira zuwa wani lokaci kafin ya sami abum yi.
Washe Gari da wuri yaje gun aiki, bayan sun gama ana zaune ya kalli ogansu, oga nifa bansan ya zanyi da filin da kudin da baba yabarmun ba ammma nace inasan zan fara zuwa kwaatano ko lagos ina saro dan kaya ko Allah zai taimaka, gaskiya kam yaddda kace hakan zaai muka sani ko rabonka yana can ne,hmmm kawai yace.

Haka rauywar ke juyawa kamar juyin waina a tanda yau gashi sati daya da fara zuwan jman inda yace zai fara zuwa yana saro kayan gyaran mota da yasan babu sosai anan garinn nasu kuma babu laifi yana samu.
Bangaren hasinat kuwa bata sake kallan garrega dinsu ba sananna baban hasinat yana san ran wani satin kayanshi zasu zo dan an sako mai su a jirgin ruwa wannan kenan.

Yau laraba kuma mom di hasinat ta tashi da ciwo sosao dama daurewa take, bayan hasimat ta gama shirinta na zuwa gun aiki ta biya dakin mom din nata dan ganin mai ya hanata fitowa da safe, da sauri ta karasa toilet din jin alamar ana amai da sauri ta karasa ta tsorata sosai har saida taja baya, saboda mom dinta taga tana aman jini, mom meke damunki ina dadddy hai sani bane, itta dai kawai jijjaga mata kai mom di take ta kasa magana hakan yasa tai fice da gudu tai bangarwen daddy nasu tana adduar Allah yasa bai fitaba, da kalllo Aisha ta bita ganin gudun da yake hakan yasa tai dakin mom din,mom di ta gani durkushe a bakin gado hakan yasa tai saurim karasa tana mata sannu tare da tofa mata addua.
Da sauri hasinat tasha gaban daddy nata da yake shirin fita, kuka tasa dadddy mom ce a,an jini take, zaro ido yai yai gaba yana fadin nayi da ittta muje asibiti ammman taki ji, gashi taja abun ya zama babbbab, tarw suka shiga cikin daki Aisha ta sata gaba sai kuka take daukan ta yayi ya fice da ittta hasinat tabi bayansu Aisha ta bisu da ido tana Allah ya bata lafiya

By hajara mami natty girl
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•ŠπŸ•Š
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•ŠπŸ•Š
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•Š
*ABDUL JEY 14*
πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«
πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠπŸ’«
*πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠHajara*
*πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«Mami*
*πŸ•ŠπŸ’«Natty*
*πŸ’«girl*

```INDICATED TO RUNKA```

*The story is for you only miss Salsabila lawan*

~FANTASTIC STAR WRITERS (FSW)~

Babban asibim dake garin ya kaita hakan yasa aka shiga da itta emergency dan bata taimakon gaggawa,sai jeka da dawowa alhaji bado ke yana addua a zuciya yasan koma maye shine sanadin shi na shigarta wannnan halin, hasinat dake zaune tana hawaye a gefe ta zuba uban ta gumi ta rasa, eke mata dadi meke damun mamanta wai.

Jin likitan ya fito ya sasu mikewa da sauri, kalllan alhaji yai to my offfice plz, tare sukaje da hasinat, likitan ya kallleshi, alhaji dama fa na dade da bata report kan cewa she has a short time to live ata fada maka ba? Kallan shi yai ban ganeba doctor habu mun bayani,.

To dai alhaji kasan tana Aid sannna kuma ga ciwon zciya so immudity na jikinta basa wani functioning saboda Antibodie nata basa wani aiki so na bata mugun guna dan tai, maka mata ammma na faa mata any time zai iya tashi kuma zaa iya rasa ta, innnalillahi kawai alhaji ke fada itta kuwa hasinat tunda aka ambaci wai AID ta shiga rudani wai aid yaushe mom dinta ta sami aid ya akai bata saniba, .

Kallla doctor habu tai nufa ban gane maye AID wai bansan inda zancen ya dusa ba, kalllan alhaji doctor yai, kallan hasinat yayi kije waje zamuyi magana, wannne waje dad bakaji mai y ce ba anya sunyi bada diagonising daidia taya za,ace mom nada Aid me yasa ni banda ittta ranar na bada jini akai amfani dashi daddy kai me yasa aka da shi ina bukatar karin bayani doctor, plz kiyi shiru zamuyi magana, kifa kai table din offfice din tana kuka, kalllan doctor yai doctor habu yanzu ya ake ciki ya jukin nata? Eh tana bacci yanzu amma gaskiya tana suffering alot,hawayen fuskanashi ya goge sannna ya kalle shi zu iya zuwa mu ganta? Eh zaku iya sannnana a bata wani abun inta farka plz, ok alhaji yace sannna ya mike ya fice hasinat na bayanshi,da sauri hasinat ta karasa gun mom nata tana kalllanta mom ki tashi ki fada mun kwata kwata ban yarda da doctor ba ta fada tana kuka,dadyn bai hanata ba ya barta tayi abunta kawai ya san shi zai sanyaya mata zuciya hakanyasa bai hanata ba, ya dauki waya ya sanar bazai sami damar zuwa office,sannna ya kira wayar gida yace Aisha ta dafa abinci takai ta karbi kudin taxi a gun mai gadi saboda driver baya nan ya aikieshi ta amsa dato,.

ba wani abinci mai wuya tai ba dan dankali ta soya da kwai sai shinkafa data diba dama ta gama dafata ta dibi miya sannnana tasa vegetables ta dauki komai ta saka a basket ta dauki hijab din ta jawo kofan sannna ta nufi gate.
Da salllama ta karasa inakwana baba? Lafiy qlau Aishatu sai ina, nan ta fdada mai sakon dddy ya kuwa bata dubu daya shima duk ya shiga damuwa shi yasa yaga dazun sun fita a hargitse yace tace yana musu sannu ta amsa da to sannnan tai gaba.

Tsaye take gaban titi tun dazun ta rasa yaddda zatai bata sami taxi ba,wata da tazo wucewa ta tare duk kaya a bayan mitan sai mutun daya dake bayan bangaren bataga face nashiba, shiga motan tai tasa kaya ammma wata jaka dake kusa da itta duk ta dameta, tsaki taja,ta kalli na kusa da ittta malam Dan Allah in wannnan kayanka ne kadan matsayar sun damen da yawa wlh,ba tare daya kalleta bayace ittama kudin kujerarta na biya saboda haka dole ta shana agun zamanta, Aishabp bata san fada amma ina dole ba zata bariba ta takura da yawa hakan yasa ta ture jakan har ta fada kan jman dake zaune, juaywa yaui dan yaga waccce tamai wannnan aikin, suna hada ido gabanta ya fadi shine wanda zai mareta ranar da sauri ta dauke kai kuma bata sake maganaba, tsaki yaja tare da rike jakan a hannunshi ya tsainci kanshi da kin mayarwa ammma niya yayi yaiwa wanda yai wannnan aikin rashin mutunci.

Haka suka tafi babu wanda ya sake magana, gun da zata sauka aka zo ta duba kudi sama da kasa ta rasa hakan ya sata hadiyar wani yawu mai daci kenan ta zubar da kudin ohhh god Allah ka taimaken ta fada a zuciya

By hajara mami nattygirl
[2/9, 5:00 PM] β€ͺ+234 806 061 7117‬: πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•ŠπŸ•Š
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•ŠπŸ•Š
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•Š
*ABDUL JEY 15*
πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«
πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠπŸ’«
*πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠHajara*
*πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«Mami*
*πŸ•ŠπŸ’«Natty*
*πŸ’«girl*

```INDICATED TO RUNKA```

*The story is for you only miss Salsabila lawan*

~FANTASTIC STAR WRITERS (FSW)~
```you are the best friend sa,adatu garba kazaure i really miss you```

Duba take sosai ta rasa kudin inda mai motan ke jiran ta bashi kudin shi ta tsaya tana bata mai lokacin tsaki yaja irin kune baku da kudi kuke shigowa mutun mota kuyi ta hada shi da Allah sai kuwa kin ban kudin indai har ba zaki nemi afuwa ba, bata ce mai komai ba kudin kawai take nema tunda taga dan rainin hankaline bari tai ta duba, kallanta jman yake da gani tana taurin kai ga zuciya dan murmushi yai idonshi ya sauka kan kudin nata dake basket amma hankalinta kwata kwata bai kai kan basket din ba, dauke kai yai shidai bazai ce mata ga kudin can ba,ji take kamar ta fashe da kuka kallan jman tai shima yayi dai dai da kalllanta suka hada ido, hawaye ya cika idon, daga mata gira yai alamar maye? Tai saurin dauke kai, kallam driver din yai muje zan baka kudin, kallanta driver din yayi yayi tsaki, ta dauki basket din.

Ta tsaya tana gani jman ya bada kudin sannna ta sauke ajiyar zuciya mai mota yaja sukai gaba, daukan basket din zatai idonta ya sauka kan kudin,kalllan kudin take kamar tayi kuka, aikuwa saida tai hawaye ta dauki kudin tare dayin tsaki sai kuma ta tuna bata cewa wannnan na motar ta gode, tabe baki tai sai mun sake haduwa tukun.

Asibutin ta tashi ta tambaya aka nuna mata ward din da zataje sannnan takai abunci hasinat na jikin gadon sai hawaye take duk sai taji tausayinta ya kamata, ajjiye abincin tai kafin ta zauna kusa da hasinat din,aunty ki daina kuka insha Allah zata samu lafiya kinji? Batace mata komai ba taci gaba da kukan ta, haka sukai tazaune suna jiran tashin ta ammma har lokacin bata tashi ba,ganin har magariba ta kusa hakan yasa hasinat tacewa Aisha taje gida kawai, sannna ta bata kudin aikinta dan dama wata ya ciki.

Jman ne shida oagansu zaune, jman gashi yanzu Allah ya buda maka sana,ar har ka fara samu kaga gara da ka fara wannan sanaar,hakane oga dama so nake in fada maka why not in samu nan gun naka ayi gini wanda zan dinga zuba ka yankaga can yayi nisa in kuna nema sai kuna kashe kudi kaga inna dawo nan abun sai yafi sauki sai mu hada hannu ma,sosai wannnna shawara ta jman taiwa ogansu dadi yaddda kace hakan zaai shikenan amma kanangani zaka iya ginin kuwa?kaiii oga ka jika da wani zancen ai Allah ya sama wannnan sana,ar albarka saboda haka karka wani damu babban gini zanyi har wannnan garage dinma zan sake mai tsari, zaro ido ogan yayi kace musa ido muyi kallo, duk yan gun suka saka dariya haka suka ci gaba da hira,.

Da sallama Aisha ta shiga gidan nasu, inna ta amsa tana kallan ta, ya na ganki haka yar inna? ba kamar yadda na saba ganinki ba Allah yasa lafiya, lafiya qlau innna wlh momy ce jikin babu dadi tana asibiti rai a hannun Allah,murmushi innma tai to da waye ranshi ba a hannun Allah ba,ki daina damuwa Addua zaki mata Allah ya bata lafiya insha Allah zata samu sauki kinji ki daina damun kanki, daga kai tayi alamar to, ga abincin ki can, dauka tayi taci, haka yau suka zauna shiru duk Aisha tabi ta ga hankalinta, kalllanta inna tai, Aisha, naaam inna bari in baki labari, murmushi Aisha tai dan tasan hakan inna ke mata indai taga bata wani walwala ko taki sakewa, hakan ya sata gyara zama

*Wani saurayine yaje gun budurwarshi hira sai ta kawo mai chin chin, yace ya koshi, tai tai dashi yaci yaki, tace shikenan ai sai tace bari inje in sanarwa mamana zaka shiga ku gaisa, yace to sannna ta shiga ciki,tana shiga in fada miki ya debi kusan rabin chin chin ya juye a cikin hular shi, sannna ya koma ya zauna, sai gata ta dawo tace yazo su shiga suka shiga,yaje ya gaisa da maman ta, to dama akwai wani karfe da yadanyi kasa a kofar shiga cikin gidan nasu, kawai yazo wucewa wannnan karfe ya janye hular saiga chin chin yana zuba, aikuwa sai ya fara rawa yana cewa ana ruwan chin chin ye ana ruwan chin chin* sosai Aisha ta dara harda rike ciki innna ta kalleta tare dayin murmushi, kallan inna tai inna ban wani labarin to, haka sukai ta labari,.

ALLAH SARKI UWA WANI YARO NE SUNA ZAUNE DA MAMAN SHI `A SANAI SUNA ABDUL`SAI TACE ABDUL YACE NAAM, TA SAKE CEWA ABDUL, YACE NAAM TA SAKE FADA YA KARA AMSAWA DATA SAKE FADA SAI YACE HABA MAMA NAFA AMSAH AMMA SAI KARA KIRA KIKE,SAI TAI SHIRU TANA KALLANSHI SAIGA HAWAYE YA KUWA SHIGA RUDANI YA FARA TAMBAYAR ME YAYI KUMA, TACE BABU KOMAI KAWAI TANA TUNA SANDA YANA YARO NE YAITA KIRAN SUNANTA BA ADADI KUMA DUK SAITA AMSAH INYA DINGA MAMA, MAMA, MAMA BATA TABA KIN AMSAWABA AMMMA GASHI SAU BIYAR KAWAI YANA NUNA YA GAJI, .

Allah sarki uwa Allah ya kara saka manasan iyayen mu ameeen

By hajara mami natty girl
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•ŠπŸ•Š
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•ŠπŸ•Š
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•Š
*ABDUL JEY 16*
πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«
πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠπŸ’«
*πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠHajara*
*πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«Mami*
*πŸ•ŠπŸ’«Natty*
*πŸ’«girl*

```INDICATED TO RUNKA```

*The story is for you only miss Salsabila lawan*

~FANTASTIC STAR WRITERS (FSW)~
Washe gari kuwa kamar yadda jman ya fada yasa aka fara aiki dan bulo na siyarwa ya siya yasai komai aka fara aiki har yan gun aikinshi abun ya basu mamaki, shi kuwa jman baiga wani abun mamakiba, dubu dari kawai ya dauka ya fara sanaa da itta amma Allah ya bude mai Allah kena if god say yes no body can say no wannnan haka yake,.

Yau jman yace zaije gidan kawun shi yana san yaje kawai, ya kuwa sai abu a hanya wa sameer sannna ya kama hanyan,.
Sallama yaiwa mai gadi ya amsa sanna ya shiga ciki,da sallama ya shiga parlour saudat dake zaune tana kallo ta dauke kai tare da hade rai shima kuwa ya hade ran kafina ya zauna, da sauri sameer ya dawo kusa dashi yaya abdul sannu da zuwa? Yauwa kanina ya gida ya skull da fatan kana kokari daga kai yayi, ok ina dad dinka, da sauri saudat ta karba imma wanu abun kazo karba ba zaka samuba dan bashi da kudi, wata uwar harara ya bata hakan yasa ta juyar da kai tana gun guni yai tsaki ledar hannunshi ya mikawa sameer gashi kaje kasha kaji, .

Kawunne ya sakko shida matarshi suna hira duk suna ganin jman suka wani hade rai shi abunma dariya ya so bashi amma ya danne, gaida su yayi suka amsah fuska daure, kalllan shi kawu yai yanzu ko kunya babu kazo ka tambayeni kudi wlh ko ina da shi bama zan baka ba, uhmmm kawai jman yace sai da ya bari kawun ya gama surutanshi sannnna yace dama zuwa nai mu gaisa, yanzu ma zan wuce, sannna ya dakkko kudi a aljihu 1000 yaba sameer gashi kasha sweet my boy, sameer ya karba tare da godiya, kawu ya bishi da ido wama ya sani ko sato kudin kayi,murmushu jman yayi abun bazai baka mamakiba ma ai saika ganni da motata hadaddiya ya fada a zuciya tare da ficewa,.

Yana fitowa ya tuna sanda yazo gun kawo neman kudi daga nan gidan gidan alhaji bado yaje hakan yasa yace bari yaje unguwar, .

Innna ni zan wuce, asibitin ma zan fara zuwa kafin inje gidan in dafa masu abinci, sanna ga kudinnnan inna kici abun da kike sofa, to kawai innan tace sannan Aishan ta fita taje tahau texi, .
Suna zuwa unguwar jman ya sauka yazo wucewa yaga inna ta fito, ittace wadda ta taimaka mai ranar, da sauri ya karasa gunta ya gaidata, ta amsa bata ganeshi yai mata kwatance ta kuwa gane,mama ina zaki haka?wlh kasuwa zanje Aisha zan siyawa kaza in mata farfesu,murmushi yai kice za muci dadi yau, sosai kuwa ta fada, to kawo inje in siyo miki kazar,mana mama kallan shi tai,Allah mama ba guduwa zanyiba zan dawo dariya tai ni bance ba kuma daga zuwa ko ruwa ban baka ba sai aike, aa babu komai wlh zanje, ta bashi kudin sannna ta koma ciki ya karba ya nufi titi sannna yahau texi,.

Aisha tana zuwa yayi daidai da tashin momy,sosai hasinat taji dadi ta tambayeta abun da zata ci tace komai ma,nan taba Aisha kudi kan taje ta siya kaji tai wa momy farfesu ta karba ta fice tana murnar tashin momy din,.

Ta tsari mai adaidaita tasu jman, tana shiga taga shine ta zaro ido kamar ba zata shiga ba sai kuma ta shiga, kallanshi tai ina wuni, baice komaiba illah juyar dakai kawai da yayi,ganin bai amsa ba yasa ittama yin shiru hara akaje inda zasu sauka suka sauka, sannnan yai gaba tana binshi a baya, ganin tana binshi yasa ya tsaya dan ta karaso yaji lafiya take wani binshi

By hajara mami natty girl
[2/9, 5:00 PM] β€ͺ+234 806 061 7117‬: πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•ŠπŸ•Š
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•ŠπŸ•Š
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•Š
*ABDUL JEY 17*
πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«
πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠπŸ’«
*πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠHajara*
*πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«Mami*
*πŸ•ŠπŸ’«Natty*
*πŸ’«girl*

```INDICATED TO RUNKA```

*The story is for you only miss Salsabila lawan*

~FANTASTIC STAR WRITERS (FSW)~


ο»ΏGanin ya tsaya ayasa ittama ta tsaya tana jiran taga ya wuce ganin yaki tafiya yasa ta karasa dan wucewa, saida tazo kusa da shi, meye kike bina?kallanshi tai babu komai wucewa fa zanyi zanje in sai abune? !e ne zaki siya?kaji ta fada tare da juyar da kai tabe baki yai muje, kallan shi tai bata gane muje ba shi ya kama gaban shi mana, amman batace mai komaiba suka jera suna tafiya kana ganin su kasan sun dace da juna Aisha ba fara bace can ba amma shikam fari ne,ammma fa duk kyan shi bai kaita ba saboda ta wuce shi sosai, .

Haka sukaje ta siyi gudu hudu shi kuma ya siyi gudu biyu sannnan suka kama hanya, saida sukaje bakin titi ba tare da ya kalleta ba yace wacce unguwa zaki, new GRA ta fada tana kallanshi,uhmm yace ganin wajen unguwar da zaije ne hakan yasa suka hau texi daya da itta sannnan aka kaisu shizai fara sauka hakan yasa ya tsaya dan nesa da gidan nasu ya biya kudin itta dai batace kala bammma tana mamamkin dama nan ne unguwarsu amma bata taba ganin shi ba a unguwar zata so ta tsaya taga gidan da zai shiga amma tasan zata batawa mai texi lokaci ne hakan yasa kawai suka wuce.

Da sallama ya shiga gidan inna dake zauna ta amsa sannnan ya shiga cikin gidan sosai gidan ya burgeshi, ya zauna tare da ajjiye mata kazar, aa ya naga ganta a yanke ai na dauka mai rai zaka siyo sai a yanka dan nasan kudina bazai kai a siyi irin wannnan ba,murmushi yai inna ai wannan yafi sauki kinga ba zakisha aiki ba, ga canjin nan ma ya mika mata 1000 dinta ;aa dannnan ba ai hakaba, haba hab,haba inna kamar uwa fa kike a guna dan na siya miki wannnan ai ba komai bane, murmushi tai tun ba yauba take san da na miji sai gashi Allah ya kawo mata ta tashi daya mikewa tai bari in wanke to sai in maka farfesun,Allah yayi albarka, murmushi yai tare da fadin ameen,.

Hasinart ce tasa mom gaba kan saita fada mata yadda akai ta sami AID ganin ta dameta yasa tai mata karyar yankewa datai da rezar da kawarta mai hiv ta yanke, sosai hasinart tai kuka har ta godewa Allah, suna zaune har wajen 12;00 sannnan alhaji ya dawo daga wajen aiki ya sanarwa hasinart kan cewa an aiko mai da kayan shi sun taho sun kusa karaso wa, to kawai ta ce mai haka sukai ta zaune har Aisha taje tayi abinci ta kai musu, .
jman kuwa saida ya ci abinci a gidan su Aisha ya taya inna hira har sun saba sannnan yai mata salllama ya tafi tace kuma ya dawo gobe.wannan kenan

Sai da aka kusa kiran, mariga kafin Aisha ta dawo gida, inna tai mata sannu sannna ta bata abincin, kalllan naman Aisha tai kafin ta kalli inna alamar tana san karin bayani, ke ni ki daina kallo na hakan yayanki ne ya siyo mana,waye yayana kuma kodai yaya salis keke nufi?bashiba yau kikao wani yaya shine ya ganni zanje in siya shine ya karba yaje ya siyo in bazaki ciba to,murmushi tai innna babu ruwana indai dan yankan kaine,dariya innar tai ke kuwa kike da ruwa yarinya nasan sai kinfi kowa daga hankali karki wani damu bashi da matsala zaku saba kinji, tabe baki Aisha tai kafin tai bismilllah ta fara ci,.

Haka abun ke tafiya komai na canzawa kusan kullun sai jman yaje gidan su Aisha sunyi hira da inna amma bai taba ganin Aisha a gidan ba, aikin jman kuwa anyi nisa har an kusa gamawa yanzu ma ya daina zuwa siyowa da kanshi saidai a aiko mai a mota sanna ya baa kudin mota dana kaya sosai sanaar tashi ta bunkasa, .

Jikin mom kuwa baa magana dan kullun kara gaba abun yake wannan kenan,.


By hajara mami natty girl
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•ŠπŸ•Š
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•ŠπŸ•Š
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•Š
*ABDUL JEY 18*
πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«
πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠπŸ’«
*πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠHajara*
*πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«Mami*
*πŸ•ŠπŸ’«Natty*
*πŸ’«girl*

```INDICATED TO RUNKA```

*The story is for you only miss Salsabila lawan*

~FANTASTIC STAR WRITERS (FSW)~

Jman ne zaune shida inna a tsakar gida, kallan inna yai, inna wai ni Aisha a ina take wannnan aikinne? Tabe baki tai ta nace ne nayi nayi da itta ta hakura da aikin taki akwai wata a gidan wai hasinart ta takura ta abun dayasa yanzu ma ta sami salama saboda maman yarinyar bata da lafiya me shi yasa ammma badan haka ba kullun indai zata dawo gidannnan ranta a bace yake, murmushi yai wanne gidane wai inna?gidan Alhaji bado ne fa ; shiru yai baice komai ba jin an anbaci gidan abokin gabar shi, kallla inna yai indai ta dawo kice nace karta sake zuwa gidan bana san aikinta a gidan,angama ta fada irin oder accepted abun yama bashi dariya haka sukaci gaba da hira,.

Su Aisha da hasinatt ne suna zaune a room din da take suna hira abum kamar wasa jikin mom din ya tashi sosai sai tari take hade da jini hakan yasa hankalin Hasinart tashi suka fita a tare itta da Aisha suka kira likata, da sauri suka shiga suda nurse dan ceto rayuwar ta, sosai hasinart ke kuka Aisha na bata hakuri ittama tana hawaye suna haka alhaji yazo duk hankalinshu a tashe da sauri hasinart ta karasa gunshi daddy mom mutuwa zatai,inta mutu bansan ya zanyi ba rungumeta kawai yayi yana lalllashi sai salati yake a zuciya duniyar tana shirin mai juyin waina me ya aikata haka(ni kuwa nace kai kuwa ka aikata abu sosai malam),.

Suna tsaye doctor ya fito,ya kellesu duk suka tsora mai ido suna san jin mai zai fito daga bakinshu duk in ka gansu kasan a tsorace suke da jin abu da zai fito daga bakinshi duk sai yaji tausayinsu, kallanshi alhaji yai ya me ye doctor meke faruwa?alhaji saidai kuyi hakuri Allah ya karbi abunshi,sosai hasinart kesan tayi fada da nunfashinta amma ta kasa sai ji sukai tayi kasa, da sauri nurse sukai kanta inda Aisha ke kuka kawai, Alhaji kuwa bango ya dafa yana salati, sannna ya shiga dakin da mom di take, an rufeta sai a lokaci n kuka ya zo mai, yana yi yana cewa ta yafe mai duk shi ya jawo,.

Sanda hasinart ta tashi a gida ta ganta dan har anwa mo m wanka kaita zaai ta tashi tai ta kuka taki bari a tafi da mom din saida kyar aka janyeta, dangin mom duk sunzo sai kuke kuke ake nan fa labari taga matar alhaji bado ta rasu, sanda jman yaji yaji tausayinta saboda matan nada kirki,.

Suna zaune aka karbar gaisuwa aka kira alhaji hakan yasa ya koma gefa ganin number din masu kawo mai kaya ne, da salllama ya daga bayan sun gaisane, mutumin ke fada mai accident din da suka samu kayan duk sun nitse a ruwan shima mutumin yana asibitine rai a hannun Allah tunda alhaji yaji labari wayar ta fadi a hannuns shi shima ya bita ya fadi a kasa a gun,da sauri mutane sukai kanshi aka tafi dashi asibiti

By hajara mami nattty girl
[2/9, 5:00 PM] β€ͺ+234 806 061 7117‬: πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•ŠπŸ•Š
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•ŠπŸ•Š
πŸ’«πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ’«πŸ•Š
*ABDUL JEY 19*
πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«
πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠπŸ’«
*πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«πŸ•ŠHajara*
*πŸ•ŠπŸ’«πŸ’«Mami*
*πŸ•ŠπŸ’«Natty*
*πŸ’«girl*

```INDICATED TO RUNKA```

*The story is for you only miss Salsabila lawan*

~FANTASTIC STAR WRITERS (FSW)~

Special greeting to you special friendπŸ‘‰KHADIJAH UMAR MATAZUπŸ‘ˆ

ο»ΏSanda aka wuce da shi asibiti kafin hasinart dake cikin gida taji labari da sauri ta fita ta karbi wayan baban nata dan ji

Please Login or Register in order to submit comment