Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusa cika.




Nasiha sosai kulu tayi musu kafin ta sallamesu tabar gidan duk da akoi kunya tsakanin ɗan fari da surkuwa, amma hakan bai hanata faɗa musu gaskiya ba domin kuwa uwa tagari ce kuma basu da wanda ya wuce ita A yanxu.


Koda Kulu Takoma gida tasamu Furera da maifiyarta suna ta shewa bata kulasuba tayi wucewarta ɗaki, saida aka yi kiran magrib tukun ta fito domin yin alwala, kunnuwan tane suka jiyo mata zancen su Furera a ɗaki, waya sanima ko ita Ameenatu ce ta boye BOƊƊI saboda ana cewa tanada kyau, *innah* tace waya gaya miki ai na daɗe da ce miki wannan yarinyar ba mutum bace yar aljan ce yanxuma sune sukaxo suka dauki abunsu, koda basuxoba idan ta girma zata bisu domin sune iyayen ta, dariya suka fashe dashi harda tafawa, jikin Kulu yayi sanyi ta wuce kawai ranta na mata kuna har yaushe wannan abun zai wuce kullum Innah da Furera bazasu rasa abun aibata waba.



Wata dariyar suka kuma saboda dama da gayya suke maganar burinsu taji kuma taji sunyi farin ciki, innah ce tace inadai kin ajiye ta inda yaka mata, Furera tace aiko Inaji yanxu haka ma bata raye ko ruwa yatafi da ita domin wannan waje ko Ameenatu nakai saita salwanta,. Dariya suka kuma yi kulu dake ɗaki tana jiyo dariyar su.



Bayan ta idarda sallah ta daga hannun ta sama, ta fara kaiwa mai komai mai kowa kukanta. Kulu kenan.,


Cikin dare tanajin matukar ciwo ta rasa meye ne ke damunta kirjinta kamar zai fito waje Abubakar yagama ruɗewa ya rasa yanda zaiyi, addu'a ya rinka tofa mata har bacci ya dauke ta.



Koda gari ya waye Abubakar ya je wajen Mahaifiyarsa bayan sun gaisane yake sanar da ita rashin lfy Ameenatu, ta jin~jina al'amarin tace yaka mata dai kuziyarci babban asibiti saboda kar a barta ba'a san me yake damun taba, gashi dukta saka damuwa na rashin BOƊƊI a kusa.


Yace shikenan Insha Allahu hakan za'ayi.



Kano state Sayyid da Farouq sun isa cikin aminci.....................




🤧Zazzabi harda mura na shirin kamani pray for me pls 🙏
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/


🌀🌀 ```BOƊƊI the beautiful``` 🌀 🌀

Story & writing
By
(Z. B. M)

Yar mutan gombawa.

Marubuciyar


~~ZAINAB abuƙaya
BANI BA AUREN SOJA
NIMA DANAWA LAIFI
Sc relationships
AUTAR MOMY
And now
BOƊƊI the beautiful~


Follow me on what'sapp
09066017177
Whatpad
Zainab7177
Gmail zbala0512@gmail.com


```Bismillahi rrahmani rrahim```




*I dedicate this page to my kids tauheeda & imam, Allah yaramin ku yabaku ilimi mai amfani.*





PAGE 7️⃣🔁8️⃣


................ Cikin aminci da yardar Allah, *Ummu* tayi matukar jin daɗin ganin su saidai kuma ta gansu da yarinya, kallo take binsu dashi takasa cewa komai.



Farouq da sayyid jikin su yayi sanyi domin basu san dawani irin kalma zasu Fahim tar da Ummu ba lokacin *Abbu* shima yashigo amma da yake falon sa direct yanufa bai san da dawowarsu sayyid ba.,

Bayan sun gaishe cikin girma mawa, sai kuma suka yi shiru kowa na jiran abunda ɗan uwansa zaice, Farouq dai yasawa ransa koda Ummu bata amshi BOƊƊI ba zai kai ta wajen mamynshi.


Ummu ne takaste shirun nasu tace! Sayyid! Farouq! Shin ina kuka samo wannan yarinya? Farouq ne yayi karfin halin fara sanar da ita dukkan abunda ya faru lokacin tafiyar su, sayyid ba'a bunda yake faɗi sai na'am, 😅 tsoron sa bai san mai Ummu zatace ba dukda ya yarda da maifiyar tashi, shiru tayi tana nazari tace to Allah ya bayyanarda gaskiya amma wannan yarinya na tausaya miki.

BOƊƊI dake hannun Farouq Ummu tasa hannu ta karba yarinya ba ƙiwa tamiƙo hannu tana murmushi zuwa ga Ummu,


Tace Allah sarki dagani ba'a yaye taba, house girl takira tace takawo mata madara dakanta ta sha yarda BOƊƊI saida ta tabbatar da koshinta sannan tasa ta a kafaɗa ta fara shafa bayanta gyatsa tayi cikin minti kadan sai bacci, duk abunda ake Farouq da sayyid suna zaune suna kallo farin ciki ya mamayesu bazaka Gane wa yafi wani murna cikin suba.


Ummu ne tace to sai kuje kusanarwa Abbu shima yasan abunda ake ciki mikewa suka yi ummu kuma ta wuce sama takai BOƊƊI ɗakin ta, ' ta kwantar soyayya da kaunar yarinyar ya kama ta, "domin ko a chan Saudiyya wannan yarinya kyakkyawa ce," bintu ce ta shigo aguje amma bakin ta ɗauke yakeda sallama, cikin Larabci tace, " Ummu naga motar ya Sayyid, ai bata kara saba tace; wow Ummu wannan fine baby ɗinfa? gaskiya tanada kyau sosai dama kince zaki haifa min baby Irina ko Ummu? Duk wannan Tam bayoyi ai sai bintu, Umma tace eh bintu wannan itace bbyn danace zan haifa miki, farin ciki sosai ya kama bintu, to yanxu kije ko, saboda bby tana bacci karta tashi, bintu tace; Ummu ina zamuna kwana tareda ita, Ummu tace eh kije to kinji saiki faɗawa Abbu aiko cikin zumuɗi bintu ta fice tayi falon Abbu.



Karo tacida sayyid zai fito daga falon, tace ya sayyid momy ta haifo min fane baby girl, yace da gaske tace eh to barinaje na ganta nima,



************************************** Gari na wayewa Abubakar suka shirya shida Ameenatu domin tafiya jalingo atare wajen da yake kasu wanci saboda rashin lafiyarta yaka mata Ace suna tare domin zuwa babban asibiti, sun sallami kowa kulu ta musu fatan nasara suka tafi cike da kawar juna.



Bayan sun isa kai tsaye asibiti suka nufa ba wani jimawa suka samu ganin likita an mata duk wani gwadi daya dace an tabbatar cewa tanada ciwon zuciya wanda tunani ya hadda sa mata,.


Abubakar yashiga tashin hankali matuka, an rubuta musu magani dakuma shawar wari da aka basu, sun isa masauki wajen wani mutumi wanda shine uban gidan Abubakar sunan sa mlm Haruna, tare suke kasuwanci shiya ɗaura Abubakar a hanya, matar mlm Haruna tanada matukar kirki ta karbesu hannu2 bayan samun labarin abunda ke faruwa da Ameenatu tausayin su yakara shiga zuciyar mlm Haruna , yayi kuma niya Insha Allah zai tai maka musu.




*************************************BOƊƊI ne ke zaune cikin falon ƙasa itada bintu ansanya mata kaya masu kyau cikin kwana biyu takara kyau dakuma sabo mutanen gidan, wasa suke tareda bintu, BOƊƊI na faman dariya dama shine abunda tafi iyawa,.


Sayyid ne ya shigo BOƊƊI na hango shi tafara daga hannaye sama alamun ya dauke ta, dariya yake mata ya wuce yaki dauka ta kuka ta saka bintu tace ya sayyid kadau keta mana, juyowa yayi ya dauke ta yana dariya itama dariya tafara tayi shiru Ummu dake saukowa daga bene. Tace Bintu kece kika samun baby kuka ko? Tace; a'a Ummu sayyid ne yaki daukan ta shine take kuka, ah ah Sayyid yaushe kafara tsokanan babyna, Sayyid yace Ummu BOƊƊI sunanta fa tace to Haka kasa mata, yace no Ummu Barrister mukaji yana faɗin haka saboda yaga kyanta, wai a fula tanci kyakkyawa, BEUTIFULL, Ummu tace wow BOƊƊI to munji yanxu muma haka zamu kira ta,.


Yauwa Abbu yace gobene zaka wuce ko? Sayyid yace; eh To kayi magana da jaddun ne? Yace inaso dai nakira shi ko inaso na musu surprise ne, Ummu tace wani irin surprise daka musu da karka musu ai duk zasu yi farin cikin ganinka kasani kaima. Sama ya haura yana cewa gara dai amsun yana dariya.



Dakinsa ya wuce domin watsa ruwa yana matukar jin kewar Nigeria da ahlin sa baki ɗaya sai lokacin ya tuna yaushe rabonsa daya ziyarci gidan kaka nunsa ,

Bayan ya fito wankane ya shirya cikin kananun kaya domin magrib tayi masjid ya wuce wanda ke maƙale jikin gidan, bayan ya fito daga masallaci yashiga motar sa jidan kakansa ya wuce, koda shigar sa yasha magana A wajen tsohuwa, yayi ta bata hakuri, ai Aliyu kam bai jefar damu ba tunda kullum nan yakecin abinci, tayita faɗa shi kuma yana bata hakuri, suna cikin haka tsoho ya shigo tace yauwa gara da kazo, shima yace yau wanake gani badai *Maleek* tsohuwa tace shine dai yau yaxo, bayan sun gaisa ne tsoho yace yanxu *Maleek* sai yau tunda kadawo Kasar nan bakaxo gidannan ba, yace kuyi hakuri wlh ban samu lokaci bane, yanxuma naxo muku sallama ne zan wuce Saudiyya gobe, suka yi salati yanxu *Maleeku* saida kaxo tafiya tukun zaka xo mana sallama, hmmmm lallaikuwa Allah ya kyauta bayanda muka iya kai namu ne dole Musa maka albarka, dariya suka yi baki ɗayansu, suka ci gabada tadi gwanin burgewa.



Washe gari................................................................🥱




Wlh I'm so tired 😴




Comments & share pls 🥰
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/


🌀🌀 ```BOƊƊI the beautiful``` 🌀 🌀

Story & writing
By
(Z. B. M)

Yar mutan gombawa.

Marubuciyar


~~ZAINAB abuƙaya
BANI BA AUREN SOJA
NIMA DANAWA LAIFI
Sc relationships
AUTAR MOMY
And now
BOƊƊI the beautiful~


Follow me on what'sapp
09066017177
Whatpad
Zainab7177
Gmail zbala0512@gmail.com


```Bismillahi rrahmani rrahim```




Kawun alƙawari cikawa saboda haka na baki wannan page ƙyauta FATIMA ADAMU kiyi yanda kikeso dashi 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼


PAGE 9️⃣🔁1️⃣0️⃣




................washe gari Sayyid ya tashi jikin sa duk babu daɗi domin Sam baya so yabar Ummu da Abbu, yana son zama tareda su, "amma bai san shi wani irin kaddara ne kowani lokacin Ace baya tareda iyayen sa"


Cikin tunani yakara sa shiri, fitowar sa kwai Ummu suke jira domin sun shirya, karfe 11 plane ɗinsu zai tashi a yanxu kuma karfe 10:15


Jikin sa duk babu kwari ya fito Ummu ne tace; ya dai Sayyid kana abu kamar mara lafiya sai mun hanzarta domin lokaci ya kusa.


"Bintu sarkin surutu taxo tana cewa" ya Sayyid Abbu yace wajen su jaddun zaka je? dan Allah nima katafi dani wlh nikam inason zuwa, Sayyid yayi karfin halin cewa Bintu idan kika tafi to wazai zauna da BOƊƊI tace to itama saimu tafi da ita,. Ummu tace babyna bazata jeba kedai kitafi, tace a'a Ummu nima nafasa dariya Abbu yayi domin yana jinsu baiyi magana bane, don yasan Bintu yau da ba don BOƊƊI ba! koya za'ayi sai taje. Sayyid yasa hannu ya karbi BOƊƊI da aka mata ado yau yaga tayi matukar kyau, yace; Ummu zanyi kewar beauty ɗinki ummu kibani ita na kaiwa jaddun, Ummu tace su, basa bukatar ta yanxu kaidai kaje kabarni da beauty na, idan Kaga mun rabu to aure namata. Gaban sane yafaɗi yace kai Ummu har anfara maganar aure tun yanxu, tace kwarai kuwa ai lokaci ne idan muna da rai to zaixo.



Saboda holdup da yake hanya sai 11/40 suka isa lokacin har an fara kiran ma tafiya. BOƊƊI na hannun Sayyid Bintu itama sai binsa take tana cewa; ya Sayyid karfa ka tafi da ita, har ya gaji da surutu irin na Bintu, shi da zai iya rufa idoma ai da ai daya wuce da ita, can ta tashi cikin yan Larabawa.



Bajimawa kuwa jirgin su Sayyid ya ɗaga zuwa Saudiyya tareda barin amanar BOƊƊI ahannunta. Ita dai sai mamaki take yi, abun kuma dariya yake bata, kai Maleek Allah ya nunamin ɗanka domin zai sha so yayya 😁


Bayan su Ummu sun dawo daga rakiyyar Sayyid suka ta rarda Farouq yaxo Abbu yace ya dai Farouq ka makara gashi har sun tashi, yace wallahi phone ɗina ne yasamu problem shiyasa gashi bansan time ɗin tafiyar ba, kawai zamuyi waya dashi, yace Ummu gaskiya kina kula da babyn ki kalli yanda takara zama fresh, Ummu tana dariya tace zakaci kanka ai,.




***************************************** Alhamdulillah yanxu Ameenatu ta fara murmurewa sai dai abunda baza a rasa ba, wato har yanxu BOƊƊI tana ranta. Mlm haruna Da Abubakar suna zaune sai Mlm haruna yace yauwa Abubakar inada wata shawara wata kila tayi maka yace ina sau ra ronka domin nasan duk abunda zakace to Insha Allah alkhairi ne awagena.


Mlm haruna yaji dadi sosai domin Abubakar ya dauke shi tamkar dan uwa, yace ; dama shawara ta itace mai zai hana tunda inada ɗan uwa a Kano kaje can domin kasuwanci yana da kuɗi sosai kuma nasan idan na tura ka zai ɗaura ka kaima, har kasamu na kanka, kuma kaga can akoi samu ba kamar nanba.


Abubakar yaji dadin maganar amma sai kuma yace ai matsala ta Ameenatu kuma gashi inada Mahaifiya a ƙauye bazan iya tafiya nabar wannan nauyin ba, yanxuma na mata nisa bare kuma Ace natafi har Kano. Mlm haruna ya numfasa! Yace; karka damu Allah yana nan kuma nasan bazata hana ka tafiya ba saidai kawai ka rike alkawari aduk inda kake katuna dasu nasan zasu yi ta maka addu'a kuma addu'ar su shine nasara a gareka, karka damu Ameenatu zamu zauna tare da ita, kamar yanda kasani bazata taba kuka na shin wani ba.



Sosai Abubakar ya shiga farin ciki. Koda yadawo yasanarwa Ameenatu ita dai batace komaiba sai tafan alkhairi datayi,

Washe gari Abubakar ya shirya yanufi kauyen su, bayanda Ameenatu batayi ba domin ta bishi amma yace ta zauna in ya so taje daga baya,.


Koda ya isa kulu tayi farin ciki ganin ɗanta takuma tambayi jikin Ameenatu yace yanxu alhamdulillah ta warware, labarin tafiyar sa Kano yabata, da farko taso ta damu amma daya Fahim tar da ita da wasu kalmomi sai hankalinta ya kwanta, musamman data tuna abunda yake faruwa yanxu furera da mahaifiyarta sun baza labari a gari cewa BOƊƊI aljana ce, shiyasa ta ɓace,. Abun na damun kulu sosai data fita sai a fara nuna ta. Hakan yasa tayi farin ciki da Ameenatu bata samu wannan labari ba domin bazata iya jurewa ba.


Fatan nasara tayi wa ɗan nata yatafi basu hadu da furera ba tana can wajen ya won gulma, sa'anninta duk sun kusa samun jika a garin. Amma ita ko auren batayiba bare ɗa.


****************************************** BOƊƊI sai kara wayo take kowa ya ganta sai son barka, Bintu kullum tana tareda ita wai dole sai ta koyawa BOƊƊI tafiya da magana ita ta gaji bata iya daukan taba don tayi nauyi yanxu.

Haka zasu zauna suyita gwalantu wani lokaci kuma tafiya anayi ana faduwa. Ummu dai dariyan su kawai take.


Sayyid ya isa cikin koshin lfy jaddun sunyi matukar farin ciki da ganin sa, ai kuwa a ranar daya isa bai bari ya kwana ba ya basu labarin BOƊƊI su kansu sunga yanda BOƊƊI tashiga zuciyar Sayyid,


Yafara zuwa makaranta abubu buwa suna tafiya yanda ya kama mata.



Abubakar yasamu shigowa garin Kano..............................





Sai amin axuri da typing kadan banida enough charging ne


Mai Ƙaunarku Z. B. M😘🥰



Share pls 🙏
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/


🌀🌀 ```BOƊƊI the beautiful``` 🌀 🌀

Story & writing
By
(Z. B. M)

Yar mutan gombawa.

Marubuciyar


~~ZAINAB abuƙaya
BANI BA AUREN SOJA
NIMA DANAWA LAIFI
Sc relationships
AUTAR MOMY
And now
BOƊƊI the beautiful~


Follow me on what'sapp
09066017177
Whatpad
Zainab7177
Gmail zbala0512@gmail.com


```Bismillahi rrahmani rrahim```



Dole ne yar uwata sister mai bani karfin guiwa HASSANA BALA kema ganaki page ɗin kiyi yanda kikeso dashi Allah yabar zumunci 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼




PAGE 1️⃣1️⃣🔁1️⃣2️⃣




................Abubakar yasamu shigowa garin Kano Bai wani wahalaba wajen gano gidan dan uwan mlm haruna, "gidane nagani na faɗa katafare iya kallon mai kallo, Abubakar yayi mamaki gamida tsoro saboda azayonsa nanɗin wani wajene, tunda yake bai taba ganin irin wannan gida ba, haka bai kuma taɓa sawa ransa akoi aduniya ba, maganar da yaji ne yadawo dashi tunani, Bismillah, ka shigo.

bai tsinkayi lamarin ba sai da aka shigar dashi wani falo akace zauna alhaji yana fitowa,

Jikin sa na ɓari yadan rakuɓe jikin kujera,, ba jimawa sai ga wani mutum ya fito fusakarsa dauke da fara'a "yace ;maraba sannu da zuwa bayan ya zauna ne suka gaisa cikin mutum ci, Abubakar ya masa bayani daga inda yake yace tabbas nasamu labarin zuwan ka, yanxu saika huta kayi wanka,

Wani dakin aka raka shi, sanin cewa Abubakar ɗan kauyene yasa mai gadin yanuna masa yanda zaiyi komai, har yafara saduda da cewa nan gidan aljanna ne 😂 bayan yayi wanka yafito ya tarar da abinci an kawo masa ba wani iyaci sosai yayiba, saboda yunwar cikin sa nema yasamu ya tsakuli kaɗan.

******************************************Aguje ta fito da lunchbox ɗinta a hannu Sanye da kayan makaranta, "Bintu wait for me pls," Ummu dake tsaye tana hangota dariya ta fara tace; gara dai su tafi tunda kullum ke kinfi so kuyi late, karasawa Tayi wajen motar tana haki kamar wanda tadaɗe tana gudun, tace Bintu dama zaki iya barina, Bintu tace daki rinka jawomin faɗa wajen uncle ɗinmu ai gara natafi, tace sorry bazan karaba to, hmmm zakiji dashi, muje driver cewar Bintu, . "
Lokaci shuɗewa yake duniya sauya wa take, abubuwa faruwa suke, kamar haka girman BOƊƊI yabani matukar mamaki, har cikin makaran tar aka shigar dasu suka fito gwanin sha'awa Bintu ta kama hannun BOƊƊI kowa yagan su sai yace masha Allah 🥰 Har kofar class ɗinsu Bintu takaita tana kuma mata gargaɗi pls banda faɗa kinji tace to Naji, ta shige ciki abun ta. Bintu ma class ɗinsu ta wuce,



Lokacin break Bintu tana zaune tana jiran BOƊƊI taxo don suyi break tare, saboda Ummu tace kar Bintu tayar da tayi break batare da BOƊƊI ba,.

wani yarone yaxo yace Bintu Kinga BOƊƊI ko. Tace;

"mekuma BOƊƊI tayi?

Yaron yace, tana magana aunty tana class nace zan faɗa shine tace saita dakeni, kuma ban faɗaba amma bayan Aunty tafita shine BOƊƊI ta jefar mun da home work Kuma anjuma uncle sani zai karba., tace sorry jekayi break anjuma zan kawo maka class kaji, yace to yauwa good boy,.


Ran Bintu ya ɓaci gashi har an kusa komawa BOƊƊI bata xoba. Har zata tashi sai ta hango ta, tana tahowa wata yarinya na biye da ita, Bintu tace da alamu BOƊƊI wani abun tama yarinyar nan, ai kuwa suna zuwa yarinyar tace ; Kinga BOƊƊI ta zubar mun da abinci na, BOƊƊI tace wlh karya take ni ban ganta bama, Saboda takaici Bintu ta Mike tabar abincin a wajen, BOƊƊI ne ta zauna domin cin abincin sai taga yarinyar ta zuba mata ido zabura tayi tayo kan yarinyar ai kuwa ta kwasa da aguje, nikaina abun yaban dariya, BOƊƊI kenan yar karama amma sai fitina.


Koda suka koma gida Bintu ta faɗa wa Ummu abunda BOƊƊI keyi a school sosai Ummu tayi mata faɗa ta ko nutsu tana sau raro kamar da gaske 🤪 lokacin islamiya suka shirya ba wasa domin BOƊƊI akoi son karatun addini.




Ban garen Abubakar saidai muce masha Allah domin fa abubuwa sunyi matukar kyau ahalin yanxu yanada shago na kansa a kwari market 😊

Ya ziyarci Ameenatu, lokacin daya je, Mlm haruna yayi matukar farin ciki sannan yace gaskiya Abubakar a yanxu yaka mata ka dauki matarka tunda kaima a yanxu kusan kasamu na kanka,


Hakane kam kuma dama inada niyar hakan nagode sosai bazan mance da khairin kaba agareni,.

Tareda Ameenatu suka je ƙauyen Genle, kowa yayi farin cikin ganin su, kulu taji dadin ganin Abubakar ɗinta yanda yayi kyau kamar ba wanda yafita daga Kauyeba a wannan lokacin ma saida suka tuna da BOƊƊI suka koka, ayanxu wata kila ma ƙashinta yayi fari a ƙasa,.😫 🥺 Hmmm BOƊƊI nacan tana tsula ciyar ta ajini da faɗi😄💃🏼💃🏼



Ameenatu ne tace inna kulu ya tunda na shigo banji ɗiriyar su Furera ba,, tace uhm " bakida labarin Furera Mlm Tanimu mai almajirai ya aureta tace Mlm Tanimu dai? Kwarai kuwa ayanxu tana gidansa, Ameenatu tace to ina Innar tata, Naji ance mutumin nan baida kyau ana zargin shi, kowa ya sani cikin garin nan kuma Shine tayar da, kulu tace Kinga kiyi abunda ke gabanki wannan kuma susuka sani, nima ina nan zaune Naji za'a ɗaura aure.


To Allah shi kyauta, yamma liss Ameenatu suka bar Genle, washe gari kuma sai garin Kano,
Dama Abubakar lokacin daya fara kafuwa ya sayi wani ɗan gida, karami amma kuma yanada kyau ba laifi,

Three bedroom plant da kitchen da toilet gidan yayi dai masha Allah 🥰.


Da dare BOƊƊI na zaune tana kallo, Bintu tace yau bakida home work ne?

"ni gaskiya nagaji inason nayi kallo ne, Ummu ne ta sauko rana cewa baby na kixo ga ya Sayyid zaiyi magana dake cikin sauri ta diro.................





💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼Yanxu ake Fara 💖



Comments & share pls 🥰
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/


🌀🌀 ```BOƊƊI the beautiful``` 🌀 🌀

Story & writing
By
(Z. B. M)

Yar mutan gombawa.

Marubuciyar


~~ZAINAB abuƙaya
BANI BA AUREN SOJA
NIMA DANAWA LAIFI
Sc relationships
AUTAR MOMY
And now
BOƊƊI the beautiful~


Follow me on what'sapp
09066017177
Whatpad
Zainab7177
Gmail zbala0512@gmail.com


```Bismillahi rrahmani rrahim```


_Wannan page Na baiwa fadeema sajidah 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼kyauta kiyi yanda kikesooooooo_ 💃🏼💃🏼💖🥰



PAGE 1️⃣3️⃣🔁1️⃣4️⃣


................Dirowa tayi ta karɓi wayar, ta gudu falon Abbu, fara masa rigima tayi yace; `wait beauty, let me call you video call," no ya Sayyid I don't wan't see you" yace sorry dear pls, let me call you yeah, OK " kashe kiran yayi, sai ga video call yashigo, baki ta turo gaba kafin taɗauka yafara shagwaba shi kuma sai biye ta yake yi.


Bintu dake staye tun lokacin fara wayar tasu, dariya ya kusa kashe ta don duk wanda yaga yanda BOƊƊI da Sayyid keyi saiya dara😆Bintu ta leƙo kanta "HI ya Sayyid, yace Bintu kina lfy? Kai ya Sayyid wallahi kana kara sakal ta taka,.

Kasan yanxu tsokana take yi a sch, wlh ya Sayyid BOƊƊI kowa ta da meshi yaran class nasu ba wanda Tabari.


BOƊƊI takara haɗa fuska ta tashi tatafi ko kallon Bintu batayiba Sayyid yace oh, Meyasa kika yi haka gashi yanxu kin kore ta. Maza kije ki lallabata,. Ya kashe wayar mamaki Bintu take irin shakuwar BOƊƊI da ya Sayyid,.


Ameenatu na zaune cikin farin ciki sai son barka amma har yanxu damuwa na nan a ranta,


Tana zaune a falo Abubakar yashigo yace yauwa kin shirya eh to muje ko, Asibitin Aminu Kano, suka nufa, sun samu ganin doctor akan ciwon dake damun Ameenatu ne an mata duk gwaje - gwajen daya dace, abun farin ciki an tarar tanada ciki na sati 3, farin ciki sosai Abubakar yayi, koda suka dawo bacci tayi tayi, harda mafarkin sahibarta BOƊƊI, bayan ta farka ne, ta gane ba gaskiya bane mafarki tayi, hawaye ne suka taru a idon ta, Abubakar ya shigo ɗakin da ledoji a hannun sa, saurin gogewa tayi, sannu da dawowa yace yauwa sarkin bacci, nayo mana take away ne saboda a yanxu kema zaki huta nayiwa wani abokina magana za'a samo wacce zakuna zama tare domin debe miki kewa,, tace to shikenan nagode, dan Allah dama inaso na rinka fita waje kozan Saba da garin, shine nace tunda naga akoi Islamiyya tanan sai na shiga, yafi zama haka, yace kuma gaskiya kam, amma keda yanxu kina juna mezai sa ki wahala, amma tunda kinaso hakan za'ayi, dariya tayi tareda godiya.


Cikin ikon Allah Ameenatu ta cigaba da renon cikin ta tana zuwa islamiya, ansama mata yarinya wacce take taya ta aikace aikacen gida, Allah yakawo mu, lokaci Ameenatu ta sauka lfy, baby ta haifo har biyu kyawawa mace da namiji murna sosai Abubakar yayi,.



BOƊƊI ta cigaba da rayuwa cikin aminci da kulawar Ummu, " yanxu Bintu tashiga ss, BOƊƊI

Please Login or Register in order to submit comment