Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigo dasu a wata qatuwar Leda dake dauke da tambarin wajen dinki

Kallansu yake bugun zuciyarsa na qaruwa β€’daa souban yasan yanda zuciyarsa ke bugu da be kaawo masa wadannan kayan yana masa wadannan maganganun bβ€’

Fararen shadda ne dall masu tsada da kyau , sun sha aiki me kyau , da hula zanna wadda dinkin dake jikin shaddar iri 1 ne da hular

Shaddar iri 1 ce sedai aikin jikinsu kawai ya banbanta wanda hakan ne kawai ze alamta maka cewar wannan na ango ne wannan bana ango bane

Souban yana murmushi yace

" Ya ka gansu ?

Duk wata jarumta tasa ya tattaro kana ya qaqalo murmushi ya dora a kyakykyawar fuskarsa sannan yace

" Sunyi kyau sosai ango !

Souban da kana kallansa zaka San yana cikin tsananin farin ciki ya kalli arman

" Godiya nake yayan amarya kuma aminin ango "

Se kawai yaji ya kar6i sunan daya kira shin amma se yace

" But ka ajje kayan nan akwai wadanda zan saka babu buqatar wadannan "

" Amma in kayi min haka baka kyauta b arman , kuma ba zanji dadi ba " ya fada yanayin fuskarsa na sauyawa

Seda souban yayi da qyar sannan arman ya yadda ze saka kayan nan .

........A daya 6angaren kuwa dakin amrah en mata ne cike a ciki kowacce da abinda takeyi

Amarya Sanah na daga gefen gadon amrahn jikinta a matuqar sanyaye saboda yau kam fargabar ta tafi ta kullum

Xataso ace yanzu haka mamama na kusa da ita ne ta samu ta dora kanta a kafadarta ko cinyarta dan tayi kuka ko zuciyarta zata samu sassauci ta rage wannan fargabar da takeji

Cikin en uwansu wata daga cikin en matan tace

" Amarya fa jiki ya faara sanyi tun kafin a daura "

Wata ta kar6e da fadin

" Ke kuwa ba dole ba , igiya uku fah !!

Se dukkansu suka saka dariya

Ita kuwa seta janye qafafunta daga qasa tana turo baki kamar zatayi kuka ta haye kan gadon tayi kwanciyarta .


A 6angare guda kuwa ana can ana shirye shiryen tafiyarsu Los angeles da zarar an daura aure , sedai hakan baze yiwu ba dole sedai su bari washe garin daurin aure su tafi .




Second ni suka hadu suka bada mintuna haka mintuna suka hadu suka bada awanni su kuma awanni suka bada rana.....

Kamar yanda ake cewa rana bata qarya sedai uwar diya taji kunya hakance ta kasance yau dinnan .

31st December...

Ranar juma'a kenan ranar data ke dauke d dumbin tarihi tarihi kala kala

Ranar data taara abubuwa wadanda baza su lissafu ba wadda saboda abubuwan data taara mutane da dama ba zasu ta6a mantawa da ita ba a cikin kundin tarihin rayuwarsu .........


Ku dai kawai ku cigaba da kasancewa da alqalamin Innocent dan jin yadda zata kasance πŸ˜‰

Amma pah hakan duk ba zata kasance ba se naga comments naku masu zafi wanda kuke bayyana min ra'ayoyinku , in ba haka ba toh gskia gobe babu update

Mhiz Innocent ce.........✍️


*β™‘β˜†A ZURI'AR ARABβ™‘β˜†* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

πŸ’–THE TALENT TROUPE WRITER'SπŸ’–

Page 28_29

*_THE MOST AWAITED PAGE* πŸ˜‰βœ…

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES πŸ˜πŸ‘Œ Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e


...........Sanah na dakin mamama fitowar ta kanan daga wanka

Afrah ta miqa mata kayan da zata saka tace

" Kiyi maza ki saka kayan kinsan dai lokaci tafiya yake se wani abu kike kamar mara laakaa jiki "

Jan kayan tayi tana kallansu sannan ta saka

Atampha ce dinkin riga d zani sun matuqar amshe ta

Amrah ce ta zaunar da ita ta mata simple dauri bayan ta shafa powder d lip gloss se kwalli wanda dama ta saba sakashi koda yaushe sannan ta yafa mayafi akanta

Ba qaramin kyau tayi ba seta fito a amaryar sakk tayi mugun kyau kamar wata zinariya se walwali take

Amrah tace

" Awwwn Mrs souban to be soon ! U look so take away "

Murmushi Sabah tayi wanda ya qara fito da ainihin kyawunta

Suna nan zaune afrah na sanya mata abin hannu yayin da amrah take daura mata sarqa , suma duk sunyi shiga me kyau a matsayin su na aminan amarya kuma en uwanta sunsha ado dan suma duk sunyi lalle d fulawar .


.......Kallan kayan ya sakeyi a karo na barkatai sannan yaja tsaki yana tunanin yadda ze saka wadan nan kayan , hadda wata babbar riga , toh ko shine angon ai se haka

Yasan yanzu haka souban ya shiga busy daze sameshi ne seya fada masa baze saka ba

Toh sedai tun dazun daya fita taho da abokansa har yanzu be shigo ba , shiyasa kawai ya yanke shawarar saka rigar kawai banda babbar riga

Seda ya taje kwantacciyar sumar kansa dake ta tashin qamshi sannan ya saka kayan , ya dakko hula zanna ya dora ta akansa

Turaren san nan dai na ko yaushe ya dakko ya saka , se kuwa dakin ya gauraye da qamshinsa me sanyi , sannan ya sake kallan kansa a mirrow , yayi matuqar kyau kyau me suna kyau , kai badan kar ace yabon yayi yawa ba da se nace " daga kyau aka nuna arman an tashi "

Kasancewar shi din ba ma'abocin saka manyan kaya bane se hakan yasa ya fito wani daban dashi yayi mugun kyau , sedai fuskarsa sam babu walwala dan a dinke take tsaff kamar wanda akama mutuwa

Madaidaicin agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya kalla qarfe 1:00pm ya nuna

Dai_dai lokacin da wayarsa tayi twuwwa , da Saudi ya daga yana Neman waje ya zauna

" Slm Alaik daddy "

Can 6angaren daddy y amsa kafin yace

" Kana ina ne yanzun ?

" Ina cikin gida " ya fada a ladabce

" Toh ka fito mu hadu a masallaci ana idar da sallah za'a daura auren " daddy ya fada

" Toh " kawai ya iya furtawa yana miqewa

Wayar tasa kawai ya dauka ya fice daga part din nasu

Yana shirin fita shi kuma imam na shirin shiga

Seya dakata suka gaisa kafin imam yace

" Pls ka jira ni mana yanzu zan fito nayi mantuwa ne "

" Ohk " arman ya fada yana yin gaba ya wuce parking lot

Mintuna 3 sega imam din ya fito , suka tafi a motar imam din shi yake driving yayinda arman ke zaune a wajen me zaman banza

Tunda suka fara tafiya ba wanda yace uffan

Se can imam ya katse shirun ta hanyar fadin

" Ashe ka dawo ?

Se yaji tambayar kamar rainin hankali amma se yace

" Yeap ! Jiya da dare "

Jinjina kai imam yayi yana cigaba da driving har suka isa masallacin na B.U.K .


Qarfe 2 dai_dai aka idar da sallah sannan aka fara shirye_shiryen daurin aure

A hankali y sulale daga cikin masallacin zuwa waje dan ya samarwa kansa peace of mind .

Har yanzu mamaki yaqi barin Abba na ganin har qarfe 2n souban bezo masallacin ba

Dan haka ya dauki wayarsa ya kira , sedai tana ta ringing ba'a daga ba

A'ah tunfa yana daukar abin a matsayin shiriritar souban har ya fara mamakin abinda ya hanashi zuwa har yanzu , dan kuwa biyu da Rabi ma ta kusa ( Allah yaso akwai wasu daurin auren se aka fara daurawa )

Toh abba na nan sega kiran souban din

Abba ya daga da sauri kuma yana fadin

" souban wane irin shashanci ne wannan da zesa har yanzu baka iso ba ?

Can 6angaren souban ya numfasa cikin sanyi yace

" Abba abinda yasa na kaasa zuwa wajen daurin auren nan , Abba bansan da wane irin ido zan kalleku na fada muku na faasa auren Sanah ba !

Abba ayi haquri a gafarceni amma bazan iya auren sanah ba bisa wasu dalilai na "

Suman tsaye Abba yayi kaana ya sauke wayar daga kunnensa ya duba , gashi nan dara_dara sunan souban ne akai amma danya qara tabbatarwa se yace

" Souban ?

" Na'am Abba ! A gafarceni don Allah "

Shikenan souban din ne kenan

" Ya salam " Abba ya furta yana Neman waje ya zauna cike da zullumi bayan katsewar wayar

Baba,daddy suka qaraso wajen suma sunsha bluen shadda duk iri 1 da babbar riga sun fito sakk iyayen amarya da ango

Baba yace

" Abban souban wai me yake faruwa ne ? Lafiya dai koh ?

Seda ya dawo daga shock din da maganar souban din ta jefa shi sannan ya fada musu abinda ya faru

Shiru duk sukayi kowa da abinda yake saqawa a ransa kafin daddy yayi qarfin halin fadin

" Kaaga baze yiwu a biye ta yaran nan ba ! Ai ba dole se yana nan za'a daura auren nan ba , kawai muje a daura in munje gida se asan yadda za'ayi "

" Me ? Inji Abba

" Ni souban ze maida qaramin mutum ? Toh wlh yayi was kansa tun farko shiya nemi auran sanah yanzu kuma yace baya so saboda haka an soke maganar nan !

Baba yace

" Ayi haquri dai a duba lamarin "

Abba ya dawo da dubansa wajen baba yace

" Wai baka gani ba saboda raini ni ya kira a waya ake fadawa ya faasa auren wai a bisa wasu dalilansa , dalilansa na banza , dalilan da basu tashi bayyana ba se ranar daurin aure ? Toh kuwa souban ze gaane wanene ni bama shi kadai ba wlh ! INA IMAM ???

saga haka suka dunguma zuwa wajen brigadier general Yusuf Arab da yake waje shima saboda wani daurin auren da ake gabatarwa a ciki

Sojoji a zagaye da baffan riqe da bindigu a hannunsu suka qarasa

Sosai Abba yayiwa baffa bayani sannan suka tattauna sosai dan kuwa seda suka kai wajen qarfe 3 kafin suka gama


Daurin auren da aka saka qarfe 2 se bashi se 3 za'a daurashi ,

Seda suka shiga wajen limamin daze daura auren shima sukayi magana sannan .

6angarensa kuwa tun yana haquri harya qosa haba ya gaji , qarfe 3 na shirin yi amma Abu yaqi ci yaqi cinyewa ? Se kace masu shirin aurar da duk en danginsu

So yake ya sulale yabar masallacin amma hakan baze yiwu ba tunda akwai idon daddy .

Qarfe 3 dai_dai dubban mutane suka shaida daurin auren SANAH ALQASEEM ARAB da ANGONTA akan sadaki naira dubu 100 .

****6angaren amarya kuwa yanzu haka tana cikin wani rantsatstsan less ne me kyau aji da tsada tayi matuqar kyau tamkar ka sace ta ka gudu

Dai_dai lokacin da agogon dakin ya harba qarfe 3:30 kuma a dai_dai sanda wata er uwassu daddy ta shigo dakin tana guda

" Aure ya dauru , sanah ta zama matar souban ?!

Se kuwa gidan dama dakin ya dauki shewa da guda anayi ana qarawa cikin farin ciki yayin da dubban en uwa aka fara sanya alkhaeri akan auran .


....Zagaye dakin kawai yakeyi dan kuwa tun dazu ya qagu ya dawo gidan

Mintuna 10 sega mama ta shigo dakin cikin wani dandasheshen less me arnen kyau

Da wani irin kallo Abba ya bita dashi

Cikin fara'a tace

" Ahh Abba Ashe kun dawo......"

Kafin ta qarasa ya katseta da fadin

" Ya isa haka ! Kinyi abinda kikeso akan danki , kinso ki wulaqantamu a idon jama'a ! Toh na barki da ikon da kika nuna akan danki , amma sedai ki sani nima zan nuna miki iko na akanki saboda haka ki jira sakamakonki da zarar an qare bikii ! Sannan ki dauki waya ki kirashi yazo taron da za'a gabatar yanzu haka a parlourn baffah "

Daga haka ya fice

Ita dai tunda ya fara magana kallansa kawai take Sam ta kasa fahimtar inda zancen nasa ya dosa , haka ta bishi da kallo kamar wata sokuwa harya fice .


..........Gaba 1 duk Wanda yake ko take a cikin zuria'ar Arab toh yana cikin parlourn baffan


Mutane da dama sunyi mamakin hada wannan taro haka bagatatan ana tsaka da taro

Abba ya kalli mutanan dake parlourn yanzu ma babu souban , girgiza kai yayi cike da fushi

Imam ne ya gabatar da addu'a kana duk aka shafa

Kapin baffah ya fara magana

" Toh dalilin daya saka aka shirya wannan taro cikin gaggawa haka shine akan wata 6araka data taso yau din nan a cikin zuri'ar na

Shiyasa a matsayinmu na manyanku sannan ga iyayenku nan zaune , a matsayinmu na wadanda zasu iya za6a muku abinda baze cuceku ba shiyasa muka magance abin tun a wajen "


Nan yayi musu taqaitaccen bayani akan abinda ya faru sedai yaiwa wasu abubuwan kwaskwarima gdun lalacewar zumunci sannan ya qaare da fadin

" Toh ahmadu ya kaawo maganar a bawa imam auranta sedai kuma bamu ta6a ji imam yayi zancen yana qaunar sanah na , toh ni kuwa na riga nasan soyayyar da arman yakewa sanah a dalilin hakan ne yasa na yanke wani hukunci !
!


Imam kallan baffa kawai yake , anya kuwa wannan tsohon be faara shan qwaya ba ? Ya tambayi kansa yana qara tattara duk nutsuwarsa zuwa wajen baffan dan jin cigaban bayaninnasa

" Saboda haka shi souban muna masa fatan samun wata yarinyar ko a cikin familyn nan ko kuma a waje amma yau kam an daura auran SANAH ko kuma nace an riga an bawa ARMAN auranta !!

Besan sanda y dago yana kallan baffa ba ido cikin ido

Wai meyasa mutanan gidan nan suke neman haukata shi ne ?

Don Allah a dena masa irin wannan wasan wlh baya so sam , Idan ba so suke su tarwatsa masa xuciya ba


Sake kallan duk en wajen yayi

" ehh tabbas iyayensa ne kuma yasan babu wasa tsakaninsu amma tabbas yau kam sunyi masa wasa wasan da idan basuyi sauri sun fada masa cewa wasa bane xiciyarsa na dab ta tarwatsewa....

Tabbas tasan kunnuwanta ne basu jiyo mata daidai ba

kawai ta saki wani murmushin gefen baki kapin ta maida hankalinta wajen manyan gidan dan jin wanda suka xa6a mata a matsayin miji tunda ga abinda souban yayi mata

Se kuwa tajiyo baba yana fadin

" Qwarai kuwa an daura auren ARMAN da SANAH !!


Ji tayi kunnuwanta suna barazanar dena ji gabadaya duk da hearing aid din dake kunnanta

Idanuwanta sun makance , qwaqwalwarta tana neman tarwatsewa , zuciya ta tsaya cak ta yadda ta dakata da aikinta na wucin gadi

ji tayi numfashinta na barazanar daukewa ta yadda seda taja wani irin numpashi kapin ta faara dawowa hayyacinta


Dama yaya ze iya auran qanwarsa ne ? Ko kuwa dama can ana iya yin hakan ?

Toh ae ko maguzawa banjin xasu aikata hakan ? Me yake faruwa ne ? Me yake shirin faruwa ? Suna cikin garin musulunci cikin musulmaei shine aka aikata wannan kwamacalar ? Ta yaya ? Ta yaya ma dan uwa ze auri wadda suke uwa 1 uba 1 ? Wae menene haka ne ?

In mafarki take zataso ta farka daga wannan mahaukacin mafarkin da bashi da kae ballantana qafa .



Tun daga zancennan bata sake fahimtar komae ba

tabbas tasan magana sukeyi amma ji take kamar wani yaren da bata fahimta sukeyi.

Shin wannan wace iriyar rayuwa ce da za'ayi haka ? Anya ba xata daga ido ta saka masa kwalli ta fada wa iyayennata hakan da suka aikata ba daedae bane ? hakan ya wuce maguzanci ?

Tabbas tasan duk cikinsu suna da ilimi amma ko ba'ace komae ba tasan yau sunyi fatali da wannan ilimin nasu akan wannan son xuciyartasu ,

Wani dumm taji kanta yayi a hankali ta faara ganin wani duhu na gitta wa ta saitinta se kuwa ta tafi luuuu cikim ficewar hayyaci ta fadi a wajen sumammiya ...........

Zuciya tah ke tayyo za6i so ya wuce wasa , zo mu zauna tare kizam abokiyar tarayyata πŸ˜ΉπŸ’ƒπŸ’ƒ

Toh ya update din yau ?Ina jiran comment naku 😻

Daga alqalamin mhiz Innocent........✍️



*β™‘β˜†A ZURI'AR ARABβ™‘β˜†* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

πŸ’–THE TALENT TROUPE WRITER'SπŸ’–

Page 30

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES πŸ˜πŸ‘Œ Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e


..........Ba Sanah kadai maganar ta ta6a ba , kafatanin en dakin in ka cire manyan mazan gidan

Cikin mamaki kowa ke kallan baffahn dake magana

Mamama kuwa da wani irin sauri bugun zuciyarta ya qaru

Cikin wani irin yanayi dana gaza fahimtar farin ciki ne ko akasinsa ?

Wasu sanyayan hawaye ne suka zubo a kumatunta " ita kam me zata cewa Allah ? Babu abinda zatayi se godiya ga Allah buwaya gagara misali , dan kuwa shi kadai ke iya chanja abu a lokacin da yaga dama "

Hannu ta saka ta goge hawayen ,wani sassanyan murmushi na bayyana a fuskarta .


......Kansa gaba daya ya kulle , komai ya xakude masa , ya rigada ya gama tabbatarwa kansa wani yaudararran mafarki yake yi , mafarkin da yake neman yaudararsa , ya qagu ya farka kafin abin yayi nisa ta yadda inya farka baze iya jurewa ba

Kai zeso ace akwai wanda yake a kusa dashi ya bashi hot slap ko ze farka ! Sedai har yanzu shiru , yaqi farkawar sannan wani yaqi tashinsa

" Oh my god " ya fada yana dafe kansa kuma a dai_dai lokacin ne sanah ta zube a wajen a sume .



******8:40pm

Kuka take tamkar ranta ze fita dan tun dazun take so ya fito amma se yanzu ta samu wannan damar

Mamama kuwa shafa kanta kawai take ba tare da tace komae ba

Dan kanta ta gaji ta dago ta kalli mamama tana sheshsheqar kuka

" Mamama dama yaya ze iya auran qanwarsa ne wadda suke uwa 1 uba 1 ?

Mamama se tambayarku nake kunqi bani amsata bansani ba koni banda wannan ilimin ko ilimi na bezo wajen ba shiyasa bansani ba

amma nidae a islamiyyar da kuka sakani mamama yaya baya auran qanwarsa " ta qarasa maganar tana sake fashewa da kuka me cin rai

Janyo ta mamama tayi jikinta muryarta a sanyaye tace

" Kiyi shiru haka sanah kukan ya isa haka ko se kin sanyawa kanki ciwo ne ?

Bata iya cewa komae ba illah kukan dake fita a hankali

Mamama ta cigaba d fading

" Ki tashi kije kiyi wanka kiyi bacci anjima in Allah ya kaimu xamuyi maganar ohk ?

Da kanta mamaman ta hada mata ruwa me dumi tayi wanka bayan ta cire hearing aid dinta sannan ta zura doguwar riga Mara nauyi da hula ta kwanta

Mamama taja mata blanket tana cewa

" Bana son kuka kinji koh kiyi bacci cikin nutsuwa uhmm ?

Gyada mata kai tayi wasu kyawawan hawaye na xubo mata kan fuskarta

Tayi sauri ta goge su tana kwanciya duk da tasan qarya take bacci ya iya daukar ta a irin wannan lokacin .


Mamama ta koma wajen baqin ta da basu gama watsewa ba wadanda suke en uwa na kusa kenan .


....Tunda akayi taron nan Maman souban bata sake samun nutsuwa ba , gashi dai tana da baqi amma ta rasa wane tunani ma ya kamata tayi ? Abba da souban suna neman su haukata mata qwaqwalwa ! Ita kam ya zatayi ???


************** " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un "

Shine kawai abinda zuciyarta keda qwarin furtawa

kallan Mamama kawai take da take mata magana

" Mamama ba itace mahaifiyarta ba ? Mamama yaya ce a wajen mahaefiyarta ? How ? Can't believe cewa ba Mamama ce ta haefe ni ba

Duk wata kulawa daya kamata uwa ta bawa erta ta bata

Duk wata hidima d uwa zatawa erta Mamama ta mata

Duk wata soyayya da uwa xata nunawa erta Mamama ta nuna mata !

Daddy pah ? Yanzu daddy bashi ne mahaifi na ba ? Shin wannan wane irin 6oyayyen sirri ne da yake a cukurkude be warware ba se yanzu ?

Shin gaskiy ne abinda ke faruwa ko kuwa har yanzu bata farka daga shashashan mafarkin da take ba ?

" Nop ! dis is reality fah sanah ya kamata ki gaane cewa duk abinda ya faru yau gaskiyane ! Xuciyarta ta raya mata hakan

A hankali ta tashi ta qarasa kusa da Mamama ta kama hannunta

" Mamama kin dauke ni kamar erda kika haifa , kin bani duk wata kulawa data kamata uwa ta bawa erta

Mamama ban ta6a kuka a dalilinki ko daddy ba ku din har abada zaku cigaba da kasancewa a matsayin iyayena ne "

" Shttttttt !! Mamama ta fada tana dora yatsanta kan bakinta

" Bana son shashanci sanah ! wannan maganar ba dan zancen aure ya biyo ba baza'a ta6a tona ta ba har abada

kuma wato yanzu da kika gano gaskiyar lamarin shine zaki daukemu a matsayin iyaye ? Bama a iyayen ba ?

Sanah tace

" A'ah Mamama abinda nake nupi kenan "

Seda ta numfasa kadan kapin ta cigaba d fadin

" Mamama ku din na daban ne a rayuwata ina matuqar qaunarku " ta fada tana fadawa jikin mamaman tare d@ fashewa da kuka

Daddy dake tsaye tun dazun ya qaraso ya zauna gefen kujera yana murmushi yana kallansu

Seda tayi me isarta sannan ta taaso ta zauna gaban daddy ta kaamo hannunsa kana a hankali muryarta a shaqe saboda kukan da tayi tace

" Daddy a dukka rayuwata bani d kamarku nagode Allah ya saka da alkhae.... "

" Y@ isa haka mana sanah " daddy y katse ta

" Shin har yanzun baki ji me mamanki ta fada bane ? karki sake gode min kinji koh ? har yau har gobe ke 'ya ta ce kuma hakan baze ta6a chanjawa ba sedai Idan ke kika chanja ”

Da sauri ta girgiza kai wasu hawayen na sake xubo mata

Daddy yace

" Kiyi haquri Sanah nine na bawa baffah amanna akan wannan auren , ba dan haka ba da yanzu baki zubar da hawayenki ba !


" Don Allah daddy ka bari ! Daddy in kana bani haquri se naga kamar ka cireni a sahun 'ya'yanka ne ! Don Allah ka bari " ta fada cikin kuka

" Shikenan toh ya isa haka kinji koh bana so na sake ganinki kina kuka uhmm ?

Gyada kai tayi tana murmushi hade da share hawayenta .

Daddy ya miqe mamama ta rakashi da addua ya fita

Ita kuwa sanah komawa tayi kusa d mamama ta dora kanta kan cinyar mamaman tana sauke numfashi a hankali

Itama mamaman se yanzu ta samu damar zub da hawayen ta dan tuna er uwatta da tayi tana kuma sake godewa Allah akan wannan al'amari

a hankali itama take kukan tana me shafa kan sanah dake kwance shiru ta fada duniyar tunani

Cewa fah akayi an daura aure na da baby ? Ta yaya ma zata iya rayuwar aure da baby ? Mutumin data dauke shi a matsayin yayanta wanda suke uwa 1 uba 1 yanzu shine ake mata zancen shine mijinta ?

" Wayyo Allahna ! Ta fada akan la66anta wasu hawayen na gangarowa daga idanunta zuwa kan fuskarta

Baby fah ? Ita kam ya zatayi da ranta ne ?

Amma fah wadannan ana magana ne akan mutanan nan da bata da kamarsu a duniyarta sune suka xa6a mata baby a matsayin miji , wanda har abada kome suka sakata ba zata iya yi musu musu ba ?

Idan kuma ta musu musu kenan sunanta ze koma butulu ? Bata jin zata iya aikata wannan abin ? Kai bama mamama ko daddy ba bata jin a cikin manyan mazan gidan babu wanda ze bata umarni ta bijire mishi , ballantana kuma daddy mutum me matuqar halacci a gareta mutum me dattako wanda tunda ta tashi a gidan be ta6a yin wani abu daze nuna bashi ya haife ta ba.

Amma ba wannan ce matsalar ba yanda zata zauna da baby a matsayin mijinta shine abin dubawar

Yah souban ? Kanta ya kulle ballantana ma tayi tunani akan abinda yasa ya faasa auranta , wane laifi ta masa ? Wane irin babban laifi ta masa haka dabe tashi fasa auranta ba se ranar daurin aure ? Shine yah souban yana cikin mutanen da suke so su tozarta ta ne ko kuwa dai meneeeee ?

Ta runtse idanunta da suke mata wani irin zugi tana yin iya kacin qoqarinta dan kar kukannata y fito fili............

Kuyi manage d wannan pls wlh bani d charge ne shys


Ku cigaba da kasancewa da alqalamin Mhiz Innocent dan kuwa akwae dramer nan gaba πŸ’ƒ hade da cakwakiya


Mhiz Innocent ce...........✍️



*β™‘β˜†A ZURI'AR ARABβ™‘β˜†* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻
πŸ’–THE TALENT TROUPE WRITER'SπŸ’–

Page 31

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES πŸ˜πŸ‘Œ Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e


Not edited

..........Daddy ne yayi qoqari wajen shiga da fita akan chanjawar tafiyar souban xuwa arman , dan haka tunda ya bar gidan ranar daurin auren be daawo ba

Please Login or Register in order to submit comment