Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka tsaya , wannan ba lokacin wata maganar bane "

Dariya black ya sheqe da ita kana yace

" Toh mu kuma wannan lokacin ne kawae damu ! Kasan meyasa muka kawoka ka nan ?

Souban ya karkata kansa alamar yana ji

" So muke ka faasa auren matar da zaka aura yau din nan "

Dariya souban yayi kana yace

" Sorry wace mata kenan ?

" Sanah ! Black ya bashi amsa da sauri

" Impossible ! Wait a cikinku ma wae waye ne yake so in bar masa ita ?

Dayan dake kusa da black yace

" Ogammu ne , karka bari ya bayyana a wajen nan ba tare da ka amsa wannan buqatar ba "

" And so ? Souban ya fada yana kallansu su duka

" Kaaga barrister ! Rashin kunyar ka ta faara yawa fah , ka sani wani matsayin ka ba zeyi amfani a wajen nan ba , kawae kayi biyayya shine abinda ze ceceka in kuma ba haka ba zakayi nadama " black ya fada a kufule dae_dae lokacin da wancan ya fita daga dakin

Wajen minti 2 se gashi ya dawo riqe da wayar souban din a hannunsa dae_dae lokacin da Abba yake kiransa lokacin da suna masallaci

Black ya kar6i wayar ya miqawa souban yace

" Kar6i ka daga wayar ka fada musu cewar ka faasa auren !

" Baze yiwuwa ba ! Souban ya fada

A fusace black yayi kansa da kan bindigar ya kwada masa a gefen kansa ya qara fadin

" Kar6i ka fada musu Cewar ka faasa auren nan "

Souban ya sake girgiza kae yana riqe da gefen kansa

Dayan da suke tare da black ya kaewa souban naushi a hanci and lokaci guda yana kae masa a ciki

Haka suka hadu su duka suka dinga dukansa kamar wadanda aka aeko sannan black ya sake cewa

" Zaka fada yanzu ko kuwa sena fasa qwaqwalwarka ?

Shiru souban yayi yana nazari , yasan idan be fada din ba zasu iya kashehi a banza , toh kuma idan ya fada din yasan daga can 6angaren za'a fasa auren ne

Toh wannan ce kawae mafita in yaso idan ya koma seya fada musu abinda ya faru , yasan idan hakan ta faru toh za'a daura musu auren su a nutse

Daga nan kuma seya binciko wadannan shashashan yayi maganinsu

hakan ce ta sanyashi fadin

" Ehh "

Black ya danna number abban kira 1 ya daga

Nan ne inda souban yake fadawa abba ya faasa auren , toh abinda yasa souban yace ya faasa ne a bisa wasu dalilansa , yasan wannan kadae ya isa abinda zesa a jirashi aji menene dalilan nasa ????

Daga nan basu sake azabtar dashi ba , yana dae zaune a cikin dakin , zasu kawo mishi abinci da ruwa da sauran kayan buqata

Se kuma ranar da sukazo suka bude masa qofar ya fito daga gidan zuwa gida....

Shiru dakin ya dauka na wajen mintuna 10 babu wanda ya iya cewa komae , kowa da abinda yake saqawa a ransa

Cikin matuqar tausayi gami da mamaki kowannensu ke kallan souban din sanda yake baada wannan labarin

Abba dake zaune a qaramar kujerar parlourn yayi shiru hannayensa riqe da juna a ha6arsa

Be ta6a tunanin haka abin yake ba , be kawo ba haka zalika beyi zaton haka al'amarin ya kasance ba , meyasa yayi gaggawa ? Ya tambayi kansa

Baffah yayi gyaran murya cike da dattako shima muryarsa a hankali da alama labarin ya tsuma shi yace

" Souban !

Souban ya daga kae ya kalli baffah sannan ya maeda kan nasa qasa kafin baffah ya cigaba da fadin

" Wato duk abinda kaga ya faru da dan adam toh dama can rubutacce ne a cikin littafin qaddararsa , saboda haka ka riga da kaasan cewa daya daga cikin cikon imani hadda yadda da qaddara ta alkhaeri ce ko akasinta "

Duk souban yasan wannan hakan yasa ya gyada kae , amma se yaji kamar ba zancen kenan ba , dan yaji kamar maganar tayi ta kumayi alaqa da kuma baudewa da abinda ya faru dashi , amma seya cigaba da jin abinda baffahn yake cewa

" Saboda haka abinda zamu ce shine Allah ya kiyaye ya kuma tsare gaba "

Abinda souban yake da buqatar ji kenan , Dan haka yace

" Ameen " shi da ragowar da suke cikin dakin

Baffah ya cigaba da fadin

" Sannan muna me baka haquri souban , a bisa wadannan abubuwan da suka faru mun daurawa Sanah aure da Arman !!!

Cikin wani irin yanayi dana kaasa tantancewa souban ya dago ya kalli baffah cikin ido abinda be ta6a ba kenan , ya cigaba da kallan nasa ba tare da ya dauke ba , Dan kuwa so yake ya hango wae wanene ma yake maganar ne ? Ko bayan tafiyar sa baffah ya haukace ne ? Ko kuwa shaye shaye ya fara ?

A hankali ya maeda dubansa ga ragowar da suke dakin yana so yaji sun qaryata abinda baffahn ya fada , sedae yaji shiru , babu wanda ya tanka , Me suke so su ce masa ne ?

Abba dae ya kaasa cewa komae Dan kuwa tausayin Dan nasa ya gama kashe masa jiki

Baba ne yayi qarfin halin fadin

" Qwarae kuwa souban ! Kayi haquri mun riga mun yanke hukunci cikin fushi ba tare da bincike ba a lokacin muka daurawa Sanah aure da Arman "

" Ina ! Baze ta6a yiwuwa ba ! Abba ashe ku da nake tare daku ma kun kaasa fahimtar wane ni , toh su wane zasu fahimce ni ? Baffah meyasa kukamin haka ? Meyasa baku tsaya kun jira na dawo kun tambayeni dalilina na fasa auren nan ba ? Meyasa zaku aurar da sanah zuwa ga wani na ? Meyasa bakwa son gani na a cikin farin ciki ? Meyasa kuka za6i ku tozarta soyayyar da muka gina ta shekara da shekaru ? Meyasa bakuyi tunani akan irin soyayyar da nakewa sanah ba ? Meyasa bakuyi tantama akan magana ta ba ? Me....."

" Souban ! Abba ya fada cikin daga murya yana kallan souban da yake magana cikin rufewar idanu

" Souban ashe baka da kunya ? Mu kake fadawa haka ?

Se a lokacin tunanin souban ya dawo , ya gane tukunna ma da wadanda yake tare " Iyayena ne " ya tunasarwa kansa

" Ya Allah ! Ka farkar dani daga wannan mummunan mafarkin da nake dan zuciya ta rana dab da tarwatsewa " ya fada a ransa .


*_Los Angeles_*

...........Kwanansu 2 a asibitin bayan yi mata aekin sannan aka sallamesu .

Ranar da suka dawo wajen maghrib ne dan haka kae tsaye daki suka wuce

Shine ya fara yin wanka , sannan ya fito ya shirya

Tana zaune akan gadon inda ya barta , sedae yanzu ta kishin gida ne

A hankali ya qarasa wajen yace

" Ki tashi kiyi wanka uhmm ?

Turo baki tayi tace

" Ni bansan tashi , na gaji "

Murmushi yayi yace

" Ae baki da damuwa ! Lem me help u " ya fada yana qoqarin daga ta

Da sauri tace

" A'ah ni fa ka bash shi "

Yace

" Nooo , pls kina buqatar taemako , ki barni na taemaka miki "

" Ni fa bana so " ta sake fada tana turo bakin dae

Ya bita da kallo yana lumshe ido

Tayi wanka ta fito cikin doguwar riga me dan baby hijab , tayi matuqar kyau kamar er tsana ya bita da kallo sanda take qoqarin ficewa daga dakin

So samu ne yanzu haka ya janyo ta jikinsa ya rungume , toh so yake ya bita a hankali a hankali harta saba dashi a matsayin mijinta ba yayanta ba shiyasa yake binta a sannu a sannu

Kae tsaye parlour ta fice ta zauna a kujera kana ta dauki remote control ta kamo MBC Bollywood ta faara kalla

Seda ya zauna yadan danna wayarsa sannan ya fito parlourn bayan yayi sallah

Tana zaune akan kujera me 3sitter hankalin ta akan t.vn

Ya qarasa wajen t.vn kamar yadda ya tsammata kuwa film take kalla

Kae tsaye ya wuce kujerar da take kae ya zauna yana maeda hankalinsa kan t.vn

Bata kulashi ba dae ta cigaba da kallanta har wajen qarfe 10

A hankali taji wani bacci me dadi yana sakadarta , hakanne yasa ta fara lumshe dara_daran idanunta

Ganin haka ya sanyashi matsowa kusa da ita , ita kuma ta samu damar Dora kanta a kafadarsa tana sake lumshe idanun

Ganin haka ya sanyashi gyara mata kwanciyar zuwa kan cinyarsa

Ita kuwa ta gyara kwanciya hankali kwance abinta ta faara baccinta cikin kwanciyar hankali shi kuma ya cigaba fa kallon , lokaci _ lokaci yana kallanta

Se da ya tabbatar baccin ya dauketa sosae sannan a hankali cikin nutsuwa ya daga ta cakk zuwa kan gado , ya gyara mata kwanciyar ta , sannan ya ja mata blanket zuwa sama

Kae kallansa yayi zuwa cute face din ta dake qara kyau idan tana bacci gashi tayi wani fayau da ita

Besan sanda ya saki wani qayataccen murmushi ba sannan a hankali ya kae bakinsa saman goshin ta ya bata light kiss , sannan ya gangaro zuwa hancinta shima ya bata kiss , se yaji kamar ana jansa zuwa bakinta , ya kae dubansa zuwa ga dan qaramin cute pink lips din ta , data turo shi gaba kadan kamar zatayi kuka , a hankali ya fara qoqarin bata kiss din dae_dae lokacin da tayi juyi ta chanja 6angaren data kwanta

Seya janye jikinsa da sauri gudun karta tashi yana murmushi , yana tunanin duk lokacin daya ta6a bakin nan yasan akwae rigima ranar .



.........Washe_gari qarfe 12:00 tana zaune a parlourn cikin rashin sanin abinyi tana jiran dawowarsa kasancewar ya fita ne

Se taji ana knocking din door , da mamaki ta kalli qofar tana mamakin abinda ya saka shi knocking din qofa yau , bayan yana da key a hannunsa

Mamakin nata ne ya katse sanda taji ana sake knocking din

A sukwane ta qarasa qofar , tunda tasan babu wanda zezo gidan nan idan bashi ba yasa kawae ta bawa kanta amannar shi ne , dan haka ta bude qofar kafin ta kalle shi ta juya cikin parlourn

Se dae me ? A tsakiyar parlourn itama ta tsaya tana kalle kalle , sanye take cikin doguwar riga baqa wadda take iya gwuiwarta , ta zubo da milk din gashin da bashi da yalwar tsayi , qafarta sanye da wani hill shoe shima baqi

Se aka faara kallan kallo tsakanin su

Catherine na mamakin irin baewar kyau da Sanah take dashi , haka zalika ta kaasa gane a wane yare ko qasa zata ajje sanah din ?

Cike da qarfin halin hali Catherine tace

" Me kikeyi a cikin gidan nan ? Ta fada cikin harshen turanci

Cikin mamaki sanah take kallan Catherine din jin wannan raenin hankali nata , toh taga alamar tazo da raenin wayo , bari ta nuna mata wajen ta tarar , se kawae ta nemi waje tayi zamanta tana janyo remote ta fara qoqarin kunna t.v

Catherine ta kufula ta qara fada cikin daga murya

" Hey u young lady ! Me ya kawoki gidan nan ? Ina Arman yake ?

Se a lokacin ta dago ta kalleta , ehh wato baby ya san da zuwanta kenan ? Shine ya saka ta tazo har cikin gidan nan ? Yanzu rashin son da baby ke mata har yakae ya kawo mata wata cikin gidan auren ta ?

Seta tashi a hankali sannan ta kalli Catherine tace

" In kin gama haushin naki , ga hanya can ki fita , shi kuma wanda kike nema din be kamata kizo nan kina nemansa ba , kamata yayi kije inda kuka saba haduwa ba cikin gidan nan ba .

" Heyy ! Koma wace ke kar kiyi qoqarin shiga rayuwar Arman , otherwise I will kill u " ta fada sounding seriously

Sannan ta dora da

" Zan tafi amma ki sani zan dawo , idan har baki rabu da lurv ba ! Ni Catherine se naga bayanki " daga haka taja tsumman qafafuwanta ta fita daga dakin


Wasu qwalla sanah taji sun tarar mata a idanu wanda cikin sakannin da basu wuce 3 ba suka fara tsere a kuncinta

Baby ? Anya kuwa ? Menene ya hadashi da mace ? Macen ma irin wannan ? Meyasa yake qoqarin tozarta ta ? Meyasa yake so yaci mata mutunci ? Mace har cikin gidan auren ta ? Tazo tana mata kashedi ? Tabbas baby ne ya bata fuska , in badan haka ba , ba zata zo ma har cikin gidan ba

Se kuwa ta sake fashewa da kuka hadda sheshsheqa

Ita ba komae ne ya sakata kuka ba , se yadda mamama da daddy suka basu tarbiyya amma gashi baby yayi fatali da wannan tarbiyyar , ashe in yazo wata qasar mace yake kawowa gidan ? Meyasa baby ya dauki wannan dabi'ar ? Ga qarin zubar mata da mutunci da yayi shine yiwa budurwar tasa kwatancen inda yake zaune babu kunya ba tsoron Allah inda yake zaune ta matarsa ta sunnah saboda ya wulaqanta ta ne ko menene ?

Catherine ! Se a lokacin sunanta ya dawo mata cikin qwaqwalwarta wato sanda suna asibiti , tabbas taji sanda suke waya dashi ! Hakan ma kadae ya isa ya nuna maka sun dade a tare , kuma da alama yau din yasan da zuwanta !!

Wani kukan ta cigaba dayi me matuqar tsuma zuciya da rauni

Seda tayi me isarta sannan taja qafafunta zuwa bedroom , ta fara hargitso kayan ta da suke cikin wardrobe tana watsatu cikin akwati yayin da zuciyar ta ta bushe qamass tanayi cike da bacin rae dan kuwa ta qudurcewa ranta daga yau ta gama kwana a Los Angeles..............



Mhiz Innocent ce...........✍️





*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

Page 37

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e


.............Cike da mamaki ya tura qofar dakin , ganinta a bude , ya qarasa cikin parlourn,bata nan ,hakana ya bashi mamaki dan sau da dama idan ya dawo yana samunta ne a parlour ko tana kallo ko tana karatu

A hankali cikin takun nan nasa me cike da nutsuwa da cikar zati ya qarasa cikin bedroom din ,

Tana tsaye a gaban gadon sanye da army green din abaya hannunta riqe da akwatin

Da mamaki ya qarasa cikin dakin kafin ya furta

" Baby ! Ya fada yana qarasawa wajen da take

" Karka matso kusa dani ! Ta fada wasu hawaye da bata shirya zuwamsu ba na zubowa kan kuncinta

Gaba 1 seya rude ganin hawayen nata , dan haka da Sauri hade da sassarfa ya qarasa wajen da take ya riqo ta sosae tana qwacewa tana fadin

" ni ka qyaleni "

Amma be bi ta kanta ba , seda ya janyo ta sannan ya mata wata kyakykyawar runguma , duk da tana qoqarin qwacewa hakan be hana bugun zuciyarsu haduwa waje 1 ba

Dan kanta da taga babu haza ta haqura ta qyaleshi

Seda yaji tayi shirun ya tabbatar data samu nutsuwa sannan ya daga ta kana cikin tausashshiyar murya yace

" Fadamin ! Meya faru ?

Kukan ta sake fashewa dashi tana yi tana qarawa

" Yah salam ! Baby plss ki bar wannan kukan ki fadamin meya faru uhmm ? Ya fada yana sake riqo hannayenta

Da sauri ta fizge hannayen nata sannan ta fara fadi cikin kukan

" Gida zan tafi ! Budurwar taka tazo har gida tamin gargadi , ni kam na gaji tafiya xanyi kawae "

" Oh god " ya fada yana yamutsa sumar kansa

" Wacece budurwata ?

" Aou tambaya ta ma kake yi ? Ae kafi kowa saninta , bayan rannan ma ina jinka kana waya da ita , sannan cin mutuncin be tsaya iya nan ba seda ka kawomin ita har cikin gidan aur...." Se kuma tayi shiru bata qarasa ba

Wani qayataccen murmushi ya saki yana sake matsawa dab da ita

Cikin zafin nama ya juyar da ita ya rungume ta ta baya yace

" Toh banda abinki baby meye na fushin ? Ko kishi na kike ?

Ji tayi wani tuquqi hadi da bacin rae sun taso mata cikin fushi tace

" Ina mamaki ne yadda kake qoqarin tozartar da tarbiyyar dasu daddy suka bamu , har mace ta biyo ka gida ? Nidae ka cika ni gida zan tafi " Ta qarasa fada wasu hawayen na zubowa

Yau kam baby so take ta sanya masa ciwon kae amma dukda haka bari yaje ya fara yin maganin Catherine dan haka yace

" Ohk zaki tafi gida but plss ki bari zuwa gobe uhmm ?

" Ni dae a'ah yau zan tafi , na sani ma kota dawo da daddare " ta fada da gaba1 amannar ta

Seya sake sakin wani murmushin kamin yce

" Noo ! ba zata dawo ba , but kedae ki bari zuwa gobe pls "

" Toh ka sakeni ni "

Seya sake riqeta da qarfi har seda ta saki qaramar qara sannan ya cikata yana fadin

" bari naje na dawo yanzun nan "

Binshi tayi da kallo harya fice tana jin wasu hawayen na sake tsere akan kuncinta

Wato ya yadda ta tafi ita kadae ? Kenan seya cigaba da zama da wannan matar ?

Ta rasa dalilin da yasa take jin wani irin zafi a cikin zuciyartah ? Amma ta dauki hakan a matsayin rashin jin dadin yadda taga wata tazo har cikin gida nemansa .


*******Yayi sa'a kuwa sanda yaje tana garden tana danna waya

Tun daga nesa ta hango sa , dan haka cikin farin ciki ta miqe tana jiran qarasowarsa

Ya qarasa fuskarsa babu ko alamar annuri kwata kwata

" Lurv ! Hala an fada maka zuwa na ? Ta fada tana rausayar da kae

" Uhmm ! Yess , Catherine banyi miki gargadi akan kar kije gida na ba ? Meyasa kika je ?

" But lurv ! Ae ka bari ka zauna ko coffee ne kasha koh ?

Yamutsa fuska yayi kamin yace

" Just tell me meyasa kika je ?

" Nayi missing din ka ne badly , so yanzu ba gashi kazo ba , ae da nasan ba zaka zo ba ! Kaga yadda ka qara kyau kuwa lurv ?

Shiru yayi ba tare da yace komae ba

Ganin haka ita kuma ya sanyata cigaba da fadin

" But lurv wace ne na gani a gidan ? Ta fada yanayin fuskarta na chanjawa

Gyara tsayuwarsa yayi yana tura hannayensa cikin aljihun wandan jikinsa kafin yace

" She is my wife , and plss stay away from me dan gobe ma zamu koma qasar mu "

Ji tayi kamar zata kifa tunda taji abinda ya fada din amma kuma se taji zuciyarta ta bushe data tuna wani abu dan haka tace

" Babu wani Abu , ae addininku ya yadda ka auri mace sama da 1 , Toh ni a shirye nake zan aure ka ko matan ka sun kae 10 ne " ta fada hawaye na zubar mata a kuncinta

" Se akace miki ni kuma auranki zanyi ba ? Ya fada akan la66ansa yana sakin wani miskilin murmushi

" And bari na shirya daga yau bazan kuma bari kayi nisa dani ba , duk inda zakaje zan bika "

Dae_dae lokacin da Dr Stephen ya qaraso wajen

Suka gaesa da Arman kafin ya maeda hankalinsa wajen Catherine yace

" Cat ! Meya faru ne ?

Cikin shagwa6a ta qarasa jikin baban nata shi kuma ya rungume ta yana fadin

" Meya saki kuka shalele ?

" Pops wae barin qasar nan ze sakeyi ! Ni dae bazan kuma bari yayi nisa dani ba , plss pops zan bishi "

Murmushi Dr Stephen yayi yace

" Is ohk Is ohk , Let him go , I promise u ni da kaena zanje na nemar miki auransa a wajen Dr alqaseem uhmm ? Ya fada yana bubbuga gadon bayanta

Seta tashi tana kallan Dr Stephen din tace

" plss pops ka barni kawae na bishi mana "

" Nooo kiyi abinda nace miki " ya fada yana kallanta hannayensa dafe da kafadarta

Shi kam dae ya hadu da jaraba , wannan naci har ina ?

" Toh Dr Arman se yaushe kenan ? Stephen ya fada yana kallam arman

" I don't even know , but may be soon "

" Ohk my regard to the family pls "

" In Sha Allah " Arman ya fada yana sake gaesawa da Stephen din kafin ya juya ya bar wajen

Ta kalli pops din nata ya gyada mata kae alamar ya bata go ahead kenan , dan haka ta qarasa wajen motar da arman din yazo da ita

Seda ya shiga sannan ta tsugunno jikin glass din tace

" Bye bye lurv pls take care of ur self for me "

Ba tare da ya kalleta ba yace

" Thanks " yana Jan motar .


......Tana zaune a gefen gadon, zuciyarta fall cike da tunane tunane kala kala

Tunanin daya mata dirar mikiya yanzun shine ya sanya hawaye zirara akam cute face nata wato

" May be ma yanzu suna can tare yana bata haquri "

Seda tayi me isarta sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya

Dae_dae lokacin daya shigo dakin, tana kallansa bata dago kae ta kalleshi ba zuciyarta ta mata wani irin suya

Ya qarasa gefen gadon ya zauna, ganin haka ya sanyata miqewa ta koma gaban mirror kamar me shirin yin Kwalliya

" Baby ! Ya fada a hankali

Bata juyo ba ballantana ya saka ran zata amsa

Ya sake fadin

" Baby ! Wae yaushe kika zama haka ? Ina miki magana kinyi kamar bakya jina ?

Seta dan juyo kadan kafin cikin shaqaqqiyar murya tace

" Aou ! Ka manta kurma ce ! Seka daga murya "

Cikin zafin nama ya finciko hannunta hakan ya bata damar fadawa jikinsa, yayinda hannunsa ke kan gadon

" Duk ranar dana qara miki magana kika cemin ae kurma ce, wlh se nayi maganin wannan mara kunyar bakin naki " ya fada yana kallan bakin da da ta turoshi

Jin abinda yace ya sanya ta taune bakin

Yana sane ya dauke hannunsa daga tokarewar da yayi musu , hakan yasa ya fada gadon gaba dayansa, ita kuma ta biyo bayansa tana qoqarin tashi ya sake riqota

A hankali ya fara matsawa da bakinsa zuwa wajen nata, yayinda ita kuma ta rintse gaba daya idanunta,

Dae_dae lokacin da wayarsa tayi qara wanda hakan ya ankarar dashi, ya sanyashi sakinta

Ita kuma tayi amfani da wannan damar ta tashi ilahirin jikinta na rawa,

Tsaki yaja ko Kallan inda wayar take beyi ba ya cigaba da kwanciyarsa .




..........Ranar juma'a suka sauka a cikin garin na kanon dabo tumbin giwa cikin matuqar kewar garin .


*****Tun kafin driver ya gama parking ta 6alle murfin motar ta fice

Ya bita da kallo yana kada kae hadi da murmushi, se kace ba ita ce yanzu ta gama cika tana batsewa ba .

A parlourn ta taradda mamama zaune kan kujera tana kallan ARTV

Da gudu ta qarasa ta fada jikin mamaman tana sakin kuka

" Subhanallahi sanah ! Lafiya kuwa ? Meya sakaki kuka ? Mamama ta fada tana dago sanah daga jikinta

Dae_dae lokacin daya shigo dakin yayi dae_dae da sanda mamama ta qara maemaeta mata tambayar

" Meya sakaki kuka ?

Dan kuwa mamama tasan wannan kukan na sanah ba kewa bace kadae akwae wani abin dae a qasa, Dan kuwa da kukan kewa ne tasan yadda sanah din ke yinshi cike da shagwa6a

Tsayawa yayi be qarasa shigowa ba ya tsaya kamar an kafeshi, yana kallan fuskar sanah din yana jiran yaji amsar da zata bawa mamaman.............


Mhiz Innocent ce...........✍️

*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

Page 38

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e



..........Cikin sheshsheqar kukan tace

" Nayi kewarki ne mamama !

Se yaji wani sanyi ya ratsa kafatanin jikinsa, se a lokacin ya samu damar qarasa shigewa cikin parlourn da sallama

Mamama ta kallesho tana amsa sallamar tasa cike da kewarsu su duka

Ya qarasa ya durqusa yana gaeda ta

Mamama ta amsa tana tambayarsa kwana 2n

Yayinda sanah har yanzun tana jikin mamaman

Ya kalleta ta gefen idanu a zuciyarsa yana fadin

" Se son jiki kamar mage "

Mamama ta maeda dubanta wajen Sanah sannan ta dubi Arman tace

" Meya faru ne Arman ? Meyasa sanah ke kuka haka ?

Wani yaqe yayi kafin ya sosa kansa yana fadin

" Uhmm ! Mamama ae kinfi kowa sanin halin diyarki, bata ganki ba ? Ae shiyasa ta fara shagwa6ar ta ta " ya qarasa fada yana satar kallanta

Sekwa ta watsa masa idanunta tana murguda baki gami da kautar da kanta gefe

Besan sanda ya saki wani murmushi ba

Mamama ta ta6a kunnen sanah tana fadin lokaci 1

" Ya aekin

Please Login or Register in order to submit comment