Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

toh abinda y kamata shine ynx haka xa'a saka bikin ne nan d 3weeks in Allah y kaemu se a daura auren sannan ranar d aka daura ranar xasu wuce xuwa Los Angeles din "

Gaba daya sukayi amanna d wannan magana ta baffa .

A take a lokacin daddy y kira yayan mahaefin sanah wato alhaji Ahmad y Sanar dashi abinda suka yanke inda y nuna musu babu komae amma se a satin bikin xasu shigo kano.



Manyan gidan ne kwae suka san d xancen amma duk yaran basu sani b .



Gadan gadan aka fara shirye shirye duk da dae abin yaxo a qurace ba wani abu xa'ayi b daurin aure ne kwae xa'ae .

Ko kayan daki ba'a siya b tunda ynxn bama a fara ginin filin souban din b sedae daga bayan biki .

Amma lefe kam har an fara hadawa hakan ne ma ya saka aka fadawa souban maganar auren nasa next two weeks ....

Farin ciki jin dadi walwala baxe musaltu b

yanayin daya tsinci kansa a ciki alqalamina be isa ya bayyana muku b........


In Sha Allah ynx kam kullum xaku na samun posting Sedae idan wani uzrinne y riqeni tunda kunsan ance dan Adam ba'a rabashi d uxuuri

Qaunarku ga littafin nan tana d yawa haka qaunarku gareni tana d yawa 😫πŸ₯Ί

Heart u owl πŸ₯ΊπŸ˜»

Naaji dadin addu'o'inku gareni Allah y bar xumunci 😻

Munyi graduation lpia se patan Allah yasa muga result me kyau πŸ˜πŸ’ƒ

Mhiz Innocent ce.........✍️


*β™‘β˜†A ZURI'AR ARABβ™‘β˜†* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

Page 24__25

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES πŸ˜πŸ‘Œ Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/F2PiRdNnrwMKT4mHlIIisl

_Cyprus_

........... Yana zaune a dakin nasa wayarsa ce a hannunsa yana dannawa can kuma se ya tsaya kamar me nazarin wani abu
Zuciyarsa zafi take sosai amma dukda haka ya kaasa mantawa da ita ya kaasa goge ta a rayuwarsa ! Toh ta Yaya ma hakan ze kasance ? Shine yake qoqarin gano hanyar

Dai_dai lokacin wayarsa tayi qara

Ko kallan inda take beyi ba ballantana me kiran ya saka ran ze daga

Kiran na katsewa wani ya sake shigowa

Tsaki yaja yana maida hankalinsa kan wayar don ganin wanda ya masa kira har 2 duk da be daga kiran farko ba

" Bro " ya bayyana kan screen din

Wani tsakin ya sake ja yana danna accept ya kaara wayar a kunnensa ba tare da yace komai ba

Can 6angaren souban yace

" Wai ina ka shiga ne ina ta kiranka baka daga ba ?

" Am on d network " ya fada a taqaice

Girgiza kai souban yayi daama yasan da wuya ya bashi amsar tambayar daya masa dan haka yace

" Hey doctor we missed u a lot yaushe zaka daawo ?

" Soon " ya sake fada cike da qosawa

Numfashi souban ya ajje kamin yace

" Uhmm always da an tambayeka tun kafin ka taafi se kace soon , Any way dai nasan zaka daawk aurena koh ?

Dafe kansa yayi ji yake kamar ya yanke kiran amma se beyi hakan ba but y gaji da wannan maganganun na souban Dan kuwa suna qara masa wani miki ne a cikin zuciyarsa

" Kasan fah saura 2weeks "

Kalaman souban suka daawo dashi daga tunanin daya tafi

" What ? Be san sanda ya furta hakan ba

Souban yace

" Bikin mana an daawo dashi kusa couz ciwon kunnen sanah ne ya tashi , so ana daura aure zamu wuce los Angeles , wait ! Wai kana nufin baka sani b ?

" Is..oh...k " da qyar ya iya tattara wadannan kalmomin ya fada a lokaci guda yana katse kiran

Ruwan dake kan side drawer ya dauka ya zuqe shi dukka be rage ko kadan ba

Zuciyarsa na wani irin suya

Me yake faruwa ne ? Yanzu qiyayyar da en gidan nan suke masa har takai haka ? Wato saboda a nuna masa kowa farin ciki yake da abin shine harda rage lokacin da aka saka a saka irin wannan gajeran lokacin ?

Yazo Cyprus dan ya manta da ita amma hakan yaqi yiwuwa , shi kam ya zeyi ? Zuciyarsa zafi take masa tamkar zata 6allo qirjinsa saboda radadi

Knocking din qofar aka farayi beko kalli qofar ba

Ita kuma jin shiru kuma bata ji motsin ruwa ba alamar baya toilet ya sanyata tura qofar dakin , akayi sa'a kuwa a bude take ta tura ta shige

Can ta hangoshi gefen gado kansa a qasa kamar me tunani

Qarasawa tayi kusa dashi kaana takai hannunta kafadarsa ta dafa tana fadin

" Lurv ! What happened ?

Cikin fushin da bata a6a gani a tare dashi ba ya ture hannunta ya dago kansa ya watsa mata jajayen idanunsa da suka rine saboda fushi sannan ya nuna ta da yatsa yana magana cikin daga murya

" Don't dare repeat dis nonsense again , Is not I will definitely deal with u , get out of my room " y fada yana nuna mata hanya

Idanunta da suka ciko da qwalla takai hannunta kai sannan ta durqushe a wajen tana sakin kuka

Se a lokacin ya gaane yadda ya huce haushinsa a kanta Dan haka waje y samu ya zauna yana dafe kansa

Seda yayi cooling kansa down sannan yace

" Sorry Catherine sorry buh pls ki fita a dakin nan "

Seda tayi kukan ta qoshi sannan ta tashi ta fita dukda dama ita ba haushinsa taji ba tsawar daya mata ne bata saba jin irinta ba .

Ze iya kasancewa mafita 1 ce gareshi itace ya bawa Catherine dama ta shiga rayuwarsa ko kadan ne koda wani abun ze sauya koda kuwa bame awa bane

Ya gaane tana mugun sonsa ta yadda bata qaunar ta ganshi a damuwa

Zeyi qoqarin cire wani kason daga damuwarsa shida kansa In Sha Allah.


**** Tun daga ranar seya kasance arman da Catherine suna fita haka lunch ko dinner kodai something lyk dat

Dama abinda take buqata kenan aikuwa ta dinga bayyana masa irin qaunar da take masa

Taaso ya batta ta dinga masa wasu abubuwan haka na soyayya lyk hug kiss and so_on , but ya nuna mata in ta cigaba da Neman wadannan gaba 1 damar daya bata ze maida ita couz he is not dah stupid yasan muhimmancin addininsa

Hakanne yasa ta barshi , damar fita dashi ma kawai daya bata ta gode masa

A hankali taaja ra'ayinsa akan hakan .


*****Tana zaune akan gadon nata tana karanta suratul isra'i a hankali cikin zazzaqar muryarta

Seda takai qarshe sannan ta ajjiye tayi addu'a tana janyo wayarta da tayi ringing tun dazu

Kafin takai ga duba missed call din wani kiran ya sake shigowa

" Sanam " tayi murmushi tana sauke ajiyar zuciya kamin ta kara wayar a kunnenta

Seda suka shafe wajen 20mins sannan sukayi sallama ta ajje wayar tana jingina kanta da pillow

haka kawai bata san dalili ba kwana biyun nan se tayi ta tsintar kanta da bugun zuciya

" Hasbunallahu wa ni'imal wakeel " ta fada tana dafe saitin xuciyarta

Dai_dai lokacin mamama ta shigo dakin tana fadin

" Sanah har yanzu karatun ne baki gama ba kizo ki daura dinner , daddynku ya kusa dawowa " ta qarasa fada tana Neman waje gefen gadon ta zauna tana karantar yanayin sanah

" Zo nan ! Mamama ta fada in a lower voice

Qarasowa tayi ta dora kanta kan kafadar mamaman

" Meya faru ? Ko ciwon ne ?

Kamar jira take kuwa se kuka hadda sheshsheqa

Hankalin mamama in yayi dubu ya tashi tace

" Subhanallahi sanah meya faru ne ?

Seda tayi me isarta sannan tace

" Uhmm mamama tsoro nakeji

Haka kurum nake jin fargaba mamama bansan dalili ba "

" Ya isa haka sanah , yi shiru kowacce mace haka takeji idan lokacin aurenta ya gabato , ki kwantar da hankalin ki dena saka damuwa a ranki , babu abinda ze faaru In Sha Allah kinji koh ?

Daga kanta tayi alamar " Ehh "

Mamama ta cigaba dayi mata nasiha me ratsa jiki .


Cigaba da shirye shiryen biki shine ya biyo baya a cikin familyn na Arab .


6angaren ango souban yanzu haka ya shiga busy ne sakamakon hada lefe d yakeyi d sauran shirye shirye dae d aka san ango yana yi .

A gefe guda kuma mamama ta kae dinkin hadaddun kayan d daddy ya siyo musu dukkansu daya wansu wanda sanah din zata saka da ita kanta mamaman harma da amrah da afrah dukka mamaman ya bawa yayinda ya kaiwa aunty ma nata kayan.



A cikin satin sega en maiduguri mata qannen mahaifin sanah sunxo su 2 da wata mata .

Ba qaramin farinciki mamama tayi ba nan ta fara ina taka saka ina taka aje dasu


A parlour suka zube ana gaggaisawa kapin aka fara gabatar musu d kayan ciye ciye da motsa baki

Suna nan zaune sanah ta shigo gidan d sallama a gajiye dan ba qaramin gajiya tayi b dan yau sun Dade a school gashi kuma daga yau universities xasu shiga strike


Qarasawa cikin parlourn tayi ta gaida baqin da fara'a dan tasan su amma fa a matsayin en uwan mamama ne

Mamama tace

" Sanah en uwana ne daga maiduguri

ga aunty umma wannan kuma aunty ilham "

Murmushi tayi se taji duk gajiyar da take ji ta tafi a hankali ta qarasa gabansu

Aunty umma tace

" amarya sanah daga makaranta kike ne ?


" Ehh aunty "

Aunty ilham ce ta kar6a da cewa

" Toh maza kije kiyi wanka kiyi sallah se kizo yanzu za'a fara gyaran "

Duk da bata fahimci abinda take nupi b amma dai ta amsa da

" toh " tana miqewa ta shige dakin.



Seda tayi wankan tayi sallah sannan ta fito parlourn lokacin duk basa nan se mamama kawai dake xaune kan dinning

ta qarasa itama dinning din tana jan kujera fuskarta dauke d murmushi ta zauna

Itama mamaman mayar mata tayi da murmushin tana fadin

" Y kunnan ?

" Da sauqi mamama ya dena zafi ma yanzu fah "

" Toh masha Allah maza kici abinci aunty umma na jiranki a common room "

Bata san me aunty umman zata mata b amma bata tambayi mamaman b kawai ta janyo plate din dake dauke d dambun cous cous wanda tana ci tasan mamaman ce ta dafa dan ba daga nan b wajen iya girki
shys itama gwana ce a wannan fannin

Kadan taci abincin dan dama ita be dame ta b cin abincin koda kuwa yunwa take ji in taci kadan shikenan y wadatar

Kasancewar mamaman tasan halinta yasa bata yi magana b da taga ta tureshi gefe

sannan taja juice din mango wanda shima mamaman ce ta mata kasancewar ta gwanar son lemon mangowaron..........

Mhiz Innocent ce.........✍️


*β™‘β˜†A ZURI'AR ARABβ™‘β˜†* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

πŸ’–THE TALENT TROUPE WRITER'SπŸ’–

Page 26

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES πŸ˜πŸ‘Œ Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/F2PiRdNnrwMKT4mHlIIisl



................Tare suka shiga dakin da su aunty umman suke suka gaesa da mamama kafin mamaman ta fita ta barsu a dakin

Aunty ilham ce ta fara mata magana

" Sanah kina xuwa makaranta koh ?

" Ehh ina xuwa amma gobe za'a shiga strike " ta fada cikin sanyayyiyar muryarta

" Wowww ! abin yazo a daedae ! Inji aunty umma sannan ta dora da fadin

" kinga wannan " ta fada tana nuna wadda ta gani daxu a parlour wato wadda suka xo tare dasu aunty umman

" sunanta hajja fati zata fara miki gyaran jiki amma babu fita , na kwana 8 ne kacal daga ranar shiknan an gama "

Da " Toh " kawae ta amsa tana kallan matar

Nan da nan hajja fati ta faara gyara sanah cikin qwarewa da sanin ya kamata .

Ita kuwa sanah daurewa kawai takeyi amma ji take tamkar ta saka kuka .


Haka aka cigaba da gyarata kamar yanda akewa kowacce amarya .

A kwana 2 da farawa harta chanja hasken ta y sake fitowa sosai , tayi wani irin kyau tayi fresh kamar ka dauketa k gudu dan ba qaramin gyara suke mata ba , ciki kuwa har mamama ba'a bari a baya ba wajen gyara erta ta .





*****6angaren mama kuwa data lura dai auran yinsa za'ai , seta zubar da makaman yaqinta ta zubawa sarautar Allah ido

Dama kuma auntyn Khalid ce ke zugata dan haka seta dauke mata qafa kawai ko ta samu zuciyarta ta samu salama .



..........Suna zaune a parlourn su 3 kasancewar Umma tana part dinsu sanah

Afrah ce ke daama musu fura , yayinda sanah t baada dukka hankalinta ga t.v da suke nuna " dil to pagal hai " a tashar MBC Bollywood

Amrah kuwa dama ba tun yanzu ba ta gama quluwa da kallan nata , dan tun dazu taqi bari a chanja channel din

Miqewa tayi ba tare da sanah din ta lura ba ta kashe socket din gaba daya

" Dallah can meye haka ? Ina kallo na zaki kashe min haka akeyi ? Ta fada kamar me shirin yin kuka

" Wlh tun dazu kin isheni da kallan film din nan yaqi qarewa , gashi kinqi bari muyi hira haka ake fisabilillah ? Inji amrah

" Allah kuwa sena qarasa kalla koma mene " ta fada tana qarasawa wajen socket din

Afrah da tunda suka fara bata tanka ba tace

" Gaskiya amrah kina takurawa aunty na !

" Waye Auntyn ? Amrah ta fada tana kallan afrah

" Aunty Sanah mana !

Se kuwa amrah ta fashe da dariya tana kallan sanah

" Amma wlh anci mutuncin aunty !

Sanah ta kalli afrah sannan ta maida dubanta kan amrah tace

" Dallah can ni aunty ce mana yanzu " ta fada a lokaci guda tana kashe kallan dan sun gama film din sannan ta dauki wayarta

A kullum a koda yaushe ta dauki wayar nan , muddin zata shiga gallery seta ganshi couz shine akan gallery wallpaper din ta

Hotonsu ne wanda sukayi tare ranar birthday dinta

Wanda ya shafa mata cream ne a fuska , ita kuma ta juya tana kallansa aka dauki hoton sunyi matuqar kyau kamar wasu indiyawa

Haqiqa tayi kewar dan uwanta kewa sosai kuwa

Amma meyasa lokaci 1 ya chanja a rayuwarsu ?

Meyasa ya koma tamkar ba babyn data sani tun yarintar ta ba ?

Meyasa shaquwarsu ta disashe a cikin lokaci qanqani ?

A hankali wasu hawaye masu dumi suka kwaranyo akan kyakyawar fuskarta

Ta saka hannu ta dauke su tana fadi akan la66anta

" Baby why ?

Afrah ta tasowarta kenan bayan ta kai furar cikin fridge ta leqa wayar Sanah taga abinda take kalla tace

" Wai har an faara kukan rabuwa da babyn ne ? Awwwn ! Ta fada irin an birge ta din nan

Amrah dai tana jinsu se kawai tayi murmushi ba tare da tace komai b

Ita kuwa sanah gallawa afrah harara tayi tana fadin

" Ke wai ina furar ne ?

Kafin afrah takai ga amsa tambayar wayarta tayi qara

" Aunty Umma " ya bayyana kan screen din

Turo baki tayi tana ajje wayar kan sofa

Afrah ta sheqe da dariya

Kafin su ankara amrah ta dauki wayar ta daga ta kaara kunnenta

" Hello aunty umma " ta fada tana kallan sanah tana dariya qasa qasa

Daga can 6angaren aunty Umma tace

" Amrah ina sanah ta shiga ne ?

" Tana nan part din , amma bari na fada mata se tazo yanzun !

" Yawwah waiting....

Amrah ta sauke wayar tana fashewa da dariya , afrah na taya ta

Ita kuwa sanah ta cika tayi fam qiris take jira ta fashe

Amrah tace

" Wai ina ke kikace auren nan kike so uhmm ? So duk abinda aka miki ke kika jawa kanki , koda yake kinsan fa gyaran duk yah souban ake mawa , so ai ba wata damuwa bace " ta fada tana sake sakin wata dariyar

Daama ya lafiyar kura bare tayi zawo aikuwa se kuka kamar wadda akayiwa wani abun

Duk kuma se suka nutsu suka koma rarrashin ta .


Yau kam da qyar akayi gyaran jikin ana yi tana kuka ita bataso a qyaleta kawae jikinta zafi yake mata

Ana gamawa Umman amrah ta shigo dakin hannunta dauke da cup ta qarasa ta zauna ta miqawa sanah tana fadin

" Kar6i maza ki shanye kinji ?

Rau rau tayi da ido kamar zata saka kuka gashi dama zuciyar a kusa take

Umma tace

" Kar fah kiyi kukan nan ki shanye kawai "

Haka dai badan taso tasha tana sauke ajiyar zuciya gudun kar tayi vomiting .


........6angaren ango kuwa yafi kwana nawa bega amaryarsa ba , dan tunda aka faara mata gyaran jiki aka hanata fita

Ranar ma da yake su aunty umma basa nan shiyasa ta sulale part din su amrah

Yayi missing dinta badly amma inya tuna kwana kadan ne suka rage ya mallake ta se yaji wani sanyi a ransa .


_Cyprus_

" Baby me kake sakawa a ranka har hakan ya janyo maka hawan jini ?

Ita kadai ce duk duniya take kiransa da wannan suna , banda ita babu wani mahaluki da yake kiransa dashi

Toh ta yaya zuciyarsa zata samu nutsuwa ? Bayan kullum ranar Allah seya tuna da ita

" Don't ever call me baby again "

Mamaki ya bata , meye aibun wannan sunan ? Koda yake duk ba wannan ba , abinda kawai take so taji shine damuwarsa Dan haka ta sake karairaye murya tace

" Lurv pls ka fadamin meye damuwarka mana ? Kaaga fah jininka ya hau !

" Babu abinda ke damu na ! Just leave me plss I want take shower "

" Ohk ina jiranka a parlour " ta fada tana qoqarin juyawa

Dai_dai lokacin da wayarsa dake kan mirrow tayi qara , kasancewar tafi kusa da wayar ya sanya ta dauka ta miqa masa sannan ta fita

Ya kar6a badan yana da niyyar dagawa ba

Sedai ganin me kiran ya sanyashi miqewa yana sake Neman waje ya zauna

Cike da mamaki dan be ta6a tunanin daddyn nada layinshi na qasar ba dan tunda yazo qasar be ta6a kiransa ba

" Barka da rana daddy "

Daga 6angaren daddy y kur6i sassanyan juice din sannan ya amsa da

" barka "

Seda daddy ya numfasa sannan yace

" Ranar juma'a me zuwa daurin auren er uwakka kuma na dan uwanka !

Abinda nake so dakai shine kayi duk yadda zakayi ka daawo daurin auren nan "

Kansa daya saara masa ya dafe yana jin dama shi mace ne da yayi kuka ko zeji sassauci a ransa da zuciya baki 1

Sedai hakan baze yiwu ba , cigaba da barin quncin a ransa shine kawai mafita a gareshi

"Daddy......" Y furta yana qoqarin dorawa daddyn ya katseshi

" Obey b4 complain ! In kasan ba toh zakace min ba toh bansan jin komae daga bakin ka

Wai arman wane irin mutum kake son zama ? Ko ince ka zama ? Gaba 1 ka chanja

Daurin auren er uwatta ka kake qoqarin qin zuwa ?

Me yake damunka ne arman ? Baka gudun bakin mutane ne ? Baka gudun idanun mutane ?

Toh ka tabbatar ka daawo qasar nan kafin ranar daurin auren nan , ko da yake koma dai menene ka tabbatar ka dawo kafin daurin auren nan kana wajen lokacin daurawar , in ba haka ba wlh arman zaka hadu da fishi na " daga haka daddy ya katse Kiran nasa ba tare da ya jira amsar arman ba dan kuwa beda buqatar ta


Wato ya lura daddy so yake zuciyarsa ta buga

Koda yake tunda uban daya haifeshi ne yake neman kaishi inda zuciyarsa zata buga babu wani abu zeje , amma fah ya tabbatar daga lokacin da akace yana gani yana ji za'a dauki sanah zuwa dakin waninsa yasan taasa ta qaare

Ya rasa yanda zeyi wannan ko cewa akayi yana da ciwon zuciya ze yadda ballantana kuma hawan jini

Abubuwan sun masa yawa , tun zuciyarsa na jurewa har yanzu ta faara rauni toh daga raunin se me ?????????

Jiya kunji ni shiru koh ? Wlh na shiga busy ne shys but kuyi manage d wannan


πŸ’–NEW TEAMπŸ’–
πŸ’–THE TALENT TROUPE WRITER'SπŸ’–

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

*4,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)

*5, BABY*
by(Mhiz Innocent)

More comments more post


Mhiz Innocent ce...........✍️

*β™‘β˜†A ZURI'AR ARABβ™‘β˜†* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

πŸ’–THE TALENT TROUPE WRITER'SπŸ’–

Page 27

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES πŸ˜πŸ‘Œ Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/F2PiRdNnrwMKT4mHlIIisl


.............Kwanakin da suka biyo baya har yanzun souban yana cikin kacaniyar busy , domin kuwa yanzu haka ma har kati an bugo an fara rabawa jama'a , dukda ba wani taro za'@yi ba amma haka gidan ya faara daukar harami kamar ana shirin aurar da duk en mata da samarin gidan .

*********Hada kayan yake jikinsa a matuqar sanyaye , bezo Cyprus danya barta nan kusa ba amma ga wannan lamari yadda ya kasance

Umarni ne daga wajen wanda baze iya musu ba dan haka dole ya bar Cyprus .

Tun dazu take a parlour tana jiyo motsinsa amma ya hana ta shigar masa daki

Yau kam se tayi fatali da wannan dokar tasa kamar yadda ta sabayi lokuta da daama kawai ta fada dakin

Duk da yaji shigowarta hakan be sakashi ya dago ba , ya cigaba da hada kayan

Cike da fargaba ta qarasa wajen nasa tana kallan abinda yake kafin tayi qarfin halin fadin

" Lurv ! Me kakeyi hakane ? Ina zakaje ? Ta fada tana riqe kayan da yake qoqarin jerawa a akwati

" Zanje Nigeria ne...."

Ai Kafin ya qarasa ta katseshi da fadin

" What ? Nigeria ? Meyasa zaka min haka lurv ?

Cikin dakiya yace

" Am not going to spend more than 5days ! So karki damu zan dawo ne !

Se kuma tayi murmushin gefen baki tace

" Sure ?

" Yeap ! Ya fada cike da qosawa

Itace ta tayashi qarasa hada kayan tana bayyana masa irin kewarsa da zatayi

Shi dai jinta kawai yake dan dama ya gaji da wannan zaman nasu.


...........Gida ya faara cika sosai kaama daga en uwan mamama ne , en uwan su daddy , harma wasu daga en maiduguri duk sun faara hallara dan bikin na rana 1 ne kawai wato ranar daurin aure .



Wadda zatawa amarya lalle ma xuwa tayi gidan ta zaane mata hannu da qafafu ta fito sakk amarya , tayi sharr da ita
tayi wani irin kyau na ban mamaki

fararen hannayenta da qafafunta sunyi matuqar kyau cikin lallen ja da baqi

Haka nan daga zarar ka xauna a kusa da ita zakiji qamshin da take me matuqar dadi haka in tabar waje ma sedae tabar muku qamshin.

Amarya dai ta fito dass d ita haka zalika shirye shirye ma suna gudana yanda ya kamata .

Lefenta an gama hada mata su har an kawo su ma dakin mamama akwati 12 ne cirrr kowacce danqare da kyawawan kaya masu kyau aji da tsada

komai ka daga sedae muce MASHA ALLAH !!!


******Lokacin daya sauka a Nigeria cikin garin kanon dabo kuma cikin gidan na zuri'ar Arab gidan na cike ne da jama'a , kowa da abinda yake yi , damma yalwar gidan ta hana ganin gidan a cike se wadanda suke aikace_aikace

Se kuma wasu dandazon da suke can wani 6angaren na gidan suna hira cikin farin ciki

Hakanne yasa koda ya shigo da motarsa kai tsaye part din mazan gidan ya wuce dan baze iya da hayaniyar mutanen dake part din Manama ba .

Sanda ya shiga part din nasu babu kowa a ciki yaaji dadin hakan kuwa dan haka yayi wanka ya chanja kayan jikinsa sannanya fito parlour ya kwanta kan doguwar kujerar yayi pillow da hannunsa yana kallan ceiling kamar me tunani , sedai zuciyarsa ce ke wani irin suya kamar yadda ta saba masa a kwanakin nan

Yana nan zaune yaji sallamar souban y shigo parlourn , be motsa ba har souban din ya qaraso yana fadin

" Bro yaushe ka dawo ne babu sanayya ! Wow gskia naji dadin dawowarka ! Y fada yana neman waje gefen kujerar da arman din ke kai ya zauna

Murmushi kadan arman yayi cike da basarwa yace

" Thanks !

" Pls tashi ka gani mana " inji souban

Kamar ya shareshi se kuma yaga rashin dacewar hakan , dan haka ya tashi ya zauna yana dafe kansa dake jahilin saara masa

Souban yace

" kayanmu na kar6o wanda zamu saka gobe " ya fada yana warware kayan daya

Please Login or Register in order to submit comment