Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yin kuka sannan ta dauki pillown dake gefenta ta jefa masa, yayi dariya yana fadin

" Wayyo baby zata hukunta baban baby "

Seda ta jefeshi da duka pillown dake kan gadon sannan ta qyaleshi, shi kuma ya janyo ta jikinsa kafin ta kae ga kwanciya a qirjinsa ya kamo bakinta ya fara bata wani zazzafan kiss wanda ya kusan tafiya da numfashinta.

Daga nan Arman ya cigaba da nuna mata irin soyayyar da kuma kewarta da ba zata misaltu ba wadda yayi, Ranar kam ta yadda ta gasgata irin soyayyar da babyn ke mata dukda dama dae soyayyarsa gareta babu haufi .

washe gari kuwa duk wata kulawa da bata samu ba a first night dinsu, yau kam ya hada gaba 1 ya bata ita, hakan ne ya qarasa ranar ta zama wata ta daban a wajensu baki 1, Ita kuwa ta saki jiki ta dinga zuba shagwa6arta, shi kam yayi ta biye mata har yaso ya sake wuce gona da iri, dan bata San in tana ta6arar tata sake tunzurashi take ba, se daga baya ta gane hakan wato yana nema ya sake wuce gona da iri ne dan haka ta saka masa kuka, se a lokacin ya dawo hayyacinsa sannan ya rarrasheta dukda rarrashin nata baya qarewa.

Yau ma kuma ta tashi da ciwon kae da zazza6i gashi kuma babu magani a gidan, sanda ya fito daga wanka ya shirya yace

" Bari na samo miki magani "

Ae bata san sanda ta miqe daga kwancen da take ba tace

" Don Allah baby karka fita, bana son wani magani, nikam na warke "

Murmushi ya saki, dan ya gaane abinda take nufi, seya tattako zuwa bakin gadon ya tsugunja yace yana kallanta cike da kulawa

" Babu abinda ze faru In Sha Allah, mintuna 10 sunyi yawa inje in daawo "

Girgiza kae tayi tana riqo hannunsa

" A'ah baby nifah na warke "

Seya hawo kan gadon ya zauna, kafin ma ya qarasa zama ta riqeshi sosae tana dora kanta a qirjinsa

Ya sake yin murmushi yana rufeta da hannayensa gaba 1.


Kwanakin da suka biyo baya love birds din suka cigaba da 6arzar amarci ba kama hannun yaro, soyayya suke nunawa junansu kamar babu gobe, kowanne so yake dan uwansa ya kasance a gefensa a koda yaushe, hakance ta saka indae suna kusa sedae ka gansu a jikin juna.


*****Tana zaune da mandon a gabanta wanda ta juyeshi a cikin wani plate tana laasa dukda yajin da take ji amma haka take sha tana yi tana jan baki

Dae_dae lokacin da wayarsa dake gefenta tayi qara, seta kalli inda take idanunta na sauka kan me kiran

" Catherine "

Bata san sanda ta dakata da shan mandon ba, ta kalli wayar tana nazarin sunan

Bata kae ga qarasa tunanin nata ba Arman ya shigo dakin yana kallanta

Ya saka hannu ya janye plate din

" Fisabilillahi me kike ji a wannan abin ? Ya fada yana kallanta, se yaga yadda idanunta sukayi rau_rau

Da Sauri ya qarasa ya zauna yana fadin

" Meya faru ? Uhmmm ?

Se kuwa hawayen zuka zubo a kuncinta kafin cikin qarfin hali tace

" Wae dama har yanzu kana tare da Catherine ?

" Oh god ! Ya fada yana dafe kansa sannan ya dora da yana janyo ta jikinsa , seta fara qoqarin tureshi amma yaqi bata damar hakan ya riqeta gam

" Baby! Inaga base na fada miki alaqar dake tsakanin daddy da Dr Stephen ba koh ? Kema kanki zaki iya bada sheda akan hakan, Wlh abinda ya saka kenan na kasa blocking ersa, amma wlh babu abinda ke tsakaninmu, kuma ke kinsani ni banason mace mara aji ? Toh ta yaya zan iya zama da Catherine ma wae ? Matar daba musulma ba ? Bata cika duk wasu personalities da nakeson mace ta cikasu ba ? Beside tunda nake ma wlh ban ta6a ganin macen data burgeni ba, dan kuwa tuntuni na dade da mallaka miki zuciyata gaba 1 taki ce ke 1 "

Shiru dae ita tayi ba tace komae ba, jin hakan ya sanyashi dorawa da fadin

" But bari ki gani, let me just make it clear " ya fada yana janyo wayarta sa

Kafin yakae ga kiran Catherine din kiranta ya shigo wayar, seya daga wayar yana sakata a hands free

Kafin yace komae Catherine ta fashe da kuka kamar wadda akama mutuwa tace cikin kuka

" Lurv ! Mummy want to kill her only daughter, Mummy bata sona yanzun, Mummy ce......................


Daga alqalamin Mhiz Innocent...........✍️




*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

Page 46_47

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e


______Mummy tace daughter dinta ba zata auri dan qasarku ba " ta qarasa fada tana sake fashewa da kuka

Seya gyarawa sanah dake kwance a jikinsa zama, yana gyara zaman wayar hannunsa sannan yace

" Wow, ur mum made a beautiful decision, and pls kibi umarnin mahaefiyarki couz daga yau ba zaki sake samun number na ba and ina miki fatan alkhaeri "

Catherine bata iya sake cewa komae ba couz she felt heart broken sema kukan data sake fashewa dashi bata sake trying na kiranshi ba dan ta riga tasan tunda mum dinta ta yanke hukunci dole ne subi.

Sanah ta dago ta kalleshi da damuwa shinfide kan fuskarta tace

" Eyyah baby meyasa zaka ce mata haka ?

Seya kalleta cikin ido, da alama maganar da take ba har cikin ranta take ba Seya dage mata girarsa kamin yace

" Ohh, seems u're talking seriously ? Ohk lem me call her again mu tattauna yadda xamu shawo kan mamanta ta yadda na aureta "

Seta ta6e baki tana miqewa

" Toh ka tafi can qasar nasu mana " ta fada a kufule

Seya riqota da sauri

" Sorry mana baby, I like dis ur qarfin hali " ya fada yana lakuce kumatunta

Se tayi murmushi tana janyo plate din daya jashi gefe, ya sake riqewa yana fadin

" Noo, pls ki haqura dashi haka nan "

Se tayi rau rau da fuska tace

" Don Allah ka bari ko kadan ne in qara "

" Tohm " ya fada yana miqa mata

Aekuwa da sauri ta kar6a ta diba da yawa sannan ya dauke ya fita dashi gaba 1 daga dakin.


__6angaren daddy kuwa gaba daya ya fita harkar aunty, baya danne mata haqqinta dan haka idan ranar kwanan tane ze shiga 6angaren nata amma fah ita kanta seda tasha jinin jikinta, gaba 1 ta gaane kurenta dan kuwa horon da daddy din yake mata bana wasa bane, hakan kuwa ba qaramin taemakawa yayi ba dan kuwa ta gaane kuskurenta, da kanta ta dauki qafa taje ta bawa su mamama harma da mama haquri.

****Su Khalid kuwa an yanke musu hukunci dae_dae da abinda suka aekata, kafin kuma a yanke musu hukuncin da kansa ya bawa souban saqon ya nemar masa afuwar gaba 1 familyn na Arab, Lokacin daya fada musu kowa fatan shiriya yayi masa da kuma nema masa afuwar ubangiji.


____Tana zaune akan gadon wayarta a hannunta da alama chart take kuma chart din na mata dadi,

Bansan me aka turo mata ba naga dae ta saki wani murmushi, dae_dae lokacin da Arman ya shigo dakin, seya qaraso da sauri yana fadin

" Madam me muka samu haka ?

Seta miqa masa wayar hannun nata gaba 1 kamin tace

" Duba ka gani "

Seya kar6i wayar yana kallan abinda take nuna masa din, ta6e baki yayi kamin ya miqa mata wayar

" And so ?

Seta kalleshi cikin rashin fahimta tace

" School fah aka koma !

" Yes na gani, meye na farin cikin ? Ya fada yana kallan ta

Se taji duk jikinta yayi sanyi, seta matso kusa dashi a hankali ta dora kanta akan kafadarsa sannan cikin sanyi tace

" Toh kayi haquri " ta fada kamar zatayi kuka

Seya shafa sumar kansa a hankali ya shafa tattausar fuskarta kamin yace

" Ni baki min komae ba, kawae dae ki bar zancen wannan makarantar, Inma zaki koma din toh ba yanzu ba se kin haehu "
Kamar zatayi kuka tace

" baby in aka wuce ni a karatun fah ?

" Baki da damuwa tunda kina dani, amma don Allah maganar makarantar nan abarta "

Seta daga kae a jikinta sanyaye, lura da hakan ne ya sanyashi dago da fuskarta ya sanyata cikin tafin hannayensa sannan yace yana kallanta idanunta na kallan qasa

" baby !

Seta sake yin qasa da fuskarta ta ba tare da tace komae ba

A hankali ya matsa da bakinsa saman qaramin cute lips dinta yadan ciza kadan, bata san sanda ta saki qaramar qara ba tana riqe bakin nata, dukda haka be saki fuskarta ta ba sema murmushi da ya saki sannan ya saukar da hannun nasa zuwa kan bakin nata ya riqe sannan yace

" Ohh sorry, ban kula bane kinji baby "

Bige hannun nasa tayi tana turo baki tace

" Ba wani nan Allah kuwa "

" Sorry er lukuta tah " ya fada yana dariya

Aekuwa seta saki kukan shagwa6ar tana yi tana bubbuga qafa, se yayi azamar riqota yana fadin

" ohh god sorry, na manta ashe fa baby na ne ya saki qibar koh ? Don't worry idan yazo zan hukuntashi, gashi kuma yana wahalar min da baby na "


Se ta dago ta kalleshi kamin tace

" Baby wae namiji ne ?

" Ehh mana young Arman ba "

Seta yamutse fuska

" A'ah nikam daddy ko mamama za'a saka plss "
Murmushi yayi yana lakutar kumatunta yace

" Yadda kikace haka za'ayi "

Itama murmushin ta sakar masa.


_____Haka suka cigaba da raenon cikinsu lokaci guda kuma suna shan soyayyarsu kamar ba wadanda ke shirin zama iyaye ba, a 6angaren sanah kuwa yanzu kam ta saki jiki tana nunawa babyn nata soyayya kamar ba gobe, shi kam dama haka yake so se suyi ta nunawa junansu soyayya.


_____Lokacin da cikinta ya shiga wata na tara, lokacin bikin souban da amrah ya taso, yana sane da ita duk lokacin data masa maganar zuwa gidan seya waske mata dan kuwa yasan indae ta shiga gidan nan ba ita ba fitowa se bayan ta haehu.

Ana saura kwana 2 bikin suna zaune a parlour, ita tana zaune a qasan carpet sanye da t_shirt da qaramin skirt wanda yake iya gwuiwarta, yayin da shi kuma yake zaune zaman dirshen hannunsa dauke da cup din kunu yana bata da cokali a nutse kamar me bawa jariri abinci, can data qoshi seta yamutsa fuska tace

" Na qoshi "

" Noo, ban yadda ba, du du du spoon nawa kika sha ? Pls ki qara ko kadan ne "

Ajiyar zuciya ta sauke tana dora hannunta akan qaton cikinta daya zauna kamar wadda zata haefe en 3, bin cikin yayi da kallo sannan yace

" Nasan baby na be qoshi ba plss....... "

Qarar wayarsa ce ta katse masa maganar da yake qoqarin fada, seya ajjiye cup din kunun ya janyo wayar yana duba me kiran, da sauri ya daga ganin kiran Mamama ne

" Yaushe zaka kawomin diyar tawa ne ? Kose nazo da kaena da dauketa ? Mamama ta fada bayan sun gaesa

Seya shafa qeyarsa jikinsa a sanyaye yace

" A'ah mamama dama yau nake shirin kawo miki ita, yanzu ma haka abinci kawae zataci mu taho "

" Yawwah toh ina jiranku " ta fada tana katse kiran

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallan sanah wadda ke sakin wani qayataccen murmushi

" Hankalinki ya kwanta koh ? Seki tashi ki shirya mu wuce tunda yanzu kin dena sona "

" Ni Allah kuwa ina sonka kullum " ta fada tana turo baki, shima ya fada ne kawae couz he knew soyayyar da sanah ke masa is uncountable amma seya baasar yana taemaka mata ta miqe suka wuce daki, shiya taemaka mata tayi wanka ta shirya sannan ya debar mata kaya kala 2 wato ana gama biki yaje ya dakko abarsa, yana hadawa yana 6a66ata rae shi ala dole wanda akayiwa dole, ita dae bata bi ta kansa ba dan kuwa farin cikin ganin mamama kadae ya isheta dan haka sanda suka hau kan titi ma suna tafiya shiru yayi yana kallan titi beko kalleta ba, se kuma taji babu dadi dan haka cikin kulawa ta zura hannunta cikin 1n hannunsa dake ajje a tsakiyarsu, seya waewayo ya kalleta yana sake maeda hankalinsa kan driving din da yake, seta langa6ar dakae gefe tace

" Don Allah kabar fushin haka baby, Allah kuwa baka kyau kamar wani zombie " ta fada tana dariya

Besan sanda shima dariyar ta qwace masa ba, seda yayi me isarsa sannan ya juyo ya kalleta ya sake maeda hankalinsa kan titi yace

" Waya fada miki zan iya fushi dake baby ? Indae kuwa hakane ashe zan iya fushi da kaena, just bansan yanda zanyi a kwanaki 2n nan da zakiyi a gida ba " ( ni kuwa nace zaka ga kwana 2 😂 )

Seta sake maraeraece fuska kafin tace

" Gida fah zanje ba wani waje ba "

" Yes na sani " ya bata amsa a gajarce.



.....Sanda suka isa gidan kae tsaye 6angaren mamama suka wuce, yana riqe da ita tana taku tinqis tinqis, tun daga nesa mamama ta hangesu dan haka da sauri ta qaraso ta kar6i sanah tana faman fadin

" Sannu "

Ita dae sanah bata iya amsawa ba ta cigaba da takawar har suka qarasa dakin sanah din, sannan mamama ta ajjeta akan gadon ta juyo ta koma parlourn.

Yana zaune kan kujera cikin ladabi ya sauko ya gaeshe da mamaman, ta amsa cike da kulawa, sannan tace

" Wato ba dan nace ka kawo min ita ba saboda rashin kunya ba zaka kawo min ita ba koh ?

Seya shafa kansa yace

" A'ah mamama ni na isa ?

" A'ah na sani ko ka isan ne "

Seya girgiza kae yana murmushi yace

" A'ah kam ban isa ba "

Itama murmushin tayi tana neman waje ta zauna suka cigaba da hirar da take tsakanin da da uwa.


***Ranar alhamis akayi dinner wadda itama dae wannan karon sanah bata samu damar halatta ba.

Ranar juma'a kuma aka daura auren Souban da Arman wanda dubban mutane suka shaeda hakan, sannan da daddare aka kae amarya gidanta cikin farin ciki da kewa.

Washe_garin daurin aure yazo daukar abarsa, mamama ta nuna masa sam be isa ba dan kuwa sanah tazo gida haehuwa, gwara ma yaje ya kwaso mata kayayyakinta in kuma baze kwaso ba ya bassu tunda tanada wadanda zata saka a gidan, haka badan yaso ba ya haqura, sedae ya kulle gidan nasu ya dawo cikin gidan na Arab da zama dan kuwa baze iya jure rashin ganinta haka duk sanda yake da buqata ba, dama yanzu babu imam babu souban hakan yasa zaman ma yafi masa dadi, indae ba aeki ze fita ba toh yana 6angaren mamama liqe da matarsa musamman in akayi sa'a mamaman bata kusa.

Ita kuwa mamama duk wata kulawa daya kamata a bawa me ciki haka take bawa diyarta ta, bata cikakken awa bata leqo ta tambayeta lafiyarta ba, duk mutanen gidan kulawa suke bata ta musamman, ga aunties dinta na Maiduguri suma ba'a barsu a baya ba dan haka ta sake zama wata er gatar danginta.


______Fitowarta kenan daga toilet ta qarasa kan gado ta zauna tana sauke numfashi, ba tun yanzu ba take jin kamar ana tsikararta amma se maazewa takeyi, yanzu kam wani irin motsawa taji mararta tayi, da sauri ta dafe cikinta lokaci guda cikinta yayi wani mugun juyawa, cikin matuqar tsoro fargaba gami da zafin ciwo da saki wata qara tana kiran sunan Allah, hannunta dafe da cikin nata......................

Baby pah yana muku bankwana 🥺🥹 dan kuwa daga haka se ince muku mu hadu a *last page* In Allah ya nupa


Mhiz Innocent............✍️



*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

Page 48_49_50
( *_LAST PAGE_* )


Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e



________Sannan ta zube a qasan carpet cikin yanayi na ficewar hayyaci, mamama dake qoqarin shigowa dakin, ta qarasa da sauri dan ta jiyo qarar da tayi, cikin hanzari ta qarasa inda sanah din take tana kamota sannan itama cikin kidima tace

" Yah salaam, haehuwar ce " tana gama fada ta fice daga dakin

Se gasu sun dawo ita da Umma da Maman souban, kafin su qarasa shigewa dakin nata sega aunty ma ta shigo, su suka taemakawa Sanah din aka sakata a mota dan bama ta cikin hayyacinta se nishi kawae take saki, mamama na riqe da diyarta ta cike da tausayawa halin da take ciki har suka isa asibiti.


.....Dukkansu suna harabar asibitin wasu a zaune, wasu a tsatstsaye kowa da addu'ar da yake karantowa,

Bayan shudewar wasu awanni, wata er farar midwife ta fito dauke da baby a hannunta, gaba 1 suka nufeta da sauri,

da murmushi kan fuskarta ta qaraso wajen nasu sannan ta miqa musu babyn dake lullu6e cikin farin haddaen towel tace

" Congratulations, ta haehu lafiya, an samu da namiji "

Dae_dae lokacin da Arman ya qaraso, ya tsinci maganar da take, besan sanda wani qayataccen murmushi ya qwace masa a kyakykyawar fuskarsa ba, sannan ya qarasa ya saka hannu ya kar6i babyn, ya bude towel din da aka rufe shi dashi, kyakykyawar fuskarsa jajawur da ita ta bayyana, lallae wannan babyn shine kyau da kansa, Dan kuwa shi ba'a sama ya dakko kyaun ba, kyau ne daya gajeshi a wajen uwa da uba

" Wow, Masha Allah, Alhamdulillah " ya fada yana bawa babyn light kiss a kumatu, sannan ya masa huduba yana miqawa mamama shi, ta kar6a cikin wani irin farin ciki daya kaasa 6oyuwa a fuskarta, ta kalleshi sannan a hankali taji wasu hawaye na sakko mata ba, ta saka hannu ta goge tana fadin

" Alhamdulillah "


Arman ya kalli midwife din yace

" Ina matata ? Ya fada yama manta mamama na wajen

Midwife din tace

" Cikin ikon Allah ta haehu lafiya amma tasha wahala dan har jijjiga taso ta farayi, se Allah ya taemake ta, amma yanzu tana dakin hutu "

" Ya salaam " suka hada baki wajen fadar hakan, Arman yayi gaba, yayinda duk suka bishi da kallo

A hankali ya tura qofar dakin ya shiga shi 1, abinda yasa be nemi suje da kowa ba dan yasan hakan ya sa6awa tsarin asibitin, shima dan likita ne shiyasa ya shiga,

Kamar yadda ya tsammata tana kwance tana bacci, ya qarasa yaja kujerar dake ajje a gefen gadon ya zauna sannan cike da qauna kulawa ya kamo hannunta ya sanya a cikin nashi yae kissing din hannun, Sannan ya miqe ya bata kiss a goshinta kana ya koma ya zauna yana fadin

" Sannu kinji baby, Uban masu gida ya bawa wannan mummyntasa wahala, Allah ya miki albarka ya baki lafiya "


.........Seda tayi kwana 3 sannan aka sallameta daga asibitin, kae tsaye gidan na Arab aka wuce da ita kuma part din mamama, Wata irin kulawa take samu daga wajen mamaman uwa Uba kuma daga wajen abin qaunarta Arman, ga sauran en gida ma da suke bata wata shahararriyar kulawa.

Ana saura kwana 1 suna, en Maiduguri suka iso da tawagarsu, wata kulawar ta sake qaruwa a wajen sanah da babynta, dan kam har yanzu bata san menene raeno ba, indae ba abinci yaron ya nema ba, toh yana wajen wata daga cikin en gidan, yanzu ma hakan ce ta kasance,

Tana zaune a dakinta kan gado waya take da Arman yana tambayarta lafiyarta dana babynsu tace

" Muna nan lafiya baban baby "

Dae_dae lokacin wata yarinya Ameerah da sukazo daga Maiduguri ta shigo da babyn a hannunta, ta qarasa ta miqa mata shi tace

" Aunty umma ce tace a kawo miki shi, wae yunwa yake ji "

Kae kawae ta daga mata tana kar6ar babyn

Arman da yaji abinda yarinyar tace yace

" Maza a bawa babynmu abinci "

Seta turo baki kamar yana wajen tace

" Fisabilillahi ayi mutum kullum cikin cin abinci yake "

Dariya Arman yayi yana fadin

" Toh ko se nazo ne an sake yin irinta ranar farko ?

Seta murguda baki kamin tace

" Zan ajje way..... "

Bata qarasa ba babyn ya tsandara kuka yana wuwwulga hannu

Arman yayi dariya

" Awwnn, kingani koh ? Baya so ki ajjewa daddynsa waya "

Turo baki ta sakeyi sannan ta kalli babyn nasu daketa wawurar rigarta.

_____Ranar suna ta zagayo, babyn yaci suna Alqaseem ( sunan daddy ) sedae za'a dinga kiransa da junior, Daddy yayi matuqar farin cikin jin takwarasa ne dan haka akwati daban daddyn ya hadawa takwarannasa alqaseem jr ,

Sanda suka dawo gida da asuba Arman na shirin shigewa baffah ya janyoshi yace

" Malam aena dauka yusuf za'a saka ! Shine aka wani saka sunan wancan tsohon, ga suja me jini a jika ?

Murmushi Arman yayi sannan ya shafa sumar kansa yana fadin

" Ahh ae babu damuwa baffah, In sha Allah Brigadier general yusuf na nan zuwa wata shekarar " ya fada yana dariya gami da wucewa

Baffah ma yayi dariya yana kae masa duka.

....Me jego tayi ado kala kala, anci ansha, sannan anyi rabon memo, sticker hadda cotton bag me dauke da sunan jaririn 6alo_6alo wato ALQASEEM ARMAN ALQASEEM ( Junior ), haka mamama ma tayi shigarta me kyaun gaske a matsayinta na uwar taro, shi kam Arman yau throughout bega matartasa da junior ba dan kuwa bema shigo gidan ba kwata kwata saboda baqin dake cikin gidan.

Bayan suna, haka Arman ya cigaba da kasancewa a 6angaren mamaman kullum sedae idan baya nan, amma indae yana nan indae yazo toh baze fita ba sedae idan zeyi sallah ko dare yayi sannan yake komawa part din mazan gidan, dama ya dade da dakko kayansa ya dawo dasu gidan dan baze iya zama yana can wata unguwa sanyin idaniyarsa na wata unguwar ba, gwara ya zauna inda duk sanda yake son ganinsu ze gansu.

....Yana zaune a dakin riqe da junior a hannunsa wanda yakewa wasa, shi kuma yana ta 6a66aka dariya, yayinda ita kuma tana toilet, mintuna wajen 10 ta fito, yana ganin ta fito ya ajjiye junior yana fadin

" Kwanta kayi wasa, dad ze taemakawa mom " ya fada yana qarasawa wajen sanah dake qoqarin saka riga, seya fara taemaka mata da zuge zip bayan ta saka din yana fadin

" Kinsan aeki na ne meye na wahalar da kanki ?

Daya gama zuge zip din, seya dora kansa a kafadarta yana qoqarin magana mamama ta shigo dakin, se tayi turus kafin ta faara sallallami tana tafe hannu

" Zo ka fita " ta fada tana nuna masa hanya

Se yaji duk kunya ta kamashi, yayi qasa dakae sannan sum_sum ya fice daga dakin, be sake cewa komae ba,

Mamama ta juyo ta kalli sanah dake wasa da gefen hannun rigarta tace

" Ke kuma kin kyauta kinji, toh karku damu dukkanku na kusa tarkataku Ku barmun gida haka nan "

Ita dae sanah ba tace komae ba, dan kuwa Arman ya gama muzantata a wajen mamaman.

____Seda sanah tayi kwanaki 42 a gida sannan mamama da kanta ta dauketa ta maedata gidanta bayan tasha gyara na musamman, shi kam Arman Allah ma ya gani haqurinsa ya qaare dan haka yau daga asibiti kae tsaye gida ya wuce part din mamama

Da sallama ya shiga dakin mamama na zaune akan kujera tana karatun qur'ani, Seda takae qarshen ayar da take karantawa sannan ta dago ta amsa sallamar tana kallansa yanda yake wani sum_sum da kae kamar munafiki, ya nemi waje ya zauna bayan sun gaesa seya shafa sajensa amma ya kaasa cewa komae, Dan haka mamama ta tari numfashinsa da fadin

" Matarka ? Na kaemaka ita gida dazun nan, dan haka ba seka 6ata yawun bakinka ba tashi ka tafi "

Besan sanda ya saki wani murmushi ba sannan ya miqe yana fadin

" Angode, Angode mamama, Allah ya qara girma "

" Ameen_ Ameen " ta fada tana binsa da kallo lokacin da yake fita daga dakin, mamama ta saki murmushi tana girgiza kae sannan ta janyo qur'anin ta cigaba da karantunta.


Cikin matuqar farin_ciki yake driving sanda ze koma gidan nasa, a haka harya qarasa.

___Tana tsaye bakin mudubi bayan ta fito daga wanka tana mulke hannayenta da wata humrah da aunty ilham ta bata ya shigo dakin, Seda ya tsaya ya qare mata kallo yadda yaga ta qara wani fadi tayi kyau abinta, se kuma a hankali ya taaka zuwa Indi take din ya rungumota ta baya, bata san da shigowarsa ba dan haka tana shirin saka qara, kyakykyawa kuma sassanyan turarensa ya bugi qofofin hancinta, seta

Please Login or Register in order to submit comment