Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta jefa wayarta ba ballantana ta kirashi dan haka kawae ta hau motar suka dauki hanyar gidan nasu na Arab

Duk wasu tunane_tunane da suke zuwar mata a qwaqwalwa haka ta watsar dasu ta cigaba da janyo duk wata add'uar neman tsari da tazo bakinta har suka iso gidan .

Ba baqon abu bane ganin sojoji a gidansu ba, amma yau ganin harda en sanda ya sanya haka kawae ta ji gabanta ya fadi

Can ta hango wani abu a kwance wanda zata iya kira da gawa a lullu6e , a take a lokaci guda jikinta ya soma 6ari tana tunanin wanda ya rasu a gidan nasu Daddy ne ? Ko mamama ?

Tunanin nata ya katse sanda ta hango mamama zaune a kan wata kujera

Jiki babu qwari ta qarasa wajen mamaman, ta zube akan gwuiwoyinta ta kamo hannayen mamaman fuskarta cikin wani iron yanayi dana kasa fahimtarsa tace

" Mamama waye ya rasu ?

Wasu sabbin hawaye ne suka sake zubowa mamama tana kallan Sanah cike da tausayawa amma ta kasa cewa komae

Sanah ta sake fadin

" Mamama pls ki fadamin wanene ya rasu ?

Umma dake gefe tace

" Kiyi haquri sanah arman...."

Kafin ta qarasa fada sanah tace

" Baby baya nan ! Ya fita, be masan na taho ba, nidae don Allah Ku fadamin "

Cikin kuka umma tace

" Kiyi haquri Sanah Arman ne ya rasu "

Seta saki hannun mamaman da sauri kamar wadda aka yiwa wani Abu, ta miqe a hankali ta fara ja da baya. tana girgiza kae fuskarta dauke d wani irin murmushi

Umma ta miqe da sauri dan riqota Sanah tace tana dakatar da ita da hannunta

" Karki Matso kusa dani ! Karki sake ki matso ! Ta yaha zaki cemin baby ya mutu ? Baby fah ? jiya fah ya gama fadamin ze kasance dani har abada, amma yanzu kinzo kina cewa wae ya mutu ? Kinsan abinda kike fada kuwa ? Ta fada tana sake girgiza kae tana hana hawayen da suke kwance cikin qwayar idanunta zuba

Aekuwa ta sake karyar musu da zuciya, Mamama dake zaune ta samu damar tasowa a hankali ta qarasa ta riqo sanah ta rungume a jikinta

Se a lokacin kukan da sanah take riqewa ya fito fili kafin cikin kukan tace

" Don Allah Ku tasheni daga wannan mummunan mafarkin da nake ! Meyasa abubuwa suke zuwa ba'a lokacin daya dace ba ?

Mamama tae sauri ta rufe bakin sanah din tana jin wasu hawaye suna tsere a kumatunta

" Mamama bafa baby ne ya mutu ba , ki fada musu , ya Riga da yamin alqawari fah mama....." Bata qarasa fada ba mamama taji nauyinta ya qaru wanda hakan ya alamta mata cewar ta suma.

Dae_dae lokacin motarsu daddy ta shigo gidan kasancewar basa nan duka Manyan gidan sun tafi wata gaesuwa

Jiki a sanyaye jikinsu suke saukowa daga motar

Kae tsaye wajen gawar suka nufa

Daddy ne ta fara tsugunnawa a hankali cikin wani irin yanayi na kidima ya yaye abinda suka rufeshi dashi , ba zakace ma hatsari yayi ba banda karcewar da gefen fuskarsa tayi

A hankali daddy ya kae hannunsa saetin zuciyar Arman din dan tabbatarwa kansa cewar da en sanda suke Arman dansa tilo, shalelensa, yaro 1 tamkar da dubu ya rasu....................


Daga haka se ince mu hadu bayan sallah In Allah ya kaemu da rae da lafiya, fatan zamuyi sallah lafiya

Nasan tambayoyi fall a cikin ranku, bari inyi shishshigi in fadi tambayoyin da nasan sune suka fi damunku a rae da zuci

Su waye suka kaewa Arman hari ?

Sgin Arman y rasu ?

Toh kuyi haquri bayan sallah duk zaku samu amsoshin tambayoyinku In Sha Allah


Mhiz Innocent ce..........✍️


*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

Page 41

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e


_Wannan page din sadaukarwa ce a gareku team Arman_

..............Daddy y kulle idanunsa cike da fargaba gami da faduwar gaba ya qarasa da hannun nasa saetin zuciyar Arman

Cikin wani irin yanayi dana kasa fahimtar a wane fanni zan ajiyeshi daddy ya juya yana kallansu Abba dake tsaye a kusa dashi , In a lower voice me cike da sanyi yace

" Baffah akwae sauran numfashi a jikin Arman !! Ya fada yana kallansu su duka , sedae kamar a hanzarce yae maganar

Wata qatuwar ajiyar zuciya dukkansu suka ajjiye, dae_dae lokacin da Daddy ya miqe

En sanda dake kusa dasu suka kalki daddy cike da mamaki

Jinjina kae daddy yayi alamar tabbatarwa yana kallan 1 daga cikin en sandan

Tuni cikin hanzari aka fara kiciniyar daukar Arman din zuwa wata motar daban wadda ta cikin gidan na Arab ce

Mamama dake gefe a tsaye ita da umma da Maman souban wadda fitowar ta kenan suka bisu da kallo cike da mamaki dan basu san akan abinda sukae magana ba .

A hankali daddy ya qarasa wajen mamama da sanah ke kwance a kafadarta

Mamama ta bishi da kallo kana ganinsa kasan jikinsa a sanyaye yake sedae ba taga wata alamar da zata nuna yasan da mutuwar ba , bayan kuma yanzu ta Ganshi a wajen

Ya qaraso sannan ya sakarwa mamama murmushi me taushi yace

" Albishirinki ?

Wasu ajiyayyun qwalla ne suka kwaranyo mata a kuncinta tana Kallan daddy cike da tausayawa dan taga alamar har yanzu besan da mutuwar ba

Umma dake kallansu ta qaraso jiki a matuqar sanyaye ta kar6i sanah sannan ta qarasa da ita cikin gidan kafin a wuce da ita asibiti

Daddy yace yana murmushi

" Rahama ki bar kuka Arman be mutu ba !!

Seta tsaya da kukan tana kallansa ido cikin ido, abinda bata ta6a ba kenan

Ya jinjina mata kae alamar tabbatarwa sannan ya dora da

" Ki tashi yanzu mu tafi asibiti, za'a dubashi dan kuwa akwae sauran numfashinsa a duniyar nan "

Haka kawae kamar wata sokuwa seta miqe tabi bayansa har suka qarasa wajen motar

Kafin daddy ya koma cikin gidan suka fito tare da umma da sanah suka wuce asibitin baki 1.


****Kae tsaye emergency suka wuce dashi dan bashi taemakon gaggawa, Cikin mintuna kadan likitoci suka hadu a kansa suka fara aekinsu cike da qwarewa sedae ya shiga coma ne dan haka har lokacin da suka gama abinda zasu masa be farka ba , dan haka aka wuce dashi wani ke6antaccen daki dake Cikin asibitin wanda ake kae masu matsala irin taasa .


.........A hankali ta fara bude idanunta tana rufewa tana budewa hakan yasa dogayen gashin idanunta suka jiqe da ragowar hawayen dake kwance a cikin qwayar idanunta

Da sauri mamama dake zaune gefenta ta miqe ta qarasa bakin gadon tana kamo hannayenta sannan cikin taushi tace

" Sanah "

Seta sauke idanun nata akan mamama wanda a lokacin wasu hawaye masu dumi suka zubo mata a kumatunta cikin shaqaqqiyar murya tace

" Mamama ina baby ?

Murmushi me hade da kuka kuka mamama ta saki sannan a hankali tace

" Ki kwantar da hankalinki sanah, Arman yana nan qalau "

Seta fara qoqarin tashi zaune , mamama ta taemaka mata ta zauna din sannan tana kallan mamama tace kamar zatayi kuka

" Mamama don Allah ki fadamin inda baby yake ! Inason na ganshi ne don Allah "

Cike da tausayi mamaman ke kallan diyarta ta

" Ya isa haka ! Ba zasu bari ki ganshi ba yanzu haka sanah, sun shigar dashi wani daki ne "

Se ta saki wani murmushi tana qissimawa ranta lallae haqiqa kenan mafarki tayi babyn ya mutu tunda gashi mamama na fada mata yana daki

Seta fara qoqarin sakkowa daga kan gadon dukda rashin qwarin jikinta ga zazza6in data kwana dashi jiya

Mamama tayi saurin riqota , sedae wannan karon bata ce komae ba ta taemaka mata tana kallan ta cike da tausayawa

" Mamama don Allah inason na ganshi " ta fada kukan da take riqewa na fitowa

Mamama ta riqeta suka fita daga cikin dakin, kae tsaye wajen daddy suka nufa, kafin su qarasa daddy ya qaraso kasancewa yana waje baya cikin office dinsa

" Ahh rahama ya akae kika fito da ita ?

" Wlh daddyn Arman ta daage ne tana son ganinsa koda yadda za'ae "

Har zece a'ah seya kalli sanah din wadda idanunta sukayi rau rau gwanin tausayi dan haka yace

" Ohk muje "

Mamaman ce dae ta sake mata jagora har qofar dakin, daddy ya bude ya tura qofar sannan ta shiga ciki, mamama na komawa da baya ta zauna dan yadda taji zuciyarta ta karye

Wayar daddy ce tayi qara yana dubawa cike da mamakin ganin kiran , dan shi kam sam yama manta da maganar Dr Stephen

Ya kaara wayar a kunnensa bayan ya sannan accept

Daga 1 6@ngaren Stephen yace

" Dr ! Na jika shiru and yarinyar ce ta damu akan lamarin shiyasa "

Daddy ya dafe kansa cikin rashin sanin abinyi sannan ya tattara kalaman bakinsa yace

" Sorry dr, but abinda yasa ka jini shiru wlh Arman dinne ya samu hatsari yau din nan "

Dr Stephen yace bayan ya jajanta lamarin

" Zamu shigo ñigeria next month har momynta couz gobe ma zamuje qasarsu mom din nata ne semu taho tare da ita mu dubashi and muyi maganar auren nasu "

" Ohk then, Allah ya kaemu "

Stephen yace

" Amen, quick recovery I pray "

" Thanks " daddy ya fada yana katse kiran

Mamama ta kalleshi dan yadda taga damuwa ta bayyana qarara a fusarsa bayan hakan ba dabi'arsa bace tace

" Yalla6ae lafiya dae koh ?

Seya sauke numfashi kamin yace

" I hope so, but....." Se kuma yayi shiru dan baya son qara mata damuwa kafin yace

" Babu komae " yana sakar mata murmushi lokacin guda yana miqewa ya dora da fadin

" Bari na koma wajensu baffah, inta fito ta janyo qofar "

" Tohm " mamama ta fada tana bin mijin nata da kallo

A hankali ta qarasa bakin gadon nasa tana kallansa tun daga kan qafarsa harkan kyakykyawar fuskarsa wadda ke manne da oxygen amma dukda haka hakan be hanata kallansa ba

Sannu a hankali ta sake matsawa dab dashi sannan cikin sanyi ta kamo hannunsa ta saka cikin nata sannan ta tsugunna tana dora kanta akan qirjinsa

" Baby ka yafemin don Allah, ka tashi ka farka Ina sonka !! ina qaunarka baby, don Allah ka farka haka nan " ta qarasa fada tana fashewa da wani kuka me tsuma zuciyar me sauraro tana sake qanqame tattausan hannayen nasa

Taku taji a bayanta alamar shigowae mutum kenan, dukda taji takun hakan be hanata dagowa ba, ta cigaba da kwanciyarta kan qirjin nasa

Ya qaraso yana harde hannayensa a qirji sannan yace
na

" Ya jikin nasa ?

Se a lokacin ta dago a hankali ta sauke dubanta akan fuskarsa

Yana nan dae kamar yadda ta sanshi a barrister souban dinsa

Seta dauke kae tana lumshe ido akan Arman tana budewa a lokaci guda sannan ta maeda dubanta kan souban sannan tace

" Alhamdulillah "

" Ae tun dazu na shigo dakin amma naga ba kiji shigowata ba saboda kin shiga soyayya " ya fada yana murmushi

Se taji kunya ta kamata dan haka ta murmusa tana sake kallan Arman din

" Allah ya qara afuwa " ya fada yana ficewa daga dakin

Seta sake komawa wajen Arman din dan yadda takeji yau din kamar tayi ta zama a jikinsa, hak kawae taji tana enjoying hakan .

**Bayan fitowar souban daga asibitin kae tsaye police station ya wuce inda aka kae wadanda suka janyo hatsarin Arman din


Sanda yaje ba'a kae ga sakasu a cell ba ana dae tuhumarsu ne

Wani dan sanda wanda ya fusata da lamarinsu yace

" Wlh za'a wuce daku court ne kae tsaye tunda an riga an kamaku red handed kune kukae causing wannan accident din "

Black ya juyar dakae yace

" Mufa bamu bane muka aekata laefin nan ba "

Wani daga cikin en sandan da shigowarsa kenan ya tsinci maganar da suke yace

" How dare u zakuce baku bane ? Ko akwae wani abun da kuke son fada bayan wannan ?

Black yace yana kallan dan uwansa

" Mufa sakamu akayi bamu da hadi da mutumin ma "

" Oh yah fada mana wanene ya sakaku ?

Dae_dae lokacin da souban ya qaraso cikin wajen idanunsa suka sauka akansu black wanda shima ya dago idanunsa suka hada ido da souban

Take a lokaci guda jikinsa yayi sanyi, toh tunda dae yaaga lamari na neman ca6ewa gwara ayita ta qare, dole su fadawa en sandan nan gaskiyar al'amari, su fada musu gaskiyar wanda yake sakasu wadannan ayyukan da suke dan kuwa yau ranar tonon silili ce............................

Kuyi manage da wannan

_Gskia team Baby Arman kun bani mamaki 😹, wae yama sunan novel din ne ? Kuyi tunani sannan ku bawa kanku amsa_

Fatan anyi sallah lafiya en uwa, Allah ya maemaeta mana yasa muna da rabon ganin ta badi Ameen 😻🫶

Daga alqamin Mhiz Innocent...............✍️



*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

Page 42

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e



.............Seya dauke kansa daga kan souban ya kalli en sandan yace dae_dae lokacin da souban ya qarasa shigowa cikin wajen

" Khalid ne yake sakamu wadan nan ayyukan !

" Waye kuma khalid ? Dan sandan ya fada a fusace

Black ya nuna souban yace

" Wannan yasan waye Khalid din !

Cikin rashin fahimta souban wamda fuskarsa ma seda ta nuna hakan yace

" Ni ? Waye Khalid kuma ?

Abokin aekin black din yace

" Khalid dae na gidanku "

Cikin matuqar kaduwa souban yake kallansu su duka yana mamakin wannan kalami nasu, anya kuwa gaskiya suke fada ? Ko kuwa sun fada ne kawae dansu kaare kansu ?

Seya kauda duk wasu tunane_tunane da suke zuwar masa ya kallesu rae a 6ace yace

" Kada kuyi qoqarin laqabawa wani laefin da beji ba be gani ba danku ku6utar da kanku, yin hakan sake jefa kanku kuke cikin matsala Wanda basu san da hakan ba "

Black ya gyara zama fuskarnan tasa kamar ko yaushe babu annuri yace

" Qwarae da gaske Khalid ne ke sakamu wadannan ayyukan, bama sace ka kadae da akayi ba, bayan kuma wannan accident din da arman yayi, ya ta6a sakawa mun sace ita kanta sanah din kwanakin baya "

Souban ya yamutsa kansa yana sake kallansu cikin kullewar kae couz he is damn speechless

Se Dan sandan ne yace

" Yanzu a ina zamu sameshi ?

Black yayi musu kwatancen inda yake da tabbacin za'a sami Khalid in be sameshi bama ya bashi wani address din in case .


.........Mamama ta qaraso ta zauna akan kujerar da sanah take zaune tace

" Sanah ki tashi haka mu tafi koh ? Dare yana yi "

Seta kwa6e fuska kamar me shirin sakin kuka tace

" Plss mamama ni anan zan kwana "

" A'ah ki tashi mu tafi haka nan "

Se tayi rau rau da ido tana kallan mamaman

Mamama tace

" Let's go ! Gobe da safe In Sha Allah se kizo uhmmm ?

Seta gyada kae tana miqewa suka fice .


Tunda suka koma gida ta wuce dakinta mamama ke binta da kallo, ta fahimci wani al'amari ya faru da diyarta ta wanda wannan qaddarar ta hanata samun kulawa daga Arman din dan haka bayan sallahr Isha'i mamama ta gyare diyarta ta tsaff, dukda kunya da sanah din ta nuna amma ita mamaman ta murje idanunta tayi kamar bata san me take nufi ba .

*****Tun daga ranar ya kasance kullum sanah a asibiti take wuni, dukda ba wani ganinsa take sosae ba kuma ba jin maganarsa take ba, bata gajiya da zuwan se dare kamin take dawowa .

Kamar kullum yauma da ciwon kan ta dawo, ta shige dakinta kae tsaye ta fada toilet tayi wanka da ruwa me dumi saboda zazza6in daya saba rufe ta duk dare, ta dawo kan gadon ta ja blanket ta kwanta

Kafin takae ga kwanciyar mamama tayi sallama a dakin, bata iya amsawa ba se miqewa zaune da tayi da murmushi kan fuskarta

Mamama ta qaraso ta zauna gefen gadon tace

" Sanah ina fah lura dake bakya cin abinci kwanan nan , meye hakane ?

Seta yamutsa fuska tana fadin

" A qoshe nake ne mamama "

" ban yadda ba, Dan haka ki tashi kwae ki wuce muje kici "

Seta maraeraece fuska

" Allah mamama bana son tashi zazza6i ne a jikina "

" Subhanallahi, bari na kawo miki abincin daki in yaso se kici anan "

Haka ba don tana jin yunwa ba ta amsa da " Toh "

Minti 10 baya mamama a shigo da plate din fried rice with lever ta qarasa gefen gadon ta zauna, kana ta miqa mata plate din tana fadin

" Oh yah tashi kici in gani "

Seta kar6i plate din da spoon ta dora kan qafarta sannan ta fara juya abincin

Sam Sam qamshin beyi mata ba hakan yasa ta faara kwa6e fuska kafin tayi maza ta ajjiye shi kan side drawer tana shafa wuyanta tace

" Mamama bazan iyaci ba Allah sosae zazza6in ya kamani fah "

Cike da tausaya mamama tace

" Ohk ki kwanta zuwa da safe idan zazza6in be sauka ba se muje hospital ko daddy ya dubaki "

" Tohm Mamama " ta fada tana komawa ta kwanta gami da Jan blanket din.


Washe_gari har wajen qarfe 9 sanah bata tashi ba, bayan hakan ba al'adarta bane, kuma musamman yanzu data Riga ta saba qarfe 8 ce take mata a asibiti, Dan haka mamama ta qarasa dakin, seta hangeta can tana baccinta hankalinta kwance

Mamama ta qarasa ta dafa goshinta se taji babu zafi ko kadan alamar babu zazza6in a jikinta Dan haka a hankali ta fara tashinta

A hankali tayi miqa tana hamma gami da addu'a sannan ta fara murza idanunta

Mamama tace

" Qarfe 9 fa sanah kina ta bacci "

Seta turo bakinta tace

" Allah bansan har 9 tayi ba "

" Toh ki tashi ki shirya ko yau ba zakije ba ?

Da sauri ta girgiza kae kamar qadangaruwa tana saukowa daga kan gadon, yayinda ita kuma mamama ta fita daga dakin

Sanda ta fito qarfe 10 ta kusa t.b na kunne tana aekinta dan haka ta zauna akan kujerar parlourn tana jiran fitowar mamaman

Ba tafi mintuna 10 ba taji wani irin bacci me dadi yana sakadarta, seta sulale akan carpet tayi kwanciyarta abinta, nan da nan kuwa cikin qanqanin lokaci baccin ya dauketa.

Mamama a sauko daga sama seta hangi sanah din kwance kan carpet, ta qarasa da sauri tana ta6ata, babu zazza6i a jikinta kwata kwata seta fara qoqarin tashinta tana fadin

" Sanah !

Ta tashi a hankali tana kallan mamaman

Mamama tace

" lafiya dae koh ?

" Ehh mamama kawae baccin ne be isheni ba "

" Ohk toh ko kawae kije kiyi baccin, gobe se kije "

Da Sauri ta girgiza kae tana turo baki tace

" A'ah zanje ni dae "

Murmushi mamama tayi ba tare da tace komae ba ta bita da kallo sanda take qoqarin fita daga dakin.

Yau kam tare sukaje asibitin da amrah,

Suna qoqarin shiga cikin asibitin shi kuma souban yana qoqarin fitowa daga ciki

Se sukayi kaci6us dukkansu suka tsaya

Da murmushi kan fuskarsa ya kallesu su duka kamin yace

" Barkanku da zuwa "

" Ina kwana ? Suka hada baki wajen fadar hakan

" Alhamdullillah " souban ya fada

Amrah tace

" Yah souban wae dama ka dawo ? Amma ban ganka a gida ba "

Murmushi yayi yana shafa gashin bakinsa yace

" Ehh ! Ina wani aeki ne shiyasa ban shigo gida ba, but na kusa gamawa, ina gamawa zan dawo In Sha Allah "

" Tohm Allah ya kaemu "

Ita dae sanah se tayi gaba couz she's eager taga babyn nata

Itama amrahn tana shirin wucewa souban yace

" Qanwata kodae kinyi missing dina ne ?

Se tayi farrr da ido tana dariya ba tare da tace komae ba

Shi kuma souban yace

" Ki wuce ku dubashin, bye "

" Ohk " tace sannan tayi gaba

Yanzu kam an dan faara bari ana shiga dakin da yake, amma sedae a ganshi kawae ba'a zama a dakin.

Qofar dakin a jaye take dan haka suka tura dakin suka shiga

Amrah batafi minti 5 ba ta fita daga dakin tana fadin

" Ina jiranki a waje "

" Tohm " sanah ta amsa da hakan tana qarasawa wajen gadon nasa

Kamar koda yaushe ta kae tattausan hannunta kan hannunsa ta riqesu gam kamar wadda za'a qwacewa shi, sannan takae kanta kan qirjinsa kamar kullum idan tazo

Yau kam se taji ya damqe hannun sosae sa6anin da ita kadae take riqewa babu wani reaction daga 6angarensa

Da sauri ta miqe daga kwanciyar da tayi tana kallan hannun nasu da yake a cikin na juna

Wata qwallar farinciki ta samu damar kwaranyo mata, lokaci guda wani sassanyan murmushi ya kubce mata

Seta maeda dubanta kan kan kyakykyawar fuskarsa tana kallansa sosae

Hakan na nufin idan ta fadi wani abun zeji ta ? Imma baya jinta tasan dole yasan itace a wajen tunda gashi ya riqe mata hannu shima, Dan haka seta ranqwago saetin kunnensa a hankali ta fara magana cikin sanyi

" Babyyy ! Ta fada tana jan qarshen sunan

Tana shirin dorawa daga nan seta lura da wani hawaye daga idanunsa na 6angaren da take

Seta kaasa qarasa fadar abinda tayi niyyar fada din ta tsaya kamar wata sokuwa tana kallansa

Ae yanzu kam ba qwalla ba seta fashe da kukan da taketa riqewa tun dazun

Amrah dake zaune bakin qofar dakin ta qarasa shigowa jin kamar sheshsheqar kuka

Da sauri ta qarasa shiga qirjinta na bugawa tace

" Sanah meya faru ?..

Kafin ta qarasa maganar sanah ta qaraso ta rungumeta tana sake fashewa da wani sabon kukan

Amrah ta sake rudewa tace

" Sanah don Allah ki fadamin meya faru ?

Seda tayi me isarta sannan tace

" Amrah, baby ya kusa warkewa ! Yau har riqemin hannu yayi fah "

" Awwwwn love kids " ( In muku irinta wata crazy sister of myn 😹 ) Amrah ta fada tana murmushi sannan ta dora da fadin

" Allah sanah bansan sanda zaki girma ba, memakon ki godewa Allah shine kike kuka "

Seta tashi daga kafadar amrahn tana harararta gami da murguda baki

Murmushi Amrah tayi sannan ta juya dae_dae lokacin da ita kuma Sanah ta koma wajen babyn .


***Tunda suka dawo Amrah na 6angarensu sanah a dakinta, wajen qarfe 8 sanah ta kalli Amrah tana yamutsa fuska tace

" Wlh kaena ciwo yake Amrah, ga wani irin bacci da nakeji, bans so in fadawa mamama kar hankalinta ya tashi shiyasa ban fada mata kullum da zazza6i nake kwana ba "

Amrah tace

" Subhanallahi, sanah ae gwara ki fada mata kinga ae ko asibiti se kuje koh ?

Seta sake yamutsa fuska tace

" Ni kam Allah ki qyaleni banson zuwa wani asibiti "

" Ohk bari na samo miki magani kisha " Amrah ta fada tana miqewa

Seta riqota da sauri tana fadin

" Ke ni bana so Allah kuwa "

Ba tabi ta kanta ba ta wuce part dinsu.

Mintuna wajen 3 se gata ta dawo da maganin a hannunta ta miqa mata tace

" oh yah take it "

Juya baya tayi tana qoqarin kwanciya

Amrah tace

" Wlh zanje in fadawa mamaman in yaso seku tafi asibitin may be ma allura za'ayi miki " Amrah ta fada tana juyawa kamar zata fita

Seta tashi zaune kafin ciki ciki tace

" Kawo !

Amrah ta juyo, ita kuma sanah ta jefa mata wata uwar harara kamar idonta ze tsinko

Ita dae amrah bata bi ta kanta ba ta dauko rubber water ta miqa mata da maganin, ta kar6a kafin ta fara sauke wasu ajiyar zuciya kamar me shirin daukar wasu kaya masu nauyi

Seda ta gama ajiyar zuciyar sannan ta sha maganin ta kora da ruwan, sannan taja blanket ta kwanta

Amrah tace

" seda safe, Allah ya qara lafiya "

Bata amsa mata ba ita kuma bata damu ba danta san haushinta take ji, dan haka kawae ta fice daga dakin.


Tana nan kwancen taji cikinta na wani irin murdawa dan haka da Sauri ta miqe zaune tana riqe cikin nata, ga wani tashin zuciya da take ji kamar wadda taci wani abu me qarni bayan babu abinda ke cikinta se tea, bata gama tunanin ba tayi wani yunquri a guje ta fada toilet tayi ta kwara amai kamar zata amayar da kayan cikinta, yi take tana qarawa harda qaramin kukanta, seda ta gama ta gyara jikinta sannan ta fito daga toilet din tayi sauri ta haye kan gado kafin ma mamama ta shigo ballantana ta fahimci wani abun na damunta .


********A daya 6angaren kuwa tun ranar dasu black suka bada address din inda za'a sami Khalid en sanda suka fara bincikensa, address na farko basu sameshi a can ba saboda haka suka yi fakonsa a

Please Login or Register in order to submit comment