Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsokane ni b shine n daketa shi km y dakeni wae mys xan dinga fada a makaranta "

cikin hade rae arman yce

" ina kika barshi ?

tce

" yana primary section tun daxu "

tare suka tafi primary section din dukkansu har souban

aekuwa sukae saa yana shirin fitowa daga section din

arman y tura shi ciki yana fadin

" me baby ta maka ka daketa ?

tintsirewa d dariya Khalid din yyi yce

" aou wato har ta kawo maka qarata koh ? Toh data kawo maka qarartawa ka isa kayi min wani abin ne ?

y kalli gefensa souban na tsaye shima fuskartasa babu walwala yce

" ohh wae hadda kae toh wato dae inna fahimta actors ne kenan suka xo wajen boss daukar fansa "

haushi y qulardasu aekam nan sukayi kansa sukayi dambe ya6e ya6e

toh dama sarkin yawa yafi sarkin qarfi

aekam haka suka bar Khalid d fashshshen baki sukayi tafiyarsu..............

Mhiz Innocent ce ✍


*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

Page 5

~08105359153~
Number dina d take always welcoming naka a DM 😍 but pls message me amfani couz number nan an tanade ta ne especially sbd ku 🌚😻

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 😍


daedae lokacin d driver yazo daukar su

dukkansu suka shiga motar sedae Khalid har ynxn be taho b

sunfi 20mins suna jiransa amma be fito b

arman y kalli driver

" pls muje gida kwae may be y tafi d kansa "

haka suka tafi gidan sanah na gefe kusa d arman ta kwantar d kanta kan cinyarsa.


Wajen qarfe 3 suna xaune shi d souban a parlourn mamama suka jiyo hayaniya a compound din gidan

dukka sukayi shiru b wanda y fita

suna nan a haka afrah ta leqo

" yah souban wae kuje inji daddy kae d yah arman "

babu musu duk suka miqe suka fito

aunty ce riqe d Khalid tana surfa ruwan bala'i

"dan shi ba dan gidan bane ae ba shine xesa a cuceshi inyi shiru b banda tsabar rashin mutunci sun maedashi wani bare a cikinsu dan yana cikin gidansu ae naga dae a wajen uwarsa yake ba wajen wani b "

daddy y faara gajiya d wannan bambamin nata dan haka y hade rae yce

" yah inaso in gyara al'amari ke kuma kinaso ki 6ata ? ki bari pah abida ki saurara kiga abinda xanyi "

sum sum souban d arman suka xube a wajen dan sunsan laefin d sukayi

daddy yce

" meya hadaku d Khalid ?

arman yce

" daddy xuwa yayi y xane baby...

yimin shiru shashasha xane ta kamar yaya ? shi Khalid din bashi d hankali daze xaneta
kae Khalid wae hakane ?

gunguni Khalid din y fara yana
" aaah..ahh..ni ba xaneta nayi b kwae dae n daketa ne sbd tayi b daedae b "

daddy yce

Toh ke kinji dalili amma kinxo kina dagawa mutane murya salon kowa ma se yaji abinda y faru "

kae souban , arman kar ku sake dukan sa ba dan uwanku bane xaku masa haka ?

" Kae kuma Khalid " y fada yana kallansa

" kada k sake dukanta ba kaga yarinya bace ? ae fada ya kamata ka dinga yi mata b duka b yaro baya jin duka sedae fadan kaji koh ?

haka dae ya cigaba dayi musu fada sosae kapin y qyalesu.


Rayuwa ta cigaba d garawa tana tafiya b tare d jiran kowa b kwanaki sukayi ta shudewa satika na wuce wa watanni suna xuwa suka hadu suka bada shekaru masu yawa shaquwa na qara shiga tsakanin arman d sanah haka tsakaninta d souban ma.


Fitowarsu kenan daga class su ukun sanah, amrah, d afrah

kansu 1 badan banbancin kamanni ba xaka iya kiransu d en 3 indae har girmansu kwae xaka kalla

yanxu haka suna jss 2 ne

ita dae sanah se murmushi take saki

afrah ce ta kalleta

" ke kuma sanah meye kike ta wani murmushi ?

harararta tayi tana murguda baki

" ae kinsan dae yau baby xasu dawo koh ? Ni wlh nayi missing nasu badly inke baki yi b "

amrah ce tayi dariya tace

" ji beta don Allah se kace wadda tae shekara bata ga babyn b "

" ehh naji din ina ruwanki ? sanah ta fada tana sake hararar amrahn

aekam cikin sa'a suka Tarar drivernsu har yaxo Dan haka babu 6ata lokaci suka wuce

sanah ji take kamar ta kar6i driving din dan gani take kamar baya gudu a haka dae suka qarasa gidan.


Mamama xaune gefen arman dke cire agogonsa se Dada kallan agogon yke

yce

" mamama wae har ynx baby shiru pah ?

" ohh ni !! Mamama ta fada tana dafe kae

se kuma ta maeda hankalinta kan qofa jin alamar tafiya tace

" toh babyn baby ae gata nan "

sanah na shigowa ta jefar da jakar bayanta ta taho da gudu tana fadin

" oyoyo baby ! Ta fada jikinsa

d sauri y dagata yana fadin

" haba baby baki ga kin fara girma bane kinfa shiga secondary school "

turo baki tayi tana murguda baki

dariya ta bashi yace

" Iyeeee wato yau babyn kike murgudawa baki koh ?

bata ce masa komae ba tae wucewarta dakin ta dan cire uniform

binta yayi d kallo yana mamakinta kenan wae hattayi fushi ?

tashi yayi xebi bayanta sedae wata uwar harara da yaga mamama ta xuba masa ita ta hanashi qarasawa y dawo da baya

tce

" jeka dakinka kae wanka mu hadu a parlourn baffa kasan dae yau Friday ( duk juma'a a parlourn baffa suke haduwa gabadaya en gidan suci abinci haka da6iar su take )

bata jira amsarsa b ta wuce kae tsaye dakin sanah din

a kwance ta sameta kan gadonta ko uniform din bata kae ga cirewa b

mamama tace

" maza tashi ki shirya ki wuce parlourn baffa "

da " toh " kwae ta amsa amma tana kwancen
bata sake cewa komae b ta fice

yana ganin ta haye sama shi kuma y fada dakin

da sauri ta dago ta kalleshi ta sake kicin kicin d rae

ganin yana shirin fara yi mata magana ya sanya ta cire hearing aid din gabadaya ta ajjiye gefe

dariya ta bashi wato bama xataji me zece mata b

a hankali y qaraso y xauna qasan gadon yana fadin

" kaena bisa wuya na baby na dena miki fada kinji ?
y fada yana dago kafadunta

juyar d kae ta sakeyi y sake komawa gabanta yana kuma kama kunnansa alamar ya dena

sannan a hankali ta saki dariya tana janye hannunsa daga kan kunnensa

kana ta maeda hearing aid din ta tace

" na haqura pah baby "

yce

" yawwah toh in kin haqura tashi muje parlourn baffa "

tce

" toh k bari in shirya mana "

yce

" ohh toh kiyi sauri ina jiranki a waje !

" toh tace kapin ta dora d fadin

" aou baby nipah banga yah souban b ba tare kuke b ?

juyowa yyi kana yce

" ehh tare muke yana 6angarensu ko xakije ku gaesa ne ?

Ta6e baki tayi tana fadin

" a'ah ni!! wannan mamantasu bata d fara'a kamar xata daki mutum "

dariya ta bashi sosae shima dama tsokanarta yayi dan yasan baasa ga miciji d mamansu souban din

seda y qarasa fita sannan ta miqe itama ta shirya.



Yau gidannasu an tashi d hidima ne

sedae ita kanta bata san wadanda xasu xo b

mamama dae tace en uwanta ne xasuxo daga maeduguri haka akayi girkuna kala kala na gani na fada.

Wajen azahar baqin suka iso musamman aka kirata suka gaesa d baqin dukda bata sansu b

Haka dae suka gaesa tunda taji ance en uwan mamama ne ta koma.

Se washegari en maedugurin suka koma bayan suma sun kawo tasu tsarabar suma kuma suka tafi d wata tsarabar d aka musu a gidan Arab din d sukazo.




Shekarun d suka biyo baya abubuwa da daama sun faaru

ciki hadda xaman Arman babban likita

sannan souban kuma ya xama babban lawyer

shi dae khalid tun daga secondary school be dora b sbd bashi d raayin karatun se shashanci

yayinda Sanah kuma da qawayenta wadanda bata d kamarsu afrah d amrah suke a ss2 gabadaya

sun xama cikakkun en mata masu ji d wanka d aji uwa uba kuma kyau d qoqari dan kap ajinsu sune on top kuma dukkansu 6angaren science sukeyi.



Agogon dake ajiye kan mudubi y dauka y daurashi a tsintsiyar hannunsa

y dauki comb y taaje kanshi wanda ke dauke d kyakykyawar suma

fari ne qal me murdadden jiki dogon hancinsa kamar an xana shi yayinda baqin kwantaccen saje y qawata kyakykyawar farar fuskarsa

kae tsaye yke kallan mudubin kafin y daawo d dubansa kan agogon dke daure a tsintsiyar hannunsa *DOCTOR ARMAN ALQASEEM ARAB* kenan

Tsaki yaja yana kallan qofa daedae lokacin d aka turo qofar dakin

sanye yake d baqar riqa d wando suit d necktie a wuyan rigar fuskarsa dauke d murmushi yke fadin

"sorry man na barka kana jirana koh ?

BARRISTER SOUBAN AHMAD ARAB kenan

tsakin arman y kuma ja yana fadin

" kwae ka bar mutane tun daxu se jiranka ake kamar kayi shanya ?

"Ae shys nace sorry koh ? kaaga ni ynx dae b wannan b k dauki kayanka mu wuce kwae

Be tanka masa b kamar yadda yayi tsammani dama kuma y riga daya saba indae halin arman ne a kwanakinnan gabadaya ya wani bi y chanja

haka dae suka fito cike d kewar Cyprus din d sukaxo hutu

basu suka isa kanon dabo b se wajen la'asar.


Cikin matuqar farin ciki d kewa suke sakkowa daga jirgin a filin tashi d saukar jirage na Malam Aminu kano .

Fararen matasan d hutu y gama ratsatu y bayyana kansa d kansa ( ko d yake ae daama ance hutu ba munafiki bane inji wata qawata 😹 )

Dukda a cikin farin cik suke sedae fuskar 1 tafi nuna alamar hakan dan dayan fuskarsa babu yabo babu fallasa but se daga baya ne na fahimci ashe nature dinsa ne a hakan *ARMAN* a kwanakin nan gaba 1 y sauya y qara xama wani miskili na qin qarawa bansani b ko yanayin aeki ne ? Ko hakan na da alaqa d dawowarsu shine bansani b.

Haka dae mota ta daukesu se gidan na ARAB.......................

Toh madallah yanxu wasan ze soma....

Pls Ku sakani a addu'a wlh bani d lapia da qyar ma nayi typing din wannan yanxu haka kwae dan karku jini shiru ne


Mhiz Innocent ce......




*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

Page 6

~08105359153~
Number dina d take always welcoming naka a DM 😍 but pls message me amfani couz number nan an tanade ta ne especially sbd ku 🌚😻

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 😍

Seda sukaje suka gaesa d duka manyan gidan kapin kowa y koma 6angarensu

tunda suka koma be jiyo motsin baby b kwata kwata sannan be tambayi mamama b

sedae be ida tunanin nasa b yaji sallamar en matan gidannasu dukka sun shigo parlourn

" laaaaahhhh baby yaushe a gari ? ta fada cikin mamaki tana qarasawa wajensa

badan fadan da yake mata b babu abinda xe hanata rungumeshi

suma afrah d amrah qarasowa sukayi suna gaedashi

duk suka ja kujerun dinning din suka xauna

jansa sukeyi d hira amma shikam yau ba'a mood din yke b

hakan yasa amsarsa bata wuce " ehh koh a'ah "

d suka fahimci en miskilancin ne a kansa se suka tashi suka qyaleshi ya rage dagashi se Sanah

Seda ta dan nisa kamin tace

" baby seems lyk baka farin ciki d dawowar koh ? meya ke damunka ?

" A@h baby me kika gani ? Kwae dae yanayi ne ya dan chanja "

Duk da bata yadda d avinda y fada din b amma se tace " toh "

kapin ta tashi ta fara xuba masa abinci

Yace

" yahh ke baxaki ci b ?

" Ehh " kwae tace dan batason taganshi cikin irin wannan yanayin

Shi kadae yasan dalilinsa na rashin walwalar kuma ya barwa xuciyarsa sani

Seya tura kujerarsa baya alamar xe tashi

Tace

" baby ina xakaje ?

Yace

" xan tafi daki ne na qoshi tunda kema kin qoshi "

Turo baki tayi tace

" toh ba kaene b "

Yce

" nine me ?

" B kaene kake ta hade rae b "

Dariya t bashi yce

" toh shknn indae nine n dena kinji koh ?

Jinjina kae tayi kapin ta jaawo spoon suka faara cin abincin.


Fitowarta daga part dinnasu yayi daedae d lokacin d souban yke shirin shiga wajen arman

kallanta y tsaya yi kana y harde hannunsa a qirji yce

"wato baki yi farin ciki da gani na ba koh gabadaya kina ta baby koh ? ya fada yana murmushi

" Kae yah souban " ta fada tana dariya gami d rufe fuska

" Ehh mana sanah ae ni nasan gskia na fada "

" Aah pah yah souban baka chanka b daxun nan pah na gama tambayar baby kana ina "

" Tohm shknn daama naxo ne in kawo miki tsarabarki "

Murmushi tayi batace komae b har seda taji yace

" gashi "

Dagowa tayi ta kalleshi wata Leda ce me yalwar girma

Tace

" yah souban meye a ciki ?

" Ahh ki kar6a mana seki duba "

Kamar b xata kar6a b se kuma taga rashin dacewar hakan dan haka seta kar6a tana masa godia sannan ta koma 6angarennasu dan ajiyewa ta fito t wuce inda xataje .


A parlour ta tadda umma t gaesheta tana tambayarta amrah umman tce mata tana daki ita d afrah itama bata dade d shigowa b

tana dab d shiga taji amrah na ambatar sunan yah arman sedae bataji me tace b

d sauri ta qarasa shigewa dakin ta haye kan gadon tana fadin

" guys yaane naji ana fadar sunan baby me yayi ?

Afrah tce

" aah bbu abinda yayi kwae xance ne y biyo ta kansa "

Bata bawa xancen muhimmanci b dan haka kwae tce

" ohk ae shknn ku tashi muje mu gaeda baffa koh ?

Amrah tce

" aekuwa kmr kinsan yau bamu gaesa b "

Sanah tce

" nasani mana tunda gashi naxo na kiraki muje kinsan pah nidin...

" Ke din me..... Sarkin surutu d yabon kae " inji afrah tana katseta kapin ta gama maganar d xatayi

Dukkansu suka kwashe d dariya.


Sallah tayi kana tayi addu'a sosae sannan ta koma kan gadon ta tana jawo ledar d yah souban y bata

a hankali ta faara budewa kwali ne d dalleliyar waya qirar iPhone 13

cikin farinciki tce

" wowww !! kana ta kunnata ta faara saeta saetawa kasancewar tasan kan waya ko dan daukar ta mamama ko baby d take

tana shirin ajjiyewa dan bacci y faara daukarta taji shigowar kira

mamaki ne y kamata kenan har Sim y dora a wayar

seda wayar ta tsinke aka sake kira kapin ta daga tana karawa a kunne

daama tasan baze wuce shi b aekuwa shi dinne

Nan sukayi sabuwar gaesawa kapin tayi masa godia sosae har seda ya nuna 6acin ransa na baeson godiar sannan ta bari

suka cigaba d hira harta faara jin bacci

daedae lokacin mamama ta shigo dakin d mamaki take kallan sanah din

" Sanah !! Wayar waye a hannunki kota arman ce kika kar6a ?

d sauri ta yanke kiran sannan ta daawo d kanta kan mamama

" a'@h ba tasa bace daama so nake na fadamk toh kuma naga dare yayi shys banxo b "

mamama ckn rashin fahimta tce

" toh gani ae ynx koh fadamin "

Miqewa xaune tayi kapin tace

" daama..daama yah souban ne y bani a matsayin tsarabar daya taho min d ita daga Cyprus "

" Mugani " mamama ta fada tana kar6@r wayar

Jinjina kae tayi sannan tace

" toh meyasa ya baki ?

Turo baki tayi tce

" nima bansani b mamama nidae kwae y bani "

"Ohk d safe in Allah y kaemu ma qarasa maganar"

mamama ta fada tana ficewa daga dakin xuciyarta cike fal d tunani kala-kala.

Ajiyar xuciya Sanah t sauke tana mamakin irin kallan tuhumar d taga mamama na mata
Bata sake bi takan wayar b taja blanket se bacci.


*********Mamaki ne y kamata ganin yah souban ne a motar yana driving

bata kawo komae b ta bude murfin baya tana niyyar shiga

Afrah ta galla mata harara

" kinga malama in xaki shiga gaba ki shiga danni yah souban y hanani shiga "

Bata kawo komae b se bude motar d tayi ta shiga gaba tana murmushi tace

"Yah souban an yini lpia ?

" Lpia qlao qanwata y karatu ?

" Alhmdlh " ta fada tana maeda hankalinta gefen titi

Haka kwae ta tsinci kanta da jin kunyar yah souban din

Seda y juya y tabbatar afrah d amrah hankalinsu nakan books dinsu sannan y fara magana a tausashe

" naso ke kadae xan dakko daga school dinn sedae hakan be yiwu b amma akwae muhimmiyar maganar d nakeso nayi dake"

D sauri d sauri bugun xuciyarta y soma qaruwa wanda ta kasa gane dalilin hakan

sedae bata tanka masa b seda taja numfashi kapin tace

" Ohk toh Allah ys b laepi nayi b "

Murmushi yayi kana yce

" we will talk later "

" Ohk " kwae tace itama ta dauki littafinta tana dubawa

Suna sauka shikuma souban y juya dan dama akwae inda xeje y biya ne kwae y daukosu dan yau bega Sanah b

Wata dariya afrah d amrah suka sheqe d ita hadda tafa hannu

Kallansu kwae sanah tayi kapin tace

" ku kuma lpia ? Wannan dariya haka se kace.....

Bata kae ga qarasawa b afrah tace

" kinga malama ki barmu muyi abarmu san rammu ! Wae shin kin dauka bamu d wayo ne ?

Amrah ta kar6e

" bar er raenin wayo kin dauka bamu san soyayya kuke keda yah souban b

Wani wawan tsaki taja tana shigewa part dinsu ba tare dt tanka musu b .


Yau ma tana shirin kwanciya se taga wayarta tana ringing ita se ynx ma ta tuna d ita dan tama manta d ita kuma gashi ko maganar basuyi d mamama b

Dauka tayi kana ta kara a kunne

Daga can akayi sallama

Ta amsa tana gaedasshi dan dama tasan baxae wuce shi din bane

Sosae suka gaesa kapin yace

" sanah kina ina ne ?

Gyara xamanta tayi tace kwanciya xanyi

Yce

" kwanciya kuma sanah 8 pah "

Tace

" ehh inaso ne in tashi d wuri gobe in Allah y kaemu "

" Ohh...ohkk toh idan babu damuwa ki fito garden akwae wata magana d xamuyi "

" Yah souban b xamu iya barinta se gove b ko muyita a waya b ?

Yce

" nop qanwata ki fito plsss !

Bata son ta cigaba d masa musu hakan yasa tace

" tohm gani nan " t fada tana katse kiran

Jalbab dinta ta dauka ta sanya kasancewar kayan bacci ne a jikinta ta dauki wayar ta wuce garden

Kamar yadda ta tsammata kua yana xaune kan 1 daga cikin kujerun wajen hannunsa dauke d waya yana pressing

A hankali ta qarasa cikin nutsuwa wadda t xame mata jiki tunda ta mallaki hankalin kanta

Ganinta ya sanyashi fadada murmushinsa yana fadin

" yawwah qanwata ko kepah !

Itama murmushin ta maeda masa tana Jan kujera ta xauna

Gaba daya hankalinsa y tattara y bata itama d taga hakan seta tattara nata hankalin ta bashi

A tausashe y faara magana

" SANAH !!

taji y fada

Ta dago t kalleshi kapin ta maeda kanta qasa gabadaya ta kasa sukuni

Seda yaja dogon numfashi y faara mata magana

" Sanah wata alfarma nake nema a wajenki ban sani b koxan samu "

Bata iya bashi amsa b tadae gyada kanta alamar tana jinsa

Y cigaba d magana yana cewa

" sanah ba tun yau b b tun jiya b b shekaran jiya b nake qaunarki a raena na dade d dakon qaunarki a xuciya ta tun kina qanqanuwarki

dukda yanxun ma b girman kika yi b kuma na yanke shawarar fada miki abinda ke cikin xuciya ta tun kina secondary school saboda kar wani y rigani

nasan ynx xuciyarki danya ce ina da yaqinin xan iya tanqwarata d yaddar ubangiji

Sanah ina fatan xaki duba wannan alamari ki kawomin dauki plsss domin na fada mk xuciya ta ta dade tana azabtuwa d qaunarki

Wani irin yanayi take ji wanda t gaza tantance shi bata ji a halin yanxu xata iya wani dogon tunani balle harta fahimci abubuwa d dama

A hankali ta miqe tace

"yah souban seda safe "

Bata jira amsarsa b ta wuce d sauri d sauri .

Binta yayi d kallo cikin rashin sanin abinyi bata bashi damar kallan cikin qwayar idonta b ballanta y fahimci koda abu kadan ne dake tattare d ita b.

D sauri ta shiga cikin dakin shima kuma yaxo juyawa ze koma ciki sukayi karo d sauri taja d baya tana fadin

" baby !

Ko kallan inda take beyi b sema qarasa shigewa dakin d yayi ya xauna a kujera zuciyarsa na tafasa

Ganin haka y sanyata shirin komawa daki

" Keee !! Taji yace cikin wata hardaddiyar murya wadda badan ta masa farin sani b xata iya cewa ba taasa bace

Bata tsammaci d ita yake b amma se taji tana so taga dawa yake ne haka ?

Juyowa tayi ta duba parloun ita dae bata ga kowa b

A sukwane ta juya xata koma dakinta sedae cikin dakakkiyar murya ynx kuma yce

" B dake nake b ? Yae maganar ynx yana kallanta

Juyowa ta sakeyi tana mamakin anya kuwa wannan baby ne ko kua dae an musanya mata shine dan tunda take dashi be ta6a fadar sunanta b balle akaega y kira ta da keee...............

Babyn baby 😹💃

Gashi nan d yawa amma pah b lallae ne gobe inyi posting b saboda wani uzuri amma In Sha Allahu in dae na samu dama xan samu inyi ko bame yawa bane

Mhiz Innocent ce.........



*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

Page 7__ 8

~08105359153~
Number dina d take always welcoming naka a DM 😍 but pls message me amfani couz number nan an tanade ta ne especially sbd ku 🌚😻

Ina miqo gaesuwa a gareku Mhiz Innocent luv u owl 😻

Cikin rashin qwarin jiki ta qarasa wajensa ta xube qasan kujera sannan a hankali tace

" baby gani "

Kamar baxe tanka b dan yanda yake jin xuciyarsa kamar xe iya mata duka ne se kuma daga bisani yace

" me kika fita yi a waje d darennan ?

Dagowa tayi ta kalleshi sedae shi b ita yake kalla b

Kana tayi qasa d kanta tace

" baby ! yah souban ne y kirani ...dama.. Kuma inaso nazo na nunamaka wayarnan shine y kawomin wae tsaraba "

B shiri y dago yn kallan wayar

" Ehh lallae d gaske souban yke " y fada ckn xuciyarsa amma a fili se yce

" Meye hadinki d souban din daze baki waya kuma sannan ynx cikin dare ya kiraki ?

" Ni b komae " ta fada tana turo baki

" Ohk ohkk toh ke kadae y saewa wayar ko kuma y siyawa su afrah ? Y fada yana tsareta d ido wanda har seda taji kallan y mata tsauri tae saurin sadda kanta qasa
Batasan sanda tace " ehh " b

" Ohk.. "y fada yana miqewa

" ga wayar nan tashi kije amma karki sake na sake ganin kin fita d dare a irin wannan lokacin kin jiko ?

Gyada masa kae kwae tayi ta kar6i wayar tana wucewa yayin d shi kuma y bita d kallo kapin y dafe kansa yn sake neman waje y xauna.

Washegari er 6oyo ta dinga yi d souban
Sam bataso su hadu sedae shi ko a jikinsa dan hatta d makaranta shine y kaesu kuma y dakkosu suna dawowa afrah ta bude qofa suka fita itama tana shirin budewa y kulle qofar

Murmushi yayi yana gyara xamansa kapin a hankali yce

" Kyakykyawatah har ynx pah baki bani amsata b nayi haquri inata jiran ganin saqonki ko kiranki amma babu ko 1 "

" Kae yah souban !! Ta fada cikin shagwa6ar data xame mata jiki wanda ita sam bata

Please Login or Register in order to submit comment