Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dayan address din Wanda suke da tabbacin zasu sameshi acan din.

Wani gida ne wanda yake a wata sabuwar unguwa wadda babu mutane sosae a cikinta, sanda sukaje qofar gidan babu mukulli a jikinta hakan ya alamta musu cewa akwae mutum kenan a cikin gidan, dan haka wasu suka tsaya a waje, wasu kuma suka shiga cikin gidan saboda babu mae gadi a gidan.

Dae_dae qofar parlourn suka tsaya wadda take a kulle, daya daga cikinsu yae knocking din qofar yana komawa da baya hannunsa riqe da bindiga....................


Mhiz Innocent ce.............✍️


*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

Page 43

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e



.........Daga cikin dakin Khalid yaji knocking din wani banbarakwae, saboda yasan ba wanda yake shigo masa ballantana yace ko maqota ne, sannan a cikinsu black ba wanda ze tsaya knocking din nan sedae kawae su kirashi a waya, dan haka seya fara tunanin ko waye ?

A hankali ya taka zuwa bakin qofar sannan fuska a hade yace

" Waye ?

1 daga cikin en sandan yace yana gyara tsaewarsa

" saqo aka bamu mu kawo maka "

Seya sake 6ata fuska yace

" Inji wa ?

Dan sandan shima a fusace yace

" Black "

Jin ya ambaci sunan black yasa beyi wani tunani ba kae tsaye ya bude qofar, sedae kafin ya qarasa budewa har sun shigo cikin dakin

Wani ya riqeshi, wani kuma ya saetashi da bindiga yana fadin

" U'RE UNDER ARREST "

" Arrest ? Ya fada cikin mamaki yana kallan en sandan hannyensa a sama

" YES U'RE FIRED "

Daga haka suka tasa qeyarsa gaba se police station.


______A hankali ta ajjiye al'qur'anin dake hannunta, tayi addu'a sannan ta miqe, wayarta ta da tayi qara ta nufa ta dauka, tana mamakin ganin kiran daddyn a wannan tsohon daren saboda baya gida a asibiti ze kwana

Seta kawar da tunanin ta daga wayar tana karawa a kunnenta

" Hello ranka ya dade "

" Na tasheki a bacci koh ?

Se tayi murmushi me sauti ba tare da tace komae ba, yayinda daddy ya dora da fadin

" Wani babban albishir zan fada miki rahama "

Seta qarasa tashi gaba 1 kamin tace

" Ina jinka daddyn Arman, wane abin farin ciki ne ya samemu ?

" Arman ya farka !! Ya fada da farin ciki wanda muryarsa ma seda ta nuna hakan

Cikin tsananin farin ciki, wasu qwalla suka kwaranyo a fuskar mamaman, se kuma lokaci guda ta koma hamdala ga Allah buwaya gagara misali wanda shike yadda yaso a lokacin daya ga dama

Daddy yace

" Ni fah ba cewa nayi kimin kuka ba ranki uhmm "

Seta fara qoqarin hadiye kukan dan karya fito tace

" Yalla6ae bansan sanda hawayen suka fito bane, Allah mun gode maka, zamu samu ganinsa yanzu ?

Daddy yayi dariya

" Hala kin manta qarfe nawa ranki ya dade ?

Itama dariyar tayi sannan tace

" Allah ya kaemu gobe da safe "

" Ameen " ya fada yana kashe wayar.


_____Washe gari qarfe 7:30 mamama ta gama shiryawa kaana kae tsaye ta wuce dakin sanah

A zaune ta sameta kan stool din gaban mirror, kamar meyin kwalliya sedae ba abinda take, mamama ta qarasa tana kallanta sannan ta juyo suka hada ido, se take ganin kamar an chanja mata diyarta ta, se yanzu ta lura da wasu sauye_sauye dake tattare da ita misali ta sake wani fari sosae, ga kumatunta sundan taasa

" Lallae zaman gida ya kar6e ki sanah, Dan bata tunanin tunda suka tafi hutun strike bayan zuwansu los Angeles babu inda ta sake zuwa " mamama ta fada tana ajjiye abincin data shigo dashi a hannunta

" Ina kwana mamama ?

" Alhamdulillah, Yi maza kici abinci akwae wani albishir dazan miki "

Seta kalli abincin kawae tana yamutsa fuska tace

" Nikam mamama tea kawae zan sha "

Mamama ta 6ata rae

" Ayi mutum kullum sedae yasha tea babu wani abu daze riqe miki ciki, toh bari na koma da albishir dina "

Seta ja plate din kamar za taci, yauma dae taji qamshin Sam be mata ba amma danta farantawa mamaman setayi 1 spoon, sedae kafin ma takae ga hadiyewa taji 'ya'yan cikinta na juyawa, da hanzari ta ajjiye plate din ta fada toilet ta fara kwarara amai seda ta amayarda duk wani abu dayae saura a cikinta har ruwa sannan ta fito jikinta a sanyaye

Tunda ta shige bandakin Mamama ta bita da kallo, abubuwa da dama suka fara mata zagaye a qwaqwalwa, seta sake qura mata ido kamar me nazarin wani abu sannan tace

" Tun yaushe kika fara aman ?

" Ba tun yau ba, kuma cikina na murdamin sosae " Sanah ta fada tana yamutsa fuska

" Amma shine baki fadamin ba ?

" Kiyi haquri "

" Oh yah shirya maza muje asibitin dae da kike gudun zuwa "

Haka ta dauko hijab jalbab ta saka sannan suka fice, har a lokacin mamama na binta da kallo.

___Kae tsaye dakin likita suka wuce akayi sa'a daddy ya fita daga asibitin

Seda yayi mata tambayoyi sosae sannan akayi mata gwaji, ita dae sanah binsa kawae take ta kaasa fahimtar abinda yake nufi.

Sannan suka dawo da wata takadda a hannun likitan dan haka suka zauna sannan likitan ya miqawa mamama takaddar, kafin takae ga dubawa yace da murmushi kan fuskarsa

" Ina mijin nata ?

Se Mamama tayi murmushi tace

" Doctor Arman Alqaseem "

Se murmushin fuskartasa ya qaru yace

" Ahh Masha Allah, ina taya doctor murna Dan kuwa ya kusa zama uba "

Su duka kallansa suke da yaga haka yaga alamar suna buqatar qarin bayani seya kalli sanah yace

" Congratulations madam, kina da juna 2 na tsawon satittika "

Dae_dae lokacin wayarsa tayi qara, a dauka yana taking excuse sannan ya fice

Wasu qwallar farin ciki ne suka zubarwa mamama akan kuncinta

Haqiqa Allah shine abin godiya, wannan irin alkhaerae dake ta samunsu waye ya isa ya musu in ba Allah ba

Mamama bata hana hawayen zuba ba, ta barsu suka zuba tana dada godewa Allah.

6angaren baby sanah kuwa, tana gama jin abinda likitan yace takae hannunta saman shafaffen cikinta

" Wae anan akwae wata halitta a ciki ? Ita ! Wae itace yau take dauke da ciki, cikin ma na babynta, itama zata haehu kamar kowa ? Se take jin abin kamar a mafarki, ita baby sanah ita ke dauke da juna 2, Wane irin farinciki baby ze tsinci kansa a ciki in yaji wannan al'amari ?

Itama hawayen ne suka zubo mata a kuncinta, ta saka hannu tana gogewa sannan tace akan la66anta

" Allah ya baka lafiya baby "

........Sanda suka fito daga office din doctor, kae tsaye dakin da Arman yake suka wuce, suna dab da Shiga wayar mamama tayi qara seta dakata a wajen ta amsa wayar, ita kuma sanah ta qarasa shiga dakin

Cikin wani irin mamaki tayi turus tana kallansa

Yana kishingide akan gadon idanunsa na kallan qofa kamar dama ita yake jira

Wani sassanyan murmushi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskarsa kamin ya tashi daga kishingiden da yake yana miqa mata hannu

A hankali kamar wata me koyar tafiya ta faara takawa cikin dakin tana dada kallansa kamar wadda taga wani sabuwar halitta

Se kuma ta dakata hawayen da suka dade da taruwa cikin qwayar idanunta suka samu damar zubowa, se kawae ta saki kukan

A hankali cikin qarfin hali yace

" Nooo " ya fada yana girgiza kae sannan ya dora da

" Is this suppose to be a welcome ? Ya qarasa fada yana tsareta da idanunsa da suka dan shanye kadan saboda dadewar da sukayi a rufe, seya bude mata hannayensa, babu musu ta qarasa ta fada cikin jikinsa, shi kuma ya rufe ta da hannayensa yana sauke ajiyar zuciya lokaci guda yana shinshinar qamshin dake tashi daga gangar jikinta dan haqiqa yayi missing dinta badly

Sun kae wajen mintuna 2 a haka sannan ta tashi daga jikin nasa ya qura mata ido kana yace

" Wait ! Ya naga kin qara haske ga wani kumatu da kika ajje, meye sirrin ? Ya fada yana dage mata girarsa 1

Se tayi qasa dakae tana wasa da yatsun hannunta, se yanzu ma ita ta tuna da wani ciki da akace tana dauke dashi, se a lokacin ya lura da takaddar dake tsakanin yatsunta, haka kawae yaji yanaso yaga meye a jikinta, dan haka a hankali ya zare ta daga hannun nata yana budewa

Seya dago da sauri yana kallanta cikin wani irin farin ciki daya kaasa 6oyuwa akan fuskarsa yace

" Is dis so ? Abinda na gani gaskiya ne ?

Se taji yau so take ta faranta masa dan haka ta daga kanta tana kallanta gami da jijjiga kan nata

Ae beyi wata wata ba ya janyo ta jikinsa ya fara bata wasu hot kisses a duk inda bakinsa ya sauka yama manta a asibiti suke, dae_dae lokacin da umma suka kawo kae zasu shigo shine sanda ya jata cikin jikinsa, se kuwa sukayi sauri suka juya kafin ayi abin kunya a gabansu,

Se ya daga hannunsa yakae kan shafaffen cikinta yace

" Yanzu dana ne a cikin nan naki baby ? God of mercy ! Which of the blessing of my lord will I deny ? (Qur'an verse)

Seta turo baki tana dora hannunta kan hannun nasa ta dauke

Yace

" So kike ki hanani jin dumin babyna ?

Seta sake tura bakin tana jefa masa hararar wasa

Aekuwa beyi wata wata ba ya dora bakinsa akan nata ya bata dogon kiss me cike da kewa da nuna qauna ga Wanda ake aekawa da saqon

Koda ya gama qin sakinta yayi ya sake janta jikinsa kafin cikin sassanyar murya ya fara fadin

" Baby don Allah kice kina sona kema !

Ae ba zata sake wannan kuskuren na qin amsa masa ba dan haka tace

" Ina sonka baby sosae fah "

Dariya ce ta qwace masa najin qarshen zancenta

Shi kam besan sanda baby zata girma ba gashi har tana da juna biyu amma sakarci se wanda yayi gaba

Seya sake riqeta gam yana tuna maganar daddy na cewa senan da 1 week za'a sallameshi, shi kam ya zeyi da kewar babyntasa dake damunsa ?


_____Daddy ya qaraso cikin parlourn da sallama dauke a bakinsa ya kalli mamama yace

" Ku shirya muje police station "

Da sauri Mamama ta kalli daddyn jin kalaman bakinsa tace

" Police kuma ? Meya faru ?

" An gano wanda yayi causing accident din Arman, bama shi kadae ba har Wanda ya sace souban da kuma Wanda ya sace sanah kwanakin baya "

Ae babu shiri mamama ta miqe tace

" Bari na dauko hijab " ta tafi tana mamakin yadda a lokaci guda aka gano wadanda suka aekata mabanbanta laefuka a mabanbantan lokaci

Sanah na kwance kamar koda yaushe da alama daga baccin ta tashi, mamama tace

" Maza ki shirya zamuje unguwa "

Bata damu da inda zasuje din ba ta miqe ta fada toilet ta wanke fuska da brush sannan ta fito ta zura hijab suka fita compound din gidan

Ga mamakin ta se taga hadda umma da mama harma da aunty

Dukkansu ta gaeshesu sannan suka nufi mota.


__Kae tsaye police station din suka wuce, suna isa souban yana fitowa, shi yayi musu jagora zuwa cikin station din sannan suka wuce wani ke6antacceb daki da yafi kama da office

Manyan suka nemi waje suka zauna banda aunty data tsaya tana kallan dakin gami da ta6e baki, ita Sam ba taga fa'idar zuwanta wajen nan ba, meye ruwanta da abinda ya shafesu ? Damuwarsu ae tasu ce haka zalika damuwarta ta tace

Ita dae sanah tana tsaye bayan kujerar mamaman tana tunanin dalilin zuwan nasu police din

Kafin ta gama tunanin wani dan sanda ya shigo sannan Khalid,black da dayan abokin aekin nasu suka shigo, dae_dae lokacin data dago idanunta ta kalli qofar shigowa din idanunta suka sauka akansu

Ko shekara nawa akayi ba zata ta6a mantawa da wadannan fuskokin ba, seta tsaya tana kallansu sanda suka qarasa shigowa cikin dakin

Aunty data ga khalid en sanda na sarrafashi ae seta rude cike da fargaba tana kallansu tana buqatar qarin bayani

Khalid ya dago ya kallesu su duka sannan ya dauke kae

Ita dae aunty ta gama rudewar ganin tilon dan nata a wajen

Souban ne ya nemi waje ya zauna sannan a hankali ya fara magana

" Sanah kinsan wadan nan ?

Seta daga ido ta kallesu na tsawon sakanni sannan ta maedashi kan souban

Souban ya kallesu sannan ya maeda dubansa gareta yace

" Karki damu ki fada mana kin sansu ?

Kowa seya maeda hankalinsa kanta ana jiran amsar da zata bayar, a hankali cikin mutuwar jiki tace

" Ehh ! Sune suka saceni kwanakin baya "

Cikin rudewa aunty ta juyo tana fadi cikin kumfar baki

" Wa kenan ? Wadannan koh ? Amma dae banda Khalid, kada ki sake ki masa sharri ah toh...."

Kafin ta qarasa daddy ya katseta da fadin

" Ya isa haka !

Seta ja tsummar bakinta ta tsuke

Mama,umma, Mamama duka suka juya suna kallan su Khalid cike da mamaki, babu Wanda ma yafi basu mamaki kamar Khalid, yaron da daddy ya riqe tamkar dan daya haefa amma shine ze saka masa da haka

Kafin su gama dawowa daga wannan shock din suka sake jin Wanda yafi na dazu

" Shine ya saka a kashe Arman ! Kuma shine ya saka aka saceni ranar daurin aure "

Ae se gaba dayansu suka sanya salati da sallallami suna kallansu cike da tirr da halayensu

Daddy ya kalli Khalid sannan ya maeda dubansa ga aunty data kasa cewa komae se baza idanu da take

Lallae yau kam yayi dana sanin sanin Khalid a rayuwarsa, yayi nadamar riqesa da yayi kamar dan daya haefa, yayi tirrr da wannan sakayya da Khalid din ya masa

Ita kuwa Sanah kuka ne ya qwace mata tana tunanin irin wannan rashin adalci na Khalid, ashe bayan sace ta da yayi har qoqarin kashe babynta yayi bayan bata tona masa asiri ba, lallae kam khalid yayi asara..................


Mhiz Innocent..............✍️



*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

Page 44_45

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e


_______Haka en dakin suka cigaba da kallansu Khalid cike da qyamar halayensu, gashi kuma sun kaasa cewa komae alamar duk abinda aka fada gaskiya ne.

Aunty dae baki ya mutu tayi shiru tana satar kallan daddy, har suka gama abinda zasuyi suka tashi dan komawa gida.

Ko a mota da suna tafiya babu wanda ke cewa komae dan kuwa kowa akwae abinda yake saqawa a ransa har suka isa gida.

Aunty na shirin sauka daga motar daddy yace

" Ki sameni a daki na "

Daga haka yayi gaba

Qirjinta ya buga da wani irin qarfi kamin a hankali ta furta

" Na shiga 3 ni er nan " se kuma tabi bayan daddyn jikinta a matuqar sanyaye

Yana zaune a bedroom din nasa na 6angarenta, ta qarasa kamar wadda bata da laaka ta zauna a gefensa ba tare da tace komae ba, kae bata masan me zatace din ba

" Kina fa masaniya akan lamarin nan ? Daddy ya tambaye ta bayan wasu sakanni

Seta dago da sauri ta kalleshi

" Wlh wlh bani da masaniya akan lamarin nan, ka yadda dani bansan Khalid yana aekata wadan nan abubuwa ba "

" Idan baki da masaniya akae, ya akayi yake sanin abubuwan dake faruwa a cikin gidan nan, bayan yanzu ba'a nan yake da zama ba ?

Jinta takeyi kamar a court a court dinma a gaban alqali, gaba 1 a rude take da wadan nan tambayoyin da daddyn ke mata

Se kuma tace

" Kayi haquri daddy, wlh ni ba da wata manufa nake fada masa abubuwan dake faruwa a gidan nan ba, naaga shima dan gida ne shiyasa idan ya tambayeni abu nake fada masa, amma wlh ban ta6a tunanin hakan daga gareshi ba "

Wani murmushin yaqe daddy yayi kamin yace

" dan gida koh ? Ina yanzu ya nuna miki wane neshi ?

Seta maraeraece fuska tace

" Don Allah kayi haquri, kada laefin Khalid ya shafeni, kuma zanje in bawa kowa haquri amma don Allah karka hukuntani da laefin da bani na aekata ba " ta fada yau kam jikinta gaba 1 a sanyaye

Ajiyar zuciya daddy ya ajje kafin yace

" Ae ko Allah ma baya kamamu da laefin da bamu sani ba, ballantana kuma mu en Adam, Amma ki sani kema da laefinki saboda haka ki saurari hukunci na "

Daga haka ya miqe ya wuce toilet ita kuma ta bishi da kallo tana tuna irin abubuwan da akace Khalid ya aekata.

...........Kafin sati 1 ta cika gaba 1 Arman ya mato akan kewar babyn tasa saboda mamama ta hanata zuwa asibitin gaba 1 tana can tana gyare diyar tata, shi kam ji yake kamar ya gudu daga asibitin dankam jikinsa ya koma normal kamar be ta6a wani ciwo ba, amma daddy yace seya cika sati 1n nan sannan ze sallameshi.

6angaren sanah kuwa dama ga yanayin ciki ga kuma gyara da take samu, aekuwa ta sake yin fresh da ita ta qara kumari, farar fatar nan tata kuwa ta qara haske na musamman kamar ka ta6ata jini ya fito, ita kanta wani fayau take jinta tana ji ajikinta ta sauya, haka zalika itama tana matuqar kewar babyn ba kadan ba.


*****Ranar daya cika 1week, daddy da kansa ya daukoshi ya kawoshi gidan na Arab, Yauma duk wani dake cikin familyn na Arab ya samu damar zuwa gidan.

A hankali ya zuro qafafunsa daga cikin motar sannan ya qarasa fitowa yana kallan gidan cike da kewa kamar wanda yayi shekara be shigo ba, kae tsaye 6angaren mazan gidan ya nufa danya watsa ruwa kafin ya fito ya gaesa da tarin en uwan nasa da suke jiransa.

..Da sallama ya shigo parlourn idansa na kallan cikin dakin yana fatan suyi kyakyawan gani su fada kanta, aekuwa addu'ar tasa ta kar6u dan kuwa akanta idanunsa suka faara tozali

Tana sanye cikin doguwar rigar atamfa me rafa da wani mayafi data yafashi, ba qaramin kyau tayi ba, seya shagala da kallanta yadda yaga kamar an chanja masa ita a cikin sati 1n da yayi be ganta ba

" Qaraso mana Arman "

Muryar baba ce ta katseshi daga kallanta din da yake, se duk suka dago suna kallansa, da alama da basu ji shigowarsa ba

Se kuma yaji kunya ta kamashi dan haka ya shafa kwantacciyar sumar kansa yana qarasa shigewa cikin dakin ya nemi waje ya zauna, duk yabi en dakin ya gaeshesu, wadanda zasu gaesheshi suka gaesheshi ana tambayarsa ya jiki da fatan tsarewa ubangiji nan gaba

Dukka en parlourn ke amsawa da "Ameen " Idan wani yayi addu'a a cikinsu

Ba'a tashi daga parlourn ba seda akayi addu'a sosae kamin kowa ya koma 6angarensa.

Tare suka shiga dakin sanah din du duka 3n

Afrah ta zube akan gado tana fadin

" Washh " gami da riqe qugunta

" Allah kuwa na gaji " ta dora da fadin hakan

Amrah ta girgiza kae

" Allah kuwa ni bansan sanda kema kika lalace dasan jiki ba, kamar waccan matar "

Sanah dake kur6ar tea ta gallawa Amrah harara sannan tace

" Wace wae ?

Amrah tace

" A'ah nikam ban ambaci suna ba, amma in mutum ya tsargu dashi nake " ta fada tana dariya

Hararar sanah ta sake jefa mata ba tare da tace komae ba

Afrah ta janyo jakarta ta fiddo wata leda me dauke da mando a ciki tana yamutse fuska tace

" Kinga wata maqociya tace ta daka taga ina sonshi shine ta bani waeko zansha, ni kuma wlh yau sam bemin ba "

Sanah ta kalli ledar sannan ta miqa hannunta ka kar6a takae hancinta, qamshin mandon da yaji hadi ya daki hancinta seta lumshe ido tana fadin

" Woww, gskia da gaji zeyi dadi "

Amrah ta kalleta galala

" Aou Allah ? Yau kuma wani sabon gulma ne haka ? Keda baki sonshi yau kuma kina so ? Ke kuma afrah da kikeso yau bakiso ?

Afrah ta ta6e baki

" Wlh kuwa "

Dae_dae lokacin wayar amrah tayi qara, seta dauka da sauri tana kallansu su duka

" Ku bani 5mins , zan dawo yanzun "

Duk suka bita da kallo kafin suka saki murmushi a lokaci guda.

Wayarta ta janyo wadda tayi alamar shigowar saqo, ta duba ganin saqon daga number baby ne

" Ki fito mu tafi, tun daxu kun wani shige daki, don Allah ki taemakawa dan bawan Allahn nan ki fito mu tafi haka "

Seta share kawae ta ajjiye wayar suka cigaba da hira da Afrah.

Suna nan zaune umma ta shigo dakin da sallama ta kallesu su duka

" Ku tashi duk ku shirya ku tafi gidajenku, ga baffah can yana fada kada Wanda ya bari dare ya masa a cikin gidan nan "

Da " Toh " suka amsa mata su duka, Afrah ta kalli sanah tana dariya tace

" Ke fah yau kike amarya hajiya sanah matar yah arman "

Seta jefa mata harara ba tare da tace kae ba ta fada toilet, wanka tayi na tsawon mintuna 20 sannan ta shafe lungu da saqo na jikinta da wani sassanyan turare me qamshi sannan ta fito, sanda ta fito babu kowa a dakin, hakanne ya bata damar shiryawa a nutse ta saka wata riga da skirt na atamfa masu mugun kyau sannan ta sake feshe jikinta ta turare tana me kallan kanta a cikin mudubin sannan ta fito.

A compound din gidan ta sami yawancin en gidan, seta qarasa sukayi sallama da Afrah kamin ta shige motar yah imam sannan ta qarasa motar da taga baby a ciki qafarsa a waje suna magana da soubanz seda ta shiga ta zauna a gaban motar sannan sukayi sallama da souban ya rufe motar sannan ya tasheta suka bar gidan.

Seda suka hau kan titin sannan yace bayan ya kalleta ya maeda hankalinsa kan titi

" Wato yau Allah ne ya taemaki mutanen gidan nan, da basu bani matata ba da sunga halin 'ya'yan yanzu ,dan kuwa yau ba daukeki zanyi ba, dakin naki zan koma da zama gaba 1 "

Seta bude baki tana kallansa

" Kae baby !

Ya juyo ya daga mata gira sannan yace

" Yess, qaramin aeki na kenan wlh "


Ita dae bata sake cewa komae ba taja bakinta ta tsuke dan taaga alama yau en rashin kunya ne akan babyn nata.

.......Yau kam se yunwa takeji tun dazun, daga zarar ta danyi mintuna seta sake jin wani yunwar, dan haka suna isa gidan mayafi kawae ta cire ta tafi kitchen danta dora tea

Kafin ya shigo parlourn harta fada kitchen din ta dora shayin, sanda ya shigo seya nemi waje ya zauna akan kujerar, yana nan zaune tazo ta shige bedroom tayi fitsari sannan ta koma kitchen din,seya bita da kallo kamar wani sakarae tayi matuqar kyau ga kayan sun zauna das_das a jikinta, yana qoqarin miqewa ya bita kitchen din ta fito hannunta dauke da qaramin cup zata sake wuceshi, se yaga kamar ma tana sane take wani wucewa ta dawo dan haka bata Ankara ba taji ya janyota jikinsa yana kar6ar cup din hannunta yace

" Ina kuma zakije yanzun ?

" Yanzun nan ruwan kitchen ya dauke, shine fah zanje in wanke wannan cup din "

Seya dire cup din kafin ya dauke ta dukanta be direta ko ina ba se akan gado

Seta ta6e baki kamar zata yi kuka tace

" Ni fah yunwa nakeji "

" Rashi na akusa dake yasa kike zatan yunwa kikeji, amma nasan yanzu ma kin dena ji koh ?

Seta sake tura bakin gaba tana kauda kae gefe

Seya fara qoqarin hawowa kan gadon, da Sauri kamar Wanda taga abin tsoro tace

" Baby !! Na bar gas a kunne fa "

Seya sauke ajiyar zuciya yace

" Ohk bari na kashe " ya fada yana ficewa

Mintuna wajen 2 se gashi ya dawo ya hawo kan gadon sannan beyi wata wata ba ya janyota jikinsa cikin tsananin kewa ya dora kanta saman faffadan qirjinsa

Babu musu ta kwanta din tana sauke ajiyar zuciya

" Nayi kewarki baby ! Ya fada sounding very serious

A hankali tace

" Nima haka "

Seya kae hannunsa saman rigar ta ya dage wajen cikinta yace

" Bari naji ya babynmu yake "

" Aou " ya fada kamar ya tuna wani abu

" Ashe fah yanzu babyn namu ba'anan yake ba " ya fada yana yin qasa da hannunsa zuwa kan mararta yace

" Our little baby is here "

Wani irin yarrr taji a jikinta dan haka ta doke hannun nasa, seya dauke yana sakin er qara kadan

" Ouuuchhh, wae ni shikenan ba zanji dumin baby na ba ?

Seta turo baki kafin cike da shagwa6e tace

" Ae dae kaaji koh ?

" A'ah nikam ban ji ba " ya fada yana kwaekwayar maganarta

Seta sake ta6e baki kamar me shirin

Please Login or Register in order to submit comment