Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki barshi dan Ba irinta nakeso Ba tace to irin wanne kakeso yace zan fada miki Ba yanxu Ba. Dan tabe baki tayi sannan tace to Allah ya kiyaye sai kun dawo. Murmushin gefen baki yayi sannan ya gyada kai ya shigewarsa mota sannan suka wuce lukman na fadin wallahi sobon nan yayi yana hajiya dashansa yazeed yace dam inajin haushinka dan wulakanci shine bayan ka shanye naka ka dauki nawa ko?lukman yace afuwan mutumina santi ke dawainiya da ni,tsaki yazeed yaja yana mai kauda Kansa izu.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀

Abangaren ango Sulaiman Kam Sai murmushi take har yashiga dakin mahaifiyarsa cikin shirinsa na daurin aure nasiha tayi masa sannan tasa masa albarka domin kuwa Ba karamin so takeyiwa dan nata Ba cikin yara uku da Allah ya azurtata dashi wato;
Na farko Sulaiman mai shekaru 29, sai abdussalam mai shekaru 25,sai kuma fadeelah wacce take yar auta mai shekaru 17-18 kuma anfi saninta da deela ta zana jarabawarta this year.

Fita yayi ya nufi mota Inda abokansa ke jiransa domin tafiya wajen daurin aure.

Suna cikin tafiya sukayi realising ai birki bayaci nan hankali ya tashi salati suka somayi yayinda motar ke wujiga wujiga dasu akan titi kamin ta karasu da wani gini.

Allah sarki!cikin su Biyar da suka fito 2 ne suka rayu wato Muhammad da Ismail wadda akayi hospital dasu rai ahannun Allah amma ango da mutane biyu take suka cika. INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!
Allah taji kan musulmi.

Abangaren wurin daurin aure kam su ango shiru har 2:16pm.

Cikin gida kuwa mata sun cikashi dam Kamar lokacin bikin minal. Ana cikin shagali Amarya tasha kyau sai murmushi take black beauty akaji mai shela na magana Kamar haka: jama'a salamu alaikum, andaura auren malama zaliha usman da malam lukman shu'aibu akan sadaki naira dubu 80 bisa malam yazeed abdulmajeed umar amatsayin waliyin ango,kuma malam abubakar Yusuf amatsayin waliyin Amarya.

Cak kowa ya tsaya gidan yayi shiru bakajin Komai sai numfashi kamin kuma ya sake kacamewa da surutu masu tambayar Dama Ba Sulaiman zata aura bane ?nayi,Masu zagi da habaici Nayi,masu al'ajabi Nayi mai suma ma tayi nata wato Amarya.

Nan Yan daurin aure suka watse akayi gidansu Sulaiman domin jana'iza.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀

Abinda ya faru kuwa shine ana cikin jiran ango sai..........

Kubiyoni acikin babi na gaba domin jin abinda ya wakana

Shin kuna ganin lukman da zaliha sun dace ? Yaya zaman nasu zai kasance?

Don't forget to comment and share with your friends.

Thank you.

Miss untichlobanty💕

12 November,2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 42*

Ana cikin jiran ango sai hayani ake ana gaggaisawa da Yan uwa da abokan arziki. Da kaga fuskokin jama'an kasan Cewa cikin farin ciki suke.

Wani matashin saurayi ne ya kutsa mutanen daurin auren sannan ya iso daidai da'iran wakilai da manyan mutane.
Sallama ya musu aka amsa sannan ya tsuguna ya Sanar dasu hatsarin su Sulaiman din.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un suka dinga maimaitawa yazeed ne ya kalli  lukman idonsa Adan zare yayinda shima lukman din yazeed din yake kalla.

Lallai Sulaiman ya kasance Dan clique dinsu lokacin da suke secondary wato su uku abokaine saide shi Baya burin zama soja sabanin lukman da yazeed.

Idanun su ne yayi ja musamman yazeed daya tuno yadda minal din keson aminiyarta zaliha. Yaya zasuyi in sukaji wannan labari matsala bibbiyu ga mutuwar Sulaiman ga rashin daurin auren.

Ganin Kamar wajen ya kara hautsinewa yasa suka daina kallon-kallon da suke.

Baban zaliha ne hawan jininsa ya tashi domin yasan yadda diyartasa ke mutuwan son Sulaiman din tabbas yasan akwai kaddara kuma ya zama dole yin tawakkali amma yaya diyartasa zata dauki wannan lamari? Abu daya ne mafita shine in ta samu Wanda zai kula da ita ya kwantar mata da hankali, to amma taya hakan zai kasance ? Da Kamar wuya tunda Ba bawa wani dama zata yi Ba.

Wannan tunanin yasa hawan jininsa tashi lokaci daya.
Bakinsa na rawa yace Dan Allah Idan akwai Wanda yasan in ya aureta zai iya mantar da ita Sulaiman dinta dukda ko bazata mantashiba amma dai hankalinta zai kwanta ya taimaka ya aureta.

Hawaye ne ya silalo a idanunsa yayinda samari suka dagashi suka sakashi acikin mota akayi asubiti dashi.

Yazeed ne ya kalli lukman kallon aboki ka taimaka ka aureta girgiza kansa ya alamun bazai iya Ba sannan yace yazeed kasan Cewa ayush nakeso kuma how sure are you Cewa yarinyar zata aminta dani?

YAZEED yace na sani lukman amma ka Duba halin da mahaifin yarinyarnan ya Shiga Ina ga ita yarinyar kuma?
Shin kana ganin kaf na wajen akwai Wanda ya cancanci ya aureta? Kana ganin akwai Wanda zai iya kwantar mata da hankali? sannan ya Daga mata kafa ta dawo cikin nutsuwarta kamin ya bukaci hakkinsa?

Girgiza kai lukman din yayi ya budi baki zaiyi magana yazeed yayi saurin Cewa Idan maryam( kanwar lukman din) ne acikin wannan yanayin fa?

Ajiyan zuciya ya sauke yace yazeed ni yanzu Idan ma na aureta ina zan ajiyeta ? Yazeed yace karka damu da wannan ka amince kawai lukman yace amma yazeed kana ganin nayiwa ayush adalci kuwa?
Yazeed yace India har tanasonka zata fahimta kuma ai ita dinma zaka aureta sannan Idan itace awannan yanayi ai bazataso aki auranta Ba.

Lukman yace amma..... Yazeed yace Dan Allah. Ajiyan zuciya lukman din ya kuma saukewa sannan yace shikenan na yarda.

Murmushi yazeed yadan masa sannan ya dafa kafadarsa alamun bada kwarin guiwa sannan.

Tashi lukman yayi ya tsaya sannan yace ni zan aureta.
Kallonsa jami'a sukayi, babu bata lokaci aka aminta dashi musamman da akaga Cewa shidin abokin yazeed, kuma shi yazeed din ya kasance suriki na gari.
Kuma ai masu iya magana na Cewa inkanason kasan halin mutum to ka tambayi su Waye abokansa.

Hakan yasa babu bata lokaci aka daura aure sannan akayi sanarwar jana'izan Sulaiman.
Nan hankali Yan cikin gidan ya kuma tashi aiko nan wasu sukasa kuka yayinda wasu sukayi shewa Suna fadin "ahaiye cass, yo dama anga mai Hannu da shuni an like masa anaso ashiga Dan aci bagas toh ta Allah Ba taku Ba zaliha dai anzama Amaryar lukmanu 😀😀😀😀 auren shige aka mata" wata mata tace yo danma mutanen suna da mutunci naji ance anbada sadaki naira tamanin kome? Kinsan gidan ya kacame banji dakyau Ba.
Wata tace naira tamanin ko sanda rake yafi haka shewa suka kuma sawa dai dai lokacin waliyin zalihan malam ado (Wanda akayiwa yarsa fyade #chapter 2)yayi sallama.

Iya dake sharar kwalla tama kasa magana saboda halin da diyarta ta Shiga domin tunda ta farfado ta kafe waje daya da ido Ba tayiwa kowa magana Ba sannan bata yi kuka ba, ta amsa sallamar sannan ta nufi hanyar kofa tana mai saka hijabinta.

Gaisawa sukayi sannan ya mata ta'aziyya,addu'a sukayi ma Sulaiman din sannan ya miko mata 80k cas Kamar yadda aka bashi sannan ya Samar mata yadda akayi lukman ya auri zalihan.

Godiya tayi masa sannan ta basa 10k nan fa ya rufe ido yace Sam bazai karbi kudin ba. Haka iya ta hakura ta tafi tana kara masa godiya.

Koda ta shigo ciki daki ta nufa ta boye kudin tunda kannenta guda 3 ne kawai a dakin sai innar minal. Matsowa kusa da zaliha data sandake da minal daketa aikin kuka iyan tayi sannan ta lallashi minal nan hankalin minal din yadan kwanta tunda lukman din da aka aurawa zaliha lukman abokin yazeed ne ba wani ba kuma yanada mutunci.

Nanfa suka fara kokarin saka zaliha tayi kuka amma shiru sanda innan minal ta matso kusa ta yi mata nasiha sannan tace ta rike mijin ta da amana ta danne zuciya tunda Sulaiman din ya tafi Anan tayi breaking ta hawaye suka fara zuba tahau shure shure Kamar mai tabin kwakwalwa. Ihu take tana Cewa wallahi ba mutu ba ni Sulaiman dina bai mutu ba,Nasan bazai barni ba ku sakeni,ni kusake ni.

Kanwar iya mai Suna iya murja ce ta fita sannan tace wa jama'a sun gode da halarta da sukayi.

Wannan matarnan ce tace yo ai bansan baban zaliha munafiki,Mara mutunci bane sai yanzu, Ashe batada hankali shine zai aurawa Dan mutane.

Tasss!taji an dauketa da tafi.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀

Agidansu Sulaiman kuwa ana sanardasu wannan labari mahaifiyarsu ta yanki jiki ta fadi hospital akayi da ita Ashe coma ta Shiga.

Laila Kanwar Sulaiman rasa Inda zatasa ranta tayi. Kanin babansu Alhaji Ibrahim shi yasanar dasu wannan labari.
Lallashin laila da sauran family yake domin sunyi rashin da saiga goje(from chapter 10) ya shigo yana fito kallonsa kowa ya tsayayi

Shoki ya kwaso ya sauke sannan ya watsa zanku. Babansa ne ya daukesa da mari sannan yace kaide bansan me zanyi dakai ba da'ace a Asibiti aka haifeka da nace an canja Mani Kai, Allah ya Shirya amma ace mutum Dan uwansa ya rasu ko ajikinsa ?

Soka earpiece dinsa da yayi a kunne sannan ya kalli baban NASA yace kai tsohonnan ka kiyayen Idan ba haka ba kauna zaka raka wacan shegen Sulaiman din. Aikin banza duk kunbi kun cikawa mutane gida da kukan Munafurci.

Ke laila ki mana ko kallon Inda yake bata yi ba yace ba dake nake ba? Ta sharesa falla mata mari yayi yace ke Dan ub*nki Dan kinga anasonki shine zakiyi wa mutane hauka?

Kuka ta fashe dashi tace Allah ya isa wallahi Allah bazai barka ba. Wani mari ya dauketa dashi sannan ya take mata kafa yayi ball da ita yace kucaka kawai.

Fitonsa ya cigaba dayi har ya fice yana fadin Daga gadon asubiti uwar taku ma ta wuce.

Hey lovelies masu Neman update gashinan na muku.

See yah!

Miss untichlobanty💕

19 November, 2019.
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 43*

Bayan daurin auren lukman ya kira ayush ya fada nata yadda akayi sannan ya fada mata yadda sukayi da yazeed tace Ba Komai ta fahimceshi.

Dadi yaji sosai kamin sukayi sallama irin ta masoya.
Sannan suka wuce wurin jana'izan da za'ayita bayan la'asar shida sauran jama'a.

Bayan andawo ananne sukayiwa iya sallama koda ta fito gaisheta sukayi tare da ta'aziyya ta amsa musu sannan sukace batun amaryan ne shine mukace bara muji yadda kuka yanke shawara saboda Asan yadda za'ayi.

Iya tace ai babu wani damuwa rana ita kuzo ku dauki amaryar ku sukace to ba matsala amma my again MJ tadanyi koda mako biyu ne tadan watstsake Daga radadin mutuwar iya tace hakan ma yayi bayan mako biyun sai kuzo. Insha Allah Nasan zaliha batada matsala.

Godiya sukayi kamin suka Koma gidansu Sulaiman domin yiwa Yan uwansa ta'aziyya.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Ya abubakar ne sanye da shaddarsa brown ya shigo gidansu Sulaiman domin yakanje once in a while Dan haka sun saba da Yan gidan bai taradda kowa ba sai laila dake zaune tama kasa kuka saboda duniyar tayi mata zafi Dana can ga rashin uba,yanzu ga mutuwar Dan uwa,ga mahaifiyarta rai a hannun Allah, ga takurar da isma'il  (goje) yake mata Dan kafin ya fita ma sanda yayi mata zagin uwa da uba sannan ya fice tareda Cewa ko tanaso ko bataso sai ta aureshi. Ga ciwon boyeyyen soyaiyar ya abubakar dake nukurkusatta tun tana karama domin tun kafin su zaliha da Sulaiman su fara soyaiya sunsan juna saboda kamin baban zalihan ya rasu yayi aiki akarkashin baban Sulaiman din,Dan haka ya abubakar kan takoshi Duba da Cewa shidin bashoda da namiji.

Anan dai ya abubakar ya zama abokin Sulaiman kuma ya saba da laila sosai tun tana shekaru 9 shi kuma 18 Inda yake ce nata baby laila har kwalliya yake mata sannan duk sanda tayi ado to shi zai fara gani. Shiyasa duk yadda goje ke mata naci ko kallonshi baikai tayi ba balle tasoshi gashi mugun Dan daba ne kuma tsaf zai iya kisa.

Sallama ya abubakar din yayi jin ba'a amsa Ba yasa ya shigo da alamu tayi zurfi a duniyar tunani Dan haka yazo gabanta ta yazauna Hannu yasa ya tallafo fiskanta dukda ko yasan Cewa bai dace Ba saboda yanxu ta girma ba kamar da ba yanzu shekarunta 17 amma yanayin daya ganta zuciyarsa ta raurawa bazai iya ganinta cikin yanayinnan Ba.

Da ido kawai ta kuresa yace baby laila Kiyi hakuri Nasan Cewa munyi dashi Kiyi hakuri kinji Allah ya jikan Sulaiman rungumeshi tayi tsam kamin ta fashe da kuka shima dai daskarewa yayi na wani lokaci domin rabon da susami kusanci irin wannan tun tana 12 barsu dai sukan rike Hannu once in aw while saboda Sabo dasukayi dayin hakan.

Kasa hanata yayi illa ma Daga baya ya zuro hannunsa ya rugumeta tsam.

Daidai lokacin su yazeed suka shigo ciki suma tunda bawani zaman makoki za'ayi Ba Dan basason bidi'a Dan haka babu mata a gidan sai waje ne ma mutane basu gama watsewa Ba.

Parking motarsu sukayi awaje kamin suka shigo suka ja suka tsaye baki a bude sallamar tasu ta makale domin abinda idanunsu sukayi artabo dashi ya Abubakar ne rungume da laila tan kuka yana shafa kansa da Hannu daya.

Kallon juna sukayi kamin suka sakewa juna murmushi.
Gira daya yazeed ya dagawa lukman yayinda lukman din ya masa thumbs up

Sidam sadam suka Shiga suka zauna a akujera yayinda ya Abubakar yace shh Dan Allah ki dena kuka sai lokacin laila ta bude baki cikin sarkewar murya tace ya abibi (yadda take kiransa) nikam na Shiga uku rayuwa tai min zafi.
Shafa bayanta ya farayi yace karki damu Komai zai wuce Allah ne gatan bawansa kuma ina tare dake ki daina kuka kinji tace to  Ummi. Yace yes Ummi tana inane muje kiraksni inyi mata ta'aziya.

Kuka ta kara fashewa dashi tace Ummi ta fadi ankaita asubiti.

Kallon juna su yazeed sukayi alamun what ? Gaskiya rayuwar yarinyar yana garari.
Ya Abubakar kuwa Cewa yayi Kiyi shiru kinji zata zamu lafiya Insha Allah Kiyi hakuri ki daina kuka. Ko kinaso nima in miki kukane ya fadi hakan a muryar wasa. Girgiza kai tayi tana turo baki yasa hannunsa yadan ja kumatunta yace good girl murmushi tayi kadan yayinda yake goge mata hawaye.

Yazeed ne yayi gyaran murya yana Dan shafe sajensa, Adan tsorace suka saki juna laila tayi saurin cewa bari in dauko hijabi na mu tafi asibiti sannan ta gudu yayinda Abubakar ke Sosa kai yana Dan dariya yace a'ah su angwayene dakansu? Ai banjo shigowanku ba.

Gyada kai yazeed yake yana smirking irin ai dole yayinda lukman kuma ya fadi abinda ke zuciyar yazeed din.
Yace mutumina ai dole bazakaji shigowarmu ba irin wannan dumi da kake sha.

Chanja zancen ya Abubakar yayi ta hangar Cewa kun Shirya my tafi asibitinne? Sukace mukam a Shirye muke shiri ai saikai. Mikewa yayi yace ai nima na Shirya sannan ya nufi kofa yazeed yayi saurin rikosa tareda Cewa  in-law dawo Duba rigarka dakyau. Lukman yace wani ai sai ya dauka dambe kayi.

Akunyace yadan Jade rigarsa squeezing din ya ragu. Lukman my man maganar nanfa bata Kare ba gara ma kaji.

Daidai lokacin laila ta fito. Gidan biki suka fara biyawa domin su dauki minal aje dubiyan da ita.

Fitowa sukayi a motan akabar Abubakar da laila daidai lokacin minal ta fito yazeed na kallonta ya saki murmushi.
Dan dunguransa lukman yayi yace my man kaima na....

ya Abubakar na kallon duk abinda ke faruwa Dan haka shima murmushi yake amma ba bakin tsokana.

Cikin gida ko zaliha ido ta rufe tace wallahi sai ta bisu. Aka buga aka raya tace Sam haka aka hakura akayi yarjejeniya da ita Cewa in aka barta toh Idan ta dawo zataci abinci.

Laila ko tana hango minal Yan hanjin cikinta suka kada domin ko bazata manta sanda suka tana haduwa sau daya ba sanda ta biyo ya Abubakar itada Sulaiman, minal ta dawo Daga islamiya ta mata duka Wai Dan tasha ruwa da kofinta. Shekaru 6 dasuka wuce.

Gaishesu tayi kamin su masa Shiga zaliha Kamar an jefota da takalmi a hannu.

Minal ne  ta zaro ido Adan tsorace tace zaliha me kikeyi awake?
Lukman ne yakalleta sannan ya kalli yazeed domin a tabbatar masa.
Kai yazeed ya gyada masa alamun itace matar tasa take yaji zuciyarsa yayi masa nauyi domin kuwa bayada interest a bakar Mace shiyasa ma yakeson ayush abinda bai sani ba shine ayush bleaching tayi.

Kara analysing dinta yake yazeed shima ya dunguresa Kamar yadda yamai dazu sannan kasa kasa yace inyi magana ko inyi shiru? Still idon lukman na kan zaliha yace yanzu fito kayi?

Ya Abubakar yace Inlaw barshi ba yanzu zamuyi magana ba sai nan gaba.

Zaliha ko binsu kawai take da ido,yazeed yace kai dallah kamo matarka kasata a mota mu wuce. Ya danyi hesitating kamin ya taka izuwa wajenta ya kamo hannunta. Wani yar yaji amma ya basar zaliha kam da hankalinta baya wajen batamasan an riketa ba ta janye hannunsa taje ta shige motar kamin tace Wai me kuke jirane? Yadda tayi magana Zaka rantse uwar su ce babu Wanda ya mata magana illa shigewar da sukayi.

Lukman ke tuka motar yayinda yazeed ke gefensa sai a abaya kuma minal tana owner's corner sai zaliha a gefenta sai laila a tsakiya sai ya Abubakar a karshe.

What do u think of laila? Kuna sonta?

Next chapter is a boom💥.


Takuce karamarsu babbarsu

Miss untichlobanty💕

23 November, 2019.
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty@nt🌹

*CHAPTER 44*

Yazeed ne yasa Hannu ya gyara mirror yadda zai iya hango minal abinda bai sani Ba kuwa shine lukman ke Satan kallon zaliha ta mirror din Dan haka shima ya hararesa bayan Yan sakanni yasa Hannu shima ya
Juya dauke kai yazeed yayi kamin shima yasa Hannu ya kara juyawa.

Duk abinda ke faruwa ya Abubakar bai lura domin duk hankalinsa ya ta'allaka a yadda yaje zaune kusada laila Dan haka ya kafeta da ido yayinda take wasa da Yan yatsunta ganin yadda ya kafeta da ido bazata iya kallonsa ba.

Minal kuwa window kawai take kallo tana tunanin rayuwa yayinda zally tayi zugum da alamu ta tafi birnin China.

Yazeed da lukman a tare suka kai hannunsa zasu juya madubin kallon juna sukayi yazeed ya harareshi shikuma ya sakar masa murmushi.

Lukman ne ya kalli cikin mirror din Anan ya hango abinda ke wakana a duniyar su Abubakar.

Nuni yayiwa yazeed daidai lokacin suka iso leka mudubin yazeed yayi suka fashe da dariya.

Zabura yayi yace har Muna ido ne ? Lukman yace bamu ido Ba Muna hanya tukunnan suka kuma fashewa da dariya su minal Kam da basu gane meke faruwa ba suka tsaya kallonsu.

Fice wa sukayi suka Shiga asibitin. Wata nurse suka tambaya Inda aka ajiye Ummi din ta nuna musu tare da cewa su Shiga bibbiyu saboda ba'ason hayaniya nan dai suka fara Shiga.

A take laila ta fashe da kuka dakyar dai aka lallabata kamin min sukayi hanyar gida.

Mayar da zaliha gida sukayi,laila kuma aka kaita gidan Kanwar mamanta.
Ya Abubakar Kamar zai mayar da ita ciki. Sai bayan isha'i suka Koma gida, yazeed yayi sallama da lukman tare da Cewa akwai abinda zasu tattauna goben lukman yace ai baki daya kakeson yin magana Ba nima akwai maganar da zanyi dakai.

Shigowa ciki sukayi kamin yacewa minal tayi wanka ta Shirya ta sauko taci abinci Toh tace sannan ta sauko.

Gyada kai tayi sai ta tuna bayason gestures sai tace Toh sannan ta haura sama.

Wanka shima ya Shiga yayi sannan ya saka kayan baccinsa ya sauko yana Cewa yunwa nakeji amma hanji na ya daure maybe I should take some cappuccino.

Sofa ya samu ya zauna kamin ya janyo wayansa ya fara scrolling messages.
Minal ce ta sauko cikin wani farin rigan bacci na satin amma Ba shara shara bane saide yana like mata a jiki once in a while.

Kallonta yake tayi har ta ido gabanshi bai ankare ba tace gaji still kallonta yake.
Hannunta tasa ta tafa a gaban fuskansa tace nace maka gani.

Hannunta ya kamo ya janyota ta fado jikinsa kokarin tashi ta fara yi ya kankameta sannan ya Daga mata gira daya yace sannu da zuwa.
Kiciniya ta farayi tana Cewa ni Dan Allah ka sakeni Wai na maka kama da yar iska ne? Murmushi yayi yace Kayan jikinki ya amsa mini wannan,sannan tunda gaki kwance ajikina ai kinzama yar iskan ko turo baki tayi ta fashe da kuka ni wallahi ba yar iska bace yace time will tell. Itadai bata kulasa ba banda ci gaba da magana da tayi tace to ai kaika janyoni kuma ka wani rikeni sai kace zaka mayar ni ciki yace to wa ya sani ko cikin zan mayar dake.

Ganin babu sarki sai Allah yasa yasa ta kwanta luf ajikinsa babu abinda ke tashi a parlourn sai sautin numfashinsu kasa kasa minal taji yace "sai Anyi magana mutum yace shi ba Dan iska bane.
Tace me kace yace tunani nake. Harararsa tayi sannan ta kuma kwanciya can sai yace Wai meyasa bakison kirana da suna nane ? Saide kawai ki fadi magana,Ko kuma kicemin oga sir. Ko bakisan sunana bane ?

Girgiza kanta tayi a kirjinsa tace na sani mana ba kaima baka kirana da sunana ba saide ka dinga cemin insaram yace to mene sunan nawa?Dago da kanta tayi tana washe ha'kwara ita a dole kunya tace kawo kunnanka kaji.
Matso da kunnansa yayi a hankali kuma a kunyace tace oga ya..zeed.

Sanda tsikar jikinsa suka tashi domi. Tunda yake bai tabaji sunansa yayi masa dadi Kamar yadda yayi a bakinta ba.
Dan haka yace me ki kace ?ma'ke kafada tayi alamun bazata fada ba.
Puppy face yayi Yace please my insaram! Turo baki tayi tace ba gashinan ba kana sake cemin insaram yace to na daina Idan kika fadamin sunana to zan chanja miki suna.
Hannu tasa ta rufe fuskanta sannan tace oga yazeed
Yace to ki cire ogan tace yallabai zansa ?yace a ah tace to yaya kakeso Insa maka yace ah ah kawai ki kirani da suna na.

Tace a ah ba tarbiyya bace in kiraka da sunanka ko ba Komai ka girmeni.
Murmushi yayi yace beauty is secretly trying to be romantic da muryar tsokana. Turo baki tayi cikin shagwaba da wasa tace wallahi ya yazeed da gangan kake min turanci Dan kasan ban iya ba yace sorry Toh na daina karki damu kema zan koya mini turanci. kinaso ki Koma makaranta gyada kai tayi yace good zannayi miki lesson a gida inyaso sai Kiyi jamb da WAEC ko ? Tace eh yace beauty tace Waye beauty kuma yace Kece mana Sabon sunanki kenan. Ya miki? Ta gyada kai tare da Cewa eh yace kinsman ma'anarsa tace yana nufin kyau ba? Smiling yazeed yayi sannan shima ya gyada mata kai yadda take mai sannan yana kumatunta yace Ashe de beautyn tawa ba laifi.

Shiru wajen ya sake dauka kamin yazeed ya sake Cewa beauty ta dago ta kalleshi yace inason ki saki jikinki in Muna tare kinji? Ta gara kai yace kinaso ki zama kawata ? Ta sake gyada kai turo baki yayi yadda take mai inya mata abinda bataso yace bazakimin magana ba? Tace inaso in zama kawar taka. Tasar da ita yayi ta daina shima ya gyada zamansa Daga kishingida sannan ya miko mata Hannu yace friends? Shaking hannunsa tayi yace bakice friends dinba tace friends sai suka kyalkyale da dariya.
Daidai lokacin cikinsa yayi masa karar yunwa abinda bai tana faruwa dashiba ko a mission kuwa.
Pouting yayi yace beauty yunwa nakeji tace muje kaci abincinka to yace nope cappuccino zansha tace cup...po  mene? Yace cappuccino kin gaba sha ? Girgiza kai ya harareta tace a ah.

Yace okay muje kitchen in nuna miki yadda akeyi kai kawai ta gyada suka nufi kitchen dauko duka ingredients yayi sannan ya nuna mata yadda akeyi tace kai Ashe da sauke itama ta hada wani cup karba yayi ya murna yaji yayi dadi sosai zai iya rantsewa bai tabashan cappuccino me dadinshi ba.

Kurba itama tayi kamin ya riko Hannunta suka hau kan kitchen island suka zauna.
Yazeed nasha ahankali yayinda a kurba uku ta tada nata har tana kwarewa yazeed yace sannu bari in dauko miki ruwa tace barshi kawai bari in hada lamurje (lemonade) Insha saboda wannan cappuccino din maka na Daga min zuciya okay kawai yace

Lemon tsami ta dauko yace Kiyi ahankali kada ki yanke tace Toh. Lemonade ta hada tana kokarin saka sugar taji cikinta ya wani murda Dan dafe cikin tayi amma Ba tayi magana ba yazeed ya lura domin tunda ta fara hade hadenta yake binta da ido.

Ajiye cappuccino dinshi yayi yazo ya rikota yace lafiya tace babu kawai sai ta saki kara kadan yace ki fadamun menene?

Girgiza kai kawai tayi sannan ta dauko lemonade din tace sha kaji yayi dadi? Kurba yayi yace yayi sosai ma kuwa kin tabbata you are okay tace eh sha Rabi sai kaban in shanye inna na cemin duk sanda mutum taci abinci to Tasha ruwan lemon tsami saboda yana taimakawa wajen narkar da abincin.
Kara kurba yayi sai yaga minal tana hade fuskatana cije lebe.

Ajiye cup din yayi ya dafa kafadarta da hannu biyu amma kamin yayi magana minal ta saki kara

Please Login or Register in order to submit comment