Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan Samar daku abinda ya dace.
Ku Duba abinda nake iya rubutawa?I am just 14 years, 11 months,20 days kuma ina university sannan na haddace takaddun addini turum. what do u expect idan nakai 18?what of 20? ba cika baki nake ba amma kuma kunsani akarancin shekarun da nake dashi inada tunanin manya.

Abin kunyane ace yar cikinki ko kanwar bayanki ta Fiki zurfin tunani.

Wani abin da ke bani haushi shine 'Yan mata masu shekaruna yanxu Kansu rawa yake,yanzu ne suke ganin Suma sun girma baza'a barsu a bayaba,Suna ganin sunyi boobs Kansu daya da uban kowa,basuda burin daya wuce ayi shigan tsiraici ana yawo a gari ana karya ka'ida da iyakar Allah,ana kara yada zina acikin alumma,tun daga fitanta har dawowanta mala'iku na tsine mata,manzon Allah ya tsine mata,bayin Allah salihai na tsine mata, ai tundaga nan ya kamata ta fahimci ta Shiga ukku,ta gama yawo ta lalace wallahi Mu kiyayi haduwar mu da Allah abin kunya ne kaje gaban Allah kana mai saba masa ka wulakanta a duniya ka wulakanta alahira.

Su mazan da suke ganinku suce u look breathtaking,u look sexy,u look hot ke tun daganan ansami matsala hot fa akace ba cool ba kinga ko anfada miki Inda mala'iku zasuyi dake ne in baki canja hali ba. Ancemiki zasu aureki ne ?babu mai aurenki lalataki zasuyi suyi gaba,wallahi ku ji kunyan randa zaku tsaya gaban Allah ana miki shari'ah keda iyayenki. Mu rufawa kanmu asiri mu nemi ilimi muyi aurenmu cikin rufin asiri har Allah ya karbi rayukan mu.)

Lovelies kuyi hakuri yau duk Mun kare a lecture wallahi rainane ya baci da abinda ke faruwa,duk mutane sun kwashe kayansu daga gaban annabi,amma karku damu I will make it up to you😉 Ku tayani da addu'a inada test guda biyu tomorrow masu zafi ne aradu; chemistry and Arabic thanks for your love

Your one and only favorite yobe girl,karamarsu babbarsu


Miss untichlobanty💕

8 September,2019.
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 25*

An daura auren minal da yazeed akan sadaki naira dubu 50,Yan uwa da abokan arziki NATA taya murna makiya ma na hassada

Allah ka barmana makiyanmu kodan su zama dalilin da zamuyi nasara. Kai jama'a Imagine life without munafukai Allah barmana Ku Yan wuta😂

Mom ta aiko da kayan abinci da abubuwan da za'ayi walimah Dan babu wani event da za'ayi. Saboda abin yazo a kurarren lokaci ko mai wa'azi ba'a sami daman kira Ba.

Bayan la'asar akayi da mom Cewa za'a daukan minal around 5 pm inji ango(mom anya wannan magana kuwa zan yarda da ita?).

Hakan yasa aka fara shirya Amarya around 3:50 bayan Anyi sallar la'asar.

Liffaya mai kyau tasa wadda aka siyo mata awajen reemah's collection. Wani sarkan gold akasa mata Wanda yake na inna ne family necklace dinsu. Babbar ya ake bawa in za'a kaita dakin miji. Kuma ba'ayarda ka siyar Ba amma zaka iya upgrading.

Kyansa yananan Dan haka ba'amayi upgrading din Ba.

Dayawa daga cikin Yan makarantansu sunyi attending, ciki kuwa harda heedaya Muhammad da ma'ani yerima Wanda suke mutunci sosai.

Yan matan ne adakin minal yayinda aketa tsokananta itako sai cika take tana batsewa wai ita batason adinga zancen batsa a gefenta.

Hidaya ce tace Nide sake fuskannaki in gama kwalliyan yayinda ma'ani ke Cewa nikam yau sai na cika camera ta da hotuna, inajin ma inna sami dama zanje in karanta photography😉

Heedaya ne tace oh mude zamuzo muji ya aka Kare a Daren farko.

Harara minal ta ballo mata,aka fashe mata da dariya Ashe ta shaka,zaliha tace kai Ku rabu da ita bari ayi Daren farkon wannan Cuno bakin da take duk zata dena saide muga mutumiyar ka an zama miji dadi

Alamun zatayi kuka muryanta yayi tana Cewa wallahi zaliha karki bari na kamaki shegiya yar.....

Innace ta shigo tace inkika karasa sainaci ubanki.

Tunda ake hirar bansa baki Ba ina zaune a gefe ina typing a wattpad dina saboda kar ace na fiya rashin kunya sai alokacin na sako baki nace "assha!inna kin bata goma boyar bata gyaru ba in ita batayiba aike kinyi"

Dakuwa tayimin tace ingo naki yar jakan uban yarinya da baki cau cau Kamar babba kodan kinganki cikin Yan mata shiyasa kika falle ko?kinsa niqabi kamar da gaske ashe dai.......shegiya Da I damu Kamar na Yan chaina

Kafin ta karashe nayi Sauri nace wallahi Nide Ba yar China bace ina turo baki,aiko inna tayi kaina na fita a 360 har inacin karo da mutum Ashe ma sakina ce da habiba (from the nemesis of sakina)yi hakuri kawai nace kamin na 'buya a zaure ina haki sannan na sauke niqabi na,na saka gilashi na saboda naga alamun maza a waje.

Ciki su sakina suka Shiga aka gaggaisa kamin suka wuce domin mazajensu na jiransu.

Kanwar dad din yazeed aunty nafeesa da Umma habiba wadda take step paternal grandma ga  yazeed sai kuma aunty nina Kanwarka mom Wanda suka iso yau da safe sune sukazo daukan Amarya tare da motoci 3 kacal saboda basuso bidi'an tayi yawa

Aiko nan aka fara tashin hankali minal fa da taga da gaske tafiya za'ayi da ita kirjinta ya fara lugude duk dadin da takeji taji babu shi ya tafi kawai sai ta fara hawaye wiwi Ba magana nanfa  wattpad fans dinta sukayi CAA anata bata hakuri amma ina kukan karuwa yake tunba sanda sukayi sallama dasu inna Ba dasu baba da ya abubakar.

Inna da baba hawaye suke hankali kwance yayinda idanun yaya abubakar suka ciko da kwalla deeje Kam an jika gaban riga ma da hawaye da majina sai alokacin na lura da kwalliyar da tayi kominta yayi matching da kayanta hatta Jan baki da eye-shadow, da brows din duka blue ne. Abin dai sai kun gani. Nikam share kwallan da zai zubo min Nayi domin tausayi. Rabuwansu was heart touching haka aka kwashemu mu 10 aka kaimu gidan amarya.

Tundaga kofa akayi mana maraba,kai Mun sami tarba me kyau dakin zakiyya aka nuna mana muka kai minal Dan bada amana mu Yan mata 8 da tsofi 2.

Ba yabo ba fallasa ta karbemu. Amma ni dai hankalina bai kwanta ba kuma naga alamun hakan a fiskan wasu daga cikin mu amma dai sai Nayi shiru. Kar aji mutuwan sarki a bakina.

nuna mana dakin minal akayi Wanda yake part din baki ne na sama kuma acikin sashin zakiyya yake ada amma an daba kuma an gyarashi kai ya hadu. Allah dai ya kyauta ya Kare Daga sharrin makiya

Aikuwa hidaya ta cika alkawari Dan photo kam gida yashashi har minal dinma sanda akayi mata pic amma sanda ta sake ado tukunnan.

Haka dai har dare yayi munata shewa da tadi kamin aunty Nina ta shigo tace mana motocin tafiya najiran mu haka Muka tattari kafufun muka tafi minal Kam kukanta ta bude sabon shafi Dan ta manta da Cewa ita daya zamu bari(saima ankai mutum kabari zai San kadaici. Allah dai yasa muyi dariya a kaburburanmu.).

Hmm ai batamasan gidan wa aka kawota Ba saboda kanta na cikin gyale har muka kaita daki kuma ai batasan yazeed Nada mata Ba kuma bata tbna Shiga side din zakiyya Ba Dan haka bata gano ba.
Lokacin ko da akayi musu maraba kuka take ga hayaniya Dan haka bata gane muryan mom ba.

Aunty nafeesa da mom ne suka shigo,mom tayi Sauri taje wajen minal yayinda ta dago chin dinta tana mai Cewa " 'yata me ya sameki?"
Kuka minal ta kara fashewa dashi ta rungume mom Dan ta dauka mom tayi attending bikin ne

Tace "mom Ashe an gayyaceki?mom Dan Allah karki tafi ki barni kamar yadda su zaliha da untichlobanty da ma'ani da nasreen da hidaya da..."

Ya isa bazan tafi in barki ba mom ta fada hakan tana me daurewan kai ?kode batasan wa ta aura ba?kai maybe de tsoro takeji saboda first encounter dinta da yazeed wasn't good.

Shafa bayanta mom  tayi tana bata soothing words har tayi shiru tana shessheka (sobs).

Kinyi sallahn Isha'i ? mom ta tambayeta tace a ah. Mom tace to tashi kije Kiyi kinji
Shiga toilet din tayi taga irin na wannan dakin da aka kaita ne sansadowa tayi kamar barauniya Wai Dan kar fanfo din yaji motsinta ya bachi da gangan har zatakai hannu ta bude saide ta fasa

Fanfon dake jikin toilet irin na tsarkinnan tace ta matsa tayi alwalanta Dan akwai irinsa a gidan aunty fauxy so ta iya aiki dashi har wani smiling take irin itama ta Waye dinnan.

After tayi alwalan bata mayar da dankwalinta ba ta fito Dan ta manta da cewa ma su mom sunanan

Smiling suka mata ta miyar musu kafin mom tayi introducing mata aunty nafeesa sannan ta tada sallah

Aunty nafeesa Kam yaba Kyan  minal take tunba gashinba shi yafi dauke mata ido.

After ta idar mom ta zaunar da ita ta mata wa'azi ya tsumata sosai.

Abinda ta fada last ne yasa minal shock.

"Daughter Dan Allah ki rikemin Dana dakyau kuma iyayi miki wani Abu ki sanar dani"

"Kina nufin oga sir?"minal ta tambaya hankali tashe.

"Kwarai shi"mom ta bata amsa. Atake minal ta.........

Yey! Alhamdulillah💃🎊🎉🎆 is my birthday your girl is finally 15years old 💃🏼💃🏼💃🏼

love you all😘

Karamarsu babbarsu ce

Miss untichlobanty💕

*18TH SEPTEMBER,2019.*
[1/11, 1:53 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆
🌹by @mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 26*

INTRODUCING NEW CHARACTERS SAFWAN AND SAHIR

Sahir and safwan 'ya'yan yayar zakiyya ce Wanda ta rasu two years ago ana kiransu sahboy and safboy tashin turaine su. An dawo dasu wajen zakiyya ne last two month acewar mamanta Wai idan yazeed bashida matsala to su zauna awajenta tunda babansu irin sugar daddy dinnanne dama dan kudi yayar ta auresa kuma sanda sukayi sharadi inta sake ta haihu tofa yaran nata ne shi babu ruwanshi Dan baya bukatan yara.

To ta haifi sahir (6 years old) and safwan (4 years old).
Yaran are very sweet kuma sun saba da zakiyya Kamar mamansu adan zamansu tare tunda dama Ba aiki take zuwa yanxu Ba kuma already sun saba kawai shakuwa suka karayi.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Atake minal ta sauke wani ajiyar zuciya aranta tace na Shiga ukku na lalace, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un sunana  death.

Da badan tana cikin matsala Ba da tayi smiling domin ta fadi kalmar death daidai

Bude baki tayi zatayi magana kawai sai taji ta kasa Cewa Komai sai hawaye mom kuwa bata kawo Komai a ranta Ba ta dauka minal tana kukan yadda dare daya Allah ya sauya rayuwanta ne(eh tabbas sauyin Shiga tashin hankali ba).

Mom tace bari inje intaho da angon naki Dan Nasan yanxu haka yana hanya idanma be karaso Ba kenan.

🌹

Abangaren yazeed kuwa tun kayanshi na daurin aure ne ajikinshi dama shadda ne fari kal.

Yana shigowa gidan side din matarsa(I think yanxu matansa zance) ya nufa dama haka yakeyi tunda suka Shirya da zakiyya inya dawo sai yaje ya taho da ita dakinsa wataran idan a sama yazo ma to Anan za'a yada zango. Watarana kuma ya samota already a dakinsa.

Yana shigowa ya kalli right dinsa wani iri yaji aransa Wai yanxu matarsa ne a part dinnan left dinshi yayi ya tura kofan dakin zakiyya gaji abude.......

🌹zakiyya tayi wa Kanta alkawari bazata biyewa yarinyar (Kamar yadda taji su mom sunce)da za'a kawo mata Ba tunda ma mijin nata bayaso ai yazo da sauki.

Sanda taji guda an shigo da Amarya wani ras ras ras ras gabanta yakeyi amma sai ta matse koda aka shigo da Amarya wajenta wani daci taji ya tsaya mata,tanaso tayi musu wulakanci amma su untichlobanty su hidaya su zasmeen su walia sun mata kwarjini.

Haka suka gaisa sama kamin suka fita itade idonta akan minal tanaso taga ma Wai wacece wannan yarinyar.

Koda suka fita wani Abu taji ya tsaya mata a wuya batasan sanda ta fashe da kuka ba kukanta take hankali tashe Wai yau ita zakiyya akayi wa kishiya da wani ido zata kalli mutane danma ita bamai kawaye bace saboda jiji dakanta.
Sahir da safwan kuwa na dakinsu.

Turo kofar dakinta taji Anyi tace Waye?yazeed ne ya shigo ta rungumeshi tare da fashewa da kuka. Sanda tayi shiru yace ina boys dina? Tace Suna dakinsu peck ya mata a kumatu yace taje ta kwanta sannan ya juya zai fita zuwa tayi ta tsaya a gabansa ta rike hannunsa "da fatan Ba dakin ta zaka kwana Ba?" Zame hannunsa yayi a hankali yace no dakina zanje na gaji sosai.

kansa ke masa ciwo Kamar zai fita kallansa tayi suspiciously tace are you sure ? Ya gyada mata kai tace ko inzo mu kwanane kasan ina tsoran rananda da zaka kwana da yarinyannan zan iya mutuwa saboda kishi

Ransa ne yabaci yace haba zakkya why are you acting like this kinsan fa aurennan mom ce ta.....

Fuck you yazeed! You are so fucking annoying i hate you just leave. Ta fada tare  fashewa da kuka Dan gani take yazeed a dakin minal zai kwana

Baice mata kala Ba Dan yanxu shi yana rasa meke damunsa Dan haka yabar mata dakin.

Sai alokacin taji wani irin saita daura aniyan zata bashi hakuri da safe.

Dakinsa ya Shiga zai fara rage kayan jikinsa saiga mom Tisa kyayarsa tayi har dakin minal dukda ko baiso hakan Ba amma shima he is curious yasan wa aka aura mass Dan yaga mom na rawan kafa akan amaryar.

Salamu alaikum suka fadi in unison yayinda mom da yazeed suka shigo dakin minal. Aunty nafeesa na zaune agefenta daga alamu nasiha take mata.

Tanajin sallamarsu ta sauke Kanta kasa kirjinta na lugude duk ta tsure cikinta ya kada.

Wa'azi sosai aunty nafeesa tayi musu harda kuka wajen bashi amana kamin ta kara yiwa minal nasiha sannan ta fita domin take ta kwanta Dan jirgin bakwai zatabi ta koma gida yayinda su mom zasubi na karfe ukun dare ita da Yan uwanta domi zuwa gida Kamar yadda tace(amma intention dinta shine ta basu Fili su wala tunda yayi sabuwar Amarya kuma bata bada ranan dawowa Ba.

Mom ne ta dafa minal tace yata ki dago da kanki kinga ni Kamar mahaifiya make awajen ki Dan haka babu wani batun kunya kinji?tsoro ne yadada balbale minal zuciyanta na dukan Tara tara yayinda captain yazeed Dada sa hankali ya zuba idanu Dan yaga face din new bride dinsa.

Shahada minal tayi ta dago fiskanta aiko stake captain yazeed ya sankare

Out of all Yan mata mom ta rasa Wanda zata aura masa sai barauniya?maybe Ba barauniya bace har leken asiri ce ko kuma ............. WAIT!so now he get it wato ta biyoshi ne last time dan taga yaya yake Dan tasamu yanda zata shigo life dinsa Gaskiya tayi making a huge mistake hmm he will deal with her

Kallon mom yayi ya mata godiya sannan yace Allah ya basu zaman lafiya tayi hakuri da abinda yayi mata. Kamar da gaske

Minal har hankalinta ya fara kwanciya tadauka an wuce shafin batasan ko bude littafin ba'ayiba.

Mom taji dadi sosai sannan ta sanar da minal Cewa yau ne tafiyanta sannan ta fita ta basu wajen domin komawa side din ta Dan agajiye take sosai.

Tana fita yazeed ma ya fito bayan yayi wa minal wani dangerous kallo yace Allah gaji kanki. Run daganan tasan ta Shiga ukku.

motansa yahau ya Shiga gari kawai ya samu wani ice cream palace ya zaun plan kawai yake nema yanda zaici ub*n minal Ba tare da mom ta gane ba. Lokacin rufewa ne yayi masu wurin suka masa magana kamin ya fita.

Daidai ya tsaida motansa a cikin gida idea ta fado masa murmushi yayi tareda danna kai cikin gidan.

Minal kam sanda ya fita aranta tace kai wannan oga sir din Anyi masifaffe ni inyazo ma wulakanci zan kafta mai. Wani zuciyan yace dubeki saikace zaki iya tuno kallon daya mata kamin ya fita tayi atake ta tsure ta kidime yanxu ya zatayi gashi mom zata tafi ta barta waiyo Allah.

Kwanciya tayi abinta sanye da kayan jikinta gyalenta kawai ta cire kamin tayi baje baje atsakiyar gado tana yaba laushin katifar. Allah sarki har tayi missing din tsohuwar gadonta da yar karama da katifarta.

Around 1 yazeed din ya dawo so direct ya shigo dakin minal domin aiwatar da aniyarsa kallonta ya tsayayi yana yaba kyanta.
Aranshi yace mutum ga kyau amma Ba hali money monger

Concentrate yazeed Karka bari kyanta ya rude ka idan Ba haka Ba bazaka iya cin ub*nta Ba 

Alokacin minal ta Dade da Shiga duniyar mafarki Wai tana baccinnan yazeed yazo ya caka mata wuka sannan ya binne gawanta a bayan gidan.

Wani wawan juyi minal tayi acikin baccin dama ita A ne wajen style din bacci ta iyasu kala kala dankwalinta ne ya zame gashinta ya bude dama ta cire ribbon din sanda zatayi alwala

Tsaki yayi aransa yace mata halinsu daya ka Duba iyayenta basuda karfi sosai amma sanda tasa wig mai tsada. Ko ina ta sami kudin? Wata zuciyarsa ce tace masa ka manta barauniya ce ko yar 419?

Bubbuga gadon yayi fiskansa babu alamun wasa domin ya daura aniya kuma sai yayi.......

Toh fa ko menene aniyan yazeed? Fans me kuke gani yazeed zaiyi?don't forget to vote and comment your ra'ayoyi.

Miss untichlobanty💕
23rd September, 2019.
[1/11, 1:54 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹@mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 27*

Juyi minal tayi tace inna bacci,Wai har asuban yayi ne?

Haushi abin yabawa yazeed hakan yasa ya wantsalar da pillow din da take kai,aiki babu shiri ta mike ganin shine yasa taji wani faduwar gaba yazo mata

Tunda take arayuwarta bata tana jin faduwar gaba irin wannan Ba kuma bata taba jin tsoran wani Kamar yadda tsoron yazeed ya shigeta a yanxu Ba.

Wani irin kwarjini yayi Wanda tayi nadamar kallon idanunsa domin kuwa ko lokacin da suka fara haduwa bata kallesa da kyau Ba

Wani kirma jikinta ya fara ta fara karkarwa Kamar mejin sanyi.

A hankali muryatta Kamar zatayi kuka tace sannu da zuwa.
Wani kallo yazeed ya mata Wanda yasa hanjin cinkinta kadawa kamin yace uban Waye yabaki izinin kwanciya akan gadonnan? Wato anzo ansami banza ko shine kikayi yi relaxing kina bacci ?

Da izinin wa kikayi bacci? Tayi shiru...
Bakida kunnene ko yaya?muryanta na rawa idanunta ya cicciko da hawaye tace kayi hakuri yace will get down zaki sauko ko saina taka ruwan cikinki?

Babu bata lokaci ta diro saga kan gadon yayinda tayi kneel down run kafin a bata umarni yazeed ko Ba tare da ya kalli inda take  Ba ya taka ahankali cikin takunsa na kasaita da isa amma cikin kuzari Wanda zai nuna maka Cewa shidin wani jarumi ne kuma namijin duniya

Har izuwa bakin gadon ya isa sannan ya zauna ya cire hularsa me mugun kyau da tsada sannan ya ajiyeta a gefe

Dago kansa yayi yanaso ya karewa minal kallo amma hakan ya gagara sabida kirjinsa dake bugamasa da Sauri da Sauri amma dai baikai na minal Ba sai ya dauki hakan amatsayin baccin rai  

Dan haka sai ya jingina Kansas da allon gadon yana mai lumshe idanu Kamar yadda yayi scan baya sanda ya fara haduwa da ita a gidansa.

Minal ko gabadaya jikinta yayi sanyi,ta sadakar Dan ita a ganinta Allah ne yake ramawa mutane irin tsiyar data musu sanda take gida.
Tayi tsuru tsuru da ido Kamar Mara Gaskiya,gabadaya jikinta ya jike da gumi ga wani fitsari ga zazzabi ya sauko mata tsabar rudewa.
Dukkanin shikashikan tashin hankali ta cikashi a halin domin ko hawaye sun Dade da fara safa da marwa a kumatunta bakinta ko yayi mata nawi ko hakurin ma takasa badawa sai tsilla ido take tana kallon kafafunsa Wanda Duke dake da Zara zaran yatsu da kuma gashi kwance luf luf akai.

Sanda suka dauki kusan minti goma a haka kamin yazeed yace sannuki da zuwa cikin masifa da bala'i hade da tashin hankali.

Minal Kam ta kasa dabbaka Komai Dan ita ko a film bata tana ganin irin yanayin  da tashiga Ba ganin take ko yaushe ma ziciyarta zai iya bugawa ta mutu zaboda yadda yake bugawa har cikin dodan kunnenta takeji

Abubuwa dayawa ke yawo azuciyar yazeed Wanda yana fahimtar wasu,Wasu kuma baya fahimtar su

Ba tare da buds idanunsa Ba yace kinsan ni soja ne jarumi kuma naga alamun kinason zama dani,kuma kinsan jarumi sai jaruma,Dan haka kamin infara considering dinki a matsayin matata sai kin cika wa dannan sharudan

Shiru ne ya biyo baya kamin yazeed yace ;
Na farko daga yau ke zakinayin dukkanin shara,moping,dusting, wanke-wanke,inkika saba wadannan to zan hada mini da wankin mota da safe sukuma masu aikin zasuyi girki da sauransu da yamma kuma zakiyi sharan bangarena sannan zaki dafa abinci kuma ni Vance ki kawomin jagwalgwalonki Ba.

Na biyu karki sake koda wasa ki na ganki a Inda nake domin ganin fuskarki kadai nakanji Kamar zanyi amai

Na uku abinda nace kiyi agidannan su kadai zakiyi idan kina neman izinin yin wani abu to ki rubuta a paper ki ajiyemin ka kibi duk umarnin da matata zata baki saboda marabarki da yar aiki shine darajar mom

Na hudu karki sake mahaifiyata tasan da wannan maganar idan Ba haka Ba to kin kusa ki bakunci barzahu

Hope kin gane ta gyada masa kai yace bakida bakine
Tace na gane

Yace good idan kinbi wannan dokokinn to zaki zauna lafiya amma idan kika saba to kema kinsan sauran.

Sannan ban yarda ki kwanta akan gadonnan Ba harsai naga how serious are

Itade taji bazata kwanta a gadon Ba sauran kuwa to kunde San sauran .

A hankali ta bude bakinta tace oga sir Dan Allah idan na cika sharudanka zaka sakeni yayi shiru kamin yace hakan ya ta allaka da yanayin biyayyarki may be in sakeki
Yana gama fadan haka ya tashi ya fice wani nauyayyan ajiyar zuciya ta sauke tare da sakin numfashinta Wanda bata masan ta rikeshi Ba sannan ta goge hawayenta sannan tadau bargo ta Komai kan kujera ta kwanta tare da rufe kafafunta

Yazeed kuwa yana komawa dakinshi yayi wanka tare da brush sannan ya fito dressing room dinshi ya Shiga ya dauko pyjama dinshi blue tare da Rigan ya saka sannan ya haye gadonsa ya kwanta yana mai lissafi yanda rayuwa ta kasance masa

Hakadai bashi yayi bacci Ba sai wuraren asuba koda ya tashin sallahn asuba Kansa yayi masa mugun nauyi hakadai ya daddafa yayi sallh yayi azkar yau ko karatun Qur'ani bai samu yayi Ba ya koma bacci. Dama Ba kullum yakeyi saboda yanayin life.

Minal ko tunda tayi asuba taje kitchen ta nemi kayan aiki aiko batasha wahala Ba ta samu ta kama aikintakarfe 8 cif saiga su atine da su larai sun shigo sukaga babu kayan aikinsu parlour suka leko jin motsin mutum aciki aiko  da gudu gudu Sauri Sauri suka karaso

Atine tace Allah sarki yar uwa yaushe Rabin da mu ganki ziyara kika kawo manane ko wajen hajiya kikazo kika bage da aiki saide kash hajiya ma jiya da daddare tabar kasan itada danginta kinsan fa mai gidan ya karo aure
Duka atinen ta fada a numfashi daya zuwa biyu Asabe ta kara da ya karo wulakanci Ba larai tace baza'aji mutuwar sarki abakina Ba

Minal ko murmushi take tana binsu da idanu Dan batada abin Cewa
Aikin sukayi kokarin karba minal tace ah ah sukace to shikenan suyi tare kamin ta yarda amma dukda haka tana tsoran kar yazeed ya ganosu 

Su kuwa sai hira suke mata yarda tambayarta ko zata kwana musu Dan sunaso suyi kawance da ita tace musu ai Ba kwana Ba kwanaki ma zanyi ta fadi haka tana bawa kwanakin karfi, aiko sunji dadi Dan su nasu gane me take nufi ba

kafin karfe 10 sun gama Komai saura part din yazeed Wanda dama tunda basu ke gyarawa Ba lukman ne kuma yazeed yayi masa message Cewa Ba sai yazo Ba.

Su atine sai janta suke da hira tun tana nokewa har ta saki jikinta sumo abin ya musu dadi, binta tace ni wallahi na kosa naga amaryar Allah dai yasa Ba irin madam zakiyya bace

Atine tace yo imma batada mutunci ai ita ya shafa minal de tayi tsit tana jinsu
Minal tace to ita bari taje sama tayi wanka larai tace Wai ko kema bikin kikazo ne naji kina Cewa bari kije sama kiyi wanka ? Rasa amsar da zata nasu tayi sai atine tace kinada kayan sawa?
Binta tace ki wani tambaya dole da kayanta zata zo mana

Minal tacewa atine Dan Allah kinga rabu dasu zo Kiyi mini wani taimako

Sukace to sai kun dawo kamin su minal suka wuce dakinta ta cire hijabinta sannan ta kalli atine

Atine ko zare idanu takeyi domin in batayi kuskure Ba nanne dakin da aka kawo Amarya

Minal tace kinga kwantar da hankalinki nice amaryar ni zoki nuna mini Inda zan sami kayan sawa
Atine ta zaro ido tace Kece ME?

Minal tace kinga shiyasa ma ban dadi muku Ba saboda ban Shirya yin bayaniba zoni ki nuna Mani

Nuna mata dakin dressing atine tayi da yadda zata canja combination din

Please Login or Register in order to submit comment