Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bacci dakyau kwana biyu saboda jiran update shi yasa na fara rubutu karfe goman dare.๐Ÿ˜œ

Waiting for your comments and don't forget to share

Karamarsu babbarau ce

Miss untichlobanty๐Ÿ’•

9th December, 2019
[1/11, 2:29 AM] Mzz_Untichlobanty๐Ÿ’ž: ๐Ÿ†๐Ÿ†KURUCIYAR MINAL๐Ÿ†๐Ÿ†

๐ŸŒนby miss untichlobanty๐ŸŒน

*CHAPTER 53*

Juyowa yayi domin ya kalli minal dake gefensa wacce ringing din wayarsa ta biyu ta tasa aiko suka hada ido tayi Saurin rufewa Kamar mai Baccin gaske.
Yazeed yayi murmushi cikin rashin kuzari saboda har yanzu bata gama sauka Ba tunda Ba saba sha yayi ba yace na kamaki kazame kallo na kikeyi.

Blushing ta fara bada San ranta Ba kumatunta yayi jaa Kamar tumatiri kamin ta tashi ta zauna tana mai rife ido da Hannu.

Tace ina kwana ? yace lafiya amma Daga yau Ba ina kwana nakeson kice min Ba. Tace Toh me zance? Motsowa yayi ya janyota jikinshi sannan cikin kunnenta yace good morning zaki ce min sai kimin sumba.

Girgiza kai tayi tace ni kunya nakeji. Yana smirking Yace humm! Amma Idan zan iya tunawa dakyau jiya rigarki ma kika cire a gabana kuma da kiketa rife ido a haka muka kwana.

Sai alokacin minal ta tuno aiko ta zabura ta fara kokarin Jan bargo yace rabu da bargo babu laifinsa.
Turo baki tayi tace ai Dan bana hayyaci nane.

Serious face yazeed yasa ya hade gira alamun tunani sannan yace zamu tattauna akan wannan ma amma yanzu karfe nawa ne? Minal ta zaro ido tace bamuyi sallah ba!!

Aiko ta tashi da gudu ta nufi toilet.
Wankan tsarki tayi dukda babu abunda sukayi amma dai a Kore kokonto.
Fitowa tayi yace ko dauko kayanki muyi sallah Anan sannan ymshima ya Shiga.
Dauko doguwan Riga irin na shan iska tayi sannan tasaka ta zauna a bakin gado tana jiranshi yayinda ta Lula tunanin me yasa aka basu Kayan maye?kuma Waye ? Sannan taga yaya aka zuba musu?

Tana cikin tunanin na batasan sanda yazeed ya fito Ba saiji tayi ya hura mata iska a fuska yace kazame me kike tunani? Tace zan fada ma muyi sallah tukunna.

Kabbara sukayi sannan yazeed ya fara rero karatu da zakin murya ga taushi ga tausasa zuciyan mai sauraro. Minal mamaki ya cikata sosai jin zakin murya yazeed,jikinta yayi sanyi sosai saboda yadda karatun ya tsuma ta.

Bayan sun idar sunyi addu'a sun shafa yazeed ya janyota yace my kazame ya akayi ne?turo baki tayi tace nifa banason kazamennan Dan dariya yayi yace zanyi tunani.

Tace ya yazeed wa kake ganin ya saka mana abin maye a abinci ko kunun mu?Sosa goshinsa yayi yana kara samawa minal mazauni a cinyarsa yace nuna abinda naketa nazari kenan. Minal tace ni gani nake so ake a hada tarzoma tsakanin mu kuma ko Waye meyin abunnan yasan abinda ke wakana a gidannan saboda kasan da bakacin abincina......

Pecking goshinta yayi yace kuskuren da na tabayi kuma kenan Ba. Murmushi tayi sannan taci gaba da Cewa Toh kaga kenan ni aka zubawa tunda ansan kai bakaci ko kasha Ba. Kenan Idan na bugu sai ka dauka ni yar shayshaye ce kuma Allah ne ya tons asiri na kaga kenan Daga lokacin kome akace ma akaina zaka yarda.

Zama ya gyara yana kara zurfafa tunanin akan abinda take fadan domin tana making sense. Taci gaba da Cewa kuma kenan zaka iya sakina at any moment saboda wannan.

Toshe mata baki yayi yace shhh bazan taba sakinki Ba! Inaso kiyimin alkawari ko me aka fada miki akaina bazaki rabu dani Ba kuma zaki tun tubeni kuma bazaki rabu dani Ba Komai zafi Komai wahala.

Tace Nayi yace nima na miki alkawari bazan tana zarginki Ba kuma bazan rabu dake Ba.
Rungumeta yayi ajikinsa sannan yace ya Allah ka karemu Daga Sharrin dukkan mai sharri.

Minal ne ta mike yace ina zaki?tace ina zuwa. Parlour taje aiko kalli wayar a Inda yazeed ya buya jiya. Murmushi tayi tunowa da irin haukar da suka dinga yi.

Wayan ta dauka ta dannan on button aiko yana kan contacts Inda yazeed yayi saving numbern shi Ba fita Ba.

Kokarin karanta sunane da yayi saving yayi tunda ta iya karatun Hausa na turancin ma Ba laifi zata rubuta zata karanta saide abinda ba'a rasa Ba matsala shine batasan ma'anan abinda take karantawa ko rubutawa Ba.

Karantawa tayi taga an rubuta yazzy baby tace Waye kuma yaz.....

Inazuwa!yazzy - yazeed , yazeed -yazzy.
Okayyy wato shiyasa jiya ya buya a gefen kujera saboda zaiyi saving number sa a wayana? Dariya tayi tace hmmm bari inje in hadu da yazzy baby a daki. Dariya ta kara fashewa dashi sannan ta nufi dakin koda taje kofa ya rufu gaba daya tunda batasan pin dinba sannan thumb print na yazeed ne zai bude sai tayi knocking yace ki shigo mana tace ai ya rufu bansan lambobin Ba. Tashi yayi ya bude meta sannan yayi wasu danne dannan shi yayce tasa thumb dinta. Sakawa tayi ya danna okay sannan yace ta kara sa'a for confirmation sawa tayi sannan ya danna green button din ma'ana OK.

A kunnan ta ya rada mata Daga yau in kinzo a kulle kawai ki daura wannan yatsan naki sai ki danna green dinnan ki kara daurawa kinji? Ta gyara kai sannan itama ta janyo kunnansa tace me yasa kake rada min kunnan ta ya kamo yace saboda kar muje akwai masu kallonmu ko jin mu. Tace ta yaya?

Yace ta na'urar camera zo muje muga abinda ya faru a kitchen a na'urar camera na.
Binsa tayi suka zauna tace yazzy baby dauko ka nunamin Toh. Kallonta yayi cikin abin tausayi yace Dan Allah ina kika sani wannan sunane ki rufamin asiri kar lukman yaji. Murmushi tayi ta hasko masa wayanta. Date kai yayi yace Allah ya tsinewa abin shaye shaye.

Dawowa tayi ta gefensa ta zauna tare da sakala hannunsa a NASA tace yazzy baby nunamin Toh.
Saman study table dinshi ya nuna mata yace dauko laptop dina a saman can. Da fatan kinsan laptop tace na sani mana. Yace ki daiyi a hankali karki fasamin Dan akwai important abubuwa akai. Daukowa tayi ta kawo masa sannan ya kuna direct na kitchen ya Shiga suka fara kalla tun daga safiyar jiya. Yaga sanda su tala sukayi su shara,can minal ta dafa abincin safe tayi su kunun ayanta har izuwa sanda ta daura abincin rana.

Bayan ta fita can sai ga wani ya Shiga yana leke don tabbatar da Cewa Ba kowa.
Direct fridge ya nufa ya bude sannan ya balli wasu capsules guda 5 ya zuba acikin wani Abu dake fridge din Wanda babu shakka kunun ayan ne tunda basu sha Komai Daga fridge dinba banda kunun ayan.

Sansadawa mutumin yayi ya fita ta back door Kamar yadda ya shigo.
Caption din gate yazeed ya Duba amma baiga fitan mutumin Ba ya Duba na suka balbabalin gidan amma babu mutumin tunda ya fita Daga kitchen yayi kwana shikenan.

YAZEED yace shit! Toh ta ina ya shigo ko ya fita. Minal tace to kodai acikin gidannan yake ? YAZEED yace ko a cikin sojojina yake da zanga ya nufi side dinsu domin canja kaya amma wannan kwanan baya yayi shikenan.

Dukda haka yazeed baiyi kasa a guiwa Ba ya kira lukman......
Ringing uku ya dauka yace ya akayine? Yazeed yace kasa sojojinnan su Duba ko ina a gidannan a tabbatar babu kowa sannan biyu su dawo ta arean back door dina Suna monitoring.

Yanda zasu iya ganin mai Shiga da fita amma bazasu iya ganin na ciki ba. Lukman yace okay sir! Amma me ya faru an sake yin wani attempt ne? Yazeed yace Idan na fito zamu tattauna. Sannan ya kashe wayarsa, minal tace kai amma nature shege ne yanzu fa Mun kalli suka balbalin gidannan Muna dakinnan. Murmushi yazeed yayi yace hakane wannan shi ake kira CCTV. Jinjina kai minal tayi sannan tace yazzy baby amma dai babu acikin gidannan ko? Kallonta cikin idonta yayi sannan ya girgiza kai yace akwai a ko'ina amma handa dakuna.

Aranshi ko yace aike har ban dakinki akwai shi.
Minal Kam ajiyan zuciya ta sauke jin yace babu a dakuna Dan tsoranta kar ace yaga duk hakan da takeyi.

Kwantar da kanta tayi tace kadan sosamin kaina Dan Allah. Core human dake kanta yayi aiko a take gashin ya zubo babu ko ribbon.

Yace nifa banason kina Karin gashi ba dole kanji yayi kaikayi ba. Dago da kanta tayi ta kalleshi sannan tace Allah ya kiyaye in saka izgan doki ko gashin roba a kaina, wannan gashi nane.

Tabawa yazeed yayi yaji laushi ga kamshin sun flower shampoo dake tashi, lumshe ido yayi sannan yace kina kudin gashinki ne wannan? Ta gyada kai hancinshi yakai yana shinshinan gashin sannan yayi pecking yace kamshi. Murmushi tayi tace kanaso ne?yace sosai ma ki daina saka hula kinji ki barmin ina gani. Gyada kai tayi sannan ta kara kwanciya ya fara Sosa mata kan a hankali sai lullumshe ido takeyi.
Can yazeed yace ina rigannan na jiya tace yanakasan wannan yace tashi ki cire wannan din.
Mikewa tayi ta core dukda tanajin kunya amma tadan fara sabawa da nuna jikinta wa yazeed.

In ka ganta sai kace yar India irin model dinnan sanda yazeed ya kare mata kallo iya son ransa itako sai kokarin gyara Rican rake Dan ko guiwa bai karasa mata ba tashi ana ganin Komai.

Kwanciya ta sake yi yaci gaba da Sosa mata kai yana mai shara bayanta a hankali a haka har bacci ya dauketa bata sani ba.
Daukanta yazeed yayi yakaita kan gado sannan shima ya hau ya kwanta a gefenta sannan ya janyota ya rufe musu kafarsu da bargo bayan ya cire jallabiyarsa.

Shidai a Gaskiya akwai wani special Abu da yakeji a zuciyarsa game da minal kuma Idan dai abinda yakeyi wa zakiyya shine so to ba son minal ya keyi ba wani Abu ne na daban shima....


*Irin wannan murmushi haka ai sai bakinki yayi ciwo. Ko duk jin dadin chaptern nanne?*

Anyway don't forget to comment and tell a friend to tell a friend

1 to tell 10 sukuma 10 to tell others.
Idan kika karanta ke daya kinyi son kai๐Ÿ˜œ

Miss untichlobanty๐Ÿ’•

10 December, 2019
[1/11, 2:29 AM] Mzz_Untichlobanty๐Ÿ’ž: *๐Ÿ†๐Ÿ†KURUCIYAR MINAL๐Ÿ†๐Ÿ†*

*๐ŸŒนby miss untichlobanty๐ŸŒน*

*Wattpad:* mzz_untichlobanty

*Instagram:* miss_untichlobanty

*CHAPTER 54*

Koda ya Abubakar ya dawo daukan Laila yayi direct sai gidan aunty fauziyya sannan yace kar ta Fadawa kowa abinda ya faru Dan bayaso su fuskanci matsala Idan yace zai aureta sannan abin zai iya shafan yaransu sannan next week zai kaita asibiti domin a tabbatar babu shigan ciki.

Itakam kuka take tayi Dan abin ya fara daura mata kai Dan har yanzu bata dena bleeding ba ga irin azaba da takeji amma dai tayi deciding zata Fadawa aunty fauziyyan matsalanta tunda ita daya ne tasan abinda ya faru da ita.

Koda suka iso sallama ya Abubakar yayi. Aunty fauziyya ta fito da Sauri domin dams su take jira ta riko Laila tana mata sannu da kai kawai take amsawa. Fiki ta Shiga da ita yayinda akabar ya Abubakar a parlour.

Direct toilet ta nufa da ita sannan tace ta fara core kayanta tana zuwa bata ta sallami ya Abubakar.
Parlour ta sameshi sannan ta tambayeshi Karin bayani tunda bayani kadan ya mata a waya.
Nan ya fada mata duk abinda ya sani da abinda Laila ta fada masa. Lokacin da ya gama bayani mamaki ya cikata tana kasa magana can ta sauke ajiyan zuviya tace Allah ya rabamu da azzaluman Yan uwa da dangi ya Abubakar yace Ameen. Aunty ni zan wuce tace tsaya kasha ruwa mana yace a ah babu Komai ai ina godiya amma aunty ki tabbatar babu Wanda yaji Dan Allah tace karma damu Insha Allah babu Wanda zai sani yace na gode Allah ya saka Idan kuna bukatan wani Abu sai Ku kirani tace Toh ba matsala sannan ta rakashi koda ta dawo ta sani Laila yanda ta barta babu wani kayanta da tacire.

Aunty fauziyya ta riko kafadan ta tace hakuri zakiyi acikin gama ya gama Koma gode Allah kin zamu mai sonki tsakani da Allah Idan ba haka ba ai Anan zaki fuskanci tashin hankali.
Acikin sheshekan kuka tace ni babu abinda ke damuna illa yadda jinin yaji ya tsaya kuma marata azaba takemin.
Shiru aunty fauziyya tayi tana nazari kamin can ta girgiza kai domin kawar da tunanin da take Dan ba Abu mai yuwuwa bane.

Ruwan zafi ta hada mata sannan tace ta Shiga ciki kuma ta tsaya akanta Dan tasan Yan Mayan yanzu ba sason ruwan zafi(Cesar tsofi)
Fire kayanta tayi amma tabar vest sannan ta Shiga ga mamakin aunty fauziyya batayi ihu ko nuna wani alamu na Cewa taji ciwo ba Kamar yadda take zubda mini. Don't ita a tunanin ta idai har taji ciwo da yake zubda wannan jinin to ko tafiya bazata iyayi ba. Kai akwai alamar tambaya Anan wurin.

Matsowa tayi kusa da ita ta zauna sannan tace Laila tana mai riko hannunta dago da rinnanun idanunta tayi ta kalleta. Auntyn taci gaba da Cewa zan miki wani tambaya bawai Dan inaso in banbaro miki tsohon ciwo ba sai Dan in gano wani abu. Gyada kai tayi alamun tanaji.

Tace kin tabbata Cewa wani abu ya Shiga tsakaninku?gyada kai tayi har lokacin hawaye basu bar sintiri a fuskanta ba tace Kiyi min bayanin yadda Komai ya faru Dan kinsan Abubakar bazai iya min bayani a faiyace ba.

Nan Laila ta fada mata yadda goje ya mata karya har ya kaita dakinsa da irin kokuwar da sukayi har izuwa sanda ta suma sannan ko da ta farfado ga yananyin data tsinci kanta.
Jinjina kai aunty fauziyya tayi sannan tace wato kina nufin bakiji sanda ya Shiga jikinki ba har kika suma kawai dai kinji maranki ya murda? Ta gyada kai.

Sake kallonta aunty fauziyya tayi tace yaushe ki kayi al'adar ki ?shiru tayi kamin tace kwana 28 da suka wuce.
Aunty fauziyya tace bayan kwana bawa yake kewayowa? Tace hakan kewayo min bayan kwana 27 ko 29 tace kina nufin jiya ya kamata ki fara. Ta Daga kai tana mai nazari domin itama ta fara hada possibilities da aunty fauziyya ke hadawa.
Tace Idan kina al'ada kina ciwon Mara ne?ta girgiza kai alamun a ah
Aunty fauziyya tace tambaya na karshe shin kinajin wani zafi hakannan Kamar ciwo Daga ciki banda na maranki? Ta sake girgiza kai.

Murmushi aunty fauziyya tayi tace ina tunanin bayi raping dinki ba. Kallon neman Karin bayani Laila ta bita dashi tace ban tabbatar ba amma alamun sun nuna bai miki Komai ba ni a ganina kafin ya miki wani abu al'adarki tazo Dan haka dole ya rabu dake.

Atake Laila ta fito Daga ruwan daya Koma jaa Dan basu ma lura da launin ruwan yana canjawa ba.
Kusa da aunty fauziyya tazo tace toh amma me yasa Mara ta kemin ciwo? Ta fadi hakan tana mai daina zubda kwallah Dan hope ya samu.

Aunty fauziyya tace abu biyu nake tunani ko stress yakawo miki cramps din ko kuma sauyin jikinki Dan wasu Idan suka fara baya musu ciwo da sunyi shekara 18 sai ya fara cramps wasu kuma da ciwo zasu fara da sunkai 18 sai ya dena wasu kuma kwata kwata baya musu ciwo wasu kuma da ciwon zasu fara kuma ko sunkai 18 baya dainawa sai sunyi aure yake ragewa.

Jinjina kai Laila tayi tace aiko 18th birthday na is few months Away. Aunty fauziyya tace bari na kira wata kawata likita ce ta dubaki.
Dakinta yaje ta dauko wayanta sannan ta kira kawarta ta mata bayani a takaice. Nan likitan tazo ta dubata tace babu wani abu daya sameta mensuration ne kawai. Dadi kashe laila. Painkillers ta bata sannan tace ta rage damuwa Dan shi yayi causing zuban jinin dayawa. Murmushi tayi tace Insha Allah Dan farin acikin daya lullubeta a wannan lokacin tama manta da Cewa an mata rasuwa kuma mahaifiyarta na asibiti.
Kiran ya Abubakar aunty fauziyya tayi tace yazo da gaggawa akwai abinda zata fada mishi shiko duk ya tsure karfa aje cikine da ita dukda ko da wuya a gane cikin kwana daya inba Anyi test ba.

๐ŸŒน........

Itakam auntyn Laila da ta dawo bata ganta ba bata wani damu ba ta dauka gida ta tafi. Itace ma me Dan kokarin da take zuwa tana Dan zama akan ummin nasu Dan wasu Daga cikin dangi Cewa sukema Wai bata lokacin ne su zauna akanta Dan babu abinda zai hanata mutuwa. Sai kace su suke kashewa.

Koda taga har safiya shiru babu Laila babu alamarta kawai sai ta kirawo nurse tace ta kula da ummin zataje gida tayi wanka.

Allah sarki umminsu lailai!duk abunnan da take fuskanta saboda ita daya mamanta ta Haifa kamin ta rasu wanda ake zargin tsafi akayi mata. Shiyasa kaf Yan uban babu mai sonta saboda irin kaunar da babansu ke nuna mata.
Auntyn nan ce ma suke dan Fadawa kaf gidan.

Gida ta wuce abina ta Shirya sannan ta dawo asibitin wayan lailan ta kira taji a rife kawai sai tace bari zata sake gwadawa anjima maybe network ne sannan ta zauna taci gaba da taryan kawayen Ummi Yan gaisuwa da dubiya.

๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน

Abangaren su minal kuwa ita ta fara tashi jinta kwance jikin yazeed yasata yin murmushi sannan tadan kamo sajen dake kwance a fuskansa luf luf tana wasa dashi........

*Gaskiya na gode sosai da supporting dina da kuke yi Allah ya biyaku.*

*Sainaji comments dinku, yau bakuga yanda na dinta murmushi da ina karantawane ba Kamar wata shashasha.*

*Insha Allah zanyi kokari ina yi muku reply*

*Ya kukaga yadda na warware matsala Laila?yayi ko?*

Karamarsu babbarsu ce fa๐Ÿ˜‰

Miss untichlobanty๐Ÿ’•

11 December, 2019.
[1/11, 2:29 AM] Mzz_Untichlobanty๐Ÿ’ž: *๐Ÿ†๐Ÿ†KURUCIYAR MINAL ๐Ÿ†๐Ÿ†*

๐ŸŒนby miss untichlobanty๐ŸŒน

*CHAPTER 55*

Yazeed jin Kamar ana Jan gemunsa yasa yadan bude ido ya kafawa minal wacce Keta jajjan sajen nasa Dan batama lura da Cewa ya bude idonsa Ba.

Hannunsa yasa ya riko hannunta da take ja masa gemu yace kazame yau kuma da gemuna za'ayi wasa? murmushi tayi tana kifa fuskanta a faffadan kirjinsa mai dumi da sanyin kamshi.

Murmushi yayi mai Sauti yace humm ! Yar kazame taga handsome. Dago da fuskanta tayi tana mai kicin da ido tace Allah yazzy baby Idan ka Kara cemin kazame zanyi fada dakai.

Rife ido yayi yace oooo not this name again please ki daina cemin yazzy baby Wai bazaki manta bane?tace har abada kuwa. Yace haba kazame na please ki dena cemin Yazzy baby tace saide Idan zaka daina cemin kazame yace to me kikeso in dinga ce miki?kinaso in dinga ce miki beauty?kindy? Sweet? Cup cake?cutie pie? Bl..........

Datseshi tayi tace ni banaso kawai ka dinga kirana da abinda kake kiran..... Um..... Ka gane ai ta fada tana kara sa dayan hannunta dake free Wanda bai rike Ba.

Yace ah ah ni ban ganeba,tace yadda kake kiran aunty uwar gida. Dan zaro ido yayi yace kina nufin zakiyya?Daga kai tayi yaja hancin ta yace na ganoki wato kishi kikeyi.

Bata rai tayi tace ni Ba kishi nake Ba yace haba my baby Nasan fa kishina kikeyi turo baki tayi tace ni Ba kishi nakeyi Ba. Yace Toh me yasa bakya kishina ? Tace saboda me yasa zanyi kishin ka?

Yazeed's POV

Shiru Nayi jin tambayan data aiko min don bansan yanda zan amsa mata Ba.
Bansan lokacin da bakina yace saboda kinaso.
Murmushi taci gaba dayi da alamu bata dauki abinda na fada da muhimmanci Ba. Girgiza kanta tayi sannan tace ni bana sonka kawai kai aboki nane.

Sanda zuciyata tayi tsalle dukda Cewa nuna ban tabbatar da Cewa songs nake Ba amma da tace bata sona take zuciyana ta fara suya. Da alamu ta lura da yanayin Dana Shiga domin atake naga damuwa dauke a fuskanta saide abinda ya bani mamaki sakan gemuna da tayi saijin lallausan hannunta nayi akan kumatuna tana goge wani Abu mai ruwa. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kuka nakeyi.

Minal's POV

Ni ban dauki abinda yake fada da muhimmanci Ba Dan gani nake wasa yakemin. Ya za'a yi mutum Kamar ya yazeed ga kudi, ga kyau, ga Suna,ga daukaka yace Wai sonshi nake?
A Gaskiya na kamu da dinshi Ba tare Dana Shirya Ba domin bansani ina sonsa Ba,sai ranan Dana sameshi da zakiyya a parlour Suna hadiye fuskan kuna ji Nayi Kamar na mutu boyewa kawai Nayi.

Ganin yana jiran na bashi amsa yasa na girgiza kaina cikin shiririta na nace bana Sonka kawai kai aboki nane. Mamaki tare da tashin hankaline suka kamani ganin hawaye na saukowa Daga idanunsa bansan sanda nasa hannuna na goge masa ba. Me yake shirin faruwa ? Me hakan ke nufi? Me yasa yake kuka Dan nace bana sonshi? Yana sonane?

MY POV

Yazeed ne ya rasa yanda zaiyi Wai kuka yakeyi?kardai dagaske Sonta yakeyi to amma yaushe ya fara sonta? Ganin shirun yayi yawa yasa ya hade bakinsu Ba tareda yayi Komai Ba abinda ya basa mamaki shine mayar masa da tayi Dan haka baisan lokacin daya kara zafafa lamarin Ba. Sanda yaji zasu mutu saboda rashin numfashi ya sake mata baki.

A Dan kunyace ta tashi ta fice Ba tareda suncewa juna komai Ba.
Dunkule Hannu yazeed yayi sannan ya naushi iska. He ruined everything! What if da haske take bata sonshi?yayi gaggawa wajen nuna mata abinda ke ransa even though it was not intentional. Shima bai Shirya ba, yanzu ya zaiyi ya gyara abinda ya bata.

๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน

Zaliha kam though time take bawa Yan Maiduguri Dan Cewa tayi dole a miyar da ita Kaduna. Duk masifar inna sanda ta hakura ta bada gari.
Nan aka lallaba zaliha akace tayi hakuri gobe gobe zasu dawo Kaduna amma sai ta yarda tasha tsuminta.

๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน

Ya Abubakar yana shigowa Laila ta danno da gudu ta rungumesa. Shidai baisan me ya faru ba amma ganin yadda take farin ciki kuma ta wartsake yasa yasan Cewa alkhairi ne ya faru.

Janyota yayi har suka zauna yana dariya yace aunty fadamin abinda yasa Laila na irin wannan farin ciki.

Dariyan manya aunty fauziyya tayi kamin tace kafin wannan yanzu dai ka saketa tunda ba'a daura auren ba sai a lokacin ya lura da yadda suka kankame juna cikin jin kunya Laila ta gudu ciki yayinda ya cire hula yana sosa keya.

Aunty fauziyya tace ja'irin yaro ina ganinka Kamar salihi murmushin borin kunya yafi yace ba haka bane aunty.
Tace to Nide albishirinka yace goro kuma fari kamin ma ki tambaya.
Dariya tayi tace todai in fada maka babu abinda ya Shiga tsakanin Laila da Dan iskan yaronnan.
Nan ta fada masa yadda ta gano da yadda suakyi da likita.
Godiya ya dinga yiwa Allah harda sujjada baisan sanda hawaye ya zubo masa ba. Zaunar dashi tayi akan kujera sannan ta Dafa kafadan sa tace ba kuka zakayi ba hamdalan da kayi shine dai-dai addu'a zaka cigaba dayi allah ya kareku Daga sharrin makiya yace ameen.

Kicewa lailan ta samoni a mota zamuje gidansu yazeed tace Toh sannan ta Shiga ciki.
Fita yayi ya kirawo almajirai. Nan ya dinga daba musu kudi sanda ya raba sama da 10k.

Laila da ta fito sai murmushi take har tayi wani Dan kyau hakannan. Kai kwanciyar hankali dadi gareshi.
Gaba ta Shiga ta kwame ya Abubakar ma ya Shiga driver's sit. Belt yasa sannan ya kunna motan hannunta ya kamo ya sumbata ta warce tana turo baki yace ya akayine gimbiyata? Tace ba'afa daura auren ba kake rikeni yace astagfirullah wallahi duk cikin dadin ne ni na manta ma Allah ya yafemin tace Ameen.

Motar su suka fita Suna masu jin dadi sai gidan oga yazeed.

๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน๐Ÿ€๐ŸŒน

Abangaren su yazeed kuwa minal cikin yar iskar rigannan ta nufi kitchen kuma bilhakki da Gaskiya yunwa takeji Dan 10am ma ya wuce ko time din canja Riga batada shi.
Hamdala tayiwa Allah Dayasa akwai sauran Mara 3 a tuwonsu na jiya Dan da babu da idomie zata dafa.
Aiko nan ta daura dumame ziciyarta na wurin yazeed da yanayinda ta barshi yayinda takejinsa a jikinta.
Yazeed ko shiru yayi kawai Dan bai Masan me ya dace yayi a halin yanzu ba kawai sai ya mike ya fada wanka bai wani bata lokaci ba ya fito dai dai lokacin wayarsa ta dauki ruri dubawa yayi yaga mom ne hakan yasashi yin murmushi Dan yayi kewarta Rabon dayaji muryanta tun sanda tayi masa fada.

Dauka yayi tare da fadin my sweetheart kaif asbahati? Murmushi tayi Dan itama tayi kewan Dan nata tace lallai Abu yayi dadi tunda har ka fara manta lokaci nida nake India ne yanzu safiyata? Yace sorry sweetheart kinsan Nayi missing dinki fah.
Murmushi tayi tace abinda yasa na kiraka kenan Dan gobe ina tafe. Murmushi yayi amma saboda shekiyanci irin na yazeed yace noo!sweetheart karki dawo zaki batamin honeymoon dina.

Kama ha'ba tayi Kamar yana kallonta tace dannan kace Abun naka ya girmama ! Lokacin Dana aurama ba iskanci zaka min ba? Ta fadi hakan sounding like a drama old lady.

Dariya yazeed yayi yace Allah ya kawomin ke lafiya my sweetheart kinsan fa you are my first

Please Login or Register in order to submit comment