Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alamun lallashi

Saida yayi mai isarsa sannan ya tashi zai fita Jamal yayi saurin rikosa tare da mikewa tsaye Suna fiskantan juna yace lallai mudin abokai ne amma abokantakan ya ya karfafa Yan uwantakan mu lallai nidin na kasance mai kuskure d............

Hannu yazeed yasa ya rufe masa baki tare da girgiza kai yace lallai nine me laifi da ban sanar dakai Ba kuma ai sanda kace zaka kawo mom saina mata bayani,na dauka wasa ne Kamar yanda ka saba Dan nima baizo kauna Cewa zakuyi min mummunar fahimta Ba saboda yanayin yarinyar. Lallai kaidin amini ne na Gaskiya saboda alkhairi kake sona dashi Dan haka karka bani hakuri.

Rungume juna suka kara yi kowannensu na hawayen farin ciki kamin kuma suka fashe da dariya suka tafi domin yin sallh Dan lokaci ya tafi.

Abangaren su mom kuwa wani daki ta kawo minal sannan taje dakin zakiyya wardrobe din ta ta bude Dan tasan pin din taga duk babu laces da atamfofin

Wani kofa acikin dakin  ta bude dakine girman sa Kamar store babu Komai aciki sai akwatina 5 wasu takalma masu kyau amma zakiyya tasa a store Wai sun tsufa alhalin Kamar saga kwalinsu aka cirosu ko kurar arziki basuyi ba

Akwatinan mom ta bude ta dauko wani lace mai kyau da takalmi da kuma hijabi sannan ta rurrufe wurin ta kawo dakin da tabar minal

Ajiye kayan tayi sannan ta kalli minal wacce ta zauna a kasa tace Yan mata tashi ki zauna akan kujera mana ayayin da take nuna mata sofan dake dakin

Girgiza kai tayi tace Ba Komai nan ma yayi
Mom ta kamo hannunta ta zaunar da ita sannan tace
ya sunanki?
Tace Amina
Mom tace ya akayi kikazo gidannan kuma me hadinki da Dana

Kallon mom minal tayi kamin ta fara kwararo mata bayani cikin nutsuwa,kamunkai da tarbiyya Kamar da gaske tun daga fitowarta daga gidan aunty fauziyya har izuwa yanxu

Not telling her that this is not the first time she met yazeed

Shiru mom tayi tana nazarta maganan

Da ta tambayi yazeed kamin ta mareshi amma ai kowaye yaga yanayin aminan abinda zai ce kenan kuma ko Ba Komai soyayya ta jawo hakan ai Dan masoyinka ke hukuntaka akan laifinka

Makiyinka ne zai ganka kana Abu Ba daidai Ba ya barka ko ya kara ma kwarin gwuiwa

Kayan ta mika mata sannan tace tayi sallah za'a kawo mata abinci kamin ta fita tana tunanin lallai yazeed bai kyautaba na azabtar da minal da yayi Ba tare da yaji mai ya kawota motansa Ba sannan taya za'ayi ta miyar da minal gida a wannen yanayin?

smiling tayi wadda ke nuna ta samo mafita

Masu aiki ta aiko da kayan abinci
Lokacin minal ta chakare tayi das da ita har taji wani fresh a jikin ta murmushi tayi tace tsabta dadi

Dakwalin ta dauko zata daura saita fasa kawai tasa hijab

Zama tayi a bakin gado tana kalon tsarin dakin

Ya mugun tafiya da imaninta

Abincin aka kawo duk babu Wanda zata iya ci sai shinkafa haka ta daure ta tuttura taci rabi Dan ita shinkafa Ba gwanarta bace

Doctor mom ta kira aka da mata su bandage a inda taciwo aka Duba kafarta targade tayi aka daure mata shima likita yace tanajin wani ciwo tace a ah Dan tasan da tace eh to tasan allura ne😂😂

*(People like me and minal come and gather here lets know our selves)*

*Karamarsu babbarsu ce fa kai yau Nayi rubutu chapter har uku fa kuma ina tunanin kara wani*

*oya ku kirawo kawayenku da Yan uwanku masoya karatu suzo su yar da zango Anan.*

Mzz untichlobanty💕

Au Ashe bansa date Ba

10 July 2019
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 17*

Abangaren yazeed kuwa suna dawowa daga masallati dakinshi ya koma ya kwanta domin zazzabine ya kamasa sallan ma daurewa yayi

Gawani tsananin tsanar minal dake taso masa

Wai yau shi mom ta Mara akan wannan kazamar bagidajiyar? Kuma har ta fidda masa jini?

Lallai sai ta gane kuranta a haka bacci yayi awon gaba dashi yana nazarin yadda zai yi maganinta minal.

Haka ta kasance Abangaren Jamal domin shima zaki ya nufa yayi d'are d'are a saman gado harda cire Riga sannan ya Lula duniyar bacci.

Abangaren su inna jikin baba Ba laifi ya Dan warware amma daka gansa kasan yana cikin damuwa.

Inna ce ta dinga yi masa nasiha tana kwatar masa da hankali har ya hakura ya fita domin zuwa gidan radio da jarida ayi sanarwa ko Allah zaisa a ganta

Aunty fauziyya ma ta daina kukan,mijinta yanajin labarin yayi gida haka zaliha ma ta tattara ya nata ya nata tayi gidansu.

Sanda mahaifiyar zalihan wato iyata sami labari kafafun ta kasa riketa sukayi.
Harga Allah minal yarinya ce mai Shiga rai dukda ko bata daukan raini ga tsiwa da tasha tayi tatul.

Hankula Kam dan banace hankali Ba sun tashi, yan anguwan su minal ma sunji tashin hankali,Yan matan nan ko da minal tayi musu saitin hamma da gyaran kafureto kwanaki sai Cewa suke Allah ya kara.
Wasu daga cikin Yan anguwan sun yi farin ciki,wasu na yada jita jitan ai iskanci ta tafi,mafi yawanci kuma na tausayawa baba saboda shidin tsoho ne mai dattako kuma ansan yadda yakeson minal shiyasa Idan tayi wasu abin ma ake boye masa.

AT NIGHT(after magrib)

Minal tana zaune a daki tayi zugum gashi bata Masan Inda wayanta yayi Ba abin duniya ya taru ya mata yawa.
Ko wani hali iyayenta ke ciki?me zata ce musu?

Kofan dakin aka turo laraba ce tace Wai hajiya tace kizo.
Amsawa tayi da Toh sannan ta dauki hijabin da aka bata tasa ta fita.

Da dingishi sannan ahankali take saukowa daga upstairs saboda tsoro da kuma rashin Sabo amma inka ganta zaka dauka damuwa ce.

Mom ce tace sauko kizo wajena kinji my daughter.
Karasa saukowa tayi taje wajen mom ta zauna a kasa. Mom tace zo zauna gefena kinji hira ta fara janta dashi itakuma sai nokewa take.
Mom tace ki saki jikinki babu abinda za'a miki kinji kai ta gyada Kamar Kadangaruwa sannan ta Dan saki jikin nata.

Suna fira kawai alarm din 8 ya buga da gudu minal ta tashi mom tace relax is time for dinner.

Batade gane me akace Ba amma ta zauna tana zazzare ido.

Maids dinne suka fara fitowa da abinci ana kaiwa dining table.
Mom ta kamo hannun minal tace muje ko Ba musu ta bita suka he wajen dinning table minal de mamaki take Wai Ashe a duniyannan akwai masu rayuwa Kamar a aljanna masha Allah dama nida su inna nane.

Sai kuma tayi chuckling to the sound of her calling inna innana.
Warmers din suka fara budewa one by one minal taga duk batasan abincin bama.

Mom tace wanne za'a sa miki minal tayi shiru domin bataso tacewa mom bazata ci Ba.

Mom ta fahimci batason abincin daga yanda tayi da fiska sai tace atine kuje kitchen tare Ku kama mata ta dafa duk abinda takeso.
Suka amsa da toh hajiya.

Mom tacewa minal tashi kije kinji kunya ne ma ya kamata taga ya akeyi Wai manya suke ramfo ka duk wayon ka ?

Tashi tayi suka Shiga kitchen din tace musu sunada dawa gyararre wanda zatayi tuwo su kace ah'ah semovita ne kawai pack daya shima ya Dade bari su Duba ko yayi expire dubawa sukayi sukaga beyi ba sai suka bata.

Tace akwai wani Abu da zata iyayin miya Kamar kuka,kubewa,ogbono,taushe sukace a'ah amma akwai ganye tace to subata nan dai ta dinga fada musu abubuwan da take so Suna dauko mata saide bata bari Susna mata hannun ba.

Haka ta fara aikinta cikin kwarewa Inda ta dafa tuwo miyan ganye ya sha kayan hadi yaji kaza tun kafin ta gama yawunta ke tsinkewa Dan mugun yunwa takeji ga kamshi daya mamaye ko ina.

Mom tana kallo a parlour ta jiyo kamshi smiling aranta tace yarinyannan ta iya data shinkafa Dan tasan yamatan yanxu akwai maitar shinkafa(Nide ahalin tuwone😉)

Koda ta gama warmers
(foodflask) suka kawo mata madaidai ta.

Tuwonta Mara(malmala) 3 ta saka a ciki sannan tace su bata wani flask din Malmala 5 tasa a ciki sannan ta basu tace suci nasu ne ladan tayata aiki.

Godiya suka rinka mata yayin da suke satar kallon junansu me ma'ana 'tanada mutunci ko me yasa oga sir ya mata abinda ya mata oho?" Sai kuma sukayi murmushi. Tray suka dauko suka daura flask din nata akai sannan suka kai dinning
Fitowa tayi daga kitchen din ta nufi palour wajen mom cike da kunya tana nazarin me zata ce?

Sai kuma ta tsaya "in banda hauka irin nawa taya za'ayi Maman oga sir taci tuwo?ehm kawai bara inyi mata godiya "

Parlourn ta karasa sannan taje kusa da mom ta zauna kanta kasa tana wasa da yatsu mom cikin wasa da accent din ta na Larabawa shigen na Jamal tace daughter har kin gama mana abincin ne? Murmushi tayi kamin ta gyada kai sannan tace Nagode hajiya da irin kyautatawan ki gare.....

Bata karashe maganan ba sakamakon riko hannuta da mom tayi tace"ni ba godiya nace kiyimin ba Dan Allah nayi sannan karki kirani da hajiya kinji?zaki iya kirana da mom"

murmushi minal tayi kamin tayi subutan baki wajen Cewa inkawomiki abincinne?

Smiling mom tayi Allah ya gani bata da niyyar cin abincin amma kar minal taga Kamar kyamanta mom take sai tace ki zuba mana tare.

Zare ido tayi tace tare kuma mom tace ehm.
Girgiza kai minal tayi tana wiki wiki da ido aiko karen haukane ya cijeta bazata taba cin abinci plate daya da mom ba taje wannan oga sir din ya ganta yaci ubanta tabe baki tayi tace ko ina yayi oho.

Muryan mom ne ya datse mata tunani ta hanyar cewa wasa nake miki kinji ki dibi naki kawai zanci anjima

Gyada kai kawai minal tayi sannan ta wuce ta dibi tuwonta Mara biyu tayi sama domin kunsanta ba wasa.

Aiko ta gyara wa tuwonnan zama sosai Dan ya mata dadi.
Abangaren mom ma haka ta kasance Dan tana diban Rabin marannan tayi dakinta ta gyara masa zama tare da yaba iya girkin minal sannan ta kara samin kwarin gwuiwa kan aniyarta.

Nikam side din masu aiki Nayi domin kar ayi bani Dan nima fa tuwonnan ya biya raina

Bazakusha mamaki ba sai sanda naci tuwo Nayi nak ai bansani yadda akayi medical yet fashion looking glasses dina ya fita ba niqabi na kam ba'a maganarsa Anan bacci yayi awon gaba dani 😴ko wanke hannu banyi ba😂

Gaskiya na gode sosai da addu'an Ku domin Alhamdulillah result ya fito kuma Nayi passing harma andawo second semester Muna shirin tafiya hutun mid semester daga nan sai test Dan haka ina bukatar wani addu'an Allah ya saka muku da alkhairi da fatan ina nisha dantar daku masoya na

Eid mubarak in advance

Nice de the one and only karamarsu babbarsu wato

Miss untichlobanty💕

5th August, 2019

Wait oooo don't forget to vote ehee..........
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYA MINAL🏆🏆

🍀by mzz_untichlobanty🍀

*CHAPTER 18*

Da asuba bayan mom tayi sallah taje dakin minal domin ta tasheta sallahn asuba
Sallama tayi ta sameta Zaune abakin gado
Saukowa minal tayi ta tsuguna tace ina kwana haji.. Au mom
Murmushi mom tayi tace lafiya kalau ya kwanan bakunta

Murmushi minal tayi domin yadda mom din tace bakunta da kaji kasan ba bahaushiya Bace kamin tace Alhmdllh

Mom tace Ashe har kin tashi? minal tace ai tun dazu ma na tashi
Smiling kawai mom tayi tace to bara in barki ko

Domin ta fahimci minal is no comfortable 

Koda mom ta fita ajiyar zuciya minal tayi domin wani azababben ciwon mara takeji ko jiya ma tayi mamaki da ciwon bai dameta ba(abinda bata saniba shine pain reliever din da aka bata jiya domin ciwon dake jikinta shi yayi aiki harda maranta)

Bayan yazeed ya dawo daga masallati alokacin dai jikinshi ba laifi ya lafa masa amma still he is not active
jallabiya ce sanye ajikinshi ya zauna abakin gadonsa yana Yan nazarce nazarcensa,can sai yaji yunwa na Dan damunsa kawai sai ya fita ko zuwa kitchen ne domin ya hadowa kansa coffee domin shi Allah ya gani bayason masu aiki Suna dafa masa abinci kawai de babu yadda ya iya ne,idan yayiwa zakiyya maganan kuma to shikenan fa sai ta birkice masa

Dan bazai manta ba akwai wani lokaci

Zakiyya ta dawo daga party a weekend ne ma gown ne ajikinta sai attachment data kwama Kamar matan pastor takalmin nan kuwa tsini yadda kikasan Biro taku take had ta isa dakinta babu Bismillah balle salati ta fada kan gado
Alokacin karfe ukun darene yazeed kam ya gaji da irin abinda takeyi ko bazataji maganarsa ba ai ta sauke masa hakkinsa ko?

Shigowa dakin ta yayi da Dan murmushi sa yazo kusa da ita ya kwanta tashi tayi awani zabure tana bata rai kamin tayi tsaki "ni Gaskiya baby kafiya jaraba haba ace mutum duk abin atakureshi yaushe yaushe kazo dakinnan na baka aka abinda kakeso is not more than 7 weeks fa shine har ka dawo,why are you acting like a sex addict pls let me be am not in the mood mtsww

juyawa tayi domin taje ta core kayanta wani wawan fincika yayi mata ya hada da jikinsa
" ke karkiga ana daga miki kafa ki nemi ki kawo min rashin kunya mana,is it not a shame to u wani yaji kina Cewa is not more than 7 weeks kika bawa mijinki hakkinsa?2 months Ba week daya kenan and u are even bragging about it.
Who the hell do u think u are da zaki kirani da sex addict,had it been am a sex addict ke do u think ko tafiya zaki iyayi ne ke kinsanni Ba wasa,but because bakisan ya kamata Ba shine amatsayina na mijinki kike fadamin all this nonsense,hakkoki na nawa na aure kike saukewa?baki min girki,baki darajani,baki ganin kimana amtsayina na mijinki, baki bani hakkina na gado,ko girki bakiyimin balle wanki yanzu haka Inda za'a tambayeki singlets dina nawa baki sani Ba balle boxers and short nickers .
Balle abinci kam da naci da banci Ba all the same talk less of ki dafamin mahaifiyata kuwa su ........

"Ya isheka yazeed enough is enough ince duk blabbering dinnan dan nace no sex ne ko ?

Kawai sai ta rarumo lips dinsa, already tasan weak point dinsa yazeed kuwa Dama ahannu yake kawai sai ya fada ruwa

Fadawa gado sukayi ita Asama shi a kasa tana romancing dinsa,yadau abin arziki za'ayi. Ashe so take ta tsokalo masa masifa ta gudu Allah sarki babu yanda ya iya haka ya rabu da ita tayi iya son ranta dan shikeda bukata koda yaga abun ba karau Ba kawai sai ya juya da ita,aiko Ba wani on your mass,set,ready kawai go ne. Aiki ya fara Ba wasa babu kama hannun yaro. Mai nuna mata imani Ba Dan sanda ya biya bukata ya huce haushi.

..........

Tuntube yayi da wani babban leda hakan ya bada gudun muwa wajen dawo dashi daga tunanin da yaje

Kayan da ya siyowa zakiyya hakan yasa ya fara nazarin ko ina ta Shiga

Karasawa yayi izuwa kitchen sannan ya janyo coffee maker ya fara hada abunshi.

*Toh Anan zan dasa aya ina jiran comments dinku*

Much love 😘

Miss untichlobanty💕

18th August, 2019
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 19*

Coffee dinshi ya hada hankali kwance dinshi yama manta da zancen wata minal

Stairs ya haura sai ya hango Kamar giftawan zakiyya tana shiga section dinta
Hankali kwance ya karasa dakin nata koda ya Shiga baisameta Ba amma yaji karan ruwa hakan yasa ya zauna bakin gado ya fara shan coffee dinshi

sip 2 yayi kamin ya laluma aljihunsa yaji babu wayarsa dayan ya duba still babu sai ya tuna Ashe yana dakinshi kuma yanaso ya Duba wasu important abubuwa hakan yasa ya ajiye coffee din sannan ya fita izuwa dakinshi

Tafiyarsa yake hankali kwance had ya isa izuwa dakinshi

Neman wanyan nasa ya farayi amma bai gani Ba
arching giransa yayi yana nazarin to ina yasa wayannasa?dube ya fara can wani mind yacemai why not ya Duba changing room dinsa tashi yayi ya Duba aikuwa ya hango wayarsa ajiye gaban mirror dauka yayi sai taga message daga mom

Budewa yayi Kamar haka:

"Good Morning habibi!
سأخرج،لا تقلق أرجع قريبا جدا إن شاء الله
(I will go out,don't worry I will be back soon Insha Allah)
Take care 

Reply yayi mata

"Good morning to u too mom,is okay take care of your self see u later

Love yah😘"

Sa wayan yayi a aljihunsa kamin ya koma part din zakiyya

ZAKIYYA'S POV

A gajiye na Shiga dakina hakan yasa direct jakana kawai na ajiye na fada toilet kayana na fara cirewa sainaji an turo kofan dakina
Shower na kunna abina

I can't remember sanda masu aiki suka fara zuwa dakina Ba tare da na kirasu Ba jin wani sannannen turare da kuma alamun an zauna a gado na ya bani tabbacin Cewa Ba mai aiki bane jarabben baby nane ya lallabo ko me yaje nema ?oho

(Oni 'yasu kajimin zakiyya da tambayar banza Wai ko me yake nema?shaa later on zan tattauna akan mata masu irin wannan hali)
Alamun Kamar ya fita naji hakan yasa nayi Wankana sannan na fito sanye da da bathrobe koda na iso gaban madubi

Hango cup Nayi a ajiye juyawa Nayi name na dauko coffee ne mai zafi
Allah sarki baby na Kamar yasan yau zan bashi good news kuwa

smiling kawai tayi ta dauki coffee din ta dawo bakin gado ta zauna tana sha domin ita ta dauka yazeed din kawomata coffeen yayi

Budo kofan dakinta yazeed yayi ya hangota zaune saman gado ta daura daya akan daya tana shan coffee while scrolling her tablet

Sakoko yayi yana kallonta,shi hallin matarnan nasa yana basa mamaki ita bata hada masa Ba Shiya hadawa kansakuma ta dauka tana sha

Gyaran murya yayi ta dago tana smiling Kamar da gaske sai yaji wani babarakwai namiji da Suna haajara
Shi Rabon da tayi masa smiling had ya manta in fact wani zubin ma sai yayi kwana uku bai sata a idonsa Ba grimacing(yake) kawai yayi ya kamin ya gama shigowa dakin

Ajiye cup din tayi tazo ta rungumeshi tare da yi masa peck

Shide kallon ikon Allah yake

Janyo hannunshi tayi suka zauna akan gadon yatinda take kan cinyanshi

"Thanks for the coffee baby"

Smiling kawai yazeed yakeyi yana Dan Sosa keya sai mamaki daya cika shi Dan Rabon da tayi masa irin haka tun 4 months after bikinsu

(Gaskiya fa koni ina mamanki balle kai Wai ! ehm muje zuwa)

"Baby surprise!!!"

Dan hade giransa yayi yace and what is the surprise?

Smiling tayi sannan ta kwantar da kanta a kirjinsa kamin tace for the next 3 month Bazan dinga zuwa office Ba I will be at home zandinga monitoring din
Work ta gida

Yazeed yace my zakky zakky bakida dama yau kuma Yan tsokananne suka motsa ?

Dagowa tayi tace am serious kasan I don't have time for jokes

Kallon idonta yayi tabbas shide baiga alamun karya Ba

Yace like seriously my zakky zaki zauna dani a gida for 3 months? tace "yap"

Tace ko bakajin dadi ne yace no no no that's not the issue Ba haka bane kawai de am shocked ne bama surprise Ba

Tace you shouldn't be kaji ko?ka kwanta bari in saka kaya inzo

Toh kawai yace da ita kamin ya kwanta yanata binta da kallo tsohon sonta na Dada hauro masa

Dogon Riga ta zaka irin cotton dinnan na zaman gida

Sannan ta dawo gaban mirror ta saka roll on kawai Dan bataso ta dagawa yazeed tsohuwar liki gefensa tazo ta kwanta ta juya masa baya

Matsowa yayi ya rungumeta tare da Cewa zakky kinsan banason ana juyamin baya koh ?

Muryarsa Kasai ya isa ya fahimtar dakai yana cikin wani yanayi

Juyowa tayi tana facing dinsa kamin tace baby am sorry we can't......

Bata karasa Ba ya fara kissing dinta sanda yayi kusan 3 min sannan ya tsaya shan iska

Zai Koma tace baby am off

Wani ras yaji Wai shikam me yasa rayuwa ke masa haka da yaga ci sai yaga rashi ?

Amma dai dukda haka bazai bar dama ta wuce masa Ba Dan haka romancing dinta yayi sosai sanda ya rage zafi tukunna ya tashi yayi wanka tazo ya kwanta a gefenta a lokacin harta bingire da bacci

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Around 7:30am su mom suka isa unguwan su minal.
Minal kam sai washe Baki take yawa gonar auduga zataga innanta da baba

Kallonta kawai mom takeyi tace daughter dadi ma kikeji zaki rabu dani ko?

Girgiza kai minal tayi tace kawai Nayi kewarsu ne shi yasa

Mom tace Allah sarki anguwanku akwai amajir dayawa gasu abin tausayi duk a ramko kayan sawa basuda shi kiga wancan Dan karamin ko takalmi baiyida shi danma saiya ya cancanta a taimaka musu they need some help

Minal tace mom Ba amajir bane fa almajiri ake Cewa sai kuma tayi Dan tunawa da turanci da mom tayi a karshe help kawai ta sani sai kawai ta basar

Tace baba bala kwanar dama zaka Shiga

Kamin ta juyo ta kallo mom tace ai almajiran unguwarmu ai sunada Khan gani akan wasu.

Wasufa ko wanka basuyi basuda wajen kwana amma wadannan Ba laifi wasu fa inkika gansu Kamar masu cutan ehmm......kwa..?!kwash....

Mom tace kwashoko

Minal ta gyada kai kamin tace kwarai shi cutan tamowa Ba

Sai tace ganan gidan mun iso

Tsayawa sukayi suka sauko daga motan almajirai da masu tuyar kosai da samarin anguwa Yan zaman kashe wando Suna bawa idonsu abinci

Acikin Land cruiser fara kal suka zo

ko minal ma tasha mamaki lokacin da akace Anan zasu tafi dan San da akayi cakwakiya da ita tukun tahau domin tala Cewa akayi in bata hau Ba za'akira oga sir

Saukowa minal tayi zata antaya da gudu mom tace daughter  tafiya zakiyi ki barni ?

minal tace Ahe tare tare zamu higa
(tofa minal wannan phonetics din Yan kauye ko daga ina?)

Shiga sukayi yayi da akabar malam bala awaje domin jira

ASSALAMU ALAIKUM INNATA !INNA!!INNAROS!

Hazbiyallahu la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem wa nakeji Kamar aminatu na

Inna ke fadin haka cikin murya mai alamun zatayi kukan dadi

Fitowa tayi yayinda baba yake biye da ita rike da hotan minal a hannunsa domin kaiwa gidajen talabijin

Let me take a nap,hmm da fatan kunyi enjoying long chapter nan mude je zuwa 

Ina team zakiyya ne ?are you happy da suka dinke da yazeed?

Team minal kada kusami damuwa everything happens for the best a gaba zaku gane dalilin dinkewar

Team yazeed how far mutumin naku fa zai danyi chilling inji Yan birni😀

Masoya Ina jiran comments dinku

Your comment determine the longness and sweetness of next chapter

Love you all takuce

Miss untichlobanty💕

23th August, 2019
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 20 HIGHLIGHT*

Am so sorry, dear readers! wattpad Suna bani headache😦,my chapter 20 is missing and I don't plan on rewriting it saina gama novel din duka so here is a summary of what it contain:

Emotional moment akayi sharing tsakanin minal da iyayenta yayinda mom tace musu ai bige minal sukayi Allah dai ya kare bataji ciwo sosai ba saboda gudun kar hankalinsu ya tashi yasa bata dawo da minal dinba.

Minal tayi 'kiw da ido mom ta mata alamun karta damu nan su inna suka yiwa mom godiya tana kara nasu hakuri.

Suna zaune cikin parlour minal tace zata gidansu zaliha akace yaje amma ta kula.

Mom tace tanson yin magana mai mahimmanci dasu daidai nan ya abubakar ya dawo daga zariya yana tambayan ko an sami minal akace aiko ba gaisuwa yayi sallama ko? Hakuri ya hada sannan yace shima ayi maganan dashi.

Nan aka gaggaisa sannan akayi masa bayanin Wacece mom. Nandai mom tayiwa su baban kalamai masu kashe jiki sannan ta nemi auren minal kuma tana fata insun yarda ta turo uncles din yazeed next week.


Miss untichlobanty💕

3 - CHAPTER 21-30
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹By @mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 21*

Shiru parlourn yayi yayinda kowa ke nazari aransa

mom tana fata Allah yasa su yarda

Yayinda baba ke nazarin me Yan anguwa zasuce ai Dan abin duniya ya aurarta

Yayinda inna ke Mazarin anya minal zata iya zaman gidan miji kuwa?

Yayinda ya abubakar ke farinciki finally dirty sister dinshi ta samu miji nagarcacce Duba da mutuncin mahaifiyarsa kuma dai ruwa da kankara Abu daya ne samfuri ne kawai ya banbanta

Baba ne ya dago ya kalli mom kamin yace agaskiya hajiya.........

Minal koda ta fito hanyan gidansu zaliha tayi malam bala ne yayi saurin kunna mota tare dayi mata horn sannan ya zuge glass yace hajiya kihau nakaiki Inda zaki mana

Allah ya gani malam bala naaon yarinyan saboda babu ruwanta gashi batada girman kai irin na madam zakiyya

washe baki tayi kamin tace malam bala da ka barhi kawai

yace a ah dai kizo muje

shiru tayi tana Neman hujjan da zata bayar da taji medulla oblongata dinta bai harbo mata Ba kawai sai tahau baya

Owners kwana ta Shiga sai

Please Login or Register in order to submit comment