Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne ya hadu da mom wacce take Nigerian-arabian wato babanta Dan Nigeria mamarta er riyad(saudi)amma a Dubai suke zaune.
Sun hadune ta sanadiyyar babanta saboda Suna kasuwanci tare sannan ya gaba da hankalinshi.
Haka dai sukayi aure kuma lokaci daya soyayya mai karfi ya Shiga tsakaninsu amma Abu daya suka rasa haihuwa haka sukayi shekara 12 Ba ko batan wata tukunna daga baya Allah ya dube su da idon rahama ya basu da namiji wadda suka samai YAZEED tun yana Yaro yakeson armies shi baya kallon cartoon irin na yara in ka Ganshi ya na kallo to sojoji ne har faint na dakin shi na sojoji ne. wata rana ALHAJI ABDULMAJEED ya tattari family dinshi gaba daya akan zasuje aikin hajji dukda Cewa wasu daga cikinsu sun sha zuwa amma wannan karon a tare yakeso suje saide mom bataje Ba itada YAZEED domin Ba tada Lpy sai akabarta tare da kakus Maman ALHAJI ABDULMAJEED.

Bayan sun sauke farali ahanyarsu ta dawowa sukayi hatsari a jirgi inda yawanci suka rarrasu wasu kuma suka sami matsalan haihuwa shi kuma ALHAJI ABDULMAJEED was paralysed. Alokacin YAZEED na shekara 13 saboda tsananin Sabon da yayi da mahaifinsa hakan yasa ya zama so moody rayuwarsa duk ta canja ya zama shiru shiru lokacin dayatafi makarantar sojoji at that tym he was 25 Anan aka aiko masa da rasuwar mahaifinsa yayi kuka har ya gaji tun daga lokacin aka dena gane kansa bayan ya kammala ya dawo anane ya saida some companies na dad dinshi to the some Arabian and British partners na dad din nasa wasu kuma ya rarrabawa family members marasa karfi sosai akan su kular mai da companies din,sai su dinga yin 50 50 atakaice de bai rike ko company daya Ba domin shi soja yakeson zama.

Alokacin da yaje wani mission a Washington Anan ne ya hadu da zaliha lokacin tana shekararta na karshe a university wasa wasa soyayya maikarfi ya Shiga tsakaninsu bayan ta kammala sukayi aure amma ita tace burinta aduniya shine ta zama businesswoman amma YAZEED yace shi bazai iya juran zama babu mace a kusa dashi Ba amma idan ta yarda zai bude mata boutique
Ganin da babu gara ba dadi yasa ta yarda plaza guda ya siya ya mayar mata boutique da office dinta aciki Dana wasu masu mukamai kadan daga cikin masu aikinta.
Amma duk da haka bai tsira Ba domin kullum batada aiki sai boutique da ka tabata boutique dinta kawai ko lokacin kanta batada shi.

Wannan kenan

Show some love by
Sharing,
And
Commenting.

Love you Lodi Lodi sweethearts

29th April 2019
Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:20 AM] Mzz_Untichlobanty💞:
🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by mzz_untichlobanty🌹

*🍀CHAPTER 5🍀*
Bayan ganin tunani bazai fisheshi Ba yasa ya shafa mai ya saka 3quater irin na sojoji da farin T-shirt ya fito mahaifiyarsa ya Tatar a parlourn tace son sai yanxu?Sosa kai yayi yace sorry mom dina na I kept you waiting ko?

Tace is okay,come and eat your food coz na sanka idan ta kai ne zaka wuni bakaci abinci Ba gashi nan yanzu ulcer ta maka kamin kawo wuka

Yace haba mom ya isa mana zanci muje dining din haka ta kama hannunshi takaishi taja masa kujera ya zauna ta zuba mai abincin yace kai mom this is too much tace see you, wannan abincin a 5 years old child can eat it but you hmm you will never change
smiling kawai yayi yafara ci.

Baifi 6 spoons yayi bah yace ya koshi babu yadda mom batayi Ba yace Sam ya koshi haka ta rabu dashi yaje daki domin ya huta

11:59pm (night)

Suna zaune a parlour yana kan cinyarta tana shafa gashinsa Suna Dan hirar su na uwa da d'a zakiyya ce ta shigo taci wani suit na mata takalminnan dogo Kamar zai karye
kwas kwas kwas kakejin takun takalmin ta koda ta shigo ta gansu kawai hannun tadanyi using irin hii dinnan kamin tace wlcm baby tawuce abinta

Girgiza kai kawai mom tayi kamin ta juyo ta lura Cewa dan nata na matukar son yabi matarsa amma kunyan idonta yakeji hakan yasa tace kai dagani ka gani bacci nakeji Ba musu ya tashi tare da mata peck yace good night mom sannan yahau stair case din dazai Sada shi da side din da matarshi take.

ZAKIYYA'S POV

Tana shiga dakinta ta yarda jakanta ta fara cire takalminta kamin ta fara rage kayan jikinta tare da daukan ribbon tana kokarin daure Malaysian attached wig dake kanta Wanda yake red,blue and black in colour taji anyi hugging dinta ta baya

Tsaki tayi kamin tace look baby am soo tired,and am not in d mood so leave me alone pls shinshinan wuyanta ya farayi yana Cewa I missed you Bea tasan sarai me yae nufi hakan yasa tayi saurin tureshi tare da fadawa toilet.

Koda ta fito yana zaune a kan gado Kamar maye yana jiranta bata ko kalli Inda yake Ba taje ta daura hannunta akan wani Dan machine Wanda zaiyi detecting tomb print dinta Wardrobe dinta ne ya baiyyana yayi typing nighties sai daya daga cikin kofofin Wardrobe din suka bude ta dauka wani brown din nylon riga tasa iya guiwa tazo ta kwannta tare da Cewa switch off d light when you are done taja bargo tare da juyamai baya

Mamaki ne ya cikashi Wai dama batasonshi ne ta aureshi koko wani abinne ya sameta coz wata matace za'ace mijinta yayi tafiya ya dawo babu ko sannu da zuwan arziki balle ayi zancen su abinci. Duk da Cewa ya saba da irin halinnan NATA amma nayau is worse haka dai yayi ta sake sake daga karshe yaje ya kwanta a bayanta yana Dan tattabata bige hannunsa tayi yace baby pls Wallahi I need you kinji ?
yadda yayi maganar ya bata tausayi hakan yasa tarabu dashi amma sai mita take masa Wai tagaji hakan yasa bai sami wani biyan bukata sosaiba masu iya magana na cewa da babu gwara Ba dadi

Koda ya tashi da asuba ya tasheta he entered the toilet did all the necessary routine,came out and found her still sleeping ya sake tashinta sannan ya fita masallati ta koma ta kwanta abinta har sai 6 ta tashi Wai bazata iyayin sallahn Ba sai ta dawo(ehm araina nace inkin dawo kuma kice kin gaji Ba Allah sai ya kyauta).

Around 7 ya dawo direct dakinshi ya wuce ya kwanta itako lokacin harta shirya tasaka pink suit mai wandon pelazu ta sauko sai shan kamshi take, ta buga uban extension akai sai yarfeshi take
Mom ce zaune a falo tana kallon news ayayinda take shan coffee,hade rai tayi domin bataso ganin mom din a parlourn ba.

Tace good morning mom,mom tace morning
Zata wuce mom tace zonan zakiyya
Zuwa tayi ta tsaya tana Duba agogonta
Mom tace yanxu abinda kikeyi ya dace kenan ki Duba wani shigar yahudawa da kikeyi koni Balarabiya banyiba,kuma ki fita tun safe sai dare sannan baki ko girmama mijinki balle ni ai ko............
Bata karashe Ba zakiyya tace sorry mom inaso boutique dina ya tsaya dakafarsa sosaine kamin in Dan dinga samun time yanxu fai Ba wa'azi nakeso Ba ince de matsalarki bana girkine to me kikeso kici?ta fadi hakan cikin Sauri tana Duba agogonta domin tayi latti acewarta.

Mom ta girgiza kai tace zakiyya kenan so nake naci koko da kosai tace okay kitchen ta Shiga tabi wata kofa Wanda zai sada ta side din ma'aikata taje bangaren masu girki tace pop out
Cikin kankanin lokaci sukayi layi a gabanta sanda tagama zuba musu kallon raini sannan tace waya iya koko da kosai duk sukayi shiru domin Continental dish yawanci suka iya
tsawa ta daka musu Ba daku nakeba ?

Emm kwanna biyu ban tsokalo muku minal ba karkudamu yanxu Muka soma tafiya

Show love by.........
Kungane ai😉

Love you all

1st may 2019

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:26 AM] Mzz_Untichlobanty💞:

🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

By miss untichlobanty

*🍀CHAPTER 6🍀*

Daya daga cikinsu ne tace na taba gani kakata tayi may be zan iya
Zakiyya tace oya do it right away and take it to that old shit watace tafito faga toilet tana bada hakuri kan Lattin da tayi wani wawan mari ta sauke mata tare da Cewa you are fired hakuri ta fara bata tana Cewa cikinta ne ya baci ta kewaya amma ko kallonta batayi Ba

Tanashigowa parlourn tace mom am off,mom tace haba zakiyya wannan kayan naki Kamar Ba musulma Ba zaki fita dasu kije ki saka mayafi mana

Bata rai tayi tana zunbure zunbure da huhhura hanci taje tasako wani Dan karamin hijabi

Tana fita ta tubeshi tare da Cewa haka kawai duk abi a takurawa mutum mtsww

Zaune take a office tana wani business deal
Telephone ta dauka ta dannan wasu lambobi bugu daya ya shiga tace coffee sannan ta kashe wata ce ta shigo dauke da kofin shayi ta ajiye tajuya tana tafiya kenan taji ruwan coffee a bayanta wani tsalle ta daka tare da Cewa jesus! Heeee I don finish oooo chai my back,my back

Zaliha ce ta wanka mata mari tare da Cewa keep your mouth shut,
Tsit tayi amma idonta bai dena zubda hawaye Ba

Are you out of your sense ya zaki kawomin coffee with white sugar while you knew that Brown sugar nakesha
Sorry ma I was not d one dat prepared the tea it was Sade.
Are you crazy?was is it not your job to make my tea? why will Sade do it?Jennifer!you are fired
Cikin kuka tace ma am sorry

Sakina is absent so I am the one attending to the customers that's why am sorry ma

Shiru tayi kamin ta juya taje ta zauna tace I will give you last chance but if you make any mistake in the future sorry for yourself
Common get out of my office

Tashi tayi tana thank you ma,Tnx u kamin ta fita

Abangaren mom kuwa Anyi mata wani busheshshen kosai da wani tsulan kunu me gudaje kawai kallon abincin ta tsaya tanayi aranta tana Cewa"ya zama dole in nemo wadda ta iya abincin gargajiya Dan ni shekaru na ya fara ja I can't always cook for my self la astadi'u wallah"

YAZEED kuwa sanda ya tashi duk ya gaji addu'an tashi daya bacci yayi Kamar haka (alhamdulillahil lazi ahyaniy ba'ada ma amataniy wa ilaihin nushuur )sannan ya sauka daga king size bed dinshi ya Shiga toilet yayi all the necessary routine sannan yayi wanka ya fito ya Shirya cikin kanan kaya

Yazeed's bedroom




sannan ya fita domin yin break fast koda ya fito mom ya tarar tasa wani jagwalgwalo a gabanta domin shi baisan me kosai bama balle wannan kosan dayayi baki Kamar za'a bawa akuya

Morning mom ya fada ganin bata kulashi Ba yasa ya fahimci Cewa tunani take

Dafata yayi kamin yace mom wats wrong firgit tayi tace son had ka tashi morning
Yace morning amma tinanin me kikeyi mom tace bakomai kawai ina tunanin karo mai aiki ne Wanda she will only cook and take care of me coz duk wannan masu aikin are modern ni kuma na fara tsufa am 54 fa danma inada jiki mai kyau wani sai ya dauka am 50 so dole na rage wasu abubuwan danake yi da kaina especially abinci na
yace to mom how do u expect us to find one

Tace assign one of your soldiers to go to any restaurant that cooks traditional food and then look for the best cook inso samune mace coz banson namiji yana yawo acikin gida

Okay I will try nande akabar wannan kosan kaddaran sukaje dining table tasha tea abinta shiko chips egg and plantain yaci
Sai brown coffee coz bai fiya shan black one Ba.
Bayan sun gama cin abincin side dinshi ya nufa yaje master balcony yana tunani rayuwarsa da zakiyya

Abangaren minal kuwa direct gidan su zaliha ta nufa bayan ta gama da Yan unguwantasu. Shiganta kenan iya(Maman zaliha) tace wa nake gani anan Kamar aminatu 'yar jagwal?yau Anyi abin kai sai yanxu aka shigo? Ai mutumiyartaki tana tanata tsumayinki.

Bata rai tayi tace haba iya ni Gaskiya ki dena ce Mani yar jagwal to me zance aminatu aike da kinzo guri sai kin kawo matsala da kinzo Guri ake sanin kinzo gashi kullum sai kinzo gidan yar tsohuwa tafadi hakan cikin tsokana.

Kara bata rai tayi kamin ta tace wannan kanki ni ina zally take

Iya tace yaran zamani da wani shekiyanci suke yanzu zalihan ne ya koma zalla Toh tana daki ai sai ki Shiga

Shiga tayi ta sameta tana bacci daka mata duka tayi a gadon baya tace shegiya baccin asara ko? ana la'asar kina bacci

Zaliha tashi tayi harda er tusarta tana zare ido Dan atunaninta iya ne domin ta hanata baccin la'asar
Tsaki ta buga lokacin da taga minal ce

Ke Wai me hakan mutun na bacci kin wani daka masa duka

Amina tace tsabar rashin Gaskiya kuma harda tusa ba
Suka fashe da dariya

Haka suka cigaba da hira kamin suka tashi sukayi sallan la'asar suka Shirya domin tafiya makaranta

Ahanyansu na tafiya ne zaliha ke Cewa minal gobe zata rakata gurin aunty fauziyya(auntyn zaliha ne wato Kanwar mahaifinta yaranta uku Aisha ,Abubakar da Muhammad tana Sana'an snacks)
Abubakar ya karye jiya a makaranta
minal tace dama Yaro da shegen kiriniya Ba dole ya karye idan Baku hanashi Ba gaba gaba har wasu zaina karyawa

Zaliha tace garashi yarone

Minal tace to me kike nufi tace me ko nake nufi?
Tace babu fa ta bude baki zatayi magane ta hango wasu en mata en Iskan anguwansu an caba ado za'aje yawon bariki Suna ganinta suka fara bata rai domin haushinta sukeji Wai ta fisu kyau,domin ko Kamar inna ta dauko amma hasken baba dukda Cewa innan ma Ba baka bace amma batada haske sosai amma akwai gashi masha Allah Wanda amina har tafita hakama kyau

Suna zuwa zasu wuce daya daga cikinsu mai Suna bilkisu(bakace er lukuta mai katon timbi ga katon lebe da boobs yadda kasan kwarya saide batada hips Wanda hakan yasa ta zama Kamar an ajiye buhun hatsi gata gajeruwa anci red lipstick,brows dinnan ba'a magana) ta bangaji Amina da kafada

Dan cika amina ta cika amma sai ta basar saboda tunda tayi mafarkin laser fever ya kasheta ta rage jagwal

Ganin bata kulasu Ba yasa sameera (doguwace siriiiiriya gashi batada shape,Ba gaba Ba baya atakaice de yadda Kasan sandar snooker ko ince 1 irinsu akewa kirarin singul amama no front no back gashi taci uwar bleaching had tafara zama danyen nama),
Tace ke Amina wannan wani irin iskanci ne zaki mangari billy ko hakuri bazaki bata ba

Amina batace Komai Ba ta ci gaba da tafiya
hannatu ce(wannan ita ba'a magana)tazo ta bankade Amina.
Ai ji kake tas! tas!! tas!!!

To readers wa aka wanka wa mari haka Indai Amina aka Mara to Ba zaman lapiya

Nide bara in labe daga bayan bishiya in debo muku rahoto

Give me some bossa !

By
Voting
Sharing
Commenting
And
Liking

Your er uwa mai nishadan tarwa da fadakarwa

Examination mode on

Mzz untichlobanty💕

12th may 2019
[1/11, 1:28 AM] Mzz_Untichlobanty💞:

🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

By miss untichlobanty

*🍀CHAPTER 7🍀*

Wani wawan mari amina ta sakewa hannatu har sanda taga tauraro
Sameera ce ta hayaiyako zata daki amina,wani lafiyaiyan mari
Amina ta aika mata atake ta dauke wuta ta suma zaliha ce tace ni amina zo mutafi kamin kisa da naushi Kiyi kisa taja hannunta suka tafi ayayinda akabar bilkisu sakoko a tsaye batada tudun dafawa gashi yau zasu wanki wani alhaji yace su ukun za'a hada lokaci daya (Allah shi kyauta)

Atake taji wani bakin ciki ya rufeta taji ta kara tsanan amina.....

Amina kuwa dasuka je islamiyya sunyi latti gashi malam isa ke taran latti ya iya bulala Kamar Allah ne ya aiko shi

Shikadai ne yake iya dealing da amina kuma tana tsoransa sosai amma tsabar bakin ciki da haushin daya rufe mata ido bata lura dashi Ba
Sai saukar bulala da taji batasan sanda ta karbi bulalan ta karya Ba hade da banka masa harara ayayinda ta murkuda cute pinky lips dinta tace Allah ya isa ta wuce

Malam isa sai da yasha jinin jikinsa domin yasan yadda take tsoranshi(saboda ya iya bulala itakuma duk abinda zai taba lafiyar jikinta bataso)
amma yau harda karya bulala wadda take tsoro Kamar maciji gashi fiskanta yayi jaaa(red)alamun Bacin rai kuma dama shima dai yana shakkunta karfin hali ne kawai irin nasa amma ya girgiza yau Dan haka satinnan dole ya Dan tsagaitawa amina idan Ba hakaba shima zai karbi rabonsa ko ta kullo masa jagwal.
Haka suka Shiga aji Amina tasha mur,zaliha nata aikin ban hakuri hakadai har aka tashi suka dawo gida tana kumbure kumbure.

Bayan sallan magriba inna ta gama abinci ta kwalawa Amina kira bata amsa Ba ta kara kwala mata kira still shiru abinda bata tabayi Ba kenan akirata taki amsawa shiga dakin inna tayi thinking that something is wrong with her daughter to her surprise Amina was sitting down on her mattress

Ke er lele dama kina jina kikai shiru to abincin ki zaki dauka she didn't reply inna rather all she did was sip water from her tiny blue cup

Inna tace er nan Ba lafiya Dan a yadda nasanki ko bata maki rai akayi baki wasa da tuwo amma yau ko motsi bakiyi
Ta fadi hakanne ayayinda take taba goshin Amina Dan inna ji take Amina batada Lpy domin ita bata wasa da tuwo

Jin ko magana batayiba yasa inna ta fita ta samu baba ta labarta masa abinda ta gani baba ne yace rabu da ita zamu hadu atakaice de ranan Amina bataci abinci ba.

Washe gari koda Amina ta tashi tayi shara da wanke wanke ta gama koko,
Sai wajen karfe goma ta tuna da Cewa zata raka zahra anguwa tashi tayi tasa hijabi taje dakin inna tace inna ni zan tafi gidansu zahra tace zan rakata anguwa

wani kallo inna ta watsa mata kamin tace shine gaisuwan ki ?

Amina tace mantawa Nayi ina kwana
Inna tace rike abinki
Sannan a haka zaki rakata anguwan kai Innalillahi aminatu yaushe zaki canza yau kwana uku kenan bakiyi wanka kuma a haka kike tunanin zaki samu miji ki Duba kullum in zahra zatazo gidannan kwas da ita amma ke a birkice

Since bakin zaninta tayi ta miko mata Dari biyu ki siyo sabulu da tirare dan d'uri da sabulun gashi kinji

Bubbuga kafa Amina ta fara haba inna zan bata mata lokaci fa
inna tace to wallahi inbakiyi abinda na fada Ba babu Inda zaki mutum sai shegen kazanta Allah ma daya taimaka bakida karnin kashi ai da mun mutu

Turo baki tayi tana guna guni har ta siyo ta dawo
Inna tace maza Shiga wanka ki wanke kanki sai kizo in miki kitso saura kiyimin gardama ma babu inda zaki
Subul subul tayi Kamar yadda inna ta umarceta ta shiga ban dakin shiru shiru babu ita babu labarinta inna tace wai me kike yine har yanzu kinsan dai jiranki nakeyi ko?

Fitowa tayi gefen kanta duk kunfa inna tace ke haka ake wankar duk dadewannan nanki baki daurayu Ba? Bata ko kula innar Ba ta shigewarta daki ta goge kan sosai ya zama saura damshi sannan ta zauna aka mata kitson ta dauko kayanta mai Dan haske ta saka sannan ta Dan shafa man baki sai tayi dass da ita.

Tana fitowa inna tace ko kefa amma ace mutum bayason wanka minal tace inna kwana biyu ne fa inna tace kaji banziya ko kunya bakiji har kina daga murya gararin makota suji

Tace to Nide na tafi tana fitowa Zaure ta hadu da baba tace baba ina kwana yace Lpy a'a aminatu ce haka ko bake bafa amma ace mutum kullum...............

Tace to baba ya isa mana tunda Nayi wankan yace yauwa er gari kinga in kina Dan kwalliyan nanne zaki samu miji ko Ba haka ba
murmushi tayi ya miko mata naira Dari yace na sanki da awara watakilla shi zakije siyowa ko innan ki ce ta aike ki
tace a'a gidan su zaliha zani zan rakata anguwa Dan auntyn ta ya karye kuma zamu tayata gyaran gida dashi ke basu Dade da kaura wannan gidan Ba
Baba yace Toh sai kin dawo amma karkiyi dare tace Toh kamin ta fita tanayi masa godiyan kudin daya bata

Tana fita tace Kamar baba yasan banda kudi wlh

Abangaren YAZEED kuwa yau ana shiri da mitimiyar domin bataje office Ba,
Ya Shirya musu evening outing zaliha anci ado makeup kamar ya zubo daga fiskanta attachment dinnan ba'a magana sai harhada rai take wai ita adole batason raini(nace uhm shi baice zaki rainashiba sai ke?)

Taku daidai take har ta iso gaban wani Mercedes Benz sai yauki take alokacin YAZEED ya Dade yana jiranta domin yace shi da kanshi zai tuka su kuma bayason escort na soldiers ko daya.

How is the novel?is it good?any suggestions?

Ramadan Mubarak and happy sallah in advance

2nd June 2019

Show some love

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:30 AM] Mzz_Untichlobanty💞:

🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

*CHAPTER 8*

Tana shigowa ya kunna mota domin yaji haushin bata masa time da tayi domin he values time so much. Tafiya suke a hankali babu Wanda ya kula kowa

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Abangaren minal kuwa ta isa gidan su zally ta sameta tana kwalliya an rike mirror da bakin eye pencil sai zana girannan ake baki wuluk abin abin dariya

'Daka mata duka tayi a cinya
Kinga abinda kika jawomin ko? kullum in zakije anguwa saboda iyayi sai kinyi kwalliya kinsa inna ta Mani kitson dole ta sani kwalliya.

Sai alokacin zally ta kalle ta tace kawai kice kinyi kwalliya kinaso ki nuna mini  shine zaki fake da guzuma ki harbi karsana!
To wallahi bashi dukannan.

Minal tace wannan ke ta shafa sannan ta zauna tace kinsan yau Dana hadu da baba a Zaure na dauka duka na zaiyi saboda tabarar danayi musu a gidan

Ga mamaki na bemin maganar Ba kuma harda bani kudi
zally tace iye lallai kwalliya ta biya kudin sabulu,wato haduwar taki har akan baba tayi tasiri, yo ina batun su babba?hararanta minal tayi taci gaba da cewa amma matsalata dake ko kwalliyan baki iya Ba kinsan mu yan boko kuma wayayyu anaso adinga yin make up mai kyau amma kin wani shafa powder da man baki

Minal tace iye sannu wayaiya yar boko.
Zaliha tace ke nifa zan cigaba da karatu domin suleiman yanason inyi karatu har kudin WAEC ya biya min a wata makarantar private kuma yace zai Nayi mini lesson in munyi aure.

Minal tace lallai ma yarinyarnan wato haka zamuyi dake? tafiya makarantar gaba zakiyi ki barni?

Zaliha tace a ah zama zanyi in jiraki harsai kin zama farfesiya

kallon zaliha minal takeyi yayinda zalihar taci gaba da kwalliyarta.

Can zaliha tace ni yanzu banida burin daya wuce in Tara kudin Indan siya man kara haske Dan ba'kina yayi yawa wallahi.

Minal tace man me?! Sauri zaliha tayi ta rufe mata baki tace toh sannu sarkin karadi so kike iya taji ko?

Tureta minal tayi tace to in tajin ma ai haka akeso ni ban taba Sanin bakida hankali bama sai yau,ke bakisan Cewa butulci wa Allah bane ace yayi ki baka kice Wai bakinki yayi yawa ? Kin FISA sanin daidai ne? Kuma ai koba Komai mayukan blitin dinnan yana 'bata fata bara kij,i kuma iyada lahani sosai saima kinji ciwo in yaki warkewa zakiyi bayani.
Karkiga ke baka ce wallahi wani zai iya mutuwa akan bakar mace kuma wallahi sai kiga fara ko a kafa aka daura masa sai ya kunceta.
Kima godewa Allah kinada kyau farare nawa ne munana?mtswww!

Ajiyan zuciya zaliha ta sauke kamin tace kuma fa maganar ki Gaskiya ne waje daya kika kwafsa Ba man blitin akace Ba bleaching ake Cewa. minal tace Koma menene Nide tashi mu tafi.

Zaliha tace Gaskiya kizo na Dan miki kwalliya minal tace Wanda Nayi ma ya isa.

Tace shiyasa bazaki taba samun saurayi Ba ki Duba ki gani kafin a tsaida lokacin aurena samarina dayawa

Amma ke wa ya taba miki kallon birgewa ma

Shiru minal tayi kamin tace kuma fa hakane wato shine sirrin baki taba fadamin Bako,Allah ya isa

Zaliha tace ai shiyasa kullum inna ke miki fada akan wanka baki gane Ba

Minal tace to me mike jira zana mini ado Yan mata

zama tayi zaliha ta shafa mata Jan powder aka zana girannan akayi mata Layin baki da green

Yadda Kasan er tashe

Fitowa sukayi zasu tafi sukayiwa iya sallama tanata kodasu Wai en matanta zasu haska titi

Koda suka fita zaliha ta ballawa Amina harara tace er uwa matsalata dake baza'a taba iya gyaraki Ba kaf duniya Ba Wanda zai iya in aka gyara nan sai asamo wani matsalan

wannan wani irin tafiyane?
Minal tace me matsalar tafiyannawa ?

zally tace kinga yanda ake tafiya yanga ta soma Kamar talotalo (lol karfa kuce ina kushe characters dina zasu Waye, just for entertainment ne 😂😂)

Minal ma ta fara kwaikwayanta abin har gwara na Zally domin minal ita nata Kamar agwagwa😂.

Ana cikin haka

Please Login or Register in order to submit comment