Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mijin ko matar sa

Aiko yazeed ne yana wani yatsine fiska Kamar yaga kashi sannan yace wato ke gaki hamshakiya ko in bada umarni ki take
Sai yayi murmushin gefen baki to ai shikenan kinga ko Ba Komai zaki ragewa washing machine dina aiki Wanda ke nufin bill din nepa da kuma kudin gas zai ragu domin Daga yanxu  ke zaki dinga wankemin singlets and boxers dina Mara mutunci gold digger kawai.(uhm yazeed kenan sai kace kuddin bill din wani Abu yaje rage masa)
Zaki tashi kije dakina ki dibo su yanzu ko sai na wanke miki wannan shegiyar fiskannaki da tafi
Jiki na rawa ta mike zata fita yace "hold on! dakata" ta jiyo wannan karan ranta adan bace
Yace ya zama dole kibi umarnin matata

Batasan lokacin da tayi kicin kicin da ido tace wallah nanne kuma kayi karya na rantse......

Aguje ta fice domin yunkurin da yazeed yayi zai kamota ya gwabe bakin da Kamar zai bita sai ya Fasa ya nufi dinning area yana mamaki Wai yarinyarnan ce ke masa irin wannan rainin wayon da fitsara?

Zuciyarsa ce tace masa what do you expect from a ghetto girl like her?inbatayi fitsara bama sai Allah ya tambayeta(fadi Gaskiya babana?

Dinning room ya Shiga abinshi ya hada tea yasha tare da cin plantain baifi 5 slice ba Sannan ya wuce gym room dinsa.

Minal ko data dauko kayan wankesu tayi tas  sannan ta shanya sannan ta koma ta nemi abinci taci

Zata koma dakinta taji ance ke!..ke!..ke! asararriyar baiwa zonan juyowa minal tayi a hasale kawai sai kalaman yazeed ya fado mata

Wani irin kallo takeyiwa zakiyya at any moment zata iya mata illa zakiyya ko dukda tana shakkun captain yayiwa minal din magana ko baiyiba amma bazata barta taci banza Ba

Zaki rama ne? Shiru minal tayi, zakiyya ta tabe baki kana tace zokiyi min tausa
Wani harara ta rafkawa zakiyyan aranta tace wallahi baki isa Ba saide mijinki ya kasheni
tasowa zakiyya tayi tana nufo minal domin dauketa da tafi minal ko rayawa take aranta irin rashin mutuncin da zata antayawa zakiyya Idan ta tabata Dan ita Ba jaka bace

Yazeed ne ya shigo cikin isa fiskannan Kamar bakin hadirin daya taso Daga yamma kamshin Cologne din da yakeyi ne ya Sanar da minal isowarsa

Atake kirjin minal din ya buga kana tsoro ya shigeta amma kunsanta da taurin kai bata nuna Ba saide tanaji jikinta har makarkata yakeyi

Wajen su ya iso ya watsawa zakiyya kallon me kikeyi Anan?tsaki taja ta wuce koda ya juyo ganin Inda minal ke tsaye  yaga empty,ta arce.

Zakiyya kam ficewa tayi Daga gidan tana Cewa malam sule idan ya dauko yaranta kar ya kaisu gida ya Kaisu su siyo cup cakes kamin ya kawosu boutique dinta Kamar yadda ya saba

Yace to hajiya Insha Allah ta wuce abinta ta shige cikin 4matic dinta ta wuce .

Don't forget to vote,share and comment pleeease because that is the only way zan gane yadda kukeson novel din.

Taku for life;karamarsu babbarsu wato

Miss untichlobanty💕

13th October, 2019.

🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹@mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 32*

Sama ya haura direct dakin minal ya Shiga ya sameta tana ajiyar zuciya yace follow me !

Ta dago idanunta ta kallesa domin neman karin bayani wani electric shock sukaji dukkansu biyu kamin ya waske ta hanyar Cewa ko bazaki iya zuwa bane kin kafeni da inu munafuka?

Shiru still tayi ya fice itama ta bisa subul subul tana mai gyara zaman yellow hijabinta
Koda ta shigo dakin akan coach ta samesa zaune ya daura daya akan daya yace bazaki iya karasowa bane?
Ahankali ta tako a tsure dukda bata bayyana hakan Ba ta tsaya a Dan gefensa
Yace closer tare da mata alamu da hannu ta Dan kara matsowa harara ya buga mata tare da Cewa cinyeki zanyi ta girgiza kai tana mai karasowa da Dan Sauri tsayuwa tayi a kansa
Ya kamo bakin hijabinta ya janyota kasa
Dan kara ta saki domin hijabin ya Dan kurji gefen wuyanta kana visa kuskure ta Dan taka kafarsa kamin ta zube,yace Dan kaniyarki haka zaki tsaya akan yayanki ta girgiza kai yace bakida baki ne tace a'a

Harara ya kwada mata yana mai hadawa da rakwashi kwas a tsakiyar kanta yace bakisan in antaka mutum hakuri ake basa Ba?girgiza kai tayi alamu tasani tana rarraba idanu Dan rankwashin ya shigeta

Janyota yayi ya matse cute pinky lips dinta  yana kalla yace wato gani sarkin mahaukata ko ina magana kin bawa banza ajiyata

A hankali hannunta na rawa ta daura akan nashi alamun ya sake bakin zatayi magana idanunta ko ya cicciko da hawaye saboda radadin da bakinta ke mata shikuwa wani yaaaam yaji Ba shiri ya saki bakin kana ya kauda kansa gefe domin jin bananarsa na kokarin kawo masa raini

Ahankali cike da in'ina tace kayi hakuri na taka ka,tsika jikinsa suka mike gabadaya yayinda hawayen da taketa boyewa ya samu nasarar saukowa

Ba tareda ya kalleta Ba yace nace miki kimin wanki shine Dan kin rainani ki kamin jika jika ko?

Muryarta na rawa tace wallahi me kyau Nayi kaga hannuna ma ta nuno masa gefen hannunta yadda yayi jaa Kamar ka taba jini  ya fita tsabar yadda ta dirji kayan

Tsaki yaja yace raguwar banza dan kin wanke singlets 3 da boxers 3 Wanda nasa jiya shine zakina wani nokewa Kamar marainiya

Batasan lokacin da tace aide nafi wasu juyowa yayi adan zabure Dan baiyi expecting ta mayar masa da magana Ba
Hannu yasa ya bige bakinta yace zaki tashi kibar gefena ko saina maujeki in canja miki halitta.

Da Sauri tabar dakin tana mai zubda kwalla,lallai tayi kuskuren amincewa da zancen auren Ba tareda ta saurari ko Waye su baba zasu aura mata ba sai a yanzu ne take kara ganin wautarta

Dakinta ta koma ta tsaya agaban madubi tana kallon yadda tayi kyau dukda kuwa ko petroleum jelly bata shafa Ba balle powder amma idanunta sundan fada ciki sannan ta zama kalar tausayi babu walwala a tattare da ita.

Haka rayuwa taci gaba wa minal yanxu har tayi wata 3 a gidan captain  tanayin aikinta Kamar kullum once in a while sukan hadu da zakiyya inta gama banbaminta minal kawai ce mata take Allah ya baki hakuri sannan ta wuce itako zakiyya babu abinda ta tsana Kamar tayima rashin mutunci ka nuna bai dameka Ba Dan haka sai tayita kumfan baki tana cika tana batsewa

Minal ko gani takeyi Kamar zakiyya taci noti kuma tana bukatan Sabo hakan yasa bata tanka mata har tayi ta gama

Aunty fauzy ta kawo mata ziyara har sai biyu Inda take kara jaddada mata girman aure da kuma yadda zata zauna da abokiyar zamanta lafiya. Ita dai minal kunne kawai ta kasa Cewa komi aranta ko tana Cewa cab ai bakisan halin abokiyar zaman tawa da mijinta ba da ko zancenta bazakiso muyi ba.

Yau saura 3 days auren zaliha Inda gobe ne za'ayi kamu
Minal nason tambayar captain izini tun last 2 weeks amma tsoro take yau kam shahada tayi ta turo kofar dakin da yar sallama a bakinta aiko abinda ta gani shi ya Daga mata hankali captain ne ya fito Daga wanka Daga shi sai gajeren wando fari kal da bathrobe Wanda ya barshi haka ba tare da ya daure igiyan ba wanda yayi sanadiyyar Nuna dukkan ilahirin faffadar kirjinsa mai dauke da gashi kwance luf luf Wanda keda laushi hamar gashin kan jariri.

Rikicewa tayi a maimakon ta fita saita fada bandaki aiko ta sule sai a kasa Inda ta bige makunin shower sannan ta gurde kafanta salati ta sake tare da sakin wata gigitacciyar kara hawaye kuwa tuni sun Dade da fara ture junansu wajen saukowa yiyinda ruwa ya mata sharkab.

Captain da bai San ta shigo dakinba yaji ihunta atake ya nufi bandakin ganinta shame shame a kasa ta jike da ruwa jakab ya sashi Jan tsaki tare da Cewa ke Dan ubanki me ya kawoki cikin bandaki na bayan yau ba ranan wankewa ba?

Kuka kawai take kamin tace Dan Allah ka taimaka mini wayyo kafata tsaki yaja da Kamar zai fita amma yadda take kuka yasa yaga bazai iya barinta ba yasa ya miko mata hannu aiko hannunta ta mika ta rike nasa take sukaji Kamar sun taba wayar wuta ba shiri ya saki hannun ji yayi jijiyarsa ta fara harbawa Wanda yasashi Cewa kaide kayi asara yazeed acikin zuciyarsa

Sake miko mata hannun yayi ya Dagata
Dingishi ta soma har zasu fita yace dakata !me kike nufi?

Kallonsa take alamun Neman Karin bayani yace au dake a haka kike nufin zaki Shiga dakina ki jika mini da ruwa saboda Yan garinku basuda lissafi?
Bata fiska tayi cikin rants tace badai garinmu ba wallahi

Yatsansa yasa ya dalle mata baki yace dani kike tayi saurin girgiza kai alamun a ah hannun yasa zai cire mata hijabin dake jikinta ta rike kyam kiciniya suka fara aiko yazeed ya riko hannunta duka biyu da hannu daya sannan ya zame hijabin da hannun daya yayi Ciro dashi

Kallonta ya farayi Inda idonsa ya tsaya kyam akan cikakkun breast dinta Wanda doguwar Riga jikinta da ta like mata har nipple dinta ana kallo wani yawun jaraba ya hadiya 'kutt kana ya kalli fiskanta aiko shi take kallo and she caught him staring at her boobs red handed
Waskewa yayi ta hanyar tabe baki sannan yace yanxu dama wadannan tsiyar ake boyewa?uhm aike yarinya bama kida abin boyewa danko tsirara zakiyi yawo bakikai akalleki ba uhm kwaila lamba daya kawai sannan ya fice ya barta a wurin minal ko tabe baki tayi tanacewa jeka dai Nasan borin kunyace kawai kumanima ai jikina tafi karfin mugu sannan ta murkuda baki

After Kamar 1min saiga yazeed ya shigo rike da wata T-shirt dinshi fari kal wulla mata tayi sannan ya fice yana yana mai Cewa yi Sauri kibar Mani daki

Domin alokacin har wani hajijiya yakeji tsabar sha'awa
Dan Rabon da yayi harka sati biyu kenan amma yanagudun abin kunya kuma ai yarinyar gold digger ce so he should be very careful kar mazakutassa takaishi ta baroshi.

Minal ko tsayawa kallon Rigan tayi wai me mutuminnan ke nufine Wai ko bazai bata wando bane?

Jin shiru bata fito ba yasa yace Wai Dan kaniyarki bazaki fita bane kullum kika Shiga bandaki Kamar mai haihuwa

Sauri tayi ta saka rigar tana mai Cewa ko yaushe ya taba ganin sanda nake Shiga bandakin oho mutum sai shegen fi'ili

Iya cinyarta rigar ta tsaya Dan haka ta fito tana jajjan rigar domin rufe jikinta
Aiko yazeed na ganinta sanda yaji numfashinsa yadanyi seizing
Kana ya dawo
Ganin yadda takeyi da fiska ya bashi dariya amma taci mur

Muryarsa Kamar yasha giya yace zonan
Zuwa tayi ta zauna a kasa domin bata manta da abinda ya mata ba sanda ta tsaya masa akai yace me yakawoki dakina ?

In ina ta fara tace dama Ami..niya..ta..ce zata..yi aure shine....nakeson naje

Tabe baki yayi yace naji zaki iya zuwa amma ko gidanku ban yarda kije ba

Kallonsa tayi alamun lafiya kake kuwa ?
Baibi takanta yace zaki iya bar mini daki kuma kitabbata kin kwashe tsummokaranki

Fita tayi tana nazari acewai mutum rabonshi da iyayensa kusan wata 5 amma Dan rashin imani ace bazashi ba ALLAH YA ISA

captain yazeed zaune a bakin  gadonsa yana buga game din chase a laptop dinsa Kiran mom ya Shigo dauka yayi

yace salamu alaiki ya habibaty

Mom tace Ameen wa alaikas salam son yakake?

Yace lafiya kalau mom i missed you amma ke naga baki damu da Babyn ki Ba

Dariya mom tayi tace Dan Allah dubeka wani kato dakai Wai baby na kai Wai bazaka barwa 'ya'yanka shagwabar bane?

Kwabe fuska yazeed yayi yadda yara keyi inka kwace musu alewa yace ai kowa da matsayinsa nidai Nasan ni Babyn ki ne ya kashe ido Kamar mom na kallonsa

Mom tace Allah ya kawo masu albarka sannan tasa serious tune tace yazeed naji shirufa bawani labari gashi har kunyi kusan wata 5 da yarinyannan kuma kasan dai daya Daga cikin abinda yasa naso maka aurenta kenan tunda naga kaida zakiyya bakuda tsarin haihuwa kusa ni sai mai shirin Haifa ta haifo mini

Hade rai yayi yana yatsine sannan ya tabe baki yace ai mom yarinyan ce tukunna ina Duba natsuwarta da hankalinta sannan inga ta dace ta zama uwar yayana koko?kuma kinga bata gama wani girma dazan daura mata nauyina Ba.

Sakin baki mom tayi jin abinda yazeed din yace

Yazeed kuwa jin tayi shiru yasa yace mom kina jina?

Kamar Wanda aka watsawa ruwan sanyi mom tace d'annan dama duk zaman da kukeyi da yar mutane Ba bata hakkinta kake ba? Kai a haka zaka rike mata biyun yazeed ?kana danne mata hakki?ja'iri shine harda wani Wai bazata iya daukan nauyinka ba sai kace wani abin arziki ka ajiye acikin wandon naka?to bara kaji yarinyar da kake renawan tsab zata daukeka harda guntu Dan jakar uba kawai........

Sai alokacin yazeed ya gane ya kwabsa Sosa 'keya ya fara kana yace mummyyy kiyi hakuri zan gyara Insha Allah

Mom tace karma ka gyara kai ka jiyota kuma zan dawo kasar inyi sati a gidan naku kamin na Koma gidana na Abuja saboda association Suna bukata na dama Hutu na dauka
Nan dai mom ta surfo masa kwadokwandon bala'i kamin tayi masa wa'azi ta kuma tunasar dashi hakkin matarsa dake kansa sannan ta kashe wayarta tana mai jinjina al'amari irin na tilon Dan nata shiko yazeed tabe baki yayi yace Allah ya kiyaye ni dayin abin kunya da jawakai raini

I will be waiting for  your comments

Miss untichlobanty💕

13th October, 2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 33*

Saukowa yakeyi Daga stair case domin zuwa masjid phone dinshi ya dau ringing

Dubawa yayi yaga mom yace yau nadebowa kaina
Picking yayi yana Cewa sweetheart har kinyi missing dinane ?
Ta dayan bangaren mom tace dan Allah ni matsa mini ka rufen baki ka sadani da dadiyata
Marairaice fuska yayi yace haba mummy abin fa baikai nan Ba mom tace yama wuce nan. Zaka hadani da ita inji muryarta koko? juyawa yayi ya fara komawa sama kana ya nufi hanyar dakin minal sallaya ya gani a hannunta alamun sallah zatayi harara ya banka mata sannan ya kika mata wayan yana mata kallon kashedi alamun inata kwafsa zaici ub**ta

Karba tayi jiki na rawa muryar Kamar zatayi kuka tace sallam alaiki, mom?

Ajiyan zuciya mom ta sauke tace wa alaikis salam diyata yar albarka yakike?
Dashi ke wayan a hands free yake  captain na jinsu tabe baki yayi yana mai lumshe idanu

Minal tace lafiya kalau mom tace ya hakuri da mijin naki?minal ta dago idanunta ta kafeshi dasu kana ta sauke tace Alhamdulillah

Mom tace sai hakuri kinsanshi baudadden mutum ne ga taurin kan masifa sai kina hakuri kinji tace Toh

Nanfa mom ta fara mata magana akan rashin hada gadonsu ita da yazeed itakam batasan Inda mom ta dosa ba Dan haka koda mom ta karashe kawai Cewa tayi Insha Allah za'a gyara Kiyi hakuri
Shiru ne ya Dan ratsa gurin jin shirun yayi yawa yasa mom tace da fatan babu wata matsala ko?minal tace babu mom tace Kin tabbata ? Minal cikin in'ina tace dama inaso inyi waya da gida ne salati mom ta rafka kamin tayi kicin kicin da ido tace to bari zanfadawa yazeed din ko?minal tace to na gode Allah ya saka da alkhairi mom tace Ameen. Sallama su kayi sannan ta jiyo domin mikawa yazeed wayarsa

Yazeed ko tun sanda mom ta fara yiwa minal wannan magana ya Lula duniyar tunani.
Tunani kala kala yakeyi kamin. A ransa Gaskiya ni sweetheart tana kwafsamin wannan ai sai tasa yarinyar ta rainani.
Haba fi sabilillah ni Gaskiya.....

Tunanin nasa ne ya datse saboda miko masa wayar da minal kallon hannunsa yayi ya zabga mata harara da tsaki sannan ya Karba ya fice yana mai banko kofar sannan ya kara wayar a kunne yace haba sweetheart ai saikisa yarinyar nan ta rainani ya zaki dinga.....

Ba karashe ba sanadiyyar mom data datseshi ta hanyar rafka uwar salati sannan ta kara da Cewa d'annan wallahi ka fita a idona na rufe kanajina ko?yazeed!yace na'am, yazeed!! Na'am,yazeed!!!sai nawa na kira sunanka yace uku tace to wallahi ka kiyaye ni ka fita daga idona in rife wato Dan wulakanci shine ka rife er mutane a gida baka bata hakinta kuma baka taba kaita taga iyayenta ba?kai ance ma haka ake auren?ko Dan kaga Nina aura ma ita shine zaka nuna min ban isa ba? Shikenan yazeed ni bazan yi fishi dakai ba amma ka sani hakkin yar mutane ma ya isheka kuma ka wuce yanxu basai anjima ba ka siyo mata waya tare da sim da kati da kuma data aciki sauran ya rage naka kuma batun raini saide kar a kuma tunda ka Riga da ka aurota....... Tiiiiitt mom ta kashe wayar

Kallo yazeed yabi wayar dashi kamin ya sauke wata nannauyar ajiyan zuciya. Shikam ya rasa yadda zaiyi da ransa wannan itace rana zafi inuwa kuna.

Koda ya fito da lukman taci Karo a hanya lukman yace boss!boss ya akayine na ganka haka na lura tun da safe Kamar wani Abu na damunka

Harara yazeed ya banka masa yace yau kuma wani fi'ili ka tsiro dashi babu kowan ma kake kirana da boss?
Dariya lukman yayi yace kai mutumi kaide baka canzawa Nide ba wannan ba meke damunka ?yazeed yace babu komai lukman yace haba yazeed na lura tun lokacin da akayi aurennan abotarmu taja baya yes nasani bamu nuna wa duniya Cewa mudin abokai ne especially ta fannin aiki amma hakan ba hujja bace dazaisa ka dinga boyemin damuwar ka kasan babu sirri a tsakaninmu, damuwar ka damuwata ce.
Kallonshi yazeed yayi irin 'look who is talking' dinnan sannan yace dama ba soja kayi ba da gidan radio ka nufa Kamar da gaske fisabillillahi luku tun Muna primary mukaci buri Cewa zama sojoji kuma masu mukami amma me sanda lokacin yayi ka kasa fadamin Cewa bazaka iya zuwa makarantar ba saboda cancer daya kama mahaifinka bakuda hali,ka boye mini sai a diploma ka kare saboda cika burinka kuma ka zama recruit shine yanxu zakana cemin Wai babu sirri tsakaninmu ai boye boye ka gama min ita mtsww.

Sauri yazeed ya fara domin ya wuce lukman amma lukman yayi Sauri rikosa yace haba aminina kar miyi haka dakai mana Nasan ko wannan mahaifinnawa ne ya Daga kar in fadi maka bada son raina bane kaima ka sani yazeed yace naji
In a bossy tone Lukman yace to shikenan idan min fito Daga masjid din sai ka fadamin matsalar ka

Kallon sa yazeed ya kuma yi kamin yace irin oga yayi magana kuma angama ko?

Lukman yace to ya ranka?table baki yazeed yayi kamin suka Shiga masallati yazeed na lissafi a zuciya lallai ba shakka lukman ya kasance amini a gareshi babu karya sudin masu kauna da rike amanar junansu ne kuma tare suke komansu kuma basu boyewa junansu matsalarsu to amma anya kuwa zai iya maganin matsalarsa? zai iya bashi wata shawara da zata anfaneshi kuwa? Toh zaide jaraba ya gani.
Koda suka fito yazeed yace muje ko?gyada kai lukman yayi alaman OK sannan suka Shiga gate din takowa suke a kaga saboda tazarar (Kamar dai yadda kuka sani kuma kuka gani a photo gidan akwai dadi da tsaki ga fili na hauka).

Hanyan garage yazeed ya nufa lukman yace zaka fita ne?gyada kai yazeed yayi kamin yace muje ka rakani
Lukman yace ina?yazeed yace zaka gani. Bugatti Byron yazeed ya nuna masa Dan haka yaje ya dauko key dinta ya dawo ya bude driver's seat ya shige ganin yazeed yayi kikam a dayan Abangaren yasa yace Shiga mana ko ka fasa ne ?

Koda yazeed ya nuna masa alamun abuse masa lukman yace aiko zaka kwana a tsaye yazeed yace an serious fa lukman yace nima haka..... Nan fa suka fara Daga karshe lukman yayi surrender yace kaide ka fita naci bata in bude ma Kafin ka cinyeni har kashi
Fitowa yayi ya bude masa kofar daidai zai Shiga lukman yakai masa kutfo a mazaunai
Shanyewa yayi ya nuna ko ajikinsa dukda ko ta ratsashi aiko lukman yana kewayowa ya Shiga zai rife kofa yazeed ya kafa masa rankwashi

Ouch! Ya dafe wajen sannan ya juyo ya kalli yazeed yace haba my guy irin wannan rankwashi yazeed Kam kauda kai yayi Kamar bashi yayi aika aikan nan ba yace inka gama zamu iya tafiya.

Hello wattys !yakuke ?

Toh kunji wata sabuwa sirrin boye kuma Ashe  yazeed and lukman are friends.
Kunyi tsammanin hakan?

Shin kuna ganin yazeed zai sami mafita a wajen amininsa?

Shin abinda mom tayi ya dace?

Ina jiran COMMENTS dinku.

Love you all😘

Miss untichlobanty💕

19th October, 2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 34*

Tafe suke babu mai magana can lukman yace ina zamu ne Wai?sanda yazeed ya dau Yan sakanni kamin yace muje makarfi plaza inason insiyo waya ne.

Gyada kai kawai lukman yayi alamun ok,Sannan ya kara speed din motar.
Chan yace inajinka. Yazeed sarai ya gane me lukman ke nufi da hakan amma saboda hali irin nasa yace kana jina name fa?

Side glance lukman yayi masa kamin yace zaka fadamin koko?yazeed yace me kenan?tsaki lukman yace sai ka rike matsalarka tunda bazaka iya fadamin Ba.

Shiru ne ya karade wajen kamin can yazeed yace ka tuna wannan yarinyar ?

Smiling lukman yayi domin plan dinsa yayi wato babu Wanda ya kaishi fahimtar abokin nasa idan  ka nuna masa baka damu da Abu Ba to Anan ne zai dauki abin serious.

Luku yace wace yarinya kenan?yazeed yace wannan yarinyar data Shiga booth?
Lukman yace wannan yarinyar daka gasawa aya a hannu kuma kaso ka gasa mata gyada a tsakiyar kai Allah ya taimaka brother Jamal ya kira mom?

Tsaki yazeed yaja yace matsalata dakai kenan ka fiya surutu yanxu waya tambaye ka duk wannan jawabin?

Lukman yace Nide Ba wannan Ba meye da yarinyar?

Yazeed yace ita...sai kuma yayi shiru lukman ya ehm ita me? Yazeed yace itace amaryar da mom ta aura min

Wani wawan birki lukman yana yana zare idanu ya kalli yazeed a tsora ce yace dude me kace ?
Harara yazeed ya aiko masa yace banson iskanci ai sarai ka jini.

'Kefta idanu yayi alamun mamaki sannan yace kana nufin yarinyar nan daka gama shekawa rashin mutunci mom ta aura maka kuma ka zauna da ita ?
Kawai sai ya fashe da dariya harda rike ciki kai mutumina Gaskiya life dinka na birgeni,Wai ina self respect din naka da ........ Ya tafi ?

Wani kallo yazeed ke aika masa if looks could kill da an Dade dakai lukman kabari.
Yazeed yace banson wulakanci ya ina maka serious magana kanamin dariya?karka batamin mood fa. Dan wulakan ci bakasan in ina magana ba'a datseni Ba?'kwafa yayi yace dallah mallam  zaka ja mota mutafi ko zaka tsaya kana batamin time?

Kunna Moran lukman yayi yana mai danne dariyarsa sannan yace haba nawan, Allah ya huci zuciyarka.
Tabe baki yazeed yayi yace in bata huce bafa?lukman yace zama ta huce Insha Allah .

Tsaki yaja sannan ya ci gaba ni yanzu Ba wannan Ba matsalarka shine Allah ya gani bana sha'awar  kusantar yarinyar nan , mom kuma ta dage ita kawai a haifo mata jikoki.

Ajiyan zuciya ya sauke sannan yace zakiyya ko Kazan yadda muke ciki da ita
Gyada kai luku guy yayi alamun ya sani sanna yazeed ya kara da kuma inks lura amaryar tayi karama dayawa bana tunanin zata iya dani.

Wannan magana ta mugun bawa lukman dariya amma to avoid issues with his amini yasa ya shanye abarsa
Yace uhm sannunku manya manya su alharijunal auwaluna

Yazeed yace wallahi luk guy ka fita matsala na rantse da Allah zanma rashin mutunci inma harijancin ne aiba laifi na bane Allah ne yaso ya ganni haka wasu da kudi suke biya dan su zama harijan ?Toh Nina zamu a'bagas sai ince banaso?

Lukman yace chill man Daga wasa yazeed yaja tsaki kasa kasa yace aikin banza mutum matanshi biyu amma ya kare da azumi. Lukman yace karka damu wata rana sai labari.
Daidai lokacin suka iso plaza din, saukowa sukayi Daga Motan lukman ya latsa mukullin ya rufe sannan suka Shiga nan dai suka zabi latest Samsung Inda suka hau musu akan kalar wayan.

Yazeed yace lallai saide a siyi fari domin yafison farin kala ko shudi (blue or ruwan bula) yayinda lukman yace ai golden zaifi tunda itadin zata hau da kowa ni kaya kamar dai sarkar gold kuma ai mata nason kyale kyale ........

Haka suka cigaba da arguing Daga karshe mai Saida waya yace wannan abu mai sauke ne su siyi fari inyaso sai asa mata cover golden.
Nan suka yarda yayin da suke hada baki wajen Cewa that's it!

Bayan sun dawo Motan ne yazeed ya kalli luku yace guy bakace Komai ba.
Shima lukman domin ya rama abinda YAZEED ya masa sai yayi

Please Login or Register in order to submit comment