Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka jibgarsa Kamar Allah ne ya aikosa.

Gwara kansa yayi da gini sannan yace lailar?lailar kayiwa haka?toh wallahi ba me rabaka dani yau sai Allah. Naushi ya dinga kirba masa yayi kaca kaca cikin jini. Kafa ya dinga masa a tsakiyar kafafunsa. Goje ganin Idan bai ceci kansa ba, to fa zai iya kasheshi Dan haka ya tattaro duk karfin dayayi masa saura ya hankadeshi ya gudu.

Da Sauri ya mike zai bishi laila tace barshi ai aikin gama ya gama.
Da gudu ya nufi Inda take ya rungumeta. Tsawo lokaci suka dauka a haka kamin yace Laila me yasa kika biyoshi bayan kinsan halinsa?Ashe bakida hankali?yanzu ga idonta nan ai ko me yace miki bai dace ace kin bishi Ba! Ya fadi hakan cikin Daga murya, fada, da kuma nuna Bacin rai.

Laila da zuciyarta ke mata kuna ganin ya Abu ya rufeta da fada, Ba tare da ya bata Samar maganaba, cikin gunjin kuka tace haka fa yacemin Wai rayuwarka tana cikin hatsari shiyasa banmasan sanda na biyosa Ba idona ya rufe har nabar mahaifiyata ita kadai😭.

Shiru ne ya ratsa wurin na Dan wani lokaci kamin ya Abubakar cikin murya me taushi da ban hakuri yace me yasa idonki ya rufe da akace rayuwata tana cikin hatsari?

Zuciyarta ne ta buga dum! Jin tambayar daya Watso mata Ba tare da ta Shirya amsashi Ba.
Shiko jin tayi shiru yasa zuciyarta tayi sabyi domin bai sani amsar da yakeson Ba. Ga mamakinsa yaga ta dago ta kalli cikin idonsa kamin tace SABODA INA SONKA! Yaya na Dade da Fadawa cikin tekun soyaiyarka tun kamin Nasan ciwon kaina.
Na Riga da na nutse kuma bana burin a ceto ni, nafiso ace na mutu acikinta.

Ya Abubakar Kam daya daskare yama kasa magana Dan ko ya bude bakinsa sai ya rufe ta. Bai masa mata Ba dukda ko tsabar dadi jiyake Kamar zuciyarsa zai fado Daga kirjinsa.

Rigarta da ajayi cillo da ita ya dauko amma me duk a yage take Ba anfanin sata take farin cikin dake zuciyarsa ta sauyu zuwa bakin ciki.
Wani kububuwan kishi ne ya taso masa yana sararsa. Idanunsa ne suka cicciko da kwalla sai alokacin ya lura da Laila wadda taci gaba da kukanta.

Tazarce ne ajikinsa Dan haka ya cire ya bawa lailan yace tasa ta samosa a waje yana jiranta acikin taxi.

Hannu na rawa ta karba shi kuma ya fice.
Tana mikewa taga jini duk ya bata katifar da Sauri ta danne bakinta domin kar ihun data kwalla ya fita.

Durkushewa tayi a wajen ta kara bude Sabin babin kuka tana fadin ka cuceni ka lalatamin rayuwata bazan tana yafema Ba.

Sanda tasha kukanta sannan sako rigar ta dauko yageggen hijabinta tayi gyale dashi yayi da tayi kunzugu da rigarta tunda har lokacin jinin bai tsaya Ba, sannan ta fito.

Direct gidansu ya kaita har cikin daki yace tayi wanka ta gyara jikinta bata ya siyo mata magani sannan kar ta Fadawa kowa abinda ya faru tunda yanzu dare ne kar hankali ya tashi. Gone sai ya kaita wurin minal tunda inna ta tafi Maiduguri da zaliha acewarta Idan tabar kadunan zata Dan manta da mutuwar inyasi Daga nan ma sai a kara mata gyaran jiki.

Juyawa yayi zai fice cikin shesshekan kuka tace dama Nasan Cewa bazaka aminta dani Ba!me zakayi da second hand Wanda Dan shaye shaye ya karbe mata budurcinta? Kayi hakuri Nayi kuskure danace ina sonka.

Dawowa yayi ya riko hannunta cikin nashi yace Niko nakeda abinda zanyi dake,kuma batun budurcinki banida damuwa tunda bada kanki kika hada ba,karkisa damuwar Komai aranki domin irin soyaiyar danake miki koke bakimin irinta.

Tace Nasan kana fadan hakan ne Dan kana tausaya min😩 wallahi Idan haka sona gara ka fadamin ya fiyemin alkhairi. Yatsansa ya daura akan lebensa yace shhhh ! Karkice haka, kinsan kuma bans miki wasa in ana serious magana wallahi ina sonki koda wannan Abu bai sameki ba ni zan aureki balle da ya kasance akwai faruwar wannan lamarin ki Nayi an kara narka min dalman sonki a zuciyata kuma in kikaga ban aureki ba to Allah ne baisoba now give me that beautiful smile of yours kamin in tafi.

Small smile tayi masa hawaye ya tsiranyo, goge mata yayi yace Idan kika kara kuka Nayi fada dake tace na dena wallahi.

Shafa kanta yayi yace saina dawo.

🌹.......................

Abangaren su yazeed kuwa minal Adan tsorace da kuma jin haushin tabata da yazeed keyi ta gama gyara dakin zuwa taji gefensa ta tsaya fuskannan a hade tace gani.
Binta yayi da kallo tun Daga saka har kasa da tabbas kayan sun karbeta ba karya.
Hannunta ya riko zai zaunar da ita a cinyarsa aiko ta mike zinbir Kamar ta zauna akan kaya.

Tace wallahi bazan zaunaba karfi da yaji nifa na ganoka ya yazeed dinnan so kake ka miyar dani yar iska ko? Juyawa tayi zatabar dakin yazeed ya janyota luuuu sai gata akan faffadar kirjinsa.....

Anan zan dasa aya, ina godiya sosai da irin soyaiyar da kuke nunawa littafinnan

Ku sanarda Yan uwa da abokan arziki Wanda kuke ganin ya dace su karanta littafinnan.

DAN ALLAH KU SANAR DANI KO KUNAJIN DADIN LITTAFINNAN? SANNAN KUMA ME KUKESO NA KARA KO NA RAGE ACIKI?

Miss untichlobanty💕

3th December, 2019.
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 49*
Kokarin tashi ta fara yi amma yazeed ya riketa kyam kuka ta saka masa tace idan ma magana kakeson fadamin ba sai in zauna a gefenka ba.

Yanzu so kake in name layinmu Na da su talatu suce na gama cika baki yanzu nima na zama kalarsu. Wallahi Idan baba yaji ub*ana zaici da takalminsa.

Yazeed da yayi sakoko yana kallonta yace wayace miki za'a ce miki yar iska? aike kinyi aure kuma nine mijinki Dan haka babu Wanda zaice miki yar iskanci Dan na tabaki. Ki daina damun kanji kinji ? Turo baki tayi tace Gaskiya saina tambayi aunty fauziyya nasani ma ko wayo kakeson kamin? Idan na fada mata yadda mukayi sai inji me zata ce.

Cikin wayo da dabara yazeed ya kwatar da minal gaba daya a jikinshi ba tare da ta lura ba yace ke in banda abin ki kin tana ganin Inda ma'aurata suka fitarda sirrinsu? Ko bakisan Cewa manzon Allah SAW yace: Idan ma'aurata suka shiga daki sukayi wani Abu sannan suka fita waje Suna yadawa to Kamar akan titin sukayi"

Tace kwarai kuwa an fadi mana a islamiya Toh amma abinda ban ganeba shine Wai wani Abu ake nufi ?

Kallonta kawai yazeed yaje cike da mamaki yayinda itako duk hankalinta ya ta'allaka akan gemunsa da take wasa dashi. aransa yace Gaskiya ina da aiki babba a gabana wannan yarinyar fresh karatu take bukata.

Yace kinason in koya miki abin ne ta gyada kai tare da Cewa em.

Hannunsa yasa ya dago da ita ta zauna still tanakan cinyar tasa yayin da take Cewa "kai Gaskiya sajenka lauhi sai kace....." Ba ta karashe zancen ba sanadiyyar hade le'bensu da yazeed yayi guri daya kasa motsi minal tayi saboda gaba daya notinan jikinta sunyi sanyi, wani bakon al'amari aka bijiro mata dashi ba tare da ta Shirya ba.
Yazeed ko tsotsan lips dinta ya farayi kamin ya fara kokarin zura harshensa cikin bakinta amma ita dai tayi tsam tana jinsa yana abunsa janye bakinsa yayi Daga nata kamin yace lesson 1. Duk abinda na miki ki miyarmin kinji ta gyara kai a hankali yace good gwadamin yadda na miki yanzu.

Kwantar da kanta tayi a kirjinsa tace Gaskiya ni kunya nakeji!yace to aiko zanje na karo aure kuma irin zakiyya zan auto Wanda batajin kunya da Sauri ta dago da kanta tace Dan Allah kayi karka karo zanyi wallahi Idan ka karomin irinta na mutu da daya ma ya nakare? murmushi kawai yazzed yayi yace yi mugani to.

Gyara zamanta tayi sosai sannan ta rufe idonta a hankali ta daura lips dinta akan nashi Kamar yadda ya mata.
Wani irin yarrr sukaji dukansu biyu yayinda abin yazeed ya mike sosai. Tsotsa itama tayi sannan ta sake cikin mutuwan jiki yace kitabbatar kin rike Idan yaso zamu daura Daga step 2 in lesson 1,sannan ki dinga yin wanka ko wani lokaci kina saka kaya masu kyau shi zai kara bani kwarin guiwa wajen koyamiki karatun kinji tace um Dan ita jikinta yayi sanyi sosai.

Kwantawa ta kuma yi a jikinsa sannan ta dukunkune Kamar yar kulya babu abinda ke tashi sai numfashinsu.

Yazeed ne ya soma magana a hankali yace ji yadda kika lafe wa mutane a jiki ayi magana mice ke ba yar iska bace😜

Dukan kirjinsa tayi tace ai kaika miyar dani yar iska dama dance zama da madaukin kanwa shine kawo farin gashi. Yace to ya kikaji babin Yan iskan akwai dadi? Daga kai tayi akunyace tana murmushi Kamar gabuwa.

Dariya mai Dan Sauti kadan yazeed yayi yanajan kumatunta alamun tsokana yace rosy cheeks dina ta zama yar iska shagwabe fuska tayi tace banaso Dan Allah ya yazeed.
Yazeed yace Gaskiya ai nake fada gobe sai in kaiki amiki register ko ? Harararsa tayi ya mata gwaliyo. Yace amma ki daina cemin yaya ki samamin wani Suna fah.
Tace toh zanyi tunani ko ka cancanci hakan. Faking heart break yayi ya daura hannunsa a kirji,table baki minal tayi tace Wai me kakeson ka fadamin dazun? Yace kawo kunnanki kiji.
Matso da kunnan tayi sannan yace Abu uku ne kinaji ta gyada kai, yace so nake nace miki kinyi kyau sosai, sannan ki dena cilli da hijabinki ta ko ina ko kinason ki wulla akan Dan aljani ne?ta girgiza kai, kuma Idan kika kara cemin kazami to zan nuna miki kazantana Kingane ko? Tace eh yace good.

Tashi take kokarin yi zata fita yace ina zaki ? tace wutan abinci zan kashe in dibo nawa yunwa nakeji, yace me kika dafa?tace dambu ne.

Dan hade gira yayi yace dambu? me kuma wani dambu? Zaro ido waje tayi tace kana nufin bakasan dambu ba yace ban sanshi ba tace cabdi ! nikam bari inje inci abincina.

Yace ki zubo in gwada ci first time in history inji ya abincinnan naku na gargajiya yake ne?
Kallonasa take ido azazzare kamin abincin Dana Daga zakaci? Yq gyada mata kai kamin yace ko zakimin rowane? Girgiza kai tayi tace kaida abinka,Ai ban isa Ba. Shafa kanta yayi yace  duk abina naki ne kinji? Kai kawai ta Daga.

Mikewa tayi har ta iso bakin kofa yace inkinsan kinyi kazanta ki barshi.
Bubbuga kafa tayi tace Allah Idan nahadu da inna ko, wato yadani take a duniya ko?
Ince na dena kazantar? Ta karashe magana fuskarta Kamar zatayi kuka.

Yazeed yace au dama kinayin kazantar yanzu ne kika dena? Gaskiya Daga yau zan chaja miki Suna kin tashi Daga rosy cheeks kin Koma YAR KAZAME.
Kuka ta saka tace wallahi Allah ya yazeed karmka sakamin yar KAZAME banasoooo😟

Kashe mata ido daya yazeed yayi tareda gwaliyo yace yar KAZAME yi Sauri ki dauko mana abincina😜
Fita tayi tana kara volume din kukan shagwaban da takeyi. Koda ta isa kitchen zuzzuba abincin tayi sannan ta danna kararrawar kitchen Kamar yadda tala ta nuna mata.

Aiko baifi 2 mins ba saiga tala tace aunty Amarya sannu da aiki minal tace sannunku ga abinciku nan sai wannan na baba sule ya dawo ba tala tace eh ya dawo ina zai iya zama da madam zakiyya? Ai ko dawasa bazaiyi kuskurennan ba.

Murmushin yaje kawai tayi Dan ta tsani akawo mata zancen wani. Tace taka nace ba; Dan Allah Ku daina muzanta mutum abayan idonta babu kyau,wannan gulmace kuma kinacin namansa ne Idan yayi Abu ba daidai ba in zaki iya magana Kiyi in bazaki iyaba ki bishi da addu'a domin kema kina kuskure ya za kiji  Idan akayi miki hakan? Ki dena kinji.

Taka wacce jikinta yayi sanyi tace  na gode aunty kuma Insha Allah bazan kara aikata hakan ba Allah ya yafemana zunubanmu minal tace Ameen.

Abincinsu ta dauko da plate biyu na ita da yazeed tareda kunun aya mai sanyi wadda tayi tun da safeta daura akan katon flate sannan ta nufi bangarensa.
Ajiye tray din tayi a parlon sa sannan ta Shiga ciki domin ta kirashi yanda ta barshi haka ta sameshi tace na kawo abincin yana parlour.

Da Hannu ya mata alamun tazo karasawa kusa dashi tayi ya miko mata Hannu alamun ta dagashi.

Gira daya ta Daga irin yadda take mata alamun Idan naki fa? Yace 'yar kazame ai baki isaba sai kin dagni duk lomar dakikeyi karkicemin ta banza ce.

Yayi hakanne dan ya tsokaneta amma ga mamakinsa yaga tasa hannunta cikin nashi sai gashi ya mike.
Zaro ido yayi abinda bai taba yiba  hakan yasa wani sihirtaccen kyawunsa ya fito cike da mamaki ya kamo dantsen hannunsa ya na lagutsawa itako ji take Kamar ana mata cakulkuli Dan haka ta soma dariya tana kokarin ta kwace.

Cikin sa'a ta kwace hannunta yazeed ya biyota yana fadin ai baki isa ba, ina kika samosa karfinnan yar kazame?kode namiji na aura ?

Haka suka dinga kewaye dakin Suna dariya kamin Daga karshe yazeed ya samu ya cafkota. Ga mamakinsa kawai sai ta rungumesa sanda ya dauki Yan sakanni ya dawo Daga shock din daya Shiga kamin shima ya kewaya hannunsa a kwankwasonta.

Babu abinda ke tashi a dakin sai sautin nufashinsu kamin minal ta datse shirun ta hangar Cewa nagode.
Yazeed yace namefa tace na Komai ma.
Shima yace nima na gode ta.turo baki tace kwaikwayona kakeyi?ya girgiza kai tace to kaima name yace nima na Komai dukanshi tayi a kirji sannan ta falfala a guje tana fadin aradu kwaikwaya na kayi.

Murmushi yayi kamin ya fito parlourn ya sameta har ta zuba plate daya zata zuba wani yayi saurin riko hannunta yace me kike shirin yi?tace abinci nake zubawa mana yace a wuri zakisa mana ta zaro ido a karo na 5 tace kana nufin tare zamuchi ? Ya Daga kai tace a ah ka......

Bata karasa Ba sakamakon pecking lips dinta da yazeed yayi yace banasin korafi zuba mana.

Zubawa tayi ta cika plate din harda tozo yazeed yace Wai mu bawa zamuci abincin ne ?tace mu biyu mana yace shine kika zuba dayawa haka sai kace mu 5 ne?
Murmushi kawai tayi ta rufe flask din .
Dauko plate din yazeed yayi yakai kan carpet yayinda yaje riko da dayan hannunta.

Masu Neman update gashinan an muku

Miss untichlobanty💕

4th December, 2019
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by miss untichlobanty🌹

*CHAPTER 50*

Janyota yayi har gaban abincin ya zaunar da ita sannan shima ya zauna itakam kallonsa kawai takeyi.
Idan tace ta taba tunanin yazeed zai zama haka to karya takeyi. Da bayan aurenta da sati daya wani ya fada mata Cewa yazeed zai zama haka da babu dalilin dazai hanata jibgarsa.

Shiko yazeed ganin ta tsareshi da ido yasa ya hura mata iska a fuska yace yar kazame ya akayi ne?ko duk Kyan nawa ne yasa ki yin muhawara da zuciyarki?

Bata rai tayi tace duk Wanda yacema kanada kyau to ya cuceka, yace zama ki fadi Gaskiya 'Yan mata.

Plate din data rufo abincin ya bude aiko atake yaji wani irin kamshi ta doki salansar hancinsa hakan yayi sanadiyar cikinsa ta bada wani kqra kuuuuu.

Minal ne ta kyalkyale da dariya yazeed kuma ya turo baki yadda take masa yace yar kazame banaso! Gwaliyo tamai tace nima banaso.

Spoon ya dauka ya dibi loma daya ya fara taunawa wth a straight face. Minal da ta nutsu tana jira taga reaction taga ya yatsine fuska. Take idonta ya cicciko da kwalla yazeed ko harararta yayi cikinbdaga murya yace me wannan kika Fadawa mutane.
Take hawayen dake makale a idonta ya gangaro tace kayi hakuri ni wal.........
Hannu ya Daga mata yace karki wani bani hakuri ya zaki Fadawa mutane abinci Kamar abincin Yan aljanna?so kuke na suma?

Tsayawa kallonsa minal tayi baki a bude yayinda ya sheke da dariya sanda yayi mai isarsa sannan.

Yasa Hannu ya rude mata bakin yana Cewa kar kuda ya Shiga bakinki,maganin mai cemin banida kyau.
Kicin kicin tayi da ido kamin takai masa naushi ya fara tarewa yana Cewa haba yar kazame na yi hakuri,haba yar kyakkyawa.

Hararansa tayi tace kaci sa'a.
Hannu tasa ta dumbuzo loma,yazeed Wanda ke shirin fauna lomarsa ta biyu ya kware a take saboda firgicin katan loman dayaga minal takai baki sannu tace masa sannan ta bashi ruwa yasha ta dawo ta gefensa tana shafa bayansa tunda dazu fuskantar juna suke.

Bayan numfashinsa ya dawo daidai yace yar kazame kicemin bana gani daidai tace da akayi me fa yace da gaske duk wannan lomar bakinki kika sa ? Ta Daga kai yace kafci ai wannan yakai inyi loma Biyar dashi. Tya kiga miko mata cokali yayi sannan shima ya dauka.

Spoon din yasa ya Dino daidai cinsa wani Dan Nasan a baking cokali yakai bakinsa yace lesson number 2, haka kakeson ki dinga cin abinci tace kafci wannan kawai kace na mutu da yunwa Gaskiya saide in gwada maka wani Wanda yafi wannan daina gani ko yayi.
Yace gwada mu gani. Cokalin ta cika sannan yakai baki yace atleast gwara wannan.
Tace to kauna lesson 1 dazan koyama shine ka dinga cin abinci da yawa bude bakinka ta fadi hakan tana ciko cokali, yace ke wannan yamin yawa ai so like in mutu?tace Allah sai kaci Idan Ba haka Ba kuma in daina kulaka. Masa bude bakinka kamin in zaneka ta fadi hakan Kamar da Dan shekara Bihar take magana.

Yazeed badan yaso Ba haka ya bude bakinka ta dinga dura masa itama tanaci sanda suka cinye tas.
Yazeed ji take Kamar an kika sa a wurin saboda irin cikar da cikinsa tayi.

Yace Inda in kara cin wani abinci sai bayan kwana 3 ya fadi hakan yana Dan nishi.
Minal ko dariya tayi alamun kana ruwa sannan tace ai bata in kara maka labari tuwo miyan taushe zamuci anjima kallonta yayi Adan tsorace yace menene kuma wannan tace zaka ganshi.

Yace to kije ki ajiye mana wannan abun anjima sai musha tace Ba sunansa abun Ba sunanshi kunun aya yace to kunun aya.

Yace yauwa har na kusa in manta duk dare zamu dinga yin karatu dake zan koya mini karatu da rubutu kamin ki koma makaranta,ko bakyaso? Washe baki tayi tace inaso mana Nasan baba zaiji dadi sosai in yaji wannan labari kuma Nayi alkawarin in maida hankali into karatu babu wasa yace good girl give me five ta miko masa Hannu sannan suka tafa Suna masu fashewa da dariya.

Mikewa tayi yace don't forget after each lesson sai kin min tausana fa karki dauka na manta ne and also Daga yau karki kara yin wani aiki kinji kawai ki dinga share part dina sai ki mana abinci. Murmushi tayi tace na gode sannan taje ta ajiye musu jug din kunun ayan fridge din falonsa,tunda tasha dazu da safe shiyasa bata wani damu dasha yanzuba.

Bayan ta dawo ta zauna yace toh ni zan Dan fita kinsan Jennifer ce tasa mana poison acikin cappuccino Dan haka dole in tuhumeta Inji Wanda ya sata.

Minal tace ikon Allah mutum mugun ice,Wanda ka yarda dashi shine zai sokeka a baya Allah ka rabamu ka kuma karemu Daga sharrin makiya. Yazeed yace Ameen sannan ya mike domin ya shirya koda ya shirya cikin khakinsa yayi mugun kyau ya fito a parlourn ya tadda ita tana kallon TV yace Toh yar kazame ni na wuce tace to sai ka dawo Allah ya bada sa'a.
Yace Ameen Ba rakiya ne?tace muje Toh in rakaka.

Har bakinka main kofa ta rakashi zata rude kofa yace baki jiba tace um? Yace Daga yau in zan fita zaki dinga min bye bye hug and peck kinji ?tace Nasan me hug din amma me kuma peck?
Pecking lips dinga yayi yace shine peck. Hannunsa ya ware ta rungumesa tanata Washe baki itakam yanzu babu abinda zatayi  sai godiya ga Allah Dan rayuwa ta ma ta dadi Alhamdulillah.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Da fatan ka yi aikinka daidai Dan banason kuskure irin na wannan banziyar arniyar Jennifer, nasa boka cuku cuku ya kaita gidanne dab tayi min aiki amma saboda rashin kwakwalwarta gashi an kamata.

Ta dayan Abangaren wayan ne akace ma babu wata matsala Nayi Komai daidai yanzu haka nabar gidan
Tace good I will transfer your balance yace thank you ma.

Datse kiran tayi sannan ta kara dialling wani number ringing biyu aka dauka tare da fadin shedaniya uwar shedanu,muguwa uwar mugu,dakalin majina a hauki a zame kihau uban mutum ki zauna daidai. Tawa ni kadai har abada Umarninki shine farin cikina.

Murmushi tayi tace daina Sakai kenan duk yadda raina ya baci to Dana kiraka nake wartsakewa.

Ya ake ciki da batun boka cuku cukun? Yace masoyiya yanzu nabar wurinsa kuma yace an gama Jennifer ko za'a kashe kowa dake numfashi bazata iya tuna Cewa ke kika sata aikin Ba balle ta fada tace good to me yaje bukata.

Saurayin yace yana bukatar jinin bakinka Kare da raguna uku ma aljanunsa naman kuma a soye ta tayi yaji sosai sai ayi dambu da naman Karen wannan nashine tace okay zan turo maka 500k sai kayi duk abunda ake bukata. Yace an gama my love tace to sweetheart sai anjima.

Wani number ta kuma dialling sannan tace da fatan kaga balance dinka yace eh na gani tace yauwa Gaskiya aikin yayi kyau boutiques din sun none kurmus shiyasa ma na kara maka akai. Sai kayi kokari duk kayan da kuka kwashen Ku kukai min warehouse din.
Yace ai nakai tun jiya tace excellent shiyasa nakeson aiki dakai baka disappointing dina. Yace na gode ma. Datse kirar tayi tana murmushin rashin imani tace just wait and see daina rushed rayuwarku gaba daya especially yazeed da zakiyya Dan kune salsalan matsalata.

🌹............

Koda yazeed ya Shiga mota domin su wuce su hadu da tawagar convoy dinsu,lukman yace mutumina karka dauka ban gani ba. Yazeed yace ni kuma Allah ya sakamin tsanan Dan sa ido ba. Lukman yace to ai ba saka ido bane tunda ina wajen abin ya faru karara a vaiyane yazeed yace kaika jiyota ai shiyslasa tunda ban yarda a Shigo min compound ko securities Suna can nesa.

Amma Gaskiya mutumi na gode domin kuwa shawar da ka bani ita na dauka kuma yanzu haka in nace babu Wanda ya kaini jin dadi banyi karya ba lukman ya sheke da dariya yace anyi abin kenan?yazeed yace kaji matsalata Sakai to babu abinda ya faru. Lukman yace zama faru ai.
Gidan da aka ajiye Jennifer suka shiga. Gaba daya fuskanta ya kukkumbura ba'a ma iya gane kamarta.

Thank you for supporting me!

Don't forget to share and comment

GOOD NIGHT

Miss untichlobanty💕

4th December, 2019.

6 - CHAPTER 51-60
[1/11, 2:29 AM] Mzz_Untichlobanty💞: *🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆*

🌹by mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 51*

Tana ganin YAZEED ta kara fashewa da kuka tana oga ka temakamin kayi min rai wani soja ne ya naushi bakinta. Atake hakori daya ya balle ya fado aiko jini ma yace baza'a barni a baya ba.

Yazeed ne yace let go of her if she is ready to talk. daya Daga cikin sojoji Biyar dinne ya falla mata wani lafiyaiyan mari yace zaki yi magana ? Ta Daga kai da Sauri tana Fiki Fiki da ido Kamar yar wuta Dan haka suka suncota.
Da gudu ta karaso gaban YAZEED ta rike kafarsa cikin hausanta Mara kyau tace sir Dan Allah kayimin rai karsu kasheni ka yafemin.
Hannunta yazeed ya yarbe Daga kafarsa sannan ya take ya murje ya muttsika har sanda jini ya fita yayinda Jenifer ke ihu tana fadin jusus!lord have Marcy !my hand!my hand!my hand ooo!

Alamu yazeed yayi da akawo masa kujera still kafarsa nakan hannunta amma baya murjewa.
Zama yayi sannan ya kamo bakinta ya matse hawaye ta somayi sai ka ganta abin tausayi yazeed yace wa ya sa ki zubamin poison a cikin cappuccino girgiza kai ta fara yazeed yadan kara danna kafarsa akan hannunsa hakan yasa tace waiyo zan fada!zan fada! Yazeed yace ina jinki tace madam.............
Wani abune taji yazo ya sari kanta a take ta rike kamin ta kwala ihu kaina!. Murmushi yazeed yayi ya table baki yace na hadu da criminals da suka Fiki so don't fool around fada min!
Ya fadi haka da kakkausar murya.
Girgiza kai ta fara tace oga na manta na kasa tuna Waye I promise yanzu naji wani Abu ya sari kaina daganan kuma naji na manta wacece ita.
Yazeed yace macene kenan ?tace yes sir yace kai ayo kuyita dukanta harsai ta tuna.
Suko abinnema ya samu nan suka juya bayan bindiga suka dinga jibgar ta Kamar ba mutum bane.

Itako sai ihu take tana fadin I promise you sir na manta I swear on my life na manta!tun tana iya magana har kaji shiru can shu'aibu yaga Kamar ta dena motsi yace Gaskiya sir wannan matar tanada taurin kai Dan koda namiji ne da yanzu yayi magana Idan ba haka ba kuma to ta

Please Login or Register in order to submit comment