Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shirrin kasan ƙarfe goma ne za'a gudanar da zaman court nin . "


































Murmurshi yayi " okay dear take care , nima zan fita sai mun haɗu a court nin " Yana fittowa yaci karo da Hajiya Amina ( Asalin matar sa Uwar Ajeeb Da Najeeba ).




















" Mai Martaba kaji tsron Allah ka gayyamin gaskiya ina yarona Ajeeb nagaji da tatsuniya da kaki min ace haryau ba' asan inda yaki ba tunda kace zaka turasa ƙasar waje daga nan abu ya chutura ace an nemi sa an rasa ". ?




















" Haba Amina wai me kikison da nine ke kanki ," sassauta murya yaye ya matso kusa da ita tunuwa da part na Umma yaki " kinsan cewa Ajeeb ɗa na ne taya zan zauna ace bana neman sa bayan shine Magaji na a yanzu haka ma ai runduna daban daban na baza duk inda akasan yana zuwa ko passport nasa biza sa duk an baza a sirrance don banson ƴan jaridu susan abinda yaki guduna sanin kanki ne ido na kanmu kota ina ƙirirs a kijira kawai ke kwantar da hankalin ke mu tafe court nan yanzu mu wargaza aniyar masuson ganin bayan mu ......"























A tare suka fita daga part nin Jingina da bango yayi jin abinda uncle Ali yagama faɗa ciki da razana Najeeb yakama zuwa ɗakin Umma ko mai ya tuna oho naushin iska yayi da firzar da iska daga bakin sa, ajiyar zuciya ya sauki ganin har Ummu ta fitta da Sameera dake kwantar da murya.




















" Please Umma nima zanbiki Please inason zuwa " haba Sameera meyasa watarana bakijin magana bakiga halin da muki ciki ba still kice zaki bimmu court ba gun " hararra Najeeb ya buga mata haɗi da giggitacen ƙara da gudu ta shiga ɗakin da aka sauke Nadrah don yafe kusa da ita ,.


















************COURT************















Bayan gabatarwa da wasu abubuwa da yakamata court tayi anan aka jira laifuffukan da ake tuhumar sarkin Gizo Kano wato Aliyu Abdallah Lashkar inda ake tuhumar sa da saffarar ƙwaiyoyyi da tuhumar kissa da ake wanzarwar ba gaggauta wa cikin masarautar da yaki mulki duk da cewa anyi ta magana.























Amma kullum abubuwan laifin ƙara wanzuwar yakiye ,sosai manyan manyan lawyer da ya ɗauka suka gurza basirar su da bajintar su ta hanyar gogge duk wata hujja ko kuma makaman da court zata kama , bayan dogon typing sai Alƙali ya rubbuta ya umarci hukumar kare hakkin mata da magana idan suna da abin cewa.











Cikin nitsuwa wata kyakyawar yarinya da bazata haura 25 ba ta miƙe tsaye cikin shigar uniform na law gyara glass na idon ta tayi .

















" My name is Suhaima Salihu ( DUHU CIKIN HASKE). nan ta kwaro dukkan bayanai na tabbatar da cin zarafin ƴaƴa mata ta hanyar fyad'i daga bisani kuma a kashe su.











Wanda yaja hankalin mutane da dama har takaiga an fara surutu da hayaniya, duk dakatar dasu akayi ta hanyar buga gudumar court bayan wani lokaci alƙali ya kamalla rubuce rubuce sa ya ɗaura da cewa..




























" Hukumar Goverment mun saurari ƙorafin ku kuma ƙorrafi ya amsu daga yau zuwa sati ɗaya ko dawo cikin court domin gabatar da hujjojin ku na cewa Lallai Sarkin Gizo wato Aliyu Abdallah Lashkar kuna tuhumar sa da saffarar ƙwaiyoyyi ta hanyar da bai dace ba ana shigo da haramtattu kaya a ƙasar mu" ......
















" Hukumar kare hakkin ɗan adam da qunƙiyar kare hakkin mata , ku gabatar da hujjojin ku nan da kwana goma sha huɗu, sanan wanan court mai albarka ta amshi ƙorafin ku don haka mun ƙarɓa sarauta daga hanun tsohon sarki da ake tuhuma Goverment zata chigaba da kula da masarautar AHLIN LASHKHAR har sai an gabatar da hujjojin da shaidu, "















" Daga ƙarshe ɓangaren da ake tuhuma zaku iya ƙarfaffa guiwarku ta hanyar kawo hujjojin da za'a tabbatar baku da sa hannu cikin zargin da ake tuhuma ku dashi ..











" COURT!!!!!!!!! ".







Ciki da tashin hankali duk suka fitoo aka tsaya kallo kallo ga ƴan jaridu dake sonjin ta bakin Tsohon sarki da court ta ƙarɓi sarautar sa a rana ɗaya , Barrister Suhaima ta fito ta nufi inda motar ta taki hango Unlce Ali taye yana aika mata da sakon " zanci Ubanku ne yarinya " tayi mishi murmurshi da ya gaza gano inda ta nufa duk cikin masarautar su suka nufa sai dai abin mammaki ƴan sanda ne kewaye da cikin masarautar ba yanda ya iya sai ya kuma cikin AHLIN LASHKHAR .





















" Haba Aunty Ajeebah wai meyasa har yanzu bakisayi ne ya zakice na taho gunki alhali masaurauta mu ta rikice bazan iya nisa da su Umma da Unlce ba gaskiya gabaɗaya a ɗimauce suki fa "











" Lallai ma Najeeb yanzu har zan maka magana kai tsaye kace min bazaiyuba to dole kazo a yau kayi gaggawar yankan tiket a yau zuwa gobe ka tahu ba shawara ba ce umarni ne " datse kirar yayi ya kashe wayar sa switch off cikin tashin hankali ya kama kansa da yaki mugun sarawa " innalillahi wa ina iallhin raji'oun "























****************AMERICA****************





" Kagani ko Honey katse kirar yayi ya kashe wayar sa wai yaushe Najeeb zai gani rayuwar sa na cikin hatsari ne musamman yanzu ga Ajeeb ma anyi garkuwa dashi ana neman sa innalillahi wa ina iallhin raji'oun ".














" Sorry dear ke tayashi da adu'a kinsan zuciya ɗaya yaki dashi basira matsala da kowa gani yakiye kowa nasani you know akaiw irrin mutanen but " katse shi da cewa " no dear Ina buƙatar ɗan uwa na kota halin ya ne bazan bare su cutar dashi ba , ni nasan bazai cutar da Umma ba saboda yana sonta .'"











Tana gama magana ta miƙi tabar ɗakin PART nata tashiga Inda taga su Asim na homework nasu ɗakin ta tashiga nan ta rufe ta buɗe box nata ta zaro ƙaramar wayar ta toilet ta shiga ta danna kira bugu ɗaya aka ɗauka ,











" Nadrah I need your help aikin ke bai ƙare ba come back and save my brother ina buƙatar ganin sa for now " .................


































AHLIN LASHKHAR BY NARNAH ƘANWAR SOJA 🖋️💞🌹










https://chat.whatsapp.com/GlC9QmyuWMG7PmC1vhGp4I



💎AHALIN LASHKHAR 🏠
* NA*


NARNAH ƘANWAR SOJA 🖋️










Facebook page : Narnah ƙanwar soja
Wattsppt numb: 08101235739


















🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
**
*Alk'alaminmu 'yancinmu*









PAGE 25 ➡️ 26



❤اللَّهُمَّ عَافِـني فِي بَدَنِي، اللَّهُمَّ عَافِـنِي فِي سَمْعِي، اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَصَرِي، لَا إِلَهَ إلاَّ أَنْتَ. اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ مِنَ الْكُفْر، وَالفَقْرِ، وَأَعُوذُبِكَ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ ، لَا إلَهَ إلاَّ أَنْتَ🥺🙏









" Nadrah i need your help aikin ke bai ƙare ba come back and save my brother ina buƙatar ganin sa for now " .................














Katse kirar tayi da yatsu biyu ta nuna Ajeeb dake gabanta cikin yanayi mara misaltawa da ƙyar ya buɗe idonsa da suka lutsa ya kumbura saboda baƙar wahala ya motsa bakinsa yayi da ya faffashe yana kallon ta .




















" Ke taimakawa rayuwa ta Teema na rantse miki sharrin shaiɗan ne yasa na aikata hakan anman tun asali ne ba haka nake ba ,"











Gyara zama taye daga kujerar data zauna " Ajeeb kinan abu ɗaya zakayi ka tsira dole ka bayyana gaskiya ka kuma shaidawa mutane lallai kaine kake lallata da yaran bayi a cikin masarautar ku sanan mahaifin ka nasa a kashe su saboda wasu banzan dalilai na sa".




















Da hannu taye musu alama wasu gardawa biyu suka matso kusa da ita " an shirya camera ne " ? " Yes Madam" , ku rufe masa baki tunda har yanzu bazai amsar laifin saba yakamata Uballen ( mahaifin ) sa yaga vedio sa kuma mu tabbatar masa lallai ya miƙa kansa ga hukuma " okay Madam ".





















Rufe fuskarta taye ta zaro ƙaramar wuƙa ta nufusa gadan gadan, ihu a ciki ciki ya fara yana motsawa " one two three go" wu'kar ta samai dai dai ƙirjin sa tasa a hankali tafara zagayawa dashi har ta kaimai yanka ta datsa igiyar daki bakin sa ihu ƙarfafa ya buga wanda ya karaɗi gidan gaba d'aya saboda azabbabin zafin dayakije a jikin sa , wasu maganganun tafara nan da nan ya hargitse ɗakin a ka jefasa cikin wane ɗaki , ta katse vedio..


















************NAJEEB ****************





A hargitse ya fito ya shiga motar sa hankalin sa duk a tashe " tsinaniyan yarinyar chan ne duk ita ce sillar komai na rantse dole nabi a sannu a sannu domin binchiko gaskiya akan wanan al'amarin tabbas akaiw wanda ya ɓoya bayan Unlce Ali ne ne nasan Uncle bazai aikata hakan ba ko ɗazun ma da yayi magana kawai hankalin sa baya ganganr jikin sane saboda tashin hankali biyu ga court ga ɓatar Yayya Ajeeb ,























Wasu manyan manyan motoci ne suka sashi a tsakiya wani mugun birki yaja ya tsaya chakk yana fitowa ciki da masifa aka buga mai allura a ta bayan sa nan ya faɗi a jikin wane gardin kama hannun sa sukaye suka shi a cikin wane 406 daga shi sai driver da wane gardin suka kama hanya .....

















AHLIN LASHKHAR gaba-d'aya ta gama rikecewa ga shi cikin mutane abun ya faru duk dangin an hallara an kuma zuba jami'an tsaron ta kowace hanyar ana bincike akan lamarin .

















Basu tsaya a ko'ina ba sai a wane kurkugun ƙaramin gida a cikin gidajen mutane kasancewar dare ne kowa na harkar gaban sa wasu kuma duk sun shiga gidajen su ......

















Kwantar dashe akayi akan ƙaramin gado aka ɗaure hanun sa cikin an'kwa kasancewar yana tashan barchi kwana ɗaya baisan inda kansa yaki ba , da murmurshi a fuskar ta tagansa taja masa bargo.














Duk tashin hankali da dangin AHLIN LASHKHAR suka shiga basukai Umma ba wacce ta tara malamai da almajirai tunda abin ya faru har aka kwana ana karatun Alqur'ani mai girma sai abinci da sa haddimai nata girke girke ana sadaka a duk wane tsangaya ana addu'ar Allah Ya fito da yaran da akaye garguwa dasu kuma Allah ya bayyana gaskiya AHLIN LASHKHAR ta fitta daga cikin kokkonto.

















WASHE GARI








A hankali ya buɗe idon sa da yayi masa nauyi yana buɗe su kaff ta haska masa huto kallon ta yaye da kyau "Teema Abdullahi kicce " murmurshi tayi ta tura sent ta ajiye wayarta murmurshi tayi wanda ya ƙara kuffalar dashi a hanzarce zai miƙi ganin an ɗaure hannun sa ya fara ƙoƙarin ganin ya tashe " AM SORRY ba da niyya nayi hakan ba but i know kna da mugun taurin kai bazaka yarda dane cikin sauki ba , but i want you to know that you are save now. "











Zaiye magana aka fara kirar layin ta duba mai kirar taye da sauri ta ƙame a tsaye ta sarra mai kamar yana gabanta "Okay sir am on my way ".






















AHLIN LASHKHAR BY NARNAH ƘANWAR SOJA 🖋️💞🌹




https://chat.whatsapp.com/GlC9QmyuWMG7PmC1vhGp4I



💎AHALIN LASHKHAR 🏠
* NA*


NARNAH ƘANWAR SOJA 🖋️










Facebook page : Narnah ƙanwar soja
Wattsppt numb: 08101235739


















🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
**
*Alk'alaminmu 'yancinmu*









PAGE 27 ➡️ 28
SECOND TO THE LAST PAGE 🔥





❤اللَّهُمَّ عَافِـني فِي بَدَنِي، اللَّهُمَّ عَافِـنِي فِي سَمْعِي، اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَصَرِي، لَا إِلَهَ إلاَّ أَنْتَ. اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ مِنَ الْكُفْر، وَالفَقْرِ، وَأَعُوذُبِكَ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ ، لَا إلَهَ إلاَّ أَنْتَ🥺🙏







SADAUKARWA 🥰





HAPPY BIRTHDAY 🎂 DOCTOR TEEMAH WANNAN PAGE NAKI NE MORE MORE HEALTHY AND MONEY DEAR ENJOY YOUR DAY.









Godiya na musamman ga Abokin nishad'i YouTube channel ,Allah taimaka ya 'kara basira da kaifin murya ga duk mai son sauraran audio book na zai iya ziyartar channel nashi ABOKIN NISHAD'I 1tv ,kar ku manta like and subscribe thank you.










COURT !!!








Kowa ya mayar da kansa inda wani qatuwar tv da aka fara haskawa yaki inda mutane sun ƙara chi chirindo fiyyeda na farko ga ƴan jaridu na neman labaru ido rufe.

















A hankali vedio ya fara tafiya kamar yadda tsarinsa yaki sai ga Teema Abdullahi a rana ta biyu tana ɗaukan maganganu da akaye tsakanin mutum huɗu babo wanda bai shaida muryar su ba sai mutumin da baya cikin makasuntar su .














Hankalin su bai gama tashi ba sai da aka hasko wane ɗauka abinda aka binne tsawon shekaru goma sha bakwai sai gashi a cikin mintuna da bai gaza goma ba ya fito a bainar jama'a inda har wasu sun miƙi tsaye domin tabbatar da zargin su akan anya kuwa mai martaba Unlce Ali ne ya aikata hakan kuma gashi a vedio ba editing ba da sautin muryar sa wacce tafito tamkar yana maganar a gidan Radio to lallai idan haka ne clap for the man that make this vedio......












********************************



FLASH BACK 17 YEAR'S BACK.












" Ɗan uwa Allah ƙara nisan kwana da dogon zango mai martaba gaskiya ne a gani na wanan hukunci da zaka ɗauka tayi tsauri dewa Allah gaffarta ma banyi maganar nan don na ma katsalanda akan sarauta ka ba but a duba lamarin " .











Shugaban fada ne ya haɗa ido da Unlce Ali ya ɗaura da cewa " gaskiya ne mai martaba Ali yayi gaskiya akan wanan hukunci ka duba lamarin mai gida tunda ba'a san wanda yaki wanan saffarar ƙwaiyoyyi cikin AHLIN LASHKHAR a shigo dashi garin GIZO ba to kar a kashe wanan mutane guda biyu kamar yanda kace a barsu a cikin korkokon sirrin har sai mun gama binciken ko waziri ?" .




















Murmurshi mai martaba yayi wanda yasa kyaun sa fitowa na musamman " Shugaban fada , waziri da kai ƙanina kaikam da babo Ruwan ka akan lamarin sarauta bansan me yafaru ba amman ba komai ku kuma inason ko sanar da hukuncin Shari'a wanda na zantar bana magana biyu don haka ba'a damƙasu ga hukuma ba har sai an kashe su hakan zaisa wanda suki aikin su su harzuƙa da taimakon Allah mu kuma muyi raff dasu ku tashe kubani wuri dare yayi yanzu ."
































" Allah gaffarta maka , Allah ya hucce zuciyar ka , Allah yaja tsawon kwana , mun amince zamuyi sanarwar hakan mu kwana lafiya" , haka suka kama hanyar fita murmurshi Sarki Abdullahi yayi ya ɗaga sautin sa wanda zaisa sujisa " ɗan uwa ina bukatar ka " .














Wani irrin sauti cikin sa ya bayar cikin wayacewa irrin ta ƴan boko kuma goggaƙun duniya ya juyo da mummunar murmurshi sa wanda ta tsaya chakk akan leɓɓen sa bata kai ga zuciyar sa ba . " na'am ya mai girma mai martaba ,"





























Miƙewa sarki Abdullahi yayi ya zare rawanin sa da cewa " Haba ɗan uwa yaushe rabon ka da shiga AHLIN LASHKHAR sai gashi yau yau ka shigo bazata baka saba min katsalanda a hukunci dana yanki ba kasancewa baka son abubuwan gidan sarauta kafi gani harkar kasuwanci " .























Cikin kunya ya sunkuyar dakai "am daman daman ai ma abin daman " da sauri mai martaba ya dakatar dashi '" zargi na ya tabbata kana ɗaya daga cikin wanda suki mana saffarar ƙwaiyoyyi cikin wannan ƙasar namu mai albarka you know what tunda naganka kazo garin nan a hanzarce kuma kasa baki da a saki mutanen nan nasan cewa lallai akaiw wane ɓangaren da kaki ciki,











Inaso a tashi hankalin wanda yaki aikata hakan idan yasan mutanen sa biyu suna hanuna ta hanyar kashesu ne zanga idon kowa a kaina sai dai Aliyu kaman ta abu ɗaya farkon Harafin sunan mu ɗaya ne anman bazaka nunamin wayo ko dabara ba yanda nafika da shekaru kaɗan a duniya to kasani na rigaka shan iskar ta nasanta tun kafin zuwan cikin ka a gun mahaifiyar ka .














Zan gayamma abu ɗaya yazama last warning kadaina wanan saffarar ƙwaiyoyyi idan ma sarauta kakiso zan iya baka idan jari ko matsayin kakiso a cikin Company mu AHLIN LASHKHAR industry zan ƙara ma anman kadaina wanan banzar tunanin ka da kakiye da wanan aikin ne wallahi bansan ma yaushe kafarata ba ."














Haka Unlce Ali ya sunkuyar dakai ciki da borin kunya ganin ashe ganin sa kawai akiye sarki yasan komai a kansa a hankali ya taki gaban mai martaba ya durgusa da ƙasƙantar da muryar sa wanda hakan yawa mai martaba daɗi koba komai yana da kyakkyawar fahimta tsakanin sa da ɗan uwan sa rungume juna sukayi yana bashi haƙuri .







1 Comments On AHLIN LASHKHAR
avatar
abasu-kala

11 months ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment