Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

 [27/03, 17:48] Elhajj

MA'AIKACIYAR
GOMNATI


1


By
Asmabaffa


Masoyana naga sakonku sosai na yabo da jinjina kan novel dina na maraicin rahma,ban San Kalmar da zanyi amfani da ita ba wajen gode muku,na gode kwarai Allah ya bar kauna,Allah ya biya muku dukkanin bukatunku na alkhairi.




LONDON na nufa a 80 jirgi ya saukeni da kyar na hada kudin zuwa ma sabo da jin dadinku readers bazan bari ya wuce Ku ba,wani gida Wanda ya amsa sunansa gida ko a kasar ba duk gida ba,ko ina ya tsaru wani handsome na hango narke a 3seater yana latsa wata dankareriyar iPad ga wata computer new design itama iPad a gefe yana ta aiki ciki hade da danna waya,tun daga yatsunsa nasan kudi da Hutu hade da jin dadi sun ratsashi,don guy karshene wajen haduwa da kyau OMAR MOHD OMAR kenan dan kimanin 35yrs sunan kakansa yaci.Baban sa mohd Omar Ibrahim shahararren dan boko ne kuma dan kasuwa kuma dan siyasa,shi kadai tilo iyayensa suka Haifa kafin rasuwarsu,yan asalin jahar gombe ne,fulanin gombe,babansa ya tsaya masa yayi karatu kafin rasuwarsa,yanzu kam mohd Omar sai yan uwa da suke gombe kawai suka rage masa,yana musu alheri da ziyartarsu, dattijon kirki yayi aikin gomnati kala kala,ya rike mukamai da dama ta fannin siyasa,yayi mulkin siyasa state rep sau daya,house of rep a abuja har sau uku,senator sau daya,ya rike minister sau 2,yanzu haka ambassador ne na Nigeria a Russia.ga kamfanoni da yawa,harkar business iri iri,ya Tara dukiya kadarori barkatai,a takaice dai hamshakin me kudine na gasken gaske dake zaune a abuja birnin tarayya.yana da mata biyu hajia amina itace uwar gida tana da yara uku dan Allah bai bata haihuwa da yawa ba,Omar shine na farko,sai abdullah dan 18yrs sai autarta suleim yar9yrs.matarsa ta biyu hajia rahina yaranta duk matane guda 5 sadiya 27yrs,Aisha 25yrs,zainab 23yrs,naja 21yrs sajida 15yrs autarta.hajiya amina yar kauyen gombe ce,dan haka batayi karatu ba iyakacinta secondary shima bayan mohd Omar ibrahim ya aureta ya sata tayi.ita bata aiki bata zuwa ko ina ta rike yaranta ta basu tarbiya tare da mijinta,

Rahina kuwa da yaranta uku manya duk suna aikin gomnati sunyi degree,kullum sai iyayi a hau mota fuuuuuuu ko wacce ta tafi aiki,in salary yazo ai ta gasa da juna. Baffa yayi yayi su fito da miji tunda sunyi degree amma sunki,shi yasa gidan ya Tara mata rida rida.gashi na bangaren amina sune sukafi kowa kyau,musamman Omar,shi yasa suka kara tsanarshi.

Basa zaman lfy ko kadan, dan hajiya rahina bata kaunar hajia amina da yaranta,dan amina tana da maza ita bata dasu,ganinta zata fita cin gado,gashi alhaji mohd yafi son amina da yaranta musamman Omar,da wannan yasa rahina dagewa lallai yaranta mata baza suyi aure ba sai ko wacce tayi degree tana aikin gomnati,suma yaran nata a akidar haka suks taso kuma halinta kaf suka dauko,ga karya,rashin mutunci da nuna su wasu ne,a junansu ma basa zama lfy,daga munafunci sai fada a titi,sai gasa da junansu ko wacce naso taga tafi kowa,gasu da bin malamai uwarsu ta dorasu,ita kuwa Allah sarki haj amina mutuniyar kirki ce mace ta gari,abin duniya bai dameta ba,ga hakuri da addini.addua kawai take zabgawa kanta da yaranta musamman Omar dan sunfi kishinsa,shi kam Sam baya shiga harkar kowannensu sai iya nasu dan yaga kannen nasa ba tarbiya.

Kyakyawa ne na karshe ko shi yayi Kansa iya yanda zaiyi kenan,omar fari ne amma ba kal ba,dan baza ace masa chocolate ba dan ya wuce yakai fari za a kirashi,dogone amma ba zankaleleba dai dai,ba ramamme ba kuma ba me kiba ba,a tsakiya yake da kirjinsa me fadi normal,hancinsa me kyau da tsari kuma baiyi tsini can da yawa ba,gashin kansa Wanda ya tarashi luf dashi baki ga santsi da laushi kamar na India,girarsa me yawa ga kyau,idanu dara dara farare kal,habarsa me dan tsayi,bakinsa das dan daidai lips dinsa su ba pink ba amma kamar light pink.baza Ku sha mamaki ba readers sai danaga yayi daria kusan sumewa zakuyi yanda hakoransa suke yar yar farare kal kal,ga wani dimple nasa,skin dinsa sumul luwai sai taushi laushi da sheki,tana sulbi,kafarsa da yatsu hannayensa duk abin kallo ne da birgewa,cinyarsa da kaurinsa gashi kwance masu kyau,kirjinsa kuwa da sauran jikinsa das suke ba komai luwai luwai.duk inda kuke kallon da tunanin kyau na Omar ya wuce nan.kowa sai ya kalleshi,hattana fararen fata dake London yaba masa sukeyi wajen tsaruwa da kyau,

Ta bangaren halaye kuwa Omar kusan 95% yake,baya shan komai,baya ko saurarar mata duk yanda suke rubibinshi, yama tsani yan mata shi,basa gabansa,baya shiga harkar kowa,bai damu da matsalar wani ba,sai in ka nemi taimako wajensa zai baka,matsalarsa akwai zucia da saurin fushi,ga girman kai,da rashin fara'a dan baya daria ba komai ke sashi murmushi ba.yana da tausayi in yaganka cikin masifa amma shi baya shiga rayuwar wani bare ya kai masa agaji sai ka nema zai maka,baya son surutu da hayaniya.yayi karatunsa na degree a London ya karanta economics,yanzu yayi masters tuni.bangaren addini kuwa ba a cewa komai yana da haddar ya kai izu 40,banda sauran wasu littafai na addini daya haddace,kuma ba laifi yana aiki da ilminsa,yana kuma addini sosai,baffa ne ya matsa masa kan lallai sai yayi aure,yana 30yrs ya nemo masa auren yar gidan wani governor wato sahar,yar boko ce itama dan medicine ta karanta tana aiki a wani babban hospital dake abj,tana da private nata guda biyu..

Sahar kyakyawace ba laifi chocolate ce amma tsabar body cream ta dawo fara tas,ga daukan wanka ammafa in zataje aiki.bata ganin kowa da mutunci ganin tana juya naira,motocinta 4 laba laba,duk ma'aikantan gidansu tsoronta sukeyi,sabo da cin mutunci,bata da tarbiya,ba kamun kai,dan a wurin aiki har tafawa take da maza,give me five saleem bam kaji sun kashe.

Haka maza suyi ta yaban kyanta da turarenta gaskia kin hadu,mijinki ya more,tayi ta zancen batsa da mazan aiki.wasu kamilallun matan ma'aikata sunsha bata shawara amma taci musu mutunci,

Tsiyar sahar bata tsaya nan ba har kan mijinta Omar bata ganinsa da gashi ko kadan,bai San mene aure ba,bai San dadinsa ba,bai San love ba bai tabayi ba,dama baffa ne ya lika masa dole,

Sahar addini bai dameta ba,ita kawai kudi da aikin gomnati,ga kawaye marasa tarbiyya,a rana sai ta fita sau biyar kullum bata gida,da anyi magana tace aikinta.

Taki yarda ta haihu Sam tace ina bata shirya ba,bataso ta lalace,Omar ma sabo da kudinsu ta yarda ta aureshi,dan ita burinta kudi.Omar gajiya yayi da bakin cikin halinta ya tafi London ya huta,ita kuwa ko a jikinta,ya mata fada da nasiha taki ji,bata bari ya kusanceta sai in bukatarta ce,ko tana son karbar kudi wajensa,shi kuwa baya sonta bashi da feeling a kanta yanayi ne don sauke hakkin dake kansa,shi yasa ma yake tunanin anya yana da lafiya kuwa danshi bai taba jin sha'awar matarsa ba Sam,mata kuma ko inda suke baya kalla bare ya gano matsalarsa.


Amma babban abokinsa sultan yace dan baya son matarsa ne shi yasa,duk ranar daya hadu da real love dinsa zatayi busting dinsa sanannan zai tabbatar lfy yake.Omar kuwa gani yakeyi karyane kawai.yaki yarda kwata kwata,yaje hospital da dama a turai sunce lfy lau yake. Wannan kenan kadan daga the most handsome and sexy OMAR.


Ku biyoni readers yanzu akafara Taku har kullum

Asmahbaffa.
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

2

By
Asmabaffa


Nigeria na dawo abuja garin da ake ji da naira.wajen gari na fita gidajen masu rangwamen gata,wanda suke kaiwa da kyar suna yar sana'a,da suke haya a wajen abuja Kafin a karasa cikin garin abuja,dai dai gefen titi na hango wata yarinya tana saida apple da dafaffen kwai,a titi take bi tana mikawa ta window na mota,apple and egg tana bi mota mota a round tana dagawa masu mota domin su siya,

Kallonta nayi sosai yarinya ce yar kimanin 15yrs ta hada gumi sakamakon ranar da ake zabgawa,sanye take da wata yar doguwar Riga ja da kadan ta wuce gwiwarta,rigar taji jiki ta kode ta jeme,ta fita daga hayyacinta da dankwalinta baki,amma kana kallon yarinyar fes da ita rigar kar kar ba dirty,da gani gidansu da tsabta,

Yarinyar na kurawa ido na kasa dauke idona sabo da tsananin kyau da tsarin sura na wannan yarinya,kerarriyar yarinyace me cikar zati,dan kana kallonta Kazan ta hada jinsi da larabawa basai an fada ma ba,da gani nan gaba za ayi mashahuriyar budurwa,duk motar data wuce sai ta kalleta wasu har tsayawa sukeyi suce suna sonta,

Santala santalan kafafunta na kalla na jinjina kai,sama nayo naci karo da makeken hips dinta da tudun mazaune wasu das dasu,nan nace to fa yarinya karama kenan nan gaba fa za asha kallo,ina yin gaba naga idon garin wato boobs dinta suma dai basu girma ba kananu yanzu suke tasowa nan gaba suma uhmmm...wuyanta na kalla naga wasu yan digo digo baki sun kai biyar Wanda ake Kira tawadan Allah, wuyanta mul dashi kadan ake ganin kashi,

Fuskarta na tafi sawa ido,bakin nan na hango light pink dan cut,lips masu matukar kyau,hakora kanana tas farare,hancinta na kalla me kyau da tsayi gami da tsini amma ba mai yawa ba,da digon baki dis a kan hancin Wanda ya kara kawata fuskarta,idanu dai dai ba manya ba ba kanana ba farare tas kamar madara,

Gashin kanta Wanda yayi luf har gaban goshinta ga saje kadan yala yala baki sidik,bata da girman goshi lol,gashinta ta tubke jelarsa har ya wuce tsakiyar bayanta,

Sa idona bai tsaya nan ba readers sai Dana kai kallona wajen kunnenta kanana masu kyau,fara ce kar,rana da wahala ma yasa ta danyi duhu a hakan.tallanta kawai takeyi a titi bata sauraran kowa,wasu dan kyanta suke siya,wasu dan ta kulasu su sami damar lalata mata rayuwa,shi yasa bata kulasu sam,dan haka tana zuwa talla take siyarwa,

Wata yar yarinya na gani baza ta wuce 9yrs ba me kama da me tallan apple da egg ita amma sai dai a kirata da light chocolate dan ba fara kar bace,hannun me saida apple ta kamo tana anty IKLAS kizo inji ummi tallan ya isa,wai yunwa mukeji ki dafa mana abinci,

Hannun yarinyar iklas ta rike tana murmushi ok suhaila dama yanzu zan dawo gida,ya schl?normal anty,ance ban biya kudin books din da akace mu siya ba,ranar Friday za a rufe.

Sorry baby akwai kudin zan baki gobe never mind,botikinta ta dauka dan tuni egg ya kare apple saura Leda biyu,gida suka wuce ita da kanwarta,nima na rufa musu baya,tafiya sukayi ba wani nisa da titi wani gida suka shiga Wanda zai iya zuwa na 3 a lalacewa kaf gidajen dake unguwar suna cikin mafi rangwamen gata.

Gidane na bilon siminti amma kamar kango tsabar lalacewa,daki biyu ne,sai toilet Wanda rabin katangar toilet din na karfen langa langa ne,sai kitchen dinsu suma na langa langa ne,gidan ko ina da simintinsa a dabe yake,dakinsu kuwa duka ledar tsakar dakice kusan sabuwace ma,abin mamaki wani bed na gani na gaske kalar na kasar waje yasha katuwar katifa,ga wata spare katifa jingine a bango,gefe guda wasu kayan kitchen ne dana cin abinci na gaske masu tsada a katon kwali har biyu,gefe can wata sip ce itama kalar bed din da gani ansha wuya wajen shigarta dakin,rabin sip din kayan sawarsu rabi kuma suke boye kayan abincincinsu da sauran tarkace,Duk a daki daya,daya dakin kuwa Leda ce da center carpet me kyau kuma da gani me tsadar gaske ne,nayi mamaki,wasu kujeru na gani na alfarma 3 seater 2 seated da 1seater,da badan ginin marar kyau ba da palon yafi haka kyau,wata TV na gani katuwa me kyau kamar plasma tsarinta girke a kan wani glass TV stand,

Gidan ko ina kal kal yake sai kamshin turaren wuta ke tashi,wata dattijuwa na hango a zaune tsakiyar tabarma tana fere doya,na kare mata kallo wannan sai dai a kirata kakarsu amma ba ummi ba da naji sun fada,jikinta suka zube wash ummi tsohuwa me ran karfe,mun gaji,ko wacce tana ta dakuna tsohuwa tace dalla Ku dagani zaku karasani,sai warin rana kuke,ke faratu tashi ki mana girki,kiyi wanka ki huta,gashi na rage miki hanya.na fere doya,na miki jajjage,to ummi na gode,bari nayi sallah tukun.

Sallah tayi ta shiga kitchen.faten doya ta yi musu sannan sukaci,wanka tayi ta shirya kanwarta suhaila ta rike hannunta sukawa ummi sallama ummi mun tafi islamiyya daga can zamuje kasuwa domin saro apple zamuje ma gidan gona siyo kwai sabo da siyarwa gobe,addua ta musu suka wuce.

Wai wace IKLAS NE

Babansu abdurrahman saddiq dan asalin kasar libiya ne,balaraben libiya a can wani kauye a yankinsu,ruwan sama aka musu mai matukar yawa Wanda ya haddasa ambaliyar ruwa a yankin,da kyar aka samu aka ceci mutane ba Sufi 10 ba,wasu kuma mutum biyar suka taimakawa Kansu da rakuminsu suka yo hanyar Nigeria,su kwana su tashi a sahara har Allah ya kawosu Nigeria,har suka sauka a jigawa state da rakumansu,maza ne su biyar,haka suke fadi tashi a kauyukan jigawa,ciki harda abdurrahman saddiq babansu iklas kenan,ana haka har mutum biyu suka rasu suka rage saura 3,sauran biyu suka koma libiyansu suka bar abdurrahman a Nigeria,yasha wuya yasha talauci a kauyuka,har ya fara Aron gona yana noma,da haka yaci gaba har ya fara samun kudi,ya mallaki gonaki, a wani kauye dake cikin roni nan ya hadu da abu bafulatana wato Babar su iklas,kishiyar babar abu ce ke gallaza mata kasancewar kafin Baban abu ya rasu sun rabu da babarta,shi yasa ya kwace yarsa abu ya bawa matarsa riko,

Nan abdurrahman ya fada sonta ya tausaya mata,da haka ya dage saida aka aura masa abu,bayan aurensu arzikin abdurrahma ya shahara ga kauyen ana masa sharri dan mafiya,haka abu ta haifi iklas wacce sak babanta ta kwaso,daga nan ya kwashesu suka koma abuja da zama tare da Babar abu wato hajia asmau,wacce yanzu suke hannunta kenan,suke kiranta da ummi tun tasowarsu sukaji mamansu da abbansu suna kiranta ummi shi yasa suka saba suma.har yau suke ce mata ummi,

Abdurrahman sai da ya mallaki gida a abuja ga har noma ta haka ya biya musu aikin hajji sannan ya ziyarci kasarsa ya nunawa matarsa yan uwansa maza guda biyu da suka rage a duniya,haka gaj asmai ummi kenan,duk ya hada musu hanyar da ko sabo da halin rayuwa zasu iya Neman yan uwansa,

Bayan suhaila Nada shekara 7 da haihuwa abu maman su iklas da mijinta abdurrahman Baban su iklas suna hanyar dawowarsu daga jigawa zuwa abuja suka tafka hatsari inda Allah yayi musu rasuwa,dukansu,anyi jaje da jimami,yayinda kakarsu ummi ta kira yan uwansa ta sanar musu,har Nigeria sunzo,kuma sun bawa su iklas nasu gudunmuwar,dan suma ba yan uwansa na jini bane,dangi ne kawai sama sama shi yasa basu dauki su iklas ba suka koma kasarsu,

Ummi kakarsu iklas ce taci gaba da kula dasu,tana sana'ar saida kayan miya,irin su citta,maggi,manja,wake,barkono etc,har abincinsu ya kare,kudin hannunsu ya kare,komai nasu ya kare kat hattana kudin makarantar su babu,lokacin iklas tana ss1,suhaila na primary 2,da haka suka yanke shawarar saida gidan da suke ciki,haka suka siyar da gidan Ganin matane yasa aka cucesu sosai aka siyi gidan arahar banza,

Da haka suka tashi suka koma wajen abuja gidajen dake kusa da garin abuja kafin a karasa cikin city,anan suka sayi wannan gidan da suke ciki,an musu tsada sosai anan kudin ya kusa karewa,shi yasa suka ebo wasu kayan na gidansu da suka siyar Wanda zasu iya amfani dasu suka zuba a gidan da suka siya,

Sun biyawa suhaila kudin makaranta tun daga primary 2 zuwa jss3 gudun kar a sami matsala,abinci suka jibge komai da suke bukata sai da sukayi dai dai kudinsu,har da jarin kwai da apple,ita kuma ummi takeyin sana'ar siyar da kayan miyarta a gida,

Islamiyya ma sun biya kudinta na shekaru,iklas ma an canja schl me saukin kudi,ta biya daga jss2 har zuwa ss3.ga saida apple da egg,tana dawowa daga schl zata wuce tallanta, zuwa 4 su tafi islamiyya,haka suke rayuwa har yanzu sun kwashe 2yrs.

Yanzu komai ya dagule musu,da tallan da iklas ke zuwa da sana'ar kakarsu ummi suke ci suna sha,da sauran abubuwan rayuwa Wanda ya zama dole.

Iklas bata da burin da ya wuce tayi karatu me zurfi tayi aikin gomnati dan ta tallafawa kanwarta da ummi,bata da burin da ya wuce tayi aikin goMnati,gashi aikin gomnati na burgeta, ita ko me aikin gomnati ta gani a titi to birgeta takeyi,ko ji tayi ma'aikata na labarin wajen aikinsu to sai ta tsaya ta saurara.

In tana tuno aikin gomnati ita kadai zaka ga tana daria,idan kana so kaga dariarta ko jin dadinta to ka mata adduar Allah sa ki zama ma'aikaciyar gomnati ko ta company,dan haka duk layinsu in ta wuce ko abokanan tallanta zakaji ana gomnati gomnati wasu suce ma'aikaciya,arnan ko gwarawa da marasa jin Hausa da suka Santa sai kaji suna kiranta the manager.murmushi take musu sosai,

Indai kana so a nuna ma gidan su iklas to kace gidan su gomnati ko ma'aikaciya,ko gidansu manager.

Ya halayen iklas sukene


Asmabaffa
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

3

By
Asmabaffa



Readers kar Ku gaji da hakuri da typing error sometimes ba time na editing.tnx



IKLAS nutsatsiyar yarinya ce kamila,ga addini hankali da sanin ya kamata,ga kamun kai,tsabta da son kwalliya,bata so ace taci baya sai gashi talauci yasa ta zama sai a hankali,gata da kokari ita da suhaila,gaskia iyayensu sun iya tarbiya kuma Allah ya amsa adduarsu ya basu yara nutsatsu,ga yarda da kaddara,Sam basu dau duniya da zafi ba.

Iklas bata da tsoro,tana da hakuri amma indai ka tsokaneta ko ka rainata to fa ba mutunci,bata kyalewa,gata tana da surutu amma ba me yawa ba,itama akwai zucia,gata da fara'a da mutunci da karrama dan Adam shi yasa kaf yankin da suke kowa ya Santa kuma ana sonta maza da mata,komai nata a nutse,ita sam bata son raini,Suhaila ita bata fiye son surutu da hayaniya ba. In dai kaje unguwar su iklas baka isa ka nunata da yatsa ba yanzu matasa yan unguwar zasu hada ma jini da majina,shi yasa suke zaune gidansu lfy.

Ummi ma tana fitowa za kaga ana kwasar gaisuwa sabo da iklas ta siyo musu mutunci.wannan ne asalin da tarihin iklas .


Ci gaban labari

Baffan su Omar ne ya kirashi a waya,Omar na daga wayar baffa ya fara fada haba Omar kasan ina Russia na bar ma komai na business dina a hannunka ga iyalinka can na jiranka amma ka tare a London kaki dawowa,bayan Kaine babba wa zai kula da harkata in ba kai ba,kasan kannenka basu da hankalin da zan dorasu kan harkata,pls ka koma gida nan da 3days.cike da ladabi yace alright baffa insha'allah zan koma yanda kace,dadi baffa yaji that's my son,yana son Omar sosai.

Omar kuwa nazari ya shiga yana tunanin yanda zai je ya hadu da mahaukaciyar matarsa wacce take bata masa kullum wato sahar.amma ba yanda zaiyi dole yabi umarnin baffansa ya koma Nigeria,

Yana cikin wannan tunani sahar ta mako masa kira,tsaki yayi hade da daga wayar dan yasan kudi zata roka ko wani shirmen,ba ko gaisuwa kawai ya London tace sannan tace baby wlh kudin da ka bani sun kare kuma gashi za muyi bikin wata yar wajen aikin mu,

A hankali yace yace OK zan miki transfer,yanzu ke sahar baza kiyi hankali ba,yanzu haka ake kula da miji.ganinki kinyi dai dai,tunda na bar gida ko kirana bakiyi ba,kiji tsoron Allah sahar,kiyi amfani da damarki kafin ta wuceki,kunkuni ta fara yanzu ya kake so na maka,kullum bani da time fa busy nake,kasan aikin mu ba daga kafa,ke kullum Aiki aiki baki

2 Comments On MA'AIKACIYAR GWAMNATI
avatar
abubakar-adam

10 months ago

Reply

Perfect

avatar
abubakar-adam

10 months ago

Reply

Perfect

Please Login or Register in order to submit comment