Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iyayensa amma dakyar
suka amince daya aurenta,
akadauramasa aure da maryam
watansu biyu suka daga makka acan
yakaita danginsa yanunata amatsayin
matar da ya auro daga nigeria amma
Dangin kabeer basason maryam
hasalima tsanarta sukayi sosai basa
shiga harkarta shima sukadaina
kulashi,
dahaka har maryam tahaihu biyu dashi
dik yaranta maxa, sulaiman shine
babba sai shureim, kuma alokacin
tanada ciki na uku, mahaifiyar kabeer
tadage saiya kara aure tanemo masa
wacce xai aura din balarabiyace
budurwa kyakkyawa da ita, aikwa
dalavari yaxoma maryam hankalinta
yatashi tafara kiraye kirayen waya gida
nigeria suka fara asiri amma abin nan
bayiba saida kabeer ya auri wannan
budurwa mai suna Tasleem akayi aure
lfy tatare nan soyayya taballe
tsakaninta da kabeer kuma yana
kokarin adalchi atsakaninsu kwarai da
gaske amma maryam batagani fadan
yaudaban nagobe daban, takasa kuma
tafara jifan Tasleem da mugwayen
asirai kala kala alokacin itama
Tasleem din kuma
cikine da ita yakuma kai wata biyu,
wata shida da auren kabeer maryam
takuma haihuwa 'yar mace taci suna
Xaienab, bayan kwana goma tanemi
taxo gida Nigeria wanka, ya amince
taxo aikwa suka dukufa asiri itada
mahaifiyarta harsaida sukauima
kabeer asirin dasaidaya tattaro yabar
kasarsa mkka yadawo Abuja da
iyalinsa
Tasleem da harkokinsa duka nasai da
gwalagwalai.
Dawowarsu Abuja yasa kabeer yasauya
yaxama wani mijin tace komi xaiyi sai
maryam. Tasashi, gacikin Tasleem
yatsufa amma baya bata kulawa sbd
anjanye masa hankali haka rayuwar su
tacigaba da tafiya akarkashin maryam
da dokarta, har tasleem tahaihu danta
namiji, haushi agurin maryam saima
kungani kwana bakwai akasama dah
suna Tijjani kyakkyawane nesa
bakusaba sbd dik yafi sauran yaran
maryam kyau sbd kakarsa yayo
tawajen kabeer, donhaka maryam
tadauki tsana tadorawa tujjani
musamman yadda taga ubansa naji
dashi yanakaunarsa sosai domin
yanafita dashi yawo da office ko ina
sunatare da tujjani

Bayanshekara 26, Alokacin ne 'yayan
maryam suka kawo karfi sbd sulaiman
da shureim sunyi aure xainab ma tayi
aure sai kannensu guda uku shahed
arfat salima
Baiwar Allah kwa tasleem batakara
haihuwa ba gashi har tujjani yaxama
babban saurayi domin yakai shekara
27 dinnan amma baruwansa damata
sai Abbansa kabeer ne yagadacewar
yayimasa aure donhaka yace yafitar da
mata yayimasa aure yaji kunya sosai
lokacin da Abbannasa yaxo masa da
maganar auren, amma haka yadaure
yace xaiduba. Watarana yaje shopping
muka hadu dashi yaxo shima siyayya
daga wannan lokacin yakamu dasona
yatambayi suna nace masa iyami yayi
dariya sbd yafuskanci kamar nidin
bayerabiyace soyayya maikarfi takullu
tsakaninmu da tujjani harta kai da
iyaye sunsani amma iyayena sukace
baxan auri musulmiba shima babansa
yace bai aminta ba ya auri arniya wacce
bata sallah ba, amma tasleem ta
amince nima nabijerewa iyayena
akancewa xan musulunta na auri
tujjani aikwa sukace mutkar na
musulunta sai sunfita daga rayuwata
basu bani harkarshen duniya haka na
amince sbd alokacin nafara sha awar
addinin musulunci, haka nasamu
tujjani inakuka nafadamasa narabu da
iyayena baran baran akan inaso
namusulunta ayi aurenmu ya
Jin hakan yasa ya rarrasheni sannan
yadaikeni yakaini gidansu mamansa ta
amsheni da mutumci kabeer daya
dawo shima jin labarin xan musulunta
yasa ya amince da auren bayan na
musulunta akasakemun suna xalihatu.
Akasa lokacin auren mu mama
tasleem ce taimin komai na aure
kabeer yayimana katon gida awata
anguwa tamasu kudi yakashema gidan
kudi domin dik wanda yaxo bikin
saiyatafi dasantin gidan abakinsa anyi
aure lfy muka tare,

Cankuwa takasa maryam da 'yayanta
sunhadu sunfara magana akanmu da
mijina, Tijjani mutum ne mai hakuri da
soyayyar 'yan uwa amma shi basa
kaunarsa sbd uwarsu tacusa musu
kiyayyarsa aransu donhaka suka
tsananta kiyayyarsu da hassada
akansa, takaida ko gaidasu yayi basa
amsawa saidai fada da xage xageke
rabasu, akwana atashi har nasamu ciki
nahaifi yata mace aikuwa tijjani yace
sunan mamansa xaisa na amince
damaganarsa akasamata suna
Tasleem sainace murika kiranta
Mowana. (Mahaifiya) shekarar
mowana goma sha biyu aduniya
kakanta yafadi yamutu kabeer yayin da
kamar sulaiman da shureim da xainab
da shahid jura suke suka rufa akan
dinbun dukiyar da kabeer yabari suka
mamaye komai ciki harda compuny
auduga dayake hannun tujjani
yanakulada shi, suka ciresa daga
manajan compuny, suka mamaye
hakan baisa yaji wani abuba yasamu
wani babban shago yaxuba kayan
sanyi yafara sayarwa amma hakan
baimusuba saida suka karyasa suka
samasa cutar komi yataba baxai
albarkaba, ganin yadda rayuwa takoma
mana, yasa mama Tasleem takamu
daciwon xuciya wanda shine yaxama
sanadin mutuwarta mutuwar mama
Tasleem yasaka tujjani dani cikin
mawuyacin hali narayuwa ga tsanani
da masifar wadannan yan uwannasa
abinci naci saimun nema dakyar muke
ci wataran ganin halin damuke ciki
kara ta axxara yake yasa nashirya naje
wajen iyayena amma sukayi min korar
kare sunce basu bani kanwata emeka
taitakuka tanaso taxo wajena amma
sukace xasu tsinemata mutkar takulani
haka nadawo jikina bakwara nasamu

tujjani rike da mowana balafiya
hankalina yakara tashi muka kaita
asubuti akace karin jini xa amata leda
biyu, bamuda kudin hakayaje wajen
yan uwansa amma suka wulakantashi
yadawo yanakuka nadauki gwal ina
nasayar akakara mata ruwan,

Danaga idan mukacigabada xama a
Abuja watarana xanwayi gari narasa
mijina da 'yata sbd yadda suke farautar
Mowana tamkar wata abokiyar
gabansa, donhaka nacemasa musayar
da gidan mukoma kano, ya amince
mukasayar da gidan milion 10,sbd
bakaramin gida bane, ana igobe xamu
tafi suka samu lbari da daddare
munakwance saiganin 'yan fashi
mukayi akanmu Allah yataimaka tujjani
ranan yaje wani guri neman aiki sbd
yafisu yaxauna anan wajen yanwansa
duk da suna cutarsa yace indai
yasamu aiki baxamu tafi kano ba gobe,
aikuwa sukayimin dukan tsiya suka
kwace kudin gidan amma badukaba
sbd nakwashe wasu naboye cikin
kwalbar bandaki daya dawo yasha
kuka ganin halindayasameni donhaka
dasanyin safiya mukayi sammakon
xuwa tasha, bamu dade daxuwaba
mukasamu motar daxataje kano Allah
yakawomu lfy mukafara cigiyar gidan
siyarwa dakyar akasamomana
maisaukin kudi wannan muka saya
muke xaune sauran kudin muka fara
cin abinci dasu kullum tujjani xaifita
neman aiki amma baya samu watarana yafita kenan saidawomana da gawarsa
akayi mota tatakeshi ko motsawa
baikumayiba awajen,
ranan munga bakinciki baxantaba
mantawa da wannan bakar ranaba,
Adeel
Tafashe dakuka tana rumgumar
Mowana itama kukan take Adeel ma
haka lallai akwai mugwayene mutane
aduniya wannan xalinci yayi girma
dayawa,
Kiyi hakuri momma Allah yana bayan
maigaskiya kuma insha Allahu xakuji
dayadda suma xasu kare. Nikuma
xancigaba da taimakonku har tsawan
rayuwata momma

Taitamasa godiya tanakuka Mowana
ma kukan take saiyaji ransa badadi
ashema yarinyar nan jinin arxikice
kuma 'yar dangi Allah yasamiki
abundasuka muku yace aransa,

Ranar monday hubba tashiry, tsaf taxo
tayima Mowana sallama xata tafi
gidan hajia bera'u aiki, hankalin
mowana yatashi gashi kafarta tafara
sauki amma batada ishashhsiyar
lafiyar tafiya aiki donhaka tadauko
xingureriyar wasika tabawa hubba
aboye tace takai dakin siyam harxataki
karba amma taji tausayinta ganin
yadda ta marairaice kamar xatayi kuka,
takarba taima momma sallama tatafi Mowana tana dangashi tarakota kofar
gida tanaji kamar tabita kotagano
mekyau. amma xata hakura harta
gama warkewa tunda yanxu kadan
take dangashi,

Sunsha kyau kam kamar xasuje gasar
kyawawa, dik shaddace ajikinsu
yaluwa amma maiduhu, ta amshesu
sosai musamman Brister Siyam
tamkar domin sa akayi shaddan wata
kyakkyawar mota naga sunnufa kalar
kayansu dikkansu abaya suka xauna
sai direba yaja suka fice, mummy ce
kewa direban kwatance ta waya
yanatafiya harsuka karasa gaban wani
tabkeken gida hadadde amma ko rabin
na su Siyam baiba brist, Siyam yatabe
baki yanajan tsaki Adeel yakallesu

Yakamata ka seseta kanka tunda
munshugo gidan

Hummm wlh dole mummy taimin
amma ni wlh tunkan naga yarinyar
naga alamar baxataiminba

Adeel yace

Look fa malam bakyaleka xa ai
axubama maka ido kawai ba girmafa
kake kullum sokake abarka katsofe ba
aure aa baxaiyuwuba mummy da
gaskiyarta ku biyu kadai ta mallaka
aduniya dole xataso ganin jikokinta
daga gareka karkAga laifinta

Humm yaharari Adeel daidai lokacin da
direba yayi paking yafito yabude musu
kofa amma saida sukadau lokaci
sannan suka fito sbd Adeel yaxauna
rarrashin mutumin nashi,

Cikin wani kyakkyawan falo akayi musu
iso yasha turare saikamshi ketashi ga
abincinan an ajemasu da kalolin
lemuna basufi minti biyar da xamaba
saiga wata budurwa tashiga saikamshi
take jikinta sanye da wani material
anyimasa dinkin doguwar riga
sitretgwin tamatseta matika ko ina
yabayyana ajikinta tasawani takalmi
maitsini saiwani banxan mayafi
dayatsaya iya wuyanta dayake dama
cillasa taikawai anyi kitsan atacch kala
ba yaxubo bayanta da gefen fuskarta
dankwalin annadashi ansa agoshi
fuskarta kuwa kwalliya akaxo hargida
akayimata tadubu goma, ko ba afadi
yanayin kwalliyar ba, dajin kudin da
akayita ansan taxanu.

Saiwani fari take tana yanga tashigo
dasallama ahankali kamar baxatai
magana, Siyam kallo daya yayi mata
yakusa fashewa da dariya sbd yadda
take tawani karairaya kamar wata
mara lfy, Adeel ne ya amsa
sunagaisawa tagaida Siyam dakyar ya
amsa yana kara kaudakai,

Fatan munsameki lfy

Tai murmushi lfy kalau sunana Ismat
xulkifulu

Siyam yatabe baki Adeel yaxunguresa

Sannan yayi magana

Siyam, Abokina kuma Adeel kinga
namiki xaki iya aurena shine yakawo ni
kawai gurinki sbd baxan iya yawon
xuwa xance ba

Tasaki dariya bawani kaminkai

😁😁Laaaa xan aureka mana bakada
makusa sosaima naga hotonka
awayar mamana kuma tun lokacin
anayimun maganarka naji ka kwanta
mun araina

Siyam yaji wani haushinta aransa
kamar yarufeta da duka bakidaya
batada kamun kai tab

Shikennan mu xamu koma yamike
Adeel yafara fita

Aa baxakuci komiba

Bakomi mungode yanafadan haka
yafice dasauri sbd idan yatsaya
yacigaba dakallonta xai iya sibutar baki
ya wulakanta ta baisaniba dariya Adeel
yake masa ganin irin hade randayake
kamar an aiko masa da sakon
mutuwar mummy,

Kai wannan wanne irin wulakancine xa
kaxo xakasani agaba kaitamin dariya

Siyam yay maganar afasace kamar
yadaki Adeel

Rufe bakinsa yayi yana cewa

Hhhh yo badole nayi dariya ba wannan
soyayya haka kagakwa yadda kuka
dace da Ismat kuwa woow masha
Allah
Duka Siyam yakaimasa yarike hannun
nasa yana dariya

Au dukana kuma xakai kawai don
nafadi gaskiya dadina dakai kin gaskiya
Brister

Siyam yayi kwafa yana janye hannunsa

Yarinyar kokadan batayimin ba hasalim
ma ni haushi tafarabani kafin komi gawata futsararriyar shiga da tayi
amatsayinta na 'yar musulmai, nikam
batamin ba amma mummy tayi
rantsuwa akan saina aureta tace kuma
dole namata biyayya wannan karon
mutkar itace ta haifeni,

Adeel yarike baki yana cewa

Ya Allah toh gaskiya kuma yakamata
kanunama mummy ka haifu
kanunamata tabbas kai dahne me
biyayya kayi wannan auren pls tunda
konan gaba kana dadamar kara ukuma
bayan ita, yes! Kana da kudinka
bamacen daxakanema takika saimara
rabo,
Siyam idansa adan lumshe yajingina
dabayan kujeran motar

Bani da ra ayin aje matannan agidana
kamar wasu awakai balle su fitineni,
kaganni nan dik wacce na aura xan
xauna da ita kawai itadaya, inxaman
yaki ne kawai sai insaketa ko na
hakura da auren duka,
Adeel yana daddana wayarsa yace

Nima wannan ra'ayin naka yakusa
kama da ra ayina
amma ni sai indai nah nah na aura toh
saina kara aure kaga kayiwa mummy
boyayya kawai ka amince
Bris, Siyam yace

Yaxanyi na amince Adeel xanfadamata
hakan idan nakoma gida inason
mummy na banason dik wani abudaxai
tabamun ita, shiyasa jiya rikici yakusa
shiga tsakanina da kawu salim da
kawu babba,

Adeel yagyara sbd yasan tsimammiyar
kiyayyar dasukeyiwa hja bera u,

Toh wai su maye matsalarsu da baxasu
hakura hakaba yakamata ace yanxu
sunsaki ransu, gaskiya laifin kawu
babbane sbd shine babba dole
shixaifadawa kawu salim da Aminu suji
wlh dai sunji kunya dik yadda Abba ke
kyautatamusu basa gani burinsu
kullum saisun tayarmasa da hankali,

Siyam yaja tsaki

Ai kabarni dasu wlh dik sainakoresu
daga gidannan dik wanda yakara
dagawa mummy yatsa acikinsu ni
babban bacin raina Adeel shine yadda
mummy takwada mun mari agabansu
sannan tace duk lokacin dana kara
tankawa kawu salim ko kawu babba ko
Aminu batayafemun ba nabarsu komi
xasuyi mata suyimata ni amatsayin
iyayena suke wannan fa rigimar ita
takara tunxura mummy tace naxo
nanemi wannan yarinyar idan tayimun
awannan watan xa ayibikin nabar
gidan, baxan iyabarin mummy
acikinsuba Adeel sbd basa kaunarta
gashi Abba baya iyamasu magana sai
siyomasa cha dama nidin suke shakka
kuma mummy tayi mun birki, wasu
'yan uwa Abba kedasu kamar shedanu

Hawaye suka shiga futowa aidanunsa
Adeel yafara rarrashinsa

Kayi hakuri amma gaskiya abindaI ya ta
axxara kuma ahakan da shi kawu
babban yakeso saika auri 'yarsa
su'adaat gaskiya yayi tsaurin ido,

Humm ba abundafa suke bukata
aduniyarsu iirin Abba yafadi yamutu
sumamaye dukiyarsa shiyasa ai suke
tadagewa saisun cusamin su'adaat na
aura, mummyna dah tayarda fa
dagabaya ne yanxu datagane
manufarsu ta bujire shine suka kara
birkicewa ta inda suka shiga batanan
suke futaba toh cikin watannan suke
so suhadu sutsai daranar aure Abba
kuma ya amince amma yace innafito
dawacce nakeso kafin lokacin xa afasa
inkwa banfuto dakowaba xa asada
su'adaat, itakuma mummy saita yanke
shawarar inxo insamu wannan 'yar
kawartata, duk basauki domin wannan ma basonta nakeba amma gwara ita da
waccen dabbar 'yar mutanen banxa.

Haka sukacigaba da tautanawa
gameda matsalolunsu harsuka karasa
gida wajen hajia bera u sukawuce anan
ma sundade suna hirakuma taji dadin
yadda yanuna amincewarsa donhaka
Alhjia yana dawowa xatasanr masa
ranar juma ah idan anxauna family day
yasanarwa 'yan uwansa aje anemo
auren, domin acikin watan nan takeso
ayi auren, donhaka murna awajen hajia
bera'u ba acewa komi

Ganin mangaruba tadoso yasa Adeel
yayiwa Siyam sallama yatafi,

Bayan yayi wanka yafuto yagabatar
dasallan mangaruba sannan ya matsa
ga tafkeken merorr dakin nasa yayi
shafe shafen mansa da turaruka yayi
tsaf yasauko kasa nan yasamu
anshiryamasa abinci adani,
yanabudewa yaga soyayyiyar taliya da
gashashshen nama sai shinkafar
Ghana, yaci abincin balaifi yamike
yakarasa ga kujera yakwanta tare da
mimmikewa sbd yadda kafafunsa
kemasa yama yama ba abundayake bukata kamar bacci fadowa akayi falon
dagudu saiji yayi anfada jikinsa ana
dariya
Helloooo yaya siyam nadawo koka
nemeni toh gani ai ni na nemeka ko
hutawa banba nace sainaxo naganka

Tsaki yaya jin wacece yanamikewa
xaune dauke da ita akirjinsa yana
dagota yamatsa

Kemiyasa wai bakya girmane kullum
su'adaat kifado kaina kawai basallama
kamar ba 'yar musulmai ba

Ta tura baki tana ruko hannunsa

Yanxu ni yaya Siyam maye laifina anan
don nayi murnan ganinka, sallama
kuma ai mantawa nayi

Yadauke kai daga kallon ta domin
shagwabarma datakeyi din ba birgeshi
take ba saiwani tarin haushinta dake
daskaremasa amakoshi,

Toh ke amatsayin ki na musulma inba
sakaciba daganganci miyasa xaki rinka
sake harki manta sallama kinga
kigyara dabi unki tun wuri sabd
wannan dabi ar ta turawa dakike dauka
ba indaxata kaiki domin nangaba aure
xaki haka xaki koyama yaranki? ko miji
nagari inkinason samu toh saikin xama
tagari tukunna xaki samu nagari

Tai dariya

Yaya aini banda matsalar miji nagari
tunda nakama nawa kuma natabbata
nagarine tunda tun inakarama nasan
koshi waye atabangaren halayya
dakyautatawa dasanin yakamata yaya
aidik wani abu da ake bukata awajen
wani dah namiji aika hada shiyasa
nake jidakai fa, ga son kyautatawa
talaka kanataimakon marayu, bakada
kyamar talaka rayuwarka duka
abarsoce.
Yakalleta kafin yamike

Xanje nakwanta yanxu yakamata kema
kije ki hutu sbd kinsha hanya

Kosauraronta baiba yawuce dakinsa
yana rufewa sbd tafaradamunsa kuma
dayawa

Hubba dasanyin safiya tasalallabo
bangaren siyam ta aje takardar da
mowana tabata sannan takoma wajen
aikinta,

Daf daxaifuta yaga takardar yadawo
daukayayi saiya danna a aljihu sbd
yanasauri office yau akwai wani case
daxaikarba.

Bayan bakin sunxo suntafi yadansamu
nutsuwa sannan yadauko takardar
yafara dubawa,

💜💜Sallama agareka yarda da Aminci
daso da kauna sutabbata ga ruhin
wanda nake bege kullim, kakasance
nutsuwar jiki da sirrin ajiyar karuwar
farincikin xuciyana nafuskanci dukkan
wani jindadina yanaxuwane Adaidai
lokacin danake atare dakai, dikkan
jinina yana aikine tare da taimakon
kaunarka, tabbataccen farinciki marar
karewa yakara tabbata agareka ME
KYAU wannan rubutaccen sako ne
daga wannan dai masoyiyartaka
wacce bakada kamar kab wadanda
keta furtamaka kalmarso, nafisu sonka
nafisu bukatar kasancewa taredakai,
sunana
TASLEEM (MOWANA).

Yadukufar dakai xuciyar cike datunani
wannan yarinyar tana danaci wannan
wanne sone takemin ne tun abunkwa
dayafaru gidan lamgu baisake ganinta
ba agidan toh waye yakawo wasikar ya
aje lallai akwai ayar tambaya awannan
abun
Yatabe baki yana dage kafada alamun
baidamu ba, wayarsa yadauka yafara
dannawa numban ismat yakirawo suka
gaisa sbd mummy tace yarika kiranta
suna gaisawa,

kuka take sosai tana burgima ajikin
momma

Idan baki barni nakoma gidan hajia aiki
ba wlh xan iyarasa rayuwa momma ki
kyaleni naje baxam iya rayuwa batare
da aikin danake agidan hajia ba,

Momma ita kam ma abin na mowana
yafara bata tsoro wannan wanne irin
aikine da baxata rayu inbabushiba
yanxu anataimaka musu da abinci da
kudin kashewa Adeel yadauki nauyin
abincin nasu amma tace saitatafi aiki
bayan yabarmata sallahu akan
kartabarta takoma aiki.

Kinga mowana fa dake nake dago
kanki nan kikalleni

Tana sharar hawaye tadago tana turo
baki gaba,

Kinajina me kika aje agidan hajiar da
harkike ikirarin baxaki rayubabu shiba

Abu mai muhimmanci arayuwata

Tafada tana kara tura baki kamar
yataba
kasa
tana matso kwallar dole

Toh kinajina vaxaki koma aiki can ba
amma na amince miki yauki shirya kije
ki dauko abin naki kidawo kikuma
gaida hajiar kifadamata kindaina aiki,

Dasauri tamike tana murna tafara
tunanin wanne kalar kaya xatasane
acikin kayan da Adeel yasiyomata taje
taxabi wata falleliyar atamfa baka mai
xanen blu dafari dinkin riga da siket da
mayafi blu saiwani takalmi shima blu
flet ne dayake Mowana doguwace

Wanka tayi ta sa kayanta wayyo Allah
xansu kuga yadda atamfarnan taxauna
ajikin Mowana tayi mata das siket
inyakamata daga sama daga wajen
kasa yabude sosai rigarma mairafa
akasa ce sai dogon hannu wanne
yamatse dayaxo gwiwar hannu
dankwalinta babba donhaka taninkashi
tai daurin aysha buhari, tasa
takalminta da mayafin agurguje
tadauki dubu daya dagacikin kudin da
Adeel yabata, tafuto tana kara jinta
tamkar wata sarauniya sbd yaune
xataga Siyam dinta wanda tadau
tsawon lokaci bataganshi ba,

Momma taitakallon yartata tana yaba
kyawunta da dirin da Allah yamata
acikin ranta kamarta sak da kakarta
har dirin lallai Mowana bakibar gidaba

Momma kamar yaya kenan banbar gida
ba aiyanxu xantafi

Momma tai dariya

Aa bawannan ba na kamanni saiyanxu
nakara ganin tsantsar kamarki da
kahkarki

Ta wangale baki tana rike kafadar
momma
Kaii dan Allah momma wlh xagina kike
mama tasleem itafa balarabiyace
cikakkiya, kuma farace tas nifa kallani
nibanason kina tsokanana irin wannan

Momma tai dariya

Ahaka din domin da mahaifinki yanada
rai dashiyafadamiki kumadama ai
tunkina yarinya itakikadauko duhun
fatane kuma ni kikayo shiyasa amma
ai ahakama kinfini haske fatarki
mekyauce

Ta rumgume ta tana jindadi

Tohm momma bari naje sainadawo

Adawo lfy Allah yamiki Albarka Allah
yabaki abindakike so

Tajuyo tanadariya aranta tace kamar
tasan abundanakeso xani nema

Amin momma

Ta amsa tanaficewa dasauri.

Sosai maxan anguwarsu ke kallonta
yadda take tafiya gashi kuma
sunganta tasauya tayi kyau gawasu
kaya dake jikinta masu kyau datsada
kai amma ta hadu yarinyar nan

Cewar wani gaye yana karemata kallo
taja tsaki tana saurin karasawa titi
tatari napep.

Lokacin datasa kafarta acikin gidan
wani sabon farinciki yamamaye dikkan
ilahirin xuciyarta ba abundatakeso
ayanxu datafara gani sai mekyau
donhaka bangarensa tayi kaitsaye tana
maikara fadada murmushinta
axuciyarta kuma tana tabiya irin
kalaman daxatai amfani dasu wajen
yimagana dashi, daf daxata shiga falon
taji dariya da magana gabanta yafadi
jin muryar Adeel datayi tadaki dodon
kunnenta rabewa tayi sbd dama
tagama gane cewa Adeel abokin siyam
ne tabbas amma tayaya xata shiga
wajensa maganar dasukeyice taja
hankalin ta tatsaya sauraronsu.

Kanaji na ai bansan ma tayaya
xanfadamaka bane wlh amma nakamu
dasoyayyar yarinyar nan sosai saidai
akwai masala sbd kamar akwai itama
wanda takeso daban agefe shiyasa
banmanunamata ba sbd kartaki
amincewa datawa soyayyar nashiga
wani yanayi amma Siyam tabbas
inason ta sosai wlh,

Siyam yayi murmushi

Ai damasalane irin wannan soyayyar
mutkar kasan yarinya tana da wanda takeso kace xakaje kaima kace
kanasonta
baxata yarda dakaiba kasan mata fa
Adeel idan suna son abu sai sunji uwar
bari suke hakuri ko tatsiya tsiya su
samu,
Sukayi dariya tare Adeel yace

Nidai inasonta kuma xangwada sa ahta
nagani yarinya fa poor girl ce amma
tanada tarbiyya da ilimi mahaifiyarta
ga kirki marainiyace mahaifinta yarasu

Gaban Mowana yafadi jin abunda Adee
l yafadawa Siyam,

kenan Adeel sona yake wayyo Allah
raina wlh baxantaba barinsa
yafurtamunba sbd yanada kwarjini a
ido na gashi yayimana halaccin
dabaikamata nawatsa masa kasa a
idoba idanyaxo dakokon barar
soyayyata ba, yasalam! Dik tabi
tadamu
Siyam taji yace

Haba malm kafada kawai nakegayama
karkawani tsaya duba talauchinsu ka
aure yarinyar nan sbd kasamu mata
tagari saikataima kesu, nima mai
tarbiyya nake nema, dik dayanxu anyi
kurinkus mummy tayi aiki

Suka tafa tare dakyakyacewa dadariya
Adeel yace

Kai mutumin bakada dadifa toh
kagatundaxu akayi sallar juma ah
amma kananan kadakata tatawa sai
hira muke bakaje family day innakuba
yanxukuma nasan harsu kawu babba
an xauna fa

Siyam yayi dariya

Ahhhh hmmm aikamar kasani
musamman yadda yake ji da ya isa
yafadawa kowa yaji babbane kwarai ajiki, amma
kwata kwata baisan meyakeba

Adeel yamike

Aaa fa babane karkabari shetan yasaka
karaina kawunka dayawa

Yaharari sa

Nanawa kuma saidai kar akara amma
tunda bayakaunar mummy wlh
nagamada tsanarsa tunyaushema,

Jin Adeel xaifuto yasa naruga bayan
wani katon fulawa nalabe inakllonsa
yafuto yanaduba agogon hannunsa
yasha kyau sanye yake cikin wani blu
in yadi maisantsi yakarbesa sosai
takalminsa baki da glass a idanunsa
shima baki hularsa baka agogon
hannunsa baki yYi matakyan dabaitaba
yimataba. Batasan dafutowar mekyau
ba aikuwa dasauri tafuto daga inda
tabuya tatari gabansa kayan jikinsa
sak irin na Adeel har hular da agogon,
amma fa Siyam dabanne tace aranta
Assalamu alaika ya habibi

Idanunsa suka sauka akan fuskar
kyakkyawar budurwar dake gabansa
dabaya yaja yanaso yatuno me irin
fuskarnan tabbas yasan fuskar nan
tayi murmushi

Au bakaganeni ba nicefa wannan
dinnan wacce keta sonka kana korarta
toh nadawo amma badaxama ba
kakusa kadaina ganina kaga xancika
maka alkawarin alfarmar danace
karoka kuma karoka ko, nicefa wacce
tayo ma sako TASLEEM (MOWANA)
CIKAKKEN SUNA KUMA TASLEEM
TUJJANI KABEER.

Kafin yamotsa dashirin yimata magana
tafuce dasauri tana kuka itakama
kanta tarasa dalilin wannan kukan nata
tabbas lokaci yayi daxata daina son
siyam lokaci yayidaxa tasan mesonta
dole ma tayakice soyayyar mekyau
acikin ranta taso Adeel shine wanda
yakemata soyayya tagaskiya, amma ta
inaxata fara, kaitsaye wajen hajia
bera'u ta nufa.

Maikyau yadade atsaye yana tunanin
yarinyar nan mowana kafin yagirgixa
kai yana jin wani abu game da ita
kamar tausayi tausayi kamar kuma
yadainajin haushinta, yanxu kuma
yagane cewa dagaske Allah jarabtarta
yayi dasoyayyarsa

Lokacin da ta isa falon hajia mai aikinta
tasamu tatmbayeta hajia tace tana
taron gidasai anjima xatadawo
donhaka tanemi gu taxauna sbd yau
inbataga hajia taimata sallama ba
hartatafi toh batasan ranar kuma
dawowartaba,

Cankuwa katon falon da suke taron
kujerune hadaddu masu tsada gaya ra
kuma awajen part din sunata wasa
dakayan wasa shugowar siyam yajawo
hankalin duk mutanen falon kansa har
yaxauna sannan su'adaat tasauke
kanta daga kallon sa kawu babba ne
yafara bude taro da addu ah sannan
kawu salima yayi magana akan
matsalolin yara game da yadda tsarin
'yan aikin gidan xa asakesa, nankowa
yakawo korafe korafensa ciki harda
siyam yadda yace yakamata akarawa
mai kulada bangarensa albashi Alhaji
Abdullateef ya amince bayan andan ci
ansha ana dan taba hira duk da hajia
bera'u batafiye maganaba, hakanyasa
matar kawu salim Sakina da matar
kawu babba mariya da matar aminu
Suwaiba sukai masifar tsanarta basa
shiga harkarta sbd suna ganinta kamar
tana nuna tafisu wani abu
tanajidakanta, kumadama hassada
alamarin nasu,

Bayan annutsu Abba yayi gyara murya
yana duban dukkan mutanene dake
wajen yana cewa

Toh allahamdulillahi dama wannan
rana tajuma ah nake jira taxagayo
kamar yadda mukasaba xama gashi
Allah yakawomu tohm yayi dama wata
magana nakeso nasanar muku
musamman kaiyaya babba dasalim da
Aminu
Kawu babba yagyara xama sbd
tsammanin sa maganar auren Siyam
xaimasa da 'yarsa su'adaat

Siyam yasamu matar aure kuma
nabincika nasama kwakkwaran bayani
akan ahlin gidan shine nace toh
xansameku damaganar saikusa
lokacin dayakamata kuje anemo masa
aurenta, yay........

Dakata kawu salim yatare masa
numfashi
Lallaine Abdullateef kacika mara kunya
daharxaka iya duba idanunmu
dawannan maganar wlh, kai yanxu
harkanada idanundaxaka iya dubanmu
ka fadamana wannan maganar
kodayake balaifinka bane sbd
aidabahaka kakeba yanxu jinin dan
uwanka kake gudu menene laifin
su'adaat anxauna anan damu dakai
akayanke maganar nan akan xa ahada
shi Siyam da su'adaat kuma ka amin
ce kawu babba ma ya amince au

Please Login or Register in order to submit comment