Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko

Eh toh shikenan ai dubasa kawai
xandauko ki kixo kiyi kwama gaisa da
mummy kinga bata taba ganinki ba
dama
Muryar ta nadan rawa rawa

Tace
Ok...... Ok tohm sai anjima

Takashe wayar tana cilla da ita kan
gado tafara rera kuka tamkar ba xata
daina wanne hali yake ciki me
yasameshi toh baxan iya xuwa
gurinsa ba sbda nayiwa kaina
alkawarin baxan sake yadda yaganni
arayuwarsa ba, duk da sonsa yagaxa
futa acikin raina har yanxu kuma kara
karuwa yake tamkar wutar da ake
xubama fetur.
Daga wurin Adeel kuwa yasauke
wayar yana cewa Siyam

Ai mutuniyar taka xuwa xatayi dubaka
gobe xankawota tadubaka gashi kace
gobe gida xaka koma

Nagaji daxaman hospital dinnan Adeel
shiyasa gwara naje gida naci gaba
dajiyyar kaina sbd nasan iya raunin
jikina ne xai warke bawaini din ba sbd
cutar datake damuna acikin raina tafi
wannan ciwon xafi, soyayya taxuba
mun dafi Adeel tashina daga wannan
cutar sai inwani ikon Allah amma
tabbas maganin cuta ta yana nesa
dani matuka,
Xaro ido Adeel yayi tamkar yafashe
dakuka yarike hannun abokin nasa

Aaa karka ce haka brister babu wani
abu daxaka nema yagagareka mutkar
kagaya wa Allah
Hawaye ne xafafa suka fara futa a
idanun Siyam
Nayi kuskure Adeel domin Allah ma
nayimasa laifi duk wanda xai
wulakanta dan adam komin yayi yake
mailaifine awurin Allah

Wa kakeso brister asanina baka
soyayya dakowa
Nima bansan yaushe yakamani ba
nafarkane kawai daga nannauyan
baccin dayadauke ni naganni acikin ta
alokacin da damata tawuce ni

Hmm Adeel yayi murmushi

Aikai mutkar agurin matane babu
wata dama daxata kure maka
kowacce yarinyace kafi karfin ta.
Kuma kanada alfarmar da agarin nan
ba mutumin daxaka nemi auren 'yarsa
yahanaka ba ai abin alfaharine agurin
ahlin dakanemi irinsu kadaina kuka ni
abokinkane kafadamun komi gameda
ita xan nemo maka ita xan kawo
maka ita xan iya SADAUKAR WA
dakai dikkan lokacina harsaikasamu
farincikin ka
Rumgume sa Siyam yayi yana
dansamun rilif axuciyar sa

Nagode maka Adeel tabbas naji dadin
kwantar mun da hankali dakayi
sannan kuma inaso nafadamaka
mutkar kasan lbri na da ita xakaji
haushina zaka tsaneni xaka Allah
wadai da halina na wulakanta
'yanmata insuka nuna suna sona
shiyasa nayanke shawara kawai
baxan taba fadawa kowa labarin abun
dayafaru tsakanina da ita ba kawai
xabar komi araina har cutar soyayyar
ta takashe ni domin nasan komi dade
komu juma mutkar banganta ba
ciwon sonta ne ajalina.

Aa haka vaxata taba faruwa ba brister
kanadani ga mummy ga Abba ba
abinxaifi karfin ka indai har yanxu ina
nan amatsayin amininka
bakasauyaniba dan Allah kabani
labarin ka da ita wacce kake fadamun
din.
Hawayene sukacika masa ido yafara
bawa Adeel labari tundaga farkon
xuwan su mowana aiki gidansu
harkawo yanxu dayake bada labari

Adeel wanda gumi yashigakaryo masa
tamkar ba sanyi ake yiba saiyanxu
yagane komi saiyanxu yagane cewa
ashe Siyam ne yakarya Mowana
saiyanxu yagane cewa Mowana
brister takeso abaya harta fada
tarkon cutarsa Mowana nansa brister
yake nema xahiri ko shakka babu
itace abunda wani bangare
naxuciyarsa yace kenan
Muryar sa awani dakile kamar
miciwon baki yakalli Siyam
Karka damu abokina xankawo maka
Mowana har gida kuma insha Allahu
kamar kasame tane xanfita neman
maka ita daganan innaje gida xanfita,

Kafin Siyam yakuma wata magana
Adeel yafuce yana maijin wani radadi
acikin xuciyarsa kuma yayiwa kansa
alkawarin SADAUKAR WA da brister
soyayyarsa har abada sbd
cancantarsa dakuma fuskantar cewa
yafisa bukatar Mowana atare dashi
dik da dinbin son dayakeyiwa
Mowana yafukarfun akarasa da
dankadan.
Dakyar ya iya jan motar yakai kansa
gida tare da taimakon Allah

😢😢
Adeel nafuta suka hadu da mummy da
Abba sundawo yagaidasu sannan
yayimusu yamaijiki
Koda suka shigo ciki sunsamu yayi
bacci donhaka xaunawa sukayi kusa
dashi karfe hudu dai dai jawwa
takaraso tare da 'yarta Rooofi'ah
wacce baxata wuce shekara 2ba

Abba ne yadauki roofi ah jawwa
tagaidasu
Mummy yajikin yayan

Dasauki gobe ma xa asallamemu ya
maigidan naki

Lfyklau mummy yacema naimuku
yamaijiki xaishigo anjima

Abba yakalleta yana wasa da roofi ah

Aidakin bari ma saigobe kyaxo tunda
gobe xamu koma dashi gida

Ashagwabe takalli Abba tana shirin yin
kuka
Abba xuciyata takasa jurewa baxan
iya ba inajin yadda mummy
tafadamun yaya yayi rauni bakidaya
nafirgice da tun ranar xanxo abban
roofi'ah shima toh ranar yayi dan
fama da xaxxabi shiyasa na hakura
naxauna,
Ayya ashe shima baijidadi ba

Wlh mummy

Toh Allah yasauwake yanxu dai ya
hajiar taku
Abba lftyrsu klau wlh

Saiwajen karfe biyar Siyam yafarka
bakaramin dadi yajiba ganin
kanwartasa itama dasauri taje tana
rike hannayensa sai kuma tafara kuka

Yaya sannu garin yaya haka yafaru
yaya banji dadi ba dama kwana 2
bakaxo gidana ba nayi kewar ka
dayawa yaya.
Yadan rumgume ta da gefen hagunsa
yana lallashinta
Toh daina kukan ainaji sauki kinji my
jawwa ina my baby roofy
Tai murmushi tana dago kanta

Yanxu suka fita da Abba xaisiyo mata
choculet
Ummm sarkin shan xaki kenan

Mummy dake gefe tadauko abincin da
jawwa taxo dashi tabude shinkaface
soyayyiya jaluf tasha kifi da karos da
kabej taxuba masa afilet tana mika
mata
Unguwa basa saikacinya abincinnan
donkaga darana bakaci komiba

Yalangwabar dakai
Mummy pls yayimun yawa inaxankai
wannan abincin

Taharareshi

Cikin ka mana

Yakalli jawwa ashagwabe

My jawwa kinji mummy ko kigayamata
baxan iya cinyewa ba

Jawwa tana dariya ta kalli mummy

Mummy xamu ci tare kawai amma
aikinsan yaya wannan abincin dakika
xuba na ranar sa biyune ahakama sai
in yakasance nawane abincin

Ke tafican dabakyanan toh nawa yake
ci, suka kyalkyale da dariya shi da
jawwa Abba yaxo shigo wa yace

Aa harda mara lfyr adariyar ko dayake
kunhadu fa saidai asa muku ido kuma
ammm Siyam Dr fa yace akula
daraunin nan naka nagefen ciki sbd
mutkar akayi wasa xaitaba maka ciki,
ka kula naga kanawasa da wannan
raunin
Ya sunkuyar dakai

Tohm Abba

Roofi 'ah ce tatafi dugui dugui gurin
Siyam tana bangala dariya yariketa
dahannunsa nahagu yana mata wasa.

Sai wajen karfe takwas mijin jawwa
yaxo ya duba Siyam yadauki matarsa
suka tafi.
Adeel yakasance cikin wani
mawuyacin hali bayan komawar sa
gida ba abunyake kallo fari bakidaya
kansan ya kulli wannan al amarin na
Siyam da Mowana musalin karfe
goma nadare mowana taga Adeel
baikirata ba gashi har lokacin
dasukeyin wayar xaiwuce don haka
ita takirasa amma baidagaba takira
yafi sau goma amma yaki dagawa
saitadauka kawai koyayi barcine
donhaka itama kawai takwanta bacci.

😢😢😢😢
yau aka sallami Siyam har sun koma
gida wanka yayi amma ba normal
wanka ba na watsa ruwa aa
yagwaggoge jikinsane da tawul
sannan yasa wando karami tree
kwata jikinsa yanxu bayasa riga sbd
yankan dake gefen cikinsa. Falo
yafuto yakwanta nan yasamu mummy
tanaxaune da filet din abinci
ahannunta tana jiransa yafuto
murmushi yasakar mata yana xauna
wa kusa da ita
Ka fito

Yace

Eh mummy kinatajira na ko

Tai dariya tana shafa kansa

Siyam karkadamu ga abincinka kaci
bari nima naje nadan watsa ruwan
xandawo anjima kadan nabaka
magani kasha

Tohm mummy

Tafuce tana daga masa hannu yadaga
mata shima tare dajanyo flet din
abincin yafaraci yana lumshe
idanunsa.
Wayarsa ce tashiga kuka Ahankali
yalallaba yadaukota sbd tana dan
nesa dashi
Adeel yaga sunan yabayyana agls din
wayar dagawa yayi

Slm

Wslm

Yah brister jikin naka

Allahamdulillahi

Gud yanxun kana hospital dinne ko
kuma kundawo gida

Mundawo daxu

shikenan anjima xanshigo

Tohm saikaxo. Kanaji kabiya ta wajen
wannan baye rabiyar ta layinku
kasiyomin dafaffiyar masara

Adeel yayi dariya

Tohm bari saina taho

Umhum

Yasauke wayar yanacigaba dacin
abincin sa.

Game da Adeel kuwa karfe biyu yaje
gidansu Mowana bayansun gaisa da
momma yake gayamata xasuje duba
abokinsa da mowana tace ai
shikenan sai sun dawo yana lekawa
dakinta gamamakinsa saiyaganta
ashirye cikin wani dankareren les baki
mai ratsin milik da mayafi milik haka
takalmima tana kokarin sa dankunne
tagansa atsaye yaxuba mata ido.

Takarasa sawa tana kallonsa

YayaAdeel yadai kashigo bako
sallama wlh kakusa tsoratani fa kiris
xuciyata bata fasheba

Ya lumshe ido sbd tayi kyau sosai
baitaba ganin kyanta xir ba irin nayau

Aa nayi bakiji bane

Ta hararesa

Kajikafa kunne nafa nakofar sbd tsaro

Tohm naji tunda dai nasameki har
kinshirya toh mutafi

Takallesa tana jan birki kamaryafa
inakuma xamu

Hummm kinajina muje kawai duba
brister mana damukayi maganar dake
jiya awaya

Ta lankwasar dakai

Ayya namanta ma bantamvayeka
mejiki ba, wlh kaga kuma yanxu jirana
akeyi yaune kamun hubba kuma nice
babbar kawar ta dan Allah kayi hakuri
kace inamasa sannu idankaje

Yabata rai sbd ganin yadda take
tawani rawar jiki bakinta ma narawa

Aibadadewa xamuyi ba dubasa kawai
xami nadawo dake gidan bikin

Tajuya masa baya tanaso taboye
damuwarta amma yanaso saiya
tilasta mata bayyanata,

Dan Allah yaya Adeel katafi wlh
baxaniba ina da uxiri kuma kaima
kasan ko wacece hubba agurina

Yayi murmushi

Humm karki damu nasani sannan
kuma inaso kitina kema dawaye
brister agurina amma shikenan tunda
sokike saikin nunamasa ban isa
insakiba ko na hanaki ba nope

Yanagama maganar yafice daga dakin

Dasauri tabisa tana rike hannunsa

Dan Allah yaya Adeel kayi hakuri muje
kawai wlh banaso nabata maka rai
koda saudaya nayi maka alkawari
batun yanxuba xankasance mai
biyayya agareka donhaka koda
xanrusa wani kudirina xanmaka
biyayya
Kallonta yayi yadda ta kankame
hannunsa anata tana kuka tamkar
wacce aka yiwa dukan tsiya

Xuciyar sa tayi rauni yaji dama yafasa
SADAUKAR WA da brister ita sbd
yafisa bukatarta yanajita har cikin
hanjinsa,
Game da Siyam kuwa yagama cin
abinci kenan saiyatashi yashiga
bedroom dinsa yana duba wasu
takardu dake kanwani table bisetbed
wata guntuwar takarda yagani tafado
kasa yadaukota yana budewa

Daya duba kwanan watan jikinta
saiyaga tun lokacin da mowana ke
aiki agidan sune sakone kamar haka

DA SOYAYYAR KA NAKE KWANA
NAKE TASHI RASAKA BABBAR
MATSALA CE AGARENI INA
MAISANAR MAKA DUK LOKACIN
DAKA RASANI TOH KWA
BAXAKATABA SAMUNA BA, XAN
SADAUKAR WA DA WANI
SOYAYYARKA KODAKWA KARSHEN
NUMFASHI NA KENAN.

akirjinsa ne yashiga bugawa fat fat
dakarfi karfi kafin wani tari yataso
masa maixafi dakyar yalallaba ya iya
futowa falo daf da shugowar Abba da
gudu yataresa yana jijjigasa amma
ina tun Siyam yana nuna kirjinsa har
yaxama hannun ma yayikasa yasaki
tamkar ya mutu kuka sosai Abba yake
kafin yakira dr mummy ma jin Abba
shuru yasa tabiyo bayansa ganin halin
datasamesa da Siyam yasa tafasa
kuka tana kiran sunan Allah
rumgume sa sukayi suna kuka
tamkar ya mutu dr Abdurrahman ne
yashigo hannunsa dauke da box din
aiki yakaraso yana maisa Abba
yakwantar da Siyam yafara
duddubasa dakyar yasamo kan
numfashinsa yadawo amma sama
sama yakasa mikewa sai abin janyo
numfashi yasamasa yadubi Abba

Am pls Alhaji koxa abincika aga
menene brister yake so baisamuba
hartakaisa dafadawa wannan yanayi
so agaskiya dai akwai matsala sosai
mutkar ba akawo masa abundayake
nema ba, sbd xuciyarsa daf take da
samun matsala kuma xai iyasamun
ciwon kwakwalwa sbd yawan tunani
dayake maixafi.
Abba yakalli mummy itama takalli
Abba tana kara sakin wani sabon
kukan takarasa inda Siyam yake
akwance kamar gawa

Wayyo Allah na

Siyam Allah yabaka lafiya amma
bansan indaxanje nanemo maka
Mowana ba danaje nasan itace
matsalar ka

Abba yaklleta

Wacece Mowana kuma

Shiyasanta Alhaji wata yarinyace

Daukar wayatayi takira Adeel alokacin
yakusa ma karasowa yanadaga wayar
mummy tafashe dakuka tanafada
masa abundayake faruwa

Hankalin sane yatashi yajuya yana
kallon mowana wacce ke gefensa

Mummy ina hanya gani nan xuwa
yanxu insha Allahu

Lfy yaya Adeel

Mowana tatambayeshi

Bai bata amsaba sbd tsabar tashin
hankalin dayake ciki

Gabantane yatsananta faduwa ganin
sun isa bakin get din gidan su Siyam

Tafashe dakuka dan Allah karka shiga
dani dan Allah mukoma

Kosauraronta baiba saidaya faka
motar apaking space sannan yabude
yafuto yanaxagayawa yabude
bangaren maixaman banxa

Yaya Adeel mekake nufi
Xaki sani idan muka shiga cik karki
tada hankalin ki bakomi
Tashare fuskarta tana saukowa tabi
bayansa suka nufi part din Siyam.

Daf daxasu shiga kamar antaba
SIYAM yafarfado yana rarraba ido
mummy tatafi wajensa taji sallamar
adeel tana dagowa taga Mowana
abayan sa
Xaro ido tayi

MOWANA tafada dakarfi tana xuwa ta
rumgume ta siyam kuwa kif kifta ido
kawai yake yana kada hannu tare da
nuni da mowana yayin da hawaye ke
xuba ta gefen idanunsa Adeel
yakarasa gabansa yana rike
hannunsa cikin nasa alamar
yakwantar da hankalin sa fixgewa yayi
yana sa hannu yacire abunda akasa
masa ahancin sa xuwa bakinsa
yamike tamkar wanda yasha giya
yana layi yanufi Mowana dake kusa
da mummy taxama tamkar gawa don
ko kwakkwaran motsi takasa yi.

Yanaxuwa gabanta yaxube bisa
gwiwoyinsa tare da hada dikkanin
hannayensa guri daya hawaye nabin
fuskarsa magana takasa futa
abakinsa saidai motsa bakin dayake
kamar maikokarin koyar magana

Kallon Adeel tayi tana kallon mummy
Abba ma taga ita yake kallo tafashe
da kuka tana rugawa dagudu bayan
Adeel tare da magana cikin tsoro

Dan Allah kamayardani gida yaya
Adeel narokeka
Mummy dasauri tagirgixa kai

Karki xama mara imani mana mowana
komi Siyam yayimiki yakamata
kiyafemasa xuwa yanxu tunda kinga
halin dakikaxo kikasamesa badan
xuwanki ba danarasa shi sbd
tsananin so daya harbesa kodan haka
kinyi masa afuwa bisa laifinsa ki
amshe sa akaro nabiyu

Adeel ta kalla tana girgixa kai

Aa mummy aa mummy kiyi hakuri
babu sauran wata dama yanxu
tsakanina da Siyam mummy inada
wanda xan aura ko yaya Adeel
baifadamuku nice matar daxai aura
ba
Bakidaya suka xubawa Adeel ido ciki
harda Siyam wanda ke tsugune
yamike yana ja dabaya Ahankali saura
kadan yadaki bango Abba yatarosa
Adeel yayi murmushi yana neman gu
yaxauna yakalli mummy da Abba da
Siyam yayin da mowana shitake kallo
idanunta basu bar xubarr da
hawayeba
Hakane mowana itace matar daxan
aura mummy. Amma tunjuya daya
bani labarin wacce yakeso nagane
mowana tace hankalina yatashi
mutka. Bankara tsorataba saidaya
faramun wasu maganganu akanta
wanda yafaru tsakanunsu abaya
nagane cewa tabbas shine wanda
mowana tafiso fiye daduk wanda xata
nunawa somatsayin miji aduniya take
nafara tunanin yadda take tilas tawa
kanta da soyayya ta bawai don nine
xabintaba tundaren jiya nake
shawarar SADAUKAR WA da brister
soyayya ta domin yafi karfin wannan
daga gareni kuma ransa yafimana dik
wani abu daxa musamu aduniya.
Wani kuka Mowana tasaki mai ciwo
tayo kan Adeel tana cukumo wuyan
rigarsa
Kacuceni kaci amanata Adeel
baxantaba manta wannan
wulakantarwa dakayi min ba agaban
wanda dama can ni wulakantacciya
ce a idanun sa. Kai harkana tunanin
xan iya sauya wata sheka nakai
kwaina bayantaka toh kasani
SADAUKAR WA dakayi mutkar tanice
batayuwuba wlh.
Xatafuce Abba yaruko hannunta cak
ta tsaya tana tsugunawa harkasa
Baxanga laifinki ba yarinya sbd ba
asan irin abubuwan dayayi mikiba
abaya sbd haka wannan abundakika
yi kinyi daidai amma kisani ran Siyam
tamkar ledace akan ruwa koda
yaushe xai iya tafiya duk dacewa
kowanne dan adam ma ahaka yake
ammakisani ke musulmace yakamata
ki tuna
Mummy kuka take kawai tana rike da
Siyam wanda keta wani xaxxafan tari
yarike kurjinsa da karfi yana kiran
sunan Allah dasauri dasauri
Kabarta tatafi Alhaji Siyam in Allah
yayi mungama rayuwa dashi dole mu
hakura dashi inko kwanansa baikare
ba xaitashi komin wahala

Adeel yakalleta afasace

Xaki wahalar da shiri ane mowana
amma har yanxu xuciyar cike take da
soyayyar brister toh kisani mama da
daddy tun daren jiya nafadamusu dik
abundayake faruwa kuma adaren
nadaukosu nakawo gidanku wajen
momma sukayi magana ta amince da
duk abindana fada kuma suduka
nakirawosu yanxu nacewa mama
subiya sudauko momma suxo tare
nan atabbatar dakinxama mallakin
Siyam yau basai gobe ba
Harara tadoka masa tana share
kwallar dakexubo mata
Dama yaudara ta kayi yay Adeel dama
basona kakeyiba sallamar su mama
yadakatar da ita tana rugawa ta
rumgume momma tana kuka
Wayyo Allah momma kinga yadda
rashin gata xaisa amin yankan kauna
rashin gata xaisa amaidani tamkar
wata kwallo, momma kitashi mubar
wurin nan
Daka mata tsawa tayi sannan ta nutsu
Dr ne yashigo tare da wasu likitocin
biyu suna gungura abundaukar
maijinya daddy da Abba ne suka
dorasa likitocin suka gungurasa suka
fita mummy xata bisu Abba yadakatar
da ita
Kibarsu suje dashi nasan dukkan wata
kulawa da inmuna tare dashi xasu
bashi dr Abdur rahman xaikulada
hakan
Dagakai tayi alamuntagamsu amma
idanunta basu fasa xubar kuka ba
Alhaji Siyam nacikin mawuyacin hali
ina tsoron inrasa yarona banida wani
madadi bayan jawwa yaya rayuwata
xata koma nasaba da dahna baxan
iya jure ma rasashi ba
Abba ya rumgume ta yana lallashi
dakyar akasamu kanta sannan suka
gaisa da mama da daddy da momma
sannan taga momma kamar yadda
Adeel yafada musu haka akasake
tattaunawa mama da daddy suka
amince da SADAUKAR WA da Adeel
yayiwa Siyam na mowana momma
ma ta amince jinhaka yasa mowana
fashewa dawani kukan xuciya tana
kankame momma Adeel ne yamatsa
akan saidai adaura masu aure yanxu
anan saidai kawai Siyam yafarka yaganta matsayin matarsa
Abba yace toh nan yaje cikin gida
yakirawo kawu babba da kawu salim
da aminu sukaxo daddy shine yabada
sadaki kawu babba ne waliyyin Siyam
momma kuma mlm liman takira yaxo
shine ya amsa waliyyin mowana.
Anan aka daura auren Siyam
Abdullateef da tasleem tujjani kabeer
akan sadaki naira dubu dari da
hamsin. Sabd daddy yace sune
ajikinsa yanxu momma kin karbatayi
tace sunyi yawa dakyar dai mama ta
amsa tasa mata ajaka Mowana kuwa
kuka harda turje turje daddy ne
yamayar da momma gida ita da
mowana sannan suka tafi hospital din
da aka kwantar da Siyam shida mama
da Adeel yanatasa wa dan nasa
albarka sbd yadda yake ta kokarin
ceton ran abokin nasa da dukkan
damarsa yaji dadi dayau jininsa
yaxama mai taimakon musulmi dan
uwansa.
Hawayen dake makale agurbin idon
Adeel suka tsiyayo
Daddy kutayanida addu ah Allah
yakarbi SADAUKAR WA ta sannan
yasamun kwarin gwiwa akanta
karnaxama mairauni
Mama tashafa kansa itama tana kara
kwarara masagiwwa.
Har akagama kamu amma amarya
hubba bataga mowana ba kuma
gashi har mangaruba yadoso takira
wayarta takira amma akashe hankalin
ta yatashi tafada daki inda tasamu
kawarsu wacce suke ji da ita itada
mowana takama hannunta
Hamsa'u wai lfy kuwa Mowana
tundaxu banganta ba agidan nan
kinga har angama kamu gashi kinsan
kuma gobe fati itaxataje wajen kboy
ta amso mana getpas kardare yayi
sannan taxo tace baxata iyaxuwa ba
Hamsa'u takalleta
Nima tundaxu nake kiran wayarta bata
shiga ba tundanaxo naduba naga
bangantaba kuma tunfa wajen karfe
biyu mukayi waya da ita tace tashirya
futowa kawai xatayi tataho
Toh akwai matsala kuwa yanxu dan
Allah kitaimaka mun kije gidan nasu
kigano mana wlh hankalina baxai
kwantaba harsai natabbatar da halin
da 'yar uwata ke ciki
Tohm shikenan bari naje.

Tafuce tana kara gyara daurinta sbd
batasan inda rabo yakeba watakil
tagamu dawani Alhajin
Tana futa titi tatari napep

Hamsin ne xuwa hamsin dawowa
cikin kankanin lokaci ta isa gidan
Momma tafara tarar wa acikin gidan
axaune tana laximi
Suka gaisa tace momma ina Mowana
fa
Tanunamata dakinta tana cewa

Tanaciki
Shigewa Hamsa'u tayi tana kwala
mata kira
Ganin yadda tasametane yasa
takarasa dasauri tana riketa
Yaya dai mowana lfy kuwa naganki
ahaka
Kinyar da dankwali kinbarbaja gashin
kanki gafuskarki fusassun hawaye
why nakinsha kuka
Babu lfy Hamsa'u kunji ni shuru ko

Eh hubba duk hankalin ta yatashi
kinga itace ma taturo ni naxo
nadubaki lfy kuwa
Ta lumshe ido kamar maijin bacci

Ba lfy Hamsa'u kifadawa hubba yau
aka daura mun aure da Siyam
sauranxancan takira ni awaya gobe
domin naji su momma namaganar
nanda kwana uku xankoma gidan su
siyam din
Farinciki ne yabayyana afuskar
Hamsa'u
Woow Mowana kin auri namijin duniya
kice saurayin da kowacce mace
agarin nan harda ketare keta burin
mallaka, burinki Allah yacika miki
dole kisha kuka har ki koshi domin
kuwa wannan wani burinkine
namusamman auren Siyam MEKYAU

Kinga da Allah kamakanki Hamsa'u
dakika sani amma bayanxu ba
kokadan bana kaunarsa yanxu
natsanesa bakuma xaitaba samuna
matarsa ba wlh
Mikewa Hamsa'u tayi tana kallon
mowana kamar amafarki take jin
Mowana na ikirarin ta tsani Siyam
lallai akwai wata akasa
Allah yahuci xuciyarki nabarki lfy
saimun xo kaiki
Dagudu Mowana tabiyota aikwa
dakyar takai kofa tana haki
Momma taharari Mowana tana jallata

Kewai yaushe kika lalacehaka
Mowana yaushe kikaxama marajin
magana au sbd wannan abun duk
kikabi kikatada hankalin ki da gashin
kanki sbd kin haukace toh kindade
kina hauka kuma wlh don aure kan
anriga da an daura idan kinje ki
yankasa koki soyasa muji kamshin. suya tunda ke kinxama abundakika
xama idanma banda muna funci
dagulma data yi miki katutu yaron
dakedakanki kika mutu asoyayyarsa
tunfarko shine dan yanxu shima. yadawo hayyacinsa yanasonki. xaitaimaka miki xaki tsiri firirita da. iyayi toh wlh ahir dinki karki sake naji. akasin abunda kikataso kikasamu. inama mahaifinki
Tafara dara kafa akasa tana kuka

Wlh bataimakona xaiba nice
xantaimakesa shi dayake akan gabar
mutuwa akowanne lokaci kuma
aidane naso shi ni yanxu ko kallonsa
bana kauna arayuwata
Dan uwanki toh ki kashesa kuma airai
ahannun Allah yake fice kiban gu
kona kakkaryaki yanxu agunnan.

BAYAN KWANA BIYU.
Siyam xaune hannunsa ansa masa
karin ruwa dasauki yanxu jikin nasa
domin kuwa yawarke harmagana
yakeyi duk dabasosai ba sbd yawan
surutu nasa jikin nasa yakara rikicewa
yanxunma Adeel ne agefen damansa
yana tabasa labarin abokanansu
nakasuwa wadanda sukaxo dubasa
lokacin dabaya hayyacinsa
Yasakarwa Adeel murmushi yana
lumshe ido kafun yace
Abundakayimun naji agurin mummy
jiyatake fadamun amma Adeel anya
kayiwa kanka adalci kuwa bakaganin
kai xaka cutu kanka nema min
farinciki kaikuma ka kuntata
atasanadin SADAUKAR WA abokina
tabbas natabbatar da amintar mu
lallai ta gaskiyace. Kuma bansan
harnakai haka awajenka ba duk da
dama ko agurina kaima kafi haka
shiyasa mummy nafadamun nace aa
kaima kanasonta kuma kafini dacewa
da ita sbd kaine kanunamata kulawa
da tararraya alokacin datake bukata
kaine katareta alokacin dana koreta
daga gareni kaxame mata gata
alokacin data ke neman taimako duk
kana nufin wannan xaitafi abanxa
k..........
Ya isa Adeel yasa masa hannu abaki

Nidakai duk dayane dan nayi wa
mowana wani abu taxama taka aiba
wanidamuwa bane tunda ni
da duk wani avu dayadaya
danganceka ne kaga xuwa yanxu
mowana taharamta agareni sbd jiya
saidana tabvatar taxama mallakin ka
sannan hankalina yakwanta kariketa
amana Mowana kanwatace domin
tamkar Aslamiyya take awajena
kodacan najingina soyayyar mu ahaka
shiyasa batai karfin daxata iya
illataniba so kagane brister kafini
bukatar Mowana akusa dakai nina
tabbatar dahakan,
Shikenan Adeel amma da naso
dawomaka da mowana gareka amma
tunda nafahimceka sosai shikenan
Allah yabamu xaman lfy
Amin hakanake son naji ango kana
samun kwarin gwiwa
Yayi murmushi
Kwarin gwiwa aikagama bani Adeel
banida tamkarka bayan mummy da
Abba da my jawwa Allah yabaka
mace tagari Adeel Allah yabaka
dauwamammen farinciki arayuwarka
Amin nagode dawannan addu ah mai
kyau haka fatana Allah yabada 'yan
tagwaye.
kwanan Siyam goma dasamun lfy
yayinda mummy suka fara shirye
shiryen shagalin bikin wanda
xaikasance jibi anhada lefe dan
ubansu wanda tsayawa lissafa maku
abunda akaxuba aciki wani sabon
lalene kunsandai waye Siyam da
iyayensa kudi tamkar banxa suke
agidansu. Akwatinana hadaddu guda
12,kowacce da abundayake ciki kuma
cike cike suke dakayan kyale kyalen
duniya, yau aka kai mowana gidan
mummy sbd acan xa ashiryata

hargidan mijin ta
Dakyar tasaki momma tanakuka
maitada hankali momma ma kukan
take tana samata albarka danasiha
mai shiga jiki innar hubba dawasu
mata biyar kawayen momma sune
suka shiryata cikin kaya masu kyau
karfe hudu motocin biyu suka karaso
wadanda xa adaukesu akaisu. Tasaki
kuka tana kankame momma
Momma tafashe dakuka tana xare
jikinta daga nata tafada daki haka
innar hubba takama hannunta suka
fita tana kuka
Basudade ba suka sauka matan duka
bubbude ido sukeyi ganindaular
dasuka shigo lallai yarinya tayi goshi
fadar wata acikin matan innar hubba
tace
Gaskiya ubangiji Allah yasanya alkhairi
bude musu motar akayi suka fiffito
tsayawa sukayi sbd basu san part din
daxasu nufa da itaba wata
kyakkyawar mata suka gani tafuto
daga wani waje tana murmushi taxo
taimusu sannu daxuwa suka gaisa
taimusu jagora xuwa part din hajia
bera'u
Xaune take cikin wani hadadden les
gwaldin yasha dutsina gefenta matan
su kawune sakina mariya suwaiba
sunata faman gyara hadaddun
abincinan da aka jere akayataccen
falon domin tarar masu kawo amarya
sai hira suke suna dariya da mummy
kai bakace anta samun wata rigima
atsakanisuba sbd yanxu suka dawo


Please Login or Register in order to submit comment