Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka yi nadama da abunda suke mata
kuma akayafi juna don duk hidimar
bikinnan dasu akeyin komi suntsaya
sosai jawwa da su'adaat ne sai
kanwar su'adaat din nihal da sauran
yan matan gidan afra da nabila sai
sumayya 'yayan suwaiba sai
madawuyya tawajen sakina wacce
take karamarsu sumayya tayi aure
tana da yara biyu nabila ma haka
yaranta uku afra da nihal ne sai
su'adaat sune 'yanmatan dayanxu
suka rage xa awa aure sai maxa
kwara biyar daya usman yayan
su'adaat da ayman sai aiyu da
Abubakar da shamsuddeen ya'yan
suwaiba.
Walimar su suka hada yau sbd jibi ta
iyayece da manyan bakin da
akagayyata nagari da gari ciki harda
sarakuna daxasu halicci bikin.
Suwaiba ce ta taro amarya tana rike
hannunta taxaunar da ita su innar
hubba suka xaxxauna kan luntsuma
luntsuman kujerun dake xagaye da
faffadan falon daya gaji da haduwa
sbd kyau har wani daukar ido bangon
falon yake
Mummy da mukarrabanta cikin
mutum tawa suka amshesu aka
gabatar musu da abincin da
akatanadar musu na musamman
sunci sunsha sosai kaji kamar banxa
agurin wasu gasasu akayi wasu anyi
farfesu wasu acikin abinci abin ba
acewa komi harka kudi akwai dadi
mlm
Saiwajen karfe uku su innar hubba
sukace xasu tafi aikuwa mummy
tacikasu da alkhairi domin kowacce
mace wata leda akabata maikyau
dauke dasunan Siyam da mowana da
date din auren nasu basu san maye
acikin ledar ba sukayigodiya sannan
tasa direbobin gida dasu dau motoci
biyu amayar dasu har gida aikwa haka
akayi
Bakidaya bakin matan yarufe sbd
sunga duniya a inda take abun har
tsoro yaso yabawa innar hubba
amma tadake sbd tanajin labarin
gidan Alhaji Abdullateef abakin
mutane dayawa ga uwa uba hubba da
idantaje taitabata lbri agidan su
mowana aka asaukesu aikuwa
sunashiga akasaki guda tare da
xaxxauna wa momma takallesu tana
musu sannu dadawo amsawa suke
tare dakowacce tahau xaxzage ledar
da aka basu atamfa ce turmi sai
kwalin turare da kudi kowacce 5000,

Heeewa kawai kikeji har waje mata
gida yakaure da labarin irin tarbar
mutumcin da akayimusu da irn
abunciccinan da aka ajemusu kamar
banxa itadai momma saidai tai
murmushi tana jindadi acikin ranta
sbd tana kyautata xaton mummy xata
kulamata da 'yarta sbd soyayyar da
Siyam yake mata.
Cankwa gidan su siyam mummy ce
takama hannun mowana dakanta
takaita bangaren Siyam tare da
lallashinta sbd irin kukan datake yi
tunda aka kawota dakyar mummy
tasamu tadanci abinci tasha ruwa
sannan tarufo mata wajen abakin part
din mummy taga su nihal da
madawuyya dasauran har da jawwa
suntaho xasu wajen Mowana mummy. tadakatar dasu tace subari
gobe dasafe sunje suganta yanxubata
gama sakewa ba
Aikuwa dakyar suka hakura suka juya
suna gunguni mummy tayi musu
dakuwa suka fashe da dariya
Kai mummy amma kina ji da 'yar
sirikarnan taki
Su'adaat tafada tana taba jawwa
Jawwa tarike haba
Wooooo sosai makuwa aibataso
mushigane muje mu isheta da surutu
musata kuka shiyasa aka hanamu
shiga
Hhhhhhh su'adaat tai dariya
Lallai dan itace shagwababbiya
saitahau kuka
Eh mana kinsan rabo da iyaye badadi
kema wayasan mexakiyi ko harda
bursusuwa ma xaki hada xaki wani
cikawa matane baki
Kaiii anty jawwa Allah yakyauta wlh
xandai danyikuka kadan tunda akwai
'yansa ido
Jawwa tai dariya
Kaii yarinyar nan aure fa kike so bari
naje nafada wa anty nabila da anty
sumayya mufara shirin fidda anko
naga inmukayi wasa saiki kaikanki
Suka fashe da dariya suna karasawa
wajen su nabilan sannan suka hadu
akaci gabada hira kamar bagobe
Game da mowana kuwa jinbatajin
motsin kowa atawajen yasa tamike
tacire mayafin tafara neman toleit
sbd tai alwala tai sllah gashi
mangaruba yadoso ko sallar xuhur ita
batayiba bedroom dinsa tashi aikwa
kamshin turarensa yadoki hancinta
har cikin xuciyarta taji wani sabon
sonsa yakanainaye xuciyarta amma
afili tsaki tayi tana kallon dakin dalla
dalla sbd haduwarsa saitaji dama
anan xasu xauna yafima daki tamkar
wani fadar shaharraren sarki maiji
dakansa saidai daxu taji mummy
namaganar gidan Siyam akeyiwa fenti
Inakallon dakin Ahankali harnahango
toilet din manne dabangon dakin
dasauri nashiga nanma saidana bata
lokaci wurin kallon kyanbandakin
kafin nayi dahara nadaura alwala
nafuto kan dirowan dake gefen
gadonsa naga sallaya nadauko
nashinfida nafara gabatar da sallar
xuhur tukunna nayi asar ina idarwa
aka kwalla kiran sallar mangaruba
dayake akwai babban masallaci
acikin gidan. Saidanayi mangaruba
sannan natashi agun nadauko
takalmana nasaka nagyara xaman
mayafina nakoma inda mummy
taxaunar dani naxauna raina
acunkushe sbd baxantaba nunawa
Siyam farinciki na da auren saba sbd
baxantaba basa farinciki daga
gareniba saiya rabu da ni kodakwa
bayaso kodakwa shine autan maxa.

Cankwa Siyam da Adeel ne sukaje sayo kayan daki domin kuwa Adeel yace shixaiyiwa kanwarsa kayan daki baiyardaba Siyam yayi sbd karma wataran yaxo yayi matagori akan hakan. Dole Siyam yahakura duk dabansan nawa yasiya ba. Cangidan nasa dake gra akakai kayan sannan sukayi sallama dajuna Adeel yawuce gidan momma yasameta cikin jama a amma yasa akakirata bayan sungaisa yadauki kudi dubu dari biyu yace gobe tajekasuwa asiyowa mowana kayan ketchin, tafashe dakuka xata masa godiya yadaga mata hannu
Aa momma karki mungodiya addu ah kawai nake bukata daga gareki tanashare hawaye tace
Yaxamar mun dole ingode maka Adeel sbd shine kadai abundaxa ka iyaji daga bakina ayanxun kaxamiwa mowana tamkar mahaifi komai da akeyiwa yarana nadaki kayi mata karshe ka SADAUKAR WA abokinka ita sbd kaga shitakeso naji kunya sosai lokacin da al amarin nan yafaru sbd bantaba xaton Mowana xan iyaba wani itaba bayankai Allah yasaka maka da alkhairi Allah kuma yabaka wacce tafita kaji insha Allahu baxaka taba toxartaba Adeel mungode mungode mun,,,,,
Amin xanwuce momma
Yakatse mata godiyar datake tajeramasa tana hawaye
Yamata sallama yatafi yanajindadin yadda tamasa addu ah amma yanaji ajikinsa babu wata mace daxai samu wacce xa tafi Mowana.don haka xaicigaba da rarrashin xuciyar sa
Sai wajen karfe takwas Siyam yasamu nutsuwa yashiga part dinsa yana sauke nannauyin ajiyar xuciya sbd sanyin dayaratsashi nafalonsa yafara cire hula sbd wanka kawai xayyi yasa kananan kaya yadan leka wajen mummy yaga amaryarsa saiyaxo yakwanta yanakokarin sawayarsa achaji kawai yaga mutum xaune akujera ana jijjiga kafa
Yakusa tsorata kafin yakara kallonta yana dan girgixa kai
Sannu daxuwa
Yace mata yana karasa sa chajin ya mike sbd ko kulasa bataiba balle ta amsa sannun daya mata
Xama shimayayi akujerar dake kusa da ita
Tamike tana jan tsaki tare da kokarin sake waje yadaga mata hannu
Nasan ni mai laifine awajenki. Ina neman yafiyarki sbd Allah kiduba girmansa ki saurareni ki kuma yimun kyakkyawan fahimta mowana yanxu fa ke matatace wannan kadai yadakatar da subucewar kwakwalwata daba abun daxai dakatar da ni da xaucewa face wani ikon Allah natabbata dacewa nagane kurena yanxu kuma natufa nagane gaskiyar al amari nafahimci yadda kike ji akaina abaya lokacin danadauke fahimta ta daga gareki, nakamu da so.............
Tadaga masa hannu tare da jan wani dogon tsaki
Wani wulakantaccen kallo tajefesa dashi tana dawowa tatsaya akansa tamkar maishirin fado masa aka cike da masifa tafara magana
Daka barfadamuni dik wani abu dayafito daga gareka Siyam sbd babu wata kalma daxata futo daga bakinka yaxam najita babu karkamanta nicefa mahaukaciyarnan maidatti haba aiba girman ka bane karinka kaskantar dakanka agabantaba humm kuma wai matar ka dakake kirana wlh kakusa kadaina domin kuwa aure na dakai ba maidore wa bane baxanta ba xamemaka matar farinciki ba mutkar inadarai yaya Adeel yabani mamaki yagama da rayuwata dahar ya iya SADAUKAR WA da mutum irinka ni sabd wata alakarku wlh saika sakeni kobakaso Siyam kai macucine bakasan darajar mace ba don haka baxan xauna dawanda baisan darajataba
Tunda tafara magana yake kallon bakinta dankarami ne yabasa sha awa wannan shine karo nafarko dayataba ganin wani abu ajikin mace yaji yana so kuma yanabirgesa bakidaya dayakarewa Mowana kallo saiyaga ashe itace irin macen daya gama xana poton ta axuciyarsa amatsayin matar daxai aura, murmushi ne ya subuce masa yamike xaishige bedroom dinsa dasauri tamatsa daga kansa sbd taga sunkusa gogar jikin juna itako asarane tahada jiki dashi
Idan kingama kixo muje mukwanta dare yayi ko
Wata muleleyar harara tahada waje daya ta xabgamasa, saura kiris yasume sbd bakaramin kyau tayimasa ahakan ba yadafekirji dakyar yana kaiwa bango
Wayyyo raina karki huda mun xuciya mana mekyau ta
Tamkar tarufe shi da duka ganin yana neman yamaida ta mahaukaciya haushi yarufe ta kallon daya ke jifanta dashi yaratsata har ko ina najikinta bakidaya kuma saijikinta yayi sanyi tafara neman hannnun mayafinta daya xame sbd tsabar rudewa bakin mayafin nakasa ita kuma sama take nemansa Siyam ne yanufo wajenta batare daya dauke idonsa akan nataba kuma baidaina jefanta da wannan kallonn nasa mai kashe jiki ba baya baya tafarayi Ahankali tana matsawa kuma takasa dauke idanunta daga cikin nasa sbd bakidaya yagama xuba mata dafi dawannan mayatattun idanunnasa masu haske da kyalli yana wani lumshe su kamar xai suma, bakidaya jikinta yaga ma yin sanyi tasadakar mutkar Siyam ya cimmata saiya daumataki akanta narashin kunyar datamasa don haka tanajin bayanta yakai bango tarumtse idon ta gam tana kaudakai gefe tasa hannunta tana rufe kirjinta inda mayafin yaxame jin yacinmata har numfashinsa na dira kan wuyanta jin shuru bai mata komi ba yasa tabude idonta saitaga yayi tsare ta da ido yana kallonta up an dwn sunahada ido yayi sauri yaykasa yadauko mata bakin mayafinta yamika mata, bata amsaba saita kuma dalla masa harara ta murguda baki
Dariya yayi sosai sbd yadda tai abun dik atsoro ce take bakidaya
Ni kaga kamatsamin daga kaina inshaki iska maikyau
Xaro ido yayi yana so yayi dariya
Ke bafa nason rashin kunya saiwani jijimun dakai kike toh barja baya niba tabaki xanba naga harwani lumshe idanu kike masu kama da na mage kina so kiji hannu lallausa yakaimiki xiyara ko humm tom baxanba inma kinsa arai kicire nima inada aji harsai kin lallasoni kin shashshafi xuciyata xan sauko haba kaikunjimu da yarinya 'yar karama sai fituna
Dandanan idanun Mowana suka cika dakwalla jin sharrin da Siyam yake jifanta dashi haka yake kallonta ashe sai hawaye shar shar
Yanaganin tafara hawaye
Yajuya yana ta kyalkyala dariya acikin ransa sbd yasan yakunsa mata haushi dole tasaki jiki inba haka yace haka takeso yanemowa kansa hanya maisauki wajen ganin yasamu kan ta.
Kifewa tayi kan doguwar kujera tafashe dakuka tinkarfinta,
Allah ya isa tsakanina dakai brister baxantaba yafemaka ba kuma wlh kakwana dasanin nifa banakaunarka banasonka banasonka
Yanajin dik abun datake fada amma baidawoba tunyana jin kukanta da surakatanta haryaji shuru alamun tayi bacci
Saidaya fesa bed shit din da turare tukunna yaxo yadauki Mowana cak tamkar wata jariri yakai yakwantar yana kokarin rabata da mayafindata cikuikuiye aciki fuskarta sharbanda hawaye alamun ba tadade dagama kukan ba taibacci cire mayafin yayi ya je yasa acoban kayansa sannan yadawo yana karewa halittarta kallo
MOWANA macace maidiri kyakkyawa musamman idan ka nutsu lokacin kallon nata doguwace irin tsayin nan mai amince ko ina acike yake duk dakasancewar ta bamaikauri ba amma sbd yadda gabbanta suke acike baxakataba gane sirantar taba musamman tasaka atamfa ko less saitaxama babba. Takasance mai doguwar fuska tare da dara daran idanu masu haske kyal. Bakinta dankarami tamkar batacin abinci dashi sbd yadda yake das tamkar taxana yadda takeso fatar mai haskece amma ba haske nafari ba haske nagoge duk dabaxa akirata baka ba sbd karmasu karatu su manta itadinfa jinsin larabawa ce. Hancinta kwa gwanin birge wa domin kuwa alokacin dakallon Siyam yaxo dai dai nan saidaya kai hannunsa yashafo hancin yanadan jan tsinin hancin nata ganin takusa farkawa yasa yajanye hannunsa dasauri badan yagaji dajin tattausan ahancin nataba. Daidai kugunta yakalla yakusa dariya sbd yadda yake daukarta yarinya karama wacce baxata fice 23,take da wannan hips haka tab yace afili ashe yarinyar bakwaila bace wayarsa yadauko yadauketa poto yafi sau goma kafin yakashe kwai mai haske yasa na bacci blu jawota yayi jikinsa yana kara mannata akirjinsa wani abu yaji yatafimai tundaga ka har tafin kafansa ya lumshe idanunsa yana kara matseta ajikinsa sbd bakaramin dadi hakan yake yimasa ba, baisan bacci yasacesaba nikwa nace asuba tagari mijin mowana
Kiran sallar asuba ne yafarkar da ita daga baccin datake maidadi sbd wani mafarki take gata acikin daji maiyalwal ciyayi koraye shar gakuma yayyafi da ake kadan kadan itakuma tana kwance kan cinyar wani mutum fuskarsa daure dawani farin kyalle yana tawasa dagashin kanta yanamata hira saita mike tace masa yaushe xamu xama masoya kamar sauran masuyin soyayya saiyace mata
nine nake sonki amma ke yanxu ba sona kike ba saitayi dariya xan iya ganin fuskarka yace eh yana kokarin bude fuskar tafarka
Ganin ta jikin Siyam yasata mamaki yaushe yakawota nan ai afalo tai bacci daddagewa tayi taturesa daga jikinta tana mikewa ganin yadda yatsorata yana mutsike idanunsa
Gamamakinta murmushi yasakar mata yana karasa mikewa
Barka da tashi matar ME KYAU
Ko kallonsa bataiba tafada toilet tare da kullewa saidatagama alwala sannan tabude tafuto kaitsaye kamar tasan inda yasa mata mayafin cover in tabude tadauko mayafinta tafice falo acan tayi sallah
Shma toilet yashaga saidaya farayin wanka tukunna yayi alwala yafuto wasu kaya yadauko masu kyau riga dawando duk yalo kasan wando atsuke yake kayan basu da nauyi yafara gabatar dasalla sannan yadauko alkur ani yafara karatu cike da iyawa cikin muryar sa maidadi
Mowana mamaki yakamata dama ya iya karatun alkur ani yana abu kuma kamar jahili bakaramin birgeta taji yayi ba amma taki barin xuciyarta takankaro masa kimarsa tada da soyayyar datake masa abaya sbd tanaganin kamar saurin karayane da kuma mika kai abanxa donhaka toshe kunnenta ma tayi da duka hannayenta sbd tadaina jin karatun gabaki daya.
Mai gabatar da aiki apart dince tafara noking mowana tataso tabude kasa tadurkusa tana gaisan da ita kallonta Mowana tayi tana murmushi
Lfy klau ya aiki
Ta ce allahamdulillahi ranki yadade maixa adafa maki
Mowana tayatsinebaki kamar taga abin kaxanta
Mekike dafa wa brister?
Yadanganta daranar sbd kowacce rana dakalar abidayake breaka fast dashi kamar yanxu kinga yaulitinin xandafa tea sai cips
Ok nikimin jalof din indomi kadai nake bukata da ruwan tea
angama
Tafice shigar mai aiki kitchin kenan yafito daga bedroom cikin takunsa na isa da ixxa saikamshine ke tashi ajikinsa mai sanyin dadi kamar yadda xuciyar Mowana ke ta fada xuba masa ido tayi sbd yadda yayimata kyau ga wani kyau dayakarayi tamkar bawanda yayi jiyya shekaran jiya ba wayarsa data yi kuka itace tadawo da hankalin mowana taga shima ashe ita yake kallo ko kiftawa bayayi takau dakanta tana murguda masa baki tare da juya baya tana kunkuni
Yayi murmushi yana gewayeta yafice wajen mummy lokacin daddy ma na nan suka gaisa yadan juma suna hira da iyayensa kafin yamike yayi musu sallama mummy tace
Siyam kafadama Mowana takintsa masu shiryata xasuxo daganan xa adauketa xuwa gidan jawwa maikwalliyar xataje can tayimata sai kaje kadauketa kuje wurin walimar
Tohm mummy amma kamar jawwan nagidan nan fa
Eh jiya taxo da daddare mikdad yaxo yadauketa shiyasa nace gwara Mowana akaita can ashiryata kotafi sakewa kaganan dai taron yawa yake xaiyikuma nangabama yan jigawa da abuja duk suna hanya ga hajia umma mutan lagos tace mota uku sukayo ita da nata ahlin yanxu haka maganar dana ke maka suna 'yankura sunkusa isowa kowa xaiso yaga matar Siyam kamar yadda idanun family yabaxu akanka sbd kaki fidda macen aure kaga vaxance baxasuganta ba sbd wani abun saiyaxama magana gwara suganta agun walima in aka kaita kuma su kwakkoma akara gaisawa kafin sutafi
Ok mummy shikenan barito naje danko break fast banyi ba
Yakamata kaje kayi sbd yanxu jama ah nafara taruwa yunwar ma baxakajita ba nikuma banaso kaxauna da yunwa kaji maxa jeka inkashirya kaxo naga adon naka ko
Yayi dariya yana rufe fuska Abba yadagokai shima dariya yake
Toh kaikaji dan mummy kaxo taga wanka niko ai munatare
Yayi dariya Abba walimar ku aitamanya ce bama xauna ba ina tare da mummy na
Yawwa Siyam
Yafice yana dagamusu hannu
Bayan yar aikin tagama komai tajere kan dani tble kamar yadda take kullum tukunna tafice
Kafin yashigo Mowana tabude indomin tafara ci cokali biyar tayi ta aje tana shan tea rabin cop tamike tana mika takoma kan kujera takwanta,
Tunaninsama bacci take shiyasa baibi takanta ba kaitsaye yafice kan dni yafara breaka fast flat in indomin dataci yabude yaga cokali aciki alamun anci ga cop din tea yayi murmushi yamagana axahiri
Dole kirasa jikin kirki kinacin abinci kamar wanda xa adurama danyaye
Tanajinsa tamasa banxa sbd batakaunar wata magana takuma hadasu
Saidayaci ya ishesa yamike tare dakomawa inda take yaxauna
Mummy tabansako nakawo miki
Dasauri tamike tana gyara xama
Inajinka yanxu dama nake kokarin natashi naje mugaisa
Aa tace basai kinxo ba aiba abude miki kaiba now abindaxa ai kitashi kishirya jikinki akwai doguwar riga dana sawo miki saiki sa dahijjabi xandaukeki yanxu ke da masu shiryaki inkaiku gidan sista jawwa
Har yamike yatsaya yana kallon agogon hannunshi
Kifa shirya b for 4:00 xandawo nakaiki
Tohm shikenan Allah yakaimu kaigaidamin da yaya Adeel donnasan wajensa xakaje yanxin
Yajuyo da sauri yana jifanta dawani kallo nabaki da hankali
Kafin yakwala mata harara yafice afasace
Wata yar karamar dariya tasaki tana cewa
Humm bakada hankali Brister sai kagane bakada wayo wlh saika yi nadamar wahalani dakayi abaya saikaraina kanka kaxama abin tausayi agabana tunda kashiga hannu xakaga yadda ake buga wasan mstww taja tsaki tana gyara kwanciyar ta hubba takira awaya amma akashe donhaka batasanma bacci yasace taba
Kamar yadda yafada haka ko akayi bayan la asar yaxo yadauketa lokacin matan daxa su shiryata su uku sunxo tare yadebesu yakai gidan jawwa bai tsaya saurara Mowana ba yabata kayan daxa tai amfani dasu yafice sbd bayaso tabatamasa rai sbd kar jawwa tafahimci wani abu
Tasha goge goge nafata ashafa wancan amanna wancan baki daya sunrikitata hartafara gajiya hakuri kawai take donkar tanunamasu fadanta axahiri tayi kyau fatarta sosai saikuma kamshi take tamkar compny tturare. Ba akammala shiryata ba dakwalliya dakomai saiwajen karfe 8pm,
Siyam dakansa yaxo daukar amaryar tasa domin kuwa Adeel yaje dauko kawayen ta nagida duk da Hamsa'u tundaxu tana tare da mowana
Suman tsaye Siyam yayi sabd yadda yaga Mowanan tasa bakidaya yakasa mallakar kansa duk yawan taron nan da ke gurin bakunya haka yajawo ta jikinsa yarumgume yana murmushi aikuwa jawwa tahau watsmusu kudi daloli sai guda gurin yadauka itako rufe idanunta tayi kam tana jin haushin abindayayi mata Ahankali taturesa tayadda mutane baxa su fuskanci komi ba ta bude mota xata shiga kawai taga yashagabanta nan ga mutane sai huto ake musu gidan tv kuma ana haska bikinnasu sbd mahaifin Siyam bakaramin mutum bane akasar nandonma baya siyasa.
Rufe kofar motar yayi sannan yasake budewa cikin wani ladabin kauna da sigar janhankalin jama ah da tsantsar soyayya yarage tsayinsa yanado kasan rigarta dakekwance akan wani kyakkyawan red kafet da aka shinfidasa tundaga falon jawwa har kofar motar daxa tashiga. Yasa tagefenta yanakamo kugunta Ahankali yajuyata tamkar yar karamar yarinya yaxaunar amotar yagyara mata rigar xuwa ciki sannan yasa hannunsa afuskansa yana kai gaisuwa tamkar a india mai karatu saima kagani mutane akadau tafi da ehu ana jinjinawa Siyam 'yan mata kuma nata jin damasune Mowana.hoto kwa anyi musu kamar ba gobe kafin kace me duniya tadauko sbd yadda hotinansu ke yawo asocial media yafi jamfa ajos ko ina kaji ana labari toh hirar bikin Brister Abdullateef Abdullateef Siyam akeyi da Tasleem tujjani kabeer Mowana
Yana shiga motar kowa yashiga aka mara tasu baya ko amotar baihakura ba janyo kayarsa yayi jikinsa yana shinshinar kamshin jikinta cikin masifa takwace kanta tana cilla masa harara
Kaga ko murmushi dakaga inayi acikin mutane alkur an don infitar dakai kunyane bawai don soyayya ba
Wannan maganar datake yi rada masa take akunne sbd abokinsa Bilal dake tukasukaryaji
Yayi dariya yanamaganar da dankarfi
Nagode amarya ta aikomi xaki yi duk acikin kaunane nidakike gani ai mallakinkine komai dake gareni mallakin kine amma dakin bari munkarasa gidanmu tunda nan cikin motane ko.
Tamkar ta ehu haka taji musamman datafahimci dasigar dayayi maganar kwalla ce ta kawo idaninta fal xatayi magana yasa hannunsa abakinta yanasabakinsa cikin kunnenta
Mutkar baxaki kiyaye harshenki wajen fadan magana ba toh kwa baki na baya tsarki nima kuma kina sake fadan wani magana xankara baki wata kunyar data fi tayanxu kimai da kukannan domin bangama ganin kwalliyar nanba hawaye kuma xaibata adon oya maaidashi.
Saura kiris hawayen su sauko tasaurin tare wa da hannunta tana shashsheka kadan kadan tana kallonsa yace
Damagana
Tagirgixa kai alamun
Aa saiyanxu taga tasa kwalliyar shaddace kalar kayanta jah maidan duhu shaddar saiwani maiko take tanadaukar ido gashin fuskarsa yasha gyara tamkar tafada jikinsa takeji amma ina tafi nan kamar yasan tunanin datake ya kwantota jikinsa yana shafa gefen fuskarta Ahankali
Bansan yadda xankwatanta muku wannan gagarumar walima ba sbd wani abun saikun gani fada baxai fadesa dukaba amma dai kunsan kowacece hajia bera'u da Alhaji Abdullateef uwa uba brister Siyam MEKYAU taro yakai taro mutane daga wurare daban daban sunxo 'yanmata kuwa akaso biyar sune kaso uku sbd kowacce budurwa tana ganin katin gayya ta a social media wata taji sanar wa agidajen redio wasu sunji agidan tv 📺 burinsu suxo bikin suga wacece wannan tasamu Siyam matsayin miji mekyau ce itama kokuma yayo xaben tumun dare cikin wadannan 'yanmata harda sufiyya sulaiman kabeer. Gamamakinta ashe karkarta hajia maryam kawar hajia bera'u ce, donhaka tare sukaxo wajen partyn sunadaga cikin manyan bakin hj bera'u axaune suke cikin mutane kan kujerun da akatanadawa mahalarta partyn hajia maryam takalli mowana takalli sufiyya itama sufiyya takalli kakartata tanacewa haijar mu kinga kwa amaryar
Naganta ko kema kinga abundana gani
Sufiyya tai murmushi
Nagani mana haka Allah yake halittansa kigadai wani ikon Allah hajia wlh ina kallon ta kamar Sabeela sak
Kyace kemadai amma wannan kamar tayi yawa kiga intana dariya mana kamar sabeela najin shakiyanci kinga haura kimata hoto mugani
Ahhh badole bama hajia aidole nakaiwa sabeela hoton 'yar biyunata don koshekara xasuyi daya da amaryar nan
Sufiyya taje kusa da mowana sukai gaisa dandanan mowana taji sufiyya takwanta mata arai itama sufiyya taji tana kaunar mowana sunhotina sosai mutanene sunyimata yawa aka amma ahaka sai da sufiyya ta kukuta tasamu numban mowana awajen Hamsa'u sbd taga sundan fi kusa
Wakar bikin uku akayi mawakannan kuwa masu tashe kuma akejidasu akasar nan sunhalaccin bikin
Naxir sarkin waka da hamisu breka gwanja ma yaje umar m shareef shima nagansa daga baya naji hussaini danko yasaki sautinsa anfara chashewa cikin wakar komai nisan tafiya kunsan danko badai kida ba wakarsa nawadatuwa da duka wanda komi kaudakanka saika taka,
Bayanshi hamisu breka ne yadora tohfa gamai xamani wajen wakokin soyayya dakawata ta kaji tamkar kanarke sbda so sai hamisu breka Siyam har wani kara matse hannun mowana yake anasa sbda shauki dakuma xaxxafan so dake motsa masa kirjinsa nasamu farinciki
Kai jama a ansha paty ankuma gyagije sbd ankashe kudi bakadanba dik wanda yaxo fita xai amsa leda maidauke da hotinansa ciki kuma atanfani da littafi da biro sai lemo,. Siyam da amaryar sa mowana sunsha kyau da ado afuwan masu karatu karkuji bansiffanta yadda amarya tashakyau ba brister Siyam MEKYAU ne yagargade ni akan hakan yace karnasoma sbd yana kishin kayar sa bayaso kokadan yaji tabirge wani bayanshi.
Adaren saida aka mika su gidansu wanda yahadu ba acewa komima abin dai namasu dashine. 😁😁😁👍.
Amma fa gidan Siyam wayyo Allah musamman falo nabiyu inda xairinka xama shi da sweetinsa tohm littafina fa karamine baxai isaba wajen xayyana yaya gidan yake ba
Kuka mowana take sosai tanarike Hamsa'u dakyar dai tacikata suka tafi bayan yashigo tamike tafada toleit bata budeba saida tatabbatar yabar dakin tafito tana leka falo tagansa xaunekan darduma yana karatun alkur ani amma axuciya bakinsane kawai ke motsa wa komawa tayi tarufe kofar bedroom dinta sannan tacire kayan da akasamata tawatsa ruwa tasa kayan bacci da katon hijabi takwanta. Kotakan ledar data gani tsakan dakin batabiba tana mitar ansamata hirgegiyar riga duk tasamata ciwon jiki tasaki tsski
Game da Adeel kuwa daren ranan kwata kwata yakasa bacci musamman idan yatino lokacin data sameshi kafin atafi walima yaxo kawomusu lemon tsani xa ai amfani dashi agyaranjiki
Tafito tashiga motar kamar abin arxiki
Baka tunanin kanka dakaina yaya Adeel kayanke wannan mummunan hukuncin maicike da makanta. Kacutar dani kacutar dakanka domin kanema ma wani

Please Login or Register in order to submit comment