Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shine
kaje ansaka adaki ankitsamaka karya
dagaskiya xakaxo mana dawata
maganar daban kunji fa xancan nan
jama ah Aminu kunaji

Aminu ya ja tsaki

Mustww Ai dama kune bakusaniba
yaya Abdul kyamarmu yake xama
madakukaga yabarmu munyi atare
dashi aidankar yakoremune duniya
taxageshi kuma wannan abun dayake
faruwa duk hadawar ta wannan
munafukar matar ne, yanuna hajia
bera'u
Karaf kalmar tadira kunnen Siyam
ransa yabaci yamike hajia da Alhaji
Abdullateef suka daga masa hannu
baisan hawaye sunfara xuba aidanunsaba yamike xaifuta kawu
babba yadakatar dashi

Inaxakaje kuma aisaikatsaya
katabbatar mana da abunda iyayenka
ke fada dagaske kafasa auren su'adaat
dik da aurenta dolenkane kobakaso
wlh tunda ita tana sonka

Tamkar wani xaki haka yajuyo yakalli
kawu babba idanunsan nan sunkada
sunjawur

Yafice kawai abakin kofar falon yatsaya
tare dajingina bayansa dakofar
hawayene kawai ke futa a idanun sa
su'adaat wacce tabiyosa tundaya futo
kasancewar taga maganar
taxamafada kuma duk da shi Alhaji
Abdullateef baitankamasuba.

Kayi hakuri karwannan abunyajawo kaji
kadaina kaunata
Afasace yajuyo tamkar wani
mayunwacin xaki yanajifanta dawani
mugun kallo maicike dawata
tsantsrtsana,

Nadade dama inafada miki bantaba
kaunarki ba daidai da scound daya
donhaka dake da mutuwata wlh duk
daya kuke natsaneki dake dadik wanda
yake tare dake yar marasa mutumci
wlh iyayenki sunyi asarar rayuwa
dabasu san komiba saikwadayi da
hassada, wlh kaihcon tushenki ki addu
ah kawai ki mutu koxaifimiki arayuwa

ran su'adaat abace takallesa tana wani
dan murmushi mai ma anoni dayawa

Ehlallai koda bahakaba dole kam yanxu
nayarda amma inaso siyam kasani
iyaye basu fi iyaye ba xakaimamakin
duk abundaxanma yanxu amma nasan
wacce xanmawa

Takoma cikin falon dagudu tana kuka
bayanta yabiyo shima sbd yaga me
xatayi kamar yadda tafada

Daidai lokacin dasuka gama shigewa
Mowana ta karaso sbd me aikin hajia
ce tarakota gani lokaci natafiya tanaso
takoma gida dawuri shiyasa tace bari
taxo nan tamata sallamar itama shiga
tayi kawai cikin falon kaitsaye
saitatsaya kuma chak! ganin
abundake faruwa kamar ba manya
agurin,
Su'adaat ce tsaye akan hajia bera'u
tana kuka tanamaganganu kamar haka

"Wlh saikin saki kurwar siyam ya aureni
dolenki natabajin mani mayyar uwa
irinki inbaki bari an auri dan nakiva
kexaki aure shi toh bari kiji wlh saikin
nadamar abundakike wlh hajia ke.........

Tauuuuuuuu kake ji andauketa da marimari
ankuma dauketa da mari Siyam ne
amma kafin yagama sauke hannunsa
kasa yaji karar mari. Tassssssss matar
kawu salim sakina tadauke mummy
da wani kykkyawan mari, dikkan
karfinsa yahada xaisauke akanta yaga
wani kykkyawan hannu siriri dogo
atsakaninsu kafin kowa ya ankara
ansaukewa sakina mari har uku ajere

Jikake tasssssaaakauuuuuuuu
fauuuuuuuuu, sannan taja tunga
mamakine yabayyana afuskokin duk
masu xaune agun ciki harda Alhj kawu babba kawu salim Aminu mariya
suwaiba su'adaat sbd bakuwar fuskar
da basu saniba ce tamari sakina ran
kawu salim yabaci ganin anrasa me
magana yataso xai rufe Mowana da duka siyam yadamke hannunsa dakyar
aka kwace sa daga hannunsa mariya
da suwaiba suka yo kanta can maxan
nafama da Siyam da kawu salim da
kawu babba sbd saimasifa yake
Mowana taja damara da mayafinta
hajia bera'u tataresu

Wlh tallahi narantse da Allah kubargani
inakyaleku duk kashin dakukeci akaina
yau taxo karshe domin duk wacce
tasake tataba wannan yarinyar
sainayimata mummunan tabo
arayuwarta,

Sakina tayo kan Mowana hajia
tadauketa da mari taxube tanakuka
tana ehu kamar ankasheta su'adaat
dake tsaye bayan mariya babarta
tadauki glass cop tafasa tacillowa
Mowana kwalbar Allah yataimaka
Siyam yagani lokacin Abba narike
dashi yakwace cikin xafin nama yayi
wani sufa yatare glass din aikwa
hannunsa bakaramin yanka yayiba jini
yafara xuba , Alhaji Abdullateef
yafashe dakuka yana xubewa kasa

Ya Allah wannan wacce irin futinace
yaya babba dan Allah kukasheni
kuhuta natabbata xuwa yanxu raina
kuma kuke nema
Mowana ce taruga gurin Siyam
tanarike hannun daya yanke din tacire dankwalinta tadaure masa gun
idanunta tab kwalla yayimata wani irin
kallo maicke da tambaya tamatsa
gefen hajia tana tsayawa,

Duk suntsaya anyi cirkui cirkui saikallon
kallo akeyiwa juna Siyam yatadashi
yamike yakama hannun mummy yanufi
kofar futa

Duk sainayi maganinku kuma
mahaifina yafi karfin ku wlh saikun
mutu kunbarshi araye yan hassada
kawai.
Mummy tayi murmushi kwarai kuwa
Siyam nayafemaka duniya da lahira
fadamusu duk abundayake ranka
wanda kadade kana tara wa inhanaka
furxarwa,
Takamo hannun mowana suka fuce
Abba nadafe dakirjinsa Siyam kuwa
mamakinsa shine meyakawo Mowana
nan harta shigar ma mamansa fada

Suna fita tayafa mayafinta xata tafi
hajia tarike hannunta

Bansan wacece keba

Basaikinsan wacece niba shidama
mutumin kirki aijama ah ne dashi
masuyawa sbd yawa wasu ba
baxaisansuba toh inacikin mutanen ki
wadanda kikataba yima alkhairi naxo
nasanar miki munsamu
abundamukeso xanbar aiki karkashinki
saikuma naxo nasamu wannan rikicin
xuciyata takasa hakuri da wannan
rashin dah ah da yaro xai iya yiwa
babba maganar dayagadama, naga
tsantsar rashin adalci darashin taRbiyya
amma kadanne wannan akan wanda
nagani tun ina ficiciya, nabarku lafiya

Taji anrike hannunta tanajuya taga
hajia
Sunkuyar dakai tayi sbd wani nauyin
hajia dataji tanaji
Mummy tarumgumeta

Yarinya ako ina kike kuma ko wacece
ke natabbata yar manyan mutanece
yanxu nafara tuna lokacin danasanki

Niba 'yar kowa bace xantafi

Abba da duk abunda suke yana kallo
yarinyar taburgesa dama ta amince ta
auri siyam dayayi sa ar mata,

Mummy ce taroketa akan taxo suje
wajenta. Dakyar ta amince Siyam nabiye
dasu abaya saiyanxu yake hasko lokacin
data cire mayafinta tadaura asaman
kanta dankwalinta kuma tadaure masa
hannunsa dake xubar jini kyakkyawa ce
ga diri komai full ofshin gata siririya
musamman daga cikinta kamar batacin
abinci kugunta kuma tanada hips kirjinta
acike dai dai santalele amike kamar
balarabiya idanunta manyane hancinta
siriri dogo kamar fuskarta haka yay ta
ganin suffarta a idanunsa saikawai yayi
murmushi yanasosai kai suna hirada
mummy yasasu agaba saikallonta yake
lokaci xuwa lokaci yana murmushi
tagansa amma sai tayi kamar
batagansaba saidatayiwa hajia alkawarin
xata dawo gobe sannan hajia tabarta
tafuto tasa direba yakaita. Siyam
yamatsa kusa da hajia..

Koda goben tayi saiwajen musalin karfe
hudu Mowana tasamu momma tabarta
tafuto shima akan xata amso kudin
albashinta daba abata ba, cikin hijabinta
harkasa tafuto tahau napep
gamamakinta wata budurwa tasamu
taxo wajen hajia axaune take akusa da
hajiar sai shagwaba takema hajia tana
magana
Itakuma hajia saiwani riritata take tana
lallashinta,
Sallamar danakarayice tajanyo hankalin
mummy kaina,
Fuskarta cike da murmushi ta karbe ni
hannu 2 tasa akakawomun ruwa da lemo
dakyar na iyashan ruwan tanadan jana da
hira kadan kadan ina tayata wannan
budurwar ce ta mike tana hararata

Mummy nifa tafiya xanayi tunda kinyi
wata bakuwar
Mummy tayi murmushi

Haba Ismat tunyanxu kuma aidakinjira sa
yadawo yamayardake gidan ko

Ta rausayardakai gefe saikuma tai dariya

Tohm mummy bari naje nakwanta
najirasa
Shikenan toh

Tahaura sama tana kara jifana da harara
wacce bansan tamayeba naga dai
tundana shigo dama take min wani
banxan kallo da harara,

Mummy tai murmushi sannunki navarki shuru ko
Hmm aa wlh jawwa ce ko mummy
Aa audama bakisan jawwa ba ke ko eh
toh baxakisanta bagaskiya sbd lokacin
dakukaxo ita anmata aure amma aitana
xuwa kuma kawai dai ba ahadun bane,
wannan Ismat kenan wacce Siyam xai
aura ai, yau anxomin yini ne daru yatashi
kuma ance xa atafi

gaban Mowana yayanke yafadi tadafe
kirjinta sbd wani abudake shirin fasa
kirjinta yafuto datakeji yana yunkurowa,
kwata kwata tadaina gane komi tashi
tayi jikinta narawa kanta dandanan
yahau ciwo dakyar take daga kafarta
tana tafiya hajia bera'u takirata amma
batamajin kirana kawai jefa kartata take
ako ina tasauka hartabar gidan

hubba datahangota dagudu tabiyota
tacimmata dakyar sbd wani mugun sauri
da Mowanan take

Lfy Mowana menene yakawoki kuma
nimafa da kokarin hada inawa inawa
nake natafi gida sbd kindaina ko
albashin ki wancan kikaxo karba

Bata kulata ba tarike hannunta ganin
xatanufi titi kaitsaye dakyar tariketa
tatari me napep suka shiga lokacin data
kaita gida momma ta tsorata da halin
dataga 'yar tata aciki dik da har yanxu
bawanda tabuda baki taiwa magana, har
hubba tabar gidan bataimagana ba
saikukan xuciya take.
Haka momma tagaji takyaleta sbd tayi
tayi da ita tafadamata amma abun ya
gagara haka dasafe karfe goma nayi
tafuce kasuwa sayo musu kayan abinci
dakudin da Adeel yabata,

Lokacin Mowana tasamu damar sakin
kukan fili dafurta damuwarta har hubba
takirata akan xataxo tarakata unguwa
inna ta aiketa

MUNDAWO.
Momma tashigo gidan kanta dauke
dakaya niki nikigawasu kuma ahannu
yaro yabiyota dasu

Yawwa sabi u sannunka dakokari
unguwa wannan kaima ka kashe

Ta amsa kayan tanabasa nera 50,
yaron yaji dadi dagudu yafuta
yanajindadi jingidan shuru yasa
taitunanin ko mowana tayi baccine
donhaka xamatayi awajen
saidatagama bubbude kayan avincin
ko wanne tagansa takai cikin dakin
tana kaidubanta ga gado amma bata
ga mowana ba can gaban mirorr ta
hangota kanta akife.
Toh Mowana mekuma kike anan
daranar nan
Takarasa kusa da ita tana dago kanta
saita ga jini afuskarta tadaure goshin
da dankwali
Salati tayi tana girgixata nashiga uku
menene yasameki Mowana

Bude ido take kadan kadan tana kallon
momma kafin tadafe goshin
dahannunta
Wash momma kaina

Rikemata hannu tayi suka fita waje
haske
Miyasameki nace ehhye

Murfin sif inmune yafadomun naje
daukar hijabi
Subhanallahi ya salam! Toh sannu
muje gaban makwararan ruwa
nawanke miki sai asa farin kwalli
agurin.
Ruwan tafara debowa sannan takama
hannunta suka karasa magudanar
ruwan tawankemata tasamata
farinkwalli takwanta ko xata iya yin
bacci.
Hajia mamaki yahanata motsawa
daga gurin yanayin dataga Mowana
tashiga datayimata maganar ismat
amatsayin matar da Siyam xai aura
shiyake tadawo mata sbd abunda
tanundin lallai akwai wata atsakani
toh ismat ce tasauko tana dariya
mummy baidawo ba ko
Eh kinga aiko yadawo yanxu yana
wajen sa saiyayi wanka ya ke
shugowa nan,
Tohm bari naje nasameshi acan

Shikenan
Tafuce dasauri bawani kamunkai
kamar ba agaban sirikarta takeba

Shugowarsa wajen kenan yana ciccire
kayan jikinsa wannan yanadaga cikin
al adar Siyam idan xaiwanka saiya
tube kayansa duk sannan saiyashiga
haka idanyagama wankan yadauko twil yadauro akugunshi,
Motsin shugowa dayajine yasa yayi
saurin fadawa toleit yadauko twl
yadaura akugu yafuto falon
Wacce yagani atsaye ne yasa yakara
hade rai yana gyara tsaiwa
Barka da yamma nasameka lfy

Yakara hade fuska

Lfy klau
Takafesa da ido tanakarewa
kyakkyawar halittar jikinsa kallo tanaji
kamar tafada jikin sa tarumgumeshi
kotasamu sassaucin masifar sha
awarsa datakeyi,
Kije wajen mummy inaxuwa

Yayimaganar ahasale sbd dik yagaji
da irin kallon kwadayin datakeyimasa
kamar wata tsohuwar mayya saibin
jikinsa take dakallo musamman daga
faffadan kirjinsa xuwa cinyarsa,

Tamatso kusa dashi tanawani kashe
masa ido saiwani narkewa take
hartakarasa daf dashi tayadda xasu
iyajin numfashin juna takashe murya
cikin salon janhankali take magana

"Haba sweethoney karkadamu
xanjiraka anan kaje kayi ko naxo
natayaka.
Tana maganar hartai nasarar sa
hannunta akirjinsa wani irin yanayi
yaji bakidaya kasala tasauko masa
yakasa jure irin abubiwan
datakemasa cikin yanayin dashima
baisan yashiga ba yafara shafata
yana rumgumota jikinsa gabadaya
tafada kansa suka xube kan kujera
suna fidda wani irin numfarfashi
bakinta tadora akannasa tana kokarin
cusa harshenta cikin bakinsa yadatse bakinsa yana tureta daga jikinsa
kamar wanda yayi bacci yafarka haka
yafara kallonta yana turota kasa
tafadi dabar tana dafe kugunta
numfashi yake dakarfi karfi kamar
wanda yayi gudu

Biri yayikama da mutum tabbas dama
haka kike 'yar iskace ke toh
kwalelenki wlh nafi karfinki kuma
barikiji nafadamiki anyi walkiya ta
haskoki donhaka nafasa aurenki
baxan auri watsatstsiya ballagaxa
irinki ba
Nadama dadana sani ne suka
mamaye ismat kunyarsa ta rufeta
miyasa takasa maida kwadayinta
akansa harsai data nunamasa halinta
naxahiri gashi yanxu gajen hakurinta
xaijawowa kanta asarar rasashi har
abada, kuka tafarayi yanakokarin
shigewa dakin tatsuguna akan
gwiwoyinta
Dan Allah kayi hakuri wlh ba halina
bane sharrin shaitan ne nima bansan
hakan yafaruba wlh

Wani dogon tsaki yaja yana rufe kofar
bedroom din yashige toleit xuciyarsa
cike dahaushin abundayafaru sam
baisan meyarinyar nan take nufi dashi
ba datuni tasa ya aikata xina kenan
hmm yagirgixa kai jikin mudubin dake
manne acikin toleit din yakarasa
yanakallon kansa ajiki shikansa yasan
yahadu kuma dik macen data kallesa
sau daya xata so takuma kara
kallonsa sau goma, musamman,
ayadda yake kallon kannasa amadubi.
Taba kasin barsa yayi tare dasakin wani murmushi kayatacce yana nuna
kansa
Kaii Siyam yakamata kayi aure fa
bakaganin kafara girmane

Yayi dariya

Bayanxu ba

Saikuma yaxaro ido yanayin fada

Tohh kabari saika tsofe babu dah
balle jika
Ummm aiwannan mayyar tawa baxa
tabarni ba aboki harfa nafarajin nima i
am inlov fa,
Saiyasosa kansa yana murmushi
tamkar yana gabanta

Tohm kadaina tantama sonta kake aboki
Yarufe idanunsa yana dariya kafin
yasakarma kansa shaya

Mafi yawancin lokaci Siyam nayin
magana dakansa amadubi tamkar
dawani abokinsa sbd yadda yake jin
abu atare dashi indamuwace
yanasamun sassaucin abun, kwana
biyu baki daya yakasa samun
nutsuwa axuciyarsa ba abundayake
damunsa irin tunanin Mowana da
muryarta lokacin datake masa
magana, ba abundake daukar
hankalin ta dashi kamar fuskarsa idan
tanakallon sa idan yakalleta shima
saiyaga idanunta nakan fuskarsa tana
kokarin hade idanunsu guri daya, bata
taba kokarin matsawa indayakeba
yayi murmushi sbd tabbas ranar
dayayi mata kallo nakarshe yaga
sassaucin soyayyar datakemasa
acikin idanunta lallai kodayaushe xata
iya daina sonsa inaaaaa

Yace axahiri yana dafe kirjinsa dake
masa wani iri dikkan numfashinsa
yana futane da sunan ta yarasa har
yaushe ne tashige masa xuciya haka
taxamemasa komai ita ciki da waje

Yaronkirki kashigo

Ya Kalli mummy dake masa magana
adan yanayin damuwa

Eh mummy yanasameki

Lfy klau ya office da aiki

Yasauke kansa kasa

Allahamdulillahi

Can shuru yaxiyarci gurin kafun
tafuskanci kamar yanada damuwa
kuma kwanabiyu yafada duk yayi
wani xuru xuru
Siyam menene yakedamunka naga
kafada gashi kwana biyun nan idanka
shigo saikaxauna kayimun shuru da
alama kamar tunanin wani abun kake
kuma komenene yanadamunka
dama ashe har akwai wata
damuwarka dabaxaka iyasamuna
kaxayyana mun ita ba nasani ehhyye

Yaja numfashi

Mummy kiyi hakuri wlh bansan
yayaxan miki bayani bane

Tadawo kusa dashi taxauna

Karka damu kanaji ni mahaifiyarkace
kuma dole nixakafadamawa dik wani
damuwarka nafuskanceka, donhaka
inajinka oya fadamun menene
yakeson damunka,

Yajidadin yadda mummy taimasa
maganar donhaka cike dakwarin
gwiwa yashiga yimata bayani akan
abunda Ismat tayimasa da halinta
datanunamasa karara,

Mamakine yarufe mummy game da
abunda taji Ismat tayi duk da dama
wani lokacin tana kallon yadda take
shigema Siyam din koda kwa
agabantane
Hum toh yanxu ni bera'u yakakeso ayi
da Abbanka gobe yakeso yaturo
anemo maka auren nata

Umm tohm mummy kaitsaye ai abun
abayyane yake tayaya xan amince na
auri watsatstsiya mummy kema
baxakiso sirikarki ta kasance ahakaba
shiyasa ma yanxu ni harnafara wani
tunanin daban

Takallesa

Maganar ka haka take dole afasa
xuwaneman auren nan amma wanne
tunani kuma kafarayi?

Yakalleta yana sosa kansa

Mummy nafara tunanin amincewa da
mayya ta ne kawai sbd naga ita
kamar tanada banbanci dasauran
'yanmatan nan, kuma itakadaice
macen danafara tunanin ta axuciyata
mummy bantaba jin wata mace
axuciyata ba kokadan amma daga
karshe yanxu mayya ta tayi nasarar
cafke min heart

Murmushi ya subucewa mummy
wannan shine karo nafarko data
tabaji Siyam yace wata taburgesa
haryaji yanasonta lallai yau ranar
farinciki ce awajenta da Allah yanuna
mata lokacin da Siyam xai aure donji
take tamkar anyi auren ne angama
sbd tunda yasamu wacce yakeso kwa
toh dole yabar Ismat kodakwa ba
asameta da waccan matsalar ba

Mummy tunanin me kike dan Allah
karki ki amincewa da maganar
danaxo miki da ita akan mayyata wlh
inasonta kuma da itane kadai xan iya
rayuwana amma duk yadda nake
sonta mummy mutkar kika nuna
rashin amincewar ki akanbatun wlh xanbarta gwara narayu cikin kunar
xuciya narasa abunsona, nakasance
mai biyayya agareki komai xan iya
rabuwa dashi amma bandaku.

Tarumgumeshi tana dariya

Allah yayi maka albarka Siyam Allah
ya albarka ci rayuwarka yadda kake
girmama bukata ta kake mana
biyayya Allah yabaka xura ah masu
yimaka kuma masu albarka, umm
karkadamu bawai ban amince bane
aa wlh saikaji irin dadin danaji acikin
xuciyata shurun dakaji nayi godiya
nake tayiwa Allah dayanuna mun
wannan rana danake tafatan xuwanta
gareni, wacce kaidakanka xakaxo
kasameni da labarin kasamo matar
aure wacce kakeso, kagakwa wannan
ai abun farinciki ne, don haka yanxu
abundaxa ai kafadamun sunan
yarinyar naji saikiranta kake da
mayyarka sannan kuma a inatake wlh
har na matsu inga sirikartawa,

Yarufe fuskarsa da hannunsa yana
karajin soyayyar mahaifiyar tasa
nakara karuwa acikin ransa

Mummy aikinsanta kuma mummy
xaki kara kara farinciki idan kikaji
wacece fa
Tai dariya

Kaga banason jan rai donkaga nabada
hankalina gunka ko toh wacece
danasanta kasan fa mutane dadama
nasansu baxan iyaganewa ba
inkabarni da na duba,

Mummy xanfadamiki amma kibari
sainadawo daddare

Tohm shikenan Allah yakaimu
anjuman kaga lokacin Abbanka
yadawo ma
Mummy xamu fara maganar dake
kafin Abba yasani sbd saikin fara
masa maganar Ismat akan anfasa
xuwa neman gobe dan Allah sbd
saiyaga kamar yawo nakemasa da
hankali
Hakane toh xanfara masa maganar.

Daddadare Alhj yagama cin abinci yaje
kiran da hajia sanawiyya mahaifiyar
sa takemasa acan yasamu kawu
babba da kawu salim da Aminu shima
yasamu gu yaxauna bayan sungaisa
da ita yagai dasu kawu ammasuka
sharesa sunadauke kai yace

Hajia gani

Tadago kai takallesa tana kallon sauran dake xaune

Abdul abundakayi kakyauta kenan? Yadago kai

Hajia Allah yahuci xuciyarki amma
bansan menayikuma ba saikin fada

Dama haka xakace kamar yadda salim
yafadamun toh kasani banjidadin
abundaya faru ba shekar jiya kuma
raina yabaci dajin abundaya faru
donhaka karkasake insake jin haka
tafaru kuma akan duk menene abun
yafaru
Kafin yayimagana kawu babba ya
amshe
Hajia ainafadamiki akan maganar
Siyam da su'adaat ne bayan angama
maganar auren kaf yanxu kuma daga
baya matarsa taxigesa tahuremasa
kunne yadawo mana da maganar
Siyam baxai auri su'adaat ba akwai
wacce yakeso kuma duk kanxon
kuregene saida yabari su'adaat
takamu dasoyayyar sa yake neman
yarusa maganar
Hajia takalli Abba

Abdul kanaji Hakane xancan muttaka?

Abba yadagakai
Hajia kamar yadda yafadamiki toh
kusan hakane amma maganar
gaskiya Siyam dama bashine
yakeneman su'adaat ba itace
takesonsa ganinhaka kuma yasa
nace ma kawu babba dayaxomun
damaganar toh shikenan saimu
hadasu ai kawai saimuka aje
maganar akan hakan, shikuma Siyam
ashe agefe akwai wacce yakeso
andankwana biyu saiyaxo munda
maganar yasamu matar aure nikuma danaga haka sainace shikenan tunda
dama baisan da maganar su'adaat ba
aisai abart sbd kar axo ayi abundaxai damu kowa.
Dama haka xakace mana amma
bashine abundakake nufiba kana
gudun jinin mudai kawai shine
abundakakeso kace

Kawu salim ya amshe maganar cike
dafada
Ya isa
Hajia tadagawa kawu salim hannu

Abdul naji abundayafuto daga bakinka
yanxu kirawo mun shi Siyam din

Abba yadauki wayansa yakirawo
Siyam dayake baiyi nisa ba yashigo
wajen mummy kenan koxama baiba
yagakiran Abba yanajin abunda
Abban yafadamasa yamike

Mummy bari naje wajen hajia Abba
nakirana wai hajia nasan ganina,

Toh Allah yasa lfy jeka

Yafice.

Cikin nutsuwar sa yayi sallama
yashiga kaitsaye wajen kahkar tasa
yanufa yanasakin murmushi yaxauna
kusa da ita

Angai da amaryar Siyam yaya kike

Ta hararesa
Yo inaruwanka da yanake aidakaso
sanin halin danake ciki dakaxo inda
nake tunkafin nakiraka
Tufa nake kwana biyu ne banaxama
hajiata
Naji baka ganin mutanen dabaxaka
gaishesu ba
Yakalli su kawu babba datanuna masa
shi baima gansuba sbd baisa
hankalin sa awajen ba,
Yagaishesu dakyar dakyar suka amsa
kamar antuttura musu tuwo abaki.

Umhum yawwa Siyam

Ya amsa
Kanajina nakirawoka ne sbd wani
magana dayaxo gabana yaudinnan
kuma banjidadi naso saina batawa
shi uban naka rai wlh amma nabari
sainaji tabakinka sbd yadda
nafuskanchi masalar kamar daga
wajenka tafara toh bafanason
abundaxaixo yahada ka da iyayenka
muttaka da salim da aminu tamkar
Abdullateef suke awajenka
iyayenkane suma tunda kannensane
duniyama tasani toh wai ko me
sukayimaka don ubanka aikai mai
tsugunawa ne harkasa kabasu hakuri sbd darajar su ma iyayenkane,amma
hardakai acikin maganarsu da shi
mahaifin naka to inma ba xamaniba
natabajin haka toh kasani kwas
kamin karya amaganar daxanmaka
yanxun wlh sainayaga maka rigar
mutumci agurinnan,

Yasunkuyar dakai ransa abace sbd
baisan mesukaxo suka kitsamata ba,

Allah yahuci xuciyarki hajia insha
Allahu xa akiyaye

Maganarka da su'adaat ya ake ciki
kaine kace kanasonta saidaiyaye
suka shuga kace kafasa kokuma yaya

Hajia nitsakanina da su'adaat
basoyayya saita xuminci sbd
nibantaba cewa inasontaba itace
takenuna tanasona har akaso
ahadamu kuma abun baiyuwuba sbd
yanxu nasamu budurwar danakeso
nafadama Abba shine abundaya faru,

Toh shikenan

Kaiyanxu inaso nafadamaka wani abu
nabaka wata biyu kayi aure idan
bahakaba wata biyu tacika saika auri
dik wacce nalalubo maka koda ba
su'adaat dinba donhaka xabi yarage
naka kokayi kokarkayi kaikuma
muttaka kabu
hakuri abar maganar nan tahadasu
sbd shi aure nutsuwa ake bukata ga
ma abotansa kaga kwa inba soyayya
babu wata cikakkiyar nutsuwa, kuma
katuro mun su'adaat din nan taxo

Kaikuma Abdullateef kabawa yayenka
hakuri akan abundaya faru sannan
kuma karnasake jin wani abu
makamancin fada yafaru akiyaye wlh
nashafadamaka cewa karike yan
uwanka ko bayan raina banyafe ba
kabarsu sutagayyara,
Abba tamkar yayi kuka
Shikenan hajia xa akiyaye nagode
siyam yakalli babannasa yanayin
dayashiga yarike hannunsa yana
dagamasa kai alamun rarrashi hajia
taitamusu nasiha daga karshe
tasallaame su,
Kawu babba
Ai insunsan wata wlh basu san wata
ba mu harmu Abdul xai wulakanta wlh
sai munmaganinsa

Kawu salim yace
Aha yaya aikaine nafadamaka kawai
musa akasheshi muhuta saimu
kwashe dukiyar duka mu bar kasar
wlh yaya har hajia xamusa akashe

Subhanallahi Aminu yafada dakarfi
yana girgixa kai
Wlh baku isaba yayaxakuce akashesu
dashi da hajia akanme kudi kudi dai Allah yakyauta baxantaba amintaba
dawannan maganar hajia tayimana
gata tunmuna yara kananu hajia taci
kashinmu taci futsarinmu tunmana
kanana bansan mahaifiyarmuba
yakamata wani abun murinka
sassautawa sbd mutanen nan
idankuka duba basa neman mu
dasharri kullum alkhairi suke neman mu dashi, gunji fa dakunnen ku
abundata fadamasa akanmu ko
wannan bai isa yasa mugane gaskya
gaskiya ceba yay.........

Kaga munji

Kawu salim yadakatar dashi

Dama kasaba samu gaba kaitamana
wa'axi toh munsan da masallaci
donhaka tunda kaineyayan namu
inkagama kasamemu

Suka tashi suna hara rarsa

Yayi shuru xuciyar sa nabasa
shawarar karyabi shawarar su

WAYE SIYAM
sunan sa Abdullateef na gaskiya
anakiransa da siyam sbd sunan
mahifinsane
Alhaji Abdullateef dah awurin hjia
Sanawiyya takasance mace
maihakuri dasanin yakamata

Itace matar malm umar tabiyu sbd
tatarar da uwar gidansa wato inna
xubaida alokcin tanada yaranta biyu
muttaka da salim xuwan sanawiyya
baisa hankalin inna xubaida yatashi
ba sbd macace ce mai hakuri da
tsoron Allah don haka taxauna da
sanawiyya lfy kalau tamkar kanwarta
haka tadauketa har ita ma lokacin
tasamu ciki tahaifi Abdullateef byan
wasu shekaru biyu inna xubaida tasamu ciki tahaifi Aminu lokacin
shekarar Abdullateef uku da sati biyu
ko yaye aminu inna xubaida batayi ba
sakamakon wani ciwon ciki
maitsanani tarasa ranta mlm umar
yayi kuka sosai shi da sanawiyya
musamman idan yatuna yadda take
mace mai hakuri da kawaici haka
sanawiyya tahada yaran duka
awajenta tarike bayan rasuwar inna
xubaida sanawiyya tahaifi yaranta
'yan biyu duk mata amma suka rasu
bayan suna haka takuma haifar danta
namiji amma saida yafara tasawa
shima ya rasu, to tundaga kanwannan
ne bata kara haihuwa ba yaxama
Abdullateef shikadai ne dan datake dashi sai marayu nawajen inna
xubaida kishiyar ta wadanda tarike su
tamkar ita tahaifesu, balaifi mlm
umar mutum ne maikokari yakasance
maihakuri da sanin yakamata sana ar
dinki yake yi 'ya'yansa maxa wani
babban abokin sane yasasu
makaranta kuma yadauki nauyin duk
dawainiyarsu lokacin da muttaka da
salim suka xama yanmatasa haka
yarasu lokacin al amura suka
cakudewa sanawiyya ga marayu
amma haka Alj ishaq yacigaba
dadawainiya dasu daga karshe yace
xai aureta tace baxata auresa ba sbd
matarsa aminyartace atakaicedai Alhj
ishaq shine yadora Alhaji Abdullateef
akan harkoki nakasuwanci kafin
yakammalla karatunsa yafara aiki
ababban compny da Alhaji ishaq
yabude na karafuna, yadorasu shida
'yan uwansa amma yaxama cewa
suna ha intarsa tunyana hakuri har ya
daina yakoresu tareda basu jari sayi
wani harkar shikuma Abdullateef
yacigaba daxama akarkashinsa
haryasamu nasa arxikin yayi aure
matarsa bera'u yasamu kudi sosai har
yabude gidan mai da compny yin
robobi da wasu asibiti asibiti biyu
donhaka ganin yayyensa nata
gararanba ba aikinyi yasa yajawosu
jikinsa yasasu akan dokiyarsa
sukuma suke abundasukeso daga
karshe yadauko su yadawo dasu
gidansa wanda ya gina mai part
10,matarsa yaransu biyu nafarko
Siyam maibinsa itace hawwa u, akece
mata jawwa sbd sunan maman bera'u
ne,
Wannan shine tushen Siyam atakaice
sai ammin hakuri sbd littafin
karamine shiyasa wasu abubuwan sai
anyanke su.
Siyam kyakkyawa ne ajin karshe sbd
namijine cikakke

Please Login or Register in order to submit comment