Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiyi dubunai shekaruma karkiyi Amma kinatareda kabir nee yin sallah wajibine. Before i show you my true Colour go now.

da alama gabadaya Amriya bata fuskanci meyace bah.

Tace. Magana.. Kayine.. Cikeda takaici kabir yace Aa bah magana nayi bah waka nakeyi. Wato tsabar kin maidani mahaukaci nayi mgn kuma kina tambayata mgn nayi tashi kije kiyi sallah ko ranki ya bacii banason bujiramewa Dad dina amma datunan kisha mari wlh.

Tashi Amriya tayi tanufi toilet tadauro alwalah tayi sallahn taa. Ta tashi tanufi kan gado inda yake

Dakamata tsawa yayi kee ina kike shirin zuwa. Amriya tace kwanciya.. Zanyi..

Kabir yace ni dake a gado daya impossible, na iya hada gado daya da karuwan titi.

Amriya tace. Toh.. A ina.. Zan kwana.. Nunamata kan sofa yayi yace ga sofa Chan kije ki kwanta hakai.

Bah musu Amriya tanufi sofan tareda kwanciya hakai. Sosai A.C dakin ke ratsa jikin tah rungume jikinta tayi hakoranta sukafara karkawa.

Kashe wutan dakin Kabir yayi ai Inaa Amriya tamike zunbur. Tareda lalubo inda wutan yake ta kunna.

Tashi kabir yayi yace kee menene hakan. Ehhh. Amriya tace bana.. Iya.. Kwanciya.. Cikin duhu.

And soo Kabir yafada ina ruwana inbakya iya kwanciya a duhun banda shashasha dalla kashe mun wuta kafun kisha hannun maza. Wlh

Bah musu Amriya takashe tanufin kan sofan tareda kwanciya.
Sosai takejin sanyi nashigarta, gabadaya sanyIn nadada shigarta. Hatake jikinta yadau zafi. Hakoranta ne suka fara karkarwa.

Kabir kamm jinta isheshi da hakoranta yasa ya kunna wutan tareda maida kallonsa gareta domin yimata fada saiya tarar ta dunkulle guri daya.

Hatake yaji tausayinta yakamashi. Yamutsa fuska yayi tareda kashe A.C dakin, Yadauki bargo ya lullube taa.


--------------------------------------------------------------------
TOH FAN'S KOYA ZATA KASANCE TSAKANIN KABIR DA AMRIYA.

COMENT PLEASE.馃檹馃檹
ALKALAMIN 馃枈锔?
BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒
2/28/24, 22:08 - AISHA M.B (Baby isha): 馃尮BISSMILLAHI RAHANI RAHIM馃尮

ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂? PAGE 30

WRITTEN & DIRECTED 馃枈锔廈Y BABY ISHA 馃尯馃尯

"""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""






Lulubeta yayi tareda yamutse fuska yakoma kan gado tareda yin adua bacci ya kwanta .

Ana kiran asuba yatashi tareda nufa toilet yadauro alwala yayi sallah tareda yin azkhar

Aka yacigabada azkhar har gari ya washe kallon kan kujeran da amriya ke kwance yayi amma saiyaga bata wajan . da sauri ya Mike tareda fadin itakuma wannan ina tashiga.

Futowa daga cikin dakin yayi yanufi dakinsu khaleed . kwankwasa kofan yayi .ba'a fi five minutes bah sadiq yazo ya bude kofan.

Kallon kabeer yayi yace mln kabir lafiya kuwa naganka a wannan lckn . kallon sadiq kabir yayi yace toh inba a wannan lckn bah a wane lokaci kake so ka ganni mtssww yaja tsaki.

Allah ya huci zuciyanka cewar sadiq . kabir yace kai ni ba wannan bah ina wancan yarinyar take .

Cikeda mamaki sadiq yace wace yarinya kuma ,aikin banza toh ina nufi wancan yarinyar mana mai kama da aljanar Chan.

Kallon kabir sadiq yayi yace Dan tsaya wai kana Amriya ,kabir yace oho koma meye sunan tah toh ita make nufi.

Aba kabir batare kuke bah da ita taya kuma zamusan inda take .kabeer yace toh ni banganta bah ,

What me kake nufi kana nufin Amriya batanan , kabir yabashi amsa da yes .

Amma kabir bakada mutunci taya zaka iya barin yarinya tafuta kuma bayan kasan ba inda tasani anan.

Kallon shi kabir yayi yace amma fah kacikai sadiq ni inazan San sanda zata futa , toh wlh kufuto da ita koma tana wajan ku

Kamar ya mu futo da ita wannan wane irin magana kake fada aka .

Khaleed daya yi labe yana jinsu yafuto daga dakin tareda fadin kunga bawai tsaya zakuyi kuna musayar yawuba abunda yakamata yanzu shine mu bazama nemonta inba akaba akwai matsala.


Kabir yace toh kuje kunemota nizanyi wani aiki.


Kallon shi khaleed yayi yace Kama isa tare zamuje wlh mune mota kokuma yanzunan nakira mom nasanar da itah halinda ake ciki


Toh shikenen mutafi cewar kabir futowa sukayi daga cikin hotel din suka bazama nemonta amma koh inuwanta bazu ganiba.


Tun kabir baya damuwa haryadawo yafara damuwa akai.



NIGERIA

Wani hawaye mai zafi ne yake bin kunci ta bude kofan taji anyi da sauri ta share hawaye ta kallon ta doct Amina tayi, tareda nufa inda take, sannan ta dafa kafa dan ta .

Tace doct Khadija kina lafiya kuwa naganki cikin damuwa aka .

Kallon doct Amina doct Khadija tayi Tace bakomai .
Bakomai kuma naga kina kuka Dan Allah kifadamun meyafaru .

Share hawaye tayi, tace na aikata babban zunubi da Allah bazai taba yafemin bah . na aikata babban laifi a rayuwata ta duniya babu Wanda zai iya yafewa . tabbas naci amana ,nayi yaudara, no muguwa ce ,kwarai banida imani, tana kaiwa nan ta fashe da matsanancin kuka,

Sosai hankalin doct amina yatashi Tace wane laifi kikayi da kikecewa Allah bazai taba yafemiki bah ,shin kinsabawa mijinkine ,Doct Khadija tace Aa, Doct Amina ta kuma tambayar ta da cewa kin yi kisan kaine?, girgiza mata kai ta kuma yi, doct Amina takara tambaya ta shin kin sabawa sharia musluncine ,shiru doct Khadija tayi Tace inason zan nuna miki wani abune amma Dan Allah ki rikeshi a sirri banason kowa yasani.

Doct Amina Tace menene nunamin.

Mika hannunta doct Khadija tayi tareda nufa inda Jakarta yake tadauko wani karamin box . tareda koma wa inda take zaune Tace kinga wannan
Box din yakai shekaru 30 da yankai ajiye kuma sbd zunubida na aikata yasa na Adana shi sbd wancan azzaluman matan inason koba yauba gaskiya tayi halinta.

Doct Amina Tace nifa bangane abunda kike fada bah , wayan doct amina ne taji yafara ringing daga wayan tayi tareda fadin gani nan zuwa ajiye wayan tayi Tace kiyi hakuri Khadija abban Yusuf ne yadawo kuma yana son ganina gobe zaki cigaba barana taci .

Shikenen toh asauka lfy. Daukan Jakarta doct Amina tayi tareda ficewa daga dakin .

Nannauyan ajiyan zuciya tasauke tace ya Allah inason na sanarwa wadanan ahali biyu nan gsk amma nakasa ya Allah ka taimakeni natonawa wannan matan asiri.



Daga sama taji ance badai yatona nawaba saidai yatona taki asirin.






Bangare su kabir neman duniya sunyi amma basuga Amriya bah.

Sosai hankalisu takara tashi . wajan shaguna suka nufah suka fara nuna photonta koh sungan ta amma bawanda yaganta


Itakam Amriya tana geden bakin titi tayi tagumi.



Manage PAGE pls
2/28/24, 22:09 - AISHA M.B (Baby isha): Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91.





BISSMILLAHI RAHAMI RAHEEM 馃尮馃尮馃尮

ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煂? PAGE 3锔忊儯1锔忊儯鈻讹笍3锔忊儯2锔忊儯
WRITTEN & DIRECTED鉁嶏笍 BY BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒

------------------------
Karasawa sukayi inda amriya take, Khalid yace Amriya menene kikeyi Hanan wajan,


Amriya tace Babu komi , Jan hannunta kabir yayi yace taso mutafi, tashi tayi, gaban kabir ne yafadi ganin yadda idanunwanta suka kada sukayi jajir.

Alamun kabir yamasu da ido, su sadiq na ganin aka suka wuce cikin hotel din.

Rike mai hannu amirya tayi gamm hawaye nabin kuncinta tace, meyasa kake son hallaka rayuwata ne, Eh Kalb, meyasa nake fuskantar tozarci da bakin ciki daga wajan kah, nuna saitin zuciyarta amriya tayi tace kasan yadda nakeji kuwa, jinake kamar na kashe kaina, Tana kaiwa nan ta fasheda kuka mai cin rai.

Karo na farko a rayuwarsa dayaga amriya tabashi tausayi, rungumeta yayi kam jikin jikinshi yace, kiyi hkr, namiki alkawari bazan sake miki abunda bazaki ji dadi bah kinji.

Dago kanta Tayi ta dora akan yatsansa, gabanta ne yayi mumunan faduwa, ganin babu zoben ta a hannunsa, cikin zuciyarta tace waiyyo Allah, zobena baya yatsan sa, yana wajan wa kenen, tunanin ta ne yatafi kan mom, tace tabbas wannan matar bazata bar kowa a Raye bah indai zobena yana wajanta, yakamata ace nakoma kafun ta aiwatar da mugun nufinta akan wannan ahalin ,

Kallonsa tayi tace Kalb, inaso mukoma gida, kabir yace kinaso mu koma gida karki damu gobe idan ma'aikatan dana tura zasuyi order na kaya suka kai saimutafi, amriya tace Aa Dan Allah yau mu koma, kaji, kabir yayi murmushin yake yayi yace Tom shikenen,
Tareda sumbatar goshinta.

Saitin tureshi tayi Jikinta yafara karkarwa, hankalin kabir bah karamin tashi yayi ganin halinda amriya tashiga,

Ihuu ta kwallah, inda mutanen wajan suka zuba ido suna kallo,

Bah abunda bakinta kefadi sai ruwa, dukanta yayi chakk yanufi cikin wajan da itah.





Da sauri doct khadija ta juyo sannan tace, meya kawoki nan, murmushin mugunta mom tayi tace, abunda kike tunanin zai kawoni mana.

Nazone na karbi memory daga wajanki ,yana ina, doct khadija tace, baya wajena kuma meyasa zan baki,

Aba meyasa kika zama Mara imani aka, bazan kara aikata kuskure dana yi Ba abaya, har yau har gobe, saina tuna ranar dakika sani nayi kuskurenda bazan taba mantawa dashi bah.

Ke wace iriyar muguwa ce, kin kashe mutane bah iyaka, kin raba da da mahaifyarsa, kin mayarda mutane bayinki, tabbas zakiyi danasanin abunda kikeyi, wlh wlh, wlh, Saikin yi dana sani, a lckn da aka zo zaran ranki, a lckn zaki San irin kuna da azabar da zare rai yake dashi.


Hahahaha, mom ta kwashe da dariya Tana mai fadin kijira kinga abunda zai farudake tukun kafun kiyanke abunda zai farudani.


Kallon sauran yan qungiyan tayi tace inason yanzunan ku kimin ita fadata, daya daga cikin mutanen yace angama shugaba..


Direct daki kabir yakaita tareda kwantar da ita akan gado, tareda dauko inhaler dinta yabata tashaka , babu bata lck tasamu nutsuwa, ajiyan zuciya yayi yace, na tambayeki, shin kinada aljanu ne koh shafar iska, Girgiza masa kai amriya tayi tace Aa,


Toh meyasa, kike yawan faduwa, kamar wata mai aljanu, gsk abunan naki akwai lauje cikin nadi.


Murmushi amriya Tayi cikin ranta tace Idan da kasan wahala da gwagwar mayar da nakesha wajan cetan rayuwarka da bazaka CE aka bah, tabbas yakamata, na koma sbd wannan azzalumar matar taruga tasaka wannan zoben ,

Kabir yace toh shikenen kishirya zamu koma yau, yana kaiwanan yafuce yabar mata guri.


Yana futa amriya, ta Rike kanta wanda yake mugun saramata, tashi tayi a daddafe tanufi toilet.



Chan cikin daji suka Shiga da doct khadija
Inda yan qungiya suka taru ,

Daddaureta akayi ajikin bishiya Wanda yan qungiyan suke kiranta da bishiyar bishiyar azaba.

Zama mom tayi, tace zan Kara tambayanki a Karo na karshe ina memory da bayanan nan suke,

Doct khadija tace bansaniba muguwa azzaluma mara imani, mai bushashiyar zuciya, Allah ya wadaran wannan rayuwa taki, tabbas bakiji dadin rayuwa bah,.

Kuma bazan Bari ki kara nasara akaina akaro na biyu bah. na rante da Allah saidai ki kasheni, amma bazan fada miki inda yake bah.


Ran mom ne yayi kololuwar baci tace wato sbd kinga ban sakar miki azaba bah shiyasa kike baki koh, toh yanzu nan zan gama dake, idan yaso kya basu lbr achan.


Daukan wuka mom tayi, tafara tsaga cikin doct khadija, wani irin azzababbiyar kara doct khadija tasaki,

Zaki fadamin koh saina gama dake, hawaye ne yafara bin kuncinta inda jini keta malala abakinta da cikinta, tace

Bazan fadaba, Kuma wlh, acikin yaranda kika bi kika mayardasu marayu, a lckn da basuji bah basugani bah, daya daga cikin su ita zata kawo karshenki, ki je kirubuta zakice nafada miki.


Murmushi mom tayi tace ba yau nafarajin aka daga irinku bah, kindauka zan rabudake nee Dan kinfadamin aka, toh shikenen tunda bazaki futoda memory bah, toh kingaishesu idan kinje.

Tana kaiwa nan ta soka mata wukan da karfi Chan cikinta har ya ratsa jikin bishiyar. Faduwa doct khadija tayi muttaciya


Daga wukan tayi tace ina bukatar jinin jariri yanzu nan , angama shugaba,


Akwaishe mun gawar wannan matar a jefa a cikin teku yadda kiyaye zasuyi abincin dare da namanta, angama shugaba.


Hawaye ne yafara zuba a fuskan aunty amarya dake tsaye, cikin ranta tace tabbas matar nan shedaniyace, mara imani, wane sirri nee yake a memory, menene takeson doct khadija tabata, tabbas akwai lauje cikin nadi.


Alhj usman ne yace ranki shi Dade, ga yata zainab tanaso ne tashiga qungiyan devilish,

Kallonta mom tayi tace, yarka CE, Alhj usman yace Eh yata ce, zainab tace ranki shi Dade nima inaso nazama yar qungiya na sha'ara yadda babu Wanda zaimin na Kyale,

Dariya mom ta kwasheda dashi tace karki damu indai zaki iya shan jini toh zaki zama yar qungiya, gobe ki hallarci taro, zaki zamo yar qungiya, kuma sannan dole ki sadaukar da abunda kika fiso,

Zainab tace komai zan iya bayarwa indai har zan kasance a wannan qungiyar .

Tashi mom tayi tace, yanzu kowa zai iya tafiya, yau karku manta kowa yasha jinin akuya, sbd jikina na bani akwai wani iftilahi dake shirin faruwa kwanan nan .

Angama uwar shedanu,

Watsewa kowa yayi daga wajan, inda aka dauki gawar doct khadija aka jefata a ruwa kamar yadda mom ta umarta.


Shiryawa su kabir sukayi tsaff, inda suka
Nufi Airport,



Daukan Wayanshi sadiq yayi, yayi dialing number Nadira ringing biyu ta dauka, Tareda yin sallama, , amsawa yayi yace, my wife to be ykk, murmushi nadira tayi tace Lfy lau, kaifa, sadiq yace ina cikin koshin Lfy kamar yadda kike.

Alhmd Nadira tafada, tana mai fadin wlh Nayi missing dinku yaushe zaku dawo, sadiq yace yau dinnan da yardar Allah.

What, ta tashi a kwance datake tace are you for real, gsk naji dadi sosai,
Shine Kuma baka gayamana bah, murmushi sadiq yayi yace, yanzu dai nafada miki kohh,.

Tom shikenen Allah yadawo daku Lfy, sadiq ya amsa da ameen .

Sadiq yace yanzu jirgi zaitashi, saimun Iso koh, Tom shikenen, ka kulamin da kanka, kabir yace insha Allah, kema ki kulanmun da kanki kinji. Tom Nadira tace, daganan sukayi sallama.

Kashe wayan nadira tayi Tareda saukarda nannauyan ajiyan zuciya,

Su Ummi dake Zaune suna Kallon ikon Allah Tace ohh wayaga su aunty nadira da soyayya, kamar bah da bah dakika mutuwar son yaya kabir. Yanzu Kuma Gashi, yaya sadiq zaki aura, inda Allah ke ikonsa kenen


Murmushi Nadira tayi tace





馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮
-----------------------
馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮

COMMENT & SHARE 馃檹馃檹馃檹

ALKALAMIN 馃枈锔忦煐婏笍馃枈锔?
BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒(AISHA M.B)
2/28/24, 22:09 - AISHA M.B (Baby isha): Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IhGI6IqdpVVABEzyBe7LGM


馃鈥嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔?
馃寠馃寠馃寠馃寠馃寠馃寠
馃挒馃挒馃挒馃挒



馃尮Bissmillahi rahamani raheem馃尮

ALJANAR RUWA CE BOOK 2 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂? PAGE 3锔忊儯2锔忊儯鈴?3锔忊儯3锔忊儯


WRITTEN & DIRECTED馃枈锔忦煐婏笍馃枈锔?
BY BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒


------------------------

Murmushi nadirah tayi tace Allah ya ruga daya kaddara cewa bani zan aureshibah, banice na dasawa kaina sonsa bah lkcn danace inason yahya kabir, idona yarufene akansa, kuma yanzu Allah yabani mafi alkhairy, kuma gashi yahya sadiq dinmah ya Maye gurbin yahya kabir . Kuma naga aibakwa sonsu aka baku.

Gabadayansu sukace mezai hana musosu, saidai fatima da Aka bawa yahya khaleed .

Yamutse fuska fatima tayi tace nifah Allah yahya khaleed inba biyayya iyaye bah bazan aureshibah. Tunda sukatafi koh kirana baitaba yibah ,sai shegen jijidakai jaraba ni nama rasa da yahya kabir da shi wanne yafi jijidakai.

Aba kema kinsan yahya kabir yayi gaba wlh cewar nadirah.
Toh susuka sani wlh koh ajikina


Nadirah tace Yanzu tsoro na daya nee, shine kada agano cewar amriya bah mutum bace shine kawai tsoron danake jii.


Dan jimm gabadayansu sukayi Fatima tace wlh abunda nima nake tsoro kenen sbd idan akasani most especially yahya kabir zai iya saa a kulleta a gidan yari.


Insha Allah mah akan bazata faruba cewar kalisat. Tashi Ummi tayi tace kunga bah zama yakamta muyi bah kunsan yau zasu dawo muje mufara shirye shirye. Oh akane fah kunga kutashi muje.

Tashi sukayi inda sukafara gyara gidan.

Kalisat dakuma nadirah suka nufi kitchen sukafara shirye shiryen girki.


Saida suka dau 1:30 minutes sannan suka gaba komai dakomai .

Dakinsu triplet salma tashiga tace sufuto abinci yayi ready. Gamunan zuwa cewar adeef.

Bayan tafuto tanufi dakinsu mom tace angama lunch food. Mom tace kee malama dallah fuce kiban guri.

da mamakin ta ummi tace Mom meyafaru kuma me aka miki Dan Allah mom idan nice namiki laifi kiyi hkr ki gayamin zan kiyaye gaba.

Kallonta Mom tayi sannan ta buga murmushi yake tace sorry ummi wlh damuwa ce tasani yimiki ihuu kinji. Shikenen mom ,fucewa tayi daga dakin sannan tanufi dakin aunty amarya.

Bayan fucewar ummi mom tayi dariyar mugunta sannan tabude drower tadauko wani dunkullalen magani. Tareda juyashi a hannunta tace yanzu aka soma wasan.

Saina kasheku gabadaya sannan dukiya gidanan yazama nawa na ni kadai. Futowa tayi daga dakin ganin bah kowa a parlour yasata nufah dining inda kuloli na abinci ke jere akai.

Kallonsu tayi tareda bude abinci gabadaya tafara barbade abinci da guba . Sannan tayi saurin rufeshi.


Ammi kiyi hkr kidaina kuka Dan Allah banajin dadi, yanzu daga yin mafarki saiki tashi kina kuka, kallonsa tayi tace aba yusuf yanzu wajan shekara 20 kenen da yan kai, bah ranar dazata tashi tafadi banyi mafarkin yata bah. Jikina yanabani cewar yata tana raye


Ammi kinayi mafarkinne sbd kinsa abun aranki, babu inda mutacce yake dawo duniya wai yacigaba da rayuwa. Gashi inason zuwa wajan aiki ankawo case wanda zan gabatar gobe a kotu. Yanzu taya zan iya zuwa kina kuka.

Daddy Dan Allah kashawo kanta. Dago kai daddy yayi yace yusuf nikam mezance .


Nace mata mu fauwala wa Allah komai, ba ita kadai take jin kunci bah nikaina mah aka, so mezanyi . Yanzu gashi har B.P ne da itah

Kuma at anytime idan tacigaba zai iya zama high. Yusuf kawai kaje wajan aikinka nizan rarrashi abata ba kaiba.

Maza maza ka wuce kaje. Amma daddy bazan iya tafiya bah batareda naga tadaina kukan bah.

Ni dadi nadai taurin kai nace maka katafi koh i know what am saying. Okay daddy shikenen zantafi amma ka tabbatar kasata farinciki, kuma kasa taci abinci. Never mind.

Fucewa yusuf yayi sannan ya shige mota dafa kan tyring motan yayi wani hawaye mezafi nabin kuncinsa.yace Allah sarki kanwata , Allah yajikanki da rahama. Share hawayenshi yayi yatada mota sannan yafuce daga gidan .


Bayan fucewarshi daddy ya tashi yaje kusada ammi tareda rike hannunta yace. Aba my ameenatuwa kiyi hkr kidaina kuka. Kinji adua yakamta mudunga mata bah kuka bah, kinji.

Ammi tace nikasakeni nayi kuka naa, aba my dankalin Hausa, kinsan mena tuna ranar auren mu dakika sha asha ado da dambareren jambaki, sai kika zama kamar indon kauye

Dariya manya ammi tayi tace kafara kohh, nace kadaina tsokanata , Aa nibazan daina bah har lckn wata mata tamiki gira wanda daya yayi hanyar arewa daya kuma yayi kudu

Hatare suka kwashe da dariya gwani sha'awa, share fuskanta ammi tayi tace kaiko meyasa koda yaushe idan ina cikin bakinciki saika San yadda zakayi kasani farinciki gsk kaidin na mussaman nee.

Daddy yace kwarai kuwa nidin na mussanman nee aii sbd ni nakine kema tawace.

Dan aka tashi muje muci abinci. Aa nibazanci bah. Masha Allah kenen yin kishiya a gidanan babu fashi kenen yafada cikin zolaya. Aba my chief Ni banaso cewar ammi,

Toh tunda bakya so kitashi muje muci kinji.
Tashi sukayi cikeda kaunar juna .


""""""""""""""""""""""""''"""
Jin hana kwankwasa kofa yasa Nadira tashi tanufi kofa tareda budewa. Ganinsu kabir nee yasata farinciki sannan tafara kiran sauran hatare gabadayansu suka iso, rungume amriya sukayi . Sosai kowa yayi farinciki da dawowansu,

Idan bangare guda kuwa ma'akata suka fara shigo da akwatuna dozen dozen da kayayyaki . Sannan suka shigardasu ciki babbar daki na ajiya suka tafi.

Futowa Mom tayi tace wow my son kundawo lfy. dasauri kabir yaje ya rungumeta sannan yace i really Miss you mom.

Murmushi mugunta tayi tace aba son yaushe kuka tafi da Jataka fara missing dina takarashe maganar tana kallon amriya. Idanuwan amriya ne yasauka akan yatsan Mom wanda zobenta ke sanye ajiki.

Sai a lkcn gabanta yakara faduwa . Tace kindai rantse saikin GA bayan wannan ahalin toh wlh muzuba mugani Allah bazai baki damar cimma mummunar manufanki akan wannan ahalinbah


Sakin Mom kabir yayi yanufi wajan aunty amarya yagaisheta sosai aunty amarya taji dadin dawowansu,


Itama amriya batayi kasa a gwiwa bah tanufi wajan aunty amarya sannan ta gaisheta, sosai aunty amarya ta tarbeta hannu bibiyu.

Aka gabadayansu sukafara gaisawa da juna cikeda kaunar junansu.

Mom tace yata amriya bah fada maiyakawo gaba, nibakizo kingaisheni bah aii. Cikeda jin takaici ta tashi tanufi wajan mom,

Sannan ta gaisheta tah. Kallonta Mom tayi cikin kasa da murya tace yakika ga salon nawa.

Murmushi amriya tayi tace yayi kuma aciki harda Nasaran daukan zobena dakikayi, kisani cewa wahalar da kanki kawai kikeyi bah wani abuba, irinku kamata ai ace kutsaya kuna tallah goro a kasuwa. Jin zafin maganar amriya Mom tayi har makogaronta.


Grandma tace haryanzu Baku gama kusun kusun dakukeyi bah. Murmushi Mom tayi tace grandma kinsan tsakani ya da uwa sai Allah. Yanzu bah wannan bah kutashi kuje kuci abinci.

Kabir yace okay mom baramuje mudan watsa ruwa muyi sallah.

Tashi gabadayansu sukayi inda suka nufi part dinsu .

Bayan sungama komai da komai suka nufi hanyar dining. Daidai lkcn itama amriya tafuto daga part din aunty amarya.

Zama gabadayansu sukayi inda mom tafara bude musu abincin. Kallonta Khalid yayi yace Mom ke bazaki ciba, mom tace eh wlh nakoshi,


Kallon abincin amriya tayi taga tabbas abincinan an zuba guba aciki. Murmushi amriya tayi cikin zucinyata tace kindai dage saikin ga bayan wannan ahalin


Serving dinsu gabadaya mom tafarayi idon kabir ne yasauka akan yatsan Mom wanda zoben amriya kesanye yace Mom dama zobenan na wajan ki , eh wlh yana waje na sanda naje dakinka naganshi akan table, nima kuma zoben na burgeni shiyasa nasaka kafun ka dawo , kabir yace amma naji dadi dakikasa sbd idan kikasa kamar nasaka nee


,Daukan chokula gabadayansu sukayi tareda yin adua suka tsokala chokali zasu faraci .

Ku dakata sukaji amriya tafada, da kallon mamaki gabadayansu suke binta dashi.


Sadiq yace amriya meyasa zakice mu dakata, amriya tace zakusan dalili, tashi tayi tareda daukan wani plate din tazuba abinci sannan tasa agaban Mom tareda daukan chokali ta ajiye agabanta.

Amriya tace aba Mom dinmu taza'ayi kina matsayin uwa agidanan bazaki ci abinci bah, ke yakamata ace kinfaraci.

Murmushin yake Mom tayi tace ai idan kunci kamar nacine, ni naruga danaci. Amriya tace amma yadda nagani shine wannan bai nuna cewa an iba bah tabbas baki ci bah.

Kinsan bamuason kisamu ulcer kinji Mom, kici kinji.

Aba amriya Mom tace fah takoshi muci kawai cewar sadiq.

Babu wanda zaici abincinan, dawani irin jin mamakin jin kalamanta grandma tace ohh ni halimatu sadiya shin amarina fadamana dalilin dayasa bazamuci abincinan bah.

Mom kuwa ranta indan yakai dubu yabaci . Amriya tace dalilina shine wannan abincin akwai guba acikinta.


Hatare suka ada baki wajan cewa guba kuma, nadira tace meyasa zamu saka guba amriya, wlh bamusa guba bah.


Amriya tace nasan baku bane kukasa, amma Mom tasani.

Zaro ido Mom tayi tace nikuma amriya sbd me zanyi kokarin cutarda iyalina, sune fah komai nawa takarashe maganar hawaye nabin fuskanta. Kuma tunda Baku yarda danibah zanci abincin daukan chokali tayi zataci abincin, dakatarda itah kabir yayi yace Aa Mom kiyi hkr Dan Allah, ba abunda zaisa mu zargeki


Dan aka babu abunda zai hana muci abincinan. Babu wanda zaici abincinan, aba amriya hankalinki guda kuwa yara susha wahala dafamana abinci kuma kice bazamu ciba grandma takarashe maganar taja chokali zata faraci.

Ganin akan yasa amriya barar da abincin gabadaya sannan ta dauki plate daya na abinci ta fuce waje.

Ganin abun nata bana sawa ido bane suka bi bayanta.

Bude daya daga cikin karnukan gidan tayi tabashi plate na abincin yafaraci, tsayawa gabadayansu sukayi suna kallon ikon Allah.

Aikwan ba'a fi ten minutes bah wannan karen yafara kururuwa yafara futa hayyacinshi jini yafara futowa tabakinsa da Ancinsa.

Zaro ido gabadayasu sukayi cikin tsoro da fargaba, basu ankarabah karen ya fadi a wajan mutacce.

Amriya tace dabba kenen shiyaci abincinan ya mutu da kunci kuma aka za ku mutu,

Kallon Mom aunty amarya da amriya sukayi , hada ido sukayi su uku batareda kowa ya lura dasubah.

Kabir yace tabbas wanda yasaka gubanan yana cikin gidanan kuma dole aganoshi.


Amriya tace bah bukata domin ni naruga danasan wanda tasaka guban nan , zaro ido Mom tayi.








馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒
TOH FAN'S ANAN ZANDAKATA,


COMMENT & SHARE PLEASE 馃憦馃憦馃憦馃憦

ALKALAMIN 馃枈锔忦煐婏笍馃枈锔?
BABY ISHA馃尯馃尯馃尯
2/28/24, 22:10 - AISHA M.B (Baby isha): Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DzIj6Y6KObvD2Bcmg8azU5


馃尮Bissmillahi rahamani rahim 馃尮

ALJANAR

Please Login or Register in order to submit comment