Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mom Grandma tayi tace, ke Karima karki dauka zaki iya tsora tani da wannan bindigar wasar da kika rike a hannu, wallahi banki na kunce kaina nayi miki tsinaniyar duka bah, ko mene zaki fada baki isa kin tsora tani bah, saidai mah ni na tsorata ki.

Dariya Mom ta kwashe dashi, ji kake, hahahahaha. Saida tayi mai isar ta, sannan tace, "nidin wai, tsoro, na rasa tsoron wa zanji saina tsohuwa, toh bara kiji har yanzu ba'a haifo wacce ta isa ta sakani na tsorata bah.

Kallon ta Nadira tayi tace, karya kike, tabbas an haifo wacce ta isa sakaki tsoro harda firgici, domin kuwa Amriya daya ce tamkar dubu, kuma ita din ce zata kawo ƙarshen zalin cin ki, dama duk inda aka samu mugu, wanda yake takama da tsantsan zalunci, toh tabbas mai maganin shi yana bayyana.

Kamar dai yadda itama Amriya itace zata yi maganin ki, domin kuwa babu inda zalinci yake dorewa, Amriya itace ajalin ki.

Kamar hadin baki gaba dayan su suka ce, "kwarai kuwa, Amriya itace zata yi ajalin ki.



COMMENT & SHARE plxx🙏🙏🙏

ALKALAMIN✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹

ALJANAR RUWA CE
🧜♀️🌊🌊
PAGE 5️⃣4️⃣▶️5️⃣5️⃣
WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY AISH'A M.B💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)

54 TO 55
,___________________________________
Idan ran Mom ya kai dubu, toh ya ɓaci?, cikin baccin rai tace, naga alamin kuna da mai tsaya muku Koh?, domin banga alamin tsoro a tattare daku bah, kuma ni akan bai min dadi bah, dole ne na dawo da wannan tsoron cikin zuka tanku.


"Khalid yace, sai dai mu, mu dasa miki tsoro, amma ke dai baki kai bah, domin kuwa kunkuru ba zai ce zaiyi gasar gudu da barewa bah. Dan aka ki koma inda kika fito, domin kuwa bamua da bukatar ku.


Gyaran murya "Zainab tayi tace, like seriously!, oh wait a minutes, kuna tunanin da mun zone domin muyi sulhu, that's impossible, idan kuna ma tunanin akan toh ku maida ta tatsuniya, domin kuwa bala'i, ne ya kawo mu, kuma kowa saiya ɗaɗana kuɗar sa.

Maida Kallon ta kan yan qungiyan tayi tace, maza _maza, ku daddaure su yanzu nan, babu bata lokaci suka nufi kansu Kabir da zimmar daure su,

A hassale gaba dayan su Grandma, suka dunkule hannu sannan suka kai musu naushi, ganin akan yasa gaba-dayan su yan qungiyan asirin suka yi kansu, kokawa gaba daya suka shiga yi, babu abinda kake ji a gidan sai karan naushi.

Yayin da gefe guda Grandma ta daura ɗan kwalin ta ƙugu, sannan ta kama kan daya daga cikin yan qungiyan, sannan ta gantsara masa cizo a kai, ihuu ya saka, yayin da yake kokarin guduwa, amma ina karfin tsohuwa ya wuce wasa.

Saka kansa grandma tayi a hammata, sannan ta fara zuba masa rankwashi ba kakkautawa, sannan ta ɗauki iron mai zafin jaraba, ta ɗoɗana mai a duwawu ta fara ironing din duwawu nasa. Sannan tace,

Yoo, wallahi dani kuke zance, Ni halimatu sadiya, za'a kawo wa hari ina cikin gidan ɗana, toh a yau saina nuna muku fushi na, dan wallahi gaba dayan ku yau saina gasa muku duwawu, sai naga duwawun ya gasu sosai, ta yadda Koh da zama ba zaku iya yi bah.

Tana kaiwa nan ta cigaba da gasa musu duwawu daya bayan daya.

Ihuun!, yan qungiyan Mom ne gaba daya ya cika gidan, yayin da aka rasa mai ceton wani.

Faduwa Nadira tayi kasa, yayin da daya daga cikin yan qungiyan ya nufe ta da wuka, wai gawa tayi bayan ta domin ta dauki abinda zata kare kanta dashi.

Idanuwan ta ne suka sauka akan wayan electric, da sauri ta mike tare da daukar wayar, sannan ta dauki bottle water akan dining ta watsa wa yan qungiyan.

Daga bisani kuma, tayi wa su Kabir alamun su matsa daga wajan, babu bata lokaci a tare gaba-dayan su, suka yi saurin barin wajan suka hau kan dining,

Ganin yan qungiyan Mom na ƙoƙarin haurowa, ya sata saurin sakin wayar, ihuun! tsoro gaba-dayan su suka saka, yayin da suke kokari guduwa!, cikin rashin sa'a lantarki yaja su, ji kake pass, girrr, pass.

Ganin babu sarki sai Allah, yasa Mom da Zainab yin kurin guduwa, hatake gaba dayan su, suka sha gaban su.

Murmushi Grandma tayi!, sannan tace, "Karima ina kike shirin zuwa?, wato yau kinga fadan yan China Koh, toh mun gama dasu, yanzu ku ya rage zamu yi fadan bahubali daki.

Tana kaiwa nan, ta janyo rigar Mom, hatake Mom ta fadi kasa, yayin da ta saki wani kara mai razanar wa!, yayin da zoben dake sanye a yatsar ta yayi haske.

Kwashe wa da dariya Mom tayi!, sannan tace, Allah sarki ita wacce ta bada rayuwar ta akan ku mah baku damu da ita bah, tana chan tana mutuwa, Ni kuma gani nan na mallaki zoben ta, yanzu shikenen zan zamo sarauniya gaba daya aljanun da Mayu, zan samu karfin iko mai dimbin yawa, zan zamo shugaba wacce babu kamar ta. tana kaiwa nan ta kuma fashe wa da dariya.


Gaban kowannen su ne ya fadi!", yayin da zuciyoyin su ya fara dukan uku -uku, jin budewar kofa yasa gaba-dayan su kallon kofar shigowa, ganin su Ammi" ga jariri rike a hannun ta, yasa kowannen su yin mamaki.

Kabir ne yayi karfin halin fadin", Ammi meyasa na ganku a firgice, kuma sannan wannan jaririn waye?, ya karasa maganar yana mai kallon jaririn.

Bashi amsa Doct Khadija tayi da fadin, wannan jaririn ba dan kowa bane, sai naka, kuma a halin yanzu muna da lokaci kalilan daya za muyi amfani dashi wajan cetan mahafiyar sa daga mutuwa.

Zaro idanu, gaba-daya suka yi, yayin da Kabir yace kenan wannan ɗana ne?, Ammi da muryar ta ya ruga ya dashe tsabar kuka, ta bashi amsa da cewa kwarai kuwa dan kane, yanzu mah ba wannan bah, dan Allah ka taimaka, ka futo da wannan zoben, domin cetan matar ka, if not we are going to loose her.

Aaaaa!, Kabir ya fada a tsawa ce!, dafa kansa yayi tare da fadin, she will not die, ba zata mutu ta barni bah, dole ne mu ceci rayuwar ta, meyasa zata tafi?, bayan kina bukatar ta, ina buƙatar ta, ɗan ta mah yans bukatar ta, bazai yu ta tafi bah, we need to do something.

Karban yaron Nadirah tayi daga hannun Ammi, sosai su Grandma ke ya bawa da irin kyau da Allah ya ba shi, ba suyi mamaki bah sai yadda suka ga jaririn yana matukar kama da kabir, yadda kasan kamar an tsara kara.

Kallon jaririn Momsy tayi tace, kenan wannan Grandson dina ne, Allah yayi wa rayuwar ka Albarka, menene sunan sa? Momsy ta tambaya,

Ammi ta bata amsa da cewa, tukun nan dai, ba'a saka masa suna bah , ku nake so ku ku zaba masa suna.

Maida kallon ta Momsy tayi kan jaririn sannan tace, from now henceforth sunan ka Aliyu hydar. Sunan mahaifina, mutum mafi soyuwa a gare ni, shidin ba ya kasance iya uba a wajena bah, shidin ya kasan ce rayuwa ta ne, ya kasance shidin duniya ta tane, dan aka kai zan rada wa sunan sa, domin kuwa Is only a special person i can give that name.

Farin ciki ne gaba ɗaya ya lullube fuskokin su, hawaye Kabir yaji na ƙoƙarin zubo masa, da sauri ya sharw hawayen shi, sannan yace Hydar ina matukar sonka sosai, yanzu zamu tafi domin muje mu tseratar da rayuwar mahaifiyar ka.

Kallon Mom yayi, sannan yace, Mom please ki bamu wannan zoben, dan Allah kinji wlh duk abunda kika tambaya zamu baki, but Please ki fara bamu zoben nan.

Dariyar mugun ta Mom ta kwashe dashi!", tare da fadin impossible, kana tunanin wannan zoben zan bar shi shi, toh ku tsaya kuji tunda wannan zoben ya riga ya shigo hannu na, toh bazai futa bah, dan aka bazan bayar bah.

Daukar takardar da Amriya tayi rubutu akai Yusuf yayi, sannan ya fara karan ta musu, jikin kowannen su ne ya dau sanyi, yayin da tsoro da fargaba gaba daya ya cika cikin zuka tansu, hatake suka ji wani irin tausayin Amriya ya kama su, yayin da hawaye ya fara sauka akan fuskan kowannen su.

Kallon Mom Ammi tayi, hawaye na sauka kan kuncin ta tace, "Karima, tunda nake ban taba tunanin zaki yi min aka bah, kada ki manta kefa yar uwa ta ce, yanzu abun duniya mah zai iya raba tsakanin mu Karima,

Hada hannayen ta guri guda Ammi" tayi, sa'annan tace, na roke ki, dan darajar ma'aikin Allah, idan kina kaunar mahafin mu da gaske, toh dan Allah ki bamu zoben nan, dan Allah . Dan Allah ki bamu, we don't have much time, and we need to rescue Amriya's life.

Dan jimm Mom tayi, kamar tana tunanin wani abu, lokaci daya kawai suka ga ta zari zoben ta mika wa Ammi",

Da Kallon mamaki kowa ke binta dashi, ganin babu musu ta miko zoben, share hawayen ta Ammi tayi tace, kin yarda na karba?,

Girgiza mata kai Mom tayi tace, kwarai kuwa na yarda, Amma da sharadi duk abinda na tambaye ku shi zaku bani,

Mike wa Ammi tayi tace, munyi miki alƙawarin duk abinda kika ce kina so zamu baki, murmushin mugun ta Mom tayi, tare da fadin, tom shikenen ku karbi zoben ku tafi.

Karbar zoben Ammi tayi daga hannun Mom, ta kalli Doct Khadija tace, yanzu a ina zamu fara neman Amriya "Khadija?,

Doct Khadija ta bata amsa da fadin ba zai wuce guri daya bah, ni nasani wajan, inda muka fara haduwa da ita, hanan tace min burin ta, shine ta mutu a chan, yanzu ina da tabbacin cewa tana chan.

Yusuf yace, Togo me muke jira, mu tafi kafun lokaci ya kure.

Nufar hanyar waje gaba daya suka yi, yayin da kowannen su ya shiga mota, tare da tada motocin, suka fuce daga gidan.....


Ana Karima, ta yaya zaki basu wannan zoben, meyasa zaki barsu su tafi?, cewar Zainab, amsa Mom ta bata da fadin,

ni kadai nasan abinda nake shirya wa, ke an gaya miki cewa na yafe musu ne, ina sane na bada zoben, sobada abinda zan tambaya saiya ninka na zoben, ni bana ya fiya, fansa ce kawai take guda na a jini na.

Maza-maza ku tashi gaba daya, nuni bayan su, mimmike wa gaba daya suka yi, yayin da suke jin jikin su na musu radadi..

Fucewa suka yi daga harabar gidan, sannan suka bi bayan su Kabir.

Saida su Kabir suka dau tsawon lokaci suna tafiya, daga bisani kuma suka isa wajan.

Koh gama parking baiyi bah, ya futo daga cikin motan, tare da kallon gaba daya jejin.
Futowa suma suka yi gaba-daya, yayin da suka fara kalle _kalle, Koh zasu gano Amriya.

Parking su Mom suka yi, yayin da suka laɓe a bayan bishiya,

Kiran sunan ta suka shiga yi, amma suka ji shiru, cikin karfafa gwiwa, suka cigaba da kiran sunan ta batare da sun sare bah.

Sheshekar kukan tane yaja hankulan su baki daya, waigawa su kayi, yayin da suka ga ta zauna a bakin Kogi tayi rufff da ciki.

Kabir na ganin aka yayi saurin nufar inda take, karasa wa wajan ta suma su kayi.

Zama kusa da ita yayi, tare da ɗago haɓar ta, zaro ido yayi ganin yadda idanuwan ta suka yi jajir duk sun Ku kumbura, uwa uba kuma ta rame tayi baki.

Baki na rawa Kabir yace, mene ne ya same ki?, meyasa kika tafi kika barni?, shin kin san irin halin da na shiga da kika tafi, na shiga wani yanayi na kunci da bakin ciki, na roke ki kiya femin kurakurai na, bazan iya rayuwa ba babu ke.

Dago kanta Amriya tayi hawaye na sauka kan kuncin ta, sannan ta dora idanuwan ta akan nass, daga bisani ta dauke kanta, tareda maida Kallon ta kan su Ammi.

zuwa Ammi tayi kusa da ita, tareda tsugunnawa ta rungume Amriya, sannan ta fashe da kuka!", tana mai fadin, ki gafar ce ni ƴata, tsawon wadanan shekarun bansan cewa kina raye bah, tabbas ban miki adalci bah, na baki dama ki yanke hukunci daidai da laifin dana aikata miki.

Rintse idanuwan ta Amriya tayi, yayin da take jin zuciyar ta na mata zugi da radadi, ɓanɓare jikin ta tayi daga na Ammi,

Tare da mikewa tsaye, ta maida kallon ta kansu tace, mene ne ya kawo ku?, me kuke nema a gare ni?,

Doct Khadija tace, Amriya mun zone domin mu baki zoben ki kada ki mutu, share hawayen ta Amriya tayi tace, shin nace muku ina bukata ne?, banaso ku rike shi a wajan ku, saida lokaci ya kure tukunan zaku kawo min zobe, Togo bana bukatar na cigaba da rayuwa, ku tafi ku kyale ni,

Khalid yace, aba Amriya ke kinsan baza mu taba iya tafiya mu barki bah, ki taimaka ki karbi zoben nan, kafin lokaci ya kure.

Tafi suka ji daga bayan su, juyawa gaba daya suka yi domin ganin waye, da mamakin su kuwa suka ga Mom rike da Hydar a hannun ta.

Cikin baccin rai Ammi tace, Karima mene aka?, ya zaki dauki jaririn, dariya Mom da Zainab suka kwashe dashi!", sannan Mom tace, wannan yaron shi nake so, kamar yadda na fada idan zan baku zobe saina tambayi wani abu, toh jinin wannan yaron nake sonsha.

Karya kike!",Amriya ta fada a tsawa ce!, Jinin ɗana bazai shawu bah, domin kuwa ɗaci gare shi, maza_maza ki bani yaro na, in bah aka bah na lahira sai ya fiki jin dadi.

Dariya gaba daya yan qungiyan suka kwashe dashi, yayin Zainab tace, Togo zaki karbe shi mana idan zaki iya, kallon yan qungiyan Mom tayi sannan tace, maza yanzu nan ku kashe su gaba daya.

Tana kaiwa nan, gaba dayan su suka yi kansu Kabir hannuwan su rike da wuka da takobi,

Fada gaba-daya ne ya gauraye wajan, yayin da suka fara fada a tsakanin su ba gaggau tawa.

Rintse idanuwan ta Amriya tayi, yayin da ta fasa wani kara!, wanda saida gaba daya dajin ya amsa. Sa'annan tayi amfani da karfin ikon ta, ta fara sama dasu daya bayan daya, tana wurgasu jikin manya_manyan duwatsuna da bishiya, hatake gaba daya kowanne su yake faduwa mutacce.

Saida Amriya ta gama dasu tass yayin da ya rage saura Mom da kuma Zainab, ganin AMRIYA na yowa kansu yasa Mom ta cilla jaririn sama, zaro idanuwa gaba daya suka yi cikin tsoro, Amriya na gannin aka tsalle daya tayi ta chafko yaron.

Kuka jaririn ya fashe dashi, rarrashin shi Amriya ta shiga yi, yayin da ta mikawa Salma jaririn.

Ganin hankulan su nakan Amriya, yasa Mom yin saurin janyo Doct Khadija, sannan ta dora mata wuka a wuya tace, zan kashe ta idan baku bani jaririn nan bah.

Maida kallon su suka yi kan Mom, zaro idanuwa suka yi ganin yadda ta dora wuka kan wuyar Doct Khadija,

Haɗa hannun ta Amriya tayi, sannan tace dan Allah kada ki cutar da ita, na roke ki.
Mom tace indai har bakua so na cutar da ita, toh ku bani wannan jaririn.

Kallon su Doct Khadija tayi tace, Aa Amriya karku kuskure ku bata wannan yaron, ni na yarda na mutu, Amma karku bayar, .
Zan yanka ta fa idan baku bani yaron nan bah, Cewar Mom.

girgiza kai Amriya tayi tace A'a, Aa, karki kashe ta, Dariya Mom tayi tace toh ai shikenen, tana kaiwa nan ta yanka wuyan Doct Khadija.

Aaaaaaaaaa!", Amriya ta saki wani razananniyar kara, wanda yasa hadari da walkiya wanzuwa, faduwa Doct Khadija tayi a wajan, kafin kace mee rai yayi halin sa...


COMMENT & SHARE
PLS🙏🙏
ALKALAMIN✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE9https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


ALJANAR 🧜♀️ RUWA CE🌊🌊
PAGE 5️⃣5️⃣▶️5️⃣6️⃣
WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY AISHA M.B💞💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)

--------------------------------------
Gurnani Amriya ta fara yi!, cikin kankanin lokaci, halittar ta ya fara sauya wa, yayin da idanuwan ta ya sauya launi.

Babu bata lokaci tayi kan Mom, ba tayi
wata _wata bah, ta shake mata wuya tare da daga ta sama.

Da sauri su Yusuf suka nufi inda Doct Khadija ke a yashe, kuka ne yaci karfin Yusuf ganin cewa tabbas mahaifiyar shi ta rasu. rungume ta yayi tare da fashe wa da kuka.

A fusa ce! su Nadira da kuma su Grandma suka yi kam Mom da Zainab, yayin da su Kabir suka nufi inda su Mom suke sannan suka dauke Hydar. Kama Zainab suka yi, yayin da suka rufe ta da duka, sosai suke jibgar ta babu gaggautawa...


Kokawa suka shiga yi a tsakanin su, inda Amriya tayi nasaran buga kan Mom akan jibgegiyar bishiya dake zaman kanta acikin wannan dajin.

Wani irin kara Mom ta saki!, yayin da ta fara ihuun ceton rai!, ba babu tausaya wa Amriya ta kara yowa kanta sannan ta daga ta sama, kakari Mom ta shiga yi yayin da idanuwan ta suka yi jajir saboda shaka.

Rintse idanuwan ta Amriya tayi, sannan ta zalalo harshen ta Wanda yake dauke da mugun dafi, ganin aka yasa jikin Mom ya fara bari,ta fara rokon Amriya ta barta da ranta.

Cike da bakin ciki da takaici Amriya tace, "menene abinda wannan baiwar Allah ta aikata miki da zaki kashe ta?, "wana laifi ta yi miki, "me yasa ni baki kashe ni bah, saki rabu da ita," bayan kin raba ta da ɗanta tsawon waɗan nan shekaru, shine yanzu zaki kashe ta.

Hada hannayen ta Mom tayi jiki na kakkarwa tace, ki gafarce ni, dan Allah kada ki kashe ni, ina bukatar na rayu, nayi miki alkawari zan chanza hali na, ki taimaka ki rabu dani, wallahi inajin radadi sosai

Rintse idanuwan ta Amriya tayi hawaye na bin kan kincin ta tace, "Allah sarki Ummi, aka ta dunga rokan ki ki barta da ranta, amma sabo da rashin imani irin naki kika kashe ta, idan har kina jin radadi a matsayin ki wanda kika dade kina aikata zunubi kina kashe rai, toh kiyi tunanin irin radadin da waɗan nan bayin Allah da kika kashe za su ji".

Kuma babban kuskuren da kika yi shine bari na da kika yi a raye, kuskure na biyu da kika yi shine kashe Doct Khadija da kika yi, yanzu lokaci yayi don gurban abubuwan da kika shuka.

Amriya na kaiwa nan, ta dauki Wuka za ta chaka wa Mom, ba zato ba tsanmani taji an rike mata hannun ta baya, waigawa Amriya tayi don ganin wanenen.

Da mamakin ta kuwa, taga Fatima da kuma Ammi gaba daya fuskokin su yayi
shaɓe- shaɓe da hawaye. Cikin sheshekar kuka Fatima tace, "Ki rabu da ita Amriya, koba komai itadin mahaifiyar mu ce, ta sanadiyar ta muka zo duniya. Ammi tace kwarai kuwa Amriya", koba komai ita ɗin yar uwa tace ta jini, bayan ita juran ganin za'a kashe ta bah, Please Amriya ki rabu da ita, Ammi ta fada tare da hade hannayen ta guri guda".

Hawaye masu zafi ne ke saukowa daga kan kuncin Amriya, daga bisani ta hajiye Mom sannan ta wurgar da wukan.

Sannan ta kalli Mom tace, Kalla ki gani, mutanen da kika dade kina kuntata musu, amma sabo da imani da kuma tausayi wanda yake tattatare dasu suka ce na barki, kije na barki da ranki, Allah kuma zai saka wa mutanen da kika kashe, saboda mugan ci irin naki.

Tana kaiwa nan, tabar wajan Mom, Mom na ganin aka tayi saurin daukar wukar da Amriya ta yar, sannan ta nufi kan Amriya za ta chaka mata.

Kabir na ganin aka ya nufi wajan da gudu, yayin da yayi saurin janyo Amriya jikin sa, ya juya bayan sa, Mom na ganin aka ta chaka wa kabir wukan.

Wani azababban kara Kabir ya saki!, zaro idanuwan gaba daya suka yi, yayin da suka saka ihuu!, a fusa ce suka nufi kan Mom, "Mom na ganin sunyo kanta, tayi saurin daukan zoben Amriya sannan ta fada a katuwar teku dake cikin dajin, wanda samm ba'a ganin karshen ta. Sannan ta kwashe da dariya,

Ba zato, ba tsanmani, taga kowane halitta na cikin ruwan na yoo wa kanta, yayin da su Aljanun ruwan suka yi kanta a fusa ce!, zaro ido tayi, sannan ta saki ihuun ceton rai, amma me karfin tayi wani yinkuri, suka janye ta cikin ruwan.

Ganin akan yasa kowanen su yin hamdalah cewa ta mutu kenen.


faduwa Kabir yayi yayin da jini ya fara ƙetowa ta jikin sa.

Jijjigashi Amriya ta soma yi hawaye na bin kan kuncin ta, Aa Kabir zan ceci rayuwar ka bazan bari ka mutu bah, kada kayi min aka. Kuka ne yaci karfin kowannen su, yayin da suna ji, suna gani, sun kasa cetan Kabir.

Kallon Amriya Kabir yayi yace, me kika ce, yau Karo na farko da kika Ambaci cikakken sunana, tabbbas ina matukar farin ciki da faruwan aka, ki taimaka ki yafe min Amriya, wannan azabtuwar da nayi ma kadai sun isa, ban ki na mutu bah, indai harke zaki rayu, farin ciki na shine na ganki cikin koshin lafiya, ba tareda wani abu na cutar wa ya same ki bah. Aa Kabir ni na yafe maka duniya da lahira, ina matukar sonka Kabir, bazan iya rayuwa ba babu kai.

Ina zuwa yanzu zan yi maka magani, Tana kaiwa nan ta mike tsaye, sannan ta shiga cikin bishiyoyin dajin ta fara tsinko ganyayyaki, sannan ta komai gare su, murza ganyayyaki 'n tayi sannan ta hade su guri guda, sannan ta dora a wajan ciwon, cije leɓen sa yayi, yayin da yake jin wani zugi da raɗaɗin a ciwon.

Dora leɓen ta Amriya tayi kan nasa, sannan ta fara zuba masa dafi,a hankali Kabir yake jin zugin da raɗaɗin na raguwa.
Saida Amriya tatabbatar ciwon yadai na mai zafi sannan ta cire leɓen ta daga nasa.

Yayin da ta fara jin jiri na diban ta, dishi-dishi ta fara gani, Babu shiri ta fadi a wajan wajan, yayin da numfashin ta fara sama-sama.

Hankalin gaba dayan su ba Karamin tashi yayi bah, ganin Amriya cikin mummunan yana yi. Da sauri Kabir ya nufi Inda Amriya take, ganin idanuwan ta sun komai jajir, yayin da bakin ta ya fara kakkarwa.

Kallon su Aunty Amarya tayi tace, " Kabir ya kama ta mu nemo zoben nan, lokaci yana dada kurewa, share hawayen sa Kabir yayi, sannan ya girgiza kai yace shikenen, zan shiga cikin wannan ruwan sannan na dauko zoben.

"Aa Kabir wannan tekun yana da matukar hatsari sosai, zaka iya illata, kuma sannan kai baka iya ruwa bah, zaka iya samun matsala, cewar Ammi".

Kabir yace," ban da mu ba, Koda zan rasa raina, mundin indai zan samu zoben nan toh komai ya wadatar". Aunty Amarya tace, inda wani hajiyayyen ƙwai, Wanda malan Haruna ya taba bani idan ina son kowane Karfi koh wani abu ya lalace,

indai na fasa shi a gefen Wanda nake son ceta, toh zai lalace, kuma ina tunanin idan na fasa shi Amriya zata koma asalin mutum yadda take tun farko.
Amma sai sai idan an kawo wannan zoben tukun an sanya mata.

Babu shiri zuka ga Kabir yayi tsalle ya fada a ruwan. Hade hannayen su suka yi, inda suka soma yi masa adua, saida aka dau kusan thirty minutes fito bah, ganin aka yasa gaban kowanen su faduwa, inda Momsy ta zauna ta fara kuka tana mai fadin, "shikenen yanzu na rasa dana, na shiga uku ni Fatima, yanzu kenen Hydar ya zama maraya kenen".

Ba zato suka ga gangan jikin sa yayo sama, ganin aka, yasa suka nufi inda yake da sauri, sannan su khalid suka fito dashi daga cikin ruwan.

Gaban su ne ya fadi!, ganin ko motsi ba yayi, sannnan kuma gefen guda ya dun ƙule hannun shi, bude hannun Sadiq yayi, sannan taga zoben Amriya.

Da sauri Sadiq ya dauki zoben sannan ya mikawa Aunty Amarya, karba Aunty Amarya tayi sannan ta nufi inda Amriya take,

Danna masa ciki suka shiga yi, amma koh alamun motsi baiyi bah, ganin aka yasa hankalin su ya kara tashi.


Saka wa Amriya zoben Aunty Amarya tayi, sannan ta dauko ƙwan wanda yake fari sall, sa'annan ta samu daidai kan Amriya ta fasa shi, tare da shafa mata shi duk jikin ta.

Ganin bata motsa bah, yasa gaban Ammi ta fadi!, sannan tace kardai ƴata ta mutu!?,
Aa insha Allahu babu abinda zai faru, ki kwantar da hankalin ki, cewar Aunty Amarya.

Motsi suka ji daga cikin ruwa, waigawa suka yi, hatake idanuwan su ya sauka akan Mom, yayin da suka

Please Login or Register in order to submit comment