Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dashi tace aba Mom Duk menene wannan Dan Allah ki kasheni ki rabuda ita, itama kamar yar ki fah take.

Allah ya kiyaye, wannan bah zata taba zama kamar yata bah, kinga kina batamin lck, kibarni na aiwatar da abunda zan aikata akanta. Daukan wuka tayi tanufi inda Ummi ke yashe cikin jini.

Durkushewa salma tayi Tareda rike kafar Mom tafara kuka Tana bata hakuri, amma koh kallo bata isheta bah, saima tureta datayi tafadi kanta yabuge bango.

Hawayene yafarabin gefen fuskan Ummi, cikin matsanci ciwo da radadi tace, mom na roke ki, na yarda ki kasheni amma Dan Allah kibari naga mahaifiyata, inason namata kallon karshe, inason na mata sallama kafun na mutu. Yanda ruhi na zaifi kwanciya.

Na rokeki dan Allah da manzonsa, kibari Nayi wa mahaifiyata Kallon karshe, nice mafi soyuwa agareta, idan kika kasheni batareda tayimin Kallon karshe bah nasan zata iya rasa rayuwanta,

Na rokeki, takarashe maganar hawaye nabin fuskanta, mom bata yi wata wata bah ta tsinka mata mari, tace wato na kyaleki kije kitonamin asiri bah impossible.

Daga wukan mom tayi zata soka mata.

Ummi tace tabbas karshenki bazaiyi kyau bah, tabbas zaki haduda fushin Allah,


Kin kashe rayuka bah adadi, sannan nima yanzu zaki kasheni, bkm ki kasheni bissmillah , rintse idanuwanta Ummi tayi Tareda yin Kalman sha'ada, hawaye na bin kuncinta.

Batareda guntun imani bah Mom ta chaka mata wukan, Kara ummi tasaki, daga nan kuma numfashinta ya tsarke, alamun babu numfashin tattareda ita.

Innalilahi wa innahilahi rajihun.

Ihuun Salma tasaki, Tareda yinkan Mom a fusace, shake mata wuya mom tayi tace indai har burina zai cika banki na kashe kowabah. Buga kan Salma tayi ajikin bango, hatake salma tafadi sumammiya.
Wajan wardrobe dinta tanufa, Tareda jan wardrobe din gefe, Hatake wani kofan ya baiyyana,

Maganganu naji tafarayi wanda nima bansan metace bah, ba'afi mintuna biyu bah kofan ya bude, tanufi inda gawan Ummi yake tajata Tareda jefata cikin wannan kofan,

Takuma daukan Salma tasakata aciki.
Hatake kofan yarufe kansa.




Azabure amriya ta tashi tareda kwallah uban ihuu dayasa gabadaya gidan ya amsa, sosai su nadira dake kusada itah suka tsorata. Tashi tayi Tareda nufa hanyar waje.

Shan gabanta kabir yayi yace ke ina zakije, menene aka, cikin zafin rai da baccin rai tace, ka matsa,

Kabir yace bazan matsaba dukana zakiyi, kallonshi tayi da brown eyes dinta Wanda suka Kara rinewa sukayi brown ta daka mai tsawa, Tareda tureshi a hassale,

Sosai hankalin kowa yatashi.

Mom kam jin karan amriya tayi uwa saukar aradu bah shiri tafara goge jini dake akasa. Tareda feshe ko ina da turare.

Ganin hanyar dakin Mom zataje ,yasa kabir janyo hannunta. Tareda rungumeta.

Ba shirt tafara kokarin cire jikinta daga nashi amma ta gaza, aka tacigaba da kokarin cire jikinta daga nashi amma tagaza, fashewa tayi da kuka, tana mai fadin ta kashesu wannnan azzalumar ta kashesu,

Aunty amarya tace wa aka kashe, sakinta Kabir yayi, suka ga tanufi dakin mom, babu bata lck suka bi bayanta,

Banka kofar amriya tayi, bah shiri Mom ta tashi, Tareda fadin yata amriya Lfy,

Kallon ta amriya tayi tace, menene suka aikata miki zaki kashesu, meyasa, sbd mee, meyasa zuciyarki tagama bushewa babu digon imani acikinta.

Kallonsu mom tayi ta fasheda kukan munafurci, tace yanzu ni amriya nice muguwa, mena miki, Duk irin soyayyar danake nunamiki amma shine kike kokarin yimin sharri.

Amriya tace bah sharri zanyi miki bah, indai akane toh kibari na chaje dakinan indai kinada gsk, rass gaban mom yafadi,

Fashewa takumayi da wani kukan tace yanzu kin mayarda ni makaryaciya kenen, Kabir kaji abunda matarka take fadamin koh, kanajinta kayi shiru, zuwa inda take yayi yace aba mom kada kidaga hankalinki nasan mah bazaki aikata aka bah, kinsan batada Lfy, shiyasa take magganganu.

Amriya tace Lfy yana kalau wannan azzalumar matar Tana neman rayuwanka ruwa a jallo, Tass, tass ya sharara mata mari.

Tareda nunata da Dan yatsa tace, kada ki kuskure kishiga tsanina da mahaifiyata, wato sokike ki hadamu koh, ke wace iriyar mahaukaciya ce.

Mahaifiyata zakiyiwa sharri toh ta Allah bata ki bah banza shashasha, Mara hankali

Dafe kuncinta tayi wanda hawaye suka Fara zarya akai, Tareda girgiza kanta,

Tafuce daga dakin, suma su Nadira suka rufa mata baya. sosai ran kowannensu baiji dadin marinda Kabir yayiwa amriya bah.


Kiyi hkr mom kinsan yarinyar sai a hankali kamar mai tabin kwakwalwa. Bkm kabir ainasani, Bb komi kaje kaci abinci kaji my son, OK mom, kuma kada ka manta ka rarrasheta.

Allah ya kiyaye Kabir yafada, murmushin mugunta mom tayi cikin ranta kuwa tace yanzu kaine nagaba a lissafina a Wanda zankashe.

Jin wayarsa yayi Tana ringing, sallama yayi wa mom Tareda fucewa daga dakin, ganin bakuwar number akan yasa yaki daukan waya, saida aka Kira wajan 10 miss call, ganin wanda ke kira bazai daina bah, ya dau wayan a fusace yace hello waye, waye yake addaban rayuwata da Kira.

Daga Dayan bangaren akace shin ina magana ne da Sir Kabir, kabir yace Eh nine ya akayi.


Dayan bangaren akace toh kazo kudauki gawar yar uwarka Ummi yana bakin titi, gabadaya police da likotoci dakuma yan jarida Sun zagaye wajan.

What Kabir yafada tareda mikewa tsaye yace gawar Ummi Kuma.

Jin aka yasa gabadayansu mikewa tsaye, gaban kowannensu yafadi.



馃ス馃ス馃ス馃槶馃槶馃槶馃槶馃槶

TOH FAN'S MUJE DAI ZUWA

COMMENT & SHARE PLEASE 馃檹馃檹馃檹

ALKALAMIN 馃枈锔忦煐婏笍馃枈锔?
BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒
2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91



馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎
馃鈥嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔?
馃寠馃寠馃寠

馃挮BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM 馃尮
ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煣滒煂? PAGE 3锔忊儯8锔忊儯鈻讹笍3锔忊儯9锔忊儯

WRITTEN & DIRECTED鉁嶏笍 BY BABY ISHA 馃挒馃挒

-----------------------
fucewa amriya tayi tanufi dayan dakin,

Kabir jiyayi kamar ya hadiye zuciya ya mutu tsabar bakin ciki, yau karo na farko a rayuwarsa da wata ta Kalli kwayar idonsa tagayamai mgn .

Mamaki yashigayi yana mai fadin ni Kabir mace tagayamin mgn kuma Nayi shiru how is that possible. Tsaki taja Tareda fadin zatasan ta tabo kabir wlh.

Kwanciya yayi akan gado saiyaji gabadaya gadon mah babu dadin kwanciya, Tsaki yaja yatashi Tareda fucewa daga dakin yanufi, dakin da amirya tashiga.

Tura kofan yayi yace toh mai guri yazo mai taburma ya nadi.

Koh Kallon inda yake batayi bah saima kara gyara kwanciyanta datayi,

Gani tayi banza dashi akan yakara hassala shi yace ke bada ke nake bah koh bakiji bah, zoki fucemin daga daki,

Cikeda bakin ciki amirya ta tashi tace wai kai wane irin Dan takura ne, kace nabar maka wancan dakin nabaro Chan nadawo nan kai meyasa kawai burinka ka ga ka batamin rai. Aba Dan Allah wannan shirmen naka ya isheni, nagaji

Nabar maka wancan dakin na dawo nan kuma ka Kara biyoni yanzu kuma kanacemin wai in futa, toh wlh bazan futa bah.

Kabir yace nikike cewa bazaki futabah, shiru tamai ta koma kan gadon ta kwanta,

Shiru yayi yana mai hayyana irin rashin mutuncin dazai yiwa amriya, Chan gefen gadon yanufa, tareda daukan pillow sannan ya kwanta . Jan bargon yayi Tareda rufawa ajikinsa.

Ganin ya debe bargon gabadaya yasata, Jan bargon ta dunkuleshi ajikinta, ganinta kwashe bargo yasa shi kara Jan bargo. Aka suka dunga ja, amriya naja shima naja.

Daga karshe yasamu ya tureta tafadi akasa, tashi tayi, cikin jin aushi ta janye bargon gabadaya ta hada dashi kabir din, luuuu kabir yatafi sai ajikin amriya,

Faduwa sukayi, numfashi kowanne aicinsu na gogan najuna, rass gaban kowannensu yafadi, kabir kamm jin jikinshi yayi wani iri, sosai suke kallon juna bako kifta ido. Kamshi turaren amriya ne kabir yasaka Hatake yaji wani irin sanyi da shauki nashigarsa, a hankali yadunga lumshe ido, sosai kamshin turarenta ya burgesa.


Gyaran murya amirya tayi sai a lckn kabir yadawo hayyacinshi

Tashi kabir yayi yakoma kan gado sannan yayi aduar bacci ya kwanta, itama amirya aka ta tashi tanufi kan kujerar dake daki sannan ta kwanta akai. Bah shiri baccin barawo yayi hawan gaba da ita.

Juyawa kabir yayi yana fuskantar inda take, Kallonta yayi, yaga yadda gashin kanta ya sauko. Murmushi yayi sannan yajuya ya kwanta.



Washe gari da sassafe amriya ta tashi inda tadora abinci na breakfast , bayan ta gama ta hajiye akan dining, sannan ta zuba wasu a kuloli Wanda zata kaiwa su DAD dake asibity.

Futowa kabir yayi cikin kananun kaya, kayan Ba karamin kyau suka masa bah, kallonshi amirya tayi, cikin ranta tace bah laifi kyakyawa nee amma sai iya shegen jaraba.

Harde hannuwanta amriya tayi tace ina kwana, koh Kallon inda take beyiba, ya nufi dining ,

Zama yayi sannan yabude kulan wani kamshi ne ya daki hancin shi, ya mutse fuska kabir yayi yace menene wannan, amriya tabashi amsa dacewa mee idonka ya ganar maka,

Murmushin takaici yayi tareda janyosa ya Kama bakinta ya murda, kara amriya tasaki, saida yaga ta jigata sannan yasaki leben.

Kara rinewa lebenta yayi tace mugu kawai,
Kallon soya da Kwan data kawo mishi yayi yace wannan Ai shashanci nee , ina kika taba ganin anci abinci mai nauyi da sassafe,

Amriya tace bantaba gani bah toh akanka za'a Fara,

Kabir yace ni bazan ci wannan Abunba, murmushi amirya tayi tareda daukan kulan tarufeshi tasaka acikin basket tace abu yazo gidan sauki, yunwan CE bakaji dakanajin yunwan da ko tuwo nakawo maka zakaci.

Ni yanzu inaso zan kai wa su mami abinci Dan aka inason ka kaini asibity, Kallon bakida hankali kabir yamata yace,

Gsk yane wuyanki ya isa yanka, ni zakice nakaiki hospital Dan tsabar kin Raina min hankali, kuma kin rainani.

Amriya tace toh in baka kaini bah wazai kaini, Dan Allah kayi sauri kada mu makara, kabir yace bazan jee bah, idan kinso kitashi sama,

Hawaye ne yafara ciko mata a ido tace, yanzu ace mami Tana asibity DAD yana asibity ga aunty amarya da gradma, na tabbata tunjiya babu abunda suka saka abaki sbd jimamin mutuwan Ummi, abincin dazasu saka fah aikinsu zan Kai musu,

Yanzu Dan Allah ... Bata karasaba taji yace shikenen, shikenen, ya isa banason takura, shirya mutafi.

Cikeda farin ciki amirya tace, Ngd, kabir yace karki dauka sbd kince nakaiki zankaiki, zankaiki nee sbd mahaifina dakuma mami suna Chan,.

Ya mutse fuska amriya tayi cikin ranta kuwa tace shidai wannan bazai taba chanzawa bah.

Tashi yayi Tareda daukan car key, yanufi hanyar waje ganin akan yasata bin bayansa .

Daidai suma su nadira na futowa daga part dinsu, gaggaisawa sukayi, inda suma sukadau mota, body guard suka bude gate din gidan suka fuce saura su amriya, Wanda yazage sai jamata aji yakeyi .

Mom ce Tafuto daga part dinta idanuwanta sun kada sunyi jajir Duk Sun kumbura tsabar kuka.

Ganin aka yasa hankalin kabir tashi da sauri yanufi inda mom take yace, mom what happened, meyafaru kinsan banason na ganki cikin Damuwa please mom kifadamin menene.

Share hawayenta mom tayi tace kabir, meyasa mutane suka fiye zalinci, yanzu ace yarinya karama kamar Ummi asamu wani mara imani ya kasheta,

Na rokeka kabir tabbas kasaka agano Wanda yayi kisan nan sannan agano Wanda yasace min yarinya Tana kaiwanan ta fashe da kukan muna furci.

Rungumeta kabir yayi, yace insha Allah mom zansa agano ko waye yanzu aka yan sanda suna bincike akan case dinsu Ummi nee insha Allah kuma za'ayi nasaran gano kowaye.


Murmushin mugunta mom tayi tareda Kallon inda amriya take ta kesta mata ido daya, ran amriya ne yakai kololuwar bacci, cikin baccin rai tace, Dan Allah kazo mutafi kada mubarsu, sunajin yunwa basuci komai bah.

Sakin mom kabir yayi yace mom bara muje mudawo zamuje asibity. mom tace toh nima mutafi tare zanje.

Cikin fusata amriya tace Aa mukadai zamuje, babu inda zaki bimu.

Kabir yace me kike nufi, amirya tace aba kalb yanzu so kake muje ta dunga mana kuka , baka ga yadda fuskanta ya kumbura bah, baikamata muje da ita, bah sbd kada taje ta dunga kuka, itama mami tafara kuka,

Kaga gwanda ta zauna a gida zuwanta babu abunda zai tsanana mana, zuwa inda mom take amriya tayi tace,

Mom kije ki huta kisha magani ki kwanta sbd baikamata ace kina ganin abunda zai daga miki hankali sbd halinda kike ciki.

Kabir yace mom amriya tafadi gsk kije ki huta, zamuje mudawo da gawar a mata sutura akaita gidanta na gsk.

Fashewa da kuka mom tayi tace za'a kai Ummi gidanta na gsk shine baza a barni naga gawar yata bah, sbd mee,


Cikin jin haushi da kunan rai amriya ta daka mata tsawa, Tareda fadin bayan kinkasheta, wato baki gamsu ta mutu bah shine kikeso kibimu, idan bata mutu bah ki karasata achan tantiriya, azzaluma, mai bushashiyar zuciya.





MANAGE PAGE PLS 馃檹


COMMENT & SHARE 馃檹馃檹馃檹
ALKALAMIN鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍
BABY ISHA馃挒馃挒馃挒
2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91


馃挮WRITER ASSOCIATION @@@@@@@@@@@馃挮


馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎
馃馃馃馃馃馃馃馃
馃寠馃寠馃寠馃寠馃寠馃寠

BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM 馃尮馃尮

ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂? PAGE 3锔忊儯9锔忊儯鈻讹笍4锔忊儯0锔忊儯


WRITTEN & DIRECTED 鉁嶏笍 BY BABY ISHA 馃挒馃挒(AISHA M.B)

------------------------

Firgit mom ta tashi daga mafarkin da takeyi, gabanta ne yafadi tace, yakamata Nayi wani abu kada yarinyar nan ta tona Min asiri.

Tashi tayi tareda daukan mayafinta tanufi hanyar waje a daddafe Dan dukan da amriya tayi mata bah kadan bane.

Futowa tayi harabar gidan, Daidai lckn taga su amriya suna kokarin Shiga mota.

Kabir tafada da Dan karfi, juyowa kabir yayi yace, mom ina wuni , mom ta amsa da Lfy son, ina zakuje aka.

Kabeer yace wlh zamu kai wa su mami abinci nee, Tom kabeer muje koh nima inason naje natayata jaje,

Kabir yace Aa mom kizauna ki huta koh.
Mom tace hutun me zan Zaune yi, yata amriya kice masa Dan Allah yabarni naje.

Amriya tace mom keda Danki ni ina ruwana, dakin ne fah, kinga kinada Dama kimasa Mgn yaji.

Kabir ya harari amriya, sannan yace shikenen mom Tunda kince aka muje, bude mata kofan motan yayi, tashiga,

Inda amriya tatsaya tazuba ido koh zai bude mata itama.

Ganin bata Shiga motan bah yasa yace ke bazaki shigo bah ne koh mee, kinafah batamin lck, amriya tace toh ni bazaka bude min kofan bah,

Binta yayi da kallo yace, Mace daya tilo takk zan iya budewa kofa a duniyar nan, itace mahaifiyata, so idan kinga bazaki iya budewa bah toh, wa kanki, musaimu tafi,

Ya mutse fuska amriya tayi ta bude kofan motan tashiga, masu gadi ne suka wangale musu kofa suka fuce.

Tunda sukafara tafiya Ba wanda ya kulla Dan uwansa saima sake sake ds kowannensu yakeyi.


Direct hospital din suka nufa, ba'afi 20minutes bah suka isa wajan, parking yayi yafuto daga cikin motan sannan yabudewa mom kofa ta futo daga cikin motan.


Sanin cewar bazai bude mata kofa bah yasa itama ta futo daga cikin motan, tareda futowa da food flask din, direct cikin reception din suka Shiga.


Tarar dasu sukayi a zazzaune kowa yayi tagumi, gaishesu su kabir sukayi, su aunty amarya suka amsa batareda walwalah a fuskokin suba.


Amriya tace Yauwa ga abinci na dafa muku, barana siyo Ruwa, Gradma tace munkoshi wlh,

Hade rai amriya tayi tace wlh Baku isa bah, sai kunci, murmushi DAD yayi yace Tom shikenen, daukan daya daga cikin flask din amriya tayi tace barana kaiwa mami nata abinci nasan tanajin yunwa.

Dad yace mushiga tare, tunjiya rabona naga yar uwata. Tashi sukayi gabadaya sukashiga cikin room dinda mami take. Da sallama sukashiga, inda mami ta amsa kasa kasa.


Murmushi amriya tayi tace mami ga abinci nakawo miki, kici kinji, idanuwan mami ne ya cika da hawaye tace Aa amriya nakoshi, kibarni da tarun bakinciki, da kuncin da nake ciki.

Amriya tace aba mami, Dan Allah kidaina fadan aka, Allah yarabamu da bakinciki, Allah kada yakawo abunda bazai wuce bah., abunda yafaru yaruga daya yafaru, Allah yaruga daya kaddara cewar Ummi zata mutu batareda kinyi ido hudu da itah bah, ki share hawayenki mami , mu fauwala wa Allah komai,

Bai kamata ace kina kuka bah aduar ki take bukata bah kuka bah,

Mami tace yanzu shikenen Ummi ta rasu, batareda ansan wanda yakasheta bah, yanzu auta tah ta tafi kenen.


Amriya tace aba mami kin manta kinadani, na miki alkawari zan Maye gurbin Ummi acikin zuciyarki,


Kuma Allah yatona asirin wanda yayi wannan kisan nan bada dadewa bah, munafukai masu idon jemage, Tafada Tana Kallon mom takeyi fari da ido.

Mami tace Dan Allah inason naga gawar yata, DAD yace bazai yuhuba sbd anruga da ankaita gidanta na gsk.

Wasu hawayen ne suka Fara zubowa, Mom tace Allah sarki Ummi Allah yajikan ki da rahama, yamiki rahama yasa aljanna firdaus ce makomarki .

Gabadaya suka amsa da Amin

Maryam wato mami cewar mom sannan tace Dan Allah kici abinci kinji,abunda yafaru yaruga daya faru zaizai Allah ya kiyaye gaba.

nadira tace, mami please, taya hankalin mu zai kwanta idan muka ganki a wannan halin.

Share hawayenta mami tayi tace shikenen Naji zanci , Yauwa mami naa, yanzu baranaje na siyo ruwa, wanda zaku sha,


Khalid yace kibarshi nizanje, Amriya tace Aa kana min bakinciki zanje Aiken mami naa, bakasan nasamu lada koh

, murmushi gabadayansu sukayi ,Tana kaiwanan tafuce daga dakin. Murmushi Kabir yayi karo na farko da amriya ta burge shi.

Kallon kabir mami tayi tace kabir gsk kayi dacen mata, kariketa hannu bibbiyu, karike matarka kuzauna Lfy, yadda hakkinta bazai aukanka bah itama hakkinka bazai aukan ta bah kaji, wlh sa'ar mata, irin Mace kamar amriya, mai tausayi da amana dakuma taimako daidaiku nee, kaji koh, kabir yace insha Allah mami Ngd, kifara cin abincin kafun takawo ruwan. Barana je nadawo yana kaiwanan yafuce,


futan shi keda wuya suka ci karo da abbansu Khalid, gaisheshi kabir yayi, abba su Khalid Ya amsa .

Tareda fadin suna ciki kuwa, kabir yabashi amsa da cewar Eh suna ciki, OK tom shikenen Ngd. Kabir yace ya hkr, abba yace wlh Lfy Ngd.


Shiga dakin yayi da sallama a Bakinsa, inda su DAD suka amsa gaggaisawa sukayi, inda su DAD suka fuce suka basu guri.



Inda ake sayarda ruwa amriya tanufa inda mutanen wajan sai binta suke da kallo.


Sallama amriya tayi, inda mutanen wajan suka amsa,

Sannan tace abani ruwa na roba, mikamata mai ruwan yayi ta karba, Tana shirin budewa tasha taji Ihuun mutane suna fadin aka mota ,aka mota.

Juyawarda zatayi taji anfado mata ajiki, daka tawa amriya tayi ta dago da matar. Daga jikinta bayan amriya matar ta tsaya sannan matar tafara mgn cikin dashashiyar muryanta tace, kada kibari su kama ni Dan Allah nidin bah mahaukaciya bace.


Daya daga cikin likitocin yace, ke yarinya ki matsa daga wajan matar nan mahaukaciya cee, tanada cutar mantau .tsintar ta akayi acikin ruwa . Yanzu sacatery za'a kaita shine take guduwa.

Kallon idanuwan matar amriya tayi tace Wacece kee, hada idanuwa sukayi da matar Hatake hankalinta yatashi, tarike hannuwan amriya sannan tace kece, kece, tabbass kece.

Kokarin cire hannunta amriya tayi tace ni Kuma menayi, matar tace ke zaki kawo karshenta, ke zaki gamadasu, dole ki gama dasu babu inda zalinci ya Dore, dole hasan cewar jaruma ta baiyyana, kada kibarsu, kada kirabudasu, ki yakesu har sai inda karfinki yakare yata.

Kada kataba gazawa, yakamata ace asan cewar kin baiyyana, mai kawo karshen zalinci ta zo. Kitashi tsaye, kitada makamai ki yake su,

Taruke kafadar amriya tace kada kirabudasu na rokeki, ki kawo karshensu, tabbas zun debo ruwan dafa kansu, ki kashesu karki Kyale kowa. Tana kaiwanan matar tafadi summamiya , daukar matar sukayi suka feceda itah daga asibity.


sosai hankalin amriya yatashi ,jikinta yafara karkarwa. Karasowa kabir yayi ganin mutane sun taru aka yasa yaja hannun amriya suka bar wajan.



Bangaren su mami kuwa, Shiga ciki abba yayi yace sannu maryam ya jiki, sama sama, mami ta amsa.


Ajiyan zuciya abban su Khalid yayi yace, nasan nayimiki babban laifi, na tauye miki hakkinki a matsayinki na matata. Bansan dawane ido zan kalleki bah, tabbas na aikata kuskure kuma nagano kuskurena, Dan Allah na rokeki kiyafemin ki gafartamin,


Na miki alkawarin cewa akan bazata sake maimaita kansa bah, Dan jimm mami tayi tace naji nayafe maka, Dan Allah kafuta zan kwanta.

Aba maryam kenen haryanzu fushi kike dani, ki taimaka ki yafemin, wlh bada San raina nake aikata, abunda nake yamiki bah, koh kishiyarki mah tuntuni na Dade da sakinta, kawai namiki karyar cewar ta tafi wajan iyayenta Hutu nee.

Mami tace toh ni ina ruwana da ita Ai bah akaina take zaune bah. Kowa zamansa yakeyi.

Murmushi dad yayi yace, matata kenen, shikenen zan tsuguna Kuma na hada hannayena na rokeki Dan kisan da gsk nake
.

Kokarin tsugunawa yake, mami tayi Saurin mikewa tace Aa, ka rufamin asiri, sokake Allah yayi fushi dani, na yafe maka, toh idan mah ban yafe maka bah mezanyi, abunda yafaru yaruga daya faru, wlh na yafe maka duniya da lahira kuma.


Nice mah yakamata ace na nemi gafarar ka sbd magganganu dana fada maka Mara dadi, Dan Allah ka yafemin.


Abba yace aini babu abunda kukamin Kuma baki min laifin komai bah, akasari mah dalilin magganganu da kika fadamin yasa na gano kuskure naa, Dan aka na yafe miki. Murmushi mami tayi tace Alhmd ina mai godiya a gareka, abba yace nine yakamata na gode miki.


Jijigata Kabir yashigayi Ganin tafara futa a hayyacinta,yasa yanufi gida da itah batareda yanar dasu DAD bah, direct daki yakaita, Tareda zaunan da ita


yace ke meyasa meki, meyafaru, Rike hannunsa tayi wanda zoben tah ke sanye tayi, tareda saita Daidai saitin zuciyarta ta dora, zoben akai, wani irin nutsuwa ne yafara ziyartatta,


dauke hannunsa zaiyi ,yaji takara kankame hannun tace, kada kacire hannunta katsaya, tsyawa yayi yana Kallon ikon Allah, rintse idanuwanta tayi sukacigaba da Tsayuwa wajan harta samu nutsuwa.


Dagowa tayi tareda sakin hannunshi tace kayi hkr na Rike maka zobe batareda izininka bah, ka yafemin, Kallonta Kabir yayi yace, meyasa wancan matar naga tarike ki, meyasa kike yawan faduwa idan kinga abu ko Kuma idan an watsa miki RUWA. Meyake faruwa dake kifadamin gsk, yau inason kifuto ki gayamin asalin Wacece kee, meyasa Duk wannan, fadamin Wacece kee.

Dago idanuwanta tayi wanda hawaye sukara zarya akan fuskanta, tace ni be kowa bace bace mutum irinka.

Yes I know, amma inason insan dalilin dayasa kike faduwa just like that, koh ki tsuma, kokuma akasarin aka, waye yayi sanadiyan faruwan akan.

Share hawayen dake bin kuncinta tayi tace, KAINE SILA . ...........






馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃寠馃寠馃鈥嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔?


COMMENT & SHARE PLS 馃檹馃檹馃檹.

ALKALAMIN 馃枈锔忦煐婏笍馃枈锔?
BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒(AISHA M.B)
2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91


ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂? PAGE 4锔忊儯0锔忊儯鈻讹笍4锔忊儯1锔忊儯

WRITTEN & DIRECTED 鉁嶏笍 BY BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*鉁嶏笍
(J.W.A)
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan 茩asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau茩i.鉁忥笍



------------------------
Jin furucinta yayi kamar saukar aradu. Juyowa yayi ya da Kallon mamaki ya kalleta, ya ce "Kamar ya kenen? Ban fahimta ba."

'Dan jim Amriya tayi ta ce "Kwarai kuwa, kaine silan komai da yake faruwa da ni."


Kabir ya ce "Ni Kuma taya na zama sila? fad'amin ina jinki." ya karashe maganar fuskanshi a had'e.

Kallonshi tayi ta ce "Eh kaine, kuma har yau har gobe zan cigaba dafad'in kaine."

Kabir ya ce "Nifa ba abunda na tambaye ki kenen bah, tambaya ta itace tayaya ni nazama sila?" Ya fad'a tare da sunkuyar da kansa gefe.

"Amriya ta ce, ta yarda na ceci rayuwarka daga teku, wanda shine ta saka haryanzu ka kasance a Raye.."

A firgice ya juyo ya kalleta, da sauri ya mike idan ran kabir yakai dubu to ya 'baci ,ya ce "Harke kinkai kimin karya, wato kin samu labarin cewar wata ta ceci rayuwata, Kuma na kamu da sonta, wato saboda kinsan rauni na shine kike son kibi ta salon yaudara ki yaudareni, that can never be possible."


'Dago idanuwanta amriya tayi wanda suka kada sukayi jajir, ta ce "Dan Allah ka yarda dani , wlh ni ce na taimakeka, zobena ne a hannunka wanda ya su'buce ya fad'a hannunka, dan Allah ka bani zoben na koma duniyata, inba haka bah mutuwa zanyi na rokeka."


"Ya isa, wannan magganganu naki sun isheni haka, bana son na karajin komai daga bakin kii, sbd kin rainamin hankali shine zakice wai kece, toh duk wanda ya turo ki wajena domin ki zo ki yaudareni toh ki koma wajansa kice inji ni na ce hakan

Please Login or Register in order to submit comment