Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki ga wasu masoya bah sun rungume juna, Dan aka kawai ki bari na siya miki.

Saurin cire jikinshi kabir yayi daga na zainab yace, ke wace mahaukaciyar ce, taya zaki rungume ni a gaban jama'a.

bakida hankali ne, kayi hakuri, kaji my love.

Cikeda takaici Amriya ta dauke idanuwan ta daga kansu, ta Kalli yusuf tace, sweetheart, ni wannan nakeso tayi nuni da hannun ta,.

da sauri kabir ya juyo jin kamar yasan wannan muryar, hada ido sukayi da Amriya Hatake gaban shi ya fadi.

Amriya ta cigaba da fadin Sweet, wannan nake soo, yusuf yace kada kida mu, zan siya miki koma Wanne,

wani irin kishi ne ya turnuke zuciyan Kabir, nufan inda suke yayi tareda Jan hannun Amriya yace, waya baka izinin futa da matar wani, kaidin waye


ke Kuma ya fada yana Kallon Amriya, Dama Ashe ke yar iska ce, uban waye ya baki izinin futa da wani na mijin, Dama abunda ke faruwa kenen idan ka auri karuwa,

Tasssss Amriya ta tsinka wa Kabir mari.

zaro idanu jama'a wajan sukayi. nuna Kabir Amriya tayi da Dan yatsan ta tace...
.


COMMENT & SHARE PLS

KUYI HKR JIYA KUNJI SHIRU WLH WAYANA NE YASAMU MATSALA,
AMMA INSHA ALLAHU ZAN GYARA

ALKALAMIN AISHA M.B ( BABY ISHA)


BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
ALJANAR RUWA CE PAGE 45&46
WRITTEN & DIRECTED BY
AISHA M.B (BABY ISHA)


---------------------------------------
Cikin baccin rai Amriya tace, har kai waye, Da zaka zo ka neman cimin zarafi agaban jama'a, shin na taba ganin ka ne ,koh kaidin mijina ne, da zaka zo kana ci min mutunci,

Bansan ka bah, baka Sanin bah, toh ina ruwan ka dani, kazo da masoyiyar ka, nima nazo da nawa, shin akwai laifi ne aciki, toh ka sani, aure ce ta hada ni dakai , Kuma yanzu ta raba, Dan aka baka da iko akaina, baka San irin muguwar tsanan da nayi maka bah, tsanan da nayi maka koh ma'auni, bazai iya aunawa bah, Kuma kayi na farko, kayi na karshe. Kada koda gigi yasa ka kara aikata min aka, Dan wallahi, abunda zan maka bazaka jita da dadi bah.


Idanuwan "Kabir ne suka kada sukayi jajir! cikin zafin rai, yace ni kika mara, kin manta waye ni, Amriya tace taya zan iya manta da Kai, Dama ai mutum baya taba manta alhery da mutum ya masa, kai baka min alhery bah, aka sin aka mah, zalunta ta , kake yi,

Kallon shi tayi tace, tsaya wa ina magana da Kai bata lokaci ne, maida Kallon ta kan yusuf tayi tace, sweet, Dan Allah ka tawo mu bar wajan nan, naga yan hassada da k'eta, sun cika nan wajan,

Zuwa daf, da wajan zainab tayi tace, ke me kike da suna, wallahi, Kabir yafi karfin ki, kada ki sake kiyi wasa da wuta, domin kuwa idan ta fusata, baza ki ji da dadi bah.

Kallon "Zainab Amriya tayi tace, ke daka ta nan , ni bah sa'ar wasar ki bace, kije kifara ji da matsalan dake damunki, kafun ki kara fada wa a wata matsalan, wallahi, Duk abunda na miki toh ke kika siya da kudin ki.

Tsintar kansa kabir da yin shiru, Amriya na kaiwa nan, ta bar wajan, bin bayanta yusuf yayi,

Tsaki Kabir yaja, ganin kallo gabadaya ya koma kansa, fucewa shima yayi daga wajan, inda zainab ta bi bayan sa, Tana Kiran sunan sa.

Shiga cikin mota yayi, ya tada motan sannan da mugun gudu ya bar harabar wajan, zainab na Iso wa taga yabar mall din.


Tunda suka Fara tafiya babu Wanda ya ceda wani cikan ka, yusuf ne yayi karfin halin fadin, Meyasa kika tozarta Kabir a bainan jama'a, Kuma Meyasa kika ce ni masoyin ki ne, bayan Kuma ni bah masoyin ki bane.

Aba Amriya, Shifa mijin ki ne, bai ka mata ace kin masa irin wannan rashin mutunci bah, bai kamata mah ki mareshi bah, why Amriya, Why?

Dago fuskan ta tayi, wanda suka jiku da hawaye tace, Duk abunda Nayi masa shiya siya da kudinsa, ni menene bemin bah, zagi, Duka, babu abunda baiyi bah.

Tabbas bai kama ta ace na maresa, bah, amma meyasa zaice min karuwa? Kalman da na tsani akira ni dashi, ba iya ni kadai bah, koh wata macen da tasan daraja da kiman ta ta d'iya Mace , ba zata, so a kira ta da Kalman karuwa bah,

Yana min Duk abunda ya gada ma, banta rama wa bah, amma yau, yakai ni kololuwar makurar karshe, shiyasa na maresa, Kuma nasan akan bai dace bah, bai ka mata na mare sa bah, amma duk abunda na Mai shiya siya da kudin sa.

Cigaba da tuki yusuf yayi, Har suka isa gida,


Tuki yake yi batareda yasan inda yake nufa bah, magannanun ta ne suka Fara mai yawo acikin kwakwalwar sa, bakasan irin muguwar tsanan da Nayi maka bah, tsanan da koh ma'auni bazai iya aunawa bah. Kuma kayi na farko kayi na karshe, kada koda gigi yasa ka Kara aikata min aka Dan wallahi abunda zan maka bazaka jita da dadi bah.

dafa kansa yayi, yayinda idanuwansa sun kada,sunyi jajir kamar garwashi. Burki yaja ya tsaya abakin hanyar titi, dafa stairing motan yayi, ya Kalli mirror cikin motan, yaga shatin hannunta a fuskarsa, shafa fuskarsa yayi, yayinda yake jin zuciyar shi nayi masa tiriri, da kuna, yace, ni Kabeer, Mace ta mara, Kuma banyi komai akai bah, how is that possible.

Duda cewar bah mutum bace, ALAJANR RUWA CE, amma akan bazai sa na kasa daukan mataki bah, dole ne hukunta ta, Daidai da laifin ta, Kuma zata min bayani wanene wancan, malohon wanda take kira masoyi. Horn yaji Hana masa, akan yasa ya tada mota yabar wajan, direct gida ya nufa, inda body guard suka bude masa gate, koh gama parking baiyi bah, yashiga cikin gidan.

Ganin ranshi a bace yasa "Mom tace, son what happened? Wani ya bata maka rai ne? Ko kuma zainab" bata yi maka bah, Kabeer yace yes, wallahi bazan boye miki bah, i don't like that girl, idan na aureta wahala kawai zata sha, domin kwata kwata, yarinyar bata kai level din da zangan ta na yaba Ba,

Please Mom ki taimaka min, Murmushi Mom tayi tace son kenen, yanzu Zainab Meyasa meta Da zaka ce bata yi maka bah, and wallahi kun dace da juna,

Kabeer yace, ba dacewa bah koma menene, nidai yarinyar nan bazan aureta bah, that's the fact.

Kabeerrr ! .... Mom ta fada a tsawa ce, Tareda nuna shi, tace idan har kaci ka Dan halak, toh kada ka aureta, Kaga abunda zan maka, tsawar Mom ne yafuto dasu Dad dakuma Aunty amarya, sai su Nadira .

Dad yace Karima meyafaru? Meyasa kikayi Ihuun sunan kabeer, Mom tace Dad kabeer can you imagine this what you called son, Dad yace i don't get you, kabir bah danki bane bah, ai bai kamata ace ki dunga tsawatar mai bah, kamata ai ace ki gargade shi, ko kuma kibashi Shawara, abunda ya kamata kenen, please Karima banason abunda zai tayar wa kowa hankali.

Tukun nan mah, menene ya faru? Dad ya tambayi Mom, girgiza kai Mom tayi tace, no need, bah bukata, kowa zai iya tafiya, rasa abun cewa kabeer yayi, nufan inda Mom take yayi yace, Mom Allah ya baki hakuri, kiyi hakuri ki yafemin, na miki alkawarin cewar bazan kara bijire wa umarnin ki bah, zanyi Duk abunda kikeso,

Bazan kara bata miki rai bah, am sorry Mom, dakatar dashi Mom tayi da fadin, i don't need your sorry, bana bukata rike abun ka, Kuma banason ka auri Zainab din, shikenen hankalin ka ya kwanta bah, toh na fada, na cancelled din auren ka da zainab.

Dama nasan Wannan
Na'ananniyar Yarinyar Chan ce tayi maka asiri, tunda nake baka taba bijire wa maganata bah, amma Zuwan Amriya gidan komai ya chabe, babu daman Nayi maka magana kaji, saboda ta asircemin Kai.

Karimaaaa! Dad ya fada a tsawa ce, Cikeda baccin rai Dad yace Karima mind your words, ina ruwan Amriya a wannan zance, Dan ita ta kasance bah mutum bah, shine kike zargin ta da mugun nufi, ni mama fara zargin ki wallahi, maybe mah abunda Amriya ta fada a kanki gaskiya ne bah karya bah,

Fashe wa Mom tayi da kuka tace, shikenen hankalin ta ya kwanta, Gashinan tana kokarin raba ni da ahalina, wannan wace iriyar masifa ce, nida gidana amma ake kokarin rabani da y'ay'ana.

Kallon su Nadira da khaleed Aunty amarya tayi, tayi musu nuni da hanyar waje, jiki a sanyaye, suka Mike Tareda fucewa daga part din.


Aunty amarya tace, Noo Mom bai kamata ace mahaifiya kamar ki na irin wannan furucin bah, kema fah kin haifa, Kuma bazaki so aci mutuncin Y'ay'an ki bah, ki kwantar da hankalin ki, komai zaiyi daidai, bai kamata kina tayar da hankali akan abunda bai Kai ya kawo bah,

Mom tace, kenen bansan abunda nake yi bah koh, koh ance miki kema bansan, kulla kullan da kike yi bah, toh wallahi zainab, ki kiyaye ni, ni bah sa'ar wasar ki bace bah, ki rike girman ki, na rike nawa, karki sa na daina ganin mutuncin ki,

Grandma tace wai, meyake damunki ne Karima, shin wani abu yau kika sha kome, yanzu tsabar rashin kunya, a gaban nawa kike fadan irin wannan magannanun, koh kunya baki ji bah, toh maza maza koh wa ya watse kafun na bata muku rai.

Kwan kwasa kofan gidan, doct khadija tayi, tashi daya daga cikin body guard din yayi, yanufi wajan gate din Tareda bude kofan, ganin doct khadija ne, ya sashi yin sauri ya bude kofan.

Shiga ciki doct khadija tayi, Ta Kalli koh ina na harabar gidan, sa'anan ta girgiza kanta tace, shekara da shekaru kenen, rabon da na dora kafana akan wannan gidan, wacce tayi sanadiyan barina gida nan, itace takuma yin sanadiyan dawowa ta, yau bah gobe bah, kowa zai San abunda kika shuka Karima.

Chan cikin gidan ta nufa Tareda Kwankwasa kofan parlour, Aunty amarya tace Grandma kamar naji Hana Kwankwasa kofa, barana je na bude kofan.

Bude kofan Aunty Amarya tayi, taga bakuwar fuska, gaisheta Aunty amarya tayi, doct khadija ta amsa , sannan doct khadija tace, Karima na nan kuwa?, Aunty amarya tace Eh Tana nan, shigo

Shigowa ciki doct khadija tayi, kamar ance Mom ta juya , Juyowa Mom tayi ,lokaci daya suka hada ido da doct khadija.

Gaban Mom ne yayi mumunan faduwa! , yayinda zuciyar ta ya fara Duka uku uku, Murmushi doct khadija tayi tace, kina mamaki ne, Kinga ban mutu bah koh, bakici galaba akaina bah,

Cikin fusata, Dad yace meya dawo dake gidan nan, bayan bakin ciki da kuncin da kika sanya mu aciki, wato Kara dawowa kikayi domin ki kara, saka mu a wani kuncin kamar yadda kikayi shekarun baya da ya wuce.

Maza zo ki futa, Bamua bukatar, ma Yaudariya, maciya amana, Grandma tace Muhammad barta tukunan, ni zanyi maganin ta

Ke khadija, kalle ni nan, Kallon ta doct khadija tayi, Grandma tace kalle ni da kyau, baka nake bah fara nake bah, wato Kara dawowa kike, domin kikara haddasa wani fituna koh, toh ta Allah ba taki bah, baki isa kin kara yiwa wannan ahalin komai bah, Dan aka maza ki fuce, kafun na dauko tabarya,

hawaye nee suka Fara saukowa daga kuncin doct khadija tace, bazan ga lafin ku bah, laifin wacce ta hada mu daku, zan gani, nazo gidanan ne badan komai, bah sai Dan na tona asirin abunda Baku sani bah, na tsawon shekara da shekaru, inason ku bani Dama, Dan Allah zan fada muku gaskiyar abunda ya faru,

Kallon Dad doct khadija tayi tace, tabbas abunda Amriya ta fada muku gaskiya ne, babu karya, first wife dinka , wato Fatima Tana raye bata mutu bah, Kuma tana kulle ne acikin wannan gidan na tsawon shekaru, batareda ansani bah, Amriya ce kawai ta iya gano, inda Matarka take.

Kallon ta Dad yayi, yace Dama wanda ya ruga ya rasu yana dawowa ne, wato zuwa kikayi domin ki cusa mun bakin ciki a zuciyata koh, leave now, banason jin komai dazai futo daga bakin ki.


Doct khadija tace, zan tafi, amma bazan bar gidanan Ba Tareda na tona asirin wannan shedaniyar bah.



COMMENT & SHARE PLS
ALAKALAMIN
AISHA M.B(BABY ISHA)



BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM.
ALJANAR RUWA CE PAGE 46 ?47
WRITTEN & DIRECTED BY AISHA M.B (BABY ISHA)

-----------------------------------------
Murmushin k'eta Mom tasaki sa'anan tace,
Yanzu khadija wane laifi na aikata da kike son wargaza gidana, mene na aikata miki? Wane abu na tsare miki a rayuwar ki .

Meyasa kike son ganin baya na ta karfi da yaji, Grandma tace, Karima ki rabudani ita, so take ta lalata miki aure, toh ta Allah na Tata bah, maza zoki futa kafun na sakar miki karnukan gidanan, suyi hawan gaba da ke.

Wani kukan bakin ciki ne ya ziyarci Doctor Khadija, doct khadija tace, ku yarda dani wannan matar shedaniya.

Mom tace DAD Kabeer Dan Allah ka roke ta, ta bar mana gida, saboda wannan matar munafuka ce.

kece dai babbar munafuka!" sukaji kalisat tafada! ,ta cigaba da fadin kwarai kuwa, kece munafukar,

Tsinka mata mari doct khadija tayi tace, Duk abunda zai faru, karki kuskure kikara ce mata munafuka, saboda a haifa ta haifi sama dake. Kuma itadin a matsayin mahaifiyar ki take.

Allah ya kiyaye, Allah ya mun katangar karfe da wannan shedaniyar algunguma, mara imani. Wannan matar bata cancan ci akirata da Kalman uwa bah, domin kuwa yin akan kuskure ne.

Dad yace, ke Kalisat," kinsan abunda kike fada kuwa, kina da hankali, bakisan cewar, Tana a matsayin mahaifiyar ki bane, ya karashe maganar ranshi a matukar bace

kalisat tace, Dad am sorry to say", gaskiya, ita ba'a matsayin mahaiyata take bah, saboda mahaifiyata ta fita daraja da kima, kuma ita wannan azzaluma ce, mara zuciyar tausayi.

Magannanun tane suka sauka akan dodon kunuwan Khalid dakuma su Kabir dake sauk'owa daga upstairs, bata hankara bah taji sauk'an mari akan kuncinta, Dafe kuncinta kalisat tayi,

Idan ran Khalid ya Kai dubu toh ya baci, yace kalisat, kina cikin hayyacin ki kuwa, wacce ta raine mu, ta kula damu tamkar yaran ta, ta nuna mana soyayya kamar yadda itama Mami iya karkarin abunda zata iya kenen, shine yau kike kallon tsabagen Idanuwanta kina fada mata magana son ranki, kamar itadin sa'ar kice.

Kalisat tace wallahi matar nan, bata son mu Illah son cutar da mu da take kokarin yi, Amriya ce kawai take dakatar da ita, amma na tunan ta gama da yahya kabeer ya kashe kowa na wannan family.

Fashewa Mom tayi da kuka!, tace, Yau a gaban idona ake min karya cewar ina kokarin cutar da ahalin nan, meyasa zanyi muku aka, kalisat. Duda irin alkhairy da nayi muku amma da irin wannan abun zaku saka min dashi Dama ance Dan adam butulu ne, Hatake ta Fara tarin karya, tana zubda hawaye

Hakuri su Kabir da Dad suka Shiga bata, cikin fusata Kabir ya nufi inda kalisat ke tsaye, Ba tareda bata lokaci bah ya fuzgo ta, sa'anan ya shake mata wuya yace, ke mahaifiyata sa'ar ki ce, wallahi Kuma idan wani abu yasami mahaifiyata saikin dandana kudarki,

Murmushi kalisat tayi tace, mahaiyar ka, ko mahaifiya yar basaja, ta dolantar daku, tasaka ku cikin duhu, babu abunda idanuwan ku ke gani sai duhu, Amriya tayi kokarin fidda ku cikin aske, amma kuka ki ku fahimce tah.

Da wacce kake Kira mahaiyar na sonka baza tayi kokarin cutar da rayuwar ka bah, idan akane meyasa ta kashe Ummi.

Da sauri Kabir ya sake ta, ya dago da idanuwansa wanda suka kad'a sukayi ja.
yace, what nonsense are you talking about.

Kalisat tace am not saying nonsense, amma ni nasan tabbas Mom itace ta kashe Ummi, kuma sa'anan ta batar da Salma.

Gabadaya suka hada Baki wajan fadin what! Dad yace toh menene hujjar ki na fadin akan, gayamin Wacece hujja.

Nice hujja . Sukaji an fada, juyawar su keda wuya suka ga, Salma duk ta bi ta rame, tayi baki. Da sauri su nadira sukaje suka rungume ta, fashewa Salma tayi da matsanan cin kuka mai taba zuciya.

Nadira tace, Salma Wacece tayi miki aka, ina kikaje cikin wadanan kwana kin, ba Tareda kin dawo bah,

Salma tace babu inda naje, asali mah Mom ita ta bayar dani, ba Tareda kowa ya sani bah, kuma tabbas itace makashiya, wacce ta raba Ummi da rayuwar ta, saboda son kanta da son abun duniya.

Dafa kanshi Kabir yayi Wanda yake mugun saramai, Kallon Mom wacce tayi zuru zuru, Kabir yayi yace, Mom" shin abunda Salma ta fada gaskiya ne koh kuwa karya take miki? Shiru Mom tayi, ta rasa wane karya zata Kuma yi a wannan karan.

Grandma tace, ba shiru aka ce kiyi bah Karima, tambaya ce mai sauk'i, shin kece kika kashe Ummi, kuma kika batar da Salamatu,

Mom" tace wallahi karya take yi, saboda me zan kashe Ummi, me ta, tare mun, menene riba ta idan na kasheta, wallahi wannan abun kawai hadamin akayi domin kawai aga an rabani da gidan aurena.

Kabir" yace toh Salma kindai ji abunda Mom ta fada, tace ita batasan wani batun kisa bah,

Salma tace Aba Mom, ramin fah karya kurarre ne, say the truth and shame the devil, kiji tsoron Allah Mom, duda cewar ta sanadiyan ki nazo duniya amma akan bazai sa na rufa miki asiri bah,

Kiyi hakuri Mom, ke mahaifiya ta ce, amma dole yau sai gaskiya tayi halinta, tabbas babu karya ke kika kashe Ummi, a gaban idona, ta dunga baki hak.. Bata karasa bah kuka ya kufce mata, sosai take kuka idanuwanta suka koma ciki sukayi jajirr.

Cikin sheshekar kuka, Salma tace, babu abunda Salma bata ce bah, don kawai ki rabu da ita, babu koh d'igon tausayi kika samu, kwalba kika fasa mata Kai, akan baisa ta daina rokon ki bah, na dafa kafanki, nace kidau raina a madadin nata, amma kika ki, saboda son zuciyar ki, aka kika samu wuka kika kashe wacce bataji bah, bata gani bah. Ta karashe maganar tareda fashewa da wani kukan.

Jikin kowa na parlour ne ya dau zafi, wani iriyar kasala ya ziyarci kowannen su.
Kalisat tace, koh yanzun mah Baku yarda bah, toh inada wani prove din, zira hannu tayi cikin aljihun rigarta ta dauko waya,

Sannan tayi connecting da TV, tasa play, Mom ce bayyane akan screen din TV , inda Ummi ke bata hakuri, amma samm tsabar rashin imani, ta kashe ta.

Cikin kowa ne ya duri ruwa, a Hatake Mom ta hade rai. Cikin dak'a tsawa Dad yace Karima! Shin wannan kece da gaske.

Mom ta Bashi amsa da fadin kwarai kuwa nice, tabbas nice nan bah kowa bah, kuma ba iya ita kadai bah, sai na hallakar da kowa na wannan family kamar yadda na tsara,

Kabir kamm ji yake kamar mafarki yake, Dad yace Karima why? Dama Allah ya Barnum raina ne domin na ga wannan bakar ranar, Dama cin amanar ahalin nan kike da koh Y'ay'an ciki kin ki, baki Bari bah, why Karima? Why?

Mom ta Bashi amsa da fadin, FANSA, tabbas na shigo wannan ahalin ne badan komai sai dan na dauki fansar abunda aka aikata min na wajan shekara da shekaru,

Kuma tabbas saina dauki fansa akan wannan ahalin, Tana kaiwa nan ta kwashe da dariya, Tana mai fadin, wallahi Baku ga komai bah,

Kai kuma Kabir, tabbas bani ce mahaifiyar ka bah kamar yadda Amriya ta fada tun farko, ni kawai na rike Kane a matsayin d'ana domin idan lokacin salwantar da rayuwar ka yayi wa qungiya ta, saina kashe ka.

hawaye ne suka Fara bin kuncin Kabir yace, Mom please na roke ki kice min karya kike, wasa kawai kike yi. Hade rai Mom tayi tace, kwarai kuwa bah karya na ke fada bah, gaskiya na fada nidin, bah mahaifiyar ka bace,

Jiri ne ya fara diban shi, faduwa Kabir yayi sumamme. Hankali tashe su Dad sukayi kansa, da sauri, Tareda fara jijigashi, babu abunda kakeji a gidan sai kukan su nadira.

Ruwa Khalid ya dauko, sannan ya watsa masa, amma still bai koh Motsa bah, hankalinsu bah karamin Kara tashi yayi bah,

Cikin baccin rai Dad ya shake wuyan Mom yace, Dama da tantiriya, nake rayuwar aure ban sani bah, ban taba zaton aka daga gareki bah, tabbas dole ki girbi abunda kika shuka.

Ture Dad Mom tayi, ya fadi, da sauri su Sadiq suka nufi inda yake, d'aga shi sukayi.
Tareda zaunar dashi. Babu bata lokaci high blood pressure din Dad wato BP, ya tashi,

Hankalin kowa na gidan bah karamin tashi ya karayi bah, fashewa da dariya Mom tayi, tace ina farin cikin ganin wannan ahalin cikin kunci da damuwa, kamar yadda kuka sakani kunci, nima saina ga bayan ku,

Cincibar Dad da Kuma Kabir sukayi, suka nufi hanyar waje dashi, cikin mota suka nufa da su, Khalid ya tada motan, sannan yayi wa su body guard magana dasu bude kofan.

Ganin koh yunkurin bude kofan basuyi ba, yasa ran Sadiq baci, futowa Sadiq yayi daga cikin motan, yace bakuda hankali ne, Baku ga rayukansu na cikin had'ari bane, maza ku bude kofan kafun, ranku ya baci.

Daya daga cikin body guard din yace, ba'a bamu umarnin mu bude muku kofa ba. Aka zalika, wannan gidan mallakin uwar shedanu ne, babu wani ma'aluki da ya isa yayi kokarin futa daga gidan nan, domin wannan gidan makabartar ku ce.

Mutuwar tsaye Sadiq da Khalid sukayi! Ya rasa abun cewa, jiyayi gabadaya duniyar ta isheshi.

Dariya gabadayansu suka kwashe dashi, daya daga cikin su yace kuna mamaki ne, toh mudin bah body guard dinku bane, kamar yadda kuka tsammani, mudin yan qungiyan asiri ne, uwar shedanu kawai muke wa aiki, Baku bah, mun zo gidan nan ne badan komai bah, sai don mu taimaka mata, ta cika burinta, akan ku.

Hada hannayen sa, Sadiq yayi waje guda, yace, Dan Allah badan mu bah, ku taimaka, ku barmu, mu futa, kuna dai ganin rayukansu yana cikin hatsari, kubari mu kaisu, asibity, Dan Allah, ya karashe maganar hawaye na shirin zubo masa.

Dariya suka kuma kwashe dashi a karo na biyu, suka hada baki wajan fadin, kuda futa, saidai gawar ku, baku bah, ran Sadiq da Khalid ne ya baci, lokaci daya, sukayi kan body guard din, domin, su koya musu hankali. Kokawa suka farayi da juna.

Cikin rashin sa'a kuwa ,yan qungiyar asirin suka hadu, suka dunga dukan su Khalid, babu gaggauta wa.

Gasu Dad da kabir rai a hannun Allah, saida suka farfasa wa su Khalid jiki, sa'anan suka wurgar dasu. Basu jisu a ko ina bah, sai jikin bishiyar gidan, yayinda kan sadiq ya fashe, yafara jini, shi Kuma Khalid ya suma.

Cikin tsanani da ciwo, Sadiq yayi yinkurin mikewa, amma akan ya cutura, Hatake jiri suka dibe shi, ya fadi sumamme.


Wallahi Baku ga komai bah, saina azabtar daku, irin azabar da ko da sunan ku baza ku iya tunawa bah.

Fatima dake d'ad'aure, tace Karima, ki dakata aka, kin ruga da kin azabtar da ahalin nan, ya isa aka, Dan Allah, kiyi hakuri, ki yafe Duk abunda akayi miki, koh Allah munayi masa laifi yana yafe mane, bare Kuma mutum Dan Adam.

Mom tace, ni kuma Banida zuciyar yafiya, bana yafe Duk abunda mutum yayi mun, kamar yadda na fada tun farko, dole saina kawo karshen wannan ahalin tukunan zan samu sukuni.

Doct khadija tace, Karima why, shekaru kenen kina gallaza wa wannan ahalin Ba tareda kowa yasani bah, aka kika rabani da ahalina kikamin sharri akan abunda ban aikata bah kika ce nayi, mene kuma ya rage, muguntar ta isa aka, kodan kinga baki samu wacce zata taka miki Burki bah,

Toh ni inada wacce zata taka miki Burki, wallahi, saikin gana wa aya zakinta.

Mom tace toh shikenen, inajiran Duk wacce zaki kirawo, ina jira,

Da sauri su, Aunty amarya da doct khadija, suka

Please Login or Register in order to submit comment