Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sake dan ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa.


Miƙewa ta yi da sauri kamar wanda aka tsikare ta gaban mirror ta je ta tsaya tana ƙarewaa kan ta kallo tamkar dai yau ta fara ganin siffar kan ta a madubi.So take ta gano muninta so take ta hango makusar ta so take ta ga ta inda Hajiya Azima ra kere mata, kyau diri iya kwalliya ko me? Amma bata hango hakan ba duk da ta san cewa bata kama ko da ƙafar komai ba na Hajiya Azimar ba amma ta san ita ma tana da nata abin yabon, gashin kan ta, ta ƙurawa ido ganin shi iya kafaɗarta ko gama sakko mata bai yi ba sai kuma ta tuno gashin Hajiya Azima da ko ɗan kwali baya iya rufeshi har gadon bayanta yake sauka ga santsi da sheƙi, ai hakan da Hajiya Hauwa ta tuna sai kawai ta miƙa hannu wurin kwalaben turaruka da ke jere akan madubin ta ɗakko wata kwalbar humra ta ɗaga ta jefawa madubin a take ya tarwatse wani ƙara da gabaɗaya part ɗin ya ɗauka komawa ta yi ta zube akan gadon har lokacin zuciyarta na tafarfasa.




Safiya da ke gyaran kicin ta jiyo ƙaran fashewar abu a hanzarce ta fara hawa step ɗin domin zuwa ta ga ko menene dan alamu sun nuna kamar ba lafiya ba.Tana gama hawa upstairs ɗin ta fara waige-waige tana son gano inda ƙaran ya fito amma bata gano ba kukan Iftihal ta fara jiyowa da sauri ta nufi ƙofar ɗakin ta tura ƙofar dan dama idan ranar girkin Hajiyar ne idan Hajiyar ta tafi part ɗin Alhaji to fa ita ke kwana da Iftihal amma a ɗakinta da ke kusa da na Iftihal ɗin da basa kwana a ɗaki ɗaya idan kuma ba girkin Hajiyar bane a ɓangaren su na ƴan aiki take kwana.


Iftihal ɗin ta hango zaune akam gado ta duƙunƙune kan ta a cikin bargo tana takure a wuri ɗaya tana ta kuka, da sauri ta ƙarasa wurin Iftihal ɗin tana kiran sunan ta sannan ta sanya hannu ta yaye bargon aikwa Iftihal ɗin ta faɗa jikinta da sauri tana ƙara fashewa da wani kukan.



"Wayyo Safiya dan Allah ki kai ni wurim Aunty tsorata ni ake da wani irin ƙara"Cewar Iftihal ɗin tana ƙanƙame Safiya.



"Ki yi shiru babu komai anan ni ma na ji ƙaran amma da na zo ban ga ta inda ƙaran ya fito ba"



"Ke ma kin ji kenan ni dai ki kai ni wajen Aunty tsoro nake ji"


"To taso mu je tana ɗakinta"


Sakkowa Iftihal ɗin ta yi sai da na duba da kyau sai ma na ga ba wata babba ba ce duka bata fi shekara huɗu ba, hannun ta Safiyar ta kama amma Iftihal ta ce ita dai ba za ta tafi da ƙafarta ba, sunkuyawa Safiyar ta yi Iftihal ɗin ta hau dan dama da wuya ka ga Iftihal na tafiya da ƙafarta rai da rai sai dai a baya, haka suka nufi ɗakin Aunty, nocking Safiya ta shiga musu amma abin mamaki bata bada amsa ba jin shiru yasa Safiya tura ƙofar dan dama haka take sai ka yi ta mata nocking ta ƙyaleka.

Kwance suka sameta ta kifa kan ta a jikin filo da alama kamar tana cikin damuwa daga bakin ƙofar da Safiya ke tsaye da goyon Iftihal suka ga gabaɗaya madubin da ya tarwatse a ɗakin, da mamaki Safiya da Iftihal suke kallon madubin sai lokacin suka fahimci ƙaran fashewar madubin ne ya cika part ɗin har ya tsorata Iftihal.


"Aunty"Iftihal ɗin ta kira sunan Hajiya Habiba tana ƙoƙarin sakkowa daga bayan Safiya.

Shiru bata amsa mata ba

"Kar ki sakko dan kar ki taka madubin"Safiya ta ce tana riƙe Iftihal ɗin dan yadda madubin ya ɓata ɗakin ko ina ya tarwatse Iftihal ɗin za ta iya takawa.Duk bidirin nan da ake Hajiya Habiba bata ko ɗago kai ta kalle su ba.A hankali Safiya ta bi ta gefen tana taka in da babu madubin har dai ta ƙarasa bakin gadon ta sauke Iftihal ɗin akan gadon, ƙarasa wa Iftihal ɗin ta yi ta faɗa kan Aunty ta tungumeta ta baya tare da kwantar da kan ta a bayan Auntyn.Ita dai Safiya daga haka ta fita ɗakin domin samo abin da za ta gyara wurin.


"Aunty ke kika fasa madubi?"Iftihal ta jefa mata tambayar.


A hankali Aunty ta zame Iftihal ɗin faga bayanta ta tashi zaune suka fuskanci juna.Iftihal ɗin kallon idon Auntyn take ganin ya yi jawur kamar dai kuka ta yi.


"Haba Iftihal ya za ayi in fasa madubi abu na je ɗakkowa shi ne ya fashe"



"Amma kuka kika yi?"Ta ƙara jefa mata wata tambayar.

"Kai na ke ciwo shi sa kika ga ya yi ja"


"Sannu kisha magani"

"Yawwa na sha magani ma"

Iftihal kan ta ta kwantar akan cinyar Auntyn, sai kuma Auntyn ke shafa kan nata , shiru suka yi babu wanda ya ƙara magana.


"Aunty yau ma bazan je school ɗin ba?" Iftihal ta jefo mata tambayar.Auntyn na ƙoƙarin bata amsa Safiya ta turo ƙofa ta shigo ɗauke da tsintsiya da abin kwashe shara wurin ta shiga gyarawa sai da ta tabbatar ya gyaru babu sauran wani madubin sannan ta fita daga ɗakin.



"Yanzu time na zuwa school ya wuce, ba a son mutum ya je makaranta a makare saboda bulala malam ke yi amma ki bari za ki je"Cewar Auntyn tana cigaba da shafa kan Iftihal ɗin.


"To shikenan, amma dai gobe zan je"



Shiru Auntyn ta mata har sai da Iftihal ɗin ta sake mata magana sannan ta ce.





"Kar ki damu"




"Zan je?" Ta sake jefa mata tambaya.


"Ki bari yanzu bana son surutu kai na yana ɗan sara min"


"Sannu " Iftihal ta ce tana tashi zaune daga kwancen da take tana kallon Aunty cike da tausayawa.



"Yawwa ai kaɗan-kaɗan ne ma " Aunty ta ce tana ɗaukan wayar ta ta kira telephone da ke falon ƙasa, Safiya na ɗagawa ta ce.


"Ki zo"Kawai ta ce ta katse kiran.


Da sallama ta shigo ɗakin bayan ta yi nocking an bata izinin shiga.


"Gani Hajiya" Safiya ta ce lokacin da ta durƙusa a gaban gadon da Aunty take.



"Ki ɗauketa ki je ki mata brush ki mata wanka sannan ki bata abinci ta ci" Auntyn ta faɗa tana miƙa mata Iftihal .



"To Hajiya an gama" Cewar Safiya tana juyo bayanta Iftihal ɗin ta hau suka fito daga ɗakin.

Bayan ta mata brush ta mata wanka sannan ta shiryata tsaf cikin riga da wando ƴan kanti pink clour masu matuƙar kyau ta gyara mata kan nata sai sheƙi yake, haka ta goyota suka sakko ƙasa ta zaunar da ita da akan kujera, kicin ta shiga ta ɗakko mata soyayyen dankali da ƙwai sai soyayyen plantain.A kan center table ta ɗora ta ɗakko kayan shayi ta haɗa mata tea mai kauri ta zuba abincin ta shiga bata a baki, suna cikin haka sai ga Aunty ta sakko daga saman ta zo ta zauna ta ɗora ɗaya kan ɗaya dan zuwa lokacin ba ta ko so ta tuno da Hajiya Azima dan tun da ta yi kuka sai ta ji zuciyarta ta yi sanyi remote ta ɗauka ta canja tasha zuwa arewa 24 sannan suka sakarwa juna murmushi ita da Iftihal.




Ita dai Safiya ba abin da ta ce tana baiwa Iftihal abinci har sai da ta juyar da kai gefe alamar abincin ya isheta.Ajiye fork ɗin Safiya ta yi ta ɗakko kofin me tea ɗin da ta haɗawa Iftihal a hankali ta shiga ƙoƙarin bata dan gudun yin kuskure dan kaɗan da aikin Hajiyar ta mareta koma ta hanata albashi wannan watan.


"kar ki bani tea ɗin da kai na zan sha" Cewar Iftihal tana miƙa hannu ta karba, Safiya ganin an karɓeta sai ta shiga tattare kayan abincin, ta gama haɗawa za ta ɗago daga sunkuyen da take aikwa Iftihal ta ɗauki wannan shayin da ke hannunta ta watsawa Safiya a jikinta har fuskarta sannan ta ce




"Bana shan abu mai zafi bayan haka bana son ana cika min madara "




Wani haushi da mugun takaici ne ya mamaye Safiya ga tea ɗin da zafi bai huce amma sai ta cije sai dai ta yi ƙoƙarin damƙe hannun ta domin ta ayyana a ranta ko za ta rasa aikinta yau sai ta naushi Iftihal a bakinta domin sai ta nuna mata cewa bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane, sannan ɗan adam Allah ya ɗauka ka shi dole ma ta nuna musu kuɗinsu ba shi bane tun da ba za su iya yiwa kan su abu ba dole dai talakan shi zai musu, hannu ta dunƙule tana duba in da ya kamata ta kaiwa mugun naushi a jikin Iftihal ɗin.





MMN AFRAH😍🥰😘



❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page9️⃣ &🔟




Wata tsawa da Hajiya Hauwa ta dokawa Safiya ita ta dakatar da ita daga shirin dukan da take ƙoƙarin ta kaiwa Iftihal, wani tsoro ne ya ziyarci Safiya dan sai a lokacin ta ji a ranta cewa lallai da ta kaiwa Iftihal dukan to tabbas da ta yi babban kuskure, dan wataƙila kafin ta rasa aikin nata sai ta fara rasa ranta dan tsaf Hajiya Hauwa za ta mata dukan mutuwa akan Iftihal.


"Wace irin marar hankali ce ke in ban da jakanci da jahilci maimakon ki yi saurin tafiya ɗaukan mopa da ruwa ki zo ki goge wurin shi ne kika tsaya kina kallon Iftihal ɗin sai ka ce wanda ta yi wani abu, ko dan baku san darajar kuɗi ba saboda baku da su shi yasa za ki bar min capet da ruwan shayi a jiki sai ya dafe yaƙi fita" Aunty ta ce tana wani zazzare ido tana bala,i.


"Ki yi haƙuri Hajiya yanzu zan gyara" Safiya ta ce tana ɗaukan kanukan ta nufi kicin domin ta ajiye su, ga wani zafi da raɗaɗi da fuskarta da ƙirjinta ke yi dan shayin akwai zafi amma saboda rashin imani na Hajiya Hauwa maimakon ta tausaya mata shi ne take mata faɗa bayan Iftihal ya kamata ta yiwa faɗan amma saboda sangarci da kuma ganin suna da kuɗi za su iya taka kowa ma hakan ya sa ta zamar da ƴarta ta sangartacciya.Sai da Safiya ta tsaya ta share ƙwallar da ta zubo mata tana da na sani akan aiki a ƙarƙashin Hajiya Hauwa da bata da mutunci ko kaɗan bare tausayi, bata koyi da sobar zamanta Hajiya Azima mata mai kima da darajanta ɗan adam pan aikinta tamkar ƴaƴanta haka ta ɗaukesu ba kyara ba tsangwama.


Tana ta saƙar zuci ta dawo falon ɗauke da mopa da burket da ta haɗo ruwa mai ɗauke da morning fresh, ta shiga goge wurin, lokacin Auntyn na lallashin Iftihal akan ta yi haƙuri za a haɗa mata wani tea ɗin marar zafi sosai marar madara da yawa.Wani haushi da takaici ne ya turnuƙe Safiya tana Allah wadaran naka ya lalace ace maimakon uwa ta zama turba na gina rayuwar ƴaƴanta akan hanya daidaitacciya mai ɓullewa wajen basu kyakkywar tarbiya amma shi ne ita Aunty ta zama mai bada gudunmuwa wajen taɓarɓarewar tarbiyar ƴarta, babu abin da yarinyar ta sanj sai sangarta.



"Dalla malama ki yi sauri ki gama ki haɗa mata wani tea ɗin"Cewar Auntyn cikin zafin rai.



"To Hajiya" Safiya ta amsa mata, bayan ta ɗakko freshner ta fesa a wurin saboda ƙarnin madarar sannan ta ɗauke kayan da ta yi amfani da su wajen gyara wurin, kicin ta koma ta ɗauki gishiri ta shafa a wurin da aka watsa mata shayin dan da alama ma kamar wurin zai tashi, bayan ta shafa sai kuma ta wanke hannunta ta sake haɗa shayin marar zafi sai dai yana da ɗan ɗumi sannan ta fito ta zo ta durƙusa ta miƙawa Iftihal ɗin, tun da ta ce da kan ta za ta sha.



Ƙin karɓar shayin ma ta yi tana kallon tv, kamar ma ba ita ake baiwa shayin ba, Auntyn kwa tana kallo ko ta yiwa Iftihal ɗin magana.



"Ga shayin na sake haɗa miki"Safiya ta ce da ta fahimci bata da niyyyar karɓa.

Banza ta yi da ita, can kuma a shelaƙe ta karɓa, kurɓa ɗaya ta yiwa shayin ta ɗaga ta watsar da shi, ta yi jifa da kofin ya tarwatse dan dai ma akan tiles ne ba akan capet ba.Safiya kai ta sunkuyar tana jin a ranta cewa lallai neman halal da wuya musamman a ƙarƙashin wanda ba su san kima da darajar ɗan adam ba.Hatta Hajiya Hauwa ranta ya matuƙar ɓaci da abin da Iftihal ɗin ta yi amma saboda bata so ta nuna mata hakan duk da cewa ita ce ta ɓata yarinuar gashi bata son kwaɓarta sai kawai ta danne zuciyarta ta ce.



"Wai Safiya baki san aikin ba? Komai sai an faɗa miki kenan? Ba za ki kula ki gyara wurin ba sai ki wani sunkuyar da ka kamar mai yin zaman tahiya yayin gabatar da salla.



"Ki yi haƙuri Hajiya yanzu zan gyara" Haka Safiya ta share wurin wurin ta goge tas, sannan ta ɗore wasu ayyukan dan wuni ake ana aiki ba kama hannun yaro.


Da daddare zaune suke su duka iyalin gidan a dinning area domin gabatar da dinner, Hajiya Azima sanye take da wani leshi purple colour an mata ɗinkin buba ta ɗaura ɗankwalinta ta sanya sarƙa da ɗankunne na gwal sai sheƙi suke ga warwaraye da zobuna sai zuba ƙamshi take tamkar dai mai shirin zuwa wani gagarumin biki ko suna. Hajiya Azima mace ce mai son ado da kwalliya gata da matuƙar tsafta, hakan shi ke ƙara wutar soyayyarta a wurin mijinta yake kuma ƙara rura wutar tsanarta a wurin sobar zamanta Hajiya Hauwa dan ta tsani duk wasu abubuwan da Hajiya Azima ke yi.


Alhaji, Hajiya Azima sai Hajiya Hauwa su ne a wurin kowa zaune yake Iftihal kawai ake jira a fara cin abincin domin komai ya kammala dan kuku ya shirya musu komai da komai duk da kasancewar Hajiya Azima mai son take yin girki da kan ta amma fitinar da Hajiya Hauwa ke tadawa yasa Alhajin dakatar da ita, dan dama ita duk ranar girkinta ita ce ke yin girki, ita kuma Hajiya Hauwa sai dai aci girkin kuku dan dama bata wani ƙware a girki ba gata kuma da son jiki, to idan Hajiya Azima ta yi girki ranar girkinta sai Hajiya Hauwa ta ringa sanabe tana cewa gishiri ya yi yawa ko dai an cika yaji ita ulcer ta za ta tashi kuma duk gassada ce dan ta ga Alhajin yana ta yabon abincin idan ana ci.Irin fitintinun da take yasa ya dakatar da Hajiya Azima da yun girki akan a bar kuku yana yi domin shi ma kukun nasu gwani ne a wurin iya girki babu abin da bai iya ba.



"Ke dai bakya gajiya da caɓa ado kamar mai shirin zuwa gidan biki"Alhajin yace yana yiwa Hajiya Azima wani kallo ƙasa-ƙasa.



Murmushi ta yi kafin ta ce



"Ai indai abu ne zan yi dominka bana taɓa gajiyawa da shi, bare kwalliya ai ni kai ne gidan bikin nawa, matuƙar na yi abin da ya birgeka to tabbas kwalliya ta biya kuɗin sabulu"



"Ai ba ma kuɗin sabulu ba harda kuɗin soso" Yace suna dariya su biyun ban da Hajiya Hauwa da ta cika ta yi fam sai bin jikinta take da kallo sanye take da baƙar doguwar riga sai ɗankwalin rigar da ta ɗaura shi ya yi baya,ko ɗankunne babu a kunnenta, ita dama ta gaji da yin wata kwalliya duk shigar da za ta yi ko wacce irin sutura za ta sanya sai ta ga bata yi mata kyau kamar yadda kayan ke yiwa Hajiya Azima.


Ji ta yi kamar ta tashi ta bar wurin saboda tsabar takaici kamar sun manta cewa tana zaune a wurin.Wata hararar ƙasan ido take bin su da ita su duka biyun.



"Assalamun alaikum" Safiya da ke goye da Iftihal ta yi sallama.



Hajiya Azima ce ta amsa mata sallama, ƙarasa shigowa ta yi sai da ta zo har wurin nasu sannan ta sauke Iftihal ɗin ta ja kujera ta zaunar da ita sannan ta juya ta fita dan idan Alhaji yana nan ba ya bari a baiwa Iftihal abinci a baki cewa yake a barta ta ci da kan ta.




"Iftihal ɗina barkan ki da dare" Alhaji ya ce yana kallonta da murmushi.



"Abie ina yini" Ta faɗa tana rufe fuska dan ta san ya fala mata cewa yaro ne yake fara gaishe da babba amma ita mantawa take in ma ba Abie ya faɗa mata ba idan sun haɗu, mantawa ma take akwai wani abu gaisuwa saboda Hajiya Hauwa bata koya mata gaishe da mutane.



"Lafiya ƙalaw my daughter bakya gaishe da mutane sai sun roƙa ko?"


Shiru ta yi tana rufe fuska da hannayenta.


"To ni kaɗai za a gaishe dani ?"Abie ya jefa mata tambayar dan shi mutum ne shi mai son ya ga yaronsa ya tashi cikin tarbiya.


"Momma ina yini" Iftihal ta gaishe da Hajiya Azima dan dama Momma take kiranta.


"Lafiya law iftihal" Cewar Hajiya Azima tana sakar mata murmushi.


"Aunty ina yini" Ta juya tana gaishe da Hajiya Hauwa.


"Lafiya" Hajiya Hauwa ta amsa a taƙaice, a wani daƙile kamar an mata dole.

Daga haka Hajiya Azima ta shiga zubawa kowa abincin amma Hajiya Hauwa da kan ta, ta zuba nata, aka shiga ci Iftihal na ci da kan ta ashe dama rainin wayo ne ace komai sai an bata a baki dan tsabar sangarta.


A haka suka kammala cin abincin, Hajiya Hauwa ta riga kowa tashi ta bar part ɗin ma baki ɗaya, su kuma suka koma cikin falon suna hira abin su cikin farinciki Abie na tambayar Iftihal batun zuwa islamiya ta ce bata je ba anan take faɗa masa yadda suka yi da Aunty da safe da ra mata zancen zuwa school.Ran shi ta ɓaci sosai da ya ji bata je islamiya ba hakan yasa ya ɗauki alƙawarin gobe da wuri zai fito domin Iftihal ɗin ta tafi makaranta dan ya fahimci cewa Hajiya Hauwa da gaske ba ta son barin yarinyar ta raɓi ilimi kowane iri sai nuna mata soyayyar banza da shagwaɓata na wofi wanda hakan bashi da wani amfani.


❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page 11&12



_Washe gari_

Tun wajen ƙarfe shida da rabi Abie ya sakko ƙasa, ko Hajiya Azima bata sani ba dan bayan ya dawo daga masallacin asuba da suka ɗan taɓa karatun qur'ani sai suka koma suka kwanta shi ne bacci ya ɗauketa.Part ɗin Hajiya Hauwa ya nufa, nocking ƙofar ya shiga yi amma shiru ba a buɗe ba dan babu alamar motsin mutum ma bare ya sa ran za a buɗe, wayarsa ya koma ya ɗakko sannan ya dawo ya shiga kiran Hajiya Hauwa, sai da ya kira sau uku amma ba a ɗauka ba.

Hakan ya sa ya koma ya shiga ta ƙofar baya wacce ake bi ta cikin kicin sa'arsa ɗaya ƙofar ba a kulle take ba amma a rufe take.Yana shigowa ya kunna fitilun sannan ya haura sama, ɗakin Iftihal ya fara zuwa ya buɗe ya kunna ƙwan ɗakin kwance take tana ta bacci abinta, tashinta ya yi sai kuma ya kira telephone na ɓangaren ƴan aiki, yace a turo masa Safiya ta zo sashen Hajiya Hauwa yanzu.Ba a ɗauki wani lokaci ba sai gata ta zo ya umarce ta data yiwa Iftihal ɗin shirin makaranta.


Yana fitowa ya nufi ɗakin Hajiya Hauwa a buɗe ya samu ƙofar bata sanya makulli ba, yana buɗe ƙofar ya kunna futilar ɗakin, sai bacci take gabaɗaya ta cika ɗakin da munshari filon da ta yi matashin kai dashi ya shiga bugawa amma ko gizau ba ta yi ba.Kallo yake ƙare mata da alama ma ko sallah ba ta tashi ta yi ba dan dama Hajiya Hauwa ibadar nan da sauƙi dan mace ce wacce bata damu da ibadah ba.


"Hajiya, Hajiya, Hajiya"Sai da ya kira ta sau uku tana ɗan bubbuga kafaɗarta sannan ta yi wata miƙa tana, tare da saurin sanya hannu ta make masa hannu dan bata ma san wa ke tashin ta ba.


"Wai ba da ke nake ba, kamar wacce ta suma ko kuma mai baccin mutuwa sai wani magagin bacci kike kamar wata yarinya" Cewar Abie a fusace dan gabaɗaya ransa a ɓace yake.

"Alhaji kai ne" Ta ce tana mai tashi zaune tare da sakin wata hamma ko bakin bata rufe ba.


"Ni ne mana kin zo kin kwanta kina ta faman bacci, babu sallah ba salati, sannan baki ji na ce yau Iftihal za ta je makaranta ba, amma maimakon ki tashi da wuri ki sanya a shiryata shi ne kika kwanta kina baccin asara sai ta makara ki ce ba za ta je makaranta ba"


"Wai yanzu Alhaji akan shirin zuwan Iftihal makaranta kake waɗan nan maganganun?"


"Ba dole na faɗa ba kina so ki koyawa yarinya ƙin makaranta tun tana ƙatamarta"

Baki ta taɓe ta fara jan jiki ta sakko daga kan gadon ta nufi hanyar bayi tare da cewa


"Koma dai makarantar neman lahira ce a barni in shiga bayi in fito in fara gaishe da ubangiji" Ta ce tana shigewa bayin ta banko ƙofar saboda ta tsani maganar zuwan Iftihal makaranta amma ta ga alama Alhaji ya kasa fahimta, dan gaka ma ta ƙudurta a ranta cewa sai ta ɗauki lokaci mai tsawo za ta fito daga bayi sannan ta san likaci ya ƙure dan bata da masaniyar Abie ya tashi Iftihal ɗin har ma ya sanya Safiya ta shiryata.


Kai Abie ya girgiza ya juya ya fito daga ɗakin nata sai da ya bi ta ɗakin Iftihal ɗin ya ga har an mata wankan ana sanya mata uniform sai murna take yau za ta je makaranta.


"Abie har an kusa gama shirya ni sai in yi sallah, ba sai na ci abinci ba ma dan kar lokaci ya ƙure"Cewar Iftihal dan bata son yau wani abu ya hanata zuwa makaranta.


"Kar ki damu Iftihal har kya ci abincin ma dan da sauran lokaci yanzu 6:50"


"Toh Abie" Ta ce lokacin da Safiya ta gama sanya mata ƙaramin hijab domin ta yi sallah.Tana yin kabbara sai Abie ya cewa Safiya idan ta gama sallah ta kawo ta part ɗin sa domin ta yi break fast acan saboda ba ya so Hajiya Hauwa ta sanya su makara.Amsa masa ta yi ya juya ya sauka ya nufi part ɗinsa, lokacin kuku har ya fara jera wasu abubuwan na break fast akan dinnig ɗin.

Sama ya haura domin zuwa shi ma ya shirya sabida tafiya office.


Safiya ce goye da Iftihal sai ta rataya school back ɗin Iftihal ɗin a kafaɗarta suka taho part ɗin Daddy, abin da take so ta zuba mata ta fara bata a baki.



Hajiya Hauwa ta daɗe a bayi sannan ta fito ta yi sallah ko azkar bata yi ba ta tashi ta naɗe dardumar sannan ta koma ta kwanta, sai da ta ga ƙarfe bakwai da arba'in sannan ta taso domin zuwa ta tashi Iftihal ta san dai yanzu kafin ta kira Safiya ra shirya yarinyar har ta ci abinci lokaci zai ƙure sai dai a haƙura da zuwa makarantar.


Tana zuwa ta tura ƙofar ta ga wayam babu kowa a ɗakin, kofar bayi ta buɗe shi ma ta ga Iftihal ɗin bata nan dan haka da mamaki fal a fuskarta ta fito daga ɗakin tana tunanimninda yarinyar take da sanyin safiyar nan.Ƙasan ta sauka nan ma bata nan, wayar ɓangaren ƴan aiki ta kira ta ce a turo mata Safiya domin ta je ta dubo

Please Login or Register in order to submit comment