Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta a cikin gidan amma sai aka sanar da ita Safiyar ta fito domin amsa kiran Alhaji.A fusa ce ta kama hanyar part ɗin Alhajin tana fatan kar hasashen ta ya zama gaskiya tana zuwa kwa ta ga Iftihal riƙe da lunch box ɗin ta har direbanta ya zo za su tafi, Alhaji da Hajiya Azima kuma zaune a dinning area ɗin.


Wani ƙaton abu ne ya tokare mata maƙoshi har yaushe ne Alhaji zai fahimci cewa bata ƙaunar Iftihal take halartar makaranta tana da ƙuduri mai girma akan yarinyar amma bata ƙaunat yarinyar ta yi wano abi wai shi karatu.Tana ji tana gani hwkw Iftihal ta fice ita da Safiya za ta rakata wurin mota, Iftihal ɗin sai ɗagawa Hajiya Hauwa hannu take amma ko ta kulata har sai da kowa ya fahimci hakan, shi kwa Alhaji ko ta kan Hajiya Hauwa bai bi ba ita ma Hajiya Azima banza ta yi da ita dan ta ga abin nata ya zama hauka, ace ƴar ƙwaya ɗaya amma ana hana ta zuwa makaranta ita ko kunya ma Hajiya Hauwar bata ji.


Ganin kowa ya shareta yasa ta koma part ɗin ta ranta na suya tana yin wani ƙudirin akan lallai sai ta ƴara tashi tsaye dan ta ga abin na Alhaji ba ƙarami bane ita kwa ta sanya a ranta cewa sai dai su yi ta fafatawa.


_ALHAJI HAMZA_

Ɗan asalin garin kano ne a unguwar zoo road, iyayensa shi kaɗai suka haifa,suna kiransa da Hamzan sa, ya tashi a garin kano tare da mahaifansa anan ya yi karatunsa tun daga primary har zuwa zuwa digree ɗin sa.Iyayensa basu da wani arziƙi sai dai suna da rufin asiri, bayan ya kammala karatunsa bai samu aiki ba sai ya fara ɗan sana'a har dai daga bisani Allah ya sa ya samu aiki a wani kamfani garin Abuja, hakan yasa ya fara zuwa wajen aiki yana dawo wa a week end, tafiya ta yi tafiya har ya samu ya samu ɗan gida madaidaici ya siya ciki da falo sai banɗaki haka ya dawo da mahaifansa kusa dashi suke zaune tare.



Daga baya yana ƙara samun buɗi sosai domin Hamza ya kasance mutum mai gaskiya da riƙon amana hakan ya taimaka masa da wurin aikinsa suka riƙeshi da kyau sanadin gaskiyarsa, Har ake ƙara masa girma.Bayan ya sayi gida mai ɓangare biyu sai mahaifansa suka ce ya yi aure haka kuwa aka yi ya auri budurwarsa Azima ƴar garin Kano ce sun daɗe suna soyayya, da suka tare a sabon gidan su a ɓangare ɗaya iyayen Hamza ma a ɓangare ɗaya haka suke zaune lafiya dama Azima uarinya ce mai biyayya da kuma girmama na gaba hakan yasa zaman nasu yin ƙarƙo.


Wata rana da ta zame musu rana mafi muni a cikin tarihi shine hatsarin da iyayen Hamza suka yi daga Kano zuwa Abuja domin sun je sada zumunci wurin ƴan uwa da abokan arziƙi hakan ne ya yi sanadiyyar rasa rayukasu.Haka aka yi zaman makoki aka tashi sai dai mu ce Allah sa mu yi kyakkyawan ƙarshe amin.



Shekaru kusan bakwai kenan su Hamza Allah bai basu haihuwa ba, gashi a lokacin har ya je ƙasar India ya ƙaro karatu, ga buɗi na arziƙi ta ko ina amma kuma babu wani labari na haihuwa hakan yasa Azima ta ɗaga hankalinta amma shi Hamzan ke kwantar mata da hankali akan komai lokaci ne.Ya sake musu gida na gani na faɗa domin yanzu shi ma ya mallaki kamfano ni da dama sai dai ma wasu su ci abinci a ƙarƙashinsa.Yanzu ma yana aiki a ɗaya daga cikin kamfanonin sa kuma mutanen da ke tate da shi suna jin daɗin aiki da shi domin mutumin da ya san kima da darajar ɗan adam



Watarana ya je Kano ziyara ya dawo sai motarsa ta lalace a Suleja, hakan yasa ya rasa yadda zai yi, wani gida da yake kan hanyar inda motarsa ta lalace mai gidan ya bashi tarbarma sannan ya bashi abinci har dai bakaniken da ya masa gyara ya kammala, sosai Hamza ya ji daɗin karramawar da mutumin ya masa hakan yasa alaƙa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu duk da cewa mutumin ya haifi Hamzan amma haka suka ƙulla alaƙa mai kyau, har ta kai Hauwa ta ƙyalla ido ta ganshi hakan yasa ta ɗauki alwashin sai ta aureshi duk da kasancewar mahaifinta talaka amma dai bata da buri da ya wuce auren mai kuɗi, shi yasa da ta ga Hamza ce sai ta aureshi ko ta halin ƙaƙa, haka suka shiga suka fita ita da mahaifiyarta, sai da Hamza ya auri Hauwa.


Tun da ta tare a gidansa ta ga yadda yake ji da uwar gidansa hakan ya ƙara rura wutar kishi a ranta, ta ji duk duniya babu wacce ta tsana irin Azima haka ta sa a ranta ita ce za ta haifawa Hamza magaji dan ta zama tauraruwa kuma ta cusawa Azima haushi na rashin haihuwa.

Makkah kwa sai da ta je sannan hankalinta ya kwanta,dan ta tsani ta ji ana kiran Azima da Hajiya.

Zuwanta da wata biyar sai ciki ya ɓullo a jikin Hajiya Azima, hankalinta ya yi matuƙar tashi haka suka dinga shigi da fice akan kar ta haihu amma cikin hikimar ubangiji lokacin haihuwa na yi ta haifi ɗanta namiji a asibiti sai dai kwanan yaton ɗaya a duniya ya amsa kiran ubagiji.Murna a wajen Hajiya Hauwa ba a cewa komai sosai ta yi farinciki.Hajiya Azima kwa ta ji babu dali ganin yadda suka ƙwalla fa rai akan cikin har ma da ɗan lokacin da ya zo duniya ita da Alhaji Hamza da duk wani masoyinta, amma haka suka fawwalawa Allah komai.


Sai da Hajiya Azima ta shekara shida da haihuwar ɗan da ya koma, sai kuma ciki ya bayyana a jikin Hajiya Hauwa, sai wani iyayi da sanabe take wai ita mai ciki za ta haifi magajin Alhaji ya gaji dukiya, shi ne fa da cikin ya isa haihuwa ta haifi Amina ana kiranta Iftihal.Hajiya Hauwa tun da ta haifi Iftihal take zaton Alhaji zai juyawa Hajiya Azima baya saboda bata haihu ba sai ta ga saɓanin hakan dan babu wani abu da ya canja hakan shi ne ke baƙanta mata tana ganin kenan dai duk da ta haihu bata samu martaba da kimar da Hajiya Azima ta samu ba a wurin Alhajin.

sai kuma ta fara zargin ko Alhaji ya fi ƙaunar a haifa masa namiji, shi yasa take ganij bata samu wani matsayi da take son ta samu a wurinsa ba.Amma kuma daga baya dai ta fahimci Alhajin bashi da wani zaɓi sai abin da Allah ya bashi ko mace ko namiji duk yana so hakan yasa take fatan Allah ya ƙara bata haihuwa ta haifi namiji duk da tana jin tun da Hajiya Azima bata haihu ba babu yafda za ayi ta haɗa kan ta da ita duka da cewa mace ta haifa.

wannan kenan.



❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page 1️⃣3️⃣&1️⃣4️⃣



_Hizbullah_

Bayan shekaru biyar


Shaƙuwarsa da Ridallah kullum ƙaruwa take, hakan yasa gabaɗaya bashi da wani wanda ya shaƙu da shi sai Ridallah, bayan iyayensa Umma Sadiya, da kuma mahaifinsa Malam Auwalu,babu wani wanda ya shaƙu dashi sai Ridallah Ita ma Ridallah haka ne a nata ɓangaren in ban da mahaifiyarta Baba Habiba dan mahaifinta ya rasu sai mahaifiyarta kaɗai ce a raye.


A haka suka taso ko yaushe suna tare babu abin da ke raba su sai bacci, tare suke zuwa makarantar boko tare suke zuwa islamiya, tare suke cin abinci tare suke komai idan ɗaya bashi da lafiya to ɗayan ma haka zai wuni a kwance wani lokacin ma shi ma ɗayan kamuwa yake da jinyar da ɗayan ke yi wannan shi ne babban abin da ya ƙara sanya iyayensu ƙarfafa zumuncin maƙotaka a tsakaninsu dan un ban da maƙotaka babu wani abu da ke tsakanin su na ƴan uwantaka.


Rayuwa na ta tafiya, da kaɗan -kaɗan ranaku ke rikiɗewa su koma sati, sati ya rikiɗe ya koma wata da sannu su ma watannin ke haɗuwa su bada shekara hakan ya kan sa shekarar ta haɗu da wata shekarar har su bada shekaru.

Hakan ne yasa wucewar shekarun ya kawo mu lokacin da Hizbullah ya kammala karatunsa na secondry school, a lokacin Ridallah tana primary 5 dan dama lokacin da take primary 1shi kuma yana J.s.s 1. Yana zaman jiran fitowar jarabarwar su ta SSCE sai kuma wani mummunan abu ya faru, wanda ya yi sanadin wargaza gabaɗaya farincikin sa da ma sanya mahaifansa cikin damuwa saboda halin da ya tsinci kan sa a ciki. A wata ranar asabar ce aka tashi aka nemi Ridallah da mahaifiyarta Baba Habiba aka rasa babu wanda ya san inda suka tafi, dan ko kaya ma ba su ɗauka ba haka suka tafi gidan ma ko rufewa ba a yi ba.

Sosai Hizbullah ya shiga damuwa da ƙunci na tashin hankali, dan yanzu ya daɗe da gano cewa ba wai shaƙuwace kawai tsakaninsa da Ridallah ba tabbas akwai wata ɓoyayyar soyayya a cikin zuciya, Umma Sadiya sun rasa yadda za su yu dashi sun yi lallashin sun yi faɗan sun yu lallamin amma dai Hizbullah ya yi nisa sosai baya jin kira.Da yake lokacin da Baba Habibabta dawo gidan da ke kusa da na su Hizbullah, lokacin Hizbullah yana ƙarami bai sani ba amma dai da wasu ƴan rani ne a gidan mata da miji da yaransu to da suka koma garinsu sai Baba Habiba ta kama gidan dan dama gidan haya ne me gidan yake bayarwa haya.


Dan haka Umma Sadiya ta shiga masa bayanin duk yadda abun ya faru tun daga lokacin da Baba Habiba ta dawo gidan da zama lokacin Ridallah tana ƴar jinjira, sosai sabuwar haihuwa ce, to lokacin ne da Hizbullah ya ƙyalla ido ya ga Ridallah sai yake zuwa gidan wurinta.Ganin halin da ya shiga har ta kai ga kwantawa jinya dan duk inda suke zaton za su gan su sun cigita amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa.Hakan ne yasa Malam Auwalu ya nemi mai gidan da Baba Habibar ke zaune domin jin ko daga ina Baba Habibar take tun da shi ya bata hayar gidan, amma abin mamaki mutumin yace wallahi bai san daga inda take ba, shi dai kawai abu ɗaya ya sani maƙocinsa ne ya haɗa shi da ita, shi ma kuma maƙocin ba wai ya san ta bane kawai dai ta je wurinsa ne akan tana neman taimakon inda za ta zauna ko da gidan haya ne tana so wai mijinta ne ya rasu ya barta da tsohon ciki shine kuma bayan ta haihu ƴan uwan mijin suka koreta akan wai ba za su bata gado ba, hakan yasa ta baro garinsu ta dawo nan.Shi ma tausayinta yasa ya haɗani da ita na bata gidan ta zauna amma ko kuɗin hayar baya karɓa.



Wannan jawabi da Malam Auwalu ya zo da shi, shi ya ƙara saka Hizbullah a cikin matsananciyar damuwa, dan dama yana tunanin a wurin mi gidan za a samu ɗan labarin garin da suka fito dan abi sawu to kuma sai aka samu akasin hakan.Da farko ma an yi tunanin ko kidnapers ne suka ɗauke su amma daga bisani an fahimci ba haka bane.Duk wanda ya ga Hizbullah sai ya matuƙar tausaya masa saboda rabuwa da abin da ka shaƙu ba ƙaramin abu bane, akwai damuwa sosai duk ya ƙare ya yi baƙi baya iya cin abinci kullum yana keɓance a ɗaki dama ba wani abokai gareshi ba Ridallah ita ce aboki ƙawa sannan ita ce komai nasa.Yanzu kwa da bata nan sai ya zama abin tausayi.Kullum yana ɗaki a rufe yana kuka rashinta ji yake zuciya da jijiyoyinsa ba za su taɓa iya jure rashinta ba, idan son ganinta ya ciyoshi haja zai fita ya yi ta yawo wuri-wuri yana nemansu gani yake kawai zai iya ganinsu idan ya gaji da yawo sai ya ya je bakin ruwa ya zauna masu kamun kifi suna ganin kamar zuwa ya yi domin yake kallon yadda ake kama kifi amma shi bai ma san me suke ba gangar jikinsa ce a tare da su amma zuciyarsa ta lula duniyar tunani da jimamin halin da ya tsinci kan sa a ciki na rashin abar ƙaunarsa ƙanwarsa wacce ya shaƙu da ita Ridallah.


A wannan hali da yake ciki ne jarabawarsu ta fito ya yi ƙoƙari sosai, domin ya cinye jarabawar gabaɗaya, amma shi ko murnar hakan ba ya yi sai dai iyayensa ne ke ta murna da farincikin hakan.Ganin hakan da Malam Auwalu ya yi, ya samu abokinsa Malam Iro da maganar halin da Hizbullah ɗin ke ciki, dan yana jin tsoro kar damuwar da yake ciki ta shafi karatunsa.Malam Iro ya baiwa Malam Auwalu shawara akan ya sanya Hizbullah ya cike scholarship ko Allah zai sa ya samu idan ya samu ya fita wata ƙasar karatu zai fi maida hankali ga karatun nasa idan ya ga ya yi nisa da ƙasar ma baki ɗaya ba kamar anan ba ko yaushe zai ke tunanin zai ganta ko zai haɗu da ita.Wannan shawara ta yiwa Malam Auwalu daɗi sosai dan yana ganin hakan shi ne mafita dan ita damuwa a cikin zuciya take babu wani wanda zai iya cirewa wani daga zuciya sai ko a taya mutum da addu'a akan Allah ya cire masa.


Duk da Umma Sadiya bata ƙaunar Hizbullah ya mata nisa domin kuwa shi kaɗai ne ɗan da Allah ya mallaka mata, amma saboda suna so ya samu kyakkyawar rayuwa da ilimi mai nagarta hakan yasa suka amince masa ya cike form ɗin schoolarship ɗin amma a ɓangaren Hizbullah shi dai bashi da wani zaɓi dan shi komai yanzu ba ya jin daɗinsa, sai dai baya so kwata-kwata ya bar ƙasarsa ta haihuwa saboda ya san akwai ɓarin jikinsa, mahaɗar rayuwarsa burin zuciyarsa a cikin Niger'a wato Ridallah.


Cikin ikon Allah Hizbullah yana daga cikin wanda gwabnati ta biya wa karatu zuwa ƙasar china, iyayensa sun yi matuƙar murna da sanya albarka a cikin lamarin.Haka aka yi ta shirye-shirye aka yi passport sannan aka masa biza da komai da komai har Allah ya kawo ranar tafiyar, ta Dutse da ke Jigawa State za su tashi haka iyayensa suka masa rakiya har airport ɗin ya yi sallama da iyayensa suna masa fatan alkairi suna kukan rabuwa da shi, shi kuma kuka biyu yake ɗaya kukan rabuwa da iyeyen nasa ɗaya kuma kuka rabuwa da ƙasar da masoyiyarsa ke ciki tun da har yau babu labarin su Ridallah ɗin.


Haka su Umma Sadiya suka tsaya har sai da jirgin su Hizbullah ɗin ya tashi sannan suka baro airport ɗin.Sun sauka lafiya a inda suka samu masaukin su da aka ba su acan ƙasar amma dai ba cikin makaranta suke ba gida ne wanda bashi da wani nisa da makarantar tasu, yawanci dama duk ƴan Nigeri'a ne wanda gwabnati ta biya musu schoolarship, da wanda suka kusa kammalawa da kuma wanda shekaru biyu ya rage musu da ma wanda su ne ƴan wannan shekarar.Gida ne mai tsari hawa -hawa wasu a sama wasu a ƙasa ɗakuna ne gasu nan kowa da nasa akwai kuma bayi a ciki har da kicin.A upstairs Hizbullah ya samu ɗaki bayan ya buɗe da makullin da aka bashi ya shiga ɗaki yana ƙare masa kallo akwai komai da komai a ciki haka ajiye jakarsa, yana leƙa ko'ina sai dai akwai ƙura dan ba kowa ke zaune a ciki ba.


Yana tunanin yadda zai yi da gyara ɗakin domin yana buƙatar tsintsiya da mopa, gashi baya so ya fita ya tambaya dan ya ga kowa harkar gabansa yake, ɗakin da ke kusa da nasa kwa ban da kiɗa babu abin da ke tashi a ciki.


"Barka da zuwa bro kai ma saukar yanzu ne?" Ya tsinkayi wata murya a bayansa.Juyowa ya yi domin ganin mai maganar, wani matashj ya gani wanda bai fi sa'an shi ba tsaye yana masa murmushi.Hizbullah duk da baya jin daɗin zuciyarshi gashi kuma baya son yawan hayaniya, amma haka ya daure ya ƙaƙaro murmushi ya ce.



"Eh saukar yanzu"


"Ayya sannu da zuwa mu kam mun ɗan wartsake gajiya, dan yau kwananmu biyu da zuwa"Matashin ya faɗa lokacin da yake ƙarasowa cikin ɗakin.


Shiru Hizbu ya yi yana tunanin amsar da zai bashi dan shi bai saba da magana da abokai ba, babu wanda ya sani sai Ridallah, ita ce abokiyar hirarsa ita ce ke sanyashi nishaɗi tun bata san me zata ce masa ba ya saba da gwalan gwalantun ta tun tana ƙarama.Wata ƙwallah ce ta ciko masa idanunsa da bai shirya zuwanta ba dama tun a jirgin yake cike da damuwa da alhinin baro ƙasar da take.Haka yake ta tunani a jirgin har dai bacci ya yi nasarar ɗaukansa.


"Haba mazaje ya da ƙwallah haka, ai fa dama rabuwa da iyaye sai an kai zuciya nesa but be a man kar kake yarda wani na ganin hawayenka, za ka saba ne dan nima nan haka na wuni na kwana da tunanin gida amma yanzu da mun yi waya shikenan" Cewar matashin yana dafa kafaɗar Hizbu.



"Ba komai ba kuka nake ba ai, kawai dai na tuna wani abu ne"


"Yawwa my bro sunana Abulkairi Abubakar ana kirana da AA ni ɗan garin Kano,a unguwar hotoro haka kawai tun da na ga zuwanka na ji kawai ka burgeni ga ɗakina can sai ka wuce shi za ka zo naka"

"Thank u, sunana Hizbullah Auwalu ni ɗan jihar Jigawa ne a garin Haɗejia unguwar ƙofar arewa"


"Masha Allah suna mai daɗi "

Murmushi suka yi a tare, kallon ɗakin Abulkairi ya yi ya ce

"Yanzu za ka ga mai gyaran wurin ya zo,kafin ya rufe bakinsa sai ga wani saurayi sanye da wasu kaya da alama ma,aikaci ne a wurin da tsintsiya da mofa ya musu sallama tare da gabatar da kansa a matsayin ɗaya daga cikin masu shara da goge -goge na gidan cikin harshen nasara.


"Mu je ɗakina kafin ya gama gyara maka nan ɗin"Abulkairi yace yana kama hannun Hizbullah tare da ɗaukan jakar Hizbullah ɗin saboda kar ta yi ƙura suka fita daga ɗakin suka ba mai sharar damar yin aikinsa.

Ɗakin Abulkairi suka shiga, gabaɗaya yanayin tsarin ɗakin irin na Hizbu ne sai dai wannan a gyare yake tsaf, saɓanin na Hizbu da babu gyara.akan ɗaya daga ckn kujerun suka yiwa kan su masauki, bayan Abulkairi ya ajiye jakar, frige ya buɗe ya ɗakko lemuka da ruwan roba ya ajiye a gaban Hizbu kicin ya wuce ya ɗakko kofi ya kawo masa.Ganin bashi da niyyar ɗaukan drinks ɗin ya sha hakan yasa Abulkairi ɗaukan ruwan ya buɗe ya tsiyaya masa a kofin ya miƙa masa tare da cewa.


"Haba bro ka saki jikinka dan Allah sai wani ɗari -ɗari kake ka kasa sakin jiki dani" Ya faɗi hakan yana murmushi.Shi dai Hizbu bai ce komai ba ya miƙa hannu ya karɓi ruwan tare da kaiwa bakinsa yana mai ambaton Bismillah, ya kafa kai ya shanye ya ajiye kofin.Yana ajiyewa Abul ya ɗauki lemon ya buɗe zai tsiyaya masa a kofi.


"Ka barshi haka ma "

"Kana nufin ba zaka sha lemon ba?"


"Eh "Kawai yace a taƙaice ya koma ya jingina da jikin kujerar ya lumshe idanunsa.

"Ka koma kan gado ka kwanta in bacci kake ji" Da yake ɗakin kato ne daga can gefe akwai gado madai daici da wardrobe sai kuma kujeru guda biyu a tsakiya sai su frige kayan kallo da komai da komai na buƙata haka kowane ɗaki yake, da kicin da bayi duk a ciki.




"Bana jin bacci" Hizbu yace cikin ƙaguwa dan ya fara gajiya da waɗannan tambayoyin.


"Na lura dai baka fiya son surutu ba" Abul yace yana murmushi, shi dai Hizbu idanunsa kawai ya lumshe bai kuma cewa ƙala ba.




Bayan mai gyara ya gama suka koma ɗakin Hizbu Abul na riƙe da jakar, suna zuwa komai tsaf sai ƙamshi ke tashi haka Abul ya zauna yana kallo shi kuma Hizbu ya shiga wanka.Bayan ya fito ya sanya kaya marar nauyi, ya fitar da sauran kayan ya jera a cikin wardrobe ɗin ya fito da wayarsa daga aljihun jakar, sai ya koma ya zauna a kujera yana ɗan danna wayarsa shi kuma Abul yana kallo dan da ya lura Hizbu ba ya son yawan magana sai ya ƙyaleshi dan a tunaninsa ko gajiya ce ta sanya yake hakan bai san ba abin a jininsa yake, surutunsa na tashi ne idan yana tare da Ridallah.



_Bayan sati biyu_



Lokacin Hizbu har an zama ƴa gari domin yanzu har sun fara zuwa school, an fara karatu ba kama hannun yaro, yanzu abotarsu ta ɗan yi ƙarfi da Abul domin Hizbu ya lura yana da kyawawan ɗabi'u hakan yasa ya saki jiki dashi sai dai idan surutu ne ya yi yawa Hizbu bai biye mishi, shima kuma Abul da ya fahimci halin Hizbu ne rashin son magana sai yake ƙyaleshi idan ƴan kuramen suka zo.Yanayin zamantakewar su abin sha'awa basa shiga harkar kowa in ba gaisuwa ba bare kula ƴan mata kowa yana yin abin da ya kaishi.


Duk da ba department ɗaya suke ba amma wani lokacin tare suke tafiya school, kowa sai ya nufi nasu ɓangaren domin aiwatar da abin da ya kaishi.Hizbu yana waya da su Umma amma duk lokacin da zai kira su sai ya ji zuciyarsa ta masa rauni saboda tuno Ridallah, sannan duk lokacin da suka yi waya sai ya tambayi labarin Ridallah ko zai ji an ganta amma magana ɗaya ce ko yaushe babu labarinsu hakan na sanya ya ji duk damuwa ta dabai baye masa zuciya dan ba ya jin dai-dai da second ɗaya zuciyarsa za ta manta da Ridallah domin ita ɗin a cikin jininsa take.





MMN AFRAH😍🥰😘


❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page1️⃣5️⃣&1️⃣6️⃣




_Ridallah_

A ranar da za a nemi su a rasa da cikin dare, misalin ƙarfe biyu da wani abu Baba Habiba ta je bayi domin yin fitsari sai kuwa take jiyo muryoyi na maza suna magana ƙasa-ƙasa, duk da bata jin me suke cewa amma ta tsorata saboda a jikin katangar gidanta suke butar ta ajiye a hankali ta lallaɓa ta fito daga bayin ta je jikin katangar gidan inda za ta fi sauraren me suke cewa dan dai ta sana tabbas akwai wani abu tun da mai zai zaunar da mutane har wannan lokacin suna magana kuma raɗa-raɗa, tana kai kunnenta kwa sai ta fara jiyo me suke cewa.


"Kawai mu haura ta katanga, tun da babu namiji a gidan daga ita sai ƴarta ta, na ci alwashin sai dukanmu mu ukun mun musu faɗe, dan ita yarinyar sai mun kasheta bayan mun mata fyaɗen saboda Hizbullah, a kanta ya ƙi amincewa da buƙatarmu yana ganin mutane a raine, to zamu gama da ita sai mu buɗe ƙofar gidan mu fice kafin asirinmu ya tonu.


"Oga ka rabu dashi zai zo hannu ne dama saboda yarinyar nan da yake so shi sa bai amsa tayin ba, amma yanzu in ya ga an yi mata fyaɗe an kasheta ta bar duniyar dole zai ƙauna ce ka ya ke biya ma buƙatarka"Ɗayan shi ma ya amsa masa.


"Yanzu ga wancan Alhajin can ya yi dare inaga daga Hotel yake kasan shi mayen mata ne, bari idan ya shige gida sai mu haura tun da yanzu ma bai gan mu ba"


"Gaskiya ne

Please Login or Register in order to submit comment