Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu duk maganar da muka yi a gefe kika ajiyeta, kinsan ko kaɗan bana son ganinki cikin damuwa, domin damuwa tana sanya ciwo, shi yasa in dai ba makaranta zan je ba ko wani uzuri mai muhimmanci ba na son na yi nesa da ke dan kar ki ke yawan tunanin nan"Hafeez ya ce lokacin da yake zaunawa daga tsugunnon da ya yi.



"Hafeez kenan sau nawa kake so na faɗa maka cewa nima ba a son raina nake tunanin nan ba, kuma ma bana sanin lokacin da nake yin tunanin sai dai na tsinci kaina a ciki, dan Allah kake min uzuri mana wannan tunanin ya zame min jiki koma in ce ya zame mini abokin rayuwa!" Cewar Ammi tana sanya hannu ta share ƙwallar da ta kwaranyo mata yanzu.



"Ki yi haƙuri Ammi, nasan da haka tun da abin nan ba ke kaɗai ke yi ba nima ina yi haka Abba ma sai dai naki ne ya fi yin tsauri, Allah ne kaɗai ya san dalilin wannan yawan tunaninnda yake nema ya zame mana kamar gado kuma abin al'ajabin ma babu wanda cikin mu zai ce ga wani abu da yake tunawa a lokacin da yake tunanin, sai dai idan wani tunain ne da ban za ka yi kuma ka tuna abin da kake son tunawa har ma ka yanke hukunci ko sharar idan akan hakan ka yi tunanin..Amma shi wannan dogon tunanin fa da ya zama kamar ibada sji baka taɓa gane inda ka dosa bare ka san inda ka je sai dai ka gama bulayinka, ya tafi ya barka da damuwa a ranka.Tunani ne da ya sha ban -ban da wanda kowane tunanin da mutum zai gane irinsa sai dai mu cigaba da addu'a akan Allah kawo mana mafita"


"Amin ya rabbi" Ammi ta ce tana bin ɗan nata da kallon so da ƙauna tabbas kowacce uwa idan ta samu ɗa mai biyayya irin Hafeez to tabbas ta yi dace.



Ganin kallon da take masa ya sakar mata murmushi tare da miƴa hannu ya ɗakko tuffa ɗin da ta ajiye ya miƙa mata, karɓa ta yi cikin jin daɗi itama tana sakin murmushin ta kai bakinta ta gutsura, haka suka cigaba da hirarsu har aka kira sallar magriba, sannan Hafeez ɗin ya tafi masallaci itama ta shiga domin yin alwala ta gabatar da sallar tana so ta damawa Abban Hafeez kunun gyaɗar da ya ce ta dama masa zai sha idan ya dawo domin ya je gidan abokinsa kuma ta san a gida zai ci abincin dare domin baya iya cin abinci a ko'ina sai a gidansa.





Maman Afrah🥰😍😘


❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️



NA


MMN AFRAH


FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



PAGE 2️⃣&1️⃣2️⃣2️⃣




_Ridallah_


Tun komawarsu garin Gumel rayuwarsu ta sauya, Mama Rahma kamar yadda Ridallah take kiranta, ita ta sanar wa shugaban Boarding pri & Junior scul da take aikin abinci, akan ya mata alfarma za ta kawo wacce za ta maye gurbinta, cikin ikon Allah kuea sai ya ce dama akwai wacce ta rasu ba' a maye gurbinta ba dan haka ta bashi lokaci zai yi ƙoƙari ya bada sunan Baba Habiba idan Allah ya sa tana da rabo ta za ta samu haka suka masa godiya da ƙoƙarin da ya musu suka dawo gida cikin farinciki.


Bayan mako biyu kwa aka nemi Baba Habiba akan ta fara zuwa wurin aikin, duk da wasu masu aikin acan makarantar suke kwana amma Mama Rahma da yake tana da kula da aikinta tana zuwa akan lokaci ga kuma cika ƙa'idoji hakan yasa idan ta gama aikinta take tafiya gida ta kwana.Ita ma Baba Habiba ta nemi wannan alfarma kima da darajarsu da shugaban makarantar ke gani ya basu dama suke zuwa suna tafiya tun da a cikin gari suke, wannan ya sa su ma suka bada himma da kuma ganin basu yi duk wani abu da zai ruguje duk wata yarda da kuma dama da aka basu ba.


Kullum idan su Baba Habiba suna kicin suna aiki sai Ridallah ta samu wuri ta zauna ta rinƙa kallon ɗalibai idan suna tafiya ajijuwa, gwanin sha'awa kowa sanye da uniform da socks da sandal sai abin ya rinƙa birgeta tana jin inama ita ce, dan tana da son karatu amma gashi sun baro garinsu, hakan ya sa Ya Hizbunta ya faɗo mata yadda suke tafiya makaranta ya kama hannunta ya yi ta siya mata duk abin da take so.Amma yanzu gashi wasu sun shiga tsakaninsu da shi, sun sanya sun baro garinsu sun dawo wani garin da bata ma jin daɗin garin saboda babu Ya Hizbu a cikin garin.


"Kasan me Ya Hizbu?"

"A'a sai kin faɗa "

"Inaso in yi karatu mai zurfi idan na gama in samu aiki"


"Allah sarki Ridallah, insha Allahu sai kin yi karatu har ya isheki, ni nan zan tsaya tsayin daka har sai kin cimma burinki, sannan in Allah ya yarda za ki samu aiki"

"Nagode Yaya na" Ta ce tana murmushi, shi ma murmushin ya mata.

Maganar da suka yi ana gobe za su baro Hadejia ta faɗo mata, hawaye ne suka zubo mata ta sanya hannu ta share tana jin kewar Ya Hizbunta har cikin ranta, ashe burinta ba zai cika ba.


"Ridallah! Baba Habiba ta kirata da ta fito domin shanya gawayi.Da sauri ta ɗago kan nata ta kalki mahaifiyarta ta da ke kallonta cike da mamaki, duk da dama tun da suka dawo Gumel tana kamata tana kuka idan ta tambayeta sai ta ce Ya Hizbu ta tuno.To itama Babar tana mata uzuri tun da ta san irin shaƙuwar da suka yi, yo kuma abu ne mai wahala ace ta yakice tunaninsa lokaci guda duk da ta san dai ba lallai ne ta manta da shi ba har abada amma dai ta san mawuyaci ne ace sun ƙara haɗuwa ma, sai dai bata taɓa ganin tana yin kuka a wajen da jama'a ke kai kawo ba, ko a gidan takan kamata ne a ɗaki ta ɓoye kan ta tana kuka.


Ajiye ƙaramin buhun hannunta ta yi wanda ra zubo gawayin a ciki, ta ƙarasa wurin da Ridallah ke zaune ta zauna akan dakalin ita ma, hannun Ridallah ɗin ta kama da hannayenta biyu ta ce


"Haba Ridallah, har sai yaushe ne zaki daina yin wannan kukan kina zubar da hawayenki? Bayan kinsan cewa Hizbullah mun baro shi a Haɗejia sannan bai san ma inda muka taho ba, bare ya biyoki amma sai ki zauna ki yi ta zubar da hawaye, abun har ya kai kina kuka a inda mutane suke ficewa kuma za su iya ganinki? Dan Allah ki sanyawa ranki haƙuri da dangana duk da nasan da wuya hakan amma daurewa za ki yi ko nima na daina tunanin halin da kike ciki idan da rabon ganawa wata rana sai ki ga kun gana ke da shi" Baba Habiba ta kai ƙarshen maganar cikin sanyin murya tana kallon Ridallah da hawayen suka cigaba da sirarowa daga idanunta.


"Hakane Baba, amma ni yanzu ba wannan ya sanya ni kuka ba"


"Menene?"


"Kawai saboda na ga...

"Baba Habiba waye ya taɓa ƴar lelen naki na ga kina ta faman lallashi?" Maganar principal ɗin makarantar ta katse Ridallah daga abin da take so ta faɗa.

"Wallahi shugaba ka ganni da ita nima ban kai ga jin wanda ya taɓo ta ba"Baba ta ce cikin jin nauyin shugaban makarantar saboda mutum ne shi mai kirki da girmama mutane.

Wurin ya ƙaraso yana murmushi tare da cewa


"Ƴar lelan Baba wa ya taɓa ki?"

Shiru ta yi tana wasa da yatsun hannunta.


"Ba magana ake miki ba?" Baba Habiba ta faɗa tana kallonta.


"Dama fa..."Sai kuma ta yi shiru.


"Dama me?" Ya ce cikin lallashi.


"Dama da na ga uara suna tafiya aji shi ne ni ma na ji inason karatu" Ta kai ƙarshen maganar tana goge hawayen idanunta.


"Kai! Allah sarki Ridallah dama akan karatu ne kika shiga damuwa, ni ma da na yi tunanin cewa Babar taki a sanyaki a makarantar nan maimakon kike zaune, to kuma sai nake tunanin ko bata da ra'ayi, amma yanzu tun da har kina so babu abin fa zai hanaki shiga aji in har ta amince" Ya ce yana goya hannayensa a bayansa.


"Na amince shugaba, ai ni dama daga ni har ita ba mu da burin da ya wuce haka, saboda Ridallah yarinya ce mai matuƙar son karatu, gata da hazaƙa tun da take ko ta biyu bata taɓa ɗauka ba a makaranta kullum ita ce ke ɗauka na farko a ajin su"


"Allah sarki! To insha Allah za a sanyata a J.s 1 ɗin idan an mata interview mun gani, Allah jiƙan mahaifin nata" Principal ɗin ya ce yana mai jin tausayinsu, dan Rahma ce masa ta yi mijinta ne ya rasu ƴan asalin Malam madori ne sanadin mutuwar tasa ce suka dawo Gumel ɗin da zama dan Baba ta hana ace daga Haɗejia suka taho dan bata so kowa ya san daga inda suke saboda wani dalili nata daban wanda ita ce kaɗai ta san hakan.


"To mun gode ƙwarai Allah sa ka fi haka, Allah ɗauka ka, ka ya albarkaci zuri'a" Baba ta faɗa cikin farinciki.


"Amin ya Allah nagode ni ma da addu'a, kuma babu komai ai yiwa kai ne, ni zan mata komai kama daga litattafai da komai da komai"



"Nagode Baba shugaba Allah saka maka da alkairi, ya sanyaka a aljanna" Ridallah da ta tsugunna har ƙasa ta haɗe hannayenta a wuri ɗaya ta ce cikin murna da farinciki.



"Ba komai ƴa ta taso mu je" Ya ce yana kama hannunta suka tafi can office ɗinsa.



Baba Habiba kwa tsabar farinciki ma ta rasa bakin magana, haka ta tsaya tana kallonsu har suka ɓacewa ganinta sannan ta ɗauki buhunta ta kama hanyar kicin. Dan so take ta je ta baiwa Rahma labarin wannan abin arziƙi da aka musu.



Sosai Mama Rahma ta ji daɗi da wannan albishir




Principal ɗin office ɗinsa ya wuce da ita ya yi mata register da komai da komai, sannan ya ɗakko mata uniform set biyu daga cikin uniforms ɗin da gobnati take bayarwa a rabawa ɗalibai.Ridallah sosai daɗi take ji a ranta baki yaƙi rufuwa sai kallon uniform ɗin take yi tana murmushi sai faman godiya take yiwa shugaba shi kwa sai cewa yake ta daina godiya, wani Malami ya kirawo yasa ya mata interview sosai suka yi mamaki daga Malamin har principal ɗin saboda yadda take bada amsoshi a nutse ko gaga ba ta yi sun gamsu da amsoshinta sosai dan haka principal ɗin ya ce ta je ta sanya kayan makarantar ta dawo, haka ta je ɗakin su Baba da ke can inda ɗakunan ma'aikatan kicin yake, duk da su, su Babar basa kwana a makarantar amma dai akwai ɗakin da suke hutawa, haka ta je ta sanya kayan tana ta murna ta linke wanda ta cire ɗin ta nufi kicin ɗin.


Da murna ta je ta rungume Baba ita ma Babar rungumeta ta yi cike da farinciki dan ji take kamar yau take sallah tana son farincikin Ridallah haka kuma ta tsani baƙinciki ko ɓacin ranta.Kowa a wurin sai dariya yake musu ganin suna murna gwanin sha'awa.Haka ta ce musu ta tafi aji, office ɗin shugaban ta je ya kalleta yana murmushi ya ce


"Ridallah an zama ƴan makarantar kwana"

Cike da kunya ta sanya hannu ta rufe fuskarta tana murmushi dan duk daɗi ya cikata ta ƙosa ta ganta zaune cikin aji tana ɗaukan darasi.

"To ga wannan" Ya ce yana miƙo mata wata jaka mai ɗauke da dukkan littattafan da ake amfani da su a ajin da za ta je sai biruka guda biyu da mathset da komai da za ta buƙata har test buke duk a ciki.

Idanu ta ɗan zaro dan ita tsabar ruɗewa da kuma murna ta ma manta da wasu abu littattafai.

"Gaskia shugaba ko dai ni za a baiwa nima in shiga ajin"Malamin nan ya ce cikin zolaya yana murmushi.


"Nawa ne waɗannan" Ta ce tana miƙa hannu cike da ladabi ta karɓa, tare da buɗawa ta leƙa ganin abin da ke ciki sai farincikinta ya ƙaru akan wanda take ciki da.

"Allah saka maka da alkairi, ya faranta maka kamar yadda ka faranta mini" Ta ce tana kallon Principal ɗin cike da girmamawa.

"Amin ya rabbi, shugaba da da Malamin suka hala baki wajen faɗa.

"Mu je na raka ki ajin " Malamin ya ce yana yin gaba ta juya ta bi bayansa.

"Allah bada sa'a" Ta tsinkayo muryar Principal ɗin lokacin da ta kai bakin ƙofar fita.

"Amin" Ta ce tana sanya kai ta fita daga cikin office ɗin.

Principal ɗin komawa ya yi ya jingina da jikin kujerarsa yana jin wani irin daɗi da nishaɗi a ransa dan a rayuwarsa yana son ya ga ya taimaki mutane, musamman yara, yaran ma marayu yana son sanya farinciki a zuciyar maraya, kasancewarsa maraya ya san zafi da raɗaɗin maraici hakan yasa yake ta ƙoƙari domin ganin ya cire su daga wani ƙunci ko baƙinciki ya sanya su a farinciki.



_Hizbullah_


Zaune yake a ɗakinsa yana riƙe da handout yana karatu, sai kofin shayi ɗan ƙarami da ke kan ɗan ƙaramin faranti, jifa-jifa yana ɗauka yana kurɓa ya maya ya ajiye, yana cikin karatun sai ya ji Ridallah ta faɗo ɓasa a rai da sauri ya ajiye handout ɗin kamar wanda aka tsikara ya dafe kansa da hannu biyu saboda jin da ya yi ya sara masa.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Ya ce yana wani runtse idanunsa da ƙarfi jin yadda zuciyarsa ke buga masa da mugun ƙarfi tamkar wacce ke neman agajin gaggawa, kan nasa ya saka ya sanya hannun nasa a ƙirjinsa saitin zuciyarsa ya dafe tabbas Ridallah ita ce bugun zuciyarsa amma yanzu bai ma san inda take ba bare ya san halin da take ciki ba. Da sauri ya miƙe kamar wanda aka tsikara ya nufi inda ya sanya wayarsa caji ya ɗakko ta maimakon ya dawo ya zauna a kan kujerar sai ya tsaya a jikin bango tare da jingina bayansa da bangon, a hanzarce ya shiga contact ya nemo lambar wayar Ummarsa ya shiga buguwa amma har ta tsinke ba'a ɗauka ba, bai yi wata-wata ba ya sake danna wani kiran a karo na biyu burinsa kawai Umma ta ɗauki wayar cikin sa'a kwa sai aka ɗaga wayar.

"Assalamu alaikum" Umma ta yi sallama daga can ɓangaren.

"Wa alaikumus salam" Ya amsa

"Hizbu na kai ne akan layi"

"Ni ne Umma, ina yini "

"Lafiya ƙalaw, ɗan albarka ya karatu"

"Alhamdulillahi! Umma ina lafiya ƙalaw"

"Masha Allah, ina Abulkairi"

"Yana lafiya"

Nan dai suka suka shiga hira ya tambayi Babansa ta ce ya fita, so yake ya tambayeta labarin su Ridallah amma kuma ba ya so ya ji labarin da ya saba ji kullum dan ya san da ace an samu labarinsu to da tun kafin ya kira da sun kira shi aun shaida masa hakan dan ya san sun san halin da yake ciki na buƙatar jin labarin.

"Hizbu na baka ji na" Muryar Umma ta katse masa tunani.

"Umma ina jinki, dama...dama..."

"Dama me? Ka faɗi abin da kake son faɗa mana"

"Dama ina so in ce miki ya labarin su Ridallah" Ya ce yana maida kan sa ya jingina a jikin bangon tare da ɗaga kan sa sama ya sauke akan ɗaya daga cikin ƙwan fitilun mai kyau da walwali da aka masa wata walkiya da wani abun walkiya mai ƙyalƙyalin ruwan gwal, tare da sanya haƙori ya danne gefen leɓensa na ƙasa yana jiran jin amsar Ummar.

"Haba Hizbu kullum a rinƙa magana ɗaya? Kasan dai da ace an samu labarinsu sai mun fara kiranka mun sanar maka kafin ka kira ka tambaya amma ace kullum sai ka kira ka tambaya wataran ma sai ka kira ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, ka kwantar da hankalinka ka dage da karatunka insha Allahu Allah zai bayyana su muna nan muna addu'a kai ma ka cigaba da yi"

"To Umma nagode sai an jima a gaishe da Baba" Ya faɗi hakan cikin raunin da zuciyarsa ta masa.

"To Hizbullah ka gaishe da Abulkairi"

Da to kawai ya iya amsa mata ya kashe wayar ya tako yana jan ƙafafunsa dakyar ya ƙaraso ya zube akan kujerar ya saki wayar ta faɗa kan handout ɗin da yake karatu.Idanunsa a rufe yana jin wani ɗaci a cikin zuciyarsa tamkar ya sanya magani paracetamol a ciki haka yake ji, a hankali ya buɗe idanunsa zuwa lokacin sun yi jawur kamar wanda ya kwana yana kuka, cikin sanyin jiki ya tashi ya tafi ya buɗe wardrobe ɗinsa, ya ɗakko wani ɗan ƙaramin kit ya koma ya kwanta akan gadon tare da ɗora kansa bisa filo, ɗan kit ɗin ya buɗe ya saya hannu ya fiddo wata flower da ɗankunne wari ɗaya ya riƙe su akan tafukan hannayen sa tare da zuba musu jajayen idanunsa a hankali maganarta ta shiga dawo masa a ranar da ta bashi waɗannan abubuwan.


" Ya Hizbu wannan flower a jikin flower Baba na ciro a ɗakinta, saboda jiya ina ganin film ɗin kwana casa'in sai na ga Yawale da durƙusa ya baiwa Rayya flower, shi ne nima na ciro na kawo maka" Haka ta durƙusa kamar yadda Yawalen ya yi ta baiwa Hizbullah flower, cikin murna ya karɓa sannan ta miƙe suke dariya su duka, tun daga wannan ranar yake ajiye da flower dan wataran ma idan ta shiga gidan su Hizbullah ɗin sai ta ce "Ya Hizbu ina flower da na baka" Har sai ya ɗakko ya nuna mata sai kuma ta ce
"Dan Allah ka jaiyeta kar ka jefar"

"Babu abin da zai sa na jefar da ita" Ita ce amsar da yake bata.

Ɗankunnen ya ɗago da yatsunsa biyu yana kallonsa duk da ɗankunnen ya daɗe amma babu abin da ya yi kasancewar sa azurfa, nan take ya shiga tuno da ranar da ta bashi warin ɗankunnen yana zaune a ɗakinsa yana gyaran littattafan makarantarsa yana sanya su a jaka ta shigo da ɗankunnen a hannunta.A kusa da shi ta zauna ta ce

"Ya Hizbu ɗankunne na kawo maka"

"Ɗankunne kuma Rida ni da ba mace ba mai zanyi da ɗankunne?"

"Dama Baba ce ta siya min sabo ta sanya min saboda ɗayan wannan ya faɗi shi ne na kawo maka, tun da maza ba kwa sanya ɗankunne ba sai ka ajiye ba" Ta faɗa tana nuna masa ɗankunnen da aka siya mata sabo a kunnenta.

Jakar ya ajiye a gefe ya miƙo hannunsa ta basa ɗankunnen yana ta murmushi itaɓa tana yi.

"Yawwa to godiya nake" Ya faɗa yana buɗe zip ɗin Babbar akwatinsa ya fito da ɗan kit ɗin da ya siya ya sanya flower da ta bashi, ya buɗe ya sanya ɗankunnen a ciki.

Bai ankara ba sai jin hawaye ya yi suna gangarowa a kumatunsa, tabbas ya yi kewar Ridallah, kewar da shi kan sa bai san yawa da adadinta ba kewar da ya san babu ranar da zai daina har sai ranar da ya sanya Ridallah a idanunsa.Juyawa ya yi, ya koma ribda ciki ya shiga yin kukan yana jin zafi da raɗaɗin rashinta na ratsa dukkan sassa da gaɓoɓin jikinsa, tabbas shaƙuwa wata aba ce mai wuyar fita daga rai, shaƙuwa tana yin zama a cikin zukata tamkar yadda kayana kayan ciki ke zaune cikin jiki, tana haɗuwa a zukata har ta zama abin da bai rabuwa wato hanta da jini.





❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YATINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️




NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...




PAGE2️⃣3️⃣&2️⃣4️⃣



"Wallahi duk abin da kike ganin za ki yi sai dai ki yi, dan tafiya babu fashi dole Iftihal ta je china ta yi karatu tun da na ga abin naki babu hankali a ciki.Kamar ba ke kika haifeta ba ƴar ƙwaya ɗaya amma ace ta tashi babu arabi ba boko sai yawon banza da kike sanyata da bin gidajen ƙwaye" Abie ya kai ƙarshen maganar tare da buga kan kujerar da yake zaune da hannunsa dan ya lura abin na Hajiya Hauwa ba na ƙare bane sai an zage dantse an nuna mata iyakarta.


"Dan Allah Alhaji ka yi haƙuri kar ka kai min ƴata karatu ƙasar waje, na yarda zan barta take zuwa makarantar anan amma ya za a yi ace kamar Iftihal har nawa ma take da za ace an fitar da ita karatu har wata ƙasa"


"Da can baki san da karatun nata ba kika ƙi kullum muna magana ɗaya amma kin ƙi ji yanzu ban da shegen yawo da yarinyar ke fita ba tare da sani na ba, ni ma yanzu ban yarda da ke ba akan zaki barta ta yi karatu kuma da kike maganar nawa take zan aikata ƙasar waje karatu ai na faɗa miki gidan abokina Alhaji Sani Habu da yake zaune acan zan kaita acan za ta yi karatun ta dan haka kisa Safiya ta haɗa mata kayanta dan bizarta tana fitowa za ta tafi"


"Alhaji ka yi haƙuri a sasanta mana tun da dai yanzu ta amince ka haƙura da kaita chaina"Momma ta faɗi hakan cikin sanyin murya da lallashi.

Idon Abie Hajiya Hauwa ta faka ta aikawa da Momma wata uwar harara me nuni da ke kika sani munafuka, sai zare ido take kamar idanunta za su faɗo ƙasa.Ita dai Momma yi ta yi kamar ma ba ta san tana yi ba dan ita tsakaninta da Allah take faɗar abin da ke ranta dan ita ma bata ƙaunar hana Iftihal ɗin zuwa makaranta da take sannan ta tsani yawon da aka buɗewa yarinyar idanu da shi, dan ta san shi Abie bai ma san har samari suke kawo Iftihal ɗin gida a mota ba, abin na damunta amma ba ta so tayi magana ace baƙinciki take saboda ba ita ce ta haifeta ba, dan akwai wata rana da ta fara ganin an sauke Iftihal ɗin a mota wani mutum ne babba da shi, a lokacin Momma ta dawo daga unguwa direba ya kai ta lokacin da hancin motarsu Momma ya danno ƙofar gjdan ita kuma Iftihal ta buɗe ƙofar ta fito suna ɗagawa juna hannu ita da na cikin motar, baki sake Momma ke kallonsu dan kwata-kwata hankalinta bai kwanta ba Iftihal ɗin na ganin su Momma ta yi saurin tura ƙaramar ƙofar get ɗin ta shige cikin gida. Horn direban ya yi aka wangale musu get ɗin suka shiga dan ko da Momma ke tambayar direban ko ya san mai motar cewa ya yi ai yanzu motoci ne kala-kala ke kawo Iftihal ɗin gida su ajiyeta a bakin get.


Dan haka tana tana fita daga motar hankali tashe ta yi part ɗin Hajiya Hauwa dan ta yi alƙawari ko me Hajiyar za ta ce mata sai ta faɗa mata abin da idanunta ya gani dan ta sani dan ta san idan ta sanar mata ko nan gaba ta fita ko a girin Allah ko da wani abu ya faru duk da ba a fatan hakan.Tana kaiwa dai -dai ƙofar da zata sada ta da falon Hajiya Hauwa sai jin wata magana ya dakatar da ita daga shiga ta tsaya tana sauraron maganar hankali tashe.

"Yanzu Alhajin da ya dawo da ke gida shi ne ya baki wannan maƙudan kuɗin Iftihal"Cewar Hajiya Hauwa muryarta cikin farinciki.


"Wallahi kwa Aunty shi ya bani dan da kuɗin da ya bani bai kai haka ba, aikuwa da muka fito daga Hotel ɗin zai kawo ni gida na marairaice murya kamar yadda kika koya min ina kashe masa ido ai nan da nan ya ƙara buɗe aljihunsa ko irgawa bai yi ba ya zuge jakata ya zuba

Please Login or Register in order to submit comment