Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau akwai kwasar gara duk da ma dai mata ba wani damun mu suka yi ba, mun fi ƙarfi a neman ƴan uwanmu jinsinmu maza, amma saboda wannan mai taurin kan gwara mu afka musu tun d....

Cikin hanzari Baba Habiba ta baro jikin katangar jikinta sai mugun rawa yake, gabaɗaya ta susuce hankalinta a mugun tashe yake burinta kawai su bar gidan kafin mazan su duru, ɗaki ta nufa Ridallah da ke kwance tana baccinta hankali kwance, hannun Baba Habiba har karkarwa yake ta ɗago Ridallah tare da toshe mata baki, da yake Ridallah ɗin bata da wani magagin bacci ta buɗe idanunta amma tsoro sai ya kamata ganin Babarta ta toshe mata baki, hannunta kawai ta kama ta sakko daga kan gadon ganin hakan yasa Ridallah gane akwai wani abu da ke faruwa.


Gani ta yi Baba Habiba ta nufi hanyar zauren ƙofar gida, duk cikinsu babu mai takalmi a ƙafarsa, a hankali Baba Habiba ta zare sakatar ƙofar gidan suka buɗe suka fita a hankali, suna fita suka zura da gudu babu kowa a titin saboda dare ne hakan ya basu damar gudu akan titi, gudu kawai suke ba su san inda suke saka ƙafafunsu ba.A can cikin gidan kuwa mazan sun sami nasarar haura katangar su duka uku, shigarsu gidan ke da wuya suka fara duba ɗakunan domin aiwatar da abin da ya kawo su, suna dubawa suka fahimci babu kowa a cikin gidan suka duba ƙofar gidan ganinta a buɗe yasa suka fahimci cewa masu gidan sun gudu ne da alama sun musu laɓe ko dai makamancin haka A take suka mara musu baya domin sun ci alwashin sai sun aiwatar da ƙudirinsu a yau ɗin nan!


Ƙarfin namiji da mace ba ɗaya bane haka gudu da juriyar da namiji zai yi ba lallai ne mace ta yi ba.Wannan dalilin ne yasa mazan nan suka fara hango su Ridallah da ke sheƙa gudu, sai dai akwai tazara a tsakaninsu.Baba Habiba da yake suna gudu tana waiwayowa amma duk da layikan unguwanni da suka yi canjawa amma sai da suka lura suna biye da su hakan yasa suna shan wata kwana kafin mazan su ƙaraso Baba Habiba tasa suka shiga cikin wani kwalbati wanda babu ruwa a ciki suka kwanta rubda ciki yadda ba za a gansu ba suna fata da addu'ar kar Allah yasa su gansu domin babu mai cetonsu sai Allah, gashi talatainin dare kowa yana gidansa yana bacci.



Mutanen nan na ƙarasowa kwanar nan su duka ukun suka tsaya, suna ta waige-waige sai haki suke na gajiyar gudun da suka yi kamar an sa su dole. Tafiya suke suna ɗan duba wa amma ba su gan su ba, haka suka zo har dai -dai kwalbatin nan suka tsaya, gaban Baba Habiba da na Ridallah sai bugawa yake da ƙarfi suna fatan kar Allah yasa su gansu.Ɗaya daga cikinsu ne yave zai yi fitsari dan haka ya ƙarasa bakin kwalbatin da su Ridallah suke, daga tsaye ya shiga yin fitsari a cikin kwalbatin, su Ridallah fuskokinsu suka sanya a tafukan hannayensu suka rufe suna jin yadda mutumin nan ke tsula fitsari a jikinsu domin fitsarima ba wai a wuri ɗaya yake yi ba kawai wasa yake da fitsarin yana watsawa ko ina, har sai da ya gama fitsarin sannan ya gyara wandonsa, sai ya juya ga sauran yace


"ina ga fa sun bi wancan layin" Ya faɗa yana musu da hannu.A guje suka tafi dan duk a tunaninsu su Ridallah suka marawa baya.


Suna tafiya, jin su Baba basa jin motsin kowa alamar sun yi nisa haka suka tashi suka fito daga cikin ramin, basu damu da fitsarin da ke jikinsu ba dan burinsu kawai su tsira da mutunci da rayuwarsu.Hanya suka canja suka cigaba da gudu har sai da suka yi nisa sosai, dan gabaɗaya ma hanyar barin garin suka ɗauka dan sun tsorata sosai haka suke gudu ga tsananin gajiya sai da suka yi nisa da gari sosai sannan suka samu wata ƴar siririyar hanya suja bi hanyar ga tsananin duhu haka suka shiga wurin a ƙarƙashin wata bishiya suka yada zango suna ta haki saboda gudun da suke yi.Haka suka kwana a wurin cike da tsoro da fargaba, da asubar fari suka yi taimama suka gabatar da sallar asuba, da duku-duku suka cigaba da tafiya dama saboda kar wanda ke nemansu suje tashar mota shi yasa suka ƙi zuwa tashar sannan yanzu ma suna iya biyo bayansu, sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa sannan suka tsaya a hanya bakin titi suka tsayar da motar haya suka shiga direban ya tambayesu garin da za su sauka Baba Habiba ta ce garin Gumel.



Sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa sannan hankalin Baba Habiba ya ɗan kwanta, ita kwa Ridallah dama tun da ta ɗora kan ta akan cinyar Baba sai wani bacci mai nauyi mai cike da tarin gajiya ya ɗauketa saboda basu runtsa ba.Har sai da suka shia cikin garin Gumel sannan ne Baba ta tasheta, a nato aka sauke su Baba ta kunce gefen zaninta da akwai kuɗin da ta ƙulle ta ɗauka ta baiwa mai mota.Napep suka tare suka shiga Baba ta ce a kai su unguwar ɗantanoma, a dai-dai wani gida aka saukesu ta sallami mai napep ɗin suka sannan suka shiga cikin gidan.

Sallama Baba ta yi, aka amsa musu tare da basu izinin shiga, suna shiga matar gidan ta ce


"Habiba?" Ta faɗi hakan cike da mamaki akan fuskarta.


Murmushi Baba ta yi ta ce



"Na'am Rahma"



Cikin kulawa ta musu iso har cikin ɗaki tana ta faman musu sannu da zuwa tare da nuna jin daɗinta da ganinsu.Ridallah ce ta fara gaisheta ta amsa cikin sakin fuska da nuna jin daɗinta.Sannan suka shiga gaisawa da Baba Habiba cikin kewa da yaushe gamo.Ruwa ta gabatar musu duk da akwai tarin tambayoyi birjik a bakinta dan ganinsu da ta yi wujiga-wujiga ko takalmi babu.


Bayan sun ɗan huta Rahma ta ce Ridallah ta shiga wanka, ba musu kwa ta shiga dan lokacin kusan sha biyu na rana dama watan buƙatar watsa ruwa a jikinta.Bayan shigarta wanka Baba ta shiga yiwa Rahma bayanin dalilin barowarsu hadejia , Rahma ta jimanta abin tare da yiwa Baba jaje akan abin da ya so samun su tare da murna akan tsallake rijiya da baya da suka yi.


A nan Rahma ta shiga yiwa Baba bayani akan
tun bayan mutuwar mijinta aka bata timunin takaba take zaune a gidan sai ƴan siye d siyarwa da take da kuma aikin abinci a wata makarantar kwana ta mata da take cikin garin Gumel ɗin.



MMN AFRA😍😘




❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...




Page1️⃣7️⃣&1️⃣8️⃣




_Hajiya Hauwa_



Zaune take a bakin gado ta haɗa hannaye biyu a kumatun ta, ta yi tagumi kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa, abubuwan da suke faruwa ba ƙaramin ɓata mata rai suke ba ace kullum magana ɗaya yanzu tun da class mate na Iftihal suka kammala primary school Alhaji ya sakota a gaba wai da gangan take hana Iftihal ɗin ziyartar makaranta yanzu gashi nan tana neman ta mata asara.


Iftihal ɗin ce ta shigo ɗakin ko sallama babu bare neman izini, sanye take da wata doguwar riga ƴar kanti wacce tsayinta iya gwiwarta ne, sai phone ɗinta riƙe a hannunta tana jin waƙa, headphone ɗin ta zare daga kunnenta, sannan ta ɗan buga jikin Auntyn nata a ɗan firgice ta ɗago domin kwa ta yi nisa cikin tunani, kallonta Auntyn ke yi tana ƙarewa gabaɗaya jikin Iftihal ɗin kallo kamar dai yau ne ranar farko da ta fara ganinta sosai yarinyar halittar ta da surorinta ke haɓaka kamar wacce ta ke shirin kammala secondry school kallonta take daga sama har ƙasa tana hasasho yadda idan ta kasa hajarta za ta samu ciniki sosai da kuma riba mai tarin yawa, wani murmushi ne ya maye gurbin ɓacin ran da take ciki wanda hakan yasa Iftihal ɗin cewa


"Aunty yanzu nan fa kika yi shiru tare da yin nisa a cikin tunani amma kuma yanzu gashi kina kallona kina murmushi"


"Iftihal kenan akwai dalilin da ya sani shiga cikin damuwa, wanda ba komai bane hakan illah yadda Abienki ke takura min akan rashin zuwanki makaranta, amma nasan ba komai ke sanyashi yin hakan ba sai rashin sani wanda ya fi dare duhu! Baisan irin ƙudurin da nake da shi akan ƴata ba shi yasa yake faɗan rashin zuwanki makarantar.Amma kuma dana kalleki sai na tuna da wani abu wanda wannan abun shi ne ya sanyani murmushi" Aunty ta kai ƙarshen maganar tana dafa kafaɗar Iftihal ɗin da ta zaunrta kusa da ita tana murmushi.


"Hakane Aunty amma kuma sai in ke ganin kamar koma menene a bayan karatuna yake domin ilimi shi ne ginshiƙin rayuwa kuma shi ne sinadarin zaman duniya har ma da lahirar baki ɗaya domin ba fa boko kaɗai kika hanani zuwa ba har da islamiya, kuma kullum in na tambayeki menene kudurin naki a kaina bakya faɗa min"


"Kar ki damu Iftihal ni dai nasan babban abin da ke sanya mutane neɓan ilimi a wannan zamanin shi ne kuɗi! To kuwa indai kuɗi ne tabbas babu makawa har sai kin taka naira da ƙafafunki, kuma batun ilimi gishirin koma menene duk wannan bai taso ba domin a wannna ƙasar tamu masu yanzu idan da za a ce a lissafo wanda suka kammala karatunsu amma basu samu aikin yi ba yo wallahi lissafasu ma kaɗai aiki ne, dan haka ki kwantar da hankalinki kuma indai kudurina ne a kan ki zan faɗa miki nan ba da daɗewa ba domin na hango lokacin na nan tafe ya ma kusa zuwa"


"To shikenan Aunty na yarda domin kuwa uwa ba za ta taɓa yin abin da za ta cutar da ƴarta ba"

Wani murmushin Auntyn ta sake yi domin Allah kaɗai ya san kudurin da ke ranta, kafin ta ce


"Yawwa Iftee na shi sa bani da tamkar ki"


"Ni ma haka Aunty shi sa ma kika ga na fi bin umarninki fiye da na Abie na"


Wani daɗi ne yasa Auntyn sanya hannu ta rungume Iftihal ɗin suna dariya a tare.


Bayan sun ɗan tattauna Aunty ta shiga koyar da Iftihal ɗin tafiya, da kwarkwasa da dai abubuwa duk da Iftihal ɗin bata san manufar hakan ba amma dai tana jin daɗi a ranta ganin mahaifiyarta na koya mata abubuwa da kan ta.




_Momma_


Misalin ƙarfe biyar na yammacin ranar laraba, zaune take akan sallayarta tana karatun qurani mai girma tun da ta yi sallar la'asar take karatun, bayan ta gama ta rufe qur'anin tare da ɗaga hannunta sama tana ta addu'a wanda ba a jin me take cewa sai dai hawaye na ta kwaranya daga idanunta har ta kammala ta shafa.Qur'anin ta ɗauka ta mayar dashi ma'ajjinsa sannan ta linke hijabin da sallayar ta ajiyesu, kan gadonta ta koma ta kwanta idanunta a sama har lokacin hawaye na kwaranyowa a idanun nata, ita kaɗai ta san me take ji a zuciyarta game da abin da take tunawa Allah ne kuma kaɗai ya san damuwarta domin duk duniya babu wanda ta taɓa faɗawa damuwarta.Amma dai ta san kullum idan ta tuno shi tana jin damuwa a ranta kuma in ba kuka ta yi ba bata samun sassauci a zuciyarta, idan kuma ta rufe idanunta shi take gani lokacin da ya faɗo daga jikinta, da kuma lokacin da aka gama gyarashi aka miƙo mata shi, Allah sarki idan kuma ta tuna lokacin da aka ce ya mutu aka sanyashi a kwali aka ce gida za a je ayi suturarsa sai ta ji zuciyarta ta yi rauni da yawa.Gashi yau tsawon shekaru goma sha shida kuma bata sake samun wani cikin ba bare ayi zancen sake haihuwa bata sani ba ko za ta haihu a gaba ko kuma shi ne kaɗai rabonta.



"Ya Allah kai kaɗai ne ka san damuwata Allah ka kawo min mafita, ya Allah ka bani wani rabon kafin na bar duniya, idan kuma shi kaɗai ne rabona ya Allah ka...kafin ta ƙarasa sai kuka ya ƙwace mata.Haka dai tana nan tana tunani har dai Suhailat mai mata aiki ta faɗa mata cewa Alhaji ya dawo haka ta wanke fuskarta ta gyara fes kamar ma ba ita ke cikin damuwa da yin kuka ba ta shafa powder da lipstick ta fito abinta sai tashin ƙamshi take.


Tana zuwa kwa ta ga Abie tsaye yana jiranta dan ko upstairs ɗin ma ya kasa hawa


"Welcome back"Ta ce tana sakar masa murmushi tare da ɗaukan jakar office ɗin nasa.


"Ni na yi fushi" Ya ce yana juya mata baya.

Wani murmushi ne ya suɓuce mata.

"Ai wanda ya yi fushi ba shi yake faɗa ba, wanda aka yiwa fushin ne ke fahimtar haka"

"Koma dai menene ni bana kulaki"


"Ni ce fa" Ta faɗa lokacin da ta zo inda ya juya ɗin.Ƙara juyawa ɗaya side ɗin ya yi.Ita ma komawa ta yi tare da ajiye jakar hannunta ta ce


"Ni ko? Afwan" Ta faɗa tana haɗe hannayenta wuri ɗaya alamar roƙo.

Da murmushi ya juyo suka fuskanci juna, sannan ya ce


"Ba ke ce ba kika ƙyaleni ina ta jiranki, kuma kinsan ba zan iya haurawa sama ba matuƙar dai baki fito ba gashi na gaji ba zan iya zuwa ɓangarenki ba"


"To ka yi haƙuri ka ji? Ina can ina ɗan maka kwalliya ne"

"To me yasa baki yi min kafin dawo wa ta ba?"

"Afwan wani ɗan abu ne ya riƙe ni har na shagala da hakan, amma ai ka san ina ji da kai"

"To shikenan na huce, ai ni na ma fi ji da ke"


"Godiya nake"Ta ce tare da ɗaukan jakar ya riƙo ƙugunta suka haura sama abinsu suna zantukan soyayya.





_JIGAWA STATE_

_GAGARAWA L.G_


Tafe ta ke a gefen titi sai sosa kan ta take tana dariya ita kaɗai, sanye take da kaya wanda suka yi wani datti kan ta babu ɗankwali gashin kan nata mai tsawo da yalwa ya bazo har gadon bayanta, ga ƙura da datti a jikin gashi da suk canja masa kama daga baƙi zuwa wani ja, kyakkyawar mace ce duk da yanayin jikinta ya nuna baya samu kulawa kasancewarta a cikin hali na hauka.


Ƙarasowa ta yi wajen wani maina inda mai shayi da kuma mai tsire a gefe da ma masu sayar da abubuwa da dama a wurin, tsayawa ta yi tana bi tana miƙa hannu a bata, da alama abinci take buƙata.


"Ke dalla kauce ki ba mutane waje sai kin je kin sakawa mutane wannan dattin jikin naki ko kim saka mana gashi kij kashe mana kasuwa"Cewar mai tsiren cikin zafin rai.Cikin sauri ta matsa dan har tsorata ta yi yadda ya zafice ta, tana tafiya tana waiwayen dan gani take biyota zai yi ya daketa, bata gani ba ta bige wa wata mai siyar da abinci kwanan miya ds yake ta tafi wurin wasu samari ta karɓo kwanukan ta da kuɗin, daga can ta hango mahaukaciyar ta mata ɓarin jar miya ai kuwa da cikin sauri ta taho tana zuwa ta sanya hannu ta damƙo gashin mahaukaciyar ta juyo da ita suka fuskanci juna da yake ita ko da ta ɓarar da miyar ma bata kawo aka ta yi wani abu ba da yake a halin rashin hankali.


"Wane ɗan iskan ya ce ki ɓarar min da miya?" Cikin tsoro mahaukaciyar ke kallonta tana tattakurewa, ai kuwa mai abincin nan ta ɗaga hannu ta ɗauketa da wani mari, cikin gigicewa ta dafe kuncinta tare da ƙoƙarin ƙwace kan ta daga gashinta da ta riƙe mata da hannu ɗayan, nan dai mutane suka taru wasu na bata haƙuri wasu na cewa bata kyauta ba tunda bata da hankali daƙer dai matar nan ta ƙyale mahaukaciyar bayan wani mutum ya biyata kuɗin miyar, sannan ya siyawa mahaukaciyar abinci a wurin wata aka zuba mata a leda dan sun ce ba za su bata a kwano ba.


Karɓar abincin ta yi ta juya cikin sauri dan dama yunwa take ji tun jiya rabonta da abinci, ƙarƙashin wata bishiya ta koma can nesa da mutane ta zauna ta bule abincin nan taliya da miya ce amma ba ruwanta da cakuɗawa haka ta shiga ci babu ƙaƙƙautawa wani sa'in ta ɗakko wurin miya wani lokacin kuma ta ɗakko inda babu miya, sai da ta cinye tas sannan ta kwanta a ƙasan wurin a take bacci ya ɗauketa.





Mmn afrah😍🥰😘

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️



NA


MAMAN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...


PAGE 1️⃣9️⃣&2️⃣0️⃣


_Jigawa state Dutse gadawur_


Gidan Alhaji Sagiru sarkin yaƙin Dutse, Alhaji sagiru ne zaune a bakin gado ya yi tagumi fa duka hannayensa, da alama dai ya yi nisa a cikin tunani sai dai shi kansa bai san takamaimai tunanin me yake ba.Kullum ya kan tsinci kansa a irin wannan halin idan har ya keɓance kansa daga mutane yana ji ya rasa sukuni yana jin damuwa da tunani sun addabi zuciya da ƙwaƙwalwarsa, amma kash sai dai baya taɓa tantance tunanin me yake, sai dai ya gaji ya haƙura da tunanin da ke addabarsa wani sa'ilin ma har sai ya zubar da ruwan hawaye sannan yake samun sauƙi a ransa.

Hajiya Suwaida ce tafe cikin wani tsadadden lashi da aka mata ɗinkin buba sai zuba ƙamshi take yi abinta, upstairs ta haura domin dubo mai gidan nata saboda ta ga shiru bai sakko ba.A hankali ta tura ƙofar ɗakin da ta san za ta sameshi, ta maida ƙofar ta rufe amma har ta ƙaraso cikin ɗakin da alama ma bai san ta shigo ba, inda yake kallo ta kalla sai ta ga idanunsa na kan wani ƙaton hotonsa da ke manne jikin bango, hoton an ɗaukesa ne a ranar da aka naɗashi sarkin yaƙin garin Dutse yanzu kusan shekaru ashirin kenan.Sanye yake da kufta da aka yiwa aikin irin na sarauta sai alkyabba da da aka ɗora akan kayan yana riƙe da sanda irin ta sarauta, ya kafe hoton da ido ga kuma idanun nasa sun masa jajawur.Yatsina fuska ta yi tare da taɓe baki, dan ta san zancen gizo baya wuce na ƙoƙi shi kullum yana tunani kuma in ka tambayeshi sai yace shi kansa bai san danuwarsa ba hasalima sai yace bai san me yake tunawa ba ita har gajiya take da tambayarsa.


Bakin gadon ta ƙarasa ta zauna, a kusa dashi amma har lokacin bai san tana wurin ba, hannu ta sanya ta dafa kafaɗarsa, shiru bao san tana yi ba har sai da ta ɗan jijjiga kafaɗar tasa sannan ya juyo a ɗan firgice.

"Hajiya" Ya kirata da ɗan ruɗewa a muryarsa saboda ya ɗan razana da ta taɓashi sanadin nisan da ya yi a cikin tunani.


"Na'am Alhajina, tunanin nan ne da har yanzu kake yi haba sarkin yaƙi mai takobin zinare kaifin takobinka zai sa kowa ya watse" Ta ce tana wani murmushi a fili a ranta kuma tana ayyana cewa ƙaryarka dubu ka tuno abin da kake son tunowa wannan ɓoyayyen sirri ya rufu har gaba da abada babu mai tunowa bare har ya fallasa.

Murmushi ne ya kuɓuce masa na kirarin da ta masa, duk da bai wani dawo daidai ba daga halin da ya shiga ba, dan har wani sarawa ya ji kansa na masa sannan yace


"Wallahi Hajiya ni kaina inason na daina tunanin nan amma bansan lokacin da yake zuwa min ba saidai in tsinci kainana ciki dumu-dumu"Ya faɗa yana dafe goshinsanda hannu.


"Ka yi haƙuri za ka daina ai da kaɗan-kaɗan zai barka tunda yanzu ba kamar da babya ragu"


"Ke kike gani ya ragu amma ni nasan bai ragubba saboda kullum sai na yi babu adadi, ni abin da ke damuna bai wuce ba rashin rashin sanin takamai man abin da nake tunawa ba sai dai fa in ƙari tunani amma tunanin nawa baya kaiwa inda nakeso ya kai saidai na gaji na haƙura"

Haka kwa za kake gajiya har abada dan babu wani abu da ƙwalƙwalwarka za ta tuna, saidai ka gaji ka haƙura, ta faɗi hakan a ranta a fili kuma sai ta ce

"Allah sarki Alhajina nima bana jin daɗin halin da kake kasancewa wallaho saidai dan ba yadda zan yi ne, amma ka yi haƙuri zaka daina watarana"

"To Hajiya Suwaida shi sa nake alfahri da kasancewarki mata ta"

"Ni ma ina alfahri da kasancewarka miji a gareni"

A haka ta lallaɓashi ya shiga wanka ya shirya suka sakko ƙasan tare, lokacin ma'aikatan gidan na ta hidima kowa ya kama aikinsa.


Alhaji sagiru ɗan asalin garin Dutse ne, kuma ɗa ne ga mai martaba sarkin Dutse, shi kaɗai iyayensa suka haifa sai ƙanwarsa da aka haifa a ranar ta mutu, yana da matar aure Hajiya Suwaida ita ma ƴar cikin garin Dutse ce sai dai Allah bai basu haihuwa ba.



Gidan Alhaji Sunusi


Hajiya Sakina ce zaune a falonta ta sanya kayan marmari a gaba sai tuffa a hannunta wanda ko gutsira bata yi ba, ta yi nisa cikin tunani sai tv da ke ta faman aiki.Hawaye ne ke kwaranya a idanunta amma saboda nisan da ta yi a tunanin ko share hawayen bata yi .

Hafeez ne ya shigo cikin falon sanye yake da t.shirt da wandon jeans baƙi sai ƙamshi yake abinsa.Da sallama ya shigo falon mahaifiyar tasa, amma kuma sai jikinsa ya yi sanyi ganin halin da ya tsinci mahaifiyar tasa a ciki, cikin sanyin jiki ya ƙaraso cikin falon har ya zo gabanta ya durƙusa amma bata ma san da zuwansa wurin ba.Da ido ya bi plate ɗin kayan marmarin da ke ajiye wanda tun lokacin da zai fita daga falon ya hangi Na'ima mai aikinsu ta fito daga kicin da ta yayyanka mata za ta kawo mata amma abin mamakin gashi har ya je ya yi wanka ya shirya duk ɓata lokacin da ya yi amma har yanzu babu wani abu da ta ci daga cikin kayan marmarin sai tunani da ta tsunduma, a ciki shi yasa kwata-kwata ba ya so ta kaɗaice ita kaɗai saboda yawan tunanin nan gudun kar ma ya yuwa lafiyarta illa.Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sanya hannu ya ɗan taɓa ta tare da cewa


"Ammi!"

Jin taɓa ta da aka yi da kuma sunanta da aka ambata shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta kai ziyara.

Dubanta ta kai ga Hafeez ɗin, sai kuma ta yi saurin kawar da kan ta gefe jin lemar hawayen da ke kan kumatun ta, da sauri ta ajiye tuffar a kan plate ɗin sai kuma ta sanya hannayen nata ta goge hawayen tare da ɗan jan hanci kaɗan sannan ta ƙaƙalo murmushi tare da cewa


"Hafeez wai kana nufin har ka yi wankan ka shirya, ko dai jiƙa-jiƙa ka yi baka fita ba shi yasa ka yi saurin fitowa" Ta ce cikin zolaya dan kar ya mata zancen halin da ya tsince ta a ciki, saboda ko da zai tafi wankan sai da ya sha lallaɓata akan dan Allah kar ta yi wannan tunanin, har da kunna mata tashar arewa 24 suna shirin mata a yau dan su ɗauke mata kewa amma shi ne ya dawo ya same ta dumu-dumu tana aikin nata da ta saba wato tunani.



" Haba Ammi

Please Login or Register in order to submit comment