Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hizbu yasa ya rufewa Abulkairi baki yana jin kamar ya hau shi da duka.

"Wai me yake skaa kake min haka ne ya za a yi macen dana fi ƙauna duk duniya bayan uwata ka ce bana ƙaunar...

Hannun da Iftihal ta ɗaga za ta ɗauke Hizbu da mari Abulkairi ya yi saurin damƙe hannun shi ya dakatar da Hizbu daga maganar da yake yi

MMN AFRAH






❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...





*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .


Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️



Page3️⃣1️⃣&3️⃣2️⃣




"Ridallah ni za ki mara?" Hizbu ya ce cikin mamaki yana ƙanƙance idanu, dan shi ganin abin yake kamar almara, yana gani wai Ridallah ɗinsa ce ke nuna bata san shi ba har tana ɗaga hannu za ta mareshi taɓɗi lallai akwai lauje cikin naɗi kenan dama ba son shi take ba? Kenan dama so ne na yarinta yanzu ta girma idanunta sun buɗe ta manta da shi ta barshi shi yana fama da tunaninta kullum cikin kallon ɗankunne da flower da ta bashi yake ba ya son ko kaɗan ya manta da ita ko da na second ɗaya ne dan yana ganin ya ci amana ya ci amanar ƙaunar da take masa da ma wacce yake mata baki ɗaya.

Kallon shi ta yi a raine tare da buga wani uban tsaki, ta fido wayarta da ke ta faman ƙara daga kiran ya katse sai wani ya shigo, tana dubawa ta ga Alhajin nan ranta ya ƙara ɓaci dan tana ganin duk shi ya jaza mata wannan bala'in da sun wucewarsu Hotel da duk haka bata faru ba yanzu gashi nan ya sanya wannan mai kama da mahaukatan yana kiranta da wani suna da bata ma taɓa jin mai irinsa ba.


"Ina jinka" Shi ne kawai abin da ta ce.



"Ya na jiki shiru ko dama baki taho ba?" Alhajin ya tambayeta daga ɗaya ɓangaren.



"Ka taho wajen hanyar fita ina wurin wani ya hanani tafiya" Ta ce dan bayan ta ɗaga wayar ma ta yi ƙoƙarin tafiya amma Hizbu ya janye Abulkairi daga gabansa ya je ya sha gabanta zai cigaba da jefa mata tambayoyi marar kai da ƙafafu.Tana kashe wayar ta kalli Hizbu cikin takaici ta ce



"Za ka gane shayi ruwa ne dan sai nasa an kulleka an koya maka karatun da baka da ilimi a kan sa tun da baka da hankali" Ta ce tana ɗauke idanunta daga kallonsa.



"Shikenan Rida na ji baki sanni ba kamar yadda kika nuna amma inaso ki faɗa min ina Baba take shin tana raye? a nan ƙasar take ko tana Nigeri'a?" Wani kallon baka da hankali ta masa ta ɗauke kai dai dai nan Alhajin ya ƙaraso dan ta tura masa hotonta yana hangota ya ganeta.

Babban mutum ne dan da ganinsa ma ya haifi Iftihal ɗin sanya yake da wandon jeans da riga mai dogon hannu sai wani uban ƙaton tunbinsa tari guda yana reto kana ganinsa kasan kuɗi sun sami wuri sun tare.



"Baby Iftee menene hakan me ke faruwaa ne?" Ya jefa mata tambayar idanunsa a kanta dan yana ganinta ya ji wata kasala ta baibayeshi, ganin irin shigar da ta yi mai bayyana surorin jikinta.


"Kalli wannan baƙauyen ne yake kirana da wani suna ya kafe dole ya sanni bayan ni ko a mafarki ban taɓa ganin ko da mai kama da shi ba" Ta kai ƙarshen maganar tana wani karkaɗa jiki dan Alhajin ya ji daɗin ɗaukan mataki.

Wani haushi da kishi ne suka turnuƙe zuciyar Alhajin lokaci guda ya kalli Hizbu da ya babbake a gaban Iftihal ya ce


"Malam halan daga turu ka fito ko? Ka taɓa ganin yadda ake niƙe mutum a maidashi dambun nama? To akan wannan yarinyar zan sanya a dandaƙa ka har sai cikinka ya haɗe da bayanka, dan haka ka fita harkarta ko a mafarki babu kai babu ita" Yana kai ƙarshen maganar yasa hannu ya hankaɗa Hizbu gefe guda sannan ya kama hannun Iftihal suka juya suka fara tafiya dan maimakon su shiga ciki hanyar fita suka nufa, ya maida hankalinsa kwacakwam kan ta ita kwa sai wani rausaya jiki take dan ƙara ɗauke masa hankali dan tana so ta samu kuɗaɗe masu yawa daga wurinsa dan Auntynta ta faɗa mata cewa ta tabbatar ta yi iya yinta dan ta wanki gara.


Hizbullah ganin Alhajin nan ya ƙara saka masa damuwa kenan Ridallah ta ma wuce inda yake tunanin wato shigar jikinta kaɗai da kuma yadda Alhajin nan ya kamata ya tabbatar da ta sanya kan ta a wata rayuwa dan da gani ba mijinta bane dn da mijinta ne da yace masa mai ya haɗashi da matar aure? Yana hango sun shige ƙofar ta rufo cikin hanzari ya fara taku zai bi bayansu dan yau sainya ga abin da ya turewa buzu naɗi ba zai taɓa barin Ridallah ba, taku ɗaya biyu Abulkairi ya yi ya damƙi rigarsa dan shi abin na Hizbullah ya fara bashi tsoro dan ya tabbata dai Ridallah ta fara masa gizo.Duk da dai bai taɓa ganin yarinyar ba ko a hoto bare ya ce ita ce ko ba ita ba ce dan Hizbullah memorinsa mai ɗauke da hotunansu ya faɗi a ranar da zai baro Nigeri'a dan haka yanzu ko hotonta bashi da shi, amma abin da ke baiwa Abulkairi mamaki me yasa bata taɓa masa gizo akan duk mutane ba sai akan wannan lallai akwai ayar tambaya tun da dai yarinyar bahaushiya ce alamu sun nuna ƴar Nigeri'a duk da a yadda Hizbu ke bashi labari ba ya jin yarinyar za ta yiwa Hizbu haka amma kaidin mata yawa gareshi kuma rayuwa da burika suna canja mutum.


"Ka saka ni kar su ɓace min"Hizbu ya ce cikin ɓacin rai.


"Haba abokina ka dawo hayyacinka mana me yasa kake hakane, shin ƙauna da tunanin Ridallah har zuciyarka ta fara ɗakko fuskarta tana ɗorawa a gangan jikin wata kana yiwa wata kallon Rifallah?" Abulkairi ya faɗa yana kama duka hannayen Hizbu da ƙarfi ya riƙe dan ya ga sai fisga yake yana so ya ƙwace ya bi bayansu.




"Abulkairi ka sake ni na ce idan suka ɓace min sai ka gwammace baka sanni ba"Hizbu ya ce yana zazzare idanu dan ya kasa ƙwace riƙon da abokin nasa ya masa saboda rauni da damuwar da ya tsinci kan sa a ciki sai ya ji gabaɗaya ƙarfinsa ma ya bar gangan jikinsa



*Gumel*


Ridallah har an shiga Senior secondry scul yanzu haja tana S.S 1 sun yi hutun first term dan haja yanzu tana gida hutu ake yi.Sanye taje da doguwar rigar jar atamfa an mata manyan fulawoyi baƙaƙe da la'asar sakaliya ne, share tsakar gidan take cikin nutsuwa.Sai da ta gama sharewa tas ta kwashe sannan ta wanke ƙafafunta da hannunta sai kuma ta je ta iza wutar da take dafa miya dan har ta gama tuwo, da ta gama wanke -wanke sai ta kwashe tuwon shi ne ta yi shara.

Ɗakinsu ta nufa inda Baba Habiba take dan iya Rahma ba ta nan ta fita unguwa gidan barkar haihuwa, zaune ta samu Babarta ta ta yi shiru shigowar Ridallah ya katse mata shiru da take yi.


"Wai Baba ko zafi bakya ji kin zauna a ɗaki ga tabarma can na shinfiɗa miki a inuwa ki fita kisha iska amma kin zauna a ɗaki kamar boka" Cewar Ridallah tana murmushi ta samu wuri ta zauna a kan katifar da ke lailaye da shinfiɗar wankekken zanin gado dan Ridallah ba dai tsafta ba komai nata tsaf gwanin sha'awa.


"Kawai dai na fi son zaman ɗakin ne"Baba ta faɗa cikin sanyin murya.



Ɗago kai Ridallah ta yi tana kallon mahaifiyarta ta dan kwata-kwata amsar ba ta gamsheta ba dan ba haka Babar ta saba mata magana ba musamman ma ta kan mata barkwanci su rinƙa dariya abinsu.


"Baba wai ko bakya jin daɗi ne yau tun safe nake ganinki cikin damuwa?" Ridallah ta ce tana matsowa kusa da Baba ta ɗora hannunta a kan cinyar Baba, hannu Babar ta sanya ta riƙo hannun Ridallah ta ce



"Ridallah babu abin da yake damuna, kawai dai wani lokacin na kan tsinci kai na a cikin damuwa idan na tuno da mahaifinki" Ta faɗa tana sanya hannu ta goge ƙwallar idanunta.Ita ma Ridallah ƙwallar ce ta ciko mata idanu jin maganar ta Baba ta sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi dan duk lokacin da aka yi zancen mahaifi sai ta tuna nata bare kuma aka yi magana a kan mahaifinta ta kan tsinci zuciyarta cikin rauni hakan yana tuna mata cewa ita marainiya ce ba ta mahaifi a raye dan ita ko a hoto ba ta taɓa ganin mahaifinta ba kawai dai ta san Baba ta ce mata kamarsu ɗaya da mahaifin nata babu abin da ta bari na mahaifinta to idan ta kalli kan ta a madubi ta hakan take ganin fuskar mahaifinta a jikin fuskarta.



"Ki yi haƙari Baba kawai mu cigaba da masa addu'a Allah lulluɓesa da rahamarsa"



"Amin Ridallah" Baba ta ce tana rungumo Ridallah jikinta cikin tausayinta dan ita ba wannan tunanin mutuwar bane kaɗai damuwarta akwai wata damuwar da ita kaɗai ta san da ita ko Ridallah ba ta san da hakan ba.





Haka dai Ridallah ta cigaba da lallashin mahaifiyarta a haka har Iya Rahma ta dawo lokacin dab da magriba ne ta kaɗa miyar sannan ta shinfiɗa musu sallayoyi akan tabarma ta ajiye musu carbinsu aka sannan ta wuce ta yi alwala.Bayan sun gabatar da sallah suka ɗore hirarsu har sai da aka yi sallar isha'i suka yi sannan Ridallah ta zubo musu tuwon su ka ci.


Haka suka yi hirarsu har wajen ƙarfe goma ganin an kawo wuta sai Ridallah ta sanya musu gidan sauro a ɗaki da yake ita Iya Rahma a nata ɗakin take kwana su kuma a ɗaki ɗaya, hakan ya sa ta shiga ɗakinta su ma suka mata sallama suka shiga nasu ɗakin.Bayan sun yi addu'a suka kwanta suna ƴar hirarsu har bacci ya yi awon gaba da su.


Cikin dare wasu samari guda uku suka diro daga saman katanga, sun tsaya suna ƙarewa gidan kallo.

"Baaba ka san fa ba mu san ɗakin da yarinyar take ba kar fa mu je ka hakewa tsohuwa" Ɗaya daga cikinsu ya faɗa yana kallon wanda ya kira da suna Baaba.

"Kai fa gara ne wa ya ce maka a duhu za a aiwatar dole ai a haska fitila kuma ko ma ba a haska fitila ba ai babu yadda za a yi na kasa banbance tsohuwa da yarinya sai ka ce wani kai" Baaban ya bashi amsa.


"Mu shiga nan ɗakin ka ga takalmi biyu da alama wannan ƙaramin na yarinyar ne ka ganshi na soso mai ɗan tudu" Ɗaya ma ya faɗa yana washe baki, gabaɗayan su suka bushe da dariya dan da alama ma ƴan shaye-shaye ne dan daga maganarsu ma ana iya fahimtar su waye su.

"Fito da bindigar nan" Ɗaya ya faɗa cikin raɗa-raɗa


"An gama Oga" Ya faɗa yana ɗaga rigarsa ya fito da bindiga daga inda ya soketa a ƙugunsa.

Karɓar ya yi ya jujjuyata a hannunsa yana dariya, su ma dariyar suka yi kafin suka ɗunguma suka shiga ɗakin da su Baba Habiba suke dan ƙofar buɗe take hatta da labulen a ɗage yake saboda zafi sai ƙaran fanka da ke ta aikinta suka sai baccinsu suke hankali kwance.

Da fitilar wayarsu suka yi amfani suka gano makunnar ƙwan ɗakin suna kunnawa kwa haske ya gauraye ɗakin, hango su Ridallah suka yi cikin net suna ta bacci Ridallah sanye da rigar bacci mai hannun shimi





An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment