Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mini"Iftihal ɗin ta ce tana dariya.Momma bata ankara ba sai jin ƙaran tafawar hannayensu ta yi alamar sun tafa dan jin daɗin halin da suke ciki.

Saurin sanya hannu ta yi ta rufe bakinta gudun kar aji ta dan abin da take saurara ya wuce hankali da tunaninta ace ƴarka ta cikinka ka zama sanadiyyar lalacewar rayuwarta sai ka ce a mafarki ko kuma a film, lallai zamanin nan da muke ciki ya ƙazanta ta ce a cikin zuciyarta.


"Ai sai kin zama abar kwatance a kaf faɗin Abuja sai an san da zamanki, ke bake ba ma hatta ni sai na yi sunan saboda za mu tara kuɗaɗen da za a yi ta kwatance da mu"Maganar Hajiya Hauwa ta katsewa Hajiya Azima tunani, a hanzarce ta bar ƙofar falon tare da baro part ɗin ma gaba ki ɗaya cikin tashin hankali dakyar take iya ɗaga ƙafafunta saboda sanyi da suka mata tana jin wani ƙunci da tashin hankali na maganganun da kunnuwanta suka jiyo mata.


"Hajiya Azima dan Allah kar ki ɓata bakin ki dan na gama yanke hukunci, babu wani abu da zan sauya daga haka" Muryar Abie ta dawo da ita daga tunanin da take.


Wani tashin hankali ne ya ziyarci Hajiya Hauwa tana ganin Alhaji Hamza zai datse mata hanyar samun maƙudan kuɗaɗen da take samu wanda shi ba zai taɓa iya bata su ba, dan idan har ya kai Iftihal China to haƙiƙa ya ɗauke mata jarinta dan ita yanzu bata ga wata sana'a ba da ke saurin kawo kuɗaɗe sama da wacce Iftihal ɗin ke musu.

"Iftihal ki tabbatar kin haɗa komai da zaki buƙata Safiya kuma ta shirya miki kayanki dan tafiya za ta iya kasancewa ko da wane lokaci"Abie ya ce yana kallon Iftihal da take ta zubar hawaye amma shi ko a jikinsa wai an tsikari kakkausa tun da ta sna wannan shi ne babban gata da zai mata.


"To Abie" Shi ne kawai abin da ta iya furtawa dan ta san dai ita a da tana ƙaunar karatu amma yanzu ko sh'awar shiga aji bata yi bare ya yi sha'awar ɗaukan karatu musamman yanzu da idanunta suka buɗe da samun kuɗi ta hanyar sai da mutuncinta da mahaifiyarta ce ummul aba'isin hakan tana ƙaramarta amma ta san bin maza amma ta san ba ta isa ta ja da amaganar Abie ba shi yasa ma ta aminci amma ba wai dan ranta ya so ba.


Hajiya Hauwa ce ta tashi buguzun-buguzun ta bar falon tamkar za ta tashi sama, tana fita ita ma Iftihal ɗin ta miƙe cikin sanyin jiki za ta tafi daga ɓangaren Abie.



"Kin dai ji abin da na gaya miki, kuma ki sani ko kin shirya ko baki shirya ba biza na fitowa za ki tafi" Maganar Abie ta katse Iftihal da ke bakin ƙofa za ta fita.


"Zan yi ƙoƙarin yin hakan kafin lokacin" Tana gama faɗar haka ta sanya kai ta fita.


Ran Momma fari tas jin wannan hukunci na Alhaji wai a hakan ma aho Alhajin bai san cewa Iftihal ɗin har maza take bi ba.Nan dai suka cigaba da yin hirar su dan yau Momma ce da girki yau Auntyn ta fita daga kwananta sai Momma ta karɓa, to dama a dinner ne da aka zo aka ci a part ɗin A bie shi ne ya ce idan an kammala yana da magana, shi ne suka tattaru a falon ashe da wannan maganar Abie ke tafe wannan kenan.


Iftihal na fita ta koma part ɗin Auntyn ta ɗakinta ta buɗe ta shiga, ta kwanta akan gado ta ɗakko wayoyinta har guda uku kowacce ta doshi 300k ta shiga waya da ƙawayenta na banza da suka haɗu a harkar bariki da kuma samarinta na wofi.



Hajiya Hauwa cikin fushi ta koma part ɗin ta, wayarta ta ɗakko cikin ɓacin rai ta zauna a bakin gado ta shiga laluɓo number ƙawarta aminiyarta Hajiya Suwaida, Hajiya Suwaida aminiyarta ce tun ta ƴanmatanci, Hajiya Suwaida ƴar garin Dutse ce da ke Jihar Jigawa sai dai tana zuwa Suleja hutu wurin ƴan uwan mamanta, to acan suka haɗu da Hajiya Hauwa suka ƙulla ƙawance da yake ta su ta zo ɗaya sai ƙawancen na su ya yi armashi har yanzu.

Har kiran ya katse ba a ɗauki wayar ba, ƙara kiran ta yi ranta baƙiƙƙirin kamar ta saki kuka ko ta samu sassauci.Wani kiran ta shiga doka mata har sai da ya kusa tsinkewa sannan ta ɗaga cikin murnar ganin aminiyarta ta.


"Aminiyata kin fi ta kowa" Cewar Hajiya Suwaida tana neman wuri ta zauna akan kujera dan fitowarta kenan daga bayi ta jiyo ƙaran wayarra ta shi ne ta zo domin kawo wa wayar ɗauki sai kuma ta tarar da kiran ma na aminiyarta ne.



"Suwaida dan Allah ki saurara ki jini wannan kiran ba na lafiya bane, akwai gagarumar matsala da ta tunkaro ni"


"Ikon Allah ya na ji muryarki haka? Allah sa dai ba sakin ki Alhaji Hamza ya yi ba zai tona mana asiri"


"Ba saki na ya yi ba amma abin ba ƙarami bane wallahi ina cikin tashin hankali"


"To ki nutsu ki mini bayani ko menene domin mu san yadda za mu yi mu shawo kan matsalar, dan babu wani abu da zai tunkaro mu face mun yi maganinsa"


"Wai Alhaji ne zai kai Iftihal karatu ƙasar Chaina, wallahi yana neman ganin bayan samun kuɗina yana kuma ƙoƙarin karya jari na"


Wani mugun wuntsilowa Hajiya Suwaida ta yi daga kan kujerar, sai ga ta a ƙasa tsabagen ruɗew da ta yi, dan duk tunaninta matsalar ƙarama ce sai ta ji girman matsalar na neman wuce gona da iri.

"Shi Alhaji Hamzan ne ya yanke wannan ɗanyan aikin, saboda shi bai san burinmu akan yarinyar ba"


"Wallahi kema dai kya faɗa amma hankalina ya tashi dan kin ga gabaɗaya so yake ya karya ƙudirinmu akan ta"


"Lallai kuwa dole a nemi mafita dan babh yadda za a yi mu haƙura da burinmu ya ma za a yi mu da bama ƙaunar yarinyar ta yi karatu shi ne zai wani ce har ƙasar waje zai kai ta ta yi karatu ba ma a Nigeri'a ba"


"Wallahi kuwa ni kai na duk ya kulle amma ki samo mana mafita"


Shiru Hajiya Suwaida ta yi tana nazari da tunanin yadda za ta samo musu mafita akan haka tun kafin haƙƙar Alhaji ta cimma ruwa.


"Yawwa akwai wata ƙawata a ƙasar China, ƴar nan Nigeri'a ce aiki ne ya kai mijinta China ina ganin za mu samu mafita a gunda dan itama shegiyar kan ta ce"


"Ta yaya? Kinsan fa shi Alhajin ya ce ba a makaranta za ta zauna ba, bare ki ce za a ruɗeta, ya ce gidan abokinsa zai kai ta"


"Mun shiga uku asirinmu zai tonu na samun kuɗi lallai da alama burinmu na zama hamshaƙan mata ba zai ciku ba"


"Ni ma shi ne damuwata wallahi da ace makaranta zai kai ta da mun samu mafita amma kuma gida ne zai kai ta"


Runtse idanu Hajiya Suwaida ta yi tana ta saƙa da warwara tana son gano mafita, can sai cewa ta yi.


"A Nigeri'a a ina abokin nasa yake ɗan wane gari ne?"


"Ɗan Kano ne...



"Haba dan Allah ya sunansa ina fatan ma ya kasance mijin ƙawar tawa dan ita ma ƴan Kano ne?"


"Sunansa Alhaji Sani Habu ana kiransa da...


"Ana kiransa da Soja" Hajiya Suwaida ta katse Hajiya Hauwa ta hanyar ƙarasa mata sunansa dan ta fahimci shi ne mijin ƙawarta Wasila da suka yi F.U.D anan Dutse.


Wani ihu mai ƙarfi Hajiya Hauwa ta sanya, jin am samo mafita.Ita ma Hajiya Suwaida sai wata dariya take ta mahaukata jin komai ya zo da sauƙi.


"Yadda za a yi zan kira ta mu yi magana nasan babu abin da zai gagara, in yaso sai a ɗora neman kuɗin a can Chinan a ɗora daga in da aka tsaya dan ai ko'ina ma akwai kalar mutanen da kake son rayuwa da u wla na banza wala na kirki" Cewad Hajiya Suwaida suna dariya cikin farinciki.



Haka suka ƙarƙare maganar su, cikin jin daɗi suka yi sallama akan cewa Hajiya Suwaida za ta kirata Hajiya Hauwa ta sanar da ita duk yadda suka yi da Wasilar haka suka yi sallama.

Sosai Hajiya Hauwa ta ji daɗin a ranta ta ajiye wayar tana furtawa a fili cewa

"In kasan wata ai baka san wata ba wallahi Alhaji da ni kake zancen mu zuba mu gani" Wayar ta ƙara ɗauka ta kira Iftihal ɗin cikin yan sakanni sai gata ta turo ɗakin ta shigo tana shigowa ta faɗa jikin Auntyn nata tare da sakin wani kuka.Bayanta Hajiyar ya shiga bubbugawa tana lallashinta har sai da ta samu ta yi shiru sannan ta shiga kora mata jawabi kamar haka.

"Ki daina kuka Iftihal babu abin da zai faru kuma ma gidan da zai kai ki na san matar gidan kuma ƙawar Hajiya Suwaida aminiyata ce dan haka ba za ki takura ba za ki yi duk abin da ranki ke so, dan kin san su dama maza ba mazauna gida bane bare ya takuraki shi abokin Abien naki.Hajiya Suwaida za ta kirata ta mata jawabi dalla-dalla.

Wani daɗi ne ya ziyarci zuciyar Iftihal ɗin ta rungume mahaifiyarta ta cikin farinciki dan dama ita a rayuwarta ta tsani takura bare yanzu da idanunta suka buɗe ba ta jinnza ta ɗauki kulle a gida kamar wata matar aure.Haka dai su ka yi ta tsara yadda komai zan kasance idan Iftihal ɗin ta je Chaina maimakon a gan su suna ɓacin rai sai aka ga saɓanin haka saboda aun riga sun samo mafita basu da matsala.

A ɓangaren Hajiya Suwaida ma ta kira Hajiya Wasila ta rattaba mata bayani, aikuwa ta ji daɗi dan dama mijin nata ya faɗa mata cewa abokinsa zai kawo ƴarsa ɗaya tilo gidansa domin ta yi karatu.Jin cewa kuma ƴar gidan aminiyar ƙawarta ce kuma ga ƙudurinsu kuma ita ma fama ƴar harka ce dan haka kwa suka ƙudurta neman kuɗi sai sun ga abin da ya turewa buzu naɗi.

Suna gama wayar Hajiya Suwaiba cikin azarɓaɓi ta kira aminiyarta ta labarta mata yadda suka yi, daɗi a wurin Hajiya Hauwa kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.




❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YATINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️




NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...




PAGE2️⃣5️⃣&2️⃣6️⃣



_Umma Sadiya_


Zaune take akan tabarma bayan magriba, Malam Auwalu ne ya shigo ɗauke da sallama amsa masa ta yi tana masa sannu da zuwa, zaunawa ya yi akan tabarmar ita kuma ta tafi ta kawo masa abincinsa tuwon masara da bushashshiyar kuɓewa.Ruwan da ta ɗakko masa a wata ƴar roba mai faɗi ya wanke hannayensa, miƙa masa ta yi ya yi Bismillah ya fara ci suna ɗan taɓa hora yana ta yabon daɗin da girkin ya yi.

"Wallahi lamarin yaron nan yana ɗaure min kai, duk da dai nasan halin da zai tsinci kan sa a ciki sanadin ɓatan su Ridallah amma yadda na ga ya ɗauki abin ya girmama kar abin ya taɓa karatun sa" Ta ƙarasa faɗa tana kallon Malam ɗin da ya dage sai cin abincinsa yake da alama daɗin ya wuce inda ake zato.

Sai da ya kai lomar ƙarshe ya ture kwanon da ta zuba masa a ciki gefe sannan ua wanke hannunsa da bakinsa ta miƙa masa ruwan da ta zuba masa a ƙaramin kofi ya karɓa ya sha sannan ya fara bata amsa.


"Duk maganganun ki haka suke amma sai dai babu yadda za a yi Hizbullah ya ki maida hankali a karatu sanadin damuwar da yake ciki, ke kan ki kin san halinsa baya wasa da karatu duk da yana da damuwa a ransa amma haka ba zai sanya ya yi watsi da abin da ya kai shi ba"


"Hakane Malam amma yadda ya damu ne abin ke tsoratani wallahi kullum fa sai ya kira ya fi a ƙirga yana tambayar an gan su ko an samu labarin su"


"Wannan duk ba wata matsala ba ce kuma ke kan ki kinsan irin yadda ya shaƙu da yarinyar a yadda ma ya yi ai ba ƙaramin yaƙi ya yi da zuciyarsa ba kuma kiran da yake yana tambaya kar ki ɗauka wani abu yana yin hakan ne da ya samu sauƙi da salama a cikin zuciyarsa saboda Allah kaɗai ya san yadda yake ji abin da nake so kawai mu ƙara dagewa da addu'a akan Allah ya bayyana su, kuma duk lokacin da ya kira ki rinƙa kwantar masa da hankali"

"Wannan haka yake, kuma insha Allah za mu cigaba da addu'a kuma zan cigaba da kwantar masa da hankali dan ya samu nutsuwa ya yi karatun"


"Yawwa to Allah mana jagora su kuma Allah bayyana su"

"Amin amin" Ta faɗa tana tashi ta shiga kwashe kayan da ya ci abincin.



_GAGARAWA L.G_


Tafiya take wasu dandazon yara biye da ita suna tafi suna mata waƙa.

"Mahaukaciya ta ɗan Bala,mahaukaciya ta ɗan Bala" Haka suke ta faman faɗa suna tafi suna dariya haɗe da tsalle-tsalle ita dai bata musu komai ba hasalima kamar ba da ita suke ba dan ita dama bata faɗa bare kuma yanzun da take tafiya kamar a gabaice ma take da alama wani abu na damunta, a daidai wata kwana kawai sai gani suka yi ta yanke jiki ta faɗi cikin razana da tsoro yadda suka ga ta yi yasa yaran ja da baya suna cewa.


"Ta mutu!!! " Suna ta maimaitawa, a guje duk suka fara watsewa suka barta anan yashe da yake layin babu mutane sosai shi yasa babu wanda ya gan su bare ya san mai ya faru.

Malam Idi mai almajirai ne tafe shi da wasu almajirai guda huɗu daga gonarsa suke suka yi aiki shi ne suka taso ganin magriba ta kawo kai, dan dama da yamma ne suka koma gonar saboda daman sun je da safe.Kwanar da suka shawo sai ganin mace suka yi kwance a ƙasa cikin hanzari Malam Idi ya yi kan ta tare da almajiran nasa, haka yasa almajiran suka kamata da yake matasa ne da ɗan girmansu kuma dama a layin gidan nasa yake.Haka yasa suka kai ta har cikin gida yasa matarsa Malama Zainab ta shimfiɗa tabarma da yake ita ma mace ce mai kirki ko yadda jikin mahaukaciyar yake bata ƙyamata ba bare ta ce ba za a ɗora mata ita ba akan tabarma.


Gabaɗaya Malama Zainab ta ruɗe da ganin mahaukaciyar dan duk tunaninta ma mutuwa ta yi, Malam Idin ne ya shiga kwantar mata da hankali akan ba mutuwa ta yi ba haka aka watsa mata ruwa Malam ɗin ya shiga tofa mata addu'a cikin iko da hikimar ubangiji sai ta kawo hankali.Tun da ta falka take ta bin su da ido, amma bata ce komai su kuma dama sun san mahaukaciya ce dan suna ganinta a layin duk da ba wata hauka tuburan take ba sai dai kana ganinta kasan tana da gushewar hankali.


Ganin alamomin yunwa a tattare da ita yasa Malama Zainab zubo mata abinci ta kawo mata, Malam Zainab na ƙoƙarin ajiye mata abincin sai ta sanya hannu ta warci kwanon abincin, cikin sauri ta sanya hannu tana ci hannu baka hannu ƙwarya, Malam sai jijjiga kai yake alamar tausayi Malama Zainab kwa ban da hawaye babu abin da ke zuba daga idanunta saboda tsabar tausayi da kuma ƙara godewa Allah da take da ya iyota cikin masu hankali lallai komai Allah ya baka yana daga cikin baiwar ubangiji.

Dan mutane da dama ba sa gane baiwa da ni'imar da Allah ubangiji ya musu ba wani kullum bashi da burin da ya wuce suke kallon wata ɗinbin dukiya da gidaje da tarin motoci da Allah ya baiwa wasu, suna mantawa da hatta lafiya da Allah ya basu babban arziƙi ne.Lafiya idan aka karɓeta daga bawa aka jarabceshi da rashinta, sai ki ga duk tarin dukiyarsa ya ƙarar da ita a neman magani amma lafiyar bata samu ba shi yasa idan Allah ya baka rai da lafiya to ka gode masa duk wani abun duniya samamme ne kuma ƙararre matuƙar kana da rai da lafiya da rufin asirinka ka ɗauke idanunka daga kan abin duniyar mutane Allah kai ma yana sane da kai wani ma abin da zai ci gagararsa yake amma kullum cikin godewa Allah yake Allah sa mu da ce.

"A gaskiya Malam sosai wani imani ya ƙara shiga ta ganin halin rashi na hankali da matar nan take ciki, lallai rai da lafiya, hankali ji da kuma gani su kaɗai Allah ya baka to ya baka babban kyauta! Duk da waɗan nan abubuwan da na lissafa abin tambaya ne ga duk wanda aka baiwa su" Ta faɗi hakan ƙwalla na cikowa daga idanunta ganin yadda mahaukaciyar ke cin abincin ko na bakinta bata cinyewa ba take ƙara tura wani.


"Wannan haka yake Zainabu amma mutane ba ma la'akari da hakan kuma wasu ba sa amfani da abubuwan wajen gyaran lahirarsu, suna duk abin da suka ga dama da su"

"To Allah ya ganar da mu gaskiya, ya bamu ikon amfani da baiwar da ya mana ta hanya mai kyau"


"Amin" Cewar Malam yana sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, tare da kallon mahaukaciyar da ta kammala cin abincin ta yi wurgi da kwanon, ta shiga waige-waige da alama ruwa take nema.

"Zainabu ki ɗakko mata ruwa "

"To Malam" Zainabun ta ce tana tashi ta ɗakko ruwan a wani kofi mai ɗan girma ta miƙa mata madadin ta sha ruwan sai kawai ta karɓa ta ajiye sai kuma ta sanya ƙafa ta ture ruwan ya zube gabaɗaya a ƙasa.Kallan kallo aka shiga yi tsakanin Malam da Malama Zainabu dan ita Malamar har wani tsoro ta ji ya ɗarsu a ranta, ita kuwa mahaukaciyar ko a jikinta ta tashi ta nufi randar da ta ga Malama ta kwalfo mata ruwa har ta buɗe sai kuma ta rufe da ƙarfi har murfin ya yi ƙara da yake wani farantin silba ne ƙarami aka rufe randar dashi.

Sai da ta je kan randar ta ƙarshe da yake randunan uku ne ta buɗe ta sanya kofin da aka kai mata ruwan da shi ƙasan sa ma akwai ƙasa haka ta dulmiya ta kwalfo ruwan da ta fito da hannun nata gabaɗaya ya jiƙe dan har hannun ta sanya a randar ta ɗakko ta kafa kai ta sha sai da ya ishe ta, sannan ta dangwarar da kofin a wurin ta juyo ta dawo inda ta tashi ta zauna. Su Malam dai kallonta kawai suke.

"Uhmmm Malam tun da ta warware kuma ta ci abinci dama ina ganin yunwa ce ta sanya ta faɗi, ai sai a nuna mata ƙofa ta tafi ko?" Cewar Malama Zainab tana kallon Malam ɗin da ya yi shiru kamar mai wani nazari.


Shirun dai ya yi bai bata amsa ba har sai da ta ƙara maimaita masa maganar sannan ya huro da iska daga bakinsa, sai kuma ya ce.

"Hakane Zainabu amma ba wai na ƙi ta taki bane sai dai ni ma akwai abin da nake hange wanda nake ganin kamar ke baki hango ba, inaso dan Allah ki bani haɗin kai mu riƙe matar nan a gidan nan" Ya ce yana kallon Malama da ta yi saurin miƙewa tsaye cikin kaɗuwa.

"Me kake faɗa haka Malam? Mahaukaciyar kake cewa ta zauna a gidan nan, haka kawai ba sanin halinta ba muka yi yo da Allah na tuba mahaukaci ma ai ba a saka shi a lissafi ba son ta je ta cutar da mu" Malama Zainab ta ce tana kallon inda mahaukaciyar ke zaune tana ta wani kurta layi da yatsanta a ƙasa sai wani maganganu take da baka gane ko fahimtar me ma take cewa.

"Haba Zainabu ya kamata ki fara saurarata ki ji manufata kafin ki yanke hukunci, kuma insha Allah za mu ajiyeta ne dan mu taimaka mata mun yi hakan da kyakkyawar niyya da yardar Allah babu abin da za ta mana"

"To ina sauraranka Allah kuma ya sa haka"Ta faɗa tana komawa ta zauna.

"Amin" Ya ce kafin kuma ya ɗora wata maganar.


"Hakiƙa Allah yana baiwa bayinsa baiwa haka kuma yana jarabtarsu ta duk inda ya ga dama, amma cikin iko da hikimar ubangiji na gano wani sirri tattare da matar nan, Allah ya bayyana tare da nuna mini wani ɓoyayyen al'amari a tattare da ita"


"Me kake so ka ce ne Malam" Malama ta katse shi.


"Inaso in ce miki wannan matar ba wai da haukar nan aka haifeta ba, asalima ba mahaukaciya ba ce daga baya abin nan ya sameta, tabbas akwai wani sihiri a tattare da ita" Malam ya faɗa idanunsa kafe a kan mahaukaciyar da zuwa lokacin kuma kawai ɗaga kai take yi sama tana saukewa ƙasa.

Ƙanƙance idanu Malama Zainabu ta yi ta kalli matar tana son gano abin da Malam ɗin y faɗa amma kuma bata ga komai ba dama ta yi zaton hakan dan tasan bata da baiwar da mijin mata yake da shi"Yanzu Malam kana nufin ka ce min matar nan da asali ba mahaukaciya ba ce, kenan ta taɓa zama da hankalinta?"

"Tabbas haka nake nufi, kuma na ƙudurci taimaka mata insha Allahu za a dace za ta dawo ras kamar bata taɓa yin haukar ba"

"Amin ya Allah, kai duniyar nan abin tsoro ce wallahi wannan wane irin rashin tsoron Allah ne da kuma son duniya za a mayar da mutum mahaukaci kawai yake yawo a gari kai Allah ka karemu sharrin mutum da aljan"Malama Zainabu ta ce tana jijjiga kai.

"Amin, ke dai bari rayuwar yanzu sai a hankali"

"To Allah tayamu riƙo ya bata lfy"

"Amin, yanzu abin da nake so da ke wancan ɗakin da ake sanya kayayyaki, za a kirawo almajirai guda biyu ko uku su kwashe su haɗa a ɗaya ɗakin, sai a gyara mata ta zauna a ciki"

"To Malam, amma wani hanzari ba gudu ba kan ganin za ta yadda ta shiga ɗakin kwa?"

"Eh za ta shiga yanzu kafin su gama gyarawa akwai wani magani da zan yayyafa mata a jikinta zai taimaka wajen shigarta ɗakin"

Da "to" Malama ta amsa masa.

Kafin meye wannan almajiran Malam sun shiga gyara ɗakin, ita kwa mahaukaciyar tana nan kwance a inda take da Malam ya watsa mata maganin anan ta ɓingire tana bacci, har sai da ɗaki ya zama tsaf sannan aka shimfiɗa tabarma da ƙaramar katifa, tana falkawa Malama Zainab ta nuna mata ɗakin cikin ikon Allah kwa babu abin da ta yi kawai shiga ɗakin ta yi ta zauna tare da miƙe ƙafa duk da baccin dama ba wani isarta ba ya yi da alama, ɗakin kawai take bi da kallo.


_Bayan sati biyu_


Jiki ya yi kyau sosai dan har sai da Malam ya mata addu'a ya kafeta a cikin gidan dan gudun fita saboda tana ta yunƙurin a barta ta fita, yanzu ma duk haukar ta yi sauƙi sai dai ta zauna ta yi shiru, ko aiki Malams Zainab take a tsakar gida sai ta fito ta zauna a ƙofar ɗaki take ta bin Malamar da ido duk inda ta yi.

Yanzu jikinta ma fes yake saboda hatta kan ta sai da Malama Zainab ta wanke mata shi ta gyara mata ta tufke mata, saboda ta fahimci bat son kitso da an kama kan sai ta rinƙa jijjiga kai alamar bata so.Kayan Malamar ne yanzu ma a jikinta dan har wanka take mata sosai sauƙi ke samuwa shi kwa Malam kullum ciki haɗa rubutu da maganin ita ce gashi yana jin daɗin yadda Zainabun ke yiwa matar ba kyara ba tsangwama.






❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YATINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️




NA





Please Login or Register in order to submit comment