Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...




PAGE2️⃣7️⃣&2️⃣8️⃣



_Ridallah_


Karatu ya kankama sosai ta maida hankali a karatun ta dan yanzu duk class ɗin nasu babu wacce ta fita ƙoƙari Malamai har mamakin irin ƙoƙarinta suke saboda iliminta har nema yake ya zarce ajin da take.Ko yaushe cikin nazari da duba litattafai take babu ruwanta da shirme ko biya ƙawaye ƙawarta gida ɗaya Anisa Bello ƴar garin Dutse ce ita ma yarinya ce mai ƙoƙari da hazaƙa shi yasa ma tasu ta zo ɗaya da Ridallah.


Shugaban makarantar shi ne ya mata siyayyar madara cornflakes da makamantan su, tabbas Principal ya yi musu alkairi da ba za su taɓa mantawa ba saidai Allah ya biyashi. Baba da inna Rahma suka mata sauran siyayyar kayan yaji da mai da sauran abubuwan buƙata yanzu ta zama ƴar makaranta, hankalinta kwance dan kullum sai ta ga su Baba hakan ke sa ta ji kamar ma ba boarding school take ba.


Da yammaci ne garin ya yi luf kamar akwai haddiri saboda lillimi da ake yi, zaune suke a ƙarƙashin wata bishiyar maina suna kan sallayar da suka shimfiɗa ga litattafan da suka ɗakko nan domin yin karatu, saidai Ridallah ta buɗe nata littafin a zahiri idan ka ganta zaka ɗauka karatun take amma a baɗini ba wai karatun take ba kawai dai tana kallon littafin ne amma ko rubutun bata iya karantawa sai hoton Ya Hizbullah kawai take gani yana mata murmushi hakan yasa idanunta suka ciko da ƙwalla saboda kwana biyun nan sosai tunaninsa ke addabarta tana ta ƙoƙari ta yakice tunaninsa da son ganinsa daga zuciyarta amma hakan baya samuwa.Anisa da ta ga wani wuri bata fahimta ba a cikin littafinta tana so Ridallah ta mata bayani ta ɗago tana mata magana tare da nuna mata rubutun. Amma duk maganar da take mata bata ko da kalli inda take ba bare kuma ta san ran za ta bata amsa.


Sororo ta tsaya tana kallonta ganin hawaye na ɗiga a kan littafin da ke hannunta, hannu ta sanya ta taɓota, figigit ta yi tana kallon Anisa tare da sanya hannu ta goge hawayenta.


"Haba ƙawata mai yake damunki ne haka har da kuka, ko Babanki kika tuno da ya rasu?"


"Allah sarki! Addu'ar da nake yiwa Babana ba ta bari na masa kuka, sai dai kawai idan na tuna da Yaya na ina jin a jikina yana can cikin damuwa kamar yadda nake jin damuwar rashin sa"


"Dama kina da Yaya amma baki taɓa bani labarinsa ba? To yana ina?"


"Ya Hizbullah ba iyayen mu ɗaya ba, maƙotanmu ne sai dai na shaƙu da shi yadda bakya zato"


"Allah sarki ! Amma wata rana zai zo ki daina damuwa ki maida hankali muke karatun mu"


"To shikenan nagode" Ridallah ta ce tana goge hawayen nata, ta nunawa Anisa inda bata gane ba suka cigaba da yin karatunsu abin sha'awa dan basu da wata damuwa kuma ma da yake su ƴan J.s 1 ne babu mai takura musu komai ma musu ake barw da aka san Ridallah akwai mahaifiyarta a makarantar ba a takura mata ga kuma an ga Malamai da Shugaban makarantar suna ji da ita saboda ƙwazo da kuma girmama mutane.





_Aunty_


Gobe ne jirgin su Iftihal zai ɗaga zuwa ƙasar Chaina ita da Abie za su je idan ya kaita akwai wani abu da zai gabatar sai ya dawo.Dan haka sai shirye-shirye ake tsakanin uwa da ƴa, saboda tsabar dabbanci irin na Auntyn har kayan mata ta haɗawa Iftihal ɗin domin ta gyara kan ta na kasa gane Aunty wace irin uwa ce da ta zama mabuɗin lalacewar ƴarta da hannunta saboda aon abin duniya. Ita kuma Iftihal saboda Auntyn na nuna mata wannan ita ce hanya mai ɓullewa hakan yasa take ganin kamar daidai ne ga kuma uwa uba yarinta da ke damunta ga rashin ilimi hakan yasa ta kasa gane gaskiya kamar yadda mahaifiyarta ta kasa ganewa.


Dama tun anan tana bata kayan mata tasha domin Alhazan da ke nemanta su ke bata kuɗaɗe marar misali su kuwa da yake ƴan akuyoyi ne haka suke more yarintarta da kuma kayan matan da ke ƙara musu armashin wajen yin saɓon Allah, Allah ka tsaremu ka tsare mana zuri'a baki ɗaya amin.Komai ta sanya mata a jakarta sannan ta ƙara koya mata abubuwan da za take ɗauke hankulan maza dan haka sai da ta shirya komai sannan kuma sun yi magana da Hajiya Suwaida akan Hajiya Wasila za ta ɗora daga inda aka tsaya.


Washe gari haka su Aunty suka raka su Airport basu dawo ba har sai da suka ga tashin su, sosai Aunty ke cike da farinciki dan tana ganin wannan wani cigaba ne da ya shigo rayuwarsu tabbas tana ganin nasara yanzu a duk abubuwan da ta sanya a gaba bata ganin duhu saidai haske!.



Sun sauka a Chaina lafiya, a inda Alhaji Sani da da Hajiya Wasila suka je taryensu Airport ɗin, sun yi murnar ganinsu saboda sun ga yarinya kyakkyawa duk da ita Hajiya Wasila haihuwarta biyu amma sun rasu sai ƴar mijinta da take a hannunta ita ma kuma ba wai tana mata riƙo bane na tsakani da Allah, ita ma ta maida yarinyar jarinta ba tare da sanin uban ba.Sun ƙaraso gidan a inda aka nunawaSun ɗakkosu sosai Amal ke murna ganin ta samu ƙawa sai janta take da hira da yake motoci biyu suka je da su ɗaya mai gidan ne a baya direba yana jan sa, sai Abie ya shiga baya, ɗayar motar kuma Amal ce a gaba sai Hajiya Wasila a baya ita da Iftihal ta kwantar da Iftihal ɗin a gefen kafaɗarta murna fal ran Hajiya Wasila da ta ga Iftihal ɗin ganin tsantsar kyau kamar ita ta yi kan ta ko ina a cike hakan yasa take hango ɗinbin nasara a tafiyar tasu dan ta lura tabbas yarinyar za ta kawo haske sosai sama da hasken da ta samu a tafiyarta da Amal tun da tana ga manyan mutane sun fi son ƙananun yara a Barker bariki hakan ya kan sanya su fitar da kuɗaɗe dan biyan buƙatarsu.



Iftihal sai ƙarewa ko ina kallo take tana mamakin yadda kowa yake sabgar gabansa ba tare da ya damu da kowa baDuk da cewa ba wannan ne karonta na farko ba zuwa China amma lokacin da ta taɓa zuwa tana ƙatama sosai suka zo, shi yasa bata iya tuno komai game da ƙasar dan ko umra ma da suka taɓa zuwa yanzu ba z a ta ce ga yadda saudiyya take ba shi yasa yanzun ma take ganinta a China kamar a cikin mafarki.Ta shagaltu da ganin garin sosai har dai suka ƙaraso gidan Alhaji Sani Habu ƙayataccen gida ne dan haka irin tsarin ginin ya burgeta, tun tsayuwar motocin mai gadin yana buɗe get ɗin ta shiga ƙarewa gidan kallo dan lokacin da ta taɓa zuwa China a Hotel suka sauka kuma ko ma a nan gidan suka sauka to babu abin da za ta iya tunawa duk da yanzun ma ba wani girma gareta na azo a gani ba amma dai tana jin kan ta kamar yadda kowacce mace ke jin kan ta.


Part ɗin da aka sauki Abie da ban ita kuma Amal ta kai ta wani ɗakin da ke ɗauke da komai na buƙata, bayan ta ɗana watsa ruwa ta shirya Amal da ke zaune kan gado tana ta danna waya ta kalleta ta ce


"Masha Allah rigar nan da kika sanya ta matuƙar miki kyau kamar dama dan ke aka ƙerata"

Tsayawa Iftihal ɗin ta yi, tana bin Amal da kallo kafin daga bisani ta ɗan yatsina fuska cikin halin ko in kula ta ce


"Thanks"

Murmushi Amal ta yi dan ita har ran ta take jin ƙaunar Iftihal dan haka bata ga laifinta ba.


"Ya gajiyarki"

"Bani da gajiya"

"Haka ake so"

Wayar Amal ce ta ahiga ruri tana dubawa ta ga Mummy, ɗauka ta yi.


"Ku fito aci abinci" Ta tsinkayi muryar Hajiya Wasila.


"To Mummy gamu nan fitowa" Tana gama faɗin hakan Mummyn ta katse wayar kallonta ta maida kan Iftihal da ke gyara ribbon ɗin kan ta ta ce

"Mummy ta ce mu je mu ci abinci"

"Okay" Ta ce tare da miƙewa tsaye tana ɗaura ɗankwalin doguwar rigar a kan ta, ta kama hanyar ƙofa Amal ta bi bayanta suka fito. A dinnig area suka samu gabaɗaya mutanen gidan har da Abie kowacce kujera ta ja ta zauna kowa ya zuba abin da yake so Mummyn kuma ta zubawa su Abie itama ta zuba nata aka shiga cin abincin, bayan sun kammala Abie da Daddy Alhaji Sani suka fita domin su ɗan zagaya gari sai murna suke domin sun ɗan kwana biyu basu haɗu ba.Suna fita Mummy ta kira su Iftihal ɗin falonta ta shiga kora musu bayani kamar haka.


"Amal ga ƙawa nan kuma ƴar uwa inaso ku zama tamkar abu ɗaya, bana so wani abi marar daɗi ya shiga tsakaninku dan sai kun haɗe kan ku sannan komai zai tafi kamar yadda nakeso na tsara" Cewar Mummy tana bin dukkanninsu da kallo.


"To Mummy insha Allah babu wata matsala da za a samu dan ni tun da na ganta na ji ta shiga raina sosai" Amal ta ce tana murmushi.

"Yawwa Amal haka nake son ji"Mummy ta ce tana maida hankalinta kan Iftihal da babu alamun za ta ce wani abu ta lura yarinyar ƴar rainin wayo ce kuma da ganin idonta ta wanke a bariki dan kar take kallon mutane.


"Babu abin da zai haɗamu"Iftihal ta ce tana maida hankalinta kan wayarta.Shiru ne ya ɗan biyo baya Mummy kuwa a ranta tana cewa

"Yarinya za ki shigo hannu ne, dole na moreki tun da a hannu na za ki zauna dole na samu kuɗaɗe ta dalilinki.


"Mummy ina son na ɗan huta" Amal ta ce cikin girmamawa, dan dama Amal yarinya ce mai biyayya duk da yanzu Mummy ta yi nasara wajen kassara mata rayuwa ba tare da sanin mahaifinta ba amma dai ha yanzu tana girmama na gaba da ita.


"To Amal ku je maza ku huta "Mummy ta ce tana murmushin yaƙe, haka suka tashi suka juya suka bar falon Mummy na bin su da ido tana girgiza kai tare da yin ƙwafa.




Sati guda Abie ya yi ya dawo Nigeri'a dan sai da aka gamawa Iftihal komai da komai na makaranta sannan ya taho dan har lesson teacher aka ɗaukar mata dan yake koya mata karatu a gida saboda duk babu abin da ta iya saboda rashin halartar makaranta da ba ta yi. A makarantar da aka sanyata ma ta su Amal da ƙer suka yarda suka sanyata a J.s 1 shima dan su Abie sun ɗan musu magiya akan za su ɗaukar mata da wanda zai ke koya mata a gida dan da suka mata interview duk ba ta ci ba, gashi kuma duk ta fi ƴan sauran ajijiwan bayan girma da yake tana da girman jiki doke dai haka aka sanyata a J.s 1 ɗin.


Tun da Abie ya tafi shi kuma Daddyn Amal ya koma wurin aiki dan dama shi baya dawo wa daga office sai magrib in ya fita tun safe, hakan ne ke baiwa Mummy damar cin karenta babu babbaka.Dan haka yanzu ma ta cigaba da nuna musu hanya marar ɓullewa sai yaran suka ɗora daga inda suka tsaya dan dama kowaccen su ta tsufa a harka yaran ƙanana da su amma an ɓata musu rayuwa, sosai suke samo kuɗaɗe wanda Mummy ke haɗasu da manyan mutane suke sheƙe ayarsu, idan suka basu kuɗi sai ta ɗauki kasonta ta basu nasu sauran kuma ta aikowa Aunty su raba da ita da ƙawarta Hajiya Suwaida sosai Auntyn ke siyan kadarori da kuɗaɗen tana jin daɗin irin yadda harkar ke tafiya dan koyaushe idan suka yi waya da Iftihal sai tana jaddada mata akan ta maida hankali wajen janye ra'ayoyin abokan tarayyarta dan dama batun karatu ma ba ta shi suke ba duniya ce kawai a gaban su.Shi kwa Daddy bai san wainar da suke toyawa ba bare kuma Abie da ke can hankalinsa kwance yana ganin ƴarsa tana can tana karatu da yace ko hutu aka yi ba za ta zo ba sai dai su je su gan ta dan baya so ta zo Aunty ta tsiro da wani abun da ban.

Mummy hatta mai lesson ɗin da aka ɗaukarwa Iftihal ta ja masa kunne akan kar ya kuskura ya faɗawa Daddy cewar ba a karatun sai take bashi kuɗi ta toshe bakin, dan Aunty ta ce ko mai koya musu karatun addini ma da ake koyawa a maƙota Daddy yace suna zuwa dan kamar islamiya ce wata mata take koya musu karatu amma haka suka hana yaran zuwa, ni kwa na ce Allah wadaran naka ya lalace.






❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...





*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .


Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️



Page 29-30


Haka rayuwar Iftihal da Amal ta cigaba da kasancewa cikin ƙazantacciyar rayuwa kullum idanunsu na buɗewa ashe mai makarantar da aka sanya Iftihal ɗin ma inda acan aka sanya Amal ita ma dai da ba zuwa take ba ba a ce makarantar su ba shi ma ɗan hannu ne dan haka suna lasa masa zuma a baki hakan yasa ya rufi bakinsa bai taɓa sanar da Daddy cewa basa zuwa makaranta ba sai dai akwai ranar tonon asiri.


*Bayan shekaru uku.*

Iftihal girma ya ƙaru kai ya ƙara fashewa idanu sun ƙara buɗewa, ta ƙara zama babbar yarinya kuɗi ya zauna, dan yanzu hatta motar da suke yawo a ciki wacce Daddy ya siya musu sun canja ta, amma Daddy kamar ma bai sani ba dan yanzu da Mummy ta sanar da Aunty yana neman ya harbo jirginsu sai suka sanya aka rufe masa baki ruf daga shi har Abie ɗin dan haka ynzu babu wani ɓoye-ɓoye dan babu wani abu da ya isa ya yi, iya shekarun nan da ta yi Abie bai ƙara ziyartar ta ba sai dai Aunty ta zo ita ma dan ta kawo musu kayan mata na gyara dan hatta zuwan ma Abie riƙe masa ƙafa aka yi.Momma ce dai ke ta addu'a domin tana lura da komai da yake faruwa sai dai bata tantance me ke faruwa a Chainan ba, amma dai rashin gaskiya ya bayyana a tare da Aunty da kuma irin maƙudan kuɗaɗen da take fantamawa da su, har mota gareta amma gamin Abie ma bai kawo komai ita ma ta ja nata bakin ta yi shiru dan akwai lokacin da ta ce za ta bi Auntyn China domin su gano Iftihal ɗin amma Auntyn ta mata gori akan cewa ba ƴarta ba ce ta bari idan ta haifi ɗiyarta ta je amma ba Iftihal ba hakan yasa Momma ba ta ƙara cewa za ta bita su kai wa Iftihal ɗin ziyara ba.



Sanye take da wasu fararen kaya riga da wando wandon ya matuƙar kama mata jiki, sai dogon takalmi mai tsini, babu ɗankwali a kan ta sai dai gashin nata ya sha gyara sai sheƙi yake jelar gashin na reto a gadon bayanta.Idan ka kalleta ba zaka taɓa zaton ta haɗa iri da Hausawa ba bare kuma ka yi tunanin tana ɗaya daga cikin musulmai.A dai dai ƙofar da za ta shigar da ita ƙayataccen Restuarant ɗin ta samu wajen da aka tanada dan yin parking ɗin motoci ta faka motarta kiɗa sai tashi yake tamkar dai motar za ta taka rawa saboda yadda ƙaran bugun kiɗan ke ɗawainiya da motar.


A hankali ta buɗe ƙofar motar cikin yanga da aji tana wani yatsina fuska, bayan ta sanya glases ɗinta ta kashe motar ta ɗakko ƙaramar jakarta, ƙafafunta ta sanyo su ƙasa ta fito tana ɗan bin wajen da kallo kafin ta maida ƙofar ta sanya makulli ta kulle motar.Jakarta ta rataya kafin ta fara takun ta cikin izza da jan hankali, taku ɗaya biyu ta yi wayarta ta shiga ruri tana neman agaji har kiran ya katse bata ma fito da wayar daga jakar ba, sai a karo na biyu da kiran ya sake shigowa ta fiddo wayar sunan Alhajin da Autynta ta turo mata no sa ta gani, daga Nigeri'a yake ya zo ganin likita China shi ne suka yi magana da Autynta akan zai je wurin Iftihal ɗin su haɗu, sunan Restuarant ɗin ya tura mata tare da mata kwatance ashe ma ta san wurin shi ne za su haɗu a nan kafin su gama daidaitawa su wuce Hotel.

Bayan ta ɗaga ya faɗa mata ɓangaren da za ta sameshi, wayar kawai ta kashe ba tare da ta bashi amsa ba, ta nufi ƙofar domin shiga wurin domin ba ƙaramin wuri bane.





" Akwai ƙofa daga damanki ki shigo zaki hangoni zaune wurin bishiya"Ta tsinkayi muryar Alhajin da ya ƙara kiranta waya.Wani haushi da takaici ne ya kama ta wato ma ba cin abincin zai yi ba yana can ciki da yake wurin daga can ciki sai aka ware wurin hutawa haka dai da ƴan shuke-shuke a wurin, wato ma ya ɗauketa wata bagidajiya irin bata san wurin ba har wani kwatance yake mata, ƙwafa kawai ta yi a ranta ta kashe wayar ba tare da ta bashi amsa ba, kai tsaye ta turo ƙofar gilashin ta shiga wurin mutane ne gasu nan birjik suna cin abincin wasu kuma yanzu ake kawo musu abincin kowa dai yana sabgar gabansa.

Cikin takunta ta shigo wurin direct wurin wani farar fata ta nufa ta miƙa masa kuɗi ya ɗauki wata takarda ya yi signing a jiki ya miƙa mata tana karɓa ta juya ta buɗe ƙofar nan ta shige.

Zaune suke akan kukeru a can ƙasan wata bishiya hira suke taɓawa jefi-jefi dan kwata-kwata Hizbullah ba ya son yawan magana, Abulkairi ne ke masa hiran shi kuma iyakarsa "Eh, a'a, hakane"


"Wai Hizbullah kai wane irin mutum ne dan Allah, ya kamata kake sakewa da ni ko da ba za kake sakewa da wani ba, saboda ni abokin ka ne amma kullum da ka saurareni mu yi magana ka gwammace ka rinƙa tunani?"


"Ba haka bane, dama can ni ban fiye son yin magana sai in dai da Ridallah ne, ya kamata ace ka fahimci bani da yawan magana a iya zaman da mu ka yi na shekaru"


"Hakane ni ma na fahimci hakan amma dai a ƙalla kake magana akan shiru dan shiru na haifar da illah ga lafiyar ɗan adam"

"To zan ƙoƙarta in ke yin hakan amma abin da ya ƙara sanyani na ƙara zama shiru-shiru tin hutun da na je gida na ƙara tabbatar da cewa Ridallah ta ɓata babu labarinsu tun daga nan na ƙara jin bana jin daɗin komai wallahi"


"Maganarka hakane ka ga ko lokacin da ka je Kano ka kai min ziyara lokacin da mu ka je hutun na ga ka rame akan zuwanmu, kuma ni ma da na je Haɗejia na kai maka ziyarar na ji Umma na cewa nake maka faɗa ka canja hali daha shiru-shirun nan kake sakewa a jama'a"


"Ai ita Umma ko yaushe laifina take gani, tana tunanin kamar da gangan nake sanya kaina a damuwa bata san ba abin daga zuciyata ya...

Shirun da Abulkairi ya ji yasa ya ɗago kai yana kallon Hizbullah domin ya ga abin da ya katse masa maganar ya kasa ƙarasawa, ai kuwa yana ɗagowa ya yi tozali da Hizbullah ya miƙe tsaye daga zaunen da yake ya maida hankali ga kallon wani waje bakinsa a buɗe.Hizbullah kwa hangota da ya yi shi ne abin da ya dakatar da shi daga maganar da yake ya miƙe tsaye yana hangota tana nufowa inda suke, fosta ya yi dan hatta numfashinsa ji ya yi yana barazanar barin gangar jikinsa saboda ɗimaucewa da kuma wani mugun bugawa da zuciyarsa ke yi da ƙarfi kamar ya yi tseran gudu na kilo miter masu yawa.Idanunsa kwa ko ƙiftasu ba ya yi har ruwa taruwa ya yi a cikinsu dan ba ya so ya ƙiftasu ya nemeta ya rasa duk da yana ganin kamar a mafarki yake ganinta.
Abulkairi dai ya tsaya shi ma cikin mamakin abokin nasa sai ya kalli Hizbullah sai ya juya ya kalli wacce ya ga Hizbullah ɗin na kallo cikin tsantsar ruɗewa, abin da ke baiwa Abulkairi mamaki wacce Hizbu ke kallo mace ce kuma Hizbu maza ma bai damu da kallonsu ba bare wasu mata ma da ya tsani zancen mace in ba zancen Ridallah ba ko na Ummarsa ba dan ko Abulkairi na yiwa Hizbu zancen tasa budurwar Bilkisu sai ya ce shi fa ba ya son surutu amma yau shi ne ke kallon mace ba Ridallah ba macen ma wannan mai kama da arnan dan gabaɗaya jikinta babu alamar da za ta nuna akwai muslunci a tare da ita.


Tana dab da ƙarasowa saitin inda suke Hizbullah ya dawo daga shork ɗin da ya shiga, cikin zafin nama ya tafi gareta yana zuwa kawai ya sha gabanta cikin wata iriyar murya ya fara magana.


"Ridallah dama kina raye? Ya aka yi kika zo ƙasar nan? Yaushe kika yi watsi da tarbiyarki kike irin wannan shigar Ridallah, yanzu ace ko tunani na ma bakya yi kin manta da ni ina nan ina cikin damuwar rashin sanin takamai man inda kike, a raye ko a mace amma kina nan lafiya ƙalaw hankali kwance kin...


"Wai ƙwalƙwalwarka ta taɓu ne? Ya daga ganin mace ka zo kana mata wasu surutai cikin gushewar hankali, shin ka manta ba a Nigeri'a kake ba? Ko kuwa wannan ta maka kama da bahaushiya dan Allah ka rufa mana asiri Hizbu" Abulkairi da ya ƙaraso gabansu ya ce yana bin Hizbu da kallon takaici, ita kwa Iftihal da ta langaɓar da kai gefe idanu kanne fuska a yatsine dan ita takaici ne ma ya hanata magana dan tana jin komai su ne ke mata kallon kamar ba bahaushiya ba.


"Wai ni kake yiwa eaɗannan maganganun? Shin ka ɗauka bana cikin hayyacina to Ridallah ce wannan kuma ni nasan tana jin hausad shi yasa ka ga ina mata magana, kai...

Ƙaran wayar Iftihal ɗin ne ya katse Hizbu daga maganar da yake ƙoƙarin ƙarasawa.Kallonsu ta yi tare da banka musu wata uwar harara kafin ta buɗe baki ta ce


"Dallah malamai ku ja jikinku a nan, ko an faɗa muku nan ma Nigeri'a ce inda kuka saba yaudarar ƴanmata to ko a Nigeri'a ai na wice ajinku da gani ma wannan gwabnati ce ta biya muku karatu kuka samu damar ketowa hazo"

Ta faɗa tana gyara glases ɗin fuskarta.Baki sake Abulkairi ke kallonta jin hausa a bakinta kamar jakin garinsu Kano dan bai taɓa tunanin ta san inda hausa ma take ba ganin hasken fatarta da kuma yanayin shigarta duk da musulman ma na irin shigarta a nan ɗin ma amma ko hula suna sanyawa su rufe kan su ko ɗankwali amma ita haka gatsal kamar inyamura.

"Au bahaushiya ce ke ashe, to koma menene waye ma zai so mace irinki ko a ƙafa aka ɗaura mana ke sai mun kunce, shi ma wannan dan bashi lafiya ne amma mai zai yi da ke ba zia taɓa ƙaunark...Hannu

Please Login or Register in order to submit comment