Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mayar da gaba ɗaya hankalinsa gare su musamman ma Alhaji Nakowa.



"Lokaci yana ja cikin lokaci ƙanƙani shekara ɗaya tana neman zagayowa da hakan ke nuni da lokaci ya kusa a ƙiyasina bai fi nan da kwanaki ashirin da Takwas ba komai zai faru kuma ya ƙare."



Shiru ya yi domin shi ba mutum ne mai son yawan surutu ko hayaniya ba. Yana sauraren maganganun da suke fitowa daga bakin kakan nasa wato Alhaji Muhammad Nakowa da ya kasance Asalin ɗan Garin Jos ne gaba da baya matar sa ɗaya ita ce Hajiya Sumayya sai 'yar su ɗaya tilo Aamalah da ƙaddara tayi sanadin rabuwar su shekaru masu yawa Baya sanadin karatu da ta tafi ƙasar waje....




__________________________________________

"Anty dama na dawo ne domin na rakaki zagaye Garin kamar yadda kika buƙata."


Teema ta faɗa tana kallon Samira Adila Dina Baturiyar baƙuwar tasu kuma kyakyawar gaske, kwanaki biyu da suka gabata ta shigo Garin ta sauko cikin masarautar Garin Gidan Sarkin Garin wato Muhammad Raees sarki mai adalci ga Al'ummar sa matan sa uku Hajiya Bilkisu ita ce ta farko tana da yara uku Junayd Muhammad Raees mahaifin Hamrarh da Amrarh kuma sanannen Alƙali ne mai gaskiya a Aikin sa matar sa ɗaya Miss Asfiya kyakykywar bafulatana da kyawunta ya zamo silar afkuwar ƙadarori da dama cikin Rayuwar su sanadin haka wani baƙin sirri da babu wanda ya san da shi ya mamaye Ahalin. Dr Salma ita ce ta biyu cikin yaran Hajiya Bilkisu sannan sai Alhaji Nawaz da yake zaune a garin tare da Iyalansa yaran sa maza biyu Ustaad Arkan da kuma Althaf.
Sai matar Sarki ta Biyu Hajiya Safiyya Yaranta Biyu, Canal Nubaid dake zaune a Lagos da iyalansa sai kuma Barrister Aeshah da take Auren wani ɗan kasuwa kuma ɗan kwangila bata taɓa haihuwa ba kuma suna zaune ne a birnin tarayya Abuja. Sannan sai matar Sarki ta uku Hajiya Asiya ɗa ɗaya tilo gare ta sannan ya daɗe da rasuwa shekaru masu ɗan yawa Baya.


Kamar yadda aka saba duk ƙarshen Shekara a gidan mai Martaba Sarki Muhammad Raees gaba ɗaya yaran nasa masu Aure a ƙasashen waje da wasu States ɗin gaba ɗaya kowa yake hallara da iyalan sa a gidan domin gudanar da hutun anan. To haka ma wannan ƙarshen Shekara ta kasance gaba ɗaya Yaran Sarki da Iyalansa sun kasance sun zo daga mabanbantan States da suke kuma tare da iyalan su domin gudanar da hutu anan kamar yadda aka saba sai dai wannan shekarar da ban mamaki lamarin ya kasance sanadin zuwan bazata da Samira Adila Dina ɗiya wurin Sulaiman Mutallab Raees tayi kowa ya yi mamaki da zuwanta duba da Irin abubuwan da suka faruwa a Baya. Sai dai kuma sun yi farin ciki da tazo sai dai ba tare da iyayenta tazo ba. Mahaifiyarta ta kasance Haifaffiyar ƙasar Turkey ce kuma acan suke zaune a halin yanzu. Samira tazo Nigeria ne ba tare da sanin iyayenta ba...


*WANNAN KE NAN KAƊAN DAGA CIKIN LABARIN TSANTSAN SO.!*
*WITH FULL OF...*


```_-_Life with Destiny, Struggle, Inclination, Merciless, suffering, Excruciation, and Negate Pure Love._```



____________________________________________
*Present Day....*



Kallon Teema Samira tayi da kyar ta gane maganar nata domin ba sosai takejin harshen Hausa ba. Tayi ƙoƙari sosai ma da ta iya harshen domin ba'a cikin masu magana da harshen ta taso ba.


"Oh sorry Ina ga zagayen Garin nan zamu barshi sai zuwa Gobe fa domin yau kam ina tare da 'Yan uwana musamman ma Hamrarh da Amrarh."


"Tohm Anty Allah ya kaimu Goben."


Teema ta faɗa tare da ƙoƙarin fita daga katafaren palon domin ji take ta tsargu ganin Irin kyawawan mutanen dake ciki maza da mata duka jikokin mai martaba sai dai bataji duk kyansu duka sun kai kyan wannan Baturiyar wato Samira.


"Ina zakije kuma Teema?."


Juyawa tayi ta kalle da murmushi ta ce.


"Zan koma gida ne domin Mamana tana can tana jirana Allah ya kaimu Goben in sha Allah da wuri zan zo."


Teema ta faɗa silently domin ita ɗin mace ce mara son hayaniya shiyasa ma inkiyarta yake Teema silent.

"Okay Bye ki gaida su Mama."



Samira ta faɗa tana mayar da kallon ta kan 'yan uwan nata da suke cike da Palon bayan Teema amsa sannan ta fita daga Palon sauri sauri.


_______________
*HAZEL POV.*

Dawowarta daga school ke nan a gajiye ta shiga gidan nasu na ginin bulo da ko arziƙin fenti bai samu ba. Granny ta hango zaune daga tsakiyar gidan tana faman Aikin wanke tumatur dake cikin bokiti da alama sun fara lallacewa ne take cire masu kyau daga ciki.
"Granny sannu da aiki."


"Yauwa Sannu kin dawo lafiya."


"Lafiya qalau Father bai dawo daga Church ba ke nan?."
Hazel ta tambaya tana a je littatafan karatun ta saman wani dogon table daga cikin baranda na gidan.


"Bai shigo ba tukunna ina ga ayyuka ne suka riƙe sa."


"Okay, bari na shiga ciki na watsa ruwa sannan na dawo na tayaki."


Hazel ta faɗa tana shiga cikin ɗakin ta, ta sauya kaya sannan ta fito ta ɗiba ruwa a baho ta shiga wanka lokaci ƙanƙani ta gama sannan ta shirya cikin t-shirt mai garejen hannu da wando mai faɗi baƙi na shan iska sannan ta saka hular Bat ta rufe dogon gashin kanta. Fitowa tayi ta kama ma Granny suka ci gaba tsince masu kyau daga cikin tumaturan...







_*Nainarh KD ✍️_*
_-_*Like Share Comment and vote 🙏💖 _-_*
____________________________________________






*_-_ For any and more information_-_*
*My WhatsApp Countact (08081129487 or 07085212808)_-_*


*💫TSANTSAN SO.💫*
*The Pure Love.*

*Daga Alƙalamin Nainarh KD.*

*The Writer Of Queen Of Beauty👑✍️.*


*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*


*Ep_Three.*




*Around 9:30am.*


Fitowa tayi jikinta sanye da Doguwar rigar yadi da alama Bacci ta tashi duba da yadda take jan doguwar hamma tare da miƙa.
Sauke idanunta tayi a kan mutanen Gidan da suka kasu kashi kashi tsakiyar gidan manyan su da Yaransu kowa yana gudanar da harkar gaban sa kama daga Kishiyar Baabarta wato Inna Sahura dake fama da yara maza da mata masu siyan koko da ƙosai ita tana toya ƙosan yayin da Ɗiyar ta mace Zahrah take faman zuba kokon wa masu siya, kamar kullum tana sababi ita ta gaji wa ya mutu wa ya tashi, Inna Sahura na jin ta sai dai ba tace komai ba, domin koda tayi maganar ba fasa sababin zatayi ba.

"Allah ya yi kin tashi ke nan har kin sama fitowa?."

Inna Lami dake gaban kaskon waina da take yi na siyarwa ta faɗa ba tare da ta kalle ta ba.


"E, Inna Lami na farga ya Ayyukan?."


Ta amsa ta tana zama saman kujerar tsugunno gaban kaskon wainar.
Amsa ma ta Inna Lami tayi da faɗin.


"Ayyukan Alhamdulillah kam gashi fa Allah ya yi dare gari ya waye mun ɗaura daga in da aka tsaya jiya."


Murmushi tayi kaɗan. Inna Lami ke nan babu ruwanta. Buɗe baki tayi domin sake wata maganar sai dai kasa faɗin komai tayi gaba ɗaya tsiyar jikinta na mimmiƙe wa idanunta akan ƙannin ta da suke gudanar da wasan felin felin daga can gefe na gidan da yake babba ne sosai.


"Ke! Aminatu menene kike haka ne wai shin bakyajin zafi ne kike saka yatsar ki kina jan layin felin felin?."


Da mamaki suka kalle ta gaba ɗaya har da Inna Lami sai dai ba ta ce komai ba.


Washe baki Yarinyar mai Kimanin shekaru goma sha biyu da ta kira da Aminatu tayi tana faɗin.


"Lah Anty Aaqilah Babu wani zafi fa, Humm ai na saba ma, ban sama ƙusa da zan ja layin ba ne shiyasa nake ja da ƙumbana."


Shiru tayi ba tare da ta ce komai ba. Har lokacin tsigar jikinta bai koma ya kwanta ba. Ji take kamar ita ke jan layin. Dama haka take ita.



"Allah mai iko wato wasan ma ba za'a bari yara suyi cikin walwala ba, yo zafin Mai zataji kuma abu da ta riga da ta saba, oh ni Sahura yau nake ganin iyayi ana wuri."



Bata kula ta ba kamar yadda taso domin tasan neman magana ce irin na Sahura ba'a saka da ita ba ta kwashe.


"Zahrah naji labarin Kun rabu da wannan mayen saurayin naki Sule yake ko wa, garin ya ya hakan ta kasance kuma na ganki garau ba'a asibiti ba, is it cewa fa kikayi ba zaki taɓa iya rabuwa da shi ba, idan hakan ma ta kasance a gadon asibiti zaki ƙare?."


Tayi maganar tare da gimtse dariya, dara daran idanunta akan Zahrah kamar yadda kowa da yasan irin Soyayya dake tsakanin ta da Saurayin nata Sule kuma rana tsaka ta ce sun rabu.



"Uhum menene ma zance Anty Aaqilah, ina gaya Miki wannan mutumin ɗan akuya ne bani yake so ba jiki na yakeso ni kuma makauniyar soyayya da nake masa ta hana na gane Hakan sai jiya Jikar Mai Sarki wannan Baturiyar dana baki labarin tazo garin nan kwanaki uku da suka wuce, ta ganar dani bisa hanya ta daidai ta nusar da ni jikina yakeso bani ba."


Tunda Zahrah ta fara maganar Mamanta Inna Sahura ta saki baki, kunne, hanci duka tana kallon 'Yar tata da mamaki har sai da taga takai aya sannan ta laylayo wani ashar ta kutuntumo ta ce.



"Kayyasa to da izinin uban wa kika rabu dashi sannan akan me, ba ce miki nayi ki ƙara jan shi a jiki ba kici arziƙi ki barsa a inda yake."


"Kai Inna Sahura kin jiki kuma wannan bunsurun zanso, mutumin da bashi da aiki sai yawo da 'yan iska kuma fa har bin matan banza yake yi, ni ban ma san ya aka yi na fara son shi ba, sai dai na gode Allah da na gane gaskiya na koma hanya madaidaiciya tun wuri, sannan da kike maganar naci arziƙi na bar sa a inda yake, ina arziƙin anan kina da labarin har kamashi aka taɓayi shi da su Bello sun shiga gidan Alhaji Nawaz zasuyi sata, kalar wannan kikeson 'yar ki ta aura har su haifo miki jikoki, ba ma wannan ba yanzu fa a gaban ki nake faɗin ba sona yake tsakani da Allah ba jikina yakeso kuma..."



Katseta Inna Sahura tayi cikin borin kunya da kumbar baki cike da rashin gaskiya, masu iya magana suka ce, da hauka ake naɗe tabarmar kunya aikuwar hakan ta fara.


"Ce ce ce ai naji ko to ya isa hakan tun da kun rabu shikenan ban san sake jin komai kuma haba."


Tayi maganar tana zazzare ido lokaci guda wani gudawa na taso ma ta tsaban tsoro na abin da zai je ya dawo saƙe saƙen mafita takeyi cikin ranta.



"Oho dai ke kika sani zakiyi bayani ne sai ma ya damƙe ki ki basa kuɗaɗen sa da kika dinga amsa da Sunan zaki aura masa ni ayi dai mu gani."


"Zaharatu."!!


Sahura ta ja sunan nata muryar ta na shaƙewa jin abin da take faɗa.


"Atoh gaskiya na faɗa."


Zahrah ta faɗa tana mayar da kallon ta kan Aaqilah da hayaniyar nasu ya ishe ta, ta miƙe cikin tafiyarta tana bubbuɗawa uwa Namiji ta nufa ƙofa ba tare da ta ce da kowa komai ba.


"Anty Aaqilah ina zaki tafi haka da sassafiyar nan naga ko Hijabi baki saka ba bare mayafi kefa mace ce."


Dakatawa tayi da tafiyar daidai kyauren gidan ta juya gaba ɗayan ta lokaci guda tana sauke dara daran idanunta akan ta.


"Ke! Yaushe raini ya fara shiga tsakanin mu da kikemin irin wannan tambayar, a je ni kikayi ko kin fini sanin abin da yake daidai da akasin sa ne?."


Cikin jan ido tayi maganar lokaci guda yanayin ta ya sauya ba kamar farko ba da alama an tunzuro mutanen kanta.


"Kai Anty Aaqilah ni ba haka nake nufi ba, to Allah ya baki haƙuri, dama gani nayi an yi ruwa kuma..."


Zahrah tayi Shiru baki a sake bata ƙari sa ba ganin wacca take maganar da ita ta daɗe ta ficewa abin ta daga gidan ba tare da ta kuma sauraren ta ba.


"Allah ya ƙara wai ke 'yar iya har wani wa'azi ki naji daɗi da ta gwale ki."



Naseeba Ƙanwar ta ta faɗa tana Dariyar sheƙiyanci.



"Munafuka ina Wasa dake ne?, zan ci kaza kazan ki anan wurin tohm..."


Zahrah ta laylayo uwar ashar Naseeba kuwa ta ce.

"Ba dai ni ba sai dai ke."


Nan suka fara sana'ar tasu dama sun saba sai dai ba'a haɗu ba saƙo da saƙo.







SAMIRA ADILA DINA (SAM POV)



Sakamakon Ruwan Sama da aka raba daren jiya ana yi ne yasa yau gaba ɗaya garin aka tashi da wani irin yanayi mai burgeni luf luf garin yake ga wata irin ni'imtacciyar iska wadatacciya da ta gauraye ko'ina tana kaɗawa kaɗan kaɗan yanayi na damina garin ya yi lumi lumi, mutane jifa jifa ne suke wucewa cikin yankin da suke tafiya ita da ƙawar tata da tayi a Garin duk da ta girme ma ta a shekaru nesa ba kusa ba, domin akalla ba'a kasara ba, zata iya bata shekaru huɗu zuwa Biyar.


Samira tana daga saman Keken ta ƙarama na hawa irin na training na safe, Teema tana tsaye gefan ta suna tafiya a hankali Teema tana ci gaba da bata Labarin yadda garin nasu yake.

Idanunta ya sauka akan wani dogon ƙarfe na service da ma'aikata suke faman aikin saka masa wani abu kamar drum haka dai a wurin ta da alama Service ɗin ba'a daɗe da saka shi ba, ko kuma har yanzu ana sakawan ne duba da yadda ba tsayi ya yi ba.



"S.K."



Ta furta sunan da aka rubuta jikin wani allo da aka kafe shi gefen hanya daura da ginin service ɗin.



"S.K shi ne sunan kamfanin da suka ɗauki nauyin saka mana service ɗin ba tare da sun Buƙaci komai daga garemu ba."


Teema ta faɗa tana Murmushi domin tasan tambayar da zata ma ta ke nan.


"Wow kice ba Gwamnati bane ta ɗauki nauyi kamar yadda nayi hasashe."


Teema tayi dariya jin abin da ta faɗa.


"Anty Sam ke nan badai Gwamnatin wannan lokaci da muke ciki ba da wannan zamanin da kowa kansa ya sani ba, babu ruwan kowa da kowa."


Teema ta faɗa Samira ta buɗe baki domin magana. Sai dai ba ta iya cewa komai ba. Ta zaro ido tana kallon wasu garɗa garɗan samari majiya ƙarfi sai dai raguwan sigari ne da ganin su, sun tare musu hanya suna sakin wani shu'umin Murmushi.


"Sule kaine menene yasa kuka tare mana hanya ku bamu hanya mu wuce menene haka?."


Teema tayi maganar a fusace tana kallon Sule da yaran da ya yi hayan su ta gane su gaba ɗaya yaran Bello (Shegen Kaya ) ne wato shugaban su haka Sunan sa yake sanannen Tantirin Matashin Saurayi ne mara aikin yi sai sace sace da daba, kowa cikin garin tsoron yake da mutanen sa kuma Sule yana ɗaya daga cikin mutanen nasa na hannun dama ma.


"Su waye su kin san su ne kike musu magana?.

Samira ta tambaya tana ja da baya sakamakon damƙa da ɗaya daga cikin mutanen yakai ma ta tayi baya ta sakar masa Bicycle ɗin tana zaro ido, ƙirjin ta da ya tsokale masa ido yaso damƙowa duk da kuwa ba hango su yake ba domin sanye take da Sagittarius shirt mai gajeren hannu sai skinny jeans kamar kullum ta ɗaure ƙugunta da rigar sanyi ta scorpio, ƙafar ta sanye da Boot shoe irin na ma ta kuma na training dogon gashin kanta mai launin baƙi rabi da kuma coffee Brown da tayi style ɗin in cute punytail ya leƙo daga cikin Baseball Cap da ta saka, ya sauka har gadon bayanta da alama tsayin sa ya yi yawa.


Ko kafin Teema ta bata amsar tambayar Sule da yake a fusace ya sheƙe da wata uwar dariya ta Bosawa kafin ya tamke fuskarsa lokaci guda kamar ba shi ne mai dariya lokcin ba ya ce.


"Oh really da gaske baki gane ko wane ne ni ba mutumin da kika raba da abar ƙaunarsa Zahrah a jiya."



Ajiyar zuciya ta sauke ita sai yanzu ta fara ganeshi.


"Menene yasa ka tare mu?.''


Teema ta tambaya a fusace tana ɓalla nasa harara cike da tsiwa, fuskarta ko alamun tsoron sa babu.


"Ke yarinya ki lafamin badan ke nazo nan ba dan wannan mai jan kunnen nazo wato uwar ɗakin naki saboda haka ki matsa gefe bakya ciki agenda na, idan kuma zaki shiga ga fili ga mai doki mai ya rage?."



"Sukuwa "


Teema ta faɗa sannan ta ci gaba da faɗin.


"Ku bamu hanya mu wuce tun kafin nayi muku ihun gwartaye gaba ɗaya...."

Bata kai ga ƙari sa faɗar abin da tayi niyya ba jin ta da ganin ta ya gushe na wani lokaci sakamakon wani bahagon mari da ɗaya daga cikin garɗa garɗan samarin ya zuba ma ta.



"Kan uban can Dan uban uwarki su waye gwartayen tsohuwar kika ga na danne ko wa da zaki kirani da gwarto?."


"Allah ya isa ban yafe ba mugu Azzalumi kuma Anty Samira tafi ƙarfin ku dukkan ku babu wanda ya isa ya yi ma ta wani abun kaf cikin ku mugaye."


Teema ta faɗa cikin ƙarfin hali tana dafe da kuncinta da shedan yatsun sa biyar ya bayyana saman fuskarta daidai wurin marin, domin ta fara sarewa da lamarin tasan su ciki da waje zasuyi sama da hakan ma da suka faɗa, sai dai zata tsaya iya ƙarfin ta da jajircewar ta wurin ganin basuyi ma Adila abin da suka ƙudurta ba.


Hannu ɗayan yakai a fusace zai ƙara kifa ma ta mari ta ɗayan side ɗin face ɗin nata gefen wurin da wanda suka kira da Toro ya fara marinta.


Teema ta rumshe ido tana jiran ta inda marin zai tsirga ta. Sai dai jin shiru da tayi ne tare da ihun da Samira ta kurma yasa ta buɗe idon ta a hankali. Zaro ido tayi waje ganin Buloo da ya kai ma ta mari zube a ƙasa riƙe da karyayyen hannunsa yana cije baki da rumtse ido.



"Shashasha ashe ma kai ɗin ragon banza ne daga saka maka hannu ka zube ƙasa ƙaramin ɗan iska kawai."



Aaqilah ta faɗa tana juyawa ta mayar da kallon ta kan Teema da take matsayin ƙanwarta uwa ɗaya uba kowa da nashi sannan ta mayar da kallon ta kan Samira. Sule ya yi amfani da damar juyawan da tayi ya dage iya ƙarfin sa ya raɗa ma ta sandar hannunsa irin tasu ta Fulani mai kauri da girma a kai.


Tangal tangal tayi zata zube a ƙasa tayi saurin cijewa tare da juyawa tana kallon sa cikin layi domin ko a bazata yakai ma ta dukan kuma ta baya da hakan yasa ba kaɗan ba dukan ya shigeta sai dai tsaban taurin zuciya irin nata yasa ko'a fuska taƙi nuna zafin da taji ta daure ta cije.



"Matsoracin banza, kai ta baya kake kai farmakin saboda kasan kai ragone da ka sani kayi ta gaba mana ƙidahumi."


Tayi maganar tana tangal tangal zata faɗi Samira da gaba ɗaya jikinta babu inda baya rawa tayi saurin tarota, yayin da shi kuwa Sule a fusace cikin jin haushin maganar ta ya kuma ɗa ga sandar zai buga musu gaba ɗaya.



Sai dai duk yadda yaso ya yi gaba da sandar ya kasa.
A hankali ya juya da jajayen idanun sa ya sauke su domin ganin wani isasshen ne ya riƙe masa sanda suka yi four eyes da mutumin da ba zai taɓa mantawa da shi ba a Rayuwar sa... To a kan me ma zai manta da mutumin da ya kusan fasa masa ido da naushi Kawai Ranar haɗuwar su ta farko, nan da nan jikinsa ya fara rawa kamar yadda bakinsa yake yi, so yake ya yi magana sai dai tsaban tsoro ya hanasa faɗin komai, ya mayar da kallon sa kansu Buloo da Toro yana bin su da kallon su kawo masa ɗauki sai dai tun kafin su gama fahimtar abin da yake nufi yaji wani irin bahagon naushi da aka maka masa a hanci da ya haddasa masa zubewa a wurin hancinsa yana zubar da jini na haɓo da ya yi masa, ganin abin da ya faru da shi ne yasa Buloo da Toro cika wandon su da iska ba tare da sun bari ya dawo kansu ba.



"Wato baka dandara da dukkan mutuwa da nayi maka ba wancan haɗuwar, yanzu kazo ka tare yaran mutane kuma mata saboda kai bunsuru ne kuma matsoraci, zaka basu haƙuri sannan ka ɓacemin daga gani ko kuwa sai na fasa maka ɗayan idon da duka?."


Jiki na rawa tsaban tsoro Sule ya kalle su tare da bawa Samira haƙuri bai jira amsawarta ba ya ruga a 360 har yana tuntuɓe ko waigen baya baya yi har ya ɓace da ganin su.



"Ƙaramin ɗan tururi kawai."


Ya faɗa tare da jan qwafa sannan ya juya da kallon sa garesu a karo na farko.



Taimakawa Aaqilah ta miƙe tsaye tana dafe kai Samira tayi.


"Kiyi haƙuri saboda ni ce ya yi miki hakan."



"No, ba saboda ke ba ne akwai tsamar dake tsakanina da shi dama, karki damu fa zamu jame ne zai gane ya daki Aaqilah Tantiriya hummm ƙaramin mara kunya na rantse da assamadu sai Sule ya raina kansa."


Ita dai Samira bata kuma faɗin komai ba, ta ɗa ga keken ta riƙe da hannu guda da sauri ta ƙari sa wurin sa ganin ya yi nisa zai bar wurin bayan ya ɗauki Keken sa da take kamar nata na training ta mafi nata tsada da komai.


"Am bakaji ba, na ce ba?."


"Menene ko akwai wata matsalar ne?."


Ya tambaya bayan sun dakata da tafiyar da suka fara shida Ƙanwarsa Arissa dama tare suke.


"No ba wani abu ba ne dama godiya zan maka bisa ceton Rayuwata da kayi hannun wancan mutumin. Na gode sunana Samira Adila Dina ana kira da Sam."



Ta faɗa tana miƙa masa Right hand nata alamun su gaisa ya bita da kallo yana maimaita Sunan a Ransa.


"Samira Adila Dina."


Sannan ya kalla hannun da take miƙe masa. Ganin haka yasa ta faɗin.


"Zamu iya zama abokai?."



Da ido Arissa tayi masa alama da ya bata hannun nasa su gaisa shima, domin tasan halin Yayan nata.



"Am Taufan Ali."


Ya faɗa a taƙaice. Cikin kamilalliyar Muryarsa da ɓacin rai ya dakusar da zaƙin ta.


"Wow pleasure to meet you Dear "


Ta faɗa daidai lokacin da hannunsa ya haɗe da nata domin gaisawa daidai lokacin kuma wurin gaba ɗaya ya bada wani haske na tartsarin wuta da yafi kama dana lantarki sakamakon gocewa da abu mai kama da drum da ɗin ya yi daga hannunsa ma'aikacin service ɗin, hakan ya yi silar hasken da ya haske wurin lokaci guda yayin da drum ɗin ya yo ƙasa gadan gadan ya tunkari saitin da Samira take a tsaye. Lura da hakan da Taufan ya yi ne yasa cikin zafin nama ya janyo ta da niyyar matsar da ita, ita kuwa ta taho gaba ɗaya ta rinjaye sa gaba ɗaya suka zube saman Bicycle nata da ya goje daga Hannunta.


Ita ce ta fara faɗi kafin ya biyo ta, ko kafin tayi wani motsi ta lura da drum ɗin gadan gadan kansu ya nufo, cikin zafin nama ba tare da ta san lokacin da hakan ta kasance ba, ta mirgina gefe tare da janyo sa suka fara gungure a tudu da kwari na wurin cikin taɓo. Yayin da Drum ɗin ya faɗa ƙasa gefe daban.



Wata nannauyar ajiyar zuciya gaba ɗaya suka sauke ganin wannan lamarin da ya faru.


"Ash Kai na."!


Ta faɗa tana rumshe ido da alama wurin gunguren ta bige kan ta ne.


"Menene ya sama kan naki iyee Adila?."

Ya faɗa da ɗan ƙarfi kuma a kiɗime yana Miƙewa tsaye ganin ta rufe idanunta tun bayan da ta ce kanta.


"Yayana suma fa tayi mu kaita Asibiti ina ga Kanta ne ya bugu."


Ya juya ya kalla Arissa da tayi Maganar.


"E, mu kaita can ɗin zai fi da alama buguwa tayi daga baya a nemo Familyn ta, ba an ce a gidan Sarki take ba?."



Aaqilah ta faɗa, sai dai babu wanda ya iya bata amsa. Taufan ya kin kime Samira.


Aaqilah taja tsaki lokacin da ya saka Samira a Napep da Teema ta tare. Tabi jikinta da kallo.

"Shashashan banza Dan Allah dubi yadda ya saka duk na ɓata kayana?."


Ta kuma jan tsaki.



"Sai dai ba komai bashi yaci zamu jame ne a gaban Sule ka kuka da kanka.''


Ta faɗa tana ciccijewa ita dole ranta ya ɓaci sannan ta bar wurin domin sun daɗe da ɓacewa ganinta. Sai dai kyakyawar fuskarsa Bata Dena ma ta gizo a ido ba haka ma kamilalliyar Muryarsa mai cike da nutsuwa cikinta daɗin sauraro kamar ana busa sarewa a ganinta. Tun da take a Garin wannan shi ne karon ta na farko da ta haɗu da shi duk da tana jin labarin sa sosai bakin Mutanen garin Especially 'yan matan da dayawa suka

Please Login or Register in order to submit comment